Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 2

Sponsored Links

 

 

 

  Asalamu Alaikum ni
zainab ina gargadin masu mayar min da novel audio don Allah su daina saboda
Allah su daina yi bada sanina ba don girman Allah da Annabin rahama.

    Banda anty Safiya
huguma data nemi izzinina ba wanda nabawa izzinin mayar min da ko wani novel
audiovisual amma sai mutane su dinga kirana waina basu lamban mai karanta min
novel,  why tsoron Allah yayi karanci a
wanan zamani haka kan abin banza mutum yaja wa kanshi nauyin siradi.

  Wanan din dana fara
na sayarwa S Zaria HAUSA TV idan wata ta karanta audiovisual din novel din nan,
 hukumace a tsakanin su Allah ya gani na
fitar maki da hakkin hakan

    Yau tun wayewar
gari yake tsaye suna gyaran gidan malam Tanimu ta dabaran daura leda sai katako
daga baya saidai dole na dan lokacine kafin su samu matsunguni har damana ya
wuce.

   Wanan ya jawo mashi
makara zuwa makaranta duk da hankalinshi na school din ga kuma madam Rukkaiya
da yake danyiwa aiki ya samu na sayan takardu da abinda zaici yasan yau zasu
kwashi yan kallo tsakanin su shida ita  .

   Don taki jinin
makara zuwa wurin aiki mace ce da duk kokarinka rana daya zaka danyi laifi sai
ta saba maka kamar baka taba kyautata mata ba.

    Yasan ranan zasu
hadu da ita sosai saidai dole ya taimakawa bayin Allah nan da yanzun suke
bukatan taimakon al, umma inda Allah ya taimakeshi jama,a sun dan fito an taru
an taimakawa dattijon aikin yayi sauri  .

   Haka yayi wanka a
gagauce duk da wankan bada sabulu bane wankane irin na i dont care na adai
watsa ruwa jiki yaji iska yafito yaudauki riganshi dake sagale ya saka.

   Sallama yaje yiwa
Dije a bakin murhun su na kasa ya sameta duk da bata da issasan lafiya amma
haka take zama bakin murhun ta  girka
masu dan abinda zasuci a cikin su wata rana kuma dan abinda ya samo acan suke
dan matsawa suci.

    Wanda saidai ya
tsankwara yaci kadan yabarwa kakan nasa saura yace da ita ya koshi don kawai
kada ta kwana da yunwa shi ya hakkura.

   Yanzun ma kokon
tsakin masaran data dade ajiye ta binciko a cikin kayan ta shine ta hada wuta
take dama masu su karya.

   Saidai ganin ya
makara ba don bazai iya sha badin yasa ya bata hakkuri don ya makara iya makara
don haka zai wuce zuwa makarantan .

   Hakkuri ya bata a
inda take zaune tana faman hura wuta a wahalce yace Dije kiyi hakkuri na makara
yau sosai don aikin nan dana tsaya kamawa malam Tanimu.

   Hakan yana dakyau
gaskiya taimaki makwancin ka ko wani musulmi dan uwanka Allah ya taimaka maka
ta hanyar dabaka taba zato ba.

    Haka rayuwa take
Amadi yau gashi duk da sherin dasu Tanimu ke bin mu dashi a unguwar nan kaine
tsaye akan rayuwan su duk masayon nasa da yake tarawa nan waje suyi gulmanka
sunki tsaya mashi yau.

  Dije ni zan tafi
Allah yabamu alheri don a katse zancen kada ta kara makar dashi tace to Amadi
alherin Allah ya bikaka duk inda kake Amadi dakai da sauran diyan musulmai na
duniya.

   Ya amsa da Amin
lokacin daya fara tafiya ya fita yana lumshe ido tare da tunanen yadda zasu
kwashe da madam dinshi wace yake hakkuri da jure wahalan irin cin fuska da zama
da ita tun kan yakai hakan .

    Duk wanda yasan
shi yasan shi a yaron madam happiness sunan shagon nasu ke nan da kowa ya sani
tun yana secondary yake zuwa kama mata aiki.

    Yana gamawa ya dan
dakata da karatun na dan lokaci saboda halin rayuwa da taimakon Allah ya koma
karatun shi bai bar kuma aiki a karkashin madam din ba.

   Da wanan din har
yau yana 300 level yana hakkuri da kokari wurin turzawa yaga ya karbi kwalinshi
da hannun shi.

 

    Tun a hanya nake
kallon irin barnan da ruwa yayiwa gidajen da titituna yadda ruwa yai barna a
garin ga mutane sai faman gyare gyaren sukewa gidajen su da wurin sana,an su
duk inda kabi.

    Bana tuki da
garaje a dan kwanan da zan dauka ya sadani da titin makarantan namu akwai dan
daji a wurin don wurin bai faye mutane dayawa ba sosai .

    Wani irin burki
naja da sauri don ganin ina kokarin kade wani tsoho ko tsuhuwace ban sani ba ko
mace ko namiji don fuskan shi a rufe yake.

   Na daija burki da
sauri na fito daga motan gabana yana faduwa nanufi maishi hankalina a tashe ina
isa na karasa wurin ina sannu baba baka daiji ciwo ba ko baba ?

  Don Allah kayi
hakkuri baba bansan da mutum bane a wurin na karyo kwanan a lokacin muje na
tsallaka dakai kafin wata motar tazo.

    Har lokacin bai
dago ba saidai duk kokarin son inga fuskan maishi bai bada daman hakan gareni
ba lokacin gashi kuma hankalina a tashe yake har lokacin.

   Amma saj naci gaba
da fadin Ko kuma muje na saukeka inda zaka yanzun din na fada a dan rude don
dai na bashi hakkuri amma har lokacin maishi bai dago kai ya kalleni ba yana
dai duke da kanshi.

   Kamar yadda na
sameshi gashi ya rufu da wani irin gwado ko bargo irin na mutanen da mai ruwan
duhu irin damuke gani a cikin film mai
nauyi a jikin shi.

   Sai wani sanda mai
gwafa mai kauri sosai daya rike a hannushi yana dogarawa gashi dauke da wani
irin buhu dake wani kara kamar ya dauko karafuna a cikin buhun.

   Hannu nakai da
zuman kamashi dasauri ya dago kai ya kalleni wani irin yarrrr naji lokaci guda
a dukan jikina ya dauki rawa kaina ya wani irin sara a lokacin.

   Don ganin fuskan
maishi da nayi ban iya tantace mace ce a gabana ko namiji ba a lokacin ga fari
kamar balarabe ga suma mai laushi duk da amurde suke.

  Kai ya fara kada min
yana fadin barshi ai na kawo inda zani nan kusa na gode a cikin wani irin murya
mai kamar balarabe yana hausa.

    Nagode baba na
kara fada cikin karfin hali don Allah ka dinga kula da titi kada masu gudu suzo
watarana su kadeka cikin rashin sani gashi wanan wurin mugun wurine sosai ka
dinga kula kaji kakana.

   Don muna da bukatan
irin ku a duniya don ku duniya ke zaune kalau muna son ku nima inada kaka a
gida ta tsufa kamar ka .

    Na fada  a cikin dan zolaya ina tura hannu a cikin
jakkata na zaro dubu uku daga cikin kudin da Abba ya ban wanda ban taba ba na
mika mai kallon kudin yayi saiya girgiza kai akaro na biyu ya dan dago kanshi
ya dubeni sai yayi saurin sada kanshi kasa.

     Yana fadin bar
kudin ki yarinya nagode kema ki dinga kula da duk lamarinki adduan ki dana
mahaifiyarki suna amfani a gareki ko yaushe.

    Baba don Allah ka
karba ko zan samu tubarrakin ka gun jerabawa zani yanzu ina bukatan adduan ka
baba na fada cikin dan marairaicewa.  

   Kai ya jijiga min
yana fadin hakane to Allah yabada sa,a ya tsaya maki ga duk lamuran ki ya fada
ya miko min hannu ya karbi kudin na dan rusuna ina mika mai tare da fadin
nagode baba.

    Hannun mu yadan
hadu da nasa a wurin karban kudin wani irin shock naji lokaci guda har saida
jikina ya kadu na juya zan wuce muryan nan dai da ban iya banbantawa a lokacin
namijine ko mace nake magana dashi a lokacin naji yana fadin .

  Ubangiji ya tsareki
ya kare rayuwan ki dake cikin  sarkarkiya
bayan wuya dadi na tafe maki idan kin daure na dan lokacine komai zai tafi.

   Ina jin shi saidai
Allah bai ban ikon in juyo ba nake fadin amin a raina na shiga mota lokacin na
dago kai na kara kallon inda na bar tsohon tsaye sai babu kowa a wurin naduba
ko zan ga inda yabi sai banga kowa a gabana ba .

   Waige waige nafara
ko zan  hango inda yashiga ko yabi saidai
babu kowa a wurin kamar ma ban taba tsayawa da wani hallita ba wurin haka naja
mota zuwa school na faka saidai nayi rashin sa,a don babu kowa a department din
namu gashi ina son yin karatu.

   Don haka nasa kai
na shiga saidai ina fara tafiya naji kamar mutum a bayana yana bina haka baisa
na juya ba don na dauka girman wurin yasa nake jin sautin kafana da nake
takawa.

    Bissimillah nayi
wanda hakan kusan dabi,an yan gidan mune haka mun karatu a fanin addini don
dole yaron gidan mu yai karatu addini yasa
littafai yadda ya dace kowa yasan zamfarawa yadda suke ga addini ga kuma
kaucewa Allah wurin marasa imani don ba duka aka zama daya ba wana haka yake ko
wani gari dama.

    Da daya daya ajin
ya fara cika da mutane kafin wani lokaci ko ina na ajin yacika da jama, a karfe
tara mun zauna jerabawa ayadda nake ganin saukin test din yasa nayi na farkon
fitowa daga Hall din.

    Direct dakin sayar
da abinci na nufa don zuwa lokacin na fara jin yunwa a cikina sai na tuna banci
komai ba da zan fito gashi har sha biyu da rabi na rana.

    Tunda na tunkari
wajen na danga taron jama,a haka na daure na karasa daga nisa nake jin muryan
matar mai sayar da abincin tana fada tare da nuna wani saurayi dake gefenta
tsaye cikin mutane.

    Gaskiya ba zan iya
ba ace sai yanzu zakazo da sunan yi mun shara da wanke wanke kuma in ka gama na
baka abinci taimakon kafa nakeyi ka sani don ka samu kayi karatun nan kaima.

   Ina karasowa dan
kallonsu nayi ina jin matar na fadin kaci arzikin wayan da wallahi yau din nan
zan sallameka don na gaji da wanan uzurin naka kuma ka sani yau bazan baka
abinci ba a wurin nan .

  Nikan nasakai na
shige cikin wurin na samu wani table daba kowa na zauna saiga wata tazo tana
tambayana hjy me za, a kawo makine ?

    Five alibe drink’s
with donut nafada ina dago kai a daidai lokacin da wanan matashin suke shigowa
da matar mai shago sai fada take ta zabga mashi .

    Bring two plate of
rice with ganishing na fada sai ta juyo nace yes ta juya ta tafi dan dakin da
suke zuba abincin bata jima ba ta dawo dauke da abincin cikin tire ta nufoni
tun kan ta karaso inda nake na mike tsaye ina fadin nawane kudin ki ?

    Sai ta kalleni
kafin tace dubu biyu da dari biyar har drinks din nace OK ina tura hannu a
jakkata naciro kudi zaikai dubu biyar na mika mata tare da fadin ki kaiwa
wancan sauran canjin ya rike ta juya inda nake nuna mata din tace wai Ahmed zan
bawa nace eh ta karba na dauki jakkana ina tura wayana a daidai lokacin data
mika mai tana nuna mai inda nake lokacin na ina kokarin fita daga shagon.

    Department din mu
na koma na zauna ban dade da zama ba ajin ya fara cika sai hiran test din da
mukayi akeyi a class din na saka airpiece dina a kunne.

    Jin an dafani yasa
na dago kai naga ko waye saidai banga kowa a bayana ba a lokacin yasa na duka
naci gaba da bin face book din da nakeyi wanda ya dauke min hankali a wurin.

     Kaina ne ya fara
ciwo a lokacin yasa na dakatar da abinda nakeyi ko zanji ya dan fada min sai
dai kamar ana karamin hakan ban tsaya har lokacin tashi ba na fito na nufi inda
motane yake ajiye.

 

 

Leave a Reply

Back to top button