Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 19

Sponsored Links

Chapter 19

Bayan fitar da maman fadila daga cikin gidan mu da makwabta sukai wasu daga ciki sun shigo har ɗaki suna bawa Anna hakuri akan abunda maman fadilan taxo tamana,yayin da suke kecewa da Anna kawai taraba Aisha da fadilan dan a zauna lafiya tunda ga hanya da yarinyarta ta ɗauko wasu na raɗe raɗen karuwanci ta fara tunda kullum ranan duniya da kalan motar da zata kawota gida gudun bacin suna Aisha kirabu da fadila Allah yasa hakan shine alheri cewar maman kausar da Amin aka amsa baki ɗaya.
Nide banda hawaye ba abunda nakiyi bayan duka sun kama gabansu Anna ta kalleni tace”kukan ya isa haka mana Aisha ai sai kanki yayi ciwo.

Faɗawa jikinta nayi nasaki sabon kuka da karfin gaske cikin kuka nasoma cewa”dan Allah anna kiyi hakuri wallahi ba….shiiiii tace tana mai ɗaura yatsanta saman bakin ta.

“Banason dogon surutu nasanki Aisha nasan halinki a kullum ina alfari da kasancewar ki ɗiya gareni mai tsayuwa kan gaskiya koda hakan zesa aga baƙinki,kwanta kiyi baccin ki tace dani ba tare da ta bani wata daman nayi magana ba.

Ahmad duk abun duniya ya taru yamasa yawa kwakwalwansa ya tsaya cak baya aiki,yama rasa wani irin tunani zeyi ta ina zai fara?
Khalid da tun dazu yake tsaya yana masa magana jinsa shiru yasa shi matsowa kusa dashi ya dafa kafaɗasa yace”komai yayi zafi maganin sa Allah kamata ka sauƙakawa kanka yawan tunani amma mutum ya zauna sai tunani shin auren haɗi kanka farau ko kanka karau sai kace ba namiji ba ka zauna kana ɓatawa kanka lokaci da tunane tunanen banza wallahi da nine kai ko,hmmm wallahi ko sau daya baxan ɓata lokaci na wajen tunani ba kawai biyayya zanyi bayan aure da ɗan watanni nima nabijiro musu da nawa zaɓin kaga shike nan magana taƙare kalass..yakare maganan yana dan ware hannun sa.

Hmmm Ahmad ya sauke nannausan ajiyar zuciya yana gyara zaman sa ya fuskanci khalid sosai yace”bazaka gane bane ɗan uwa”idan ka fahintar dani mai zai hanani ganewa shima ya faɗa masa.
Nan Ahmad ya kwashe komai dake faruwa yasanar da shi ta ɗaura dacewa kasan basma kasan halinta na rashin ganin kan kowa da gashi gata da son wulakanta na ƙasa da ita ga rashi iya komai ni fa bana tunanin ko dafa tea wannan ta iya sannan wani karin haushi wai ni zan tare gidan su koda me suke taƙama kuma Alhaji ya biye musu.

“Gaskiya abokiya da aiki a gaban mu yanzu de ba wannan ba nifa ina ganin irinsu yarinyar nan Aisha zaka samu idan kasami irinta gogawa zasuyi da basma duk tsiyarta dan da alama bata da tsoro,
kallon baka da hankali Ahmad ɗin yamasa ƴar dariya khalid yayi ya cigaba da cewa wallahi Im serious kai bakaga yanda ranan ta shararawa wancan guy ɗin mari ba,
Kuma bata burgeka ba ranan?

Kadeyi tunani idan kuma bata ma ba nide gaskiya yarinyar tamun tun ranan da nafara ganin ta naji wani abu ya ɗarsu a raina gami da ita kawai zan fara yaɗa munufata kafin wannan shamsu yayi mun tsakiyar da ba ruwa”zubar da aji cewar Ahmad yana jan gajeran tsuka”oho de kwara na xubar da ajin dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa wani ajine ga namiji dama duk ajin ka duk jiji da kanka wataran sai karamar yarinya ta zautar dakai tasaka kuka a bed jifansa da pillow Ahmad yayi ya cafke yana dariya shima din dariyar yayi da cewa wallahi khalid baka da kunya.

“Basma basma basma
Kaman bata jin kira haka ta sauko down stairs ko sleepin dress dake jikin ta bata cire ba,sai wani yatsune fuska take da alama baccin be gama isarta ba”Daddy gani irin wannan kira haka sai kace nayi lefi,ta kare maganan cike da rashin tarbiya
Washe bakin sa yayi cike da so da kaunar ɗiyar tashi dan ko kaɗan shi bemaji haushin rashin amsa mishi kiran da yamata batayi ba yace”ki shirya anjima Ahmad ze zo ku sasanta kanku dan mun rigada mun gama komai da babansa ku kawai muke jira ku sasanta sai musha biki….wani irin tsalle tayi ta rungumi daddyn nata tace”luve you daddy”love you too dear maza jeki ki shirya tarɓansa yace da ita da gudu tayi hanyan kitchen tana kwalawa lantana kira dariya hajia mariya tayi tace”oh yaran yanzu ba kunya dubi yanda take murna da zuwan saurayi shima Alh sunisu dariya yayi irin tasu ta manya yace”barta tayi abunta.
“Ai ko yanzu ban riketa ba.
“Ina da buri mai yawa akan auren nan nasu mariya ki nutsar da ɗiyarki karta kwafsa mana idan komai yayu ina burin mallakan cibiyar nan ta Al-hakk baki ɗayansa yazama mallakina dan haka dole sai mun tashi tsayin daka mun kuma haɗa karfi da karfe wajen ai watar da wannan manufa tamu.

“A hayyeh ayyiriririi kace duniya sabu zamu maganan jiji dakan hajia ma’arufa dan daga lokacin da ɗanta yayarda ya tare nan gidan daga sannan kace sunan ta sorry ba ita ba ɗa.
Dariya suka kwashe baki ɗaya nan suka zauna sukai ta tsara yanda komai ze gudana.

Daddy ishaq
Zaune yake bayan ya gama nafilfilun sa kaman de yanda yasaba koda yaushe,dan bashi da abokin hira sai istigfari da hailala da yake kullum dakuma addu’an Allah ya aramasa tsawun rai yaga faɗuwar su Alh sunusi da ire iren sa,
A ƙiyasi yau shekara takwas kenan yana tsare kar kashin ƙuntatawa na alh sunusi sannan a ƴan kwanakin nan kullum ya kwanta bacci yana yawan mafarkin Aisha na mawuyacin hali tun randa yaji amon muryoyi suna kiran wannan sunan a filli ya furta”sunusi karshenka yakusa dan wannan hadin aure da zakayi tsakanin ƴarka da ɗan alh badamasi wannan shine kuskure mafi girma da zaka aikata sannan sadaukar da jinin aisha a ƙungiyarku wannan yana nufin tarwatse warku yazo dariya ya ƙyalkyale dashi kaman yana tare da wani ya cigaba da cewa narantse da sarkin da ya busan numfashi bazan fasa kai ƙararka gareshi ba har sai naga durƙushe warka.

Leave a Reply

Back to top button