Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 8

Sponsored Links

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

Bisimillahirrahmanirrahim.
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*

*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*meson karanta paid book ɗina tsawon shekara guda batare daya sake siyaba to 1500 ne register dani,meso seta tuntuɓeni a 07044600044*

*8*

“Prince mafitace fa wannan me ɓillewa akanme zakace bazaka yarda ba kode kashiryawa rabuwa danine?”cewar fadila cikin damuwa….

“look fadila banasone muzo muyi abunda agaba zamuyi danasani nidake baki ɗaya,akan me?”labeeb ya faɗi cikin damuwa.

Kuka fadila tasa masa me tsuma zuciya tana faɗin”hajiya nasan dole zatasaka kayi aure, inko matar da zaka aura daga hajiya take ay na kaɗe,dan Allah ka sakeni yanzu kamin zuwan lokacin”

A gigice ya kamota ya haɗeta da jikinshi yace”kina haukane fadila in sake ki in zauna dawa ni kuma,kinga faɗamin ya kikeso inyi zanyi amma dan Allah karki kuma cewa in sakeki.”ya faɗi kamar zeyi kuka.

Share hawayenta tayi tace,”ni nasamo maka wacce zaka aura,nanda sati guda,kuma nace musu mu zamuyi komai, kuma sun amince da sharaɗina dan haka kai shiryawa zakayi kaje garin nasu yarinyar kaganta”

“hmmm fadila kenan to ni meye na wani zuwa ganinta,ay zan auretane badan ina sonta ba sedan biyan buƙatarki dan haka no need inje”ya faɗi fuska ba faraa.

“kadaure de kaje prince don Allah, ka yarda dani ba wata matsala”ta faɗi cikin sigar rarrashi.

Shuru yayi yana nazari kamin yace “to shikenan kisa rana”

Ayko rungumeshi tayi tana murna dan taji daɗin yardar da yayi,duk da tasan hakan nada nasaba da maganin matan ƴar chadi.

*******;

“Hajiya aurene dama zan ƙara nan da sati guda, da ƙanwar abokina,shine nakeso kisamin albarka,”cewar labeeb lokacin daya isa ga hajiya.

Faraace ta bayyana a fuskar hajiya,dan taji daɗin maganar gyara zamanta tayi tace”amma labeeb aure da wuri haka ?”

“Hajiya so nake ajarraba agani kan matsalar rashin haihuwarnan shine abokina yaban ƙanwarsa”ya faɗi a ladabce.

“To masha Allahu abu yayi kyau sosai kuma ina murna Allah yayi albarka zan sanar da kawunku dan ashirya zuwa ɗaurin auren”

“Yauwa hajiya base anyi gayyata sosai va,kawai in su kawun ma sukaje ya wadatar tunda abune na gaggawa ba wani shiri akayiba.”

“Hakane labeeb Allah ya sanya alkhairi,bazan tambayeka tarbiyyartaba dan yanzu tarbiyyar da zaka gani avwaje daban da wacce zaka gani aciki,dan haka Allah ya tabbatar da alkhairi.”

“Amin hajiyata nagode da goyon bayanki”

******

“Kishirya da kyau farida yaune da mijin naki zezo kuga juna dan Allah ki kama kanki kar yaga wani abun dabe masa ba”cewar ƴar chadi.

“mama ki kwantar da hankalinki in har mijinane zan aureshi koda gyara ko babu dan haka kidena wahalar da kanki dan Allah.”cewar farida.

“Farida wannan babban kifine fa inaso kisan hakan banaso ya kuɓuce mana”

Murmushi farida tayi kawai dan ta rasa mezata cewa mahaifiyartata.

Da misalin ƙarfe biyu Labeeb ya shigo garin na kano,inda ya isa ƙofar gidan na ƴar chadi bisa jagorancin kwatancan da take masa a waya.

Farida cikin natsuwa da shigarta ta kamala ta isa bakin motar ta labeeb domin masa jagoranci zuwa cikin sitroom ɗin gidan nasu.

.Tunda ta taho hankalin labeeb yayi kanta,sosai ta tafi da imaninsa dan farida ba ƙarya mace ce ta nunawa saa.

Koda ta iso bakin motar sallama tai masa fuskarta ɗauke da murmushi,shima murmushin ya sakar mata.
“ka fito mu shiga daga cikin gida”ta faɗi a ɗan kunyace.

Buɗe masa ƙofar tayi ya fito tace “barka da zuwa birnin dabo”tana ɗan rusunawa.

Murmushi yayi yace”koda me nazo anfini ko?”yayi maganar yana ɗaga gira.

Rufe fuskarta tayi tana dariya tai gaba ya bita abaya bayan ya rufe motar.

A sit room tai masa masauki sannan taje ta kawo masa abincin data dafa masa da abun sha me sanyi.

Yana ɗan janta da hira ya ci abincin yasha kunun ayan daya masa daɗi sosai.

Bayan ya kammalane ya dubeta yace”malama farida right?”

Murmushi tayi ta gyaɗa masa kai,cigaba yayi da cewa.

“Sunana labeeb daga kaduna,nazo neman aurankine bisa amincewarki inkin amince nan da sati guda zaayi komai kuma banason kuzo da komai gidana zan miki”

“Sati guda beyi wuri ba kuwa?”cewar farida asanyaye.

“beyi wuriba malama farida.”

“To ay bamu fahimci juna ba naga”

“inmukayi auran semu fahimta”ya faɗi yana dariya.

Shuru tayi kamin tace”to Allah shige mana gaba”

Sosai yaji daɗin hakan,sun jima tare kamin tai masa iso gurin mamanta suka gaisa tashin farko dubu ɗari biyar ya bata nata sannan ya basu milyan guda asiya mata lefe.

Se gab da magriba ya baro kano.danshi zubi da tsarin farida ya masa har zuciyarshi tuni ya mance da batun wani auran kwangila.

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button