Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 2

Sponsored Links

Chapter 2

__fuuu Alhaji badamasi yabar musu falon cike da ɓacin rai,sauke numfashi sukai kusan a tare shafa kansa hajia mardiya tasoyi shiko yayi luf ya ɗaura kansa saman cinyarta kaman wani karamin yaro,shagwaɓe fuska yayi yace.

“Mama wai meyasa Alhajin nan naki bayason farin cikina ne sam?”kul kakuma cewa haka Ahmad yaza’ayi mutum ya haifi ɗan sa amma yace bayason farin cikin sa.

Kawai de ina ganin yanason zumunci tsakanin sa da abokin nasa ya ɗaure ne wajen kulla auratayya tsakanin ku”hmmm yace kawai yana sake nitsuwa jikin mamar tashi dan yasan ita kanta hakuri kawai take da halin mijin nata kasancewar ta mace mai hakuri amma ba dan tanajin daɗin zama dashi bane ba.

Aisha
ina shiga cikin gidan mu naci karo da kayan wanki dila guda wai na wankau cike da taƙaicin wacce takawo wankin nayi sallama ciki ciki amsamun anna tayi ƴan ƙannena suka tahu da gudu suka rungumeni suna mun oyoyo.

Shafa kansu nashigayi nace”ya bakuyi shirin zuwa islamiyar ba?kallo na sukai kaman zasuyi kuka murmushi nasakar musu dan nasan matsalan nasu yunwa sukeji kuma sunyi ƙokarima dan tun kunun kokon hansin damuka tattaɓa da safe ba abunda sukaci ko kuma ince ba abunda mukaci.

Anna ce ta katseni da cewa”Aisha matso mana kon tsaya da bakin ƙofa matsowa nayi ina kallon tulin kayan wanki dake ajiye gabanta nace”waƴan nan kayan fa?nunomun matashiyar yarinya dake tsaye tayi tace”hajia mariya ce ta aiko da kayanta takuma ce tana bukata gobe.

Juyowa nayi na kalli yarinyar dake tsaye sai yatsine take ita ala dole ƙyanƙyami mai da kallona nayi ina bin madaidaicin gidan namu da kallo nide banga wani abun ƙazanta ba,dan gidan namu a share yake tass na maida dubana gareta nace”ƴan mata ɗauki kayan kimai dasu inda suka fito ki faɗa mata mai wanki tadena dan bazamu rinƙa ɓata lokacin mu da karfin ga waƴanda basusan darajan mutane ba.

Ina kaiwa nan najuya na shiga ɗan madaidaicin kitchen ɗinmu dan jiƙa mana garin kwaki da nasayo mana a shagon mati,bansan yanda sukai ba kwai nafito na tadda hajia mariya tana zazzaga masifa wa anna ta cikin waya,wai har cewa take ita ba faƙiriya bace wallahi tafi karfin mumata wulakanci.

Murmushi nayi mai faɗi nace”hajia duk faƙirancinmu ai bamuje gidanki maula ba,ki adana fushinki zai miki amfani wani lokaci ba bayinkin bane mu balle mumiki aiki bazaki biyamu hakkinmu ba.

Sannan kitsaya kina wasu maganganu ai ko a addinance amfiso mutum idan yamaka aiki tunkafin gumin sa yabushe kaɗauki hakkinsa kabasa.

“Nikike faɗama magana Aisha dama ashe fitsararriyace ke bansani ina taimakonku nayi danake aiko muku da wankin ai biya nake ba kyauta kuke mun ba.

“Idan wannan shine biya riƙe abunki bama buƙata mu da Allah muka dogara ba dawani ba”au dan banzan dubunku biyar dake hannuna kike neman rainani kinsan koni wacece?cike da ƙosawa da yawan maganan ga yunwa na damuna har wani dishi dishi nake kallon kunsan idan mutum yajin ƴar gusau a wuya yake dan haka kana taɓashi kaɗan ze soma zazzagama maka masifa to nima hakance ta faru dani dan haka a ƙufule nace da ita”kewaye kewaye?be shafeni ba koma keɗin wacece kawai abunda nasani wankine anna bazata sake miki ba.

Sannan kina kiran banzan dubu biyar ai saboda sanin mahimmancin sa yasa kika riƙe mai yasa baki bada kin huta ba,sai wani kurin kike kina kiran kewacece mtsss naja gajren tsaki.

Iya hasala hajia mariya ta hasala dan haka cikin ɗaga murya tafara zazzaga masifa kaman ta ari baki ji take kaman ta jawoni ta cikin wayan takifkifamun mari,sai da tayi mai isanta nide bansake anƙata ba.

Sai hakuri da Anna ke bata nikan tasa ƴan ƙannena nayi gaba muka soma shan garin kwakinmu hankali kwance,can aka kashe kiran yarinyar da naji hajia mariya takira da Basma ta bude pouse ɗin dake hannun ta taciro ƴan dubu dubu guda biyar ta miƙama Anna tana wani yatsene fuska kaman taga kashi”gatsiyar ku nan daidai zata juya tace da Anna.

Saurin amsa nayi nace” godiya muke ɗiyar ƙaruna umma tagaida ashsha,juyawa tayi tasoma tafiya harta kusa kaiwa ƙofa sannan hankalina ya kai wajen kayan wankin da tabar mana nace”amm Basma kike kowa?kinbar kayan fa?kobakiji yanda mukayi da hajiyar taki bane ai daga yanzu mundena wanki basai anjima ko gobe ba.

“Sai ki biyoni dashi tafaɗa a gadarance,ƴar dariya nayi rin mai ƙulawar nan gawanda a kaima nace”ayyar ƴar gidan ƙaruna saide ba nice nashigo da su ba,dan haka sai ki zo kiɗauki tsiyarki kice da ita matsiyatan da tace sunce bazasu sake aikin wahala ba.

“Haba Aisha nifa banason irin wannan hali naki na kafewa akan abu guda da rashin hakuri haba Aisha sai kuma ta sassauta murya tace bana son haka a irin haka na rasa mahaifinku nazo ina rayuwa kaman wacce tayi lefin kissa nake ɓoye kaina daku baki ɗaya duk saboda ku….

Kuka sosai Anna take wanda yasa muma muka tasa namu nakuma yi danasanin biyewa zuciyata danayi dan gani nake kaman nice nasa Anna kuka jiki a sanyaye nace”dan Allah Anna kiyi hakuri idan har amsan wanki shine zai faranta miki rai bara nace su maido,nafaɗa ina ƙoƙarin miƙewa tsaye sauri riƙo hannun tayi tace.

“bawai ina kukane saboda abunda kika faɗawa hajiya mariya ba,a’a kawai inayine saboda tunawa da nayi da mahaifinku a rayuwa Aisha kizama mai hakuri dakuma kawar da kai akan komai banason rashin hakuri Aisha abunda hakuri be baki ba rashin sa baxe baki ba,takare magananta tana mai rungumo dukkan mu jikin ta inasonku ƴayana sanyin idanuna”muma munasonki Anna uwa ɗaya tamkar ta dubu a garemu.

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Na
Zahra Ali Abdullahi

Bismillahir rahmanir rahim.

Leave a Reply

Back to top button