Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 4

Sponsored Links

Chapter 4

A tare suka shigo falo mama na zaune tana kallon labarai a tashar aljazeera yayinda auta marwan ke zaune daga gefe yana duba littafinsa.

Murmushi mama ta sakarmusu da kiran”masha Allah fatan nasara”amin khalid ya amsa shiko oga Ahmad sharewa yayi dayin gaba.

Assalamu alaikum yafaɗa sanda na iso bakin kofan sanin mahimmancin sallama yasa na amsa da
“Wa’alaikum salam.
Shirune ya ɗan ɗaukemu ganin bashi ba da abun faɗi yasani katse shirun da cewa malam hafiz ina da abunyi zan iya komawa?

“Am am wato malama Aisha am naga baki koma ba shisa nabiyo bayanki nagani de ko lafiya?kallon sa nayi a mamakance araina nace kaji rainin wayyo wato shi abunda yamun be ɗauka abinkin komai ba kenan.

Amma a zahiri murmushi nayi nace”in badan abunka ba malam hafiz ai dama ni nakai kaina shagon naka neman alfarma kuma baka koreni ba kamun alfarma harma nasamu nayi aiki da kai kakuma biya ai sai godiya.

Saurin katseni yayi da cewa”dan Allah Aisha kiyi hakuri nasan ban kyauta miki ba,a lokacin amma dan Allah kibani wata daman wallahi zan biyaki hakkinki kaman yanda kika buƙata tashin biya kokuma adadin ɗinki da kikayi a rana adadin biyanki duk yanda kikace haka za’ayi ina bukatar ki a shagon mu.

“Nagode malam hafiz saide kasani ba abunda ze sake kaini shagon naka kaman yanda kaimun kora da hali to nima yanzu dan biyan bukatan kanka da kanka bani zuwa,dan nasan da biyu kabiyo sawuna ba haka kawai kazo ba, idan waƴanda nama dinki susukace ni suke bukata namusu ɗiki sai kakoma kasan yanda zakayi dasu da mutuncina da darajata banza ƙaskantar dakai gawani bawa yanemi takani ba,Allah kaɗai shine wanda ya cancanci haka kuma yasan dani baze taɓar dani ba.

Sautari mutane sukan so wulakanta mutane ƴan uwansu batare dasanin ƙimansu da darajar suba,kuma basusan baiwa da Allah yama bayinsa ba,da zamu zauna mu mutane mu nitsu da wallahi zamu karu da baiwarda Allah yayima wasu daga cikin bayin sa,wulakanci bashi kyau ka wulakanta dan uwanka amma bakasan abunda shi wanda ka wulakanta ze zama nan gababa na barka lafiya nakuma gode da ziyara da haka nayi wuce wata gida nabarshi tsaye kaman wani dogari.

“Wai nikan Ahmad bazamu danyi mata shoppin ba haka zamu hannu rabbana?ɗan tsuka yayi yana kauda kansa gefe yace”haka naga daman zuwa ko kana da jaa akaine?murmushi yayi yana cewa”wane ni ni na isa jada ango to be,mtsss tsuka yayi mai faɗi yace”kanka akeji mutum sai shegen surutu wallahi idan bakai ma mutane shiru ba yanzun nan sai mukuma,daga haka shiru yaɗauke su Ahmad na driven shikuma khalid yakai hannun sa gefen set kugera abunda ya taɓone yaja hankalin sa saurin ciro abun yayi abun hannune mata irin ta duwatsu ɗagawa yayi yana karewa abun kallo.

Shide a iya sanin sa yasan Ahmad baya hulɗa da mata to mai yakawo wannan abun nan?”wannan abun ɗan wai gowa kaɗan ahmad yayi ganin abun ke hannun khalid yasa shi ɗan cizan lips ɗin kaman yanzu yake ganin ta yafurta sai na koya miki hankali”ita wa?”wata fitsararriyace kullum da ita nake kwana nake tashi amma haryau komai kama da ita bansake gani ba ba ita.

Fadila dake kwance gefen wani Alhaji saman makeken gadon yana shafa mata sassan jikinta yace”baby kinsan harkar nan bani gishiri inbaki manda ne kuma kinsan na kwaɗaito da wannan ƙawartaki.

“Hmmm Alhajina kenan Ai inde Aisha ce gaskiya jawota wannan harka ba abune mai sauki ba,dan wallahi ko shekara zasuyi basuci abinci ba,banajin zata yarda amma kabar komai a hannuna.

Dayake ansan da zuwan su tarɓa ta musamman suka samu daga gimbiya sai wani ƙwarƙwasa take kawai dan ta burge masoyin nata,amma shi ko kallo bata ishe shi ba.

A sittin room a kai musu masauki ƴar aikin gidan takawo musu ɗan abun taɓawa ta jera musu,har tamiƙe zata tafi basma ta ƙwaɗa mata tsawa,wanda yasa hanta cikin mai aikin kaɗawa”uban wa zeyi saven ɗinmu koso keki ninayi biyanki aike ba kyauta kike mana aikin ba idan kinga bazaki iya ba ƙofa abude take ire irenki yauwane dasu.

jiki na ɓarin matan takoma ta raƙuɓe daga gefe ta tsaya,kallonta Ahmad yayi da kaman bazeyi magana ba sai kuma yace.

“Kin tsaida ita mezata miki bara kiji a tsarina ba ƴan aiki kinfi kowa sanin gidan mu tunda kina zuwa dan Allah jibeki yanzu bakiji kunya ba wajen yiwa wanda a haife tama haifeki irin wannan tsawa kawai dan tana aiki aƙarƙashinku idan zaki gyara ki gyara idan baki gyara ba yarage naki daga haka yamike fuuu yafita baki sake tabi bayansa da kallo har taɓacewa ganinta dama tun kafin tazo sai da Mamatar wato hajia mariya taja kunnen ta kan halinta nayiwa ƴan aiki tsawa da sanin waye ahmad..

“Abokina harla fito kenan cewar khalid dake zaune cikin motar dama sanin hali yasa bebishi sun shiga ba,taɓe baki yayi yana maida zaman glass din idon sa yace”to ma mai ze tsaidani bayan ita ɗin bawata halittace ta daban ba,wani irin tuƙuƙin bakin ciki yasake turniƙe basma data biyo shi a baya dan ta bashi hakuri.

Masu karatu karku manta wannan littafi na kuɗine kibiya 300 kacal dan samun labarin har kashe.

 

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Na
Zahra Ali Abdullahi

Bismillahir rahmanir rahim

Leave a Reply

Back to top button