Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 5

Sponsored Links

Chapter 5

Ba tare da tanuna ɓacin ranta ko da a fuska ne ba,ta ƙaraso inda suke tsaye cike da duniyanci tana wani shaƙe murya tace”barka da yamma abokin mu.

“Yauwa barka de amaryar mu yakike?
Ya gida?
Yakuma su mama?
Fatan kowa lafiya duka tambayan yayi sune a tare”kowa lafiya ta amsa masa da murmushi saman fuskarta.

“Am my dan Allah kai hakuri kazo mukoma ciki muyi magana tawani marairaice kaman zatayi kuka yanda tayi dole tabaka tausayi amma gogan ko a kwalarsa sai ma kokarin bude motar da yakeyi sauri dakatar dashi khalid yayi”dot mushiga mu gaisa da hajia mana in kungama da gimbiyar taka kaga ba daɗi muzo kuma bamu gaisa ba.

Wata uwar harara ya kamawa khalid shiko khalid dauke kansa yayi kaman bashine yayi maganan ba,kwafa yayi sannan yarufe mufin motar da karfi tabbacin ransa aɓace yake gaba kawai yayi batare da kalli kowan su ba.

Zaune suka tadda hajia mariya tana waya da kawarta hajiya bilkisu tana cewa”hajiya balki wai kaman ni ƴar mitsisiyar yarinya dako ƴunwan cikin su be mutu ba take gayan magana ɗan shiru tayi da alaman sauraron wanda suke maganan tare takeyi sai kuma tace so nake kawai kiyi duk yanda zakiyi tazo tafaramun aiki a gidan nan wallahi sai nayi ƙasa ƙasa da ita mara kunyar ƴa sai nasa su Abdul sun yayyagamun wannan bakin nata na rashin kunya wallahi.

Sallamarsu Ahmad shiya katsemata magana tashiga washe baki”a’a my son angirma ya mamar taka?lafiya yace kawai fuska ba walwala dan yaji maganarta ta ƙarshe a zuciyarsa cewa kawai yake to wace zata saka Abdul ɗin yayyagawa lalle wannan mata batada imani.

Zungurin sa khalid yayi jin hajia na magana amma hankalinsa baya gunta”zamu tafi yace yana mai miƙewa tsaye”harzaku tafi fatan de kunɗan taɓa wani abun”a’a badamuwa idan munsake zuwa ma taɓa sauri muke dan munada mettin da wasu baƙi ne.

Yakare magana yana mai kallon agogon dake hannun sa”Allah yatsare ka gaida mun da hajia ko amsata beyi ba yayi waje,bin bayansa hajia mariya tayi tana mai fashewa da dariya tace ɗan iska zaka shigo hannu ne ai idan ka tsallake wannan tarkon akwai wasu tarkunan da naɗana maka masu yawa sai inga ta yanda zaka tsalleke duka.

Anna yana yau kaman jikin naki yayi nauyi?nayi maganan fuskata nanuna tsanyar tausawa mahaifiyarta mu gashi bamu da halin kaita asibiti bare kuma takaimu ga iya saya mata magani idan an rubututa Allah de yakawo mana mafita.

Ganin kaman nashiga damuwa Anna tace”ke zo ki zauna kusa dani tana mai nunan gefenta ba musu nazo na zauna riƙo hannu na tayi tace kinga kar ganin halinda muke ciki yasa ki zubarda mutuncinki saboda abun duniya.

Aduk lokacin da kika tsinci kanki awani halin to kisaka Allah ranki shi zekawo mana mafita sannan a rayuwa kirinƙa kallon na ƙasa dake karki kalli wanda yafiki kiyi duba da yatsun hannunki zakiga ba kansu ɗaya ba, Allah shiyasan hikimar sa nayin hakan,tashi maza ki kawomun ruwan bunun nan naɗan sha sai kuma ki leƙa gidan hajia bilkisu ta’aiko ayi kiranki ɗazu.

“Dot gaskiya abunda kayi kwata kwata baka kyauta ba wallahi?”da nayi fa?shima ya maida masa da tambayan hararar sa khalid yayi yana maida hankalin sa ga tuƙin da yake dan shi ya amshi tuƙin yanzu,murmushin gefen baki yayi yana mai cewa”inde akan wancan yarinyar kake fushi kamanta kawai inaga tafiyanmu ahakan zefi dan bata da hankali.

Hmm”kai kuma sai kabiye mata haba dot wai sai yaushe zaka fara sakewa da ƴan matane,mata fa duniyace dan Allah ka gwada son wata koda da wasane zaka yarda da abunda nake nace ma”yen yen yen bakada bakada magana sai ta mata mata so so nifa wannan duka abun baya genda na amma da zaran nasami wacce tazo daidai da ra’ayina ko auren wucin gadi nayi da ita”wucin gadi kuma?yayi tambayan yana mai zaro masada idanun sa.

“Aisha sai da na waigo naga ashe fadila ce amsawa nayi fuska sake”kwana biyu ƙawata kinyi wuyan gani?tace dani tana ƴar dariya nima dariyar nayi nace”wallahi Anna ce bata ɗanji daɗin jikinta ba shisa kika jini shiru.

“Allah yabata lafiya”amin fadila nagode nace data” kai gaskiya talauci beyi ba wallahi a rayuwa yanzu kiduba in banda talauci ai ba abunda zesa mubarta a gida da ciwo,dan wallahi ko mahaucine yaga Anna yasan bata da lafiya dauriya kawai take kai ina.

Shisafa nake yawan cemiki natsani talauci duk da acikin ta aka haifemu mukakai har wannan muzalin amma wallahi bazan auri talaka in kare rayuwata a talauci ba,ɗan murmushi nayi ina kallonta dan kullum lamarin fadila kara bani mamaki yake.

Dan Allah yanzu ke kanki Aisha a ranki idan kika zauna bakya tsanan talauci ko kiji wani irin ƙunci a ranki idan akawayi gari ba abunda zaku dafa a gidan ku?murmushi mai ɗaci nayi sannan cikin sanyi murya mai cike da rauni nace”zancen gaskiya fadila bana jin haushi ko ƙuncin kasancewar mu a matalauta abu ɗayane idan aka wayi gari nake jin wani iri idan bamu dashi abinci.

Murmushi fadila tayi to amma fa bawai hakan zesani jin ƙunci ne araina ba a’a kawai inajin ba daɗine idan naga yunwa ta hanawa ƴan ƙannena walwala da sukuni sannan ga Anna itama ba lafiya bane ya isheta tunani na ako da yaushe ya za’ayi nasamu aiki da zamu dogara dashi fadila duk da Allah yayimu mata muna da karfin zuciya dakuma ta jiki ta yanda zamu iya yin amfani dashi dan ganin mun taimakawa iyayenmu.

“Taya Aisha bayan muna mata kinsande bazamu iyayin dako ba,a’a kosokike muje bakin titi muna suyan awara da doya takare maganan tana huci wani lokacin wallahi har mamaki fadila ke bani idan tana irin wannan maganan.

“Yi hakuri kawata maida wukar nace da ita”Allah Aisha keɗince wani lokacin da kayan ban haushi ta faɗa tana ƙaremun kallo kaman maison gano wani abu a gareni.

“Fadila nakira sunanta sannan nace suyan awara dake cewa itama sana’ace na rufin asiri ni kinganni nan wallahi ko aikatau nasamu zanyi matukar zan samu abunda zamu rufawa kanmu asiri burina a duniya be wuce naga Anna cikin ƙoshin lafiya ba sannan ƴan kannena suyi karatu kaman kowa bani da burin saina ganni cikin wata daula Allah dayayimu a hakan shi yasan hikimarsa Allah de makawo mana mafita kede kawai fadila abunda zance dake kirage buri ki sanyaya zuciyarki hakan da hakan zefi.

Mtsss”wallahi duk kin ɓatamun rai harma kinsa na mance abunda nazo miki dashi”share kawata idan kin sauka kika tuna saiki faɗamun,nace da ita kinga tunɗazu muna ta tsaye anan kizo kirakani gidan hajiya bilkisu to tace jerawa mukai da ita gwanin sha’awa muna hira har mukaje gida sallama mukai a baki falon gida.

Mai aikinta tafito tana ganin mu tawashe baki dayake tasanni ina zuwa yima hajia wanki tace”a’a Aisha kece yau agidan namu”wallahi nice tani gaisawa mukai sannan tace kushigo itade fadila tatafi duniyar kallon gidan saida na dan zungureta sannan ta sauke numfashi tana cewa”Aisha kalli gida dan Allah kaman baza mutu ba.

Daidai muna zama daga kasat carpet hajia bilkisu ta fito daga wani coridor cikin da shiga ta alfarma,fuskarta sake ta ƙaraso ta zauna saman ɗaya daga cikin kugerun falon gaidata mukai ta amsa mana fuska sake tana kallon fadila tace”wannan?”ƙawatace na amsa mata”yayi kyau ya Anna da karfin jiki?”Alhamdulillahi nakuma amsamata.

Gyara zama hajia bilkisu tayi sannan tace badan komai na aika akiramun ke ba,dama kawata hajia mariya dam gabana yabada sauti tun kafin tafaɗi abunda take shirin faɗi Aisha ki nitsu dan ganin kaman yanayina yacanza tace dani.

Dama mai aikinta tayi tafiya to tana neman wanda zeriƙa mata kafin tadawo shine nace ko zakije tunda ba abunda kikeyi a gida”sai na faɗawa Anna duk abunda tace zan faɗa miki.

Na amsa mata dan gaskiya hankalina be kwanta ba da wannan aiki gani nake kaman matar tashirya cimun mutuncine tunda nace bazamu sake yimata wanki ba haka kawai naji zuciyata ta amince mun da hakan.

“Haba Aisha mena saikin faɗawa Anna kinde san bazata hana ba”duk da haka tanada hakkin sani ko hanani na amsa ina miƙewa nafita gani haka itama fadila mikewa tarufamun baya daidai bakin get naji na mangari mutum baya nayi zan faɗi yayi saurin riƙoni”yi a hankali bakiji ciwo bako?ware manyan idanuna dasuke a lumshe nayi saman fuskarsa cikin rawar murya data jiki nace kaine ina nunashi da ɗan yatsa.
Saurin sakemun hannuna yayi yaga goge hannun sa da handkerchief ya ɗago da daidai zeyi….

 

Leave a Reply

Back to top button