Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 55

Sponsored Links

CHSPTER 55

Dariya suka kwashe dashi gaba ɗayansua tare kaman wasu bosawa saida sukayi mai isarsu suka buɗe kwalban barasa shamfe suka shiga kwankwaɗa nan Alh sunusi yake sanar dasu ƙudurinsa”saka hannun wannan mai taurin kan ɗan nasa nake bukata fiyot a wuce wajen.

“To ita kuma ɗiyar taka ya zakayi da ita kasan yaran zamani da shegen hange hangen su wai SO kartaƙi yimana yanda muke so saboda soyayya kasan soyayya ba abunda baya sawa mutum yaƙiyi soyayya maida maƙiyi masoyi.

“Nabi soyayya da gudu ai bazan bari soyayyar ɗan miƙiyina ya tasirantu a zuciyar ɗiyata ba dole itama ta fifita buƙatana sama da komai na duniya dan wallahi ko ɗan yatsan hannuna ne naga ze shiga tsakanina da nasarata da muradina to wallahi guntule shi zanyi kagako ba abu mai wahala bane kawar da duk wanda ze nemi kawo mun cikas ko yun ƙurin cin amanata daga doron duniyar nan,mukut su biyun suka haɗiyi wani ƴawu mai kauri dan Alh sunusi idan ya furta abu ba makawa to kuwa zeyine kamande yande ya samu nasaran kawar da abokan kasuwancin su da dama ace warsa maciya amana ne.

BAYAN KWANA BIYU
Yau aka sallamo Aisha daga asibiti da tarin magunguna Aisha dake zaune bakin gado ta zubawa guɗaya ido da alama tunani take yayinda Anty malika kuma tashiga harhaɗa masu kayansu dan tayi waya da Anty hajia ma tace tayi zamanta yanzu suma za suzo tunda an sallame su,dr sufyan nagani zaune a office ɗinsa sai rubutu yake a wata doguwar paper yana rubutawa yana sakin murmushi dr irfan daya shigo ya’iskesa yayi murmushi yana girgiza kansa dacewa”lalle iska yana wahal da mekayan kara.

Ɗagowa yayi ya banka masa harara sannan yasake maida kansa ya cigaba da rubutun da yake,zama dr irfan yayi kan kugera dake fuskantar abokin nasa yace akan wannan zaman rubutu da kake mai ze hana kaje ka tunkareta gaba da gaba da bukatarka kasan fa yau shine last chace ɗin dan yanzu haka na barota sai haɗa kayansu take kaga kuwa tafiya zatayi sunan ta kawai kasani ba address ba ba ba ba…yakare da zolayarsa zunbur dr sufyan yamiƙe yana kallon dr irfan da shima shidin yake kallo yace”karkace mun haka”to shike nan tsaya kallon ruwa ƙwado yama ƙafa.

Be ma sake bin takan dr irfan dake faman yimasa tsiya ba yayi waje da mugun sauri shiko dr irfan mai zeyi inba dariya ba yana cewa hmm su so manya daa idan ance akwai so kaine kan gaba wajen musawa mutum babu so yanzu ko wace ƙaniyarce kuma wannan yana kare faɗin shiɗin ma fita daga office din yayi yaja masa ƙofa dan dama zuwa yayi ya faɗamasa mutuniyar tasa fa sai faman haɗa kaya take.

Hajia mariya nagani zaune sai zabga murmushi take wato bukata tabiya kenan ta dauki waya takira aminiyarta Hajia balki a waya kira ɗaya ta daga kaman dama jira take”kawata kice tasamu kenan kira a wannan lokaci haka?

Dariya hajia mariya ta kwashe dashi tana cewa”oshe ita hajia balkin dariya tayi daga nata ɓangaren tana gyara zamanta saman gado tace ban nasha da dumi dumin sa.

“Ƙawata komai yayi daidai wato wannan magani da kika bani bala’ine wallahi musibace bakiga yanda Alhaji ya susuce akaina ba wallahi,ai bayan komai ya lafa ina kawo masa buƙatata be wani ja zancen ba sai cewa yayi ai dama can gani yayi kaman nice banida sha’awa yin kasuwanci take ya cakemun 10m inja jari ke in faɗa miki harda babban shago dakuma store ajiye kaya.

“Wayyo daɗi kice duniya sabuwa ƙawata yanzune zaki faso gari,yanzu yaushe kike ganin yadace muje mufara miki sari kinsa ance da zafi zafi ake dukan karfe.

Ɗan jim tayi kaman mai tunani sai can kuma tace”ca nayi mubari harsai an gama bikin basma tukunna kinsan wannan satin ne kuma inajin kaman gobene zasu fara wasu event din.

“Shike nan hakanma yayi amma kisamu kizo mukoma wajen bokan nan ta yanda zaki samu kan Alhajin sosai duk da shima tsaye yake amma bazaki zauna ki zuba masa ido ba.

Ahmad sai yau ya shirya zuwa gidan su karfe goma daidai na safe yasame shi a ƙofar gidan saida yashiga ya daidai ta parkin din motarsa ya fito yana tafiya kaman wanda bashi da laka ajikinsa main falon gidan nasu yanufa kansa tsaye bakinsa dauke da sallama.

Auta meera ce tamiƙe da gudunta tana masa oyoyo daukanta yayi ya ɗagata sama yana juyata kaman wata bebi itako sai dariya take Fadwa ma tazo ta faɗa jikin sa tana cewa”ya Ahmad ina kashiga kwana biyu baka nan kullum Ammi sai tayi kuka gashi kuma daddy bashi da lafiya wai wai ….sai kuma tayi shiru tsareta da ido yayi zuciyarsa dake faman bugawa da sauri da sauri meera ce ta amshe da cewa”a school dinmu ba wai kawayen mu cemana suke daddyn mu macucine yana cutan al’umma da saida musu da ƙwaya da sunan magani shiyasa aka rufe masa company da muka faɗawa uncle Sam sai yace ai gaskiya aka faɗa mana mu yaran maci amanan kasane yau kwana biyu bamuje school ba saboda ko munje yara da malamai zagin mu suke.

Besan sanda ya dire meera ƙasa yanufi ciki ɗakin Ammi da sassarfa ba,zaune ya taddata ta saka daddy gaba da ban baki yasha koda tea ne,amma yaƙi amsa yayi baƙi kirin ya rame cikin kwana biyu kaman wanda ya kwanta ciwon shekara,zuba masa ido sukai suna kallon sa”Ammi wai me nakeji daga bakin yaran nan yanzu?

Ajiyar zuciya ta sauke tana maida kanta kan Alh badamasi dake zaune cikin sanyi murya tace”wai ana zargin sa da sarrafa miyagun ƙwayoyi ba bisa ka’ida ba,shine aka rufe wajen.

Kai ina kashiga kwana biyu wayanka baya shiga ina kake tsawon kwana biyu baka da labarin abunda yake faruwa a garin?ta tambaya tana tsareshi da ido”yanzu de ba wannan ba Ammi shi daddyn wani irin mataki ya dauka dan kare mutuncin kansa dama companyn nin baki ɗaya.

“Babu nadeji ɗazu yana waya da Alhaji sunusi yana cewa zasu sami manyan akan maganan?

Wannan ba yi vane Ammi

Kallonsa daddyn nasa yayi yace”kadamu danine da katsallaƙe kayi tafiyarka kwana biyu batare da ka waiwaye mu ba?

“Yi hakuri daddy yanzu ba lokacin yin wannan magana bane inason sanin shin akwai waƴanda suka saka hannu jari a company ko kuwa?

Shiru yayi dan yasan da zaran yace Alhaji sunusi yanzun nan zasu haushi da masifa shisa ma koda faisal yazo jiya du tambayan da yayi masa be yarda koda wasa ya ambaci sunan sa ba.

Jin shirun yayi yawa yasa Ahmad miƙewa rai a ɓace yace”daddy zanyi duk iya yina dan ganin nakare mutuncinka da martabanka da ƙimar wannan gida tamu koda zan rasa raina ne amma fa hakan baze samu ba harsai ka bani haɗin kai,daddy idan har ba wani abu mara kyau a wannan company naka ba bukatar bin manya da basu cin hanci.

“Ahmad company nawane ko naka?
Alhaji badamasi ya tambaya rai aɓace dan wani mugun haushin Ahmad yakeji,abu yau kwana biyu bayanan sai yanzu ne ze zo masa dawani zancen banza.

“Naka Ammjn ta amsa masa
“To inde nawane ba ruwansa”da ruwan sa harda tsakin sa dan hakkinsa ne kare mutuncun gidan nan matsayin sa na magajin ka.

Banga dalilin da wani bare da ze saka bakinsa cikin wannan magana ba,idan bada wata a ƙasa ba mai nawani cewa za bada kuɗi abi manya dan kawai son rashin gaskiya idan ba wata a ƙasa abar jami’an tsaro suyi aikin su kaman yanda suka bukata idan kuma dama kasan da wata aƙasa kayi gaggawan fayyace mana ta yanda zamu gane.

Menene alaƙanka da Alhaji sunusi dan shi kaskane raɓi….”ya isa yafaɗa a tsawace da daurawa da cewa kufita kubani waje.

“Zamu fita yanzu kaman yanda ka bukata saide abu na farko kuma ba karshe da zan faɗa maka shine babu zancen wannan bikin na Ahmad cikin wannan sati kaman yanda kuka tsara harsai komai ya daidaita dan baza’ayi biki aure ana cikin wannan hali ba tana kaiwa karshen maganan ta taja hannun Ahmad daya kafawa daddyn nasa ido suka fita daga ɗakin.

*******
“Aisha Aisha Aisha har sau uku Anty malika na kiran sunanta amma bataji taba saboda nisa datayi da tunani da take,barin abunda takayi tayi taxo ta zauna saman gadon kusa gare tana mai dafa kafadanta firgigit tadawo hayyacinta tana ƙakalo murmushi da iya kacinta kasan saman leɓɓen tane tace”Anty malika karde hankin gama?

Gyaɗa mata kai tayi cike da tausayinta tariƙo hannunta tace”nasan da wuya ace rana tsaka karabu da abunda kakeso dakuma ciwo amma idan kika saka hakuri aranki kika kuma dauki abun da sauki saiyazo miki da saukin.

Hawaye datake ƙokarin tsayarwa ne yasamu nasaran xubo mata daga gurbin idanunta tace”Anty malika hakika nayi rashin masoyin gaskiya shin faɗa masa gaskiya danayi kafin yaji abakin wani yaɗauka na yaudare sane kuskurene yin hakan?

“Bakiyi kuskure ba koka ɗan hakan da kikayi shine daidai”to amma Anty meyasa koda sau ɗayane be tsaya ya saurari abunda nake faɗa masa koya nuna yajini ba sai shirun da yayi kinko san yaren shiru kuwa Anty malika wannan shiru yana neman kasheni naso ace koma yayane ya tsaya ya fuskance ni nide wallahi an cuceni da wannan auren wucin gadin nan wallahi ta faɗa tana sake fashewa da sabon kuka,dr sufyan daya zo shiga ɗakin yaji dukkan abunda suke tattaunawa baya yayi a hankali batare dasun san da tsayuwar sa awajen ba.

Suhail tunda yashiga ɗaki yarasa meke masa daɗi yasan tabbas gaskiya Aisha ta faɗi dan betaɓa kamata dayi masa karya kokuma wasa irin haka ba,shin awani mizani yakamata yaɗaura kalamanta cin amana ko yaudara”la la la yafurta a fili to ma waye wannan dayayi musu ƙatsalandan shiga cikin rayuwarsu bayan sun riga sungama tsara yanda zasuyi rayuwarsu ƙarƙashin inuwar aure.

Kukansa yayi mai rai da lafiya dan yasan kukan ne kaɗai ze iya saukar masa da abunda yajiki a ransa gwara yayi ko ze samu sassauci da salama a zuciyar sa amma de yasan yayi rashi rashi irin wacce bazai taɓa maida irin sa ba.

Leave a Reply

Back to top button