Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 72

Sponsored Links

CHAPTER 72

Hajia mariya bata tashi farkawa ba saida sanyin asuba ya kaɗata a zabure tafara”kiran dan Allah matattu kuyi hakuri wallahi ban shirya zama dakuba idan kuka barni baxan sake xuwa inda kuke ba,baba inna kullu inna hajara baba babba ku kun daɗe cikin su kuce suyi hakuri duk wannan iface ifacen da take taƙima bude idon ta balle tasan a inda take ita a tunanin ta harsan nan a can ɗin take duk ta jiƙe da zagumi sharƙaf ta firgice ta ɗimauce”mariya mariya buɗe idonki ke idan anyi mafarki addu’a akeyi ba ihu ba,cewar yayarta hajjo da sukazo auren.

Jin muryan yayarta hajjo hakan yasata ta buɗe idonta ɗaya tana kannewa tare da tsoron abunda zata ganin addu’a take ita anata sai karanta “baa sin mi aa ra take da iya karfinta itafa a dole addu’a take idan ka tambaya, sai maimaita take da karfi itade fatan ta karda ta ganta wajen jiyan”ke wai me haka kikene addu’a akace kiyi ba karatu ba,cewar yayah hajjo.

Bude idon ta shigayi ga mamakin ta sai taganta a gida kwance saman gadon ta ganan yaya hajjo zaune gefen ta tana mata faɗan tayi addu’a sai gwaggo tani dake zaune itama a kasan saman carfet tana kurɓan shayinta hankali kwance tana ƙarawa da soyayyar ƙwai sai ta cika bakinta da kwai soyayye sannan take korawa da shayi tana cewa”yanzu hajjo irin daula da mariya ke ciki kenan amma kiduba shine mu tabarmu a kauye muna fama da rayuwa Allah yatsine arzikin da zakaci kai ɗaya batare da ƴan uwa ba.

sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta cigaba da cewa hajjo duba kiga tunda mudawo yau kwana biyu kenan nama saide muci iya cinmu muture amma bawai dan yaƙare a gidan nan ba,haka kaza daya amsa sunan kaza shima saide muci muture mai ramo ko soyayya kai harma da gasasshe,duba kiga wannan kwaice guda goma nasa wancan mai aikin nasu ya soyamun kalli shayi mai kauri haɗin majinyaci amma Allah yasa tsakanin mu dake mariya kina irin wannan abun kin barmu da cin tuwun dawa arniya mai shockin(miyar kuka kenan) kullum mukenan cin abu ɗaya da dare kaci kayi ɗumamen sa da safe”dan Allah gwaggo tani kiyi hakuri kiyi shiru ke taci kike niko ta lafiyar ƴar uwata nake ki bari dan Allah idan ta dawo hayyacin ta kya faɗa mata koma menene dan Allah badan ni ko ita ba kiyi shiru kinjide abun da likitan yace ɗaxu dayazo duba ta ko”sai kawai ta gyada mata kanta tana cigaba da cin kwai da shayi.

Jin wannan maganganun nasu yabata daman buɗe idon tar da kyau saide tayi mamakin ganin ta gida a ɗaki kuma saman gadonta kwace take a komai abunda yafaru da itane yazo mata kaman yanzu akayi,zumbur tamiƙe zaune tana.

Tana faɗin nashiga uku waya kawoni sai kuma ta ɗaga kafarta ɗaya daya maƙale jiya a cikin rami tagade lafiyansa lau sai kuma tasake ɗaga ɗayan taga shima lafiya ganin tana lafiya lau tasauke ajiyar zuciya sai kuma ta kalli yayarta tace”yaya hajjo waya kawoni nan?
Kallon juna gwoggo tani da yaya hajjo sukai sai kuma suka maida kallon su kanta yaya hajjo tace”amma kanki ɗaya mariya?mafarki kikai ko kuma wani abun kika aikata kike kiran matattu yardasu baba?Take zufa yakaryo mata da jin irin tambayar da yayar tata tamata cike da tuhuma.

***********
Su Aisha suna nan a asibiti sai bayan magariba suka koma gida tare da anty hajia datace ita fa tawarke kawai a sallameta,dole likitan yayi sallama dan angwada BP yasauka,koda suka koma gida bedroom ɗin anty hajia suka shiga da Aisha tare da Ammi suka sakata tsakiya da tambaya ko anmata wani abu”bude bakin tayi cikin rawar murya hankali idon ta natara ruwan ƙwalla nan take suka tuna mata da Annanta ta sande duk duniya uwace kadai wacce zata shiga damuwa akan ƴarta dakuma tsoron kowani abu yasame ta,sai gashi Allah yabata ahali masu sonta da kaunarta masu damuwa da damuwarta.

Faɗawa jikinsu tasaki kuka tanayi suma nayi su tsoron su kartace wani a taɓata itako kukan take na tuna mata mahaifiyarta dasukayi saida sukai mai isarsu sannan sukai shuru dan kansu bude bakinta tayi tace”wallahi anty hajia Ammi ba abunda akaimun ba wanda ya taɓani kawai ina kukane tunawa danayi da Annata banyi tsammanin zan samu waƴanda zasu mayemun gurbin ta ba.

Wannan ne yasani kuka,share mata hawayenta Ammi tayi tace”Aisha bakomai ai ɗa nakowa ne tashi kije kiyi wanka sannan ki huta ƙannenki suna can gidan namu anji malik ze dawo dasu munyi waya,da tom ta amsa cikin sanyi jiki tafi ta koma ɗakin su koda ta koma wanka tayi tafito daure da towal da karami riƙe a hannun ta tana tsane ruwan jikinta zama tayi saman stool din gaban mirrow tana shafa jikinta da tsadaddun mayukan ta masu kyau da sanyin kamshi ta murza turare a jikinta saida tabi lungu da tsaƙo na jikinta tamulke da turaren sannan tamiƙe cikin takunta da nutsuwarta ta nufi canza kayanta data ajiye saman ƙofa taji an turo ƙofa,saurin ɗago da kanta tayi tana sake rigar da ta dauka ƙasa.

Saboda tsaban rudewa da tayi batasan sanda ta duƙa kasa gaban mirrow ba tana ƙanƙame jikin ta gada kallon da yake binta dashi,tanajin idanuwan sa masu kaifi dake yawo akanta,takuwa yayi a hankali cikin takunsa mai nuni da shiɗin cikakken namijine isowa yayi inda take yakai hannun sa danufin ya ɗagota tayi saurin make masa hannu tana sake riƙe towel dinda take daure dashi.

Sake kai hannunsa yayi a karo nabiyu cikin rawar murya dake nuni da tsoro tace”dan Allah kafita idan wani yashigo ya ganmu a haka fa?

Taɓe bakin sa yayi yace”to mai aciki mutum da matars…kafin yaƙara sa yaja masa wani dogon tsaki….ai kafin tadire ya fuzgota cikin fushi yace”ni kike jawa tsaki ko?yau zanyi maganin wannan bakin na tsiwa ta yanda gobe idan ance kima wani ba zakiyi ba.

Tun kafin yakare maganan nasa ta fizge daga rikon da yayi mata zata gudu ko toilet ne ta ɓoye kanta,taku ɗaya biyu yayi karaf ya caf kota ya matseta da jikin bango ɗakin yamata rumfa da faffadan kirjinsa hannun sa yakai cikin zafin nama ya fizge towel din da take ta rirriƙewa ai batasan sanda ta kwalla ihu ba.

Sa’ansa ɗaya ƙofar ɗakin a rufe take da abude yabarta ba abunda ze hana su anty hajia dake zaune a falo jin ihun nata.

Faɗawa jikinsa tayi ta rungumesa da karfi so tight dan gudun karya kallar mata jiki wani irin shockin kaman na wuta lantarkine yajasu dukkansu su biyun take zuciyoyinsu yashiga sama da ƙasa kusan a tare dana juna zuciyar tasu ke bugawa,ɓagaren Ahmad wutane ya dauke masa itako Aisha a ruɗe take saboda yanda ta ruɗen jikinta harkaɗawa take kaman mazari.

Sun dauki a kallah minti uku zuwa hudu a hakan tuni hawaye masu ɗumi sun wankema Aisha fuskarta na tsaban takaicin abunda yamata,gashiya gama kallen mata jiki badaman tace zata bar jikinsa a yanda take tsirara ganin baze gane ya barta ba kawai sai tadaga murya tashiga raira masa kuka,kukan tane yadawo dashi daga shockin ɗin da yake ciki.

Saurin tureta baya yayi tasake fadawa jikin sa tana kuka tana cewa”wallahi nide banyafe maka kallan mu jiki da kai ba kuma kabani towel dina kuma saina haɗaka da Anty hajia ai ni ba ƴar iska bace da zaka shigo mun ɗaki kana neman…..saikuma tayi shiru bata ƙasara ba tana sake ƙanƙame shi.

Tureta baya yasoyi amma taƙi barin sa cike da jin haushin kansa da kansa waime yagani gawan nan ƴa yarinya dabaya iya rike kansa harsaya dangana gareta(niko nace so da kauna)

Ganin taƙi sakin sa kawai a zuciye saiji tayi anyi sama da ita be direta ko ina ba sai saman gadon dake ɗakin yana jefata yabi ya danneta rintse idonta tayi da karfi gashi yasake mata duka karfin sa badaman tayi koda motsin kirkine ba bakin tsiwa sai hawaye batayi aune ba taji saukan tattausa lips dinsa masu danshi da dumi saman nata yashiga tsotsan bakin ta kaman wanda yasami lollipop da zafi zafi yake tsotsan ganin yana neman rasa nutsuwar sa yayi saurin sakinta yana mirginawa gefe tare da sauke tagwayen ajiyar zuci, tayi saurin jan zanin gadon tayi tarufa har saman kanta tana kuka dajin haushin abunda yamata.

Saida ya daidaita nutsuwar sa sannan ya sauka daga saman gado saida yayi taku ɗaya biyu yafara mata magana yana cewa”gobema kika sake mun tsiwa haka zan miki wannan shine hukuncina ko kuma yacinye bakin tsiwar nan naki yana gama fadin haka yasa kai yafita daga dakin yayi sa’a be samu kowa a falon ba dan haka yafita waje.

 

Wayane kare akunne yayinda sauran abokan nasa ke zazzaune mikewa yayi a zabure yana nace”what abunda yayinne ya jawo hankalin sauran kansa duka miƙewa suke suna tambayan sa ko lafiya.

Ai besan sanda wayan ta suɓuce ta faɗi ƙasa ba take zufa ya yanko masa dukda uban ac dake kunne a falon sannan ga fanka”bala bashir karshen yazo watan talaucewar mune yakama an kame mana.

Yana faɗa musu haka suka shiga zagaye falon sai jikike ƙwarr sun gora kansu dana junan su,dama gashi Alh bala shi be iya shiga tashin hankali ba yanason cewa Alhamdulillahi sai kawai yaɓige da faɗin ALI YAMUTU LILLAHI….

Leave a Reply

Back to top button