Hausa NovelsKurkukun Kaddara Hausa Novels

Kurkukun Kaddara 6

Sponsored Links

https://chat.whatsapp.com/Fg5z8TEO5Mk0NwptyjrKjq

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

*_Daga alƙalamin Boss Bature_*

Dedicated to Aunty kubra💞

*E6*

Jinjina kai Taj ya yi”Yanzu menene mafita”?
Uzair yace”Mu tayata da addu’a, Sannan Muyi ƙoƙarin ganin mun bi duk wasu sharuɗɗa na bata kariya da malam mai salati ya faɗa maka, in Allah ya yarda za’a dace ne,”

Taj yace”Allah Ya yarda, duk na damu wlh,”

Uzair yace”ka kwantar da hankalin ka, da yardar Allah zamu San abun yi,

Sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa tare da uzair kafin ya yi mashi sallama ya tafi gida,

Tundaga wannan Lokacin, bai ƙara yin sakaci wurin kula da ita ba har tahfeez ya sanya ta, ya ci wahala kafin ya samu tafara zama Makarantar islamiyyar, da yake a kusa dasu makarantar take, idan ya kai ta yana barin makarantar take kamo hanya ta dawo gida, Kowa ya yi mamakin yadda a kai ta ke guduwa daga makaranta, dakyar ya samu tafara zama, tun tana yi ma shi kukan ba ta so harta haƙura ta zauna, bai ta6a bari ta zauna tana shiririta ba, Kullum sai ya tasa ta gaba tana maimaita karatun haddar da aka bata, babu abunda bai siya mata ba, Wanda ya danganci karatun addini, Cikin ikon Allah sai ga shi tafara sanya naci tana yin karatun tunkafin ma yace mata ta yi take yi, wani lokacin ko bacci take yi ta dinga sambatu kenan tana Bitar karatun da a ka koya mata, Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yi mashi ba, Uzair da aneelerh ba ƙaramar rawa suka taka ba, wurin taimaka ma taj akan angel, dama sun ɗauketa tamkar ƴar su, Allah ya bata kaifin basira,wani irin ƙoƙari gare ne ita duka boko da islamiyya ko’ina yabon ta su ke yi, Kowa sonta yake yi, duk wani Competition da za’ayi Tsakanin makarantu, ita ke ciyo ma school ɗinsu, shiyasa su kansu malaman Ji su ke da ita, duk in tayi fashi bata zo school ba, Sai sun kira taj a waya sunji dalili, sometimes har gidan suke zuwa ganinta,

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah Angel ta shiga Cikin shekarata Goma, a wannan Lokacin suka Shirya Mata Party na taya murnar zagayowar ranar haihuwar ta, tun ana saura kwana biyu, Aneelerh ta kai ta wurin Saloon, gyaran gashi akayi mata mai kyan gaske, tare da ƙunshi na jan lalle, da ya rage saura kwana ɗaya birthday ɗin nata, gaba ɗaya suka shirya don zuwa yi mata siyayya A shopping Mall,

Kaya sosai suka siya mata a kasuwar, sai da suka gama kashe mata kuɗi, Tasa masu rigima akan Tana son a siya mata Piano da kuma drawing materials, A lokacin sunyi ƙarƙaf, sun gama kashe ƴan canjin da suka rage masu, Lallashinta su ka soma yi akan tayi haƙuri next time idan suka ta shi dawowa zasu siya mata, Ƙin yadda ta yi a ƙarshe ma ta rushe masu da kuka tana fadin ita dai su siya mata su take so, ko kuma amaida sauran kayan da aka siya mata don kuɗin su isa a siya mata Piano, sosai Angel ta sanya masu rigima, tun mutane basu lura ba, har hankalin kowa ya dawo kansu, Ganin Yadda yarinyar take ta ruskar kuka, Aneelerh taso ta siya mata, Taj ne ya hanata saboda yasan ba isassun kuɗi gareta ba.

A haka suka koma gida, Sosai ya yi mata faɗa akan ta daina yi ma shi rigima Cikin mutane, tunda yace mata ba shi da kuɗi meyasa zata takura shi, so take ta kunya ta shi a idon jama’a, daga ƙarshe yace mata ta yi hakuri idan ya samu kuɗi zai siya mata komai take so, shi kan shi baiji dadin yadda ya gaza siya mata Abubuwan da takeso ba, Don ta ƙwallafa rai a kan su sosai,

A washe garin ranar ya kasance Juma’a, ranar birthday ɗin ta, Gagarumin party suka haɗa mata, tun bayan sallar asuba aka soma shagali don a wannan lokacin ne Angel tazo duniya, Ƴan uwa da a bokan arziƙi duk sun hallara don tayata murnar birthday ɗinta, Kaya kala Uku ta sanya aranar, aneelerh ce ta shiryata ta yi mata kwalliya, Musamman aka ɗauko photographers, Su ka yi masu hotuna, taro yayi albarka Anyi kulu washrabu hani’an, Kowa ya shaida ya nishanɗantu

Angel ta samu Kyaututtuka masu yawan gaske daga wurin a bokanan aikin shi, Wasu gifts ɗinma baisan su wanene suka aiko mata dasu ba, baba mai gadi ake aikowa daga waje,ya kawo mata su cikin gidan, bakomai ya fi Ba shi mamaki ba, face wata kyuatar bazata da a kayi ma angel, Abun ya ɗaure mashi kai, Abunda angel ta kwallafa rai akan shi ne Aka samu wani ya siya mata su, piano da kuma kayan zane da ta sa masu rigima a shopping mall, Ya yi mamaki sosai har baba mai gadi ya tambaya waye ya aiko mata da gift ɗin don shi ya miƙo su Cikin gidan, Baba maigadi yace ma shi bazai Iya shaida fuskar wanda ya kawo ba, Matashin saurayi ne dai kuma ya sanya facemask a fuskar shi, Sannan kuma Acikin mota ya zo, har tambayar baba maigadi ya yi kobya lura da kofato a ƙafar mutumin daya kawo su? Baba gadi ya yi dariya Tare da cewa Bazai iya tantance ƙafafune ko kofato ba,tunda ya sanya takalma,

jikin taj dai yayi sanyi sosai, ko angel bai bari taga kayan ba, Ya 6oye su a ɗaya daga Cikin ɗakunnan gidan, Kafin a kammala shagalin sun ke6e da Uxair ya sanar da shi game da kayan da aka siya ma angel, shima ya yi mamakin jin hakan, Amma sai yace mashi Ya kwantar da hankalin shi, Shi yafi tunanin Cikin mutanan dake kallonsu A mall ɗinne lokacin da angel tasa rigima akan su siya mata kayan, Shine aka samu wani na Allah ya siya mata su, don haka ya cire damuwa aranshi Ya bata kayanta, kada ya hanata yin amfani da su, Iya ka ci dai kafin tafara amfani da su, Ya tofe su da addu’a, kuma kada Ya dinga barinta tana yawan yin kiɗa, ko ƴan zane zane sai ya dinga lura, Sosai Uzair ya ba shi shawara, Har saida yaga hankalin shi Ya kwanta,

Bayan kwana ɗaya da yin Birthday ɗin nata, Sai ga ɗan saƙo an aiko daga wurin Alhaji ubaid, Gift ne Ya aikoma jikarshi, danƙareriyar waya ƙirar i phone tare da Laptop, Bayan ya kar6esu daga hannun ɗan saƙon,Yakaisu ɗakinshi ba zato ba tsammani Sai ga alert na 1.5m ya shigo wayarshi, again daga alhaji ubaid, Ba ƙaramin farin Ciki ya yi ba, Yana ƙara Jin ƙaunar mutumin kodan saboda kyautatawar da yake yi ma ƴar shi, shi kaɗai ya damu da ita duk cikin family ɗin benazir babu wanda ya ta6a tuntu6ar shi koda a waya ne ya tambayi ya angel ta kwana, duk da yasan halin su ko lokacin auran shi da benazir dayawansu basu so ya aure ta ba, saboda arziƙin shi bai kai ya mallake ta ba, shiyasa sam babu ruwansu da abun da ya shafi tajudden, Alhaji ubaid ɗin kaɗai ne ya damu da su, kusan kullum sai ya kira don yaji ya lafiyar jikar shi,

har uzair ya tuntu6a Don su yi shawara da shi game da Kuɗin da alhaji ubaid Ya turo mashi,Yace mashi Yayi amfani da su,Wurin Gyara mata bedroom ɗinta, Inda zata koma da kwana, ya sanya mata kayan wasanni da zasu dinga ɗebe mata kewa, Sauran kuɗin Kuma Akwai hidindimu masu Zuwa, ya ajiye mata su, Duk yadda taj yaso ya ɗauki wani a bu daga Cikin kuɗin yaƙi kar6a, Sai da ƙyar ya samu ya kar6i dubu ɗari,

a tare da aneelerh suka tsara mata komai na bedroom dinta, Wani haɗaɗɗen gado suka sanya mata, Headboard ɗinshi Sak Jikin butterfly ne, Komai na bedroom ɗinta Pink Colour ne, Ba abunda ba’a sanya mata ba, Yaci wahala kafin ya samu angel ta koma kwana dakinta,Saboda sabon da su ka yi da juna, sai ya bari bacci ya ɗauketa tukunna yake kaita ɗakin ta, idan tafarka ko ƙarfe nawa ne na dare saita sauko daga Upstairs ta dawo ɗakinshi da yake ya dawo downstairs bayan sun raba daki, Sai dai kawai yaji ta Kwance ajikin shi,

sai da yabi komai asannu tukunna ya samu Tafara sabawa da kwana a ɗakinta, yanzu da kanta take yin wanka ta sanya kaya har ma tayi kwalliya, har lokacin angel batasan an bata gift din piano da Kayan zane ba, Saboda ya 6oyesu Laptop kaɗai ya bata, wayar kuma da aka bata shi yaci gaba da amfani da ita, don bazai bari ta ruƙe waya ba, Saboda wayon dake gareta, kuma zata iya ɗauke mata hankalinta daga yin karatu,

Acikin waɗannan kwanakin taj yaso yaje buzaye wurin Dangin shi, Amma Uzair ya dakatar da shi, Akan ya bari Su uncle su dawo Nigeria, in ya so sai su ɗunguma su tafi a tare, ba don yaso ba Ya amince ma shi,

Tuni angel ta kammala primary school ɗinta a yanzu haka tana a Jss 3 Sunyi Exam na first term, tunda suka samu hutu ba inda take zuwa Kullum tana gida bata zuwa ko’ina, taj Ya damƙa mata Piano ɗinta, Idan ta zauna ta soma yi masu kiɗa ko gajiya ba ta yi, Sai in Lokacin Karatunta ya yi ko sallah take tashi, sam ya hanata Yin kallo In ba cartoon ba, Shima cartoon ɗin Sai ya tabbatar Baida wani abu da zai 6ata mashi yarinya tukunna yake barinta ta kalla, Ya sanya mata ido sosai, duk wani motsinta a tafin hannun shi, idan zai tafi wurin aiki, Gidan su Aneelerh yake turata, koda basa nan mai aikin gidansu Ana tana nan, A wurinta take zama kafin su dawo

Wannan kenan,

a gajiye ya ke driving a daidai bakin gate, ya soma dannawa mai gadi hon, Da hanzari baba mai gadi Ya fito daga ɗakinsa, ya buɗe ma shi gate ya shigo da motar Jikin gidan, Fitowa daga Cikin motar ya yi, Jikin shi na sanye da Shadda green Colour ba ƙaramin kyau tayi ma shi ba, Sai daya fara tsayawa suka gaisa da baba maigadi tukunna Ya nufi Cikin gidan,

Tunda yayi sallama a palour Yaji shiru ba’a amsa mashi ba, ran shi ya ba shi cewar Ko bata dawo gida bane, yanke shawarar zuwa bedroom ɗinta Yayi, walking slowly Ya nufi stairs ɗin ya haye, a tsanake ya ke tattaka steps ɗin benan harya samu Ya haye sama, Kaitsaye Ya nufi inda ɗakinta yake, Da sallama a bakin shi ya tura ƙopar ɗakin, Yana shiga idanuwanshi suka sauka akan gadon, wayam baiganta ba, Hakan na nufin bata dawo ba, tana agidansu aneelerh, Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da juyawa zai bar ɗakin, Karaf idanuwan shi suka sauka akan Zanen fuskar shi da angel ta yi a jikin bangon ɗakinta, Cike da mamaki Yaci burki tare da nufar Bangon yana kallon Zanunnukan da ta yi, da kuma rubuce rubucen da ta yi duk a jikin bangon,

Motsa lips ɗinsa ya soma yi yana karanta abunda ta rubuta a jikin bangon

_To my biggest hero_

_There’s no better role model than you,_
_There’s no one I’d rather look up to than you._
_I’m so proud to be your daughter_
_You’re my one and only dad, and you’ll always have a special place in my heart._
_Dad, you’ve made all my favorite memories._
_Dad, you’ve always been my hero._
_I’m so lucky to have your love and guidance in my life_

ya ma rasa mi zai ce lokacin daya kammala karanta Rubuce rubucen da ta yi ma shi, Wani irin tsantsar farin Cikine Ya bayyana akan Fuskar shi, Tuni hawaye su ka wanke ma shi fuskar shi, slowly ya zube saman gwiwowinsa, a yayin da hawayen ke cigaba da bin kuncin shi, kalamanta ba ƙaramin faranta ma shi rai su ka yi ba, maimakon Ya ji haushin 6ata bangon ɗakin da tayi sai ma yaji ya ƙara sonta a cikin zuciyar shi,

Haƙiƙa angel ta ba shi mamaki, ta san ya shi farin Cikin da bazai ta6a mantawa ba,

Da sauri Ya juya ya kalli ƙopar ɗakin Jin motsin mutun, Bakowa bace face angel
Jikinta na sanye da jallabiya, daidai tsayinta, Tayi rolling mayafi akanta,

“Daddy sannu da dawowa Nayi missing ɗinka sosai” ta ambaci hakan fuskarta ɗauke da murmu shi, buɗe mata hannayen shi ya yi alamar tazo gare shi, da gudu ta ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan kirjin shi, Ya sanya dukkan hannayenshi Ya rungumeta sosai, Yana faɗin”kin sani farin Cikin da bazan ta6a mantawa ba angel, I luv u so much, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin bayyana maki irin ƙaunar da nake yi maki, Allah yabarnmin ke angel, Allah ya kare mun ke daga sharrin maƙiya da mahassada, Allah ya yi maki albarka”
Amsa ma shi tadinga yi da ameen daddy, kusan mintuna goma suna manne da juna, batare daya raba jikin shi daga nata ba, wani irin yanayi yake ji attare da shi, sam baya son yana tuna mutuwa, Saboda yasan ita kaɗaice zata Iya raba shi da angel, ko yana so ko bai so, dolene bayan ita kuma sai wata ƙaddarar rayuwar wadda baya fata,

Ɗagowa tayi daga Jikin shi ta sanya hannu tana goge mashi tears ɗin dake sauka akan fuskar shi”daddy kadaina pls, banason ganin hawayen ka na zuba”

Kallonta ya yi da runannun idanuwan shi waɗanda su ka yi jawur da su, sam ya kasa furta mata komai,

Huggin ɗinshi ta ƙarayi tana shafa sumar kanshi, bacci ya soma Ji hakan yasa shi miƙewa Ya lalla6a ya haye saman gadonta, ya kwanta duk da ya yi mashi ƙanƙanta,

Gefen gadon ta zauna tana kallon shi, jikinta duk ya yi sanyi tace”daddy baka lafiya”?

Eyes ɗinshi arufe yace”kinci abinci”?

“Naci a wurin aunty aneelerh, Ko inje in kar6o maka naka” girgiza mata kai yayi”a’a,Bana jin yunwa, kizo mu kwanta muyi bacci”

Ƙarasa hawa saman gadon ta yi a gefen shi ta kwanta, Ya sanya hannu ya janyo ta jikin shi, Cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da su,

Wuraren ƙarfe 4 ya farka daga Baccin, Lokacin a nata kiraye kirayen sallar la’asar, saukowa daga saman gadon yai tare da nufar toilet ɗin ɗakin ta Ya shiga ciki,

After some minutes ya fito yana share ruwan alwalar dake a fuskarshi, Kafin ya nufi inda angel take a kwance tana bacci,

Cikin sanyin murya ya soma kiran sunanta”My angel!”shiru bata motsa ba, hannu yasa tare da ɗan bubbuga ƙafarta, nan take ta farka tana mutsu mutsun bude idanuwanta,

“Lokacin Sallah yayi, Ki ta shi kije ki yi alwala, ni zan tafi masallaci”

Muryarta a disashe tace mashi”a dawo lpy daddy,”

Bayan tafiyar shi, ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,

Jim kaɗan tafito ɗaure da alwala, ta ɗauko carpet ta shimfiɗa, Ta zura hijab ajikinta a tsanake ta soma Yin sallah,

Lokacin data idar da sallar zama tayi saman dardumar tana karatun alqur’ani mai girma daga cikin kanta,

Tana cikin yin qira’ar, Ya dawo daga masallaci, murmushi yasaki Yayin da ya ke shigowa Cikin ɗakin, Ba ƙaramin daɗi yake ji ba aduk lokacin daya sameta, Saman darduma tana Yin sallah ko tana yin karatun al’qur’ani mai girma,

Sai da takai ƙarshen ayar da ta janyo tukunna ta juyo ta kalleshi”daddy sannu da dawowo”

“Yawwa daughter, Kin daiyi mana addu’a ko”? jinjina mashi kai tayi”eh,Ae kullum sai nayi”
“Haka nakeson ji, My daughter”

Shiru ya ɗanyi kafin Yace”Zamu fita tare da daddy uzair ɗinki, Zaki zauna a gida ko In kai ki wurin aneelerh”?

“Daddy bazaka tafi dani ba” aɗan shagwa6e tayi maganar,
“Am sorry, Ba cikin gari bane bazan iya yin tafiya mai nisa dake ba,”

Tuni idonta sun Ciko tab da kwalla sam bataso yana tafiya yana barinta a gida, musamman yanzu da babu school, islamiyace kaɗai yau kuma Alhamis ne basa zuwa da juma’a,

“Dan Allah daddy…….”tunkafin ta ƙarasa yayi saurin katse mata hanzarinta”yi mun shiru nace maki ba cikin gari bane,”

Shiru tayi Ƴar kwallar da take 6oyewa ta soma gangarowa akan fuskarta,

Ƙarasawa Yayi tare da sanya hannayen shi gaba ɗaya ya ɗauketa, yana ɗan bubbuga bayanta”Idan kikayi mun kuka Allah zan fasa zuwa buzaye dake ne”
Cikin shessheƙar tace”bazanyi ba”
“Haka nakeson ji my angel”
Sauke ta ƙasa ya yi tare da ruƙo hanunta, suka fito daga ɗakin ya ja ƙofar ta rufe, Kaitsaye suka nufi gidansu aneelerh, lokacin da suka shiga falon gidan a tsaye suka gansu shida Aneelerh, Ya kammala shirin shi cikin boyel, aneelerh kuma na sanye cikin Turkish dress, Riga da wando blue, ta ɗaure kanta da mayafin kayan.

Gaisawa suka fara yi da aneelerh kafin Ya damƙa mata angel,

Batare da 6ata lokaci ba, su ka yi mata sallama atare a cikin motar Uzair suka tafi,

Saman Sofa suka zauna ita da aneeleerh,
“Kina jin yunwa”? ɗaga mata kai tayi alamar eh,
“Hawayen menene akan fuskarki”?tayi tambayar tana kallon fuskarta,
“Daddy inata roƙon shi ya tafi dani amma ya ƙiya”
Murmushi aneelerh tayi”Shine kike kuka? idan ki ka yi haƙuri ae ba kwana zasuyi ba,” ta ambaci hakan tare da miƙewa ta nufi kitchen,

Kishingiɗawa angel tayi tana jiran dawowarta, fitowa aneelerh tayi daga Cikin kitchen ɗin hannunta ɗauke da plate, mai ɗauke da farfesun naman Kaza, da alama ba’ajima da kammalashi ba, don sai huci ke tashi ga ƙamshi,

A saman table ta ɗaura plate ɗin,tare da samun wuri gefen angel ta zauna,

Jin ƙamshi Yasa angel mikewa ta gyara zamanta,
“Aunty aneelerh,duk ke kikayi wannan”?
“A’a bani nayi ba, Ana ce ta yi shi”
Yatsina fuska angel tayi”wannan matar kamar munafuka,Ni ban yadda da ita ba Allah, Kullum tana aɗaki kunshe, Ita bata fitowa sai zata yi girki ko gyaran gida,
Dariya sosai Aneelerh tayi”Zaki fara tsegumin naki ko”?
Ta6e baki ta ɗanyi, tare da zura hannu cikin plate din tana ɗan tsakurar naman, Har wani jinjina kai take yi saboda daɗin da ya kai mata karo, zuba mata ido aneelerh tayi tana kallonta,
“Aunty aneelerh,”
“Menene”?
“Mutane dayawa suna cewa Ni matar Manyace, irin matan masu kuɗinnan, Allah idan na girma mai kuɗi zan aura, inda zanje in huta, Bani aikin komai sai dai Ƴan aiki suyi mun ina daga kwance,”
Tunda ta soma zuba, Aneelerh ta ƙura mata ido tana kallonta,Wato Zuzuta kyanta da mutane suke yi suna cewa ita matar manya ce, Shine ta haddace maganarsu acikin kanta, har tafara sawa ranta aure inda zata huta,
“Bakya son talaka”baneelerh ce ta jefa mata tambayar,
Yatsina fuskata tayi”ae annabima yace mu nemi tsari da talauci,”

Murmushi Aneelerh tasaki, tasan halin angel da gaddama, shiyasa bata ja zancen da tsayi ba,
“kinga daddy yaƙi yin aure, Da a lama sai na fara haifa mashi ƴan jikoki” takai karshen maganar tana sakin ƴar dariya,
Murmushi aneelerh tasa ki a ranta tana mamakin yadda take maganar aure har da haihuwa ko kunya babu halin angle sai ita kafin tace”mai zai hana kisa ma shi matar aure”
ɗan zaro ido tayi bakinta cunkushe da naman data tura, ahaka tace”Tab, salon tazo ta mallake mun daddyna, Ƙwara yayi ta zaman shi a haka babu auran,”dariya sosai aneelerh tayi”Angel kenan mai abun ban mamaki” ta ambaci hakan tare da mikewa tace”zan shiga daga ciki inaso na kwanta, Idan kin kammala ci, Ki kai plate ɗin a kitchen, kizo ki same ni a ɗaki muyi karatun haddar da aka baki islamiyya”

Ta amsa mata da toh”sai da angel ta kammala shan farfesun tukunna ta miƙe ta nufi kitchen, Bayan ta ajiye plate din,ta fito ta nufi ɗakin aneelerh
*** *** *** *** *** **

A 6angaransu taj kuwa, gidan wani abokinsu suka fara zuwa kai mashi ziyara, sun jima a gidan bayan sun baro gidan abokin nasu, Suka Nufi gidan Gonar uncle abdallah, da niyar suje su duba yadda komai ke tafiya, Kafin su dawo gida,

Gidan Gonar acan bayan gari yake cikin daji, lokacin da motar su ta ƙarasa Cikin dajin, Adai dai bakin Gidan gonar uzair ya yi parking ɗin motar, Wani tsohone daga waje saman benci yana sauraron radio da a lama shine ke kula da gidan Gonar,

Tunkafin Suyi parking ɗin motar, Ya miƙe yana ta faman washe baki don ya gane motar uzair ce,

At same time suka fito daga Cikin motar, A hanzar ce suka ƙarasa inda yake a tsaye, Jikin shi na sanye da riga da wando na yadi, Zariyar wandon har kasa kamar wani ta6a66e, Gashin kanshi duk hurhurace, Fari ne sol kanshi da rawani irin na buzaye,

“A’a wa nake gani kamar Tajo?’ cike da mamaki ya yi maganar yana kallon tajuddeen, miƙa mashi hannu taj yayi fuskar shi ɗauke da fara’a yace”Nine mana, baba buzu ashe kana a raye” ya yi maganar da zolaya,
“Amana batace haka ba tajo,Yaushe rabon da in sanyaka a idanuwana tun kana ɗan matashi,”
“Yau dai gani nazo, kuma bada wuri zamu tafi ba, har sai ka gaji da gani na,” yakai ƙarshen maganar yana dariya, shima dariyar ya yi”wuni kuka zo mun kenan aikuwa har masara zan gasa mana muci muna fira,

Kafin taj ya yi magana uzair yace
“Fatan mun same ku cikin koshin lafiya, Ya komai ke tafiya”
Tsohon yace”alhamdulillah, Ku ƙaraso mu zagaya cikin gonakin mana,” Gaba ya yi su ka bi bayan shi, suna ɗan tattauna fira atsakaninsu”

Sunjima suna kewaye gonakin har cikin gidan gonar suka shiga, koda aka fara kiran sallar Magrib, atare da baba buzu su ka yi sallar Acikin gidan gonar, ba su tashi tafiya ba, sai bayan da akayi sallar Isha’e, tukunna su ka yi sallama da shi,

Taj ne ya kar6i driving ɗin, Uzair na gefen shi, motar su na haurawa saman titi, wasu dankara dankaran motoci masu black tinted suka shararo da gudun gaske kusan su shida, A jere suka Kurɗaɗa cikin dajin,

Duk akan idonsu tajuddeen, Da mamaki akan fuskar Uzair yace”kosu wanene a cikin motocin can? Kuma ina zasu dosa ne? Ni dai a iya sanina babu wani gida dake acikin dajin nan,”

Taj yace”May be ko wani party ne za su yi, ba abun mamaki bane”

“That’s impossible, Party kuma arasa inda za’ayi shi duk faɗin garin mu sai cikin dajin nan, Gaskiya ni ban yadda ba Allah, tabbas inaso nasan me zasu yi a cikin dajin can, Ka juya motar mubi bayan su”acewar uzair,

Taj yace”Ni bazan bi su ba, kawai daga ganin motoci sun shiga daji sai kace mubi su, for what reason?

“Nidai kawai kayi a bunda nace maka, Kada ka manta mu fa ƴan jarida ne,

rai a ɗan 6ace taj yace”Mu ƴan jarida ne, Ba jami’an sirri ba, Don haka ni bazan bisu ba, Gida zamu koma”

Yana ƙoƙarin juya sitiyarin Uzair ya damƙi hannun shi, juyowa yayi suka haɗa ido,

“Ka yi abunda nace maka, In ba so ka ke in sauka daga Cikin motar nan ba, in bayansu da ƙafafuna”

Sanin kafiyar Uzair ne, Yasa Taj Juya motar Ya nufi Cikin dajin, Zuciyar shi duk a jagule don ba ƙaramin takura shi uzair yayi ba,

“Ka rage gudun motar” acewar uzair, a takure taj ya rage gudun motar, yayin da yake kurɗaɗawa cikin dajin har Allah ya kawo shi wurin da waɗannan danƙara danƙaran motocin su ka yi parking, A jere su shida a bakin wata ƙorama,

Daga nesa dasu taj yayi parking ɗin motarsu, tare da kashe hasken motar su, don kada su gansu, Amma su suna iya hangensu saboda sunbar nasu hasken motocin su a kunne,

Natsuwa su ka yi suna jiran ganin Su wanene zasu fito daga Cikin motocin,

Kusan ƴan mintuna, kafin a buɗe motocin, kamar a shirin film suka fito a tare, Kowannansu Na sanye da suits ajikin shi black colour, fuskokinsu na sanye da mask, daga ganin bodyguards ne, At same suka buɗe murfin Back seat na motocin,

Wasu Manyan mutanene suka soma saukowa daga Cikin motocin, kowannan su na sanye Cikin shigar hausawa, Daga ganinsu dattawane sun kwan biyu aduniya,

Kallon juna taj da uzair sukayi a lokaci ɗaya kafin suka mayar da hankalinsu kan abunda suke kallo,

Bayan Alhazawan sun kammala fitowa daga Cikin motar, Ɗaya daga Cikin bodyguards ɗin Ya zagaya bayan motar ƙarshe, Ya buɗe boot ɗinta, Hannu ya sanya ciki tare da danƙo rigar Wani bawan Allah dake naɗe cikin boot ɗin, Ya wurgo shi waje, Gaba ɗaya mutumin ya kife ƙasa, Rawanin dake naɗe a kan shi Ya warware, Jikin shi sai kerma yake yi, kamar wanda sanyi ya kama, daga ganin shi dai Malami ne, duba da irin shigar shi,Jallabiyace ga kuma rawanin shi, hada cazbaha a hannun shi lokacin daya ɗago, La66an shi nata kerma Yana ambaton”Innallahi wa’inna ilaihirraji’in, La’ila ha’illah anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin,’duk yabi ya susuce,

Cike da taku irin na majiya karfi, Bodyguard ɗin ya kuma takawa Zuwa mota ta biyun ƙarshe Ya buɗeta,

Wasu ƙananun Yara ne guda biyu, Gwanin ban tausa yi sun ƙankame junansu mace da namiji, Sun cunkushe acikin boot ɗin,Yadda kasan irin kifin gwangwanin nan,

Damƙo wuyan rigunan jikinsu yayi tare da ɗago dasu Ya wurgo dasu ƙasa, Gaba ɗaya suka kife saman Ciyayin dake a wurin,Sautin kukansu ya ƙarade wurin, Miƙewa Yaran su ka yi da gudun gaske suka nufi wannan malamin daga gani ubansu ne, Rungumesu ya yi a jikinshi sunata kuka, A ƙalla macen bazata wuce shekara Takwas ba, Namijin kuma goma,

Tsananin tsoro ne Bayyane akan fuskokin su, Hankalinsu amatuƙar tashe yake, Daga gani bada shiri aka ɗaukosu ba, Saboda kayan dake a jikin yaran duk na bacci ne, Ita macen ko kalli babu a kanta, ɗan kitson Shukkun da akayi matane, ƙafafuwansu ko takalma babu,

Ƙawanya waɗannan Alhazawan Sukayi masu, Suka sanya su a tsakiya, Yayin da bodyguard ɗin ke a bayansu,

Wani irin kallo suke binsu dashi, kafin daga bisani wani dattijo daga cikin alhazawan Ya soma magana”Malam wa kake da suna”?muryar na kerma Malamin yace”Jazuli”

Jinjina kai dattijon yayi”sau nawa ina jan kunnanka”?

“Sau biyu” cikin shessheƙar kuka ya yi maganar,

“Okey,Saboda kafiya da taurin kai irin naka Baka daddaraba ka sake shiga hurumina ko? Meyasa ka tsananta bincike akaina? Ka sanni ne? ko ina da wata alaƙa dakai ne?ya yi tambayar idonshi akan malamin

Shiru Malam Jazuli yayi, yana ta faman mazurai, Hannunshi bibbiyu ya tallabe ƴa’ƴan shi,

“Koda zaku cutar dani, Ina roƙan alfarma ɗaya a wurinku, dan Allah kada ku ta6a ƴa’ƴana,”

Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayan su, mai sautin gaske,

Taj da uzair dake la6e acikin mota suna kallonsu, Tuni sunsha jinin jikinsu, buɗe murfin motar su uzair ya yi da niyar ya fita, da sauri taj ya ruƙo Hannnunshi murya ƙasa ƙasa yace”baka da hankali ne, Idan suka kama mu fa”
Uzair yace”bana jin abunda suke cewa, dole na fita” ya zame hannunshi daga ruƙon da taj yayi mashi, yasa kai ya fuce daga Cikin motar, kasa zama Cikin motar ya yi ya ƙwammace yabi bayan uzair komai zai faru ya faru, Buɗe motar ya yi tare da fitowa Yabi bayan Uzair Cikin sanɗa suke tafiya har suka ƙaraso gab da su, a bayan wata gabjejiyar bishiya, suka la6e suna kallon su,ɗan Jarida da kasada,

“Nifa inaga,Yakamata mu tafi uzair”acewar Taj,
Girgiza kai uzair yayi”Kaɗan jira muga Mai zasuyi ma shi, bari ma na ɗauki video,”yana ƙokarin zaro waya, Taj ya buge hannunshi”ashe baka da hankali, So kake hasken camera ya tona mana asiri, ba don yaso ba Ya haƙura da ɗaukar video ɗin,

Suna Cikin yin Maganar nan, Su ka ji wani irin gurnani mai matuƙar tsoratarwa, A ruɗe suka ɗago suna kallon su,

Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take yazama wata irin halitta mai matuƙar tsoratarwa,Ya shiga girgiza jikinshi Yana wani irin gurnani,

(Tashin hankalin da ba’a sama shi date,😳😳😳 mu haɗu on monday don jin yadda zata kaya, wanda suka shirya yin payment zasu iya yi mun magana 500 ne, 08103884440)

Leave a Reply

Back to top button