Auren Wucin Gadi 56
CHAPTER 56
Suna gama wayan ta sauke jiki a sanyaye take sanar dasu abunda ke faruwa da mijin yayar tata kowa dake wajen sai da jikinsa yayi sanyi kuma sun kaɗu dajin wai cid aka jedashi wannan yana nuni da cewa case ɗin ba karami case baneba tunda harda su cid aciki”Anty hajia ko zaki kira yah faisal ki sanar dashi abunda yake faruwa cewar Aisha”nima abunda zancd kenan kika rigani inji malika.
Koda Anty hajiya takira wayan faisal cemata yayi yanzu haka suna cid office shida Ahmad amma bawani feedback tunda aka shiga dashi ciki kuma sunnemi gabawa da manya amma babasu wannan daman ba ajiyar xuciya ta sauke kana tace”karka bar ɗan uwanka shi kaɗai katsaya dashi dan ganinka tare dashi ze bashi kwarin gwiwa,amsa mata yayi da In shaa Allah Anty hajia bazan taɓa barin sa shi kaɗai ba duk yanda ake ciki zan kasance dashi,daga haka yakashe wayan.