Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 62

Sponsored Links

CHAPTER 62

Masha Allahu walaƙuwata ubangiji yayi halitta anan besan sanda ya furta hakan a fili ba,yana nan tsaye de har suka zo Aisha ta gaida khalid ya amsa yana zolayarta da cewa”kode gasan kyau zaki bamu sani ba ƙanwas murmushi kawai ta sakar masa tana jan hannun Anty malika dake tsaye saida suka dan gilmashi sannan khalid dake tsaye yana kallon sa yaɗan bigi saman motar da karfi nan Ahmad yayi firgigit yadawo daga duniyar tunani daya tafi sake kallon hanyan babban shagon yayi hajiya hanas din yayi murmushi hajia hanas dake tsaye a gaban sa ta sakar masa dole ya maida mata da murmushi yaƙe ganin yanda yake dan kalle kalle yasata cewa”gasu can sun wuce.

Wayancewa yayi yana cewa”oh na gansu bani acct dinki,ba musu ta karanto masa yasaka nan take sai ga alart zaro ido hajia hanas tayi cike da jin daɗi irin wannan kyautan hakan yasake tabbar mata dacewa lalle aikinta yayi kyau kuma wanda akai domin sa yayaba,dama ance yaba kyauta tukuwici gashi kuwa tagani godiya tashiga yi masa har tana haɗawa da khalid cewan yata yata godiya wajen Alhaji sannan ta juya baya tanasake jaddada masa duk sanda madam takeda bukatar gyaran jiki lalle ko wankin gashi dama ƙitso ko waya kawai yayi ba matsala ko gidane zaje aimata godiya yayi mata ta koma cikin shagon ta cike da murna irin wannan kyauta da tasamu.

Shiko Ahmad ganin yanda khalid ya tsastsare sa da ido yana ƴar dariya ƙasa ƙasa yasake haɗe fuska shi ala dole bayason wargi yace”me kawani tsareni da ido kaman zaka haɗiyeni?

khalid besan sanda wata irin dariya da karfi ya kubce masa ba ganin raina masa hankali Ahmad kesonyi kaman bashine yanzu yagama kallon yarinya dayake kiran Auren wucin gadi yayi da ita ba.

“To malam me nawani haɗa rai ai sai kaje kakira ta mutafi kasan tun tuni su faisal na can mu kaɗai suke jira amma mutum kawani sake baki kana kallon gwailan yariyan da banaji ko ƙirgen dangi ta gama kaida za kawo maka classic lady me nawa westin time kan wannan abar yakare magana yana ɗauke kansa daga kallon inda Aisha da malika ke tsaye jikin motar malika kuma yayi hakan ne kawai dan son kunno da abokin nasa ai kuwa ya kunno,dan wani irin tuƙuƙin bakin cikine ya turniƙe masa zuciya besan sanda yayi kwafa yana ce masa to me zan gani anan ɗin karkaga dan nakawo ta nan anyi mata ƙunshi kadauka wani abunne wannan din hakkine akaina banason ana taron baki yazama itace kaɗai batayi ba,yana kare fadin haka ya yafito malika da hannu shikuma fuuu yakoma cikin mota duk takaici yagama isar sa yama rasa abunda ke masa daɗi khalid ma ya kalle ta haka ina ga wasu kenan haka ake kallonta ji kawai yayi kaman yafasa ma tafiyan da ita wajen yace da malika kawai su koma gida,amma kuma idan ta koma shirin sa ze rushe haka ya danne zuciyar sa.

Malika na isowa yace”jeki kirawota kinsan koma amma kinason ɓatamun rai”yi hakuri bro wallahi tun ɗazu nake fama da ita amma ta kafe bazata wajen wani party da wannan shigar haka ba saide a nema mata hijabi.

Besan sanda yaja wani gajeran tsuka mtsss yana cewa”matsalata da irin waƴannan yaran kenan rashin wayewa to wama ze kalleta a wajen idan munje ana ta manyan mata wake ta gwaila irin dallah malama kizo karki batan lokaci,yanda yayi magana har saida yabasu dariya amma duka suka waske basuyi ba,sai ma khalid ne yace”bara na taimaka maka da wannan yanufi bakin motar malika yasami Aisha tsaye yace”ƙanwas kefa muke jira tuntuni kuma kinzo kin tsaya anan,marairaice fuska tayi tace”wallahi yaya khalid banajin zuwa wajen partyn ne haka”ina ina kanwas saide fa yau ɗaya kiyi hakuri yah faisal ma yace yana jiranki a can gakuma kawarki laila ita tana bakin hanya tana jiran muje madauke ta dan haka kiyi hakuri keɗin kibi motan Ahmad kuje tare nikuma da malika zamu biya ta inda laila ke jiranmu muɗauke ta”amma yah khalid i zamu iya zuwa tare mu dauketa ko?”naa ba zauyu muje dukkan mu mubar ba kede muje kawai kutafi muma gamunan tafe.

Haka Aisha ta hakura zatabi motan Ahmad amma badan saboda tanaso ba dande kawai karta kafe khalid yagani kaman taƙi jin maganar sa ne,har bakin motan ya rakota saida yabude mata gidan gaba tashiga ta zauna khalid harda gyara mata riga saboda tsokala ai kuwa ya tsokalo dan yana ɗagowa yasamu guzurin mugun kallo daga oga Ahmad dake tsaye murmushi yasakar masa dacewa a kular mana da ƙanwa banda tuƙin ganganci dan naga kaman ka haura sama”dallah malam ware kukesa kananun yara suna raina mutane surinƙa ganin kansu daya dakai dakayi magana,dariya khalid yayi malika natayasa duk da tana ɓoye dariyar tata kar yayan nata yagani amma abun ya gagara dan saida dariyar ta fito fili,daƙyar ta danne dariyar tana cewa”yaya in banda abunka ai koda ƙwana daya ka girmi mutum ai ka girme sane balle kaida kaba da shekaru shima yah khalid ɗin yafaɗi hakane kawai dan ya tsokaleka kuma kai kanka kasani har abada ba raini tsakanin mu dakai wallahi ko ita Aishan ma banajin zatayi tunda ba halinta bane,wayan Ahmad ne tayi ringin wannan shine kiran da faisal yamasa na biyar kenan tunda sukazo daukar su Aisha ɗaga wayan yayi yana cewa to malam sauri ba wajen zuwa gamu nan yanzun nan na daukota kasan sha’anin mata komai ƙanƙantar mace wajen wanka kadai sai taɓata a ƙalla minti talati wajen shafa mai ma haka sannan wajen kwalliya wannaan itace uwa uba dan sai taɓata awa guda sannan……”yaushe kazama haka Ahmad faisal ne ya katse shi dafadin hakan murmushin gefen baki Ahmad yayi yana maikafe Aisha dake zaune a mota da ido duk da kallon gefen ido yake binta dashi sai kawai yakashe wayan yana maida abun sa cikin aljuhu shima yashiga motan ya zauna saida yamata key yabata wuta sannan ya cillata saman kwalta dama tuni khalid sun tafi da motar malika tunda yasa Aisha a motar Ahmad ya anshi key daga hannun malikan bayan yagama tsokalan Ahmad yatafi.

Saida ya daidai nutsuwar sa sannan ya kalli Aisha yana taɓe baki yace”wannan wace iriyar shigace dako tsari babu,ɗagowa tayi ta kalleshi ganin ya zuba mata ido ko kifyawa bayayi tayi saurin cewa”na shiga uku kalli gaban ka yanda tayi dole yasa ka tsorata kokai wayene ai kuwa da sauri Ahmad yamai da duban sa gaba yana kaucewa wani mai mashin ajiyar zuciya duka sauke a tare tana tura baki gaba tana cewa mutum in be iya tuƙi ba ai ba dole sai yayi ba.

“Magana kike na?
“A’a ni bance komai ba ta amsa tana kauda kanta gefe ganin taƙi kallon inda yake shikuma be gama kallon kwalliyar tata ba,tuki yake da daya hannun sa sannan yakai daya hannun ya kamo hannun ta yakai bakin sa yamanna mata kiss yana dan kallon jan ƙunshin yatsun hannun ta da zanen fukawan sun zauna ɗas gwanin burgewa yace”inason ganin hannun mace da kunshi ba karamin burgeni yake ba,ko sanda ina yaro duk sanda Ammi na tayi kunshi haka zan sakata gaba ina kallo shisa koda yaushe nake addu’ar Allah yabani mace mai son ƙunshi”ai kuwa addu’ar ka bata harɓo ba dan ni bana daga cikin masuson yinta koda ina so kaima kanka kasan bazanyi duk wani abu da ze burgeka a zaman wucin gadi da zamuyi ba,ta ƙatseshi da fadin hakan.

Shi Ahmad har mamakin Aisha yake duk sanda kafaɗa mata wani abu kaman dama amsan na bakinta nan take zata baka kuma ta fuske abunta kaman ba itace tayi maganan ba.

Yana riƙe da hannun nata yana murzawa a hankali hankali duk yanda taso ƙwatan hannun nata hanata yayi ƙarshema cemata yayi sadakin da su Ammin sa suka bada yake taɓawa ai ita din halalin sace dole ta haƙura amma duk yasakar mata kasala dan wani irin yanayi da batasani daba tasoma tsintar kanta cikin muryan menuna mutum yanason yin kuka tasoma magana”ai wannan kwartonci ne aina aka halasta maka yin hakan wannan ai rashin sanin darajan mutum ne kawai kanason ɓatani a banza kabari ma bagade yanzu zamuje wajen wacce kakeso take sonka sai kayi mata amma a ƙarancin shekaruna kakeson koyamun abubuwan banza na rashin ɗa’a sai ga hawaye sharr sharr sun soma zubomata daga ƙurmin idonta,parkin motan yayi dayake yariga da yashigo cikin hotel din da ake gudanar da party,dan waigowa yayi ya kalle ta kaman bazece komai ba ganin kukan take bilhakki da gaskiya yace”malama ai saiki goge hawayenki mushiga ciki saura kinuna ƙauyancin ki a fili ɗan riƙe miki hannu kawai danayi duk kinwani sake kaman fulawa da tasha bugu,wani irin haushin maganan nasa yabata sai kawai tasake fashe masa da kuka na gaske watom itace ma takai kanta gareshi ganin yanzun kan da gaske take kuka dole yashiga rarrashinta yace”wai ke ɓakisan wasa bane nifa wasa da wasa nake miki ai kedin mai sa’ace tunda kika sameni matsayin miji kinyi goshi saiki gode Allah batasan sanda ta ɓalla masa harara ba tace”ko kuma kaine kayi sa’an samu na matsayin mata ba badan wannan kaddararren aurenka na wucin gadin nan ba da yanzu haka ina dubai tare da mijina abun sona amma saboda wannan auren naka gani a inda basan darajata ba sa….wani irin tsawa ya dakamata saurin rufe bakinta tayi da tafukan hannunta duka biyu ta zaro idon ta waje kaman zasu fado kasa,matseta yayi jikin set ɗin yasaka hannun sa cikin rigarta ta baya bayan ya zuge zip din rigar a rikice Aisha yasoma yimasa magiya”dan darajan iyayen ka kayi hakuri wallahi kuskurene bakina ne ya tsubuce bazan sake maka rashin kunya ba na tuba nabi Allah nabika yaya Ahmadin Ammi.

Dariya ma maganan tata taso bashi amma ya fuske yace”a’a bari kawai nayi maganin bakin rashin kunyan yana faɗa yaciro hannun daga bayanta yayi mata wani irin kyakkyawan runguma ringin ɗin wayansa shiya katsashi daga abunda yayi niya sai da yasaita kansa sannan ya dauka murya ashake kaman me mura y amsa da gamu a parkin lot yana gama fadin haka ya kashe wayan a dayan bangaren faisal rike wayan kawai yayi yabi screen din waya da kallo kaman ze ga Ahmad din taciki to mai yake damun Ahmad kuma yafadi haka yafi akirga sai can ya wayance yana kallon khalid yayi yar dariya yace”kaida malika kuge can parkin lot ku taho dasu sai mushiga dukka mu atare.

Haka kuwa aikai suna isa suka iske Ahmad yayi tsaye yana maida numfashi ita kuma Aisha ta hada kai da gwaiwa sai kuka take suna zuwa khalid yace”me kayima ƴar mutane take irin wannan kuka haka?

Kallon kai waye Ahmad ya jefi khalid dashi sannan yace”tambayeta mana me zanyi da wannan gwailan mema takeda da zantaɓa ajikinta mamuni grass dinta dako lemun tsami bekai ba zantaɓa kome?

Duka shiru sukai jin abunda yace ba lefin kabane lefi nane dana tursasa mata binka amma ba damuwa cewar khalid da ranshi yagama baci da rainin hankalin Ahmad din kasa yarinya mutane kuka amma idan an tambayeka kanuna bakasan komai ba.

Dakyar malika ta rarrasheta tare da khalid ta hakura malika tasake gyara mata fuska sannan ne tafito daga cikin motan suka nufi zuwa inda sauran abokan sake jiran su duk wannan abun da akeyi na rarrashi Aisha Ahmad na tsaye yaki tafiya Anty malika ce ta duka daidai kunnen ta taraɗa mata wani abu data sakata sakin fuskanta tana murmusawa a haka suka jera suka karasa ciki tun daga wajen ajiye motoci zai tabbatar maka da bikin na ƴar gatane duba da yanda aka faka motoci masu kyau da dama sanda suka isa inda su faisal ke tsaye tun dazu dr sapwan yana ganin su yace”sannunka da shukamu da kai tundazu kata nadi abunda cewa gun amaryarka tunda acike take dakai saura kaɗan ta fashe…zungurinsa da nawwar yayi shiya sashi yin shiru duk da besan ma’anarsa nayin hakan ba gaishe su Aisha tashiga yi daya bayan daya suna amsa mata cikin sakin fuska bayan gama gaisuwar su suka dunguma zuwa ciki inda ake gudanar da fatin ai suna sako kai DJ yasaki kiɗa Mc kuna nasanar da karasowan ango da tawagan sa take hankulan mutane baki ɗaya yayo kansu Ahmad shine a gaba hannunsa sarkafe dana Aisha dake neman yanda zata kwaci hannun ta bayan sa dr sapwan ne da bebinsa latifa sai khalid da laila sai kuma nawwar da malika daka mara musu baya sai faisal shine karshe tunda Ahmad yasoko kai hall din baka iya ganin komai sai hasken camara da aka soma haska su tako ina madu waya nayi masuyin video ma nayi rikicewa Aisha tayi had batasan sanda ta kankame hannun nasa ba,yanda suka shigo wajen duk kushen mai kushe karyansa yace basuyi kyauba kuma gasu sun dace da junansu kai kace itace ma amaryan saboda yanda ta haɗun sannan yanda suka shigo da tsari basu da yawa da gani kasan antsara abunne cikin wayewa.

Ahmad saida yakai Aisha yanema mata maxauni yaja mata kugera ta zauna sannan suma sauran yan tawagan nasa suka samawa kansu wajen zama,sannan ne ango yanufi inda amaryar sa ke zaune tacika tayi fam kaman zata fashe gefe daya kuma kus kus kakeji kananun maganganu suna tashi.

Ahmad sobada iya taku yana ƙarasawa inda amarya basma take ya riko hannunta ya sumbata yana cewa”amun afuwa bisa rashin ganina da bakiyi a kan lokaci ba,kafin basma ta amsa sai ga wani ɗan jarida yaƙaraso inda suke yana cewa”Ahmad Alh badamasi a ƙa’ida akanga ango atare da amaryarsa yayi gudanar da wani irin shagaling biki tsaɓanin kai da yanzu muka ganka da wata ko zamu iya sanin wace alaqa ke tsakaninka da ita?

Kallon inda Aisha ke zaune yayi sannan ya maida duban sa ga basma data kafesa da ido sake sumbatar hannun nata yayi a karo na biyu yana kallon cikin idonta yace”ita din takasance Abokiyata ce
“Abokiya ɗan jaridan ya maimaita sannan yace amma mr Ahmad Abota iri irine wanne kake nufi daga ciki?
Murmushin gefen baki yayi sannan yace”duk wanda kaga yadace to shine ze sake magana ya ɗaga masa hannu yace karka sake mun wata tambaya idan kana da shima zaka iya adana abunka dan zema amfani wani jiƙon.

Dole dan jaridan yabar wajen bawai dan gamsu da amsan da Ahmad din yabashi ba,bayan barin dan jaridan wajen basma zatayi magana Ahmad yarigata da cewar wala tajassasu kada ki cika son bincike dan idan kikace zakiyi hakan wataran zaki binciko abunda ze hanaki bacci.

Daga haka suka maida hankulansu wajen da ƴan mata da samarin dake rawa hannuwan su sarkafe da najuna lokaci lokaci Ahmad yakan ɗago ya kalli Aisha dake zaune dasu malika da laila itama kuwa kaman baki duk sanda yadago ze kalleta sai sun haɗa ido,mc ne yawage baki cikin loudspeaker yana kiran ana neman ango da amaryarsa nan take suka bayyana tsakiyan fili inda akasake kiɗa nan da nan abokan ango da amarya suka taso suka soma liƙi yayinda amarya basma tazage tatiƙi rawarta kaman ba gobe dan ace warta idan batayi yau ba yaushe zatayi maƙale Ahmad tayi ta juya masa baya tana goga masa maxaune tana wani irin rawa matsari Aisha dake zaune taƙura masu ido haka kawai taji ranta naɓaci da abunda basma keyi da sunan rawa tsab tamike tafita daga wajen basma tabita da wani irin mugun harara dan dama duk motsinta tana hankalce da ita,kuma ko rawan da gayya tayi.

Leave a Reply

Back to top button