Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 3-4

Sponsored Links

Page 🖤3••4🖤

 

“Karka damu baba dama bakwana kawai nazoyi,hankalin ka zai kwanta sosai,domin a kallah kusan Shekara guda ban juyo ba”
“Hmmm wannan auren ma kenan niyyar kasheshi kikayi koh”
“Ahah baba dama ba aurene irin kowanne ba,na yarjejeniyane akwai ranar mutuwar sa”
“Kai Addah Bombee ko shiyasa wannan matar tazo nemanki ran…..”
Kafin tagama magana inna laari ta buge bakinta tareda zabga mata harara.
“Kaga malm ba wannan ba,tazo ta fice daga gidannan,bankwanan ya ishemu haka,kada ta shafa mana tsiyar datake tattareda ita”
Runtse ido Bombee tayi jin abinda inna laari ta faɗa,saidai maimakon hakan yasaka shiga yanayi na baƙin ciki ko kuma karya lagonta,saima tunzurata daya sakeyi,bude shiɗayen idanunta tayi akan inna laari tareda cewa.
“Ke na gama yimiki bankwananki,amma bangamawa wacce tayimin shamaki da ɗaiɗaita birbishinki ba wato innata,dan haka inaga ko kinfi kuturu naci baki isa hanani shiga na ganta ba,kokai kin ƙarisata bansani ba?…… Inaaa bakida wannan ƙarfin gwiwar tukunna,har yanzu dai ina matsayin ƙadangariyar data zauna a miki akan tulunki”
Hanyar dakin innarta tanufa,wacce take zaune kaman koyaushe akan kujera tanajin abinda Bombee takeyi,saidai batada ikon kallonta ko kuma maida mata magana.
A gabanta ta tsugunna tareda daukar hannunta tariƙe akan nata.
“Inna ni zan tafi,amma zan dawo ko domin ke,dan bawai natafi kenan ba,duk yadda zanyi sainayi wajen ganin nagano mai yake damunki,wannan shine kaɗai burina daban cikaba a wannan garin”
Jijjiga kai Danejo tayi da sauri,tareda matse hannun Bombee cikin nata,ma’ana karta dawo kenan kaman yanda take ikirari.
“Ahah inna zan dawo,ko badan aure bama saidan idan lokacinsa ya ƙare,domin ba aurene dama na zama ba,kedai kijira dawowata inna,kafin na tafi zan tabbatar bata isa yimiki komai ba har na dawo,ni banyadda da wannan matar ba sam inna,mutanene ke ganinta ta arziki,amma jikina yana faɗamin sai an bincika garinnan kaf kafin a samu ya ita wajen shu’umanci,tana da baƙin ruhi a tattareda ita,wanda inajinsa idan mutum yana aiki da aljanu,ko kuma akwai shihiri a jikinsa”
Itadai inna Danejo duk abinda Bombee take faɗa tana jinta,amma batada ikon maida mata magana,har tagama sambatunta a cewarta bankwana takeyiwa innar tata.
Saida ta gama kafin ta tashi tafito daga ɗakin,lokacin data fito mlm Ahmadu bayanan ya fita,kokuma ya shiga ɗakinsa. Harara inna laari tasake mata itama ta rama,hadda nunawa da hannunta inta dawo zata yanke mata kai.
Inna laari tana ganin Bombee tafita a gidan tasaki wata ajiyar zuciya.
“Lallai tsugunne bata ƙareba,da sauran rina a kaba”
Ajiye wankin datake tayi tareda tashi tsaye,lelleƙawa tayi ta tabbatar babu kowa a kusada ita kafin tashige ɗakinta da sauri.
Gadonta na ƙarfe ta ɗaga tareda ɗakko wata baƙar tukunyah dakuma wani ƙaton madubi,wanda yayi mutum a tsaye tsayinsa.
Jinginashi tayi a jikin katangar ɗakin,kana ta buɗe jan ƙyallen da aka rufe bakin tukunyar dashi.
Wasu kalmomi tafara karantawa cikin wani yare mai kamada da dalasumai,kafin wani lokaci kuwa tukunyar tafara tafasa shuuuuu wani abu yana fita daga cikinta kaman baƙin hayaƙi.
Shiga madubin dayake gabanta yafarayi,wanda kana gani kasan ba madubine na Allah da annabi ba,domin koda mutum ya tsayah a gabansa baya bada hoto kaman sauran madubai.
Wata mata ce tafara bayyana a jikin madubin,tana ɗauke da jajayen kaya masu kamada na saƙi,ƙyaƙyƙyawace da kana gani kasan ba kyaune na Zahiri ba,sannan fuskarta tana ɗauke da kalar mugunta sosai,wanda baƙin kwallin datayi ado dashi ma yaƙarawa siffartata fitowa da ainihin mungun kallonta bayyana a fili.
Kallon inna laari take wacce take tsugunne a gaban madubin tayi sujjada tamkar taga kashi.
“Meyasa zakiyi ƙirana a yanzu ina tsaka dayin wani aiki?”
“Eh ranki yadaɗe shugabar matsafa ZILIYYAH nabar kowa nabiki ke kaɗai,dama wannan yarinyar ne da kikayi aiki a kanta tsawon lokaci,ta fitine ni kullum barazana takemin idan muka haɗu,wannan dalilinne yasa na saka Mijina korarta,to wani lokacin har a mafarki take zuwamin”
“Hhhhhh laari tun ba’aje ko ina ba harkinyi nadamar zabinki??,duk aikin daza’ayi miki zabi biyu ake baki,kike daukar daya. Lokacin dazan fanɗarar da yarinyar nan nasaka mungun halinta ya zaga duniyah,saida na cemiki shin na tura mata aljanu ko kuma na kasheta? Kika zabi na juyah tunanin ta,haka ma ga mahaifiyar ta,muncemiki mu kasheta komu nakasa ta,kika zabi a nakasa ta.
Jaririn da aka haifane kaɗai kika buƙaci a kasheshi mu kwashe jininsa,kuma munyi miki hakan”
Cikin rawar murya da shiga ha’ula’i Inna laari tasake ƙasƙantar dakai tareda cewa.
“Tabbas nina zaba kam,saboda a lokacin so nake su wahala basuyi mutuwar sauƙi ba labarinsu ya shafe,sona ke suyi dasunsanin shiga cikin gona ta nida mijina,amma yanzu ita yarinyar baza’a iyah kashemin itaba?”
“Wai meyasa kike manta sharadin da muke bakine,kinsan fah duk abinda kike mana na sakarci ƙyaleki mukeyi saboda jikin ƴar uwarki dakika bani nake amfani dashi ta fitowa a gaban ku…..idan na kashesu yanzu to fah duk abinda yake jikinsu kanki zai dawo dukka,shin kin yarda da hakan”
Saurin girgiza kai tayi tareda cewa.
“Ahah ranki ya daɗe banason hakan,shikenan babu dama a kawar dasu yanxu,dana sani da tunda aka kashesu ma”
“Hhhh karki damu munji barazanr da tayimiki,kuma inamai tabbatar miki dagaske takeyi zata aikata,yarinyar tana da ƙarfin ruhi,duk da baƙin Aljanu suna riƙeda ragamar tunanin ta,wani lokacin takan iyah turasu baya,amma zamu kafeta a garin dazata ce mu hanata dawowa harsai kinsamu abinda zamu umarceki ki samo.
Da sune kaɗai zamu iya amfani mu kasheta,batareda aikin damukayi musu yadawo kanki ba”
“Yawwa nasan babu abinda zai gagareki a faɗin duniyar nan(Azubillahi),to shikenan a kafeta a garin,nikuma koma menne zanyi ƙoƙarin samowa kafin ta dawo”
“Wata bishiyace datake rayuwa a Sahara,tanayin aƙalla shekara ɗari biyu a raye,sannan takanyi fure duk bayan shekara biyu,wannan shekarar tayi furenta,kuma nayi amfani dashi a wasu,dan haka dole saidai kijira zuwa nan da wani furen bayan shekara biyu tukunna”
Kana ganin fuskar inna laari kasan abinda aka faɗa bayyi mata,saidai babu yadda zatayi dole tayi jiran hakan. Koƙarin kawar da zancen tayi ta hanyar cewa.
“Uhm nace ba maganin farin jinin innayi fah har yanzu ba’a samu ba”
“Wannan kuma nan da wata shida zanyi miki magana,akwai abinda na shiryah akan ta,inajinta tamkar ƴa nima,ko kinmanta da ƙoƙarin dalasimaina aka samu cikinta….sannan kuma akwai alƙawarin damukayi dake gameda ita tun kafin haihuwarta…..!?
Shuru inna laari tayi tana zazzare ido,wanda yake nuna ta tuno wani abin tashin hankali daya faru da ita,saidai duk da hakan bata tanka dan tasan maganar matsafiyar gaskiyane……(toh fah yaya takene?)
“Hhhhhh nasan bazakice komai ba,saidai abu daya nakeso ki sani shine ba’a tsallake maganata koma waye,sannan ba’ayin yarjejeniya dani a saba,batun wanccar yarinyar kuma ki zuba ido gobe zata bar garinnan,ba jibi ba kaman yanda tace”
Jingina kanta tayi bangon ɗakin tana ɗan jijjiga haidar dayake kan cinyarta,baccine yafara daukarta,can cikin bacci taji ana cewa.
“Kibar garinnna bamason garinnan saikin bar garinnan zaki bar garinnan…………hhhhh mutafi bazamu zauna ba”
Buɗe ido tayi tareda tafe kunnuwanta guda biyun wanda maganar take shiga ciki,ta haddasa mata barazanar fashewar kanta da kuma ciwon kai mai tsanani.
Cize baki tayi har fatar bakinta tana fashewa saboda sakata datayi tsakanin haƙoranta.
“Ku dakata haka ya isahhhh!!!!!”
Tafaɗa da ƙarfi a cikin kanta ba’a zahiri ba,dan hakane kaɗai ta koyi control ɗin muryar datake zugata a cikin kanta wani lokacin.
Jin maganar bata daina bane yasa ta ajiye yaron dayake kan cinyar ta a gefe. Zaman dirshan tayi a tsakiyar gadon tareda rufe idonta kana kuma ta dunƙule hannayenta.
Tunani tafarayi tayanda zatayi blocking maganar da akeyi mata.
“Kudaina damuna kuna takurawa rayuwata,nasan turoku akayi domin ku fitar dani daga garinnan,saboda naje nayi mata gargaɗi koh,hmmm ashe dai tana tsorona. Babu wanda ya isa fitar dani daga cikin garinnan har saidai idan nice nayi niyyar tafiyah”
Bombee tafaɗa cikin kanta cikeda taurin zuciya,wata ƴar dariyah ce ta jiyarci kunnanta mai kamada munafurci.
“”””Haaaar idaaan muka cuutarr da wannnanan…..yyyyaaaarooonn maa baaazaaaki tafiiiibaahhhhh hhhhhhhhhhhh””””
Aka ƙarisa maganar cikin dariyar mugunta.
Saurin buɗe ido Bombee tayi tareda saukeshi akan ɗannata farincikin rayuwarta.
Aikuwa taga alama,dan lokaci guda ya callara ƙara tareda saka kuka a zabure.
“Ahah kubari kada ku tabashi zan tafi,amma fah sai gobe ba yanzu ba,dan yanzu dare yayi”
Haɗiye yawun baƙinciki tayi tareda cigaba da jijjigen ɗannata,dan kana gani kasan batayi niyyar tsayawa da wasan ba,saidan ya hau kan rayuwar ɗantane,ta yarda komai suyi mata akan su tabashi.
“Matsorata kawai,mai yin barazana da wani abun ma yana tsorone”
Bombee tafaɗa a hankali kan fatar bakinta.

Washagari da sassafe Bombee ta shiryah ita da yaronta suka kama hnayar barin garin gembu cikin motarta,saboda ko badan itaba tana tsoron rayuwar ɗan ta,yanzu babu abinda yake cikin ranta sai muradin rabashi daga cikin garin,saboda tasan sun riga sunsan shine masomin karya lagonta a yanzu.

Lubnah ce a kwance akan gadon ta na gidansu tana danne danne a waya, hankalin ta yayi nisa wajen hirar dasuke da ƙwayenta. Ƙara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinne yasaka jan tsaki tareda kawar da dogayen kitson attach ɗin take kanta,kana ta juyo ta kallo ƙofar.
“Miye kuma,ba yanzu kika sharw ɗakin kika fita ba?”
“Ahah hajiya ba wannan bane,wata mai aikice ta zo nemanki daga Gidan mijinki”
Saurin tashi tayi ta zauna tareda fitowa wajen,dan tasan bazata wuce Bishirah ba,dan dama kafin tahowarta jiya tasaka ta kawo mata rohoton duk abinda yafaru a gidan.
Aikuwa ita ɗince tana zaune a ƙasan carpet ɗin falon,tasaka hannunta tana wasa da zare zaren carpet ɗin.
Muryar Lubnah ce tasakata saurin ɗagowa tareda gyara zamanta kaman mai shirin karbar gafara.
“Yaya mai ya faru bayan tahowata daga gidan”
Lubnah tafaɗa bayan ta zauna akan kujerar dake gefenta,cikeda zumuɗin son jin abinda ya faru.
Bishirah bata kai ga magana ba wata dattijuwar mata tashigo falon,tadan manyanta,Barr Na’imah Hashim kenan,mahaifiyar Lubnah.
(Sorry a baya nace mahaifinta ne brr amma mahaifiyar ta ce,shi mahaifinta General ne babba a barikin sojoji Gen Abdu Manga)
Duk da ta manyanta,amma kanaganinta zaka san cewa anyi boko harda bokoko ma. Itama zama tayi a kujerar dake facing ɗinsu,laptop ɗin dake gefenta ta dauka ta ajiye a kan cinyarta,tareda gyara ɗan karamin glass ɗin dake idonta.
“Wannna kuma wacece Daughter?”
“Uhm mommy wacce nasaka ta dunga kaomin rahoton abinda yake faruwa ce,yanzu tazomin inaga da wani labari ne,ke ina jinki mai ya faru bayan na taho?”
Gyara zama Bishirah tayi jin an bata lasisin yin magana.
“Ai wato hajiya dazu naji wani zance wai an gyara anihin sabon part ɗin yallabai na gidan,a can wai amarya zata zauna,har yau ma’aikatanta sunje sun ƙawata part ɗin yadda take buƙatarsa. Sannan wai tunda wacce Hajiya ta taho da ita ba amaryar bace,amaryar bata zo ba sai gobe zata iso tukunna,kuma naji ance hajiya ma shakkarta take,yanda takeyin nan nan da yaran da suka zo dasu”
Zaro ido Lubnah tayi lokacin da mummunan labarin ya doshi kunnnenta,sabon part??? Ita bata koma part ɗin ba tsawo zamanta gidan sai wata kucaka data zo yanxu itace zata buɗe wajen?
Lubnah ta faɗa a ranta cikeda takaici.
Tashi kije zan biyaki idan na dawo,yanzu banida kuɗi a hannuna.
Tashi Bishirah tayi ta rawar jiki tabar gidan bayan tayi musu sallama.
Lubnah kaman jira take,tana ganin tafita tasaka kukan sakarci.
“Ahahahha mommy kingani koh,Allah zan kashe wannan uwar tasa daga ita har wacce ta aura masan,nagaji da kaicinsu danake sha gaskiya”
Hmmm karma ki soma,saboda bakida hankali kina ganin in wata matar tasa ta mutu baza’a zargeki ba ne,meyasa mahaifiyar sa bata aura masa Wannan yarinyar ba(Jawaheer),sai suka aura masa wata can daga wani gari,wacce bata san mai yake faruwa ba,saboda suna so itama ki kasheta ne,wanda baya zarginki ma daga lokacin yafara idan yaga mata uku sun mutu a jere. Kinga lokacin dazasu ɗaureki da igiyar da bazaki iya kuncewa ba,sai su aura masa ita suyi zaman ƙalau an kawar dake,dama suke shayi zan tsayamiki a shari’ah,amma daga lokacin da kika kashe wannan da kuma uwar mijinki to fah abin nima zaimin wuyah. Sauyah salon zamanki dasu zakiyi yanzu,karki kashe kowa,yanzu kiyi amfani da kissa bayan zulungum ma,ki tafiyar da abu tayanda babu mao zarginki,sannan idan sukaga baki kashe wannan ba,to zasuyi ƙoƙarin Jawaheer ma,wanda nasan kinfi tsanarta,a nanne zaki tafiyar da ita a boye batareda kowa ya sani ba,ke daka Kashe mutun shikenan gwanda ka haɗashi da abinda sai ya ƙwammaci ya mutu ma”
“Eh kuma fah hakan mommy to yanzu yakike ganin zanyi kenan”
“Keba mace bace,bakisan yanda zakiyi komai sai kisa kawai,saboda matsoraciya ce ke,bakya tunkarar abu saidai kaimasa hari ta baya,halin ubanki ne sakk dake”
Lubnah taji haushin maganar mommyn tata,amma kuma tasan gaskiya ta faɗa,ita bata jurar bin abu a hankali,takanyi duk abinda zuciyarta ta raya mata ne.
“Toh…. Toh…kinaga fah nadawo gidannan ma har yanzu bai zo nemana ba,taya zan koma kenan?”
“Haka dai zaki ƙare,nace miki komai yafaru ki zauna a gidanki kiga mai akeyi,sannan ki kasa ki tsare amma kinki ji,saiki dawomin kina min kukan sakalci waike kin gaji,kinada kafafu biyu ai kiyi amfani dasu mana ki koma”
“Toh mommy yakike so nayi,aure fah wai ya ƙara,kuma nace yasaketa yaƙi sakinta,idan nayi masa magana bayajin maganata,kaman yanda abbah yake jin taki,narasa yanda zanyi dashi,sainayi da gaske wani lokacin nake samun kansa,gashi inasonsa banison wata a kusada shi,kiji wani sabon tsirin wai a sabon part zata zauna”
“Ke ma saiki koma gobe da wuri ko rigata komawa,ko wanda tazaba kikeso dole tafita kishiga tunda kece babba a gidan,yanzu kiyi shiri ki koma gobe da safe,da badan akwai abinda nakeson haɗamiki ba,da a darennan ma zaki koma”
“Yawwa mommy,zaki kaini wajen bokanyarki,ni wancan zulungum ɗin yanzu bani sonsa sosai”
“Ahah ni kaɗai zanje bazaki bini ba,har yanzu bakiyi wanann girman ba na ganinta,sannan kinsan kafin ki yakice zulungum a jikinki zaki daɗe,tunda yasan yana samu daga gareki,kuma karki damu shima aikinsa yana ci sosai,kece ma zaki bawa wasu labari”
“Ni naso yazo dakansa ya ɗaukeni,baya wai na koma dakaina ba,bari zan ƙira Yaseerah tazo mu tafi tare da safen,kutt harma wani ta zabi part banida masaniya”
“Hmmm dama ki tsayah kallon ruwa,shidama kwaɗo ai ƙafa zayyi miki”
Barr Na’imah tafaɗa tareda cigaba da abinda take a labtop ɗin gabanta.

Har Hilyaan tafara bacci da daddare taga ƙiran Bombee,dagawa tayi tareda yimata sallama.
“Hello inace dai lafiyah,ko haidar ne ya hanaki yin bacci kai?”
“Ina cikin abuja yanzu haka,na sauƙane a hotel,da safe zan shigo gidan,dan haka kituro min address ɗin zanyi installing ɗinsa a kan Motata zuwa safe”
Tashi Hilyaan tayi ta zauna cikeda mamaki tace.
“Abuja kuma,meyasa kika taho yau ina sai gobene zaki dawo”
“Menene kuma na razanar shin ban isa sanja ra’ayi bane saikin tuhumeni iyee,ko akwai abinda baku gama bane kike tsoro”
“Ahah mun gama komai,mun zabamiki part ɗin dayake gefen lambun wajen,ta ƙofar baya zaki shiga,sannan yanada girma daidai gwargwado,mun shuka wasu fulawoyi ma wanda bazasuyi wata biyu ba zasu girma,amma dan Allah meyasa kika taho yau,ko kin matsu kai kiga angonnaki ne?”
“Hilyaan zan…….kidaina shiga hnacina fah da zancen rijalun ɗincan tamm,batun dawowata basai kinjiba daliline boyayye,wai hadda fulawa kaman nace muku ina buƙata?”
“Kai anty maryam nifa dama nasan zaki ce haka,amma ki bari saikin gani da idonki,ina tsoron shiga fah Bad side ɗinki,anyi komai yanda ya dace. Matar tasa ma naji ance wai batanan tunda taji zancen ƙarin aurensa”
“Tafiya kuma,batasonsa ne ta tafi tabarshi,ko kuma taji tsoro? Ashe ma ƙaramar ƴar isaka ce”
“Amma nikuma nafi zaton ko tafiya tayi tasake shiryowa zama dake,tunda ance bata ragawa kishiyoyinta”
“Hmmm ba shiryawa ba intanaso ta ɗauko mai yimata aikin ma su dawo gidan,hakan bai shafeni ba,tun bansan kaina ba ake bankamin,dan haka an shanin na warke,ki bari ina shigowa cikin gidan da safe”

To matan fah zasu shigo a tare kenan,ku jirayi na gaba domin haɗuwarsu a bakin ƙofar jaan estate.😂😂😂

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button