Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 41-42

Sponsored Links

Page 🖤 41••42🖤

 

Sanyin harshe taji yana bin fatar jikinta,tana farkawa taga Jabeer ne yake lasar ƙafarta tamkar kare.
Zabura tayi da zauna,da sauri ya matso inda take,jikinsa har rawa yake.
“Lubnah lafiya naga kin tashi a razane,mai yasameki ki faɗamin koma menene.
Na haɗa miki ruwan wanka da kuma abinci,kayan ki ma na zabomiki wanda zai yimiki daɗin sakawa yanzu,bayan haka kuma mai kikeso uhm”
Wani murmushin jin daɗi tayi tareda jawoshi jikinta.
“Finally ka dawo gareni bayan tsawon lokaci,wannan karon kazo kenan bazan taba bari ka koma garesu ba”
“Dama ba inda naje nina nakine ke kaɗai,yanzu ma idan kinaso saina sallamesu dukka”
“Ahah kabarsu su ɗanayimin bauta na ɗan lokaci,koya kace toh?”
“Duk yadda kikace haka za’ayi”
Cike da taƙama da farinciki lubnah tasaka Jabeer ya ɗauketa zuwa banɗaki,bayan sun fito yasaka mata kaya,yasake ɗaukarta zuwa dining.
Bayan sun gama cin abinci ma a falo suna zauna yana yimata tausa ta hakimce akan kujera.
Waya ta ɗauka taƙira Mahaifiyarta,tun kafin tace wani abu lubnah tafara magana.
“Mommyyyyy!!!! Aiki yaci fiyeda yanda kike zato,yanzu komai yana hannuna sai yanda nayi dashi mommy,wooww dama haka kikeji da kike mulkar abbah,gaskiya da daɗi.
“Eh da daɗi amma saikiyi taka tsantsan,kin tuna sharaɗin da kukayi da Matsafiya Zilliyyah kafin ta yarda da turomiki masuyin aikin koh.
Jinin kuliyar da kika basu shikaɗai bai isa ba,lafiyar ki na hannunsu,ƙaramin kuskure zakiyi shikenan komai zai lalace.”
“Nasani mommy i will take care,yanzu dai ya batun kuma shirin mu nagaba”
“Ahhh daga farawa,ki murji wanann lokacin da wannan damar tukunna,komai zaizo daga baya”
Ajiye wayar tayi ta kwanta Jabeer yacigaba dayimata tausa.

Kwana guda kwana biyu babu wanda yaga Jabeer ya fito daga ɗakin lubnah,tun abin baya damunsu har yazo kowa abin ya dameshi.
Babu ya hajiya Zeenah da kuma su Jaleelah.
Inda babu motarsa sai a yi zaton ya yi tafiyane,amma motarsa tana nan babu abinda yasameta.
Maleekah ce tashigo sashen bombee cikeda da damuwa.
“Anty maryam kema bakiga yah Jabeer ɗin ba”
“Naganshi mana,amma nima jiya na ganshi naje sashensa”
“Amma lafiyarsa kalau kuwa,mai yake a sashen anty lubnah to har yanzu,ga nan Mommah ta gagara haƙuri ta nufi sashennasa,yanzu ma tace na faɗamiki ku sameta a can ɗin,dan tun ɗazu take buga ƙofar ba’a buɗe ba”
“Ahh menene na abin damuwa kuma,mallakeshi akayi sannan aka hanashi fitowa,domin jiyan ma haɗuwa nayi dashi ya ɗauki takardun Companyn sa zaikai mata”
“Whattt……kuma hankalinki yake kwance anty maryam”
“Ohh tashi zayyi nawa hankalin,yaje ina?
Mallakarsa da tayi baya cikin plan ɗina,koyana ciki?”
Takaici ne ma ya ishi maleekah tarasa mai zatace.
“To yanzu anty maryam kina ganin menene mafita,dan Allah ki saka hannunki”
“Ehh akwai mafita idan naga dama,amma kafinni ku nema a wajen Allah,domin babu abinda yagagareshi”
Fita tayi daga falonta da nufi sashen lubnah,badan kiran da akayi mata ba sai dan tanason taga mai zai faru.

Kukan Hajiyah Zeenah suke jiyowa a falon tun kafin su ƙarisa.
Jaleelah da Jawaheer suna tsaye kaman gumakai,ita kuma sarauniyar tana zaune akan kujera ta ɗaro ƙafa ɗaya kan daya,Jabeer na tsugunne a gefenta,daga shi sai gajeran wando da kuma vest,kwana biyu yayi baƙi ya rame kaman bashi ba.
“Honey kace ma wannan tsohuwar ta bani waje na sha iska mana”
Tafaɗa tana nuna Hajiyah Zeenah,wacce take ta rubzar kuka.
“Uhm Mommah dan allah ki tashi ki tafi sashenki,na faɗamiki idan har na gama abinda nake zanzo na ganki in anjima,yanzu zafi takeji tana buƙatar iska”
“Wayyo Allah na ni Zeenatu,inda ranka zaka ga komai a wannan duniyar,mai zan gani,ɗana na cikina aka mayarmin shi kaman dabba?”
Bombee ce taja hannun maleekah wacce itama take kukan.
“Ke yanzu ba lokacin kuka bane,kija mahaifiyar ku ki fita da ita daga nan wajen ,in baso kike ku kwana yau a asibiti akan ta ba”
Ɗaga kai maleekah tayi tareda kama kafaɗar Hajiyah Zeenah, suka fita daga wajen.
“Yawwa ita waccar tsohuwar ta karbi nata lesson ɗin,shima ya karbi nasa nayimin bauta saboda auroku,sauran kuma kuma naku horon na shigomin gida da kukayi..
Bazan saka yasakeku ba,zanso ku baza ido ku kalli yanda zan zuba mulkina a gidannan,ku naku aikin shine bauta,ku tashi ku bani waje.
Idan anjima zan koma sashen honey da zama,ɗaya zata dunga yimin wanke wanke,ɗaya abinci,ɗaya kuma wanki.
Duk wacce taga bazatayi ba toga hanya nan zatayi waje a lokacin.
Ku bace ku bani waje.
Dukkansu su Jaleelah da Jawaheer barin falon sukayi,suna ganin yanda akayi da wanda suke zaune danshi,inaga kuma su karan kaɗa miyah.
Saidai kowaccensu da abinda yake ranta.
Bayan sun bar wajen saura bombee a tsaye kawai tana kallon Jabeer,wanda yagagara haɗa ido da ita,
Hannu tasaka a aljihun bujen wandonta,tareda jero feɗuwa mai ƙara.
“Weldone tun zuwana gidannan naga wani abu very interesting.
Karki damu kanki Lubnah da son taming ɗina da magani kokuma burga nayi miki abinda kikeso.
Ita kanta shugabar taku wato Zilliyyah,tun bansan kaina ba ta sakamin igiya a wuyah,saidai tana girma wuyannawa sai yayi kauri har ya ɗashe igiyar.
Kaman yanda nake faɗamiki har yanzu bakisan koni wacece ba,sannan mallakar shi wannan da kika baya cikin Plan ɗina.
Kicigaba da mulkinki a tsakanin matansa,ko babu magani a jikinsa ma bazai sameni ba bare yanada shi.
Inna gama aikin soon ma zan iya barin garin,dan haka kiyi harkar gabanki,batun abinci kuma da kike kallona na girka wai na girka miki,bazanyi ba,amma bansaniba komai magani kikeso na girka miki irin wanda ake yiwa beraye?”
Cigaba da feɗuwarta tayi zata fice,har tazo hanyar waje tasake dawowa.
“Amm lubbyyyy ki zama cikin shiri,wannan karon kinyi babban moving,wani karon Salon nawa ne,ƙwallota ce zata zura a raga,ki sha sha’aninki zan miki talala”

*** ***

Maleekah tana kuka tashiga sashen sayyada-tateen bayan ta raka Hajiyah Zeenah ɗakinta ta kwantar mata da hankali.
“Iyahh wlh wannan matar yah Jabeer ɗin bazata taba ganin rahama ba inshaallah”
“Wacce ina wannan mai ɗan shegen,dama menene da arziƙi a wajenta,matar da cimmana mutunci,nidama na fita harkarsu ne naga iya ina zasu tsaya”
“Kai iya ba wannan ba ni,waccar lubnah mana mai zubin kafirai,tun shakaranjiya ake neman Yah Jabeer ashe yana can sashenta ta maidashi kamar kare,banda aiki dare da rana babu abinda yake”
Saurin ajiye kofin kunun tsamiyar da take sha tayi,tareda zaro ido.
“Ke mekikace ƴar nan,mallaka tayi masa”
“Ai ƙazama ma iya sayyada”
“Muje ki kaini naga shi jabeerun,ko tofi ai sai ayimasa”
“Hmmm tofi koh,kina zuwa zata sakashi yayi waje dake,haka zai kalli tsabar idonki yace fitah!!!!”
Maleekah taƙarisa da ƙarfi cikin bacin rai,aikuwa sayyada-tateen tana jin haka idonta yayi ƙififi.
“Haka abin yazama,maxa ɗakkomin to mayafina ki rakani gidan malam Audu wali,nasan bazai rasa taimakon dazai bamu ba.
Yi sauri maza maza”
Jiki na rawa maleekah ta ɗakko mata mayafin suka shiga mota driver yajasu,har sannan bata daina jan majina ba.

*** ***
“Abban haneef wlh da gaske nake,yanzu nakeji a wajen mai aikina wai Lubnah ta mallake Jabeer,sai yanda tace yakeyi,hatta ƙofar gida bai isa fitowa ba saida izininta.
Koda wannen malami tayi aiki mai ƙarfin wannan oho?”
“Ohh kema kiji waye kiyimin koh?”
Alhj Abdullahi ya faɗa jikinsa a ɗan kware.
“Haba nayi maka irin wanann asirin,baka yarda dani ba haka?”
“Uhm da yarda nayi dake,kema ai sai a hankali”
“Yaushe kikaji wanann zancen ma tukunna”
“Yanzunnan aka faɗamin,wai Hajiyah Zeenah ma data je sashennnasa da kuka ta dawo.
Baka ganin yanzune lokacin dazamu sake ɗana wani plan ɗin?”
“Eh to hakane,amma dan yana ƙarƙashin ikonta bashi ke saka shikenan bazai ƙara zuwa aiki ba,dan aiki dole zaije aiki,saida abinda duk za’ayi a Company kuma sai abinda tace.
Keda kike cewa mu ɗana plan,kin manta hannun da muka haɗa da gen abdu manga,ni inaga shima akwai abinda yakeso,gashi ƙarin takaicin bansan inda takarduna suke ba,idan har aka gano basa hannuna,ko meeting fah bazanje ba kinsan”
“Karka damu za’a nemosu da kadan kaɗan a hankali.”
Bayan bombee ta koma ɗakinta runtse ido tayi tareda zama jagwab akan kujera.
Ita kadai tasan yarda zuciyarta take ganin halin da Jabeer yake ciki,waye zai hanata ɗaiɗaita iyalan gen abdu manga ne,sun gama cutarta da kowacce hanya,lokaci take jira dazasu girbi abinda suka shuka.
Tashi tayi kaman an jabureta tayi hanyar waje,ɗakin zaleeha ta nufah wacce ta dawo a daren jiyah,saida taje gidanta tayi magani kafin ta dawo..
Saida bombee ta kwanƙwasa bakin ƙofar kafin tazo ta buɗe mata,hadda fitowa da sauri kada taga mai yake ciki,murmushi bombee tayi batareda Zaleeha ta gani ba.
“Inkingama abinda kike,kizo yanzunnan ina jiranki a sashena”
“Hajiyah aiki ne?”
“Eh aikine babba ma kuwa,dan haka kiyi sauri”
“Yawwa Hajiyah nagode fah da asibitin dakika kaini”
“Karki fara min godiya tun yanzu,kizo ina jiranki a falo”
Komawa tayi tasake zama akan kujerar falon tana jiranta,dolene yau taji mai yake going gameda abinda sukayiwa Jabeer,da tace bazata shigaba amma kuma zuciyarta takasa barin abin ya wuce haka nan..
Idonta a rufe tashigo falon har ta samu waje ta tsugunna.
“Gani Hajiyah”
“Naganki,amma da farko zaifi kyau ki daina ƙirana da wannan Hajiyan,kinsanni wacece kuma nima nasan ke wacece,dan haka babu boye boye a ciki.
Tambaya naƙiraki nayi miki akan wani abu daban,dan haka kada ki batamin lokaci ki gaya min gaskiya.
Wanne irin asiri kika bawa lubnah tayiwa Jabeer?”
Zaro ido zaleeha tayi tana muzurai,saidai a matsayinta na ƴar duniyarce, lokaci guda tayi fuskar rashin sanin abinda bombee take faɗa.
“Hajiyah bangane……”
“Matsafiyah Zilliyyah tambaya kawai nayi miki fah,bana cikin mood ɗin jan magana,saidai idan hakan kike so”
Zumbur zaleeha ta tashi tsaye tareda murtuƙe fuska,girgiza tayi kayan jikinta suka sanja zuwa ainihin nata wanda take bayyana a mafarki da madubi.
“Hmmm dan kingane ni wacece shine me,kina tunanin harkinkai girman dazan faɗamiki duk abinda kika tambayeni ne,kema kanki a tafin hannuna kike dama sauran guda biyun,wato uwarki da ƙanwarki”
Saidai bombee tabari ta gama surutun kafin ta ɗan zaune daga kishingiɗen da take,idonta da suke lumshe ta buɗe tareda yin murmushi.
Hannunta ta ɗaga na dama tayi ƙass dashi..
Take kuwa Zilliyyah ta faɗi ƙasa tana birgima tareda riƙe ƙirjinta,saida ta galabaita kafin bombee tace.
“Turning off my robot”
Nan da nan Zilliyyah taji kaman an zare mata ƙaya a kahon zuci.
Yage rigarta tayi tana kallon inda zafin yafito,saitin zuciyarta tane wajen insa likita yace anciremata tarin jini.
“Taya haka ta faru”
“Me kike tunani Zilliyyah,banda ke daƙiƙiyace dan kawai kinsan maganin gargajiyah dana aljanu,kuma kina kashe mutane da mummunan aikin ki wasu kuma ki ɗaiɗaita rayuwarsu,sai aka cemiki baza’a iya ɗaiɗaita rayuwarki da fasahar zamani ba.
Na’urah nasa aka dasamin akan zuciyarki,wanda baza’a taba iyah cireta ba batareda kin mutu ba,sannan zan iya juyata yanda nakeso kaman yanda kike juya aljanu.
Idan na bada sauti na ƙass to zata hura zafi a jikin zuciyarki,idan kuma na tafah hannu to zata matse zuciyarki har sai ta maidata tamkar Fatar tsohuwa.
Karki kuma kice wai iya nan ne,duk maganar dakike inaji da ita,sannan duk inda kikaje ina gani a wayata da computer ta.
Sannan ba iya nikaɗai nakeda madannan ba harda likitan daya dasamiki dakuma wasu mutane guda biyar suma.
Idan nawa yasamu matsala to duk zasu danna a tare ne,”
Cikin haki da razana Zilliyyah tafara magana daƙyar,har sannan numfashinta sama sama yake fita.
“To koda kin kashe ni kina tunanin zan barki hakane,saina ɗaiɗai rayuwarki ne,indan asirin dana yiwa mahaifiyar kine da kuma ke toki sani bazan taba cirewa ba,koda kuwa zaki kasheni ne”
“Ahah dakata tsohuwa,menene na yanke hukunci da wuri haka.
Ai bake zan kashe ba,kinga wanda zan kashe.
Bombee tafaɗa tana nuna mata hoton ɗanta wanda taboye a kogo a cikin daji.
Abinci yake ci hankalin sa kwance bai sam mai ake ba,gefen fuskarsa a rufe sa farin ƙyalle.
Hannunta ta ɗaga ƙass,bayan da danna wani jan abu dayake hannunta,wanda zayyi connect ɗinta dana jikinsa.
Take kuwa yazefar da kwanon abincin yana fizge fizge kaman mai shirin fitar rai.
Hannun Zilliyyah ta haɗa biyu tana roƙon bombee akan ta dagata,saida taga dama kafin takashe abin.
Shuru yayi a ƙasa hana nishi dayaji abinda yake cinsa a zuciya ya daina.
Ajiye computer bombee tayi tareda maida kallonta ga Zilliyyah,wacce taga tashin hankali da sabon tantiranci muraran a wajen bombee.
“To Zilliyyah kinga dai yanda ɗanki yake burburwa koh,idan bakyason nacigaba da gana masa wannan azabar,to dole sai kinyi abinda nakeso.
Maganar farko itace ki tabbatar daga nan zuwa gobe kin warware abinda kikayiwa innata,inada wajen daza’a kaita ayi mata magani,zuwane bazanyi ba saboda bazan asarar ƙwandala ta ba,yanzu kike ɗaura haka zaki kwance shi.
Bayan wannan kuma yanzu kiyimin bayanin komai gameda shirin da lubnah suke itada uwarta”
“Batun shirinsu zan faɗamiki dukka,indai zaki rabu da ɗana,saidai asirin dayake kan Innarki idan aka warwareshi to Laari bazata taba warkewa ba daga cutar ƙurajen da takeyi,sanann kuma makantar da kurmantar dukka zasu koma kanta ne”
“To ina ruwana,idan tanaso ta mutu ma mana nina kasheta,ke nifah mutuwar wani bata dameni ba inshi yajawa kansa,nikaina nakashe ba adadi bare kuma dan wani ya kashe.
Ina saurarenki wanne irin Asiri kika danƙarawa bawan Allah can,kokuma yanzu aradu na baje zuciyar wancan mushen ɗannaki,kema na baje taki.
Abinda kike tsoro na rashin samun magaji ta tabbata yanzu nnan”
Tun kafin ta rufe baki Zilliyyah tafara bayani tiryan tiryan abinda yake faruwa.
“Karfa tayimasa,wacce bata taba karyewa har sai wanda kayiwa ya mutu ko kuma kai ka mutu,karyewarta ɗaya sai idan kaika karya dokarta da kanka.
Wata uku da ɗauka tana bawa aljanu jinin baƙar kuliyah duk wata,kafin suka yarda sukayi mata aikin,shima kuma saida tasake bada wani abun wanda yakeda muhimmanci a rayuwarta”
“Me tabayar?”
“Lafiyarta tabayar,amma da sharaɗin bazamu karba ba harsai tayi wata bata kalli wanda tayiwa ba tukunna,burin mallakar mijinta ne a ranta,shiyasa bata kulada abinda ta ɗorawa kanta ba.
Ita kuma mahaifiyarta hallitun haihuwar dukka ƴaƴanta ta bamu,ta ƙwammaci ta datse zuri’arta akan ta rayu da kiahiya a gidanta,wannan dalilinne yasa dukka ƴaƴan ta basa haihuwa”
“No wonder biri yayi kama da mutum,to amma ina ɗanta kuma matarsa tana da ciki”
“Ba dansa bane na wani ne daban,Mahaifiyar sa tayi shurune saboda kada ace batada magaji a cikin zuri’arta”
“Kutt tasanma batada magajin kuma shine take son mallakar Company?
Yanzu dai idan na raba ta dashi har na tsawon wata guda shikenan asiri ya karye”
“Ehh hakane,amma idan kika rabasu yanzu ba lallai yayi aiki ba,saboda bata daɗe dayin aikin ba,yanayin daɗewarsa yanayin jinyar dazata gamu dashi”
“Wata biyu zayyi ina daga nan zuwa kafin na rabasu kenan koh?”
“Ehh hakane”
“To tashi kitafi na sallameki,inkina so ki dau mataki akaina kinji,ni wandon robace,da yamma ki sharemin bayan gidana,sannan inzakiyi magana ta madubinki shegantakarnan taki,saikin faɗamin tukunna nagaya miki abinda zaki cewa brr na’imah,idan kuwa ba haka ba saikinyi wata guda a sume a gadon asiviti.”
Tana gama maganar ta dannna yellown madannin dake hannunta,haka Zilliyyah ta riƙe kirji tana tafe a hankali harta isa ɗakinta ta kwanta,baccin wahala ne ya ɗauketa,dan ma wahalar ba kaman ta ɗazu ba.
A garin tazo tarwatsa rayuwarta ita kuma tata rayuwar na shirin tarwatsewa a hannun bombee.

 

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button