Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 58

Sponsored Links

CHAPTER 58

Tsunkayar dakai Ahmad da faisai sukai cike da kunya suko su Alh sunusi abun ba karamin burgesu yayi ba,bubbuga mata bayanta yashiga alaman rarrashi ƙuri suka zura masu ido suna kallo can Anty hajia tayi gyaran murya tana murmushi tace”to su yayah abawa baƙi hanya sushigo.

Sai a sannan ma takai hankalinta garesu cike da kunya tasaki daddy tana cewa dasu”a’a Alh kune tafe ashe sannunku da zuwa kushigo daga ciki ta fada tana raɓawa ta gefen daddy data sake tayi cikin falo shigowa sukai suka zazzauna kafin aka gabatar musu da ruwa da lemu da dan abun motsa baki.

Bayan yan gaishe gaishe nan Alh sunusi ya gyara zama ya fuskanci su Ammi sosai yace”hajia wato maganace nakeso muyi da ku akan auren yaran nan sai kuma ya danyi shiru”to to ko wani abunne kuma akace yafaru?

Saurin amsa mata yayi da”ko ɗaya saide abubuwa dake faruwane kamande yanda kikaga wannan abun yafaru da Alhaji dande Allah ya takaitane da bamusan inda ze tsaya ba,Allahde yakare gaba”da amin sauran suka amsa sannan Ammi ta dubi Alh sunusi da kyau tace”Allah de yakare gaba amma ko yanzu dole ne mubibiyi masu son yimana zagon ƙasa dan dole dasaka hannun wasu tayu makusantan mu komade manene…sai kuma tayi shiru”mai kike nufi Hajia ko kina zargin wanine?yanda yayi tambayan kaman tana ɗan firgice dan murmushi yaƙe tayi tace”banace ba saide kawai nafaɗi hakanne saboda duniya ba gaskiya wanda kayarda da shi shine ze cuceka kokuma ya haɗa kai damasu son ganin bayanka,duk ba wannan ba mukoma ga maganan da kaɗauko Alhaji dan ina ganin kaman zatafi wannan ɗin mahimmanci.

Ba haka yasoba daso samune yaso yaji kode tana zarginsa ne ya canza taku,sai yan kame kame kawai daya fara yakasa samun nutsuwa zuciya data ruhi yayi danyin magana haka kawai yatsinci kansa da shakkar hajia kwarjini yaji tana masa tacika masa ido da kwarjini abunda tunda yake mutum ɗaya yakeji yana masa irin wannan aduk sanda ze masa magana ko wani saide yakan haɗa da karfin zuciya wato ishaq tunawa dayayi da shi take yaji zufa yakaryo masa ajiki dukda sanyi Ac daya cika falon amma shi zufa yakeji,sai Alh shehune yace”ranki yadade hajia wato munriga mun gama magana da shi Ahaji badamasi tun tuni dama yardan yaro dakuma naki muke jira to Alhamdullahi yanzude zamu iya cewa komai kaman yazo karshe tunda shi yaro ya amince da auren dakuma tsarin tarewan sa can gidan ta bakin ki kawai mukeson ji.

Duk yanda Ammi taso ƙin amincewarta da wannan tsarin nasu marairaice mata Ahmad yayi dole tayi shiru badan ta so hakan ba,amma duk da hakan saide tace”Alhaji tunda sun fini yawa na amince nima duk da ba haka naso ba,daso samune naso ace nima na zauna da ɗana da surukuwata tare amma hakan beyu ba amma fa kasani Ahmad yanada wata matan bayan basma dan tarewarta kawai muke jira saboda haka inason kasani dole ze raba musu kwana inma ƙwana ɗai ɗaine ko biyu biyu duk de yanda yatsarawa kansa amma kasani bazan sake yarda da wata tsarin bayan wannan ba,tana kare faɗin haka tamiƙe tanufi ɗaki Anty hajia ta mara mata baya.

Bayan barin Ammi falo ijiyar zuciya suka duka dusan a tare kana Alh sunusi yayi kasa da murya yace”Alh badamasi ashe taurin kan Ahmad ba ƙasa yadauko ba,saide inason kasani kokuma ince kafi kowa sanin wanene ni dakuma abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba,kajawa matarka kunne idan tace zata kawomun matsala zata iya rasa rayuwarta”karka kuskura kasa Ammina cikin matsalan nan dan ita ba abunda tasani illa soyayyar mijinta da ɗanta tanason ɗanta fiye da yanda kakeson ɗiyarka dan haka katsaya iya inda yadace ba ruwana da suruki koda mahaifina ne yace ze cutarmun da uwa sai inda karfina yakare yana kkare maganarsa yayi gaba dan maganan sa yayi cikin hocky voice dinsa dakuma murmushi kwance saman fuskan sa sai karantse abun bedame sa ba,saida yayi magana sannan Alh sunusi ya ankare ashe dashi awajen kafin yace zece wani abu dan kare kansa tuni yaɓacewa ganin sa yafita a falon faisal na mara masa baya.

Dafe kansa yayi tashin hankali goma da ishirin dole yaje yagana da dodo a yauɗin nan dan wannan vabban al’amarine ba abunda ze tsaya sanya ba,idan yace ze tsaya yin sanya sai wankin hula ya kaishi gayin dare.

“Kaga irinta ba,wai meya kawo wannan maganan yanzu idan hajiya taji fa duk yabi yaruɗe sai masifa yake dole de Alh sunusi karshe shiya kwantar dakai suka bawa Alh badamasi hakuri sannan sukai sallama suka katafi tun a hanya yakira basma a waya yamata albishir wani irin ihun murna tasaka dayasa shi dole sauke wayan akunnen sa,nan tashiga kiran ƙawayenta tana faɗamasu auren next week ba fashi nan danan gida ya dauki harama kasan abunka da masushi tun saura kwana biyar ƴan uwa na nesa suka fara zuwa.

Ammi tana komawa ɗaki takai gware takai mari tama rasa yanda zatayi shin kuka zatayi ko daura hannu zatayi aka tayi ta ihune,dafata Anty hajia tayi tace”yayah dan Allah ki kwantar da hankalinki abi komai a sannu bamusan me yasa Ahmad din amincewa haka dawuri ba,addu’a zamuyi masa Allah yakare shi daga sharrin sa ina ganin akwai wani abu da yasani mu bamusani ba ko kuma yakeson ganar da mahaifinsa”hmmm Allah gamu gareka Allah kakare mun ɗana daga sharrin masu sharri”Amin yarabbi yanzude zama be ganni ba dole zanje ni nima nafara shirri ɗiyata kar abarmu abaya.

********
Shirye shiryen biki ake daga kowane ɓangare ba kama hannu yaro amarya basma ansha gyara ciki da waje dan ba karamin kuɗi hajia balki ta ansa ga wajen ƙawartata ba acewarta na gyarane,haka shugaban kungiya yaso Alh sunusi yakawo basma tayi kwana biyu dasu amma wannan karon ya tuɓure yace saide kungiya tayi hakuri yayi masa alkawarin daren farkon auren ahmad ze amshi budurcin ɗaya matar yakai musu jinin budurcin kaman yanda suka bukata,da wannan suka hakura.

Ma aikata da aka ɗiɓo masu girki da masu kula da baƙi dade sauran su ciki kuwa harda daddy ishaq da yaransa inda sukai shigar ɓat da kama yana daya daga cikin masu kula da sashin ɓaki shige da ficensu dakuma abunda ya danganci abincin su da abun shan su.

Aisha tana ɗaki ƙudundune kwance taƙi ci da sha sai aikin kuka da take,Anty malika da su ummu salma dasu laila har khadija ba barta a baya ba sunje sunyi ƙunshi da gyaran gashi amma amarya taƙiyin komai saima zazzaɓi daya rufeta tayi luf cikin bargo ba abunda yake sake sakata kuka idan ta tuna wai aurenta za ayi ba dangin uwa balle na ubanta ba saka albarkarsu ina Anna ta take ga ranan da kike ta ƙulafucin gani Allah yakawo amma ba ke ina kike Anna wayyo Anna nayi rashinki kusa dani nayi kewar ɗuminki nayi kewar komai naki naso ace kina tare dani dukda auren naɗan wani lokacine amma nasan zakiyi farin ciki daganin wannan rana,haka tayi ta sumbatu tana kuka.

Ɓangaren amarya basma kuwa yau suke party da ƙawayenta a wani hotal da ganin yanda aka tsara wajen kasan naira tayi kuka basai an faɗama ba,wajen kansa sai kanada get pass sannan zaka wuce taso ango ya halarci wannan taron saboda abokanta da suka zazzao daga nesa wayanda sukai karatu tare amma yaƙi kaman zatayi kuka haka tasamu daddynta da magana ya rokar matashi koda minti ashirinne yabata cikin lokacin sa.

Lokacin da Alh sunusi yakira wayan sa yana hanyansa ta zuwa gidan Anty hajia dan Anty malika ta kira ta faɗa masa tun safe Aisha take kuka taƙi cin komai kuma ko ƙunshi taƙi yarda amata da yaso basarwa amma ganin tanada hakki kansa yasa shi yace gashin nan”da sallama ya ɗauki wayan bayan sun gaisa sai Alhaji sunusu yace”am kana jina ko?
“Eh inaji Alhaji
“Dama ina neman wata alfarmarce dan Allah ko zaka aramana minti goma lokacinka idan ba damuwa?

Dan shiru yayi be amsa masaba sai da yasake cewa”hello ko baka jina ne?
“Ina jinka saide ina da abunda nake yanzu ko zamuyi magana a waya ina sauraron ka?

“No ba maganan waya bace dama cewa zanyi ko zaka halarci party da basma zasuyi yau na yau ɗaya kafiddata kunya saboda abokanta da sukazo na nesa,cikin ƴar ƙaramar murya yayi maganan.

“Banajin zan iya halartan koma wani kalan party ne dan munriga da mun yi wannan magana da ita tun farko,inma duniya gaba ɗaya zasu halarci partyn ta to karta saka dani so yanzu banga abun damuwa ba.

“Amma abunda zakayin yafi zuwa kafiddata kunya mahimmacine? Alh sunusi yasake tambayansa danson yaji mai ze hanashi zuwan.

“Eh Alhaji kusan hakane dan yanzu haka ina hanyata ta zuwa kai matata ƙunshi ya amsa basa cikin halin ko in kula.

Daga basma har mahaifinta suman wucin gadi sukai sannan basma ta fizge wayan daga hannun mahaifin nata tasaka masa kuka a ganinta ko ze tausaya mata yace zezo……manage this

Leave a Reply

Back to top button