Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 12

Sponsored Links

 

Volume:12 Injection
Duk yadda taso kadaici Malik ya hana. Asalima sai ya hana kowa zama da ita, idan ba Abbas ba, domin shi daya ne kawai yaƙe zama da ita su sha hira. Kuma abin da ya fahimta, maganar Jalilah yana damunta idan ta zauna zata yi shiri ta dinga tunani. Haka yasata jin wani kamar idan ta cigaba da mu’amala da Malik tow akwai matsala, don haka ta fara tunanin hanyar da zata yakince Malik, don haka ta cigaba da bin shi da idanu, kuma abin da yake d’aga mishi hankali kamar shiru nan da take tana bin shi da idanu. A cikin kwana biyu, shima tafiya ta kama shi zuwa kasar Malawi akan kasuwancinshi, ya bar Elbashir.
Duk da ya bar Amanarta a hannun Elbashir, amma rashin yarda irin na Malik sai da ya kara da Abbas da Inna domin ya gane tsohuwar tana da mutunci da kamun kai, yasa shi sake mata amanar Zeeno.
Ya bar garin da kwana biyu, Jalilah ta dira asibitin. Inna ta fita sayo goro, shi kuma Abbas bai zo ba. Iya Zeeno ce ita ɗaya a dakin. Turo kofar da aka yi ta d’ago kanta. “Zeenobia Nas Hadejia ko?” Dauke kai tai bata ce mata kome ba, harinta take ta shigo ta shaƙe ta, ai kuwa tana zuwa gabanta tayi wani tsalle ta shaƙe wuyarta, sosai domin cike take da haushinta.
“Kin azabtar dani don baki san wace ce Ni ba.” Cikin fisgar numfashi ta ce mata. “na ji labarin cewa kin shiga cikin mutanen da suka damfari Malik ko nawa ne kudin na biya domin san da shi ya miki dabaibay”
Ture ta zeenobia tayi ta ce mata. “Fita ki bar min daki!” “Ki gaya min meye alaƙarki da Malik?” Murmushi yayi sannan ta ce mata. “jeki tambaye shi!” “Ba zaki gaya min ba kenan!”
“Idan naki akwai abin da zaki iya min ne?”
Murmushi Jalilah tai, ta ce mata. “zan saka ki faɗa!” “Fice min a daki!” Ta faɗa tana sauka a gadon, tashi Jalilah tayi tana faɗin.”zan fita name da tsanani!” Ta fice Zeeno ta koma ta zauna, can nurse ta shigo dauke da magani da allura, ta ajiye tun ganin fuskar Nurse din babu rahama yasa Zeeno share ta, ta kauda kanta tare da zame rigarta. Ai kuwa ta mata allurar. Sannan ta bata kwayar ta sha.

Tana fita ta ɗan kishingida ta kwanta, tare da lumshe idanun ta. Takai minti ashirin a wurin kafin ta bude idanunta, duk da bata shan kwaya amma yau tana jin kamar allurar da aka mata akwai kwaya, domin kuwa idanunta a rufe amma take ganin jiri. Koda ta bude Jalilah ta gani zaune ta daura daya akan ɗaya. “Gaya min, meye alaƙarki da Malik!”
Yadda bata niyyar magana ba,haka bata kulata ba. Karshe da Jalilah ta matsa barci ta kama yi, sai da ta mari cinyarta ta bude idanunta. “Meye alaƙarki da Malik?” “Abin da kuka yi da kuruciyarki muke da shi, nayi laifi ne?”
“Kina sha’awar mutuwa ne?” “Waye ya gaya miki Ina tsoron mutuwa?” “Tow gaya min mene ne a tsakaninku?” Dariya ta saka sannan ta ce mata. “idan kika iya biyana miliyan ɗari huɗu zan iya gaya miki gaskiya!” “Me zaki yi dasu?”
“Malik zan biya kuɗin shi!”. “hmm sai me?” “Zai fasa aurena!” “Kin tabbatar!” A matukar buge ta sauke kanta, kafin ta d’ago shi tana faɗin. “Idan kina ganin karya ne, ki tambaye shi mana!” “Kwanta ki yi barci zan baki kuɗin ke kuma ki fasa aurenshi!” “Malik dole ka zama nawa, idan ka ji labarin bata raye ai aurena dole ne kayi!”
Haka kawai tana fita, taki yarda ta sanarwar Lalla Salmah, domin duk cikin su da Shatima babu wanda yake bata shawarar tabi kome a sannu, sai a gaggauce. Koda Inna ta dawo ta samu tana kwance, amma kuma ba irin normal barci ba, gyara mata kwanciyar tayi. Ta cigaba da barcin wanda take yin shi a mugun wahale.
Idan ka ganta, dole zaka dauka barci take nan kuwa karfin maganin ne yake kassara lafiyarta. Kafin zuwa dare jikinta yayi wani irin pale. Abin da ya dame Dr Wardah kenan, ita d wasu Drs suka tsaya a kanta. Al’amarin ya da ya d’aga hankalin Elbashir yaki gayawa Malik, karshe wayarta ma kashewa yasa Ammy tai. A lokacin da abin ya faru, Shatima yazo lekenta ya ji labarin abin da ya faru, mara lafiyar Malik tana cikin halin ƙaƙanikayi.

Dakin tsaro ya wuce tare da basu umarnin, su bincika mishi su waye suka shiga dakin. Can kuwa sai ga lokacin da Inna ta fita, kawai sai ya dauke babu alamar wanda ya shiga. Abin ya dame shi. Bai ce kome ba, ya fita kai tsaye gidan Lalla Salmah ya wuce. Koda ya isa ya samu Jalilah, yana isa kanta ya shaƙe wuyarta. “Me kika yiwa Zeeno?wallahi idan baki gaya min ba, sai na saka an kashe min ke, keeeeeeee! Wallahi kiyi fatan na kashe ki domin Malik avin da zai miki sao yafi nawa Muni. Me kika saka aka mata!”
“Ciniki muka yi da ita na saya kuma ta sayar min sai nayi laifi?”
“Ke wacce irin mara imani ce? Da zaki sayi rayuwar ta?” “Kaga Shatima sake min wuyata, ta sayar na saya, so me ya rage? Alamari ne na cinikin rai ban ga dalilin d’aga min hankali ba, don haka kayi tafiyarka, ko ka kashe ni ba zata dawo ba, ka bini a hankali, ina son Malik ya zo da kafar shi ya ce zai aure ni, sai na gaya musu abin da za mata.”
“Har sai yaushe zata kai?”
“Zata iya kai wata guda, jininta yana tsotsewa ana kara mata, sannu a hankali hantarta zai fara kumbura, kodarta ma haka. Kafin sati biyun farko za a ta saka mata jini da ruwa yana karewa. Har sati biyu. Bayan sati biyu ne organ na jikinta zasu fara lalacewa. Kasan mene ne a jininta? Zazzafar alluran mutuwa ce da aka hada da miyagun sinadarai. Maza Malik ya tawo nan, ya mashi aurena……
Wata ta samu matsala ne, amma in sha Allah daga yau xan koma yadda nake typing……
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button