Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 73

Sponsored Links

CHSPTER 73

“Wa’in wa’in wa’in shikuma Alh bashir haka yaketa fadi shikuma Alh sunusi sai kiran labbaika labbaika yake saboda tsaban ruɗewa cikin su ba wanda ya iya ambatan Allah dukkan su sunbi ruɗin duniya,sun mance da Allah belle sukira sunan sa.

Sunɗauki lokaci mai tsawo cikin wannan yanayin kafin daga bisani Alh sunusi ne yayi karfin halin fadin”dole mu haɗau da boka najadu a yau ɗinnan dan ya kawo mana dauki cikin lamuranmu(wa’iyazu billa mutane suna mancewa da Allah suriƙe wanin sa dan neman taimako ko biyan buƙatarsu,duk wanda yabar Allah yakama wanin sa haƙiƙanin gaskiya yataɓe Allah yasa mudace yakare mu da imanin mu amin)

“Mummy mummy mummy turus tayi tsaye tana kallon su ganin mummynta kwance saman gado tayi zuru zuru duk tafaɗa kaman wacce ta shekara kwance lafiya naganki kwance shame shame kaman me shirin haihuwa?

Tayi tambayar ta cikin ko in kula da halin da taga uwar tata,duka kallon ta sukai cike da taƙaici gwaggo tani tamata daƙuwa tana cewa”ungo wannan ja’irar yariyar irin wannan tarbiyar da iyayen naki suka baki kenan ko?

Yo in banda shashanci wani ɗan albarkane zega uwarsa kwance haka hankalin sa be tashi ba,ban dake shashashace angaya miki uwa abun wasace ai duk wanda yarasa uwarsa haƙiƙa yayi babban rashi arayuwa.

“Kinga tsohuwa badake nake ba dan haka kishafa mun lafiya ko yanzun nan kijiki a waje road kizo kina….”ke basma ki iya bakin ki baki taɓa ganin wanin mu yazo gidan ku da nufin cin arziki ba yanzun ma dalili yakawo mu ki bari idan kingan mu jibi bayan auren ki sai kimana rasharin kunyar taki yayah hajjo ce ta katseta da fadin haka ranta a mungun ɓace take maganan sai kuma ta juya tana kallon ƴar uwartata tace kinga irinta ko,saboda baki ɗauke mu bakin komai ba yasa ƴarki….katse ta hajia mariya tayi bata bari taƙare abunda takeson cewa ba tace”haba dan Allah yaya hajjo barcewa haka basma ai yarinyace yarinta ke damunta wataran idan kince tayima ai bazata yi ba.

mugun haushin hajia mariyan tabata dan haka miƙewa kawai tayi tafita daga ɗakin tana cewa”kinga gwaggo taso kibarmusu ɗakin da alama tattaunawa zasuyi da ƴarta,kafin gwaggon ko hajia marian ɗayan su yayi yunƙurin yin magana tuni tabar dakin,kallon ta gwoggo tayi ita miƙewa tayi tafita tabar musu ɗaki da harara basma dake tsaye ta raka gwaggo dan mugun haushin tsohuwar takeji dama.

Ahmad yana fitowa motarsa yafaɗa ko sallama betsaya sunyi da mutanen gidan ba gida yawuce kai tsaye,koda ya isa parka motarsa yayi yafito a nitsu yanufi ɓangaren sa dake cikin gidan,wanka yayi tare da ɗaura alwala yafito ɗaure da towel a ƙugunsa saide betsaya wani ɓata lokaci ba kaya yasaka marasa nauyi na zaman gida ya feshe jikin sa da turare sai baza kamshi yake yanufi ɓagaren iyayen nasa tunda bakin ƙofa shigowa falon yakejin kaman ƴar hayaniya dan haka cikin sauri yakarasa shiga Ammi ya hango da farar takarda a hannun ta tsaye shiko Alh badamasi sai kumfar baki yake,take kirjinsa yabuga dan shi zaton sa takardar saki Abbansa yaba Ammin sa.

Da sallama abakin sa yakarasa shiga falon amsawa Ammin tayi tana cewa”yauwa gashi nan ma yaxo take zuciyarsa tabada sautin rasss cikin rarrabuwan harshe yace”la…la….fiya Ammi?

Takardan hannun nata tamiƙa masa hannunsa na rawa yamika hannun yakarɓa yana karantawa saida yagama karantawa yaɗago da kai yana kallon mahaifin nasa yace”Alhaji wai meke faruwane haka?ni nakasa fahintar komai kaman akwai abunda yake faruwa da bakason musani ninayi wannan tunanin tun randa akazo aka tafi da kai cid office da zuwan abokanka belin ɗinka nasan dawata a ƙasa bayan kafin zuwansu bayan da banyi ko da dpo ne nagani sunƙi yarda ba amna da zuwansu sai gashi kira ɗaya tak yayi akace wai an barka batare da wani tambaya ba case close kaima kasan wannan ba abunda hankali ze dauka bane amma kake ɓoyuwa Alhaji shin idan mu baka faɗamana ba wakake da waƴanda suka fimu?yakare maganan yana tsare mahaifin nasa da ido.

“Ai cewa mayayi kar’a faɗamaka sai gaka kaima kazo,cewar Ammi.

“Kar’afadamun kuma?yasake tambaya da mamaki”eh ninace karta fada maka saboda banason katada hankalin ka,kumama menene dan an fadama din amfanin me jinnaka zeyi?eh sosai sukai mamaki da yanda yake magana duk ya birkice sai yanzu ma Ahmad ta lura da yanda falon yake a hargetsa.

Ɗagowa yayi ya zubawa Ammin sa ido itama shiɗin take kallo idonta na cikowa da ƙwallah”dawowata kenan daga gidan ikilima na tadda duk ya birkita komai bama falon kadai ba hatta da ɗakin kwanan sa sai kaga yanda yayi filla filla da komai duk ya birkita komai kaman mai neman wani abun, waya Ahmad yaciro bayan yagama sauraron Ammin nasa yakira family dr dinsu da yazo yaduba Alhajin ko alluran baccine amasa.

Ba ɗauki lokaci mai tsawo ba kuwa saiga dr balami yazo wayan Ahmad din yakira yace gashi a ƙofan shigowa falo fitowa Ahmad yayi yashigo dashi saida ya gwada masa bp ɗinsa sannan yamasa alluran bacci,yace bara zeje ya haɗo masa magani yatafi kawowa shikuma Alh badanasi be jima ba bacci yayi awon gaba dashi nan suka sauke ajiyar zuciya Ammi ta sauke.

****Aisha kallo nan juyawa tayi tana kallon abunda ake nuna matan” jarida kuma?tafaɗa tana karɓa a hannun anty malikan head line ɗin kawai ta kalla.

Cikin zaro ido tana dan rufe bakinta da hannu tace”Anty malika dama haryanzu ana safaran mutane kaman wasu kaya bayan ta miyagun ƙwayoyi da akeyi?

“Nimade abunda nagani kenan abunne da daure kai wallahi Aisha yanzu a yanda ƙasarmu take muna da ƴan sanda soji mobil ace ana irin wannan abun kuma wai ace basu da masaniya ai akwai ayan tambaya suma akansu.

“Yanzu anty malika idan na fahinceki daidai kinason cewa jami’an tsaron mu na ƙasa basa aiki yadda ya kamata kenan?

“Kusan hakane Aisha?”to yanzu idan basu din bane suwaye suka kame waƴan nan din?tayi tambayan dan son kore zargin ta”wasune da ba’asan ko suwaye ba Aisha ai wannan ma abun taƙaicine kiduba irin yanda yah faisal yake aiki tuƙuru ba dare ba rana amma ace wai wasu daba jami’ai bane zasuyi wannan aiki daya dace ace sune sukai.

“Kinga Antya malika shirya dawuri muwuce kar ayi bamu wajen kuma magana dakike ai ko ke zaki iya saukakawa jami’an tsaro nauyi idan kinga wanda baki yarda dashi ba ko kinga ana wani abun da baki yarda ba sai kiyi shiuttt dan a kamesu”hmmm Aisha kenan wai yanaga kaman yau kinma fini zumuɗi da zuwa gidan su antyn takine wai me sirri?takare tana ɗaga mata giranta ɗaya’kawai de inason zuwanne saboda inga yau kuma wacce ƙaryar za’ayi”kede faɗi gaskiya hajia kode kode”a’a wallahi anty ko wancan na sameta nabata hakuri kuma ita ta buƙaci naje ɗin,shiru Anty malika tayi dan kanta ya kulle”kika bata hakuri kikace?

“Eh anty
“Kan wani dalili kika bata hakuri kuma yaushe kuka haɗu da ita kode ita tasa akayi kidnapin dinki?”anty duka wannan tambayan lokaci guda wanne kike son na amsa miki”duka tace tana tsareta da ido kafin Aisha tayi magana saiga khadija tashigo da gudu tana cewa”anty wai kuyi sauri inji yah malik.

Da sauri Aisha ta miƙe tayi waje dan gujewa amsa tambayar anty malika tana cewa”kisamemu waje daga haka ta riko hannu khadija sukai waje saida suka biya ta ɗakin anty hajia sukai mata sallama tana sake jaddadawa Aisha takula da kanta banda keɓewa ke kaɗai ki zauna cikin mutane inma kinji bazaki iya zaman ba to yi zaman ki a gida.

Aisha dake da target akan tafiyar tayi sauri tana cewa”karki damu anty hajia zan zauna bazan tashi ba,tafaɗa nan anty malika tasameta tare suka fita inda malik ƙe tsaye da mota yana jiran su.

Tare suka shiga bayan mota da ummu salma autan anty hajja khadija ce tashiga gaban tafiyar minti ashirin ya kaisu gidan Alh sunusi inda anan zasuyi taron,kasancewar gidan babba gidane anƙawata inda za’ayi taron amarya da ƙawanta duka sun saka kaya iri ɗaya sai taka rawa suke mai kiɗan ƙwarya nayi amarya na zaune hakimce.

Gurin amarya suka fara zuwa sukai ggaisa sannan suka koma gefe suka zauna suna tafi can Aisha ta duna agogo dake daure a tsintsiyar hannunta tayi tsuka tasake yin tsukan akaro na biyu kallon ta anty malika tayi tace”lafiya ke kaɗai kike ta tsuka?”fitsari nakeji kuma banson tafiya ni kaɗai.

in banda abunki ai nan cikin gidane kinga jeki kiyi kidawo,mikewa Aisha tayi tanufi cikin gidan bayan tasaka face mark ɓaki tana shiga falon tafara ƴan dube dube Alh sunusi ne ya leƙo daga can saman beni yana tambaya”waye anan ɗin? cikin kamewarta tajuya tana kin kallon sa tace”nice fitsari zanyi bayi nake dubawa.

Zonan ki biyoni yafada yanayin gaba bin sa abaya tayi tana hawa benin tanabin ko ina da ido bayan ta seta cameran dake jikin veil ɗinta wata kofa yanufa tana biye dashi a baya mutum ukune sune zaune a ɗakin tagane Alh shehu saurayi fadila kawarta daya kamo yace ita yakeso,sai Alh sunusin da kansa ɗayan ne bata sanshi ba.

Shiga can ki haɗo mana coffee akwai komai gyaɗa masa kanta kawai tayi batare da tayi magana ba,tana shiga inda yanuna mata tafara jin kaman nishi tawani ƙofa dake kulle ta cikin kitchen din jikinta ne yaɗauki bari take wani irin zufa yashiga karyo mata ta ƙofofin gashi dake jikinta.

A hankali take takawa harta isa bakin ƙofan dakin leƙawa tayi ta ɓulin makulle”kee yi sauri kikawo magana da tajine ya hanata lekawa taga komai aciki komawa tayi da sauri kunna gas tayi ta haɗa masu ta zuba cikin flaks tahaɗa da kofi ta dauka ta kai musu,tana ajiwa tamiƙe jiki na kyarma ta nufi fita daga ɗakin”ina zaki bayan kin gane mana sirri saura kaɗan Aisha ta saki zawo yanda cikin ta yamurɗa ganin yanda ta ruɗe yasa suka kwashe da dariya dukkan su Alh shehu yana nunata yace”kalli fuskarta jeki wasa muke miki ya sunan ki?saboda yanda ta ruɗe batasan sanda tace izawaka’a ba sabida tsaɓan ruɗewa tana fita a ɗakin da gudu,bayan fitan ta Alh sunusu ko me yatuna oho yamiƙe tsaye kaman wanda aka mitsina yace”kai ina da tantama akan wannan yarinyar izawaƙa’a take ko ya?gudu gudu sauri sauri yamiƙe yabiyo bayan ta amma bega kowa ba harde wajen taron yan matan yashiga yana kiran”izawaƙa’a da babban murya ita ko Aisha sai sake lafewa take bayan anty malika.

 

Leave a Reply

Back to top button