Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 36

Sponsored Links

35- Salatin da yazo bakinta tare da agajin wani mutum, da bata san waye ba ya dauke hankalin mutanen da suke wurin. Ita kanta idanunta a mugun rintse yake, numfashinta na hawa da sauka. Jira take kawai ta jita a kasa, amma wani hukuncin Allah taji ta rike a jikin mutumin. “Sannu ko?” Bude idanu tayi tana kallonshi, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana jin kamar zuciyarta zata buga. “Sannu!” Ya kuma faɗa a karo na babu adadi domin jera mata sannu yake yana karawa. A hankali ta mike tana jin bayanta ya amsa mata, “sannu, sannu Zainab!” Inji Ammyn. Kamar zata yi kuka ta ce. “Ammyn na auna arziki fa.” “Eh wallahi Allah ya kiyayye na gaba!” D’ago kai tayi tana kallon shi, ta ce mishi. “Na gode!” Murmushi yayi sannan ya ce mata. “Don worry yourself, tunda kin wuce baki fadi ba, ki gayawa Baban Baby. Ya kira ya min godiya, domin na cancanci yabawa!”
Gyada mishi kai tayi tana kallon shi, har ya gama maganarshi. Da zai tafi ya tsaya yana kallon yadda Ammyn take matsa mata hannun. “Sannu huta sai mu tafi ko!”
Murmushi yayi, sannan yq ce mata. “Babu abin da zai same ta, ai ta tsira. Suna na Tahir Sani Malami Jajja ni likita ne anan asibitin a bangaren Yara, da fatan zaki rike wanna card din nawa!?” Gyada kai tayi tana kallonshi. “Mun gode sosai!” Daga haka suka mike, yana d’aga mata hannu. “Zainab muje!” Mikewa tayi tana cizon bakinta, domin bayanta sai da ya amsa da ta kusan faduwa.
Suna fita suka samu drive yana jiransu, daga nan, suka wuce gida. Suna shiga ta zube a kujera tana faɗin. “Washi Allah na!”
“Sannu uwar uku, ai wannan cikin idan ba wani hukuncin Allah ba, uku ne ko biyar.”
“Hajja Yayye! Ki min fatar sauki wallahi bani haihuwar uku ko biyar.”
“Idan kika haifa me zaki bani?”
“Ni dai na gaya miki gaskiya bani haihuwar biyar, sai kace wata akuya.”
“A toh ko na akuya ba, wai zaki haifa mana, dama jibi zani umra sai na miki addu’a!” “Hajja Yayye, kin ga yau sauran na fadi a asibitin.” Ta fada tana tura baki. “Ke Yar nan, kin auna arziki fa.” Nan suka yi ta hira aka kawo mata abincin dan wake ne, sai kayan salat, tana ci tana lumshe idanunta. Shiru tayi lokacin da girkin Malik ya dawo mata, kamar ruwa ya cinyeta sai da idanunta suka tara kwalla. *Yanzu shi kenan sun rabu kenan?* A hankali ta ture abincin. Ta mike dakyar ta koma dakinta. Rufe dakin tayi ta fashe da kuka, bayan ta zauna a gadon. Tana kuka tana karawa, Allah ya gani tayi missed dinshi. Bukatar shi take, amma pride irin nata, yasa tana jin kamar tana nimanshi class ɗin ya zube.

Don haka ta cigaba da kukanta, domin shi yafi dacewa da ita, bayan ta gama kukanta, yayi sallah ta kwanta domin ba zata iya da ciwon kan da ya tasata a gaba ba.
★★★
Bayan sati
Elbashir kan, kasa sake jikin shi yayi domin gani yake kamar an sayeta baki daya zata iya kashe shi. Duk da yaga nadamar haka a tattare da ita, amma baki daya yaki yarda da ita. Sai da yayi sati biyu don kada Malik ya ce bai ji maganar shi ba, sannan ya fara fita ranar da su haɗu da Malik, ya sha tsokana. Kamar ba gobe kuma gefe guda babu abin ya bashi mamaki kamar yadda ya ga Malik din babu wata matsala a tattare da shi, haka ya bashi mamaki, har ya kasa hakuri ya tambayi Malik din.
“Malik ko kun shirya da Zainab ce?”
“Me ka gani?”
“Kawai naga kamar hankalinka kwance yake.”
“Tow so kake na.kashe kaina saboda mace? Yarinyar da koda na mutu babu ruwanta aure zata yi? ”
“Kai haba?”
“Wallahi kuwa, wacce take kaunarka ce zata kai shekara biyu bata yi aure ba. Wacce dama kuɗinka take so, babu ruwanta. Kana mutuwa zata buga aurenta, don haka babu ruwana da wata mace naci mana da da madara. Baka ga kibar da nayi ba, domin na samu sauki.”
“Dama baka da lafiya ne?” Ya tambaye,
“Hidimar mace ai lalura ce me cin gashin kansa, idan da na biyewa Zainab sai na lakad’a mata dukar tsiya, amma bana jin ta kai ni makurar da haka zai faru!”
“Allah ya kyauta, bana jin haka zai faru ai kasan me kake yi, kana da nutsuwa da aji.” Girgiza kai yayi yana dariya, ya ce.
“Aji sai kace mace, kawai abin da na sani mata irinsu Zainab ka barsu akan ra’ayinsu, ka sake suka rike maka wuya, sai kasan Allah daya ne, irin Zainab biyu wallahi sai ka kusan hauka. Bana jin masu mata biyu zuwa uku suna cikin salama.”
“Kai Malik kara bani tsoro, gaskiya ba zan iya rayuwarka ba, domin Zeenobia ta baka wahala.”
Dariya yayi ya ce masa. “Kuma sonta nake kamar na cinye ta danye.”
“Allah ya kawo maka ɗauki, domin ka zare!”
Tashi yayi ya zuba hannu a aljuhun wandon shi yana kallon waje. “Baka san wani abu ba ne, idan har zaka so mace kada ka sake ta ja ka a kasa, duk tsiya kada ka bari ta reneka. Da ace na sake Zainaba ta rena nani tow da na kad’e har buzuna, a haka ya aka kare hmmmm!” Murmushi yayi ya me sauti yana me shafa kanshi har zuwa wuyar shi.
“Malik me yasa ba zaka bincika ka ji halin da suke ciki ba, na ga kusan kwana uku kenan da tafiyarsu.”
“Tana lafiya, ita da abin cikin.”
“Masha Allah, ya batun aikin.”
“Ban san kome ba, ina jiran abin da zasu ce ne!”
“Allah ya raba lafiya!”
Gyada kai Elbashir yayi, yana mishi fatan alkhairi, d’aga wani riga Malik yayi ta cire wasu passport yayi ya wurgawa Elbashir ya ce masa. “Honeymoon!” Ya faɗa yana d’aga mishi gira. Kasa magana yayi yana kallon Malik. Daukar rigar shi yayi ya saka a arm dinshi, ya ce mishi. “Ka rufe baki Bashir, ina da wani Meeting a can Hall idan zaka zo muje, yana da kyau ka ji akan meye!”
“Zan je!”
Daga haka suka fita, suna hira har zuwa inda zasu yi Meeting. Sake baki yayi ya ga Lauyoyin Malik da lauyarshi. “Me zaku yi anan, Barista Hayatu!” Murmushi yayi, bayan Malik ya bashi kujera ya zauna. A hankali ya zauna yana kallon su. Ciro wasu takardun Lauyoyin Malik suke suna mika mishi yana cikewa, yana gama na farko sai ya tura su gefe sannan ya kuma. Sannan ya kalli Elbashir ya ce musu. “Wannan file din, na Elbashir ne baki daya da na amsa na Mr Jamal Arab, da aka kwace shekarun baya. Wancan da kuka saka hannu, shares na Zainab ce da abin cikinta.”

Hadiye yawun bakinshi yayi yana kallon Malik. Kamar yayi kuka ya gama aikinshi sannan ya ce. “Akwai masana’antar sarrafa man fetur, na shine na saya mishi shekarun baya, ga kuɗin shi. Mahir na gode!” Ya ajiyewa Elbashir ya ajiye mishi kome yana murmushi. “Na sallame ka, daga yau kada ka kuma makale min!” Ya fada yana dariya. Hawaye ne sharrr ya zubo mishi. Ya kasa magana, “kasan mata da buri ba zata ji dadi ta ga mijinta yana aiki ƙarƙashi mijin kawarta ba, ko ni ne ba zan yarda ba, salon muyi faɗa matata ta mata gori.”
“Har abada Zainab ba zata tab’a mata gori ba.”
Ya fada yana rungume Malik, cikin wani irin kaunar shi. Don abin da dan uwarshi na jini. Sai da aka gama suka fita. Su kansu Lauyoyin ba karamin alkhairi yayi musu ba. “Malik kamar zaka tafi wani wuri ne!” Tsayawa yayi yana kallon takalmin shi. Wani irin fisgar Elbashir yayi ya cillar da shi can, harbin ya wuce ta gefe can. Komawa bayan motar da suke wurin suka zauna. “Sannu babu abin da ya same ka ko?” Yana jin yadda ake harbe harbe, gashi mutane kowa ya gudu. Hannunshi ya kai kafarshi. Ciro wata karamar bindiga yayi ya saka hannu a cikin Aljahun wandonshi wani abu ya ciro. Ya saka a bakin bindigar.

Kafin kace wani abu ya gyara tare da cewa. “Ka zauna anan, kada ka sake ka matsa nan da can. Na hadaka da Allah.”
“Tow Malik”
A hankali, ya kalli jikin wata a’a BMW, baka wuluk. Yana kallon me harin, kafin ya juya da sauri ya shiga harbinsu. Kafin kace me ya harbe su. Sannan ya gama dasu, sannan ya mike yana gyara tsayuwar shi. Harbi aka kai mishi a hannun da yake rike da bindigar ya fadi can.
★★★
Rike take da bowl din fruit, wani irin faduwar da taji tare da juyin da cikinta yayi yasa ta sake bowl din, tana rike cikinta a mugun tsorace take kallon fruit ɗin, kallon Ammyn tayi tana son sanin da waye take waya, ganin yadda ya tsare ta da idanu yasa ta. Mikewa tana me dauke idanunta da yayi jajjur.
“Innalillahi wa inna illahirirajuun Ubangiji, ya tsare na gaba, wani hali yake ciki!”
“Eh tow, a halin da ake ciki sai du’a’i kawai amma al’amarin ana cikin wani hali da”
“Allah sarki Zainaba, Ubangiji ya kawo mata dauki daga ita har shi.”
“Wace ce Zainab kuke magana?” Sake wayar Ammyn tayi tana kallonta. “Wata Zainab ce yar uwar Abbanku!” Hawaye ne ya zubo mata, “shi kenan!” Daga haka ta wuce waje tana jin kuka ya kwace mata. “Hajja Zainaba, lafiya?”
“Hajja Yayye, kawai kukan ne ya zo min”
Duk da bata san me ke faruwa ba, amma jikinta ya bata babu lafiya, sai babu halin gaya mata. A hankali labarin ya bazu a cikin gidan, har da familyn Babanta kowa ya sani. Amma ita har lokacin babu wanda ya gaya mata, domin ana tsoron cikinta.

A daren ranar mugun zazzaɓi da nakuda ya hanata barci, dole aka tafi da ita asibiti, ganin halin da take ciki yasa ka shiga da ita aiki domin aka bari tayi nakuda za a rasata ko jinjirin cikinta. Haka aka shiga da ita aiki, basu fito ba sai karfe hudu na asuba, aka fito da yaran biyu maza, mace daya kamar yadda Inna da Hajja Yayye suka yi fatansu.

Yaran farare tass kamar Uwarshi, dole aka saka su a incubator, domin kuwa babu me ɗaukarsu.
★★
Maganar gaskiya har zuwa liuokacin, babu labarin makomar Malik, domin kuwa anfi karkata da mutuwarshi, Elbashir shi ya dauki Malik, har zuwa asibitin. Jikinshi jinin Malik ne kamar an yi mishi wanka…
*Allah sarki Malik!*
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/27, 10:26 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button