Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 36

Sponsored Links

Chapter 36

Kafin tasauke hannun ta nima nakai mata maruka dama da hauni ba ita ba hatta Ahmad abun yaba shi mamaki dan betaɓa tsamanin zata iya rama wannan marin ba duba da yanayin tazaran shekaru dake tsakaninta dasu dakuma wayewa uwa uba ƴaƴan manya.

Zafin marin be gama sakin salaha ba ta tsinkayo muryata nama basma magana cikin ladabi kaman ba itace tayi wannan abun ba yanzu”anty basma kifayi hakuri kinsan ni bana barin bashi komai ƙankantar sa,bare kuma ga taɓamun lafiyata tunda nake ko uwar da ta haifeni ma bata taɓa saka hannun ta ajikina ba bare kuma wata,ɗan dafe gishinta tayi kaman wacce tayi mantuwa sai kuma ta ɗan kalli salaha tace sorry fa kawar Anty.

Wani irin malolon abune ya takare makoshin ta harma ta kasa cewa uffan.

Juyowa tayi ga Ahmad dayake hakimce saman kugera duk wannan abu kaman baya gun,saboda ya maida hankalin sa kacokan saman systerm ɗin sa,

Azahiri kenan amma a baɗini duk abun nan da ake yana ganin su”gani tace dashi ba tare da tako kalli inda yake ɗin ba,banza yamata kaman ma besan da wata halitta mai suna Aisha a wajen ba.

“Ok basma kuna iya tafiya dan ina da aiyuma masu tarin yawa”kuttt yanzu My saboda wannan kucakar ƙasƙantacciya ƴar wanki shegiya wacce….”ya’isa taji an katseta a tsawace yanda tsawan yashigeta har saida taɗan zabura abunka da wanda yataso ba gwaɓa.

“Ya’isa ya’isa tasake maimaita hakan cike da ɓacin rai dakuma baƙin cikin yanda wasu masu kuɗi basu ɗauki talaka bakin kamai ba,mai zan so ga wannan saurayi naki ƙwala ƙwalan idon ko kuma farin fatan,Allah ya sauwake mun keda kike ga abun burgewa a gun kyayi,amma bar wani haɗani da wannan abun ko kusa.

baya daga cikin gerin miji da nakeso in kina abunki yatsaya tsaka ninku amma kibar sakani cikin tsabgarku,duk talauci da ƙaskancina Alhamdullahi bantaɓa zuwa gidan masu kuɗi danyin bara ba,gumina nakeci kuma ko wanki da kike goranta tamun bafa sata nake ba balle naji kunya sai na wanke miki ɗan kamfe harma da ƙunzugu sabida rashin sanin dajara a hakanma sai na tsaya tsayin kada kafin abani hakkina ko da saura bayan wannan?

Wani irin zabura rahaina tayi cike da borin kunya kunyata kawartasu da wannan yarinyar tayi dakatar da ita nayi da cewa”haba raihana ke kuwa mai naki na zabura haka kode neman suna kike?
Da kin tsaya matsayinki da baki ɓata lokacinki wajen daukar jakar mace ƴar uwarki ba wallahi kuke saka ana raina mu ƴaƴan talakawa saboda ƙwaɗayi da rashin sanin ciwon kai.

Daga haka ta juya da nufin barmusu office ɗin harta kama handle din kofan zata buɗe taji ance”waya baki izinin fita?

Sake handle ɗin tayi a hankali ta juya ta kalle shi shima ita ɗin yake kallo hartayi ƙasa da kanta jin idanunsa masu kaifi a kanta saide tunawa da tayi da abunda yamata ɗazu hakan yasata banka masa harara ta juya da sauri tafita waje tana rufe masu ƙofa da karfi daya ba sautin garammm.

Rintse idonsa yayi shi kaɗai yasan abunda yakeji akanta,amma ƙwarin gwiwarta da rashin tsoron ta yana burgeshi besan sanda murmushi ya suɓuce masa ba.

Ganin murmushi saman fuskansa abunda tunda take dashi take mararin ganin sa dashi amma bata taɓa gani ba sai yanzu,hakan yasake tunzurata ta fashe masa da wani sabon kuka tana cewa”wato abunda wannan ƴar sharan tamana ma be ko dameka ba,sai ma murmushi dakake binta dashi tunda nake dakai bantaɓa ganin ka dashi ba,kullum kazo guna fuska cunƙushe kaman wanda aka faɗawa sakon mutuwa.

Wallahi daddy zankira in faɗa masa beyi yunƙurin hanata kiran ba dan yana ganin alama tanan tafi kauri kai ƙara abu kaɗan daddy be gama tunanin da yakeyi ba ta miƙomasa wayan tana ƙananun kuka.

Karɓan wayan yayi a hannunta ya kara kunne sa,sallama yafara masa madadin amsa masa da sallama da yayi sai tsinkayo muryar Alh sunusi yana masa faɗa da tada jijiyoyin wuya beyi kunkurin katse shi ko bashi hakuri ba,saida yakai aya a maganar tasa sannan cikin ladabi Ahmad din yace”sorry Alhaji ban hanata party ba inma duniya zata gayyata sani yarage nata nine de bazan samu daman halarta ba saboda wani aiki mai mahimmanci danake dashi a wannan lokacin.

Da mamaki basma take kallon sa dan batayi tsamman tsaurin idon ahmad ɗin yakai yima mahaifinta musu ba.
Bata sake tsinkewa da lamarin nasa ba saida taji yana cewa gaskiya Alhaji wannan abun yafimun wannan shagalin dama auren baki ɗaya bana jin zan fasa wannan tafiya tawa,shiru yayi da alama yana sauraron abunda Alhaji sunusin ke cewa sai kuma taga yamiƙa mata waya yana cewa dasu salaha ku ɗan bamu waje zamuyi magana simi simi sukayi waje kaman wasu munafukai.

Rufe kofar yayi sannan yatako zuwa inda take tsaye kallonta yake ido cikin ido har saida taji kallon da yake mata yafara gundurar ta ita tasoma jaye nata idon dan bazata iya cigaba da kallon cikin idon nasa ba.

Basma yakira sunan cikin murya mai amo”ya zama yaune rana na farko kuma karshe dazaki kai karata wajen mahaifinki,dan na yarda da aurenki hakan bawai yana nufin zakuna juyani yanda ranku keso ba.

Sannan zance tarewa a gidan ku dakuka tsara matukar kina sona kuma kin shirya zaman aure dani to kishirya tarewarki a gidana,idan gidane muma muna dashi idan kuma ɗakine inada shi bana bukatar komai daga iyayenki ke kaɗanki kin isheni komai.

Wannan umurni nake baki kai tsaye bawai shawaranki kota tsuffinki nake nema ba.
Tunda nake a tarihin duniya bantaɓa ganin inda akace ango yatare gidan surukanka sa ba,dan haka baxa fara wannan rashin M ɗin akaina ba.

Tunda yafara magana tasake baki tana kallon sa saida yakai karshe sannan tasake fashe masa da sabon kuka tana cewa”yanzu ni yakake son nayi kasan inasonka kuma wannan abunda kake magana akai……kice musu ke mijinki zaki bishi dan zakufi sakewa can dashi yakatseta da faɗin hakan.

Rugumesa tayi tana”amma kasan inasonka kuma zan iya komai saboda soyayyarka ko?

“Eh nasan zaki iya ya bata amsa.

“Amma gaskiya baxan ɓata musu shirin su ba.

Tureta yayi daga jikinsa yana karemata kallo dayasa tasha jinin jikinta,ta duburburce tace”ina nufin shirin su nason haɗa kan family ɗinsu waje ɗaya aikama kana ɗaya daga cikin mu yanzu ko?

Shiru yamata tabbas akwai wata a ƙasa kuma bazai nuna mata komai ba.

Dan haka saiya saisaito da muryar sa yasake shigar da ita jikin sa da kyau takoyi luf tana sauraron bugun zuciyarsa.

“Basma inason kisan wani dan na aureki hakan bayana nufin nine zan tare gidan ku ba,matsayin ki na ƴa mace kece wacce zadauka akaita gidan mijinta kamar ko wace ƴa.

Kaman yanda shi mahaifin naki yakeson ganin ya haɗa kan family ɗin sa nima nawa mahaifan suna so”amma ai daddy yace da amincewar daddyn ka tafaɗa tana sake shigewa jikin sa.

Burin mahaifina yasha bamban da tawa burin dan ni burina befi na ganni zaune da iyayena da ƴan uwana da matata dakuma yarana dukkan mu family ɗaya zaune saman dining munacin abinci a tare ba dan haka muddin kina sona bakya son kiyi aure kikare rayuwarki a gidan ku ba to saifa kin tare gidana dakina mushimfa rayuwarmu kaman ta sauran ma aurata.

“Amma ai…..”wannan shine burina bazan kuma canza zance na ba,kaman yanda nafaɗa miki mutuncin ƴa mace akace ɗakin mijin ta.

To kinga bafa faƙiri bane ni dazan biki gidanku saboda wani abu na mahaifinki kingane ko bawai ina alfahari bane,a’a inason kisan cewa ko dako zanna dauko ɗan abunda de zannemo matata da ƴaƴana suci Allah bezai hanani ba.

Balle kuma Allah yawadata ni na tsaya da kafafuna bana dogoro da dukiyar daddyna,na baki awa 24 kije ki zauna ki nutsu kiyi tunani shin wannan tsarin da suka dauko na son tarewa ta gidan ku yayi kokuma na tarewarki gidana shine mutuncinki?

Kawayenki nawa akayiwa aure shin ba gidan mazajensu aka rufe musu kai aka kaisu ba?
Kokuwa gidagen su angwayen suka bisu?

Ke akaran kanki tarewarki gidan mijinki shine ƙimarki ko kuma shi mijin yatare gidanku ɗakinki gaban iyayenki wace irin rayuwa zakuyi wace irin sakewa zakiyi da mijinki al hali kina zaune cikin gidanku gaban iyayenki.

Idan ko kinƙi janyewa daga wannan ƙuduri nasu karshe kece zaki wahala dan ni mijin mace huɗune ina daman ƙara aure kefa?
Kinga saide kikare rayuwarki a gidan ku ke ba bazawara ba ke ba ga mijin ba.

Yana kare fadin hakan yarabata da jikinsa yayi gaba wayan sa kawai ya dauka yafita yabarta a office ɗin tsaye ƙiƙam kama wata wacce aka dasa a gun.

Aisha tana fita daga office Ahmad ta hango khalid tana ganin sa ta daidaita kanta miƙo mata waya yayi sabuwa dal a kwalinta yace”Suhail yamatsa shine yatura ƙudi naje nasayo miki ta,kiduba idan batayi miki ba sai muje tare kizaɓi wanda yamiki akwai sim aciki da karfe biyar ɗin yamma ze kiraki kinga nima yanzu na huta da kira yakare magana yana ƴar dariya,yana dan sassauto muryar sa yace wai ƙanwata menene sirrin wannan farin jini haka na kwara kan zaratan maza haka.

Murmushi kawai na nasakar masa nace”masha Allah waya tayi kyau ya khalid gaskiya ka iya zaɓe.

Murmushi shima yasaki yana ɗan bubbuga kafadan sa.

Daren yau kaman yanda basma bata rintsa ba,tana ta tufƙa da warwara karshe de topic tasaka a social media wanda matasa da samari suka shiga tafka muhawara kan wannan maudu’in.

Ahmad ma nashi ɓan garen hakance ta kasance dan daya kulle idon sa Aisha yake gani yana sumbata yaja karaman tsuka yana gyara kwanciya a ransa ko cewa yayi idan ma aljanace ke to haka zaki barni.

Aisha kuwa hankali kwace tatafi da wayanta gida koda tanuwa su,anty hajia da anty malika murna suka tayata malika ita ta zauna ta tura mata Apps da tasan zata bukata,dadare bayan sun kwanta suhail yakira suka sha hirar su.

Leave a Reply

Back to top button