GUZIRIN MAI HAILA KASHI NA UKU
بسم الله الرحمن الرحيم
Misali mace tana yin haila duk wata kwana uku, amma wani trace ranar juma’a daya. bata yi ranar Asabar ba sai tace Lahadi biyu, bata yi ba ranar litininba sai tace talata uku kuma koda tsallaken kwana nawa yake yi. haka zatayi Lissafinta na Kwanakin da taga jini,
Amma a maganar bata karfi kamar ta farko. sannan musali idan mace jini yazo mata rana daya a wata, bata sake ganin jini ba har sai bayan kwana takwas, to wanda yazo bayan kwana takwas din to sabuwar haila ce. to amma a wani fadin ance tayi haila amma bata sake ganin jiniba sai bayan kwana Goma sha biyar, to shi jinin da yazo bayan kwana Goma sha biyar ya zama sabuwar haila, wato maganar farko tana nufin indai akwai kwana takwas a tsakanin jinin da wani jini na biyu sabuwar haila.
{3} ABUBUWAN DA HAILA TAKE HANAWA
SUN KASU KASHI BAKWAI :
1- SALLAH
mai haila baza tayi sallah ba. domin Annabin Rahama yace”idan mace tana haila baza tayi sallah ba “. (BUKHARI)
2- AZUMI
Idan mace tana haila baza tayi azumi ba amma zata rama bayan jinin ya dauke Annabin Rahman” “yana fada in mace tana haila baza tayi azumi ba.
(BUKHARI).
3- DAWAFI
Mai haila baza tayi dawafi ba domin Annabin Rahama yana cewa” Shi dawafi (kamar) sallah ne sai dai shi anyin magana a cikinsa. (TIRMIZI DARU KHUDNI).
Sanan Annabi yana cewa ” A’isah kiyi duk abinda Alhaji yake yi amma banda dawafin dakin Allah” wato mai haila zatayi komai na aikin haji in banda dawafi.
4- DAUKAR AL~KUR’ANI MAI GIRMA
Mai haila baza ta taba ko shafar Al-kur’ani ba cikin mafi yawan maganganun Malamai domin Allah yana cewa” SHI Al-kur’ani mai girmane babu mai shafarsa sai masu tsarki.
Annabin Rahama yana cewa “Karka shafi Al-kur’ani sai kana da tsarki Amma babu laifi Abuda ta karanta ko tilawa wato karatu da ka batare da rike Al-kur’ani ba.
5- SHIGA MASALLACI
Mai haila baza ta shiga masallaciba,saboda Annabin Rahama yana cewa” bazan halartawa mai haila ko janaba shiga masallaci ba.
(ABU DAUDA)
6- SADUWA
Mai haila mijinta bazai sadu da ita ba saboda Allah yayi hani a cikin Al-kur’ani ‘ inda yake cewa Manzon Allah ( S. A. W.) ” suma tambayarka abisa masu haila to kace musu shi haila cuta ne ku kaucewa mata in suna haila kar ku kusancesu har sai sun sani tsarki.” kuma har sai sunyi wankama za’ a kusancesu.
Sanan Annabin yace”kar a sadu mata har sai sun sami tsarki. amma babu laifi ayi wasa dasu in dai saduwa akayi ba. saboda Annabin Rahama yace” ku aika ta komai da mata. amma banda saduwa.
7- SAKI
Baza a saki mace ba in tana haila saboda wata rana Abdullahi dan Umar ya saki matar sa tana haila sai Annabi ya bada umarnin adawo da ita in yaga dama bayan ta gama hailar ya saketa ko ya rike matar sa amma malamai sunce koda mutum ya saki matar sa tana haila to sakin ya zartu
wato ta saku.
وبالله التوفيق.
daga dalibinku
musa s zage
15-07-2019