Hausa NovelsInda Rai Hausa Novel

Inda rai 22-23

Sponsored Links

*INDA RAI…*🥰🥰🥰

*MARYAM ABDULLAHI*

( 💋 Oum Shaheed 💋 )

*Daga ƙungiyar, ko da kuɗinka…..*

*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION✊🏼✊🏼💔💋*

*Page 22 – 23*

 

A yau ne aka yi addu’r uku da rasuwar Raheem, bayan komi ya natsa Abee yake shaidawa Mimi duk abun da ya faru a asibiti….. tas ya bata labarin komi, a gigice Mimi take kallon zu Abee, zuciyarta na ɗagawa da sauri sauri, “kana son cemin zuciyar ɗana daya mutu aka cire aka sawa wani, kenan sayarwa kayi kenan, a’ina ka taɓa jin anyi hakan,? maganganu kawai take yi babu alamar zata dakata, “kamo hannunta yayi ya mannata da jikinsa tana ƙwacewa ya saka ƙarfi ya riƙo ta sosai, sai da ya tabbatar tayi laushi sannan ya sassauta riƙon da ya mata, a hankali ya ɓuɗe bakinsa cikin tattausan lafazi ya shaida mata dalilnsa na yin hakan. da silar faruwar hakan, ya ƙara da cewa, “Balkisu! ban yanke wannan hukunci ni kadai ba sai da amincewar Daddynki, da sauri ta kallesa jin kalaman da suka fi to daga bakinsa, ganin yadda take masa wani kallo mai cike da zargi yasa shi ciro wayarsa ya kira sirikin nasa, magana suka yi sosai kafun ya kashe wayar ya maida hankalinsa ɓangaran da take yace mata
zasu je gida bayan sallar magarib, acan zakiji dalilimmu nayin hakan.

Lamo tayi ajikinsa gaba ɗaya sun yi shiru kowa da kalar tunanin da yake yi a ransa, suna haka sukaji sallamar Amrish, bayan sun amsa mata suka bata izinin shigowa, ita ma a jikin Abeen tayi wa kanta masauƙi, duk tayi sanyi kamar ba ƴarsu da suka sani mai kuzari ba, kullum tana cikin nishaɗi ba ‘a cika gane ɓacin ranta ko fushinta ba, a aikace ta keyin duk wani abu nata ba tare da ta furta ba, kawai aiwatarwa take.

Abee ya ɗago fuskarta yace, “lafiya kuwa ƴar gidan Abee, ƙara tura baki tayi ta kalli ɓangaran da yake tace. “Daddy ban ma san ta’ina zan fara ba, but i dont now how to explain, ina son komawa Jamus, sai kuma ta fara kuka, ai Abee bai ma san lokacin da ya tureta daga jinkinsa ba, ya juyo a hasale, kamar zai kai mata mari sai kuma ya sassauta fushin nasa jin Mimi ta riƙo hannunsa tana shafa ƙijinsa a hankali, kallonta yayi ta girgiza masa kai, mai da kallonsa yayi gefen da ƴar tasa take, gaba ɗaya ta firgice, kiyi haƙuri Amrish, bazaki koma ba domin aure zammiki nan da watanni biyu kacal, zuba masa dara daran idanunta masu maiƙo da sheƙi tayi, wanda suka rine suka zama kalar brown a take, “aure Abee? na ce maka Humait ya shirya ne? Mimi ganin yanayin da Amrish ta shiga na shork yasa cikin sauri ta riƙo hannunta tana mata magana cikin sanyi da nuna alamar lallashi, “wasa yake miki fa, nima kaina sai dana razana, ba tare da sanin ta ba taga Abee ya miƙe zai fita, ƙalb! ka tsaya ka shaida mana wasa kake mana, kallonsu ya yi gaba ɗaya kafun yasa kai yayi ficewarsa, duk yanda yake son ahlin nasa bazai hanasa amfani da wannan damar gurin cikar burinsa ba.

Ƙarfe biyar daidai suka isa gidan sirikan nasa, daga Mimin har Amrish jiki a mace suka fi to a motar suka ƙarisa cikon parloun gidan, da sauri Amrita ta ƙarisa ta faɗa jikin kakarta Hajiya Saudat, mace mai cikar kamala da haiba, “oyoyo my rigimata, yau kune tafe da wannan yammacin,? ta faɗa tana kallon ƴarta Balkisu dake ƙoƙarin zama akan ɗaya daga cikin kujerun da sukayiwa parloun kawanya, wlh mu ne Mama, tare muke da Abeen nata ma, yana waje, “to wannan ai shirme ne, kunzo kun zauna kun bar bawan Allah a tsaye, maza tashi ki masa iso can ban garan Daddynki, ai yana gida shima, da’alama baƙi zaiyi shima, shiyasa yau ɗin ya shigo da wuri.

Bayan dogon gaisuwa da hira kaɗan da ta gudana a tsakaninsu, Alhaji Bashiru yayi gyaran murya, addu’ar buɗe taro yayi sannan ya ɗaura da faɗin, “ke Balkisu nasan akwai tarin tambayoyi a ranki,yaja dogon numfashi ya ɗaura da faɗin, “ba kowa aka sakawa zuciyar ɗanki ba sai Imran, yaron Alhajin yara, a tare Mama da Mimi suka miƙe a matuƙar razane, gani suke yi kamar shine a gabansu, a zuciyar Mama tunani take wace zuciya kuma,? a ɓangaran Mimi kan tana jin tabbas mijinta da mahaifinta sun samu matsala a kansu, Amrish dai ta zama ƴar kallo, domin ita bata ma san akamme suke magana ba, “ku zauna, Daddy ya basu umarni, zama suka yi kowa a ɗo fane, gani suke yi suma sun zama abun tsoro a garesu, Daddy yace, “duk wanda yake da tambaya yanzu zaiji komai…

BAYAN WASU SHEKARU DA SUKA GABATA

Ni Alhaji Bashiru haifenfen garin Adamawa ne, acan muke da zama nida dangina, ina da mata ɗaya Saudata, na ka san ce mai neman na kansa, ta hanyar nema muka haɗu da wani Alhaji Auwal, na masa laƙani da Alhajin yara, mutum mai taimakon na ƙasa dashi, mun haɗu ta silar gate Man ɗinsa Sunusi, ina noman wake sosai shi kuma yamin hanya yana muka fara kasuwancin tare, a haka har muka saba da juna, abokina Sunusi shima yana da matarsa da ƴara biyu, Aminu sai ƙanwarsa Haulatu, yana son iyalinsa sosai kuma yake kulawa dasu, har zuwa wannan lokacin Allah bai nufi matata Saudat da samun haihuwa ba, har matarsa ta sake samun ciki na uku kwatsam nima tawa matar muka wayi gari ta samu juna biyu, munyi murna da farinciki sosai, sannu sannu kwana nesa har suka kai lokacin haihuwa, ranar wata litinin abokina Sunusi yazo cikin dare yake shaidamin matarsa Maimunatu babu lafiya, da sauri na ɗauki mota muka nufi gidansa, kafun mukai ga zuwa asibiti jini ya ɓalle mata sosai take zubar dashi, muna zuwa aka shiga da’ita ɗakin haihuwa, wanda anan asibitin rai yayi halinsa, Allahu’akbar, munga tashin hankali a wannan daran, haka muka ƙarɓi gawa muka wuce gida, a gidana ake yin komi kasancewar bayi da kowa a gadin, ita kuma Maimunatu ba ƴar garin bace ba ta da kowa anan, haka aka gama zaman makoki a watse, sai fatan rahma a gareta, tofa daga nan naso yaran su dawo hanuna amma fir yaƙi ya bani, a cewarsa suna ɗebe masa kewar matarsa, bayan wata biyu da rasuwar matata ta haifi ƴa mace kyakykyawa da ita, ran suna na saka suna Balkisu, na daɗe ina da burin samun ɗiyar dazan sakawa sunan, ina son sunan sosai. Tafiya tayi tafiya yara suna ta girma ina yawan ɗauko Aminu da Haulatu suzo su wuni a gidana, har suka kai sawa a makaranta, dakyar Sunusi ya yadda na saka su, wai baya son suyi nesa dashi, a haka har su kayi nisa a karatu, sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Aminu da ƴar wajena Balkisu.

Wata rana da ban zan taɓa man tawa ba shine. Ina zaune a wajen aikina Sunusi yazo min hankali a tashe, ruwa na bashi mai sanyi yasha sannan na tambayesa mai yake faruwa, gaba ɗaya a firgice yake, sai da bari ya samu nitsuwa sannan yake shaidamin cewar.

“Yau ina zaune a kan benci ina jin gidan radio sai horn na ji mai razanarwa, da sauri na tashi na buɗe abun da na gani yayi matuƙar razanani, Alhaji ne da abokansa sai ƴan mata biyu da aka fi to dasu daga cikin motar, da’alama basa numfashi, bayan sun wuce ciki sai naji zuciyata sam taƙi nutsuwa, ta bayan window na zagaya na laɓe inajin lokacin da ƴan matannan suke ihun neman taimako, narasa yadda zanyi kawai na zagaya na shiga, a’uzubillahi, da sauri na ɗauke kaina, ya sharce zufar dake kwaranya a jikinsa yaci gaba. “gaba ɗayansu sunyi tsirara suna ai kata masha’a da ƴan matannan babu ko tsoron Allah, salatin da nayi da ƙarfi shiya dawo dasu duniyar hankalinsu, a firgice suke kallona, da sauri naja zanin gadon na suturce jikin ƴan matan, sannan na maida hankali garesu ɗaya bayan ɗaya na dinga binsu da kallo. domin gaba ɗaya nama rasa mai zance musu, ɗaya daga cikinsu ne ya matso inda nake yace min kai ɗi waye,? kuma daga ina kake,? kafun na kai ga yin magana naji Alhajin yara ya kwashe da wata irin dariya ta marasa imani, ya tako har inda nake tsaye, a take ya murtuke fuska, yakalleni yace. “mai kazoyi,? ganin banida niyyar magana ya hau bani labari mai firgitarwa, ana yake faɗamin aikinsa kenan satar ƴammata ya musu fyɗe daga baya kuma idan yaga asirinsa zai tonu sai kashe ƴan matan, yanzu yamin kashedi idan har na faɗawa wani wannan zan can kasheni zaiyi nima, ya ƙarisa maganar yana mai zub da hawaye sosai yake kuka, gaba ɗaya nima jikina rawa yake yi anan yake shaidamin gaba ɗaya ƴa’ƴansa Imran da Sudais ba shine ya haife suba, shi Imran bama daga ƙasar ya same shiba, Sudais kuwa ɗan abokinsa ne, a garin kawo maza cikin gidan Mommy ta ɗinke da wani a ciki, har ta samu cikin Sudais, sunyi tashin hankali kafun daga baya suka bar zan can kasancewar itama tasan komi akan Imra. Haka muka yanke shawarar zai bar aiki a ƙarƙashin Alhajin yara, zan buɗe masa shago nasa na kansa, to a wannan ranar cikin dare muka samu labarin rasuwar mahaifin matata sanadiyar haɗari, a washagari tun assalatu muka kama hanyar Mubi ta’aziyya, dogon numshi yaja sosai ya kalli Aminu da ya sunkuyar da kai idanunsa sunyi jajir yace masa, ” ka faɗa musu abun da ya faru bayan tafiyata.

“A daran da daya dawo gida yake shaidamin zaibar aiki a gidan Alhajin yara zaka buɗe masa shago, muka ta ta murna nida ƴar uwata,, muna zaune da mahaifimmu yana mana nasiha kan rayuwa kamar yadda ya saba,muna zaune sai gani muka yi wasu ƙattin maza majiya ƙarfi sun shigo, daga bayansu kuma Alhajin yara ne ke biye dasu, agan mahaifina dani Alhajin yar ya ketawa Haulatu haddi byan yasa an riƙeni nida mahaifimmu, ya sake masa kashedi akan kuskuren da zai sake na faɗawa wani kisa ne, ashe yasa an bibiyi mahaifimmu har inda yaje da kuma faɗawa abokinsa da yayi, bauan sun bar gidan nayi kan ƴar uwata dake yashe a ƙasa na ɗagota ina kuka kamar raina zai fita, ganin Baba bai motaba yasa na kwantar da ita na ƙarisa inda yake, ina taɓasa naga yayi baya ya faɗi, wannan faɗuwar ashe bata tashi bace, rai yayi halinsa, zuciyar Baba ta buga, naga tashin hankali a wannan ranar, da gari ya waye mutane suka shigo suka ga wannan tashin hankalin, sunyi har sun gaji amma na kasa ce musu uffan.

Bayan wata uku kawai sai ga ciki ya ɓulla ajikin Haulatu, har wannan lokacin abokin Baba bai dawo ba, muna zaune a hannun maƙocimmu ne, bayan jin wannan labari na ciki yasa naje gidan Alhajin yara amma ban samu ganinsa ba, na dai bar masa wasiƙa ta hannun sabon mai gadinsa na kuma gida.

Wata rana ina zaune agun da nake yin aikin ɗinkin takami sai ga mai gadinnan da kuɗi wai nasan yadda zamuyi muzubar da cikin, tun daga wannan ranar muka fara fuskantar matsala ta hanyar kaimi hari, ganin banida mafjta sai kawai na shirya mana guduwa zuwa garin kano, acan na samu aboki mai suna Bukar, ganin yanayin da ƙanwata take ciki naga banida halin zama ban nemi kuɗi ba,anan gidansu Bukar nabar Haulatu da cikin wata biyar,abun da na lura dashi daga Bukar har mahaifiyarsa makwaɗai tane, nan na basu sauran kuɗin da Alhajin yara ya barmin na musu sallama tana kuka na wuce na tafi naiman kuɗi, ina samu ina musu aike har nasamu labarin Haulatu ta sauƙa ta samu ya mace, bayan ta haihu ne kuma aka ɗaura musu aure da Bukar.

 

 

*INA SONKU MASOYANA*🙏🏼🙏🏼🥰🥰🥰✊🏼

Leave a Reply

Back to top button