Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 52

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/23, 10:05 AM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA
UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣2️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

   Allah sarki masu
ganin laifina rashin sani yasa hakan amma duk wanda ya biya kudi yake karantawa
a matsayin hakkin shi yasani saidana basu shawara tun farko.

   Cewa zan dakatar da
rubutu saboda yanayin karatuna a yanzu sukace naci gaba duk ranan dana samu
dama na rubuta masu suna biye dani.

   Su sunyi hakkuri
amma sai masu karatun Allah ta isa suke korafi kan wai bana turowa kullun sai
najawa mutane rai.

   Yar uwa ki kwatanta
da kanki mana idan kece kullun kike abinda nakeyi a yanzu zaki iya koda rabin
yadda nakeyi din ?

   A karshe ina maiba
masoyana hakkuri don sunsan halinda nake ciki ban ci gaba da rubutu ba saida
nayi shawara daku cewa zakukaga banbamcin a yanzu sosai.

   Don Allah ku kara
hakkuri dani don Allah yan uwa bama

 Nayi mamakin ganin
wace na gani tsaye kofan namu rike da buta a hannuta daya tana fadin shi yana
inane wane irin bacina kukayi haka tun yanzu ya fara rashin zuwa sallan jam,i ?

    Yana masalaci ai
mama na fada bayan naji takai aya ga zancen ta na durkusa ina fadin ina kwana
mama alokacin ne ya dawo daga sallah yana bin mu da kallon mamaki a fuskan shi.

    Banji ta amsa min ba sai cewa datayi oho ai
na zaci ko baku tashi bane har yanzu kuna kwance nidai na shige na barsu a nan
ban koma dakin kwanan ba na dan fara gyaran falon duk da baida wani datti
lokacin.

    Naji ya shigo
falon yana rufe part din da sakata zuwa ciki sam bansan ya kawo gareni ba sai
ji nayi ya rungumeni daga baya har na dan zabura kadan alaman tsoro.

     Aikin me kikeyi
haka ki koma ki kwanta ki huta ki bari idan mun tashi zanyi komai ya fada a
hankali kanshi na saman kafadana yake maganan.

    No bari in nagama
na kwanta don na saba da hakan tunda ina sammakon fita zuwa school kullun kada
na zama lazy.

   Ko kin tafi ina nan
ai zan dinga gyarawa kafin ki dawo aikin me nakeyi yanzu da safeni ki barshi
kawai kada ki matsawa kanki da wani aiki a yanzu.

    Zan iya ai don ina
son in saba idan baka nan wa zai dinga min aiki gara kawai in saba da hakan
tunda ba kullun ne kake gidan ba ai.

    Sai kawai naji ya
kara matseni da hannayen shi ya fara dan murmushi kafin yace kamar a cikin rada
yanzun ko da nake nan nace ki huta ni zanyi komai har girkin da zamuci duk ni
zan girka muna shi.

    Jin hakan dayai
min yasa na dan lumshe idanuna saidai maganan shi ta karshece yasa nayi kokarin
juyowa in kalleshi sai bai bani daman hakan ba don kuwa ji nayi ya daukeni cak
kamar wata yarinya karama zuwa cikin dakin kwanan mu.

  Tsakiyan gado ya
ajeni tare da hawa gadon shima ina kokarin mirginawa ya samu daman cafkana a
lokacin yana fadin No zahra kada kiyi kokarin hanani jin dumin jikin ki bayan
Allah ya halatta min hakan gareki a yanzu.

    Baki na dan turo
sai hannuwan shi naji saman bakin nawa ya cafkesu yana fadin kin san dai
haramun kike kokarin aikatawa ga hakan da kike kokarin yi a yanzu.

    Kaji nace zan
aikata abinda Allah zai yi fushi da, , , ban kai karshen maganata ba naji
saukan nufashin shi a fuskana ban kumayi aune ba lokacin naji bakin mu ya hadu
wuri daya da nasa abinda yasa na runtse idanuwana ke nan lokaci guda.

  Abinda hannuwan
shikeyine a lokacin yasa ni jin wani yar ga dukkan sasan  jikina lokaci guda na kara lumshe idanuwana a
cikin jin bakon yanayin da ban taba jin irin shiba arayuwa na ba.

  Mun kai wani lokaci
a hakan dashi yana abinda yaga dama da sassan jikina duk inda yaga dama yana
tabawa.

    Yayin da idanuwana
suke fitar da wasu irin hawaye masu dumi ina jin kamar na kurma ihu azo a
ceceni don jin hakan nake kamar a dole yake min hakan.

  Kada kadakiga
laifina mai karatu don na fadi hakan a yanzu idan zakiyi min adalci duba ga ba
wani cutship mukayi dashi ba iyaka sabone amma bana soyayya ba sabone kawai da
muke jin junan kamar yan uwana jini a zamana dashi.

   Dolene a yanzu
zanka abin a wani bambarakwai duba ga yadda auren namu yake dashi ba wani
shirin hakane a zuciyana ba dole ko inga hakan a girshi gareni.

  Muryan shi naji
cikin sanyi yana fadin idan na bata maki rai Zahra kiyi hakkuri dole hakan ya
kasance a garemu tunda muna daki daya dake.

   Nina mijine mai
lafiya a jikina ba zan iya zura ido ina kallon kyakyawan suranki yana min gizo
da yawo a idanuna ba ba tare dana tabaki ba alhalin kina matar sunna a gareni
yanzu.

    Yana fadin hakan
naji mikewan shi can naji ya shige bandaki motsinshi naji yana wanka bayan ya
fitone najishi yana dan gyare gyaren jikinshi.

   Har lokacin ina
kwace rub da ciki ban motsa a yadda ya barni ba na zata fita zaiyi a lokaci sai
kawai naji ya hau gadon ya kwanta daga bayana yana fadin.

    Ki samu barci ki
huta ki natsu najishi yana gyara kwanciyan shi
tashi nayi tsab naje na shige ban dakin kafin in watsa ruwa a jikin
saidana tsaya na gyara ko ina na bayin na samu natsuwa don na saba ban dakina
ni kadaine a gida don haka yanzu abin ya zama min bakon yanayi a yanzu sai nake
ganin an takura min a haka a rayuwana.

   Nayi wanka kamar
yadda sharia ya koyar ayi duk da nasan bamu shiga juna nidashi ba amma zuciyana
bai bani ba saida nayi wankan tsarkin na samu natsuwa a zuciyana.

    Nafito na zauna na
gyara jikina ban biye masa ba bayan na gama sai na mike na fita zuwa kitchen
dina sai karan bude kofana da yaji kawai lokacin ya fara barci don shi ya samu
dan natsuwa a zuciyar shi a hakan daya faru tsakanin mu din.

  Kitchen din nabi da
kallo naga komai akwaishi a lokacin cikin kitchen din shawara nayi na dauki
roba na dauko na debo arishi na fara ferewa.

    Allah ya taimakeni
nan da nan na gama na dora mai a wuta kamar yadda ummah ta koya min idan za a
soya don haka kawai wata rana idan muna hutu ummah zata shigo da safe tace in
fito muyi girkin abinci.

  Wunin ranan gaba
daya tare zamuyishi muna girki koda Tani tazo saidai tace ta huta ko tayi dan
gyare gyaren gida a wanan wunin.

     Hakan yasa na
koyi wasu abubuwa da dama a rayuwana ummah kance gara na koya don ba,a san
gidan da zan fada ba sai wanan lokacin nakan tuna da abubuwan da suke faruwa in
muna ta jajirce tana koya min abubuwan daya kamata ya mace ta koya tunna gida
don irin wanan kaddaran akewa gudu dama.

     A tsanake nagama
duk abinda nake sonyi na zuzuba a cikin warmers na aje na iyayyenshi a gefe
daya don ina jin kunyan shiga part din nasuni.

    Daki na koma na
gyaro ko ina sai gadon da yake kwancene kawai ban gyara ba lokacin duk da
gajiya ban yarda na kwanta ba a lokacim saima wutan abincin dana dora a lokacin
don ba saurin aikine dani ba.

   Yasa nayi hakan son
kada na dinga jimawa suga nawata har suzo muna ganin laifin juna dasu don dole
in dinga girki dasu kodon hakkin makwabtaka dana haihuwa.

   Yayi mamaki daya
tashi yaga irin aikin danayi duk yana kwance yana barci yake ta gaidani da aiki
yana fadin sannu da aiki har sau biyu.

   Na dan juyo daga
inda nake zaune ina kara kwaliyan a fuskana ina gadin abincin su mama na nan a
kitchen barin dauko maka ka mika masu don Allah.

   Yace haba dai aida
bakiyi dasu ba don suna da komai suma a part din sun an aje masu wannan namune
nan nidake aka aje muna ai.

    Haba dai ka taba
ganin hakan zai yuyu na dafa abinci a gidan nan ban zuba masu ba ai sai a
zageni idan nayi hakan tun yanzu.

   Wa zai zageki kan
hakan dole ki daina don duk abinda na sayo insha Allahu zan saya dasu don me za
a dinga yin girki biyu kuma ?

   Ki dafa iya cikin
mu daga yau ninace kiyi hakan aiba wani ba yana fadin hakan ya fice zuwa wurin
su bayan ya dauki abincin ya fita dashi zuwa part din.

   A waje ya samesu
suna hada shayi ya gaidasu suka amsa mai ya aje kayan abincin a gaban Dije dake
zaune yana fadin Dije ga abincin amarya tace a kawo maku.

   Don da Dijen yafi
sabawa kuma ko banza tana gaba da uwar tashi ai kuma ga kara kannen shi da
sauri suka taso suna bude Dije na kwabe masu hannu tana fadin nida aka kawowa
ban bude na gani ba zaku bude.

  A, a innan mu Allah
sa dai ba kwajabon yaran zamanin nan bane wai abinci aka kawo maki kici ki zure
zuwa anjima uwarshi ta fada.

    Kema ke sani misun
ka iya yanzu balle wanga da ta fito gidan masu kudi mizata iya banda kwaliya da
saka turare mai kamshi.

   Yana jin su ya kara
daure fuska ya mike yana fadin zan duba dabbobin nan don yau da dare uwar garke
wani kuka naji tanayi kamar taga wani abu.

   Wace su zasu tsaya
jiran ka har wanan lokacin kana can kwance kana kwana tun wuri kada ka dauko
wanan hutun na safe ya tabama bidan ka.

    Bai juyo ba yasa
kai ya wuce wurin dabbobin a baya  a
lokacin ne Dije take fadin wai Rashida mi da baki kama girman kina ?

   Shiru sukayi gaba
dayan su wurin kafin can mahaifiyar nasa tace a, a wallah in ya koma maki baran
bujen mace aike zaki ganin takaici nai ke daya.

   Ke inna mu gara
aimai fada ya gane hakan da ya dauko mata bashi da amfani tun wuri kada azo da
baya abubuwa su biyo baya kuma.

    Bamu ganin komai
sai alheri tunda ita tace tana sonai da amarai mi zaya biyo baya kuma amren da
sunkayi na soyayya tsakanin su ?

   Tana fadin haka ta
dauki kwano ta shige daki ta barsu da kayan a wirin don haka yar babban ta jawo
basket din ta bude tana kallon abinda ke cikin warmes din tana yamutsan baki
tare da fadin.

    Wanga abu aiko ni
daya ina iya cinyeshi innan mu kega abinda akan zubu muna wai mu duk addashi
haka tana karkata abin abincin don takaici.

    Cikin kashe murya
kada Dije taji su uwar tace a,a wallah waka magana yanzun innan mu tayo cikinai
tace za a damu yara.

    Walle magana akai
ke tai kice ta karo muna wanga ko ku baya isa balle mu duka yar naima da bakin
rowan tsiya kamar nagode wanga abincina za a kawowa mutane shiya.

    Ina daga cikin
dakin zaune ina zancen zuci naji muryan sama sama ana sallama a gadarance na
bude labule ba gaisuwa ko wani magana yarinyar ke fadi a wullakance .

   Wai inno tace ki
zubo muna mai yawa wanga daki bayar baya isan mu ko muna balle dasuwa na kasa
fahintar mai take fada saida ta kara maimaita mun maganan ta na gane.

   Cikin dan fara,a nace
ayyah wallahi shi kadai na zuba babu wani sai naga tayi min wani kallo kafin ta
juya tana magana kasa kasa cikin fisge fisge ta tafi.

   Na juya ina shiga
daki tare da dinbin mamaki bansan lokacin da hawaye ya zubo min ba a fuskana
natakaici da bakin ciki don bawa kowa rainin wayau banso kuma ni ayimin hakan
ko kadan.

   Ga wa yan nan
mutanen da alama suna da irin halin wullakanta mutane din nan irin na nakasa
dayiwa mutum kallon rainin wayau da wullakanci.

    Mii kawoki sashena
ya tsare kanwar da tambaya tayi tsuru tsuru da idanu nan ta fara inda inda tana
fadin innota tace in taho a karo muna abincin don baya isan mu .

    Idan bai isa ba
kuba zaku iya dafawa ba koba akwaishi a wurin kuba an kai maku naku nan dai ya
tsare yarinyar da fada sosai yaci mata mutunci ta tafi .

   Tana shiga part din
su ta dangware kulan dake hannunta ta fara cicika uwar ke tambayan ta da mi
ankai maki kuma kinka dawo kina wagga cika haka ?

    Ni dai naji motsin
shigowan shi dakin amma banga ya shigo ciki ba naji fitan shi kuma can ya
samesu a part din baiga Dije ba a wajen ya shige dakin Dije din ya sameta
zaune.

  Yake fadin Dije mi
da baku dafa abincin ku ba nan ba komai na aje maku ba ga kuma wanda aka kawo
gidan su princess.

    Wani abu akayi ko
wanda ta sako muna kaka magana kaine yake fada mata an tura Asmau ta karbo wani
yanzu wai wanan baya isan su.

  Sallati Dije din ta
saka tana kokarin mike tsaye ta tashine kanwar mahaifiyarshi ta shigo tana
fadin kai dan Dije karanmu kakawo inda innan mu don mun aikawa matarka ta kara
muna abinci wanga data sako muna bai isan mu ?

    Inna Shatu dole in
yi magana yarinya ga bata saba da rayuwa haka ba yanzu yanzu da kawota zaku
daga mata hankali don gudun hakana hau yasa na kawo komai nan na aje maku.

    A,a yanzu ai shike
nan ni gobema tahiyata zanyi gida dama son tasan wadda akayine ta gyara yasa
ankayi mata magana nikan gobema gidana nayi gumi zan komawata.

    In ke tashi kitai
anka nice kitai anka wane irin dabia na haka wai kuka son tsirowa mutane dashi
yace dije saida nace kadama tayi da kuwa.

  Tace a, a ko banza
akwai hakkin makwantaka bata iya girki gaku gida bata saka maku shiya ba data
bi maganata ta kyale da duk wanga ba ayita ba tsakanin mu.

   Waishi hauda yakayi
don abinci walle da yaranga basu cishi ba da an maisuwa masu da abincin su kaka
zuwa nan ka kawo wa mutane diban albarka wai kai mai mata.

   I aniya in baka
koma mijin tace ba gidan nan jin fadan mahaifiyar nasa yasa ya mike ya tsaye ya
fice daga dakin dije din kaitsaye ya shige su ya fice suka bishi da kallo.

   Ayadda nake ya
sameni yana sallama ban iya amsa mai ba yake fadin lafiya ko wani abin tazo
tayi maki a nan din ?

   Kai na iya girgiza
masa don ba zan iya magana ba shiko yayi min tambaya kala kala ina bashi amsa
da kai don ban iya magana da baki don yadda nake ji a lolacin nadai nuna mashi
ba komai a lokacin .

   Yace zahra idan
kina wanan yanayin ba zanji dadi ba don sai in dauka ko nine bakiso ko yanayin
gidan namune bai maki ba .

   Yana fadin hakan na
mike na shige daki na kwanta rub da ciki naci gaba da kukan da nakeyi harda
shesheka ina hadiyan zuciya.

    Can ya shigo ya
dan tsaya yana kallona tare da fadin o,o zahra tun farko gudun haka yasa na
fada maki kiyi girkin ki iya bakinmu mu kadai.

   Can kuma ya kai
zaune yana fadin haba zahra idan na bata maki rai ko wani nawa don Allah ki
daina kukan nan kiyi hakkuri don Allah.

    Da kyat na iya
budan bakina murya ciki ciki nake fadin No Master ba hakana bane na daiga na
zuba masu abincin ai kuma zasu dawo har yarinyar na nema tayi min rashin kunya
haka ?

   To kiyi hakkuri ki
daina kukan nan ni zan dauki matakin hakan da kaina don ko zan hanasu shigowa
part din nan ga baki daya.

    No ka barsu idan
kayi magana tsanata zasuyi ga baki daya kaga kuma hakan ba zai min dadi ba don
Allah ka kyalesu kawai nima ba zan kara kula haka.

    Ya zauna yai shiru
ya dade zaune a hakan ba tare da yai magana ba sai zuwa can yace kiyi hakuri
don Allah nasan ki da hakkuri ki kara har zuwa lokacin da Allah zai bamu namu
wurin mu tashi daga nan din insha Allahu.

   Ba komai nace na
juya nayi shiru kowan mu yana tunane kafin a kirani a wayata na duba ummah ce
don yanayin muryata naki dauka.

   Ya kalleni yace
waye ke kira ba zaki daga wayan ba ki amsawa maishi ummah ce na bashi amsa yace
ki dauka mana sai hawaye ya zubo min na kifa kaina a filo ina kuka ganin hakan
shi ya daga wayan ya dauka.

   Tare da sallama
yace ummah ina kwana ta amsa mai yake fadi cikin ladabi wallahi ummah gata
kwance bata jin dasin jikintane tayi barci.

   Allah ya sauwa
ummah din ta fada tare da fadin dama kannen kune suke son a kawosu wurin ku
tunda basu da lafiya a bari sai wani jikon
ya aida an barsu sunzo ummah tunda gani.

    Tace su bari wani
jikon sazo yau dai kan suyi hakuri kuma takardun ta suna nan kaf na hada mata a
wuri daya zansa Tani tazo mata dasu anjima ta duba jikin nata yayi mata godiya
ta kashe wayan.

Leave a Reply

Back to top button