Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 29

Sponsored Links

29-. Ji yayi kanshi ya dauki matakin wani irin zafi. A gefe guda ya kura mata idanu yayi, duk yadda yake bukace da ita, ya watsar da ita domin ba zai kuma bin ta kanta ba, ba zai dauki reni daga mace ba, duk kaunar da yake mata. Don haka ya dauke kanshi daga kanta, yayi alƙawarin ba zai bukace ta ba, ba zai nime ta mishi wani abu ba. Haka yasa baki daya ya kame kanshi sama da can baya. Kafin dare gari ya dauka an kaiwa Mayor da matar shi hari a airport. Wurin karfe tara Elbashir ya shigo gidan yana bin Malik da kallon banza. “Kayi hakuri! Tsoro nake kada wani abu ya same ka!”
“Shi ne zaka kulla min sharri?” “Idan akwai abin da ya fi sharri my friend zan maka domin na kubutar da kai!” Zama yayi ya cilla mishi wayarshi. “Sakon Shatima!”
*Idan kana tare da Malik sai ya maka butulci, yanzu ma gashi ya saka an kama ka, ka haɗa hannu da ni!*
_Bana hada kai da maciyi amana!_ Elbashir ya tura mishi, “nima ya turo min number Zainaba!” Zunkud’ewa Elbashir yayi kamar zai fado kasa. “Yana nufin zai gaya mata ne?” Murmushi Malik yayi ya ciro wayar Zeeno yana nuna mishi. “Na dauke wayar lokacin da take jarabarta da ta saba, yanzu haka na cire layin yana kan wayata, na mai da mata daya layina da babu kowa a kai.”
Shiru yayi yana kallon yadda Malik ya kware a kowani fuskar. “Amma da zaka yi film sai ka samu Oscar awards.”
Girgiza kai yayi yqna faɗin.”ba haka ba ne, ina fama da ita da wani rikicin ne, taya zan kuma barin wani abu ya kunno min kai? Ina son magance matsalar mu, shi yasa na dauke wayar a jakarta tana can tana jin haushina.”
“Allah ya kyauta!” Daga haka suka tsinke da hira. Jama’a Madam tunda ta shiga dakin shi, tayi wanka da sallah, ta tsaya a gaban Mirror tana kallon cikinta, da ta gaji ta koma ta zauna hannaunta biyu akan cikinta, tana murmushi ta manta da abinci da zarar cikin ya motsa zata tab’a wurin.
A hankali yunwa yayi ta damunta, ita da abin cikin, ganin Malik bai shigo yasa ta mike tana me nufar hanyar waje daure d towel. Allah yasa shi yake fuskar kofar fita Elbashir ya bata baya, ganinta daure da towel, tana gyara rikon da tayiwa towel din yasa shi daka mata wani irin tsawar da sai ta ta juya da mugun sauri, tana me fashewa da kuka. Shi kanshi Elbashir sai da ya firgita. “Lafiya?” Jikinshi yana rawa ta nufi cikin gidan, ya same ta a durkushe tana kuka. “Da kin sake kin fito Elbashir ya ganki wallahi da na makantar da shi, ke wawuyar ina ce? Zaku futa daga ke sai towel?”

“Tow ba yunwa nake ji ba! Tunda nazo hanci abinci ba, baka kawo min abinci ba ka bar ni a daki Ni ɗaya!” Shiru yayi yana kallonta, sai kuma ta bashi tausayi yasan bata iya kome ba, nufar wurin kayanta yayi ya bude jakar, ya shiga ciro mata kaya dakyar ya samu wata gown mara nauyi da takura, ya saka mata. Idanunshi yana kan kirjinta. Janye idanunshi yayi ya nufi hanyar waje, tana bin bayanshi. Yana zuwa ya nufi kitchen dake a falon yaƙe. Daga falon kana hango abin da ake yi, ya fara bude firji ya sauko kwai shida. Da indomitable.
Ya daura ruwa, ya daga mata guda biyu. Saura hudun ya ciro kayan miya, green pepper, red pepper, carrot, chicken breast. Ya fara yanyankawa sannn ya saka a wata yar ƙaramar turmin karfe. Ya saka namar ya dake shi tass, ya juye a wankakken frypan.ya d’iga mangyada ya daura akan wuta, yana ya tattara yankakkken kayan miyar ya zuba a cikin frypan din, ruwan da ya daura na tafasa taliyar indomitable ya rage karfin wutar ya saka taliyar yana kallon yadda take hadiye yawu.
A ran shi ya ce. *Kamar da gaske, nan kuwa tafi kowa fitina!* Yana soya kayan miyar ya juye namar ya saka yar gishiri da sinadarin dandano, ya zuba garin citta, kanumfari da garin tafarnuwa ya nuna mata curry ya ce mata. “Kina so ko na bari?” Lumshe idanu tayi tare sa gyada kai, a hankali ya zuba kadan, take kitchen da falorn yq dauki kamshi. “Allah ya tona asirinka, wato girki kake don mugunta shine har sa daka tsawa na dawo nima zan ci!” Ban za yayi mishi yana fadin. “Yawwa ka duba can akwai key din dakin da yake sama, mu zamu zauna a kasa, ka zauna na wani lokaci muga yadda zamu shawo matsalar!”
Sannan ya koma ya cigaba da aikinshi, dole ya kara indomitable din, ya juye na farko ya daura wutar na biyu, ya cigaba da aikin namar shi na nuna ya fasa kwai a wani bowl, ya zuba kayan kamshin indomitable ya kada sannan ya zuba akan sauce na naman nan, ya zauna yana motsawa har ya nuna ta rufe a hankali.
Dauko flat yayi yana faɗin. “Yanzu zaki ci kinji!” Gyada kai tayi, bude firji din yayi ya dauko aya, kankana, apple, da sauran kayan fruit ya markade mata su, ya juye mata bayan ya tacce. Sannan ya dauko parsley leaf ya tsinke guda biyu masu kyau bayan ya juye abincin, sannan ya zuba mata miyar a gefe, ya saka mata ganyen nan a saman abincin yakawo gabata ya ajiye mata.
“Oya digging!” Yatsuna fuska tayi tana faɗin. “ban tab’a cin girkin namiji ba!”
“Karya kike domin duk girkin da kika ci kafin muje Keivroto Chef yake yi.”
Tura baki tayi ita ya ƙaryatatta, haka ta cinye abincin, bayan ya gama nasu da Elbashir. “Uncle Elbashir abincin nan yayi dadi, matsalar yayi citta ne dayawa.”
“Ke kin san waye Malik kuwa?” “Maza antaya lomarka, akwai wanda ya zai bada labarin Malik bayan ni ne?”
Girgiza mata kai yayi yana faɗin. “Elbashir sai Shatima.”
“Ni fa?”
“Hmmm! Lokacin muna gidan yari, shi yake dafa abincin gidan tare da Chef!”
“Aha ashe kun jima da Chef din”
“Sosai mana” kamar abin arziki ta zauna ana hira da ita. A ranshi ya ce kafin an jima ta birkice, can ta fara hamma. A hankali ya isa gaban ta, ya dauke ta cak.
“Nayi nauyi fa!”
“Eh ba laifi kan sai flour, ya sa baking powder. Ya kada sai da ya hadu sosai ya fara soya mata a nonstick. Yana zubawa ya koma gefe ya dauko wani karamin tukunya ya zuba sigar ya diga lemon tsami, ya bar shi ya narke sosai, sannan ya kashe wutar, ya barta, ya cigaba da soya fancake yana ganawa ta ce mishi. “Me kake yi ne?”
“Abu ne ina zuwa!” Ya bata amsa, sannan ta nufi wurinta da kayan ya ajiye mata.
Ta zauna tana kallonshi. “Ka sani jin kamar da ban fito ba!” Tun da kuruciyar shi yayi fatan zama kamar mahaifinsa, wurin yiwa mace hidima.
Cigaba da aikinshi yayi ta zauna a kasa ta ware kafa, tana kallon tvn. Kallonshi tayi tana jin wani abu yana yawo a jininta da jikinta,dakyar ta hadiye yawu. Ta koma ta zauna sai da ta cinye ta matsa jikinshi tana jin dumin jikin shi.
Yana sane da ita, musamman yadda take kara shige jikinshi. Janye ta yayi yana faɗin. “Kin ga ni ina fama da basir!” Sake baki tayi ta ce. “Basir!” “Eh!” Kamar tayi kuka haka yake ji, don haka ta kwanta a jikinshi tana kuka kamar wacce aka zane ta.
Dakyar ya lallabata, har tayi barci ba don kome yaki ba, sai don ba mamaki gobe ta narka mishi rashin arzikin, shi mutum ne da yake da mugun taka tsantsan akan mutane ba kowa yake sakewa jiki ba, shi yasa lokacin da ya fara jin ya aureta yayi tunanin haka. Yan matan yanzu basu da kunya, kuma abin da ya guda kenan kada ta rena shi, ya za ayi taga girmanshi har da furfuran. Yayi wanka a gabana dole renin ya kara ta’azara.
A hankali ya nufi dakinta da ita, ya kwantar da ita zai mike ya janyo shi ya ɗan sunkuya. “Ka kwanta a nan”
*Tab’ gobe ki karta min rashin mutuncin!*
“Ina aiki ne idan na gama zan dawo” ya fada mata haka, don ta kyale shi. Yana futa ya sauke ajiyar zuciya, Bashir ya samu ya saka Påñçäkęš a gana yana ciki a hankalin shi kwance.
“Kai dai wata rana sai ka samu wanda ya zuba maka, shinkafar bera a abinci”
“Ya kyauta min! Don bakin hali ina cewa kullum abincin waje muke ci tunda matarka tazo ka daina mana oda sai dai muce na hannunka”
“A da bana tsoron abin da zamu ci, amma a yanzu Shatima niman cutar da makusanta na yake taya zan bude ciki na ci abincin waje.”
“Kai kuma kana tsoron kada mu mutu ko? Bayan ko a kan idanunka ne mutuwa zamu yi balle a bayan idanunka.”

“Kula da kai yafi bada sako, da na ji zafin wani Gara na kiyaye daga kaina.” Haka suka yi ta hira har dare ya raba, sannan suka yi sallama, Bashir ya koma sama, shi kuma ya kashe wutar gidan baki daya, ya haura can samar gidan ya shiga dakinshi na musamman. Computers ne da manya manyan wall TV, na ilahirin titunan garin ne .
Sai wani karamin computer, wanda yake da shi na musamman. Abu ya saka a kunnen shi. “Ya yarinyar take?” “Suna lafiya da kanwar mahaifiyarta!” “Ubanta ya san ina bibiyarta, don haka ka kula sosai.”
“In sha Allah”
Daga haka suka ya rufe laptop din, yana kallon airport ɗin da kuma yadda aka samu maharan. Wayar da ya samu a dakin ya kira wani layi ya ce masa. “ka tafi titin Nelson Mandela, akwai wata bakar Prado. Ka tabbatar min idan ka ganshi ka turo min number motar!”
Bayan kamar minti ashirin, aka sake kiranshi. “Eh na gani, me za ayi?”.
“Ka bar wurin, zan gaya maka yadda zaku yi;”
Daga haka ya cigaba da wasu binciken, shigowar Lalla Salmah yasa shi murmushi, yayi ya ce a ranshi. *Kin kyautawa kanki! Sharrinki zai biki*
Haka ya gama latsa wayar,ya tura musu.
“Kada ku tsaya,kama Shatima ko Lalla Salmah. Ku barsu halinsu zai kama su.”
“Yes sir” fita yayi daga cikin gidan ya kunce wasu masufaffun karanunkan da ya kiwota su da fushi. Suka samu wuri suka boya.
Sannan ya koma dakin Zeeno ya samu tana ta barci, burge shi tayi ya wuce tare da rufe mata kofar. Ya dawo Falo ya kwanta.
Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button