Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 19

Sponsored Links

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

Bisimillahirrahmanirrahim.

**
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*

*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

 

*19*

 

Saida fareeda ta kwashe kwanaki bakwai da tafiya,labeeb be nemeta ba,dan gaba ɗaya fadeela ta gama cikashi da soyayyarta,ko kaɗan beson rabuwa da ita,ko office a dole yake zuwa.

Fadeela yanzu ba faɗa ba hayaniya ta riƙe mijinta kam a hannuntw yadda takeso yake mata,ba tare datasha maganin mata ba.

Wanda hakan sosai yasa ta tunanin ajiye shan magani na har abada akaro na biyu.

******

Anata ɓangaren fareeda tun bataso mahaifiyarta tasata dole ta dawo tana so,shan magunguna kamar hauka,sabida ƴar chadi tayi imani da magungunanta fadeela kesha yasa be biyo sawunsu ba.

“fareeda zaman nan haka baze yiwu,dole musan abunyi,kina kallo yanzu da biyu ake shigowa gidannan dan aganki aga zaman me kikeyi to ni nagaji number mahaifiyarshi zaki bani”cewar ƴar chadi cikin damuwa.

“mama kar yaga kamar an haɗashi da itane aje baa gyara biyar ba a ɓata goma”ta faɗi a sanyaye.

“shashasha a haka aka ƙwace miki miji,ke komai baki iyaba se ankoya miki”

Number fareeda tabata ba dan ranta yasoba,se dan bata da yadda zatayi.

Bugu ɗaya ana biyu hajiyar labeeb ta ɗauka,bayan sun gaisane ƴar chadi tace”hajiya mahaifiyar fareeda matar ɗanki labeeb ce”

Ayko cike da faraa hajiya ta ƙara gaidata samnan tace”wlh munata ƙoƙarin zuwa Allah be nufa ba tunda abun na sauri akayi,gashi lokacin data tare nan naje yola bana nan,basuzo guna ba banje ba gunsu nima,suna lfy deko?”cewar gajiya tana murna .

“Allah sarki,yanzuma hajiya wata ƴar matsalace ta faru tsakaninta dashi,to tazo gida yau kwana takwas be zoba be kiraba shine yasa nace duk yadda akayi bakusan da maganarba”cewar ƴar chadi.

“amaryar labeeb ɗince har tayi yaji,me akayimata agidan to wlh bazan ɗaukaba,barni dasu zani gidan anjima gobe yana nan zuwa wlh kuma aba yarinyar haƙuri kuma kuyi haƙurin”cewar hajiya cikin faɗa

suna sallama ƴar chadi ta dubeta tace “to da kince kar akira yanzu ba gashi kiram yayi anfaniba”ta faɗi tana murmyshi.

Itade fareeeda ba baka sai kunne burinta be wuce taga mijinnata.

Itako hajiya suna gama wayar tasa driver yakaita gidan nasu labeeb kasancewar week end ce tasan zata sameshi agida.

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button