Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 68

Sponsored Links

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/10, 10:40 PM] +234 706 815 1331: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣8️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Jiki wasa wasa yaki dadi gareni a kullun sai kara gaba gaba
yake min hakan yasa har na dauke kafa ga zuwa makaranta a lokacin.

   Tun hankalin inna
bai dagaba har wani dare dole ta fito da damuwanta fili ta nuna tausayawanta
gareni tana fadin kalamai a tausashe saboda ta tsorace da yadda tagani kwance.

   Ganin zan mutu a
gida sai magani nake sha ba a san makarin ciwo ba yasa nasa hannatu kiran ummah
ta fada mata halinda nake ciki din.

   Sai cewa ummah tayi
yanzu hannatu ya kuke son nayi tunda nauyin ta ba a hannun mu yake ba yanzu
kawai dai ku kira mijinta ku fada mai abinda yace sai ai hakana.

 Ga hankalin hannatu
duk a tashe yake shi kuma macan hakane gashi suna test a lokacin suna gab da
zana jerabawan fitane a lokacin.

  Data kirashi cikin
daren tana  mashi bayani hankali tashe
murya kamar mai kuka yake fadin don Allah ummah tayi hakkuri a taimaka mashi ga
halinda yake ciki.

  Amma sai hannatun ta
kasa kiran ummah din don yadda sukayi da ita da farko dole dai shi din da kansa
cikin dare da inna taga zan mutu ta kira shikuma ya kira sai hankalinta ya daga
sosai ta kira shehu da daren nan yanzo suka kamo hanyar gidan mu din.

    Da karfe Biyar da
rabi na asuba ummah sukazo da shehu aka daukeni zuwa asibiti muna zuwa fada
suka fara cewa yaya akayi har na gala baita haka ba a shigo dani asibiti ba.

    Nan dai suka
karbeni baya  korafi da sukasha wurun
nurse din tayi muna hanyan ganin likita ya auna yasa a sayo ruwa da magani aka
dora min sai lokacin na samu barci mai nauyi ya daukeni sosai.

   Ana idar da sallah
asuba yana kiran layin wayana yajishi kashe sai na ummah din ya samu tana kuma
azzakar bata magana a lokacin sai ta idar.

  Hakan ya daga mai
hankali ganin ya kira har sau uku karshe ma ta kashe wayan gashi duk sauran
wayoyin nasu basa shiga a lokacin nan ya soma shirin baro zaria duk da yasan
test din dake gareshi yana da muhinmanci sosai a lokacin.

    Ya gama shiri zai
fito wayanshi ya dauki kara ummah ce mai kira a lokacin gabanshi na faduwa take
fadin tana sallah a lokacin yasa bata daga waya ba.

   Bai tsaya gaida
itaba yace ummah ya mai jikin kuma tace da sauki sosai ta samu barci gata nan
kwance tana barcin tunda aka fara karin ruwa.

  Sauran gwaje gwaje
sunce sai gari yawaye za ayi ka kwantar da hankalinka don da sauki sosai insha
Allahu zata samu lafiya yace to ummah da yanzu zan biyo hanya inzo.

  Tace a,a ba ance
kuna test bane kokazo me zaka iya mata kadai mata addua shine take bukata ta
samu lafiya sosai fa yanzu don numfashin nata ya koma daidaima a yanzu.

  Jin hakan yasa shi
ya tsaya ba don yaso hakan ba a lokacin anyi duk wani abinda yadace ayi amma
sai cewa sukayi maleria da thaphod ne ke damuna a lokacin.

  Karfe takwas ummah
ta kira gida take shedawa mama suna asibiti dani tunda safe mama din ke fadin
me kuma ya sameni tace zazzabine dai tayi Allah ya sauwaka ta kashe wayan a
gundure.

   Bayan ta kashe take
jan tsoki tana fada su gwaggo shafa ne dai sukai tawaga sukazo dubana anyi sa,a
lokacin Tani ta kawo kayan da ummah ta umurceta da takawo muna asibitin.

   Da badon hakan ba
babu komai da inna tayi yunkurin biyomu dashi asibitin saidai sunzo dubana ita
da yaranta tunda farar safiya shine kawai gaskiya kokarinta a lokacin.

   Karfe daya saura
yana cikin gusau asibitin ya nufo daga nan ko gida bai isa ya aje kayanshi ba
yazo har dakin da nake kwance har lokacin barci nakeyi sosai don gaskiya na
wahala.

  Kwana biyu bama
barci da hannatu data zauna a wurina a karshema har makarantan itama ta daina
zuwa tana zaune tare dani a gida tana kula dani don har mutanen gidansu saida
sukazo gaidani.

   Mamako Abba ta kira
tana fada wai ummah tana kokarin raba daya biyu duk hakkurin da takeyi da halin
ummah zata kaita makura wai suna asibiti dani amma ummah bata fada mata ba sai
da ranan nan donta dauketa muguwa kome ?

   Amma ta fada min ta
kiraki tun takwas na safe ma don na tambayeta ta kira ta fada maku tace eh
yanzun ta gama waya dake ta sanar maku.

   Wai halin hjy
salmane kuma baka sani ba ni dai na fada bana son hakan da take min gaskiya da
wani abune da yanzu ta kira tana fadama sai kawai ta kashe wayanta lokack guda
a hasale.

  Duk da yaji mamakin
hakan  data fada amma kuma ba zai iya
cewa komai ba a lokacin karshema kiran ummah yayi yana fada don me bata fadawa
mutanen gida zancen ciwona ba.

   Ina wani abune
aiduk ita tajawa kanta wanan wullakancin tunda ita tanacewa wanan fakirin yaron
tace shi zata aura yanzu duk wullakancin daya biyo baya ai ita tajawa kanta
kuma ?

    Ummh,humm ka gama
kada ka mace da duk mai rai baya wuce kaddaransa a rayuwa ni ban raina da auren
zahra da yaron nan ba don bansan dalilin da Allah ya hadasu tare ba.

   Kuma ai naga banina
aurawa yarka shiba kai kaga dama ka aura mata shi a matsayinka na ubanta koka
taba jin inda mace ta aurawa yarta aure koda kuwa shegiyace ita ?

   Sannan ita hajiyan
datace ban fada mata ba Allah ya sheda karfe takwas na kirata na fada mata
itace mutum na farko dana fadawa kuma har kusan duk yan uwa sunzo asibitin nan
duban mu.

   Kawai idan wani
tsegumi takeji dashi ta fada zaifi amma ba wanan ba taje tayishi a wurin ka
kaida kake daukan tseguminta ba bincike ko yaushe ni ba wanan bane a gabana
yanzu ba.

   Tana fadin hakan
ranta ya gama baci sosai a lokacin don haka ta kashe wayan a hasale Allah ya
taimaka daga ita sai tani dake shirin zuwa gida a lokacin sai koni dana falka
banyiwa kowa magana ba nake jin yadda sukeyi da Abba din.

  Da kuma fadawa Tani
abinda ya faru din da takeyi a hasale tana hawaye tare da fadin kasheni suke
son yi ni wanab abin ya isheni a yanzu gaskiya idan kayi magana ace kayi
hakkuri don yara kuma.

   To hjy idan ba
hakkurin ba me za a baki yanzu halin hjy maimuna ne kin saba dashi makircine
kawai irin nata ta dauka wani kudi zai turo maki ai laluran nan dashi shine
take kokarin bata tsakanin ku ayanzu.

   Makircine kawai
irin na mata ita dai kada taga anyiwa yar uwa wani hidima sai a yaranta kadai
gashi kuma Allah ya kadara yaran nata da yan uba.

   Ni bashiba Tani
yadda Alh ke biyewa maganan ta ya rufe ido yana neman yaciwa mutum mutunci akan
zancen ta haka suka kwasa da hjy karima wanan zuwan da sukayi akan dan abu
kadan yaso ya bata mata kanta ita kuma ta rufe ido taci masu mutunci dukkansu
gaba daya.

   Karshe sukai
tafiyan barambaram suka koma kowa da tasa tafiyan jin hakan tani tace kin gani
ba haka take ta kokarin yi gareki amma hakkurin ki ya hana tayi nasara akanki
shiya take kara kaimi ga aniyarta din.

   Kiyi hakkuri hjy a
kullun shi muke baki kinga kar yar nan ta falka ta sameki a cikin yanayin bacin
rai haka kuma ba zataji dadin ganin ki hakana ba gaskiya .

  Ni yanzu zan koma
kada yaran su dawo su samu ba kowa a gidan kuma su shiga damuwa don ba wani
kulawa zasu samu a wurinta ba.

   Mummy kizo wai inji
daddy yana falonsa zaune Salima ta fada daga kofa inda take tsaye hanbayenta na
cikin aljihun rigan dake jikinta lokacin.

   Ta dago cikin
takaici tana kallon yar nata tare da fadi
sai yace idan kinzo ki mun kerere a kai ki fada min ko wai Salima meyasa
baki da tunane ke kullun kina abin yara ?

    Mummy shiyasa na
kiraki ba nina fadi hakan ba ta fada cikin shagwaba tana junawa zata bar dakin
a lokacin tace kaji sakarai ina magana kina kokarin wucewa.

  To kiji da kyau duk
wanan sakarcin yanzu ya kamata ki daina shi ki nuna kin girma kinsan ciwon
kanki don bamu kadai bane a gidan nan yanzu don kinga ya kwaso muna wa yancan
mutanen duk da nasan anyi hakan ne da wani manufa a garemu.

   No mummy ba matarsa
bace don haka yana da right din da zai kawota nan mana ta zauna damu saidai
abinda  ban yarda ba shine tace zata  rainamu.

   Wani kallon ashe
kina da wayau uwar tayi mata ta kawar da kanta gefe daya tana fadin zamuyi
maganan hakan anjima yanzu kice masa kin samu ina bayine amma kin fada min.

    Koda ta je fadawa
mahaifin nasa saita samu hjy murja a falon zaune zakace bata taba sanin taba a
duniya sai cewa da tayi daddy na samu tana bayi amma na fada mata yace is
alright zaki iya tafiya.

  Ta juya zata tafi a
lokacin hjy murja tayi karfin halin fadin salima mun sameku lafiya ya karatu ?

    Lafiya kawai ta
amsa dashi tana ficewa suka kalli juna da mijin tayi wani irin guntun murmushi
mai nuna cewa dama na fada maka ai.

    Sai ji tayi yace
dama wai baka ga juna bane tun jiya din tace ga alama ka gani kuwa irin abinda
nakewa gudu ke nan tun farko nace ka barni gida can din yafi min rufin asiri
don nasan halin hjy da yaranta sarai.

   Zasu iya komaiwa
mutum idan sunyi niya balle a yanzu gidansu nazo na samesu don haka zasu
shiryawa hakan baiyi magana ba sai zuwa can da yace nasan da hakan amma wanan
shine tsarina a yanzu naga na hada kan iyalina a wuri daya.

   Sun kai wani lokaci
a zaune wurin kafin ya kalleta yace zaki iya tafiya ki barni da ita nan gaba
zamu zauna zan fita yanzu zuwa office tayi mai Allah ya tsare ta mike ta fita.

   Shima bai dade a
zaune ba ya mike ya shige ya shiryo zai fita suka hade ko kallonta baiyi ba
yasa kai zai fice take fadin salima tace kana kirana ?

    Banda wanan time a
yanzu ya fada yasa kai ya fita taja tsoki itama ta fice daga falon zuwa part
din ta har ta zauna wani zuciya ya debeta ta mike zuwa part din da bakin nasu
suke.

  Zaune suke dukkansu
a falo suna hira saigata ji sukayi kawai an fado dakin ba sallama hakan bai
hana dayan tace a, a hjy Yabi ce yanzun muke maganan ko kun tashi muje mu
gaisheki ai.

   Hannu ta daga
alaman tayi mata shiru a lokacin kafin ta bisu da kallo daya bayan daya ta
sauke idonta akan hjy Murja din tana fadin murja meya kawoki gidana a wanan
lokacin?

   Hjy murjan ta dago
ta kalleta tayi dan murmushi kafin tace amma dai musulmai kika samu a dakin
akala kyayi sallama ko zamu san damu kike zancen a yanzu ?

    Murja watau har
kin dauka wuyan ki ya isa yanka a gidan don dan wanan asirin naki da ayanzu
kike ganin yana aiki akan Alh ke nan to barin fada maki kiji kuma ki rike idan
kina tafiya da rana tsaye ni yabi dare da ranan duk a tsaye nake indai akan
gidanane kece kika fara yanzu.

   Lalai kuma kinyi
sa,a malamin ki ya iya aiki harda ya iya karya dokana yasaka Alh ya dauko ki
daga kauye zuwa wanan gidan a yanzu saidai kinyi kuskure babba na yin hakan .

  Don in kishigone ta
gaba ta birkice zaki koma wata kilama wanan karon ba inda kika fito zaki koma
ba sai wani bakon waien.

   Kowa na dakin sai
binta sukeyi da kallon mamaki daga can inda yan matasan yan matan ke zaune da
sauri  dayan ta kunna waya tana daukan
komai dake faruwa a dakin lokacin saboda yarinta.

   Hjy yabi ke nan ban
kara tabbatar da cewa ke din jahila bace sai yau din nan da kike wanan ikirarin
haka a gaba saidai ki sani .

  Ni murja ba yar
matsafa band ba kuma jikansu bace a gidanmu musan Allah da Annabinsa tsagwaron
su haka kuma da shi na dogara a rayuwana don shine boka da malam din gidan mu
kinga tunda har Allah ya amsa min addua na akanki saina kara gode mashi.

   Karya kikeyi
munafukan Allah duk inda kike zuwa ai munsani don abin duniya ba boye yake a
kasan nan indai indai bera bai daina yawon dare ba wata rana su hade da mage
wurin yawon ai.

   Ta jiya a fusace ta
bar dakin cikin kunan rai tare da mamakin canzawan hjy murjan don bata taba
tsamanin irin haka ba gareta wanan abin ya bata mamaki matuka.

   Abin mamaki baya
karewa  sai ga hjy yabi din na fadawa Alh
wai yayiwa hjy murja iyaka da ita don ta nuna ba zaman lafiya tazo yiba a nan
don tana ganin kamar ka daure mata yanzu.

    Har tana nema taci
min a  mutunci a gaban yan uwanta har
tana fadin zataga iyakanta yanzu a gidan ke nan dama da wani manufa tazo nan ke
nan.

   Ya juyo ya bar
abinda yakeyi din gaban mirror dinshi yana fuskantar ta abinda ya dade bai faru
tsakaninsu ba ya dan murmusa yace.

  Cikin kada kai Yabi
kada ki manta da  cewa ni din nan ni na
aje kowan ku a gidan nan haka kuma nasan halin ko wacen ku.

  Don haka ke me
kikaje nema a part din ta don naga ni kaina na nemi kizo nan kika bata min
lokaci ki kaki zuwa don ki nuna mata koni ban isa dake a gidan nan.

    Don haka kina
tsanmanin yanzu zaki samu wani girma a wurin murjan ke nan a gabanta fa kika
nuna banda daraja ko kima har a idon yayan ki ?

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/15, 10:17 AM] +234 908 769 2191: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

 

Leave a Reply

Back to top button