Masarautar Qamar Hausa Novel
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
Bismillah Rahmani Raheem
By Khadija (KMU)
Page 1&2
Tafiya takeyi a hankali kanta a sama har ta isa inda take saida Awara hada kayan suyar ta tayi wanda daman an riga an kawo mata su tun kafin ta taho nan da nan ta fara soya awarar ta nan da nan ta fara ciniki as usual kafin kace kwabo ta saida awararta ta amshe kudin ta tass
Yara uku ta samu tace su daukar mata kayan awarar ta saida yaran sukayi gaba ta biyosu
A hankali take tafiya wadda kamar dagan gan take yinta dogayen kalaba ne guda hudu a kanta wanda suka zubo mata har gadon bayanta gashi nan nata bakir kirin earpieces ne a kunnenta tanajin wakar rush by ayra star daidai majalisar su tareeq tazo wucewa zayyad ne yace gafa demoness nan ja’afar ne yayi dariya yace to kaje ku gaisa yace ka rufamin asiri tareeq ne yace bullshit yace meyasa kuke maida kanku baya wai sai yayi shiru zayyad ne ya kwashe da dariya nasan mi kakeson kace miyasa muke tsoronta to ai naga kai baka tsoronta don Allah I dare you to go and confess your love to her right now dan iska inji zayyad shidai ja’afar dariya kawai yakeyi abinshi.
Tareeq cikin muguwar hasala ya nufi daidai inda take.
Hurriya jin wakarta takeyi hankali kwance da yar karamar wayarta Mai malatsi kallon tareeq tayi da idanunta masu kyau wanda duk bala’in ka baka iya minti daya cikinsu frowning face dinta tayi tana raising brow daya irin miye matsalar ka kasa kallonta yayi kallonshi tayi in a mocking way tace ka fara gadi ne ko kana bina bashi the girl is beautiful not just beautiful but extremely beautiful she’s got this flawless caramel skin that looks like miloo and creamy milk that are put together to give her this perfect and flawless skin idanunta are dark brown which made her look intimidating she’ thin and tall the girl is almost perfect with nothing left for people to criticize sai dai bata kama da Nigerian’s kwata kwata she’s more like an Ethiopian tareeq da banda kallonta ba abinda yakeyi don he can swear wannan yarinya sune hurul tin wato masu kyaun duniya Hurriya ta kalleshi tace hey i’d slap you but that will be animal abuse ta ida maganar da wani tone na raini get lost tace tareeq da daman kamar abinda yake jira kenan yayi sauri ya nufi wurin abokanashi da suna ta kallon drama tasu Hurriya saida tazo ta saitin su ta kallesu tace bunch of idiots sannan ta wuce tayi hanyar gidansu dukansu bayanta suka bi da kallo wanda gashin kanta kawai ke lilo
Da yar sallamarta ta shiga gidan da take zama, tabawa bata amsa ba itama Hurriya ko a jikinta ta kusa shiga dakinta kenan taji tabawa nacewa shigar mutum kadai ta isa kasan kowaye mutum a hankali tayi maganar yadda bata tsamanin Hurriya taji abinda tace saidai fa Hurriya Allah ya horeta da ji don kamar giza gizo haka take dawowa Hurriya tayi saida taje saitin tabawa ta zuba mata idanun ta masu masifar kyau saidai ba maisan kallon su saboda abinda suke fiddawa wato flame ta kalli tabawa tace gwara ni nawa a bayyane yake naga taki diyar kuma kullum cikin hijab take Amman sana’ar ta wato saida jiki from this man to another ta amso maku kudi kullum ita ake kallo a matsayin ta kirki nice ta banza Tace and i don’t give a damn because people always think about what they see and believe what they want to believe so I’m at your service shegu masu kan kwarya tana gama maganar ta shige dakinta tabawa da ta hangame baki bude duk inda sabo ma ta saba Amman Abun Hurriya kullum kara karuwa yake
Hurriya kam risho ta fiddo ta kunna ta dora ruwa ya mutu ta juye abokiti ta shiga ban dakin su tayi wanka tayi alwala wata hijab ta nemo sannan tayi sallah duk da cewar sallahr bata wani iya ba Sosai ba Amman tana kokar tawa sosai hijab din ta ajiye sannan ta ciro kudin awarar da tayi ta fidda kudin siyyarta sauran kuma na adashe ne da takeyi abinta. Yunwa ta dan dameta don haka ta zari dari biyu ta fito jeans ne a jikinta sai wata yar karamar riga maroon ta fito duk inda ta gifta kallonta ake but she don’t give a damn saida tayi tafiya mai dan nisa sannan taje wani shago ta siyi indomie guda daya ta juya ta koma gida dan risho dinta ta kunna ta dafa indomie din tana gama ci ta kwanta sai bacci domin ta gaji bata samu asuba ba don sai karfe shidda ta samu ta tashi daga baccin tsakar gidansu ta fito ta shiga tayi alwala sannan tayi sallah.
Wani blue din wando ne jikinta sai t-shirt Mai zanan zaki fuskar ta fayau sai dogon gashinta da ta nade sosai gidan mai-anguwar su taje hade da sallamarta a tsakar gida iske matar gidan wadda Kamar ita take jira wanke wanke aka fiddo mata ta zauna tayi abinta bayan tagama tayi shara da sauran ayyyukan gidan.
Kallonta laminde tayi wadda tagama dafa shayi zata kaima Mai unguwa tace Hurriya angama ne daga mata kai Hurriya tayi wadda ta samu kujera ta zauna tana jin wakarta ,ta saba indai Hurriya ce duk yadda kaso kayi fira da ita bata baka dama abinda ya kawota shi kawai zatayi ta kama gabanta
Laminde bayan ta kaima mai unguwa karin kumallo ta zuba ta mika ma Hurriya itama shayi da bredi amsa tayi ta cinye ba tare tace ta gode ba tana kallon Hurriya tagane nufinta don haka ta miko mata dari biyu kudin aikinta sannan ta kama hanya ta tafi gida saman katifar ta haye ta danyi bacci bayan ta tashi daga bacci ta wanke fuskarta sannan ta fita ta bada kudin adashen ta wanda take zubi kullum
Tana fitowa daga gidan adashen ta nufi yar karamar kasuwar da take siyen waken suya da murmushi Saminu ya tarbi Hurriya ya gaisheta as usual don duk idan zata zo wurin shi bata taba gaishe shi ba sai ya kasance yana gaisheta da kanshi saboda ko zata kula ta gyara Amman ina idan ya gaisheta zata daga kafada ne taki amsawa yasan batasan dogon bayani tafison duk abinda tazo ayi mata shi lokacin da takeso don haka yace Hurriya bani da wake yau amman ga ashiru can ki siya a wurin shi daga kai Hurriya tayi ta nufi ashiru dake awo kallonshi tayi da idanunta tace a bani wake kallonta yayi sama da kasa sannan yace kindai san kudin waken Hurriya batace mashi komai ba har ya fara zuba waken cewa tayi batasan shi ta nuna mai kyau tace ya zuba mata ashiru kam ya bata fuska yayi banza da ita ya cigaba da zuba wake Hurriya batace mashi kala ba ya miko mata waken bude ledar tayi kamar tana dubawa ashiru yace malama ki bani kudina kina wani leka abu kamar An cuce ki bani san shegantaka idan bakiso ki bani kayana Hurriya batace kala ba daukar ledar waken tayi ta juye mashi abinshi sannan ta sanya tiya ta auni mai kyau ta juye a ledar ta ajiye mashi kudin shi ashiru da mamakin ta ya kamashi daman waye baisan shi a kauyen ba saboda fitinar shi masifarfe ne na bala’i kuma tijarare don haka saitin da Hurriya take tafiya ya tsaya yace yau rashin tarbiya da rashin da’ar kaina tazo karuwa to baki isa ba don wallahi yau sai na cin mutunci ki don ba’a haifi wani a garinan da Zaici man mutunci In kyaleshi ba daga hannu yayi da niyyar marinta Hurriya bata matsa ba kuma batace kala ba saidai flames din idanunta da suke fita a idonta bama gaskiya bane don wani mugun kallo tayi mashi wanda ya sanya dole saida ya aje hannunshi kasa sannan tace I dare you to slap me tayi wani tauna lebenta sannan tace sakarai waye duk garinan bai sanka ba da molesting yaran mutane ba kowa yana tsoron ka saboda rashin mutunci ka and you’re here calling me a whore ko cikin ni dakai waye babban dan iska ta nuna kanta tace ni ko kai sannan tace to idani karuwa ce dakai nayi karuwancin ko kuma da tsoho shiru ashiru yayi sannan ta kara zuba mashi wannan idanun nata tace daga yau na karajin kayi abinda bashi bane sai na kira ma hukuma sun tafi dakai sun bama karensu ya cinye ta ida maganar tana mashi kallon cewar Ina maka gargadi tace sakarai Dan Akuya sannan tayi gaba abinta tabar ashiru da sakin baki da kowa na layin mamakinta yake saboda abinda bai taba faruwa ne ya faru shikanshi ashiru kasa matsawa yayi daga inda yake lallai hausawa sunyi gaskiya yaro baisan wuta ba sai ya taka.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 2&3
Hurriya tana soya awarar ta mutane nata siye maza a gefenta suna zaune a benci wasu ta zuba masu a plate wasu kuma a leda Ashiru ne yazo inda take saida awarar ya fara surfa ruwan Bala’ da masifa yace yau sai ya kona mata fuskar da take takama da ita cikin garin Hurriya batace mashi cikanka na shikuma ashiru karshen kulewa ya kulu
Hurriya mutumin ya cika mata kai da hayaniya yana neman daga mata hankali mazan wurin kowa kallonshi yake da mamaki saboda idan shi ashiru tijara ne to ita demoness ce without any emotion Hurriya da taga abin nashi yaki ya kare ta mike tsaye ludayi ta dauka ta debo mai mai shegen zafi ta watsa mai akafar damar shi sannan ta kalleshi tace kalma daya na karaji daga bakin ka to sai na juye maka man awarar nan duka a munmmunar fuskar ka wawa dakai
Ashiru da azaba ta isheshi ihu ya saki yana kallon rashin tsoro a idonta kuma ya tabbatar da cewar zatayi mashi abinda yafi hakan matasan mazan dake wurin dariya kawai suke suna ihu ashiru kam daya rasa mi zaiyi sai ya juya yana dangeshi har ya samu ya bar wurin da take saida awarar Hurriya kam hidimarta ta cigaba don duk ihun da yan maza ke mata bata kalli kowa acikin su ba har ta gama ta amshe kudinta tass
Hada kayan da ta soya awararta tayi sannan ta samu yara tace suzo su daukar mata tare suka jera kunnenta da earpiece as usual wakarta takeji ta overloading don yadda take bin wakar kamar ita ta rairata har suka zo kofar gida kallon yaran da suka kawo mata tayi sannan ta zaro goma goma ta basu aiko nan da nan sukai ta tsalle suna ihun murna Hurriya ta shiga gida da yar sallamar ta .
Tabawa ko kallon inda take batayi bare ta amsa mata itadai Hurriya d’âge kafada tayi saboda tana kwasar adashenta Zata canza gida mai dan dama dama ta siye yar babbar wayarta da dan kayan abinci sai kayan sawar ta don Hurriya Allah yayi mata son sutura saidai bata da halin sanya expensive kayan Amman dai tana kokar tawa.
Tana shiga dakinta ta cire dan wandon da ta sanya ta sanya bomshort sannan ta fito tayi wanka tayi alwala ta shirye cikin wata yar rigar ta half gown ta kabbara sallah da sauri ta gama
Cire hijab din tayi ta fito ba karamin kyau tayi ba cikin jar rigar wanda duka dogayen kafafunta a bude suke banda salki babu abinda sukeyi Hurriya yau batajin dora tukunya don haka taje wurin iliya Mai shayi tace ya soya mata kwai guda daya sai ya bata ruwan lipton da biredi mazan dake zaune a wurin dukan su hankalin su na kanta Amman ba wanda ya isa ya tunkareta.
Ilya ya bata abinta ta amsa ta kama gaban ta
Shidai iliya maganar gaskiya yarinyar na burgeshi don duk garin nan bata daukar raini don ga kyau na fitar hankali gashi ba wanda ya isa ya tunkare ta ga Kuma sai shigar da ta ga dama Amman dai ba wanda ke binta da maganar banza don mafi yawan yan garin nan kusan duk sun bada kansu kuma kullum zaka gansu cikin shigar mutunci amman banda ita shigar banza ce irinta turawa wadda tsantsar turawa keyi
Hurriya ta gyara zama sannan ta cinye duk abinda ta siyo tasha ruwa ta wanke hannunta ta dan kishingida kanta saman katifa kafin ta samu a kira sallahr isha’i ta dade tanajin wakar don har isha’i ta gifta bata sani ba saida taji bacci yadan fara figarta sannan ta tashi tayi alwala tazo ta kabarta sallah
Kwanciya tayi a hankali bacci ya dauketa.
Yau dai ta tashi sallahr asuba tana dadewa bata tashi ba Daidai lokacin asuba don mafi yawan lokuta sai safiya take sallah to yau ta tashi Daidai asubar don har raka’atanul fijr tayi duk da batasan cewar sallahr ta micece ba Amman tasan anayita kafin sallar asuba tana gamawa ta linke hijab ta koma baccin ta
Karfe takwas na safe Hurriya taje gidan mai unguwa as usual matar Mai unguwa ta fito mata da kayan wanke wanke sannan tayi shara da sauran ayyuka ta biya ta da kudin aikinta karin kumallon yau a leda tace ta juye matashi idan taje gida sai taci.
Hurriya ta zauna tana maida numfashi bayan ta huta kadan ta dauki kwano ta juye taliyar da take da zafi saida ta fita ta daurayo hannun ta sannan ta dawo ta fara ci bintu ce ta shigo dakin Hurriya tana kuka ta kwanta saman katifar Hurriya cin abincin ta cigaba dayi bata tanka ba har saida ta koshi taje ta wanke hannunta,batace ma bintu kala ba don earpieces ta sanya tanajin wakarta
Bintu da tagama kukan ta tabbatar ya isheta sannan tayi ma Hurriya magana Hurriya da taga alamun tagama kukan ya sanya ta cire earpiece din ta kalleta Bintu tace Hurriya idan ba zuwa nayi wurin ki ba baki taba zuwa wurin da nike
Hurriya tayi shiru bata ce komai ba Bintu tasan daman ba zatace komai din ba murmushi bintu tayi don duk garin nan tafi kowa sanin halin Hurriya tasan cewar Hurriya din tayi kewarta kwana biyu da bata ganta ba Amman tasan cewar baza ta taba tambayar lafiya ba saidai idan Bintu ta fada mata don haka bintu ta rike mata hannu tare da sakin murmushi a hankali Hurriya ta zare mata hannunta ta kalleta irin kallon kinsan banason ana tabani bintu ta turo baki tace kiyi hakuri
Bintu ta kalleta tace nidai bazaki kara ganina ba tunda bazaki tambayeni lafiya ba Hurriya ta kalleta sannan tayi shrugging kafadar ta tana kokarin mikewa Bintu da tasan hali tace zauna nagaya maki a hankali Hurriya ta zauna bintu ta kalleta tace lalu ya dawo shekaranjiya da daddare na fito zanzo wurin ki na hadu dashi a zaure a buge yana ganina ya taho yana kokarin rike mani kugu sai na kauce shikuma da yaga haka sai ya chakumo ni daganan muka fara kokowa dashi bugu kadan nayi mashi shine ya fadi kasa nikuma da naga haka na ruga cikin gida na kwanta
Shine fa yau sai ta fashe da kuka Hurriya dai tanajin ta don ita bata iya lallashi ba ko kadan saida ta gama kukan sannan ta cigaba da bata labari shine yau larai da lalu suka hau ni da duka wai sai sun kasheni suna ta dukana shine na rugo na taho wurin ki
Hurriya bazaka iya gane miye a fuskar ta ba fuskar nan blank koda yake ita duk bala’e baka iya reading emotions dinta don fuskar nan kullum a hade take
Muryar ta mai dadi don ba fluent hausa take ba saboda mixed din yaren Ethiopia da English da take dashi ta kalli Bintu tace kinajin yunwa Bintu ta daga mata kai taliyar da ta rage saura ta bata Bintu ta amsa da godiya Hurriya tana kallon yadda take cin taliyar tamkar wadda bata tabacin abinci ba.
Bintu bayan tagama cin abincin ta kalli Hurriya da kitson kanta ya Dan fara tsufa tace In kwance maki kitson nan girgiza mata kai tayi alamar Aa Bintu turo baki tayi tace kai Hurriya shiru tayi ba tare da ta tanka ta sannan ta dauki tsinke ta fara kwance kalabar
Murmushi Bintu tayi don tasan halin Hurriya na rashin son wani ya taba mata ko yatsa
Fira suka fara har ta gama kwancewa ta sharce kan Bintu tace Hurriya kinada gashi damani Hurriya ta yamutsa fuska sannan tace inaso in rage gashin yana damuna Bintu tayi dariya tace don’t even start don ba kyau shrugging Hurriya tayi sannan tace I don’t bloody care Bintu da tasan halinta sai tayi shiru tabar maganar.
Tare sukaje kasuwa inda ta saba siyen waken Awara da murmushi mutumin ya tarbesu Bintu itama maida mashi murmushin tayi Hurriya kam ba wani murmushi bare gaisuwa don Bintu sai washe baki take suna gaisawa dagan gan yace kinga murmushi ma sunnah ne a musulunci dariya tayi Mahnoor da tariga tasan da ita yake kwata kwata bata damu ba.
Hurriya jam da tagaji da surutunshi cikin zakin muryarta da accent dinta mai dadi tace mashi ya sanya mata waken idan kuma ya cigaba da surutu zata canja wurin siye saboda ita ba magana ya kawota ba she’s here for a business tana kallon tsakiyar idonshi tayi maganar murmushi yayi sannan ya zuba mata waken ta amsa ta kama gabanta.
Ashiru kam tunda yazo yake kallonta yana zaginta a ranshi yayi alkawarin bazai taba yafe mataba don lokaci kawai yake jira ya dauki fansar shi
Hurriya yau tare suka soya awara itada Bintu banda murmushi ba abinda Bintu takeyi don duk wanda yace abashi awara sai tayi mashi murmushi Hurriya kam ita take soyawa suna gama soyawa suka tattara komai suka tafi gida.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU )
Page 5&6
lokacin da suka dawo anata kiraye kirayen sallah magriba Don Hurriya zaiyi wuya takai bayan magrib a wurin suyar Awara Bintu tayi alwala sannan ta shigo dakin kallon Hurriya dake kwance saman katifar tana jin waka tayi idonta a lumshe suke Bintu ta kalleta tana admiring irin kyaun da Allah yayi mata long lashes dinta da suke kwance kamar tayi fixing dinsu dogon hancin ta sai kuma cynical mouth dinta banda glowing ba abinda fuskar ta take because of her smooth and flawless skin a hankali ta kalli shafefen cikinta wanda kamar bata sanya mashi komai Hurriya is extraordinary beauty duk wanda ya kalleta yasan tana da kyau kuma har ka gama rayuwarka da ita baza ka lura da wani muni nata ba saboda kana kallonta a kullum tana kara maka kyau irinsu ne wanda ake gasar kyau dasu kuma tayi imani da cewar idan daHurriya zata fito gasar kyau ba abinda zai hanata cin wannan gasar irinsu ne za’a iya biyansu ko nawane don su kasance manya manya models irin nasu france da america Everything about her is screaming perfection with nothing left to criticize
Sallah Bintu ta kabbara har tagama sallah Hurriya bata matsa konan da can ba Bayan Bintu ta gama addu’a ta kalli Hurriya tace Hurriya ki tashi kiyi sallah lokaci na tafiya Hurriya kam da batajin Mai take cewa don ta kure volume a burin yar garuwarta Bintu kara mata magana tayi shiru tayi Bintu da taga kamar batajin mi take cewa sai ta sanya hannu ta taba ta Aiko kamar an tsunkuli Hurriya din da a firgice ta tashi tana Bintu wani irin mugun kallo ta Hurriya kallon take sosai Bintu kam da tasan yadda Hurriya ta tsani wani ya tabata don tanada tabbacin idan wani ne ya tabata ba ita ba to saukar mari ne kawai zaiji Hurriya tace Bintu don’t ever repeat this mistake again Bintu tace ki tashi kiyi sallah lokaci na wucewa Hurriya ta daga mata kai sannan taje tayi alwala da sauri tayi sallah don Bintu kallon yadda take sallah kawai sannan girgiza ta kai kawai
Hurriya ta kalli Bintu sannan tace kina jin yunwa Bintu tace inajin yunwa Hurriya
Hurriya daure gashinta tayi saboda wanda tayi taji yana damunta so take tasamu lokaci ta rage gashin don ya kara taruwa da yawa gashi bata san takura tana gama gyaran gashin ta kalli Bintu tace bari na samo manah gari can shagon Bintu tace zan rakaki
Tare suka jero suna tafiya su biyu duk inda ta gifta kallonsu ake ba Kamar Hurriya don crop top ce jikinta pink sai wani bakin wando gashin kanta ta da yake a bude sai sheki yake har suka zo shagon da ake saide saide
Da murmushi a fuskar shi yace Hurriya mi za’a baku gari tace ya sanya masu na dari sai sugar na hamsin gyadar hamsin Hamza da murmushi yace su Hurriya gari za’a sha wani kallo Hurriya tayi mashi ai sai ya fara to to sannan ya miko garin da suga da gyada Bintu ta amsa sannan tace mun gode Hurriya dai banza tayi dasu dukan su.
Suna shigowa suka ga talatu a zaure itada tasi’u hannunshi sanye cikin rigarta tana ta dariya kasa kasa kwata kwata basu lura dasu Hurriya ba da suka shigo don Bintu ba karamin tsorota tayi ba don sauran kadan ta fadi Hurriya kallo daya tayi masu ta dauke kanta tayi gaba har ta sanya kanta taji maganar su kasa kasa tasi’u yace ya za’ayi da yarinyar can ne ni wallahi duk unguwar nan ba wanda yake burgeni Kamar ta yarinya shigar banza kuma Kamar tsohuwar baturiya Amman ace duk unguwar nan gani nan bari ina da burin in lasa wannan yarinya nima tasi’u yace ma talatu dariya tayi sannan tace Hurriya ai karuwa ce ta karshe kawai dai ta iya allonta
Ganin Hurriya da tayi a tsaye saida gabanta ya fadi wani irin mugun kallo take mata fuskar nan kwata kwata babu emotion tana a yadda take kamar kullum tasi’u ta kalla cikin ido hannun tasi’u dake cikin rigar talatu ta kalla sannan cikin muryarta mai dadi ta kalleshi sannan tace nima ka sanya hannunka cikin rigata tana kallon tsakiyar idanunshi tsotsar bakinta tayi kadan tace ka sanya hannuka cikin rigata mana
Shiru tasi’u yayi yama kasa kallonta duk ya daburce don wani irin kwarjini da tayi mashi kilan saboda kyaunta take da irin wannan kwarjini frowning face dinta tayi in a mocking way tace kai dan akuya ne? Are you mad kallon shi tayi sannan tace kaje ka kalli kanka a madubi sannan tazo saitin talatu kallon cikin idanunta tayi sannan tace miye ma’anar karuwanci shiru tayi talatu tace ina tambayar ki shiru tayi
Hurriya tace sana’ar kice keda tabawa and please stop sleeping with young boys masu empty pockets idan zaki kwanta da namiji gwara ki nemi baban tasi’u yadda idan yagama zai baki koda dari biyu ce wadda zaki iya cin tsire wawaye makwadaita.
Earpiece dinta ta maida tayi cikin gida abinta kamar batayi komai ba she hate nonsense mutanen yanzu you’v to stand and for yourself ita batama ga dalilin da zaisa mutum ya zageta tayi shiru ba she doesn’t care ko waye kai zata kalli tsabar idonka tayi maka daidai abinda kayi mata Amman dai ba ruwan ta da kowa kawai miskila ce ta karshe and don’t talk behind her back saboda Allah ya bata wani irin ji sosai kilan shine baiwarta Don tana iyajin magana daga nesa Sosai wadda nisanta ya wuce tunani Amman cikin ikon Allah zataji lokacin da bata ma iya hausar ba Sosai don ko magana taso ta fada ma mutum marar dadi to ba lallai yaji mi take cewa ba saboda she’s using British and Amacharic Amman yanzu idan ta yanko maka magana kamar daman asalin yaren hausan takeji don duk kalmomi mararsa dadi ta iya amfani dasu.
Bintu kam har ta jika masu garin tanata jiran Hurriya din tazo domin susha suyi sallah su kwanta Bintu ta kalli Hurriya tace ina kika tsaya ahankali tace waje tasan bata cika san magana ba don ta tsani unnecessary zance don haka Bintu taja Bakinta tayi shiru
Tare suka sha garin don ita Hurriya a hankali take sha don har tagama shanye nata Hurriya bata shanye ba tanajin waka tana kada kanta Bintu murmushi tayi sannan ta fita ta wanke kofin tayo alwala sannan ta kabbara isha’i tana gama sallah tana lazimi saiga sallama
Hurriya idonta lumshe Amman duk abinda Bintu suke cewa tanajin su Bintu ta kalli Hurriya tace Hurriya na tafi baba ya dawo yace a kirani tana goge dan hawayen da ya zubo mata Hurriya tayi shiru kamar bataji mai Bintu take cewa ba sannan Bintu ta fita tana dan gyara ma Hurriya labule.
Bintu na isowa kofar gida gabanta ya fadi don batasan mi zata tarar ba a gidan a hankali tasa kanta a soron Gidan tana tafiya kamar munafuka lalu da suka shirya abunsu da larai daman yasan dole zata dawo gida shiyasa ya tsaya zaure ya tarbeta saboda ya lalubi rabonshi
Daidai inda take yazo yana wani munafukin dariya yace wa naka ma matsowa ya farayi tana matsawa baya yana Dariyar har saida ya kawota karshen bango riketa yayi gam yana dariya yellowing hakoranshi suna bayyana kugunta yarike yana kokarin sanya mata hannu cikin riga tureshi tayi yayi baya ya kalleta sannan yace ni zaki ture to yau Mai rabani dake sai Allah kugunta ya rike aiko suka fara kokowa karfinta ne ya fara karewa sosai
Hurriya da take kallon ikon Allah zuwa tayi daidai inda yake ta dauke lalu da mari a harzuqe ya dago da niyyar sauke ma kowaye ya mareshi ruwan tijara saidai da kyar ya iya hadiya maganar shi da kuma yawun dake bakinshi kallonta yakeyi da yar crop top din da ko cibi bata rufe mata ba sai bakin wandon dake jikinta gashin kanta kam ba’a daure ba tunda lalu yake bai taba ganin halitta mai kyan mahnoor ba saidai kyawawan idanunta da Allah ya basu matukar kwarjini Hurriya ta janye bintu daga wurin lalu tana mashi wani irin banza kallo da kyawawan idanunta cikin muryarta mai dadi da tace duk randa na karajin wani Abu makamancin haka ya faru sai kaji a jikin ka sakarai mai karamar kwakwalwa
Bintu kallon Hurriya tayi sannan tace nagode Hurriya kam baka iya karantar yanayinta don ta kwarai wurin shutting emotions dinta
Tare suka shiga inda suka tarar abbanta na kwasar tuwo larai na kusa dashi Larai na lura da shigowar su ta saki wani munafukin murmushi Abbanta da ya kula dasu aiko zumbur ya taso da hannunshi duk miya zai mari Hurriya cikin sauri ta rike hannunshi tana rikewa ta saki don kamar ta rike kashi tana kallonshi Abba da ya harzuka yace daman kina wurin wannan shedaniyar marar tarbiya marar addini.
Hurriya a kalleshi sannan tace babban shedani ya wuce bayanka wanda har zai tsallake kafa ya tafi gantali ba tare da tunanin halin da diyarshi zata fada ba a hannun kishiyar uwa bakasan mi taci ba bakasan mi tasha ba baka san wazai lalat maka diya ba kallon Larai da tabata fuska tana kallonta tayi sannan tace koda yake ba abin mamaki bane tunda duka jikin ka daure yake da asiri.
Rashin addinina da Rashin tarbiyata duka dauka nayi a wurin wanda baisan hakkin diyarshi ba ido cikin ido tace sakarai wawa mijin tace Bintu da take kallon komai tasan a haka Hurriya na ganin mutuncinta tasan idan tayi wani abun ba zataji dadi ba.
Hurriya ta kalli Bintu sannan tace ai baki jin yunwa ko Bintu ta daga mata kai tace muje dakinki Hurriya na gaba Bintu na baya har suka zo dakin kallonta tayi mata da ido ta shiga kuka take shirin yi Hurriya ta nuna mata alama da tai shiru.
Abba da Larai kam sunsan halin shegiyar Hurriya ldinan da ta zame masu karfen kafa a cikin garin nan don bata da mutunci
Hurriya tazo ta kallesu sannan tace idan har naji ko harar Bintu kunyi to zan kira maku hukuma ta kada kai ta bar gidan lalu da yake boye yana kallon su duka ya fito yana kallon Larai yace wacece wannan Larai ta kalleshi tace fitacciyar marar kunya kenan don haka duk abinda tace to ba mamaki zata iya aikata shi.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 7&8
Gida Hurriya ta koma tana shiga ta kwanta a katifar tana tunani bata gama tunanin ba bacci ya dauketa sai karfe bakwai ta tashi ruwa ta dan kashe sannan ta juyeshi cikin bucket tayi wanka kanta ta fara wankewa sannan wanka tayi alwala saida ta sanya gashin kanta saitin fan ya bushe tukunna scissors ta duba inda take ajewa bata gani ba dubawa tayi sosai bata gani ba tsoki tayi ta gyara gashinta ta daureshi kawai don taso ta yankeshi saboda gashin ya fara yi mata yawa wani dan karamin box ta fiddo can cikin kayanta ahankali ta bude tana kallon sarkoki guda biyu masu masifar kyau Rufe box din tayi ta maida sannan ta fiddo wani jeans blue ne sosai Amman yanada dan fadi kasan shi sai tsagar dake a cinyoyin wandon da gwiwar wandon shiryawa tayi cikin wando ta sanya bakar riga yau kawai taji tanason ta sanya dan kwali don haka ta zaro wani blue and black vintage scarf ta daura ma kanta saida tagama shiryawa tsaff sannan ta dan murza dan oil turaren ta mai saukin kudi
Saida tagama komai sannan ta kabbara sallahr asuba don har takwas da mintuna tayi da sauri tagama komai ta nufi gidan mai anguwa .
Tadan makara yau wurin aiki tana shiga laminde tace kina raina Hurriya yanzu nike da niyyar daman In sanya a Duba ki ko lafiya Hurriya ta share tambayar da tayi mata tace ina kayan murmushi laminde tayi ta fiddo mata kayan yau cikin sauri take komai saboda yau zata kwashi adashenta kuma tanaso ta siye kaya saida ta tabbatar tagama komai don ko laminde ko Bankwana batayi ma laminde ba ta fito
Hurriya kam saida taje gida ta fiddo asusunta har ta maida wurin maida asusun ne wani dan box 📦 ya fado a hankali ta bude tana kallon sarkoki guda biyu da banda kyalkyali ba abinda sukeyi maidawa take kokarinyi kawai sai a ranta tace bari ta sanya it’s been a long time a hankali ta warware sarka guda daya wadda plain ce kawai Amman gold ne a sarkar ta sanya Kallon dayar sarkar take wadda kamar diamond ce Amman stone din anyi mashi carve da H Maidawa tayi a box din sannan ta sanya shi a aljihun wandonta Emotions din da taji ya fara taso mata ne ya sanya kawai ta cire kudin asusun wanda suka kama dubu takwas ta tafi gidan Asabe wadda ta kasance uwar zubin adashen Hurriya ba sallama ta shiga gidan a tsakar gida ta iske asabe tana shan rake
Asabe saidai ganin mutum tayi a kanta don ta tsoro ta matuka Hurriya ta kalla daga sama har kasa tace Nagode ma Allah kece cikin gidanan namu da ace bake bace da sai anjimu dake yau Hurriya kallon Asabe tayi fuskar ta babu alamun murmushi ko daya tace nazo kwashe kudina
Dariya Asabe tayi sannan tace oh kece fa kwasar karshe kusan kowa yasan halinki shiyasa duk angama maki zubin adashen ki tun kafin ma kizo ta ida maganar da dariya hurriya batace mata kala ba saidai ta jawo kujerar dake kusa da Asabe ta zauna
Asabe tace kinga bari na dauko maki kudin ki labule asabe ta daga ta shiga daki sai gata tafito da yar lalitar tsaff ta kirga ma Hurriya dubu sha biyar da dari takwas tace ga kudin ki kece daman zaki ida zubin yau shine zai kama dubu sha shida kenan Hurriya amsar kudinta tayi daman hannu biyu tayi zubin na wata biyu kenan kuma itace kwasar karshe ta hada da dubu takwas din da ta fiddo daga asusun ta wanda suka kama dubu ashirin da uku
Amsar abunta tayi ba tare da tace ta gode ba asabe har zata wuce asabe tace yawwa Hurriya ga fa irin kayan da kike sawa gwanjo ki duba Hurriya alama tayi mata da ta miko cike da murna asabe ta shiga daki don tasan indai Hurriya ce sai ta siye kayan kusan dubu biyar indai tanason Abu zata siya gashi ita bata taya kaya duk yanda aka batasu saye takeyi
Kulli guda asabe ta fitoda kayan tana nuna ma Hurriya murmushi tayi tare da bude kayan tace kalla Hurriya kallon da Hurriya take ma kayan kawai zai tabbatar maka da cewar sun burgeta a hankali ta fara zabar kayan masu kyau har kusan kala goma sai hula kala uku Asabe ce ta kalleta sannan tace Hurriya gafa wata jalabiya zatayi maki kyau ki hada da ita Hurriya kallon jalabiyar tayi sannan tace ta sanya mata da murmushi asabe ta sanya hada wani dan kwali Mai silbi sai hijab Mahnoor kallonta tayi sannan tace nawa ne duka kudin kayan Asabe ta gyara tsayuwa sannan tace dubu shida Hurriya ba tare da bata lokaci ba ta kirgo dubu shida ta bama asabe
Asabe kam dadi kamar ya kasheta daman tasan Hurriya bata da bakin ciki indai tanason Abu zata siya à yadda ka batashi leda ta dauko ta kwashe ma Hurriya kayan sai zuba kam godiya take da addu’a Hurriya bata bi takanta ba ta fito daga gidan ta nufi gidan mai unguwa cikin aljihun wandonta ta sanya kudin tabo aljihun tayi kawai sai taji dan karamin box dinta tsoki tayi ta maida kudin a dayan aljihunta
Da isowar ta kofar gidan mai unguwa taga kofar gidan cike da motoci fararen bus ne na hias masu kyau ga yara da iyayen yara shake a wurin
A hankali Hurriya ta kutsa kai gidan mai anguwa samudawan dogarai ta gani sai mazurai suke da idanu frowning face dinta tayi ganin su da wasu uniform ga kuma rawani daure a kansu hango laminde da Hurriya tayi ne ya sanyata kutsa kai har inda take ganin ta , Duka wurin kallonta suke ba tare da ko kyaftawa laminde kam kallonta take tana mata alama da ta fita Amman Hurriya ba tare da ta kula kallon da ake mata ba ta iso har inda take fuskar ta sai fidda wani irin kyau take Amman kwata kwata babu murmushi ko sauki a fuskar ta laminde ta kalla sannan tace namanta ban amshi kudin aikina ba laminde tace oh oh bari na dauko maki
Mai unguwa kallon Hurriya yayi cike da tausayinta saboda ya tabbata baza ta koma gida ba yau don kallon da dogarawan kadai ke mata ya isa ya baka amsa laminde ta fito da Dari biyu ta bata tana kallon ledar hannunta da kuma wuyanta gaban laminde ne ya fadi ganin sarkar gold din da ta fito baro baro a wuyanta tasan zalincin dake masarautar Qamar don haka a hankali tazo saitin Hurriya gabanta na faduwa saboda kada wani ya lura da abinda zatayi itadai Allah ya Sani tana kaunar Hurriya har cikin ranta duk da ita bata nuna wata alamar girmamawa amman a haka take kaunarta a hankali tazo ta gyara mata wuyan riga tare da zurma sarkar cikin riga Hurriya kam wani irin kallo take mata murmushi laminde tayi sannan tace kada ki yadda wadanan dogarawan suga sarkar dake awuyan ki a hankali tayi mata magana yadda ko mai unguwa da yake nesa dasu bazai iya ji ba ki kula da kanki
Hurriya .
Hurriya a daga kai tayi tana rike da ledar kayan ta ta doshi hanyar fita wata tsawa aka daka mata Daidai ta kai kofar akace ke yar matsiyaciya ina zaki
Hurriya cigaba tayi da tafiyar ta wata tsawa ce aka kara daka mata ke kaskantarciyar karuwa ina zaki Hurriya bata taka ba kuma bata juya ba tsaye tayi tana jiran isowar ko waye da yake mata tsawa har haka don tun lokacin da ya fara tasan da ita yake
Salati laminde takeyi ta kalli mai unguwa dake gefe sannan tace ka taimakeni ka rufama yarinya asiri kasan halin Hurriya Daidai take da duk wanda ya kwana ya tashi kasan masarautar Qamar basu da imani mai unguwa shiru yayi
Kowa ma shiru yayi yana kallon ikon Allah Hurriya da take tsaye fuskar ta blank baka iya cewa ga yanayin ta Kumurci yazo saitin ta sannan ya daka mata tsawa wadda saida ta girgiza kusan kowa a wurin Amman Hurriya ko gezau duk da saida yan hanjin cikinta saida suka kada Amman tayi kokarin gyara tsayuwarta tana frowning fuskar ta Mai fidda zallan kyau tana kallon cikin idanun kumurci
Kumurci kallonta yake da mamaki sannan cikin daga murya yace kaskantaciya yar gidan matsiyata wadda tarbiya gabaki daya bata wadata iyayenki ba har suka baki ba yana magana cikin hargagi da wulakanci yana kallon ko ina na jikinta
Hurriya tace Are you mad kana hauka ne cikin zazzakar muryata mai dadi da dadin sauraro saboda yanayin maganarta hankalin kowa ya dauku ya dawo kanta tarbiya bata wadata iyayena ba kai kuma jahilci ya wadata naka iyayen tunda gashi kana juya abinda suka koya maka cikin doddar kwakwar ka Animal Asshole
Kumurci banda radadi ba abinda zuciyar shi takeyi don ba’a taba maida mashi martani irin yau ba kuma cinkin mutane daga hannunshi yayi zuciyar shi banda tafarfasa ba abinda takeyi zai sauke a fuskar shi Hurriya ganin marinta zaiyi da sauri ta cire dankwalin da tadaura yau cikin sa’a ta sanya dankwalin ta rike hannunshi tana rikewa tayi sauri ta saki kamar ta kama kashi kowa kallonsu yake itama tana kallon cikin idonshi tace Kana hauka ne ?sai tadan tsotsi bakinta kadan
Kumurci kam kallonta yake har baya kyaftawa tunda yake baitaba ganin mace mai kyaun ta ba don lokacin da take mashi magana ya kura mata ido har gold din dake ratsin hakoranta biyu saida ya gani saboda irin kallon da yake mata Hurriya kam lura da hakan yasa tayi shiru tana kallon tsakiyar idanun shi Kumurci kallon dogon sumar gashinta yake don baitaba ganin wani da irin gashinta ba ko subira da take take takama da kyau da gashi Hurriya ta fito don nata cike yake ga tsawo ga yawa wannan yarinyar dole ya tafi da ita masarautar Qamar Hurriya daukar ledarta tayi tace wawa dan akuya sannan ta kama hanyar kofa
Kumurci kam daya saki baki yana kallon ta Sauran dogarawan kam kallom Kumurci sukeyi don ya kasance Azzalumi kuma marar Imani Amman yau wata yar matsiyaciya yar talaka kuma karawu zata zauna ta Gaya mashi magana
Laminde kam tsoro da fargaba ya cika mata ido tanason Hurriya bata kaunar wani abu ya sami yarinyar dama bata zo ba saboda ta sani sarai bazasu barta lafiya ba.
Kattin dogarawan dake tsaye gefenta ne suka tare mata hanya a hankali ta dan ja baya jin saukar wata azababbar dorina ya sanya ta juyowa wasu ta gani guda biyu dukan ta suka farayi ba ji ba gani da wani irin rashin imani suke dukan ta laminde kam kuka take don duk bulala daya idan akayi mata sai ji takeyi kamar ita ake duka mai unguwa saidai dauke kai yayi
Hurriya kam tana durkushe don tun bulala daya da sukayi mata ta durkusa ta dukar da kanta ta hade kafafunta da gwiwowinta dukanta suke ba ji ba gani duk wanda yaga Hurriya sai ya tausaya mata don idonta sun kada sunyi jawur kukan zuci take wanda yafi ko wani kuka zafi da radadi fargaba da tsoro duk ya cikata laminde matar Mai unguwa kuka takeyi kamar ita ake bugu kasa jurewa tayi ta rugo ta wurin saitin masu bugun ta dan ture Hurriya aka zabga mata bulalar Ai laminde fitsari ne kawai bata saki ba saboda azaba Hurriya dago jajayen idanunta tayi ta saukesu akan laminde kukan da Hurriya zata iya cewa rabon da tayi shi har ta manta ne yazo mata laminde kallonta tayi ta girgiza mata kai ta daina kuka
Bulalar suka kara zuba ma laminde Hurriya zuwa tayi ta ture ta tana masu wani kallo Mai unguwa ne ya kalli dogarawan sannan idonshi na taruwa da kwalla yace don Allah kuyi hakuri ku taimaka kuyi hakuri ta gane kuskurenta yanzu Saminu ya kalli Kumurci wanda yake kallonsu yana kallon Hurriya wadda tayi ligis Kumurci yace sharadi dayane zamu baku Mai unguwa yace ka fadi koma wani irin sharadi ne zamu cikashi In Sha Allah murmushi yayi sannan yace ko matarka ta bimu masarautar Qamar ko kuma wannan matsiyaciyar ya nuna Hurriya shiru Mai unguwa yayi Hurriya da idonta sukayi jajir ta dago tana kallonshi wani murmushin mugunta yayi mata laminde tayi sauri tace ni zanje wallahi ku kyale yar marainiyar yar nan ku taimaka don Allah Hurriya kallon laminde take wadda banda kuka ba abinda take matar ta sota duk da hali na kin kulawa da take bata Amman bata taba gajiyawa da ita ba laminde ta kalli maiunguwa da idon shi sukai ja tace ga Hurriya nan don Allah ka kula da ita Maiunguwa cewa yayi laminde tare zamu tafi mubar Hurriya a garin nan ni zan biki murmushi tayi tace idan mun tafi kuma mubar ma wa ita? Hurriya da zuciyarta tagama karewa ta bude baki kamar tana tsoron magana tace I will go with them cewa tayi banji Mai kikace ba Hurriya tace zan bisu Kumurci wani murmushi ya saki yace da kin taimaki tsohuwar da take tsugune tana rokona Don wannan matar idan har ta bimu sai na sanya ta Zama baiwa mafi kaskanci a masarautar Qamar kuma sai na tabbatar da ko wani kaskantar bawa ya kusanceta yayi dariya Hurriya kam idonta kadai inda ka kalla zakasan tana cikin zallar bacin rai ga galabaitar da duk tayi laminde girgiza kai kawai take tace ba inda zaki ni zan tafi tana kuka tana girgiza kai Hurriya kam abinda bata tabayi ba shi tayi lallashi don bata iya ba ma kwata kwata Amman daga jin yanayin muryarta zakasan kokari ne take tana magana zan dawo zan kira shine abinda tace Kumurci kam kokarin turata ya farayi juyawa tayi ta kalleshi tace kada ka sake ka taba ni da kazamin hannunka a irin yanayin da tayi maganar zaka san ba abinda bazata iya ba idan har ya kara Kumurci kallonta yayi yaga yadda idonta ba wani abu wai shi tsoro shiru yayi sannan yace yarinya zaki gane kurenki a masarautar Qamar don karnukan suna da yawa ya fada a zuciyar shi.
Hurriya jikinta duk ya mutu saboda dukan da akayi mata laminde kuka kawai takeyi don abun yafi karfin ta Jikinta sai kyarma yake ledar dake yashe ta kayanta ta dauka
Kumurci ya kalli mutanen da dogarawan yace su fito su tafi kamarshi ake jira aka tasa kyayar samarin suna turasu kamar jakuna
Hurriya gashinta duk yayi budu budu saboda bata maida dankwalin da ta cire ba lokacin da zata rike hannun Kumurci shikam Kumurci da ya juyo ya kalli yadda take struggling yakejin gabanshi na faduwa saboda yadda yakejin zuciyar shi ya kosa su isa masarautar su Mai cike da zallar zalincin he can’t wait to have her in his bed
Cikin hiace din emirates din ake ta tura maza saida aka cika mota guda uku Hurriya dai tana tsaye bata matsa ba saboda duk duniya ta tsani taji jikin wani kusa da ita gashi duka marmatse suke saidai fa ko zata mutu a wurin bata shiga motar nan don waye ma baisan Hurriya Faisait hamood ba duk wanda yayi gigin tabata da hannunshi saidai yaji saukar mari
Daya daga cikin dogaren ne yazo ya zuba mata bulala ke yar matsiyaciya shiga banza tayi dashi don wani bansan kallo tayi mashi bata ko daga baki ba ballantana yayi tunanin zata bashi amsa kara mata wata bulala yayi har tana durkushewa kasa da kayanta shegiya matsiyaciya ki wuce ki shiga Dukanta ya fara kamar Allah ya Aiko shi yana zagin Hurriya da ta shiga motar Amman shiru tayi saidai fa ba hawaye amman idonta sunyi ja saboda radadi da azabar da take ciki Kumurci ne ya buga mashi tsawa yace shaho ya isa hakanan shaho badan ya gaji ba ya daina dukan ta ya lura wata isa gareta alhalin ita din ba kowa bace face kaskantarciya Kumurci ne yazo saitin da take yace Mai kike jira da bazaki shiga ba banza tayi dashi kamar batasan da ita yake magana ba kara tambayar ta yayi banza Hurriya tayi dashi har cewa yayi zai kira shaho ya kara mata still bata ko motsa ba Hurriya kam taki ko matsawa kowa mamakin Kumurci yake da aka ga yana lallabata saboda waye baisan Kumurci ba saida Hurriya ta mula sannan tace ban iya zama kusa da kowa cikin motar I want to seat alone kallon yadda take magana yake fuskar ta a daure kuma kamar tana bashi order abun ma dariya yaso ya bashi Amman da yake Kumurci ne yayi saurin murtuke fuska ya kalli motar da duk maza ne a ciki sannan ya fitoda mutum biyu yace ta shiga da kyar take tafiya Hurriya saboda dukan da tasha ,har ta kawo wurin cikin motar kayanta gam a hannunta kamar daman sune rayuwarta kusan duka mazan saida suka juyowa suna kallonta saboda kyaunta ga gashin dake yawo a bayanta tsawa Kumurci ya buga masu dukansu suka shiga taitayinsu Hurriya bayan ta zauna ta fara sauke ajiyar zuciya tunani take yanzu to ina rayuwa zata kaita lokacin da bata tsammani haka ya faru da ita saidai duk inda zata tana fatar Allah ya bata ikon jurewa don ga dukkan alama sun nuna ba wurin jin dadi bane a hankali ta duka ta nemo safa cikin kayanta ta sanya dukar da kanta tayi yadda ba wanda zai iya ganinta ta cire sarkar dake wuyanta da kuma dayar sarkar ta sanya su cikin safarta harda kudinta duka ta sanya su wayarta ce kadai ta bari a aljihunta tafiya ne suka fara Sosai don tunda ma aka fara tafiyar Hurriya wani bacci ya dauketa tafiya sukayi sosai don kusan tafiyar awa biyar sukai don lokacin har amfara kiran sallah la’asar shine suka tsaya domin yin sallah
Hurriya jin hayaniya ya sanya ta bude idonta a hankali nan taga sun tsaya masu gyada nata tallah masu rake panke awara duk da sauransu cikin rashin kuzari ta sauko Amman jikinta yayi mata mugun tsami don da kyar take tafiya wasu panke manya guda biyu ta siya aka bata canjin ta sannan ta koma chan gefe ta zauna ta fara cin abunta
A hankali take ci ba don dadi ba sai don yunwa Hurriya taji ankira ta da mamaki ta dago kanta sai taga Bintu.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 9&10
Mika ma Bintu fanke daya tayi kato cikin jin dadi ta amsa tace nagode Hurriya ,shiru Hurriya tayi tana kallon yadda Bintu ke cin panke a hankali ta kara kiran mai fanken cikin muryarta Mai dadi kara mika mashi kudin tayi tace ya bata na dari guda biyu ya kara bata mika ma Bintu tayi amsa tayi tace inason ki Hurriya sannan ta rinka cin fanken kamar bata taba cin abinci duniya ba Girgiza kai Hurriya tayi Bintu ce tace ma Hurriya kalli abinda dogarawa can keyi Hurriya mun bani Hurriya kallon saitin da dogarawan suke tayi taga sun sanya sun jera layi layin maza daban na mata daban Hurriya batasan ma cewar akwai mata ba sai yanzu da tagansu jere a layi kallon Bintu tayi tace tare dawa kukazo Bintu da har ta fara kuka ta kalli Hurriya tace da wadancan azzaluman dogarawan daga kai Hurriya tayi tace ya akayi kika biyosu kuka Bintu ta fara tace muna zaune a tsakar gida saiga kawar Larai nusaiba ta shigo daki suka shi itafa Larai nusaiba tace ga yan masarautar Qamar nan sunzo zasu dauki ma’aikata da bayi. Shine tace kawai ta tura ni aiki ba bauta ba suna biyan kudi Sosai kuma ita za’a rinka bama kudin ina labe inajin su har nusaiba ta fito kallona tayi tace kuma naji ance sun fison mata kyawawa kuma kinga Bintu ba daga baya ba sai Larai tayi dariya tace kedai bari ba karamin taimakona kikayi ba nusaiba zan yadda kwallan mangwaro In huta da kuda gshi kuma Abun riba biyu dariya kawai nusaiba tayi tace ai kin yanman albashin nata ko?? Larai tayi dariya tace abinda yafi albashi ma don bakaramin taimakona kikayi ba suka kalli Bintu Larai ai nasan ubanta baida matsala nusaiba kenan ya bani matsala ma yaga ikon Allah
Bintu ta kalli Hurriya dake kallonta shine fa suka sanya na biyo dogarawan Hurriya daga mata kai kawai tayi ta juya saitin dogarawan tana kallon tsantsar zalincin da sukeyi Maza da matan dake jere a layi ake cajewa duk abinda aka ganka dashi sai a amshe har cikin riga suke lalubar matan cikin tsantsar zalinci abun gwanin ban takaici Hurriya a hankali ta zaro sauran kudinta dake cikin aljihu ta sanya su cikin safarta gyara safar tayi yadda ba wanda zaiga abinda ke a cikin kafarta cikin sa’a kuma ba wanda ya kula da lokacin da ta dauke kudin Shaho ne da yake kusa da Kumurci suna zaune suna kallon duk abinda ake don kamar sune manya kaga wata yarinya Mai kyau kamar ita tayi kanta nifa bantaba ganin mai kyau irinta ba dogon gashinta ya bani mamaki nace anya bahaushiya ce kuwa ko yanayin shigarta kadai zata nuna maka haka saidai fa kaga yadda take kallonmu girgiza kanshi yayi Kumurci nifa idanuwanta tsoro suke bani Kumurci yarinyar can fa na cikin hadari saboda karnukan dake masarautar mu fa sunada yawa gashi ba babba ba yaro don ko nifa sai na lasa yana karasawa da lashe baki Kumurci wani kallon banza yayi mishi wanda ke hade da gargadi shiru shaho yayi cikin ranshi yace wallahi sai na lasa ai kaima nasan manufar ka munafuki
Wani dogari ne ya kalli saitin dasu Hurriya suke kai tsinanu yan gidan matsiyata kuzo nan Hurriya ko motsi batayi ba Bintu tace mata Hurriya ki taso don Allah mu tafi kadasu dake mu banza Hurriya tayi da ita don maganar duniya taki ta tashi su Kumurci da shaho duka suna kallon abinda ke faruwa Bintu zuwa tayi ta shiga layi kwalla na zubo mata dogarin kau cikin hasala yazo saitin Hurriya kallon shi tayi cikin ido shine ke sanya hannunshi acikin rigar mata tashi tayi tsaye tace da uwarka da ubanka sune manyan matsiyata da har suka haifo wanda baisan dajar halitar mata ba kaskantarce kuma duka halayenka ke defining kaskanci Bullock wata muguwar ashariya shaho ya saki yace kaga wannan yarinyar Kumurci shuru yayi kowa ma shiru yayi yana jira yaga abinda zai faru Azuciye dogarin ya daga bulalar ya zuba mata a baya,mata da mazan wurin duka tsigar jikinsu tashi tayi suka juya itakam Hurriya kwalla ce ta zubo mata abinda ta dade batayi ba a rayuwarta wato kuka ta kasance a kullum rayuwarta ita Mai kukan zuci ce har tana jin dama zata iya irin kukan da Bintu keyi kilan ta samu sanyi ko yayane a ranta bulalar da yayi mata har cikin kanta taji azaba matuka wanda ta durkusa kasa hawaye na zubowa Daga hannunshi yayi da niyyar kara dukanta Kumurci ya rike hannun yace ya isa haka Garba ajiye hannunshi yayi ba don yaso ba sannan Kumurci ya yace tayi shiru sannan yace ki iya bakin ki idan ba haka ba to kina hanyar da bazata bullar dake ba don masarautar Qamar sai yayi murmushin mugunta Hurriya tana durkushe a hankali ta shafo hawayen don ta tabbatar da idan nagaske ne kallon hawayen tayi fa dagaske sune tasan ba lallai ta kara maimaita irin wannan kukan ba saboda yau sau biyu tayi kuka sannan ta kasance zuciyar ta Mai rauni ce saidai idan kaganta zakayi mamakin minene ya sauyata har haka da ba abinda yake girgiza ta ko ya bata mamaki kuma fa rashin ganin mutumcin kowa duk girman ka Daidai take da kowa don ko yaro yajefeta da magana sai ta maida mashi martani da wadda tafi tashi zafi shine kawai abinda ke sanya ta magana ko sai kuma idan tana tare da Bintu don Bintu zata iya awa tana mata magana baifi ta bata amsa daya ba saboda miskilancin ta Bintu har ta saba.
Kumurci kallonta yake saboda yasan akwai matsala a masarautar nan idan har Hurriya ta shige ta don ya lura bazata taba saukar da kanta kasa ba don haka yake tunanin hanya daya zai bi don tasamu barin masarautar batare da ansamu matsala ba shine yace baiwa ya samota kuma yaroki alfarmar ta zama Baiwa hakimi shine kawai mafita anma ta cigaba da haka baisan a hannun wazata mutu ba don princes da princesses din masarautar nan basu da imani ga kuma dayar matsalar don Kumurci yayi nadamar tahowa da Hurriya don yasan ba karamar wuya zatasha ba don ko yaran sarki kadai sun isheta don sun tsani wani yafisu kyau duk da daman masarautar kyawawa akafi kaiwa saidai ba wanda san dalili to zai iya rantsewa tunda ake kai kyawawan mata a masarautar baitaba ganin Mai kyaun wannan yarinyar ba don su kansu yaran mai martaba sai sun raina kansu.
Kallo daya zakayi mata kasan ta jigata ba karamar jigatuwa ba ma don wandon dake jikinta duk yayi datti fuskar ta kuma duk ta kumbura ga babu annuri kwata kwata saida fa annurin kyanta nan don sai salki takeyi Kumurci yace ki tashi ki shiga mota mu tafi yanzu bada hargagi yayi mata maganar ba don zuciyar shi ta dan karye kadan Kallonshi tayi da idanunta masu kyau da wani kaifi Kumurci ya daga mata kai tare da fatar kada tayi kafiya irin wadda tayi dazu.
A hankali take takawa amman zaka iya hango zallar mulki dake cikin tafiyar tata har ta shiga motar a hankali Kumurci girgiza kai yayi don ya hango kurar dake tafe da ita saidai Allah ya kyauta don aikin gama ya riga ya gama.
Bintu kam lokacin da ta koma layi cikin sa’a ba ba wanda ya lalubeta saboda hankalin kowa da ya koma kan Hurriya tanajin su karime dake gabanta cikin layi suna dariya suna cewa Allah ya kara sa’ade ce tace kinsan dadin da nikeji yadda ake bugun Hurriya karime tayi murmushi tace naki kika sani ni yarinya ta dade tana bani haushi shegiya ga isa ga iko sai kace wata shegiya sa’ade tace bata da mutunci Hurriya kinga cin mutunci da tayi ma mahaifina kuwa harda watsa mashi man awara akafa bayan tagama zazzageshi cikin mutane karime yo naji maganar tana yawo agari ki bari idan munje mu hade kai mu ci ubanta don ni ta dade tana bani haushi don kiga duk anguwar mu ace mazan ita kadai suke kallo to yanzu lokacin mune idan munje muyi maganin karuwa Mai ma maza jiki.
Bintu duk tanajinsu don harda kukan ta wurin da suka ce mata karuwa don tasan karya sukeyi Allah ya saka maki Hurriya inji Bintu ta fada cikin ranta.
Hurriya da ta koma wurin zamanta ta jinginar da kanta jikin window tana rufe idonta saidai kyarma kawai takeyi tana harhade hakoranta ga sanyi da ya isheta dankwalin da ta daura ta rufe gashinta dashi ta koma ta kwanta saidai sanyi ya matsa mata don bata daina jinshi ba ledar kayanta dake gabanta ta jawo saboda Asabe hada kyautar doguwar hijab tayi mata don lokacin har ta kawo zaure Asabe ta kwala mata kira a hankali asabe ta mika sabuwar hijab doguwa maroon tace Hurriya ko bazaki sanya ki fito ba ai nasan kina sallah to ki rinka sallah da ita inda so samu ne ki rinka fita da ita sai kuma ta tabe baki tace nasan yaudarar kaina nike ba inda zaki da ita tace Hurriya ki godema Allah don wallahi inasonki duk wanda yaji nayi kyauta sai ya kusa suma saboda mamaki kindai sanni da san kudin tsiya Hurriya batace mata komai ba har tagama maganar ta sai Hurriya ta mika mata ledar alamun ta sanya Asabe kam sauri ta dauko ta sanya Hurriya ta tafi ba godiya bare sallama.
Hijabin ta lalubo ta sanya ta dunkune kanta ciki a hankali bacci ya dauketa.
Sosai suka sha tafiya har suka iso Babbar masarautar Qamar bata sani ba don kowa ya fita a motar ya barta Kumurci ne ya kula da babu ita don har anfara kada kyayoyinsu Kumurci ya bude motar yazo inda take bacci da yake bai san sunanta ba don haka yace ke ki tashi mun iso shiru Hurriya tayi saida yayi mata magana kusan sau uku sannan ta bude idon wadanda sukayi mata nauyi Sosai har lokacin tana jin jikinta na kwankwatsa Kumurci yace ki fito munzo kuma kada kiyi ma mutane kafiya da rashin kunya don kece zaki sha wahala Hurriya da batajin karfin jikinta kwata kwata don ko yadda take numfashi zaka iya lura tashi tayi ta rungumo kayanta saidai tana tafiya biyu ta sake su Kumurci da yayi gaba yaji karar kayan da tasaki don haka ya juyo ya kalleta sannan ya daukar mata kayan suka fita duk da suna zuwa ana sallahr magriba don duhu har yafara Bayyana Amman bazaka iya gane cewa rana ce ko dare ba saboda haske da ya wadaci ko ina a babbar masarautar Qamar Masarautar kanta abun kallo ce girmanta gari guda ne tunda ga floor din dake kasan masarautar da ginin da akayi mutum zai gane cewar masarauta ce maiji da tsantsar dukiya kuma da karfin mulki .saidai Hurriya ba Abu daya wanda ya burgeta don kallo daya tayi ma komai wanda bata kara kallon wani Abu ba
Su Bintu da su karime kam Murna sukeyi kamar su ciji duwawunsu basu san masarautar Qamar, bawuri bane da ya kamata ace ya burgesu ba ko su kasance masu farin ciki Don masarauta ce wadda take cike da tsantsar zalinci da rashin imani.Kusan duk wadanda sukazo dasu sakin baki suke suna kallon ko ina.
Tasa keyarsu akayi ana bugunsu kamar tumaki suka shigo ciki inda ba abinda kake gani sai dagorawa dake tsaitsaye fuskar su hade kamar zasu je yakin basasa hannunsu daya narka narkan bulali Dayan kuma hannu dogayen bindigu kowane,Ba wanda bai firgita ba da ganin wadanan dogarawan don fuskar su babu alamun sassauci
Hurriya da da kyar take tafiya saboda zazzabin da take wani bakin dogari ne ya sakar mata bulala wadda saura kadan ta fadi da kyar ta cigaba da tafiya
Kumurci da yaga banda dukansu ba abinda akeyi yayi dauriya yace basu bane bayin ,Dukansu tsaya sukayi suna kallon Kumurci saboda dokar masarautar ce duk wanda yafi ka matsayi dole kabi umarninshi kuma duk abinda zaiyi ba wanda ya isa ya dakatar dashi saidai idan har akwai wanda yafika matsayi zai iya hanaka to
Kallon Kumurci suke da idanunsu masu sawa mutum ya shiga zullumi Kumurci da duk ya tsure yace Allah ya gafarce ku Kumurci yana Neman sassauci. Saminu ne ya iso don kusan duk yafi su matsayi ya kallesu yace lapya?cike da rusunawa ya fara mashi bayanin abinda ya faru wani kallo Saminu yayi masu wanda nan take suka bar wurin ya kalli Kumurci yace ka shiga dasu ciki kuma duk wanda ya tareka kace ni na baka umarni shiga dasu daga ciki sannan ya bar wurin.
Kallon su shaho yayi da yan matan da suka taho dasu da mazan,saitin Hurriya ya kalla yaga tanajan numfashi da kyar ta hade gwiwar ta da kanta,tunda aka tsaidasu ta kwanta Kumurci ba karamin dadi yaji ba lokacin da yaganta da hijab ya tabbata da ace ba hijab jikinta da yanzu wani ya shiga dakinshi da ita gashinta kuma da tuni an datse saidai cikin ikon Allah ta rufe duka jikinta harda kusan rabin fuskarta.
Tafiya sukayi inda suka kara nitsa kansu cikin masarautar sakin baki kusan Dukansu sukayi don haduwar masarautar tafi bayyana yanzu akan wurin da suka baro a baya kuyangu ne da bayi da hadimai wadanda basu da iyaka kowa da hidimar da yake kuma kusan kowa da kalar uniform din dake jikinshi wasu green and red wasu green and orange wasu green and yellow wasu green and blue.
Su karime kam yau sun samu Tv don suna kashe ma kwarkwatar idon su haka suka rinka tafiya don daga inda suka baro zuwa inda sukazo yanzu tafiya ce Mai wani irin nisa don dukansu sun gaji shaho yace a kira uwale uwar bayi ta raba masu aiki tun yanzu Kumurci ya daure yace ai kasan ka’idar abun dole sai sunkai gobe saboda jakadiya tana shiyar uwargijiyar ta yanzu to bari na nemo uwar bayi Shaho ya tafi don nemo uwar bayi ba tare da wani bata lokaci ba sai gashi sunzo fuskar ta ba annuri bare fara’a Kumurci ne ya gaisheta cike da girmamawa ya mikasu wurinta Kumurci Kallon Hurriya data gama galabaita yayi cikin aljihun shi ya fiddo paracetamol da ibuprofen ya bata kin karba tayi don kusan sau uku yana mata magana ta amsa Amman ko kallon inda yake batayi ba bare har ya sanya ran zata amsa a ranshi yace zaki sha wuya ne a masarautar nan don duk kafiyar ki sai kin ajiyeta don dubunki ma sunyi sun gama
Kumurci ya dora mata maganin saman hijab sannan ya juya ya bar wurin,su karime kam sai kallon yadda ta zukana sukayi she looks so pale and weak yanayin da ba wanda ya taba ganin ta dashi tunda take rayuwarta she’s always strong and fierce don haka Dukansu da mamakin yadda take suke sai Abu na biyu da ba wanda ya taba ganin ta dashi wato hijab tunda duk wanda ya kwana ya tashi ba wanda ya taba ganin Hurriya da hijab a unguwar su shiyasa suke kallonta da mamaki uwar bayi ce ta kallesu tace wai Lapia kukayi tsaye kallon mazan tayi tace zata kira halliru ya shigar dasu ta kalli su Bintu tace su tafi.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 11&12
Uwar Bayi ce gaba suna biye da ita tafiya sukayi Mai nisan gaske kafin su iso wani babban gini kallon wurin su Bintu suka rinkayi ita dai Hurriya ta kosa ta kwanta don kiris ya rage mata ta daina tafiya saboda kasusuwan ta da suke kwankwatsa kusan dukan su itace karshe wurin tafiya uwar bayi ce ta shiga dasu cikin ginin wanda yake da bangare iri da iri a ciki
Kuyangi ne kowace da uniform dinta suna hidimar su tunda suka shigo yan matan dake zaune suke binsu da wani irin kallo Hansa’u ta tabo barira tace kinga mun samu sabbin zubi yau Barira da take kallon Ko wanne a cikin su daya bayan daya cikin izza da takama tace uwar Bayi daga ina aka samo mana sabbin tumakai su sa’ade da karime duk suka bude baki Hurriya da tanajin sun saidai ta kanta takeyi Uwar bayi kam batace komai ba ta wuce suka bi bayanta
Hansa’u ta kalli barira tace kinga yan mata tsala tsala nifa harna hango wacce tayiman Barira yadda take zaka dauka wata diyar sarkice saidai kawai saboda tafi su mukami kuma tanada saurayi a cikin dogarawan don haka take baza nata mulkin a inda ya kamata cikin izza da mulki tace kudai bi a hankali kada wata acikin ku ta shiga gonata sannan ta tashi tana wani juyi wanda kamar dagan gan takeyinshi su Hansa’u Dukansu biyota sukai abayanta.
Uwar Bayi wani babban daki ta kaisu wanda yake da Bayi kusan duka manya mata ma ko ina shimfede da katifa kowa kallonsu yakeyi da tausayi don ace yara da kuriciyar su sunzo azzalumar masarautar nan don neman abun duniya but basusan cewar lalatar rayuwar su sukazo yi ba don a masarautar tasu miye ba a aikatawa na kazanta babu shi Duk abinda baida kyau shi akeyi ga zalunci.
Uwar Bayi ta kalli yan matan da tazo dasu tace to nidai ga makwanci don haka ku nemi inda zaku kwanta kafin gobe tayi a rarraba maku wurin bacci Dukansu godiya sukayi mata sukaje neman wanda zai taimaka yadan rabasu kafin zuwa goben da tace.
Hurriya kam tana duke bata motsa ba bare tayi i tunanin tafiya Uwar bayi ta kalleta tace kiyi maza kije ki nemi wurin kwana ko ki kwana a kasa tunda ba’a gidanku kike ba Hurriya dagowa tayi ta kalleta wani irin kwarjini tayima Uwar bayi Uwar bayi batace komai ba ta tabe baki ta fita.
Bintu kam har tasamu wurin kwana matar Mai kirki kamar ma budurwa ce ita ta kara Bintu kuma katifar katuwa ce zata ishesu su biyu Tunawa Bintu tayi da Hurriya don ba taganta ba tunda suka iso a hankali ta fara o dubata kafin ta hango ta zaune a tsakiyar dakin cikin sanyi sai kallonta akeyi da sauri Bintu ta nufi inda take tace Hurriya a hankali ta dago idonta da sukayi jajir ta zuba ma Bintu hankali tashe tace Hurriya mike damunki baki lafiyane? Subahanallah ta dora hannunta saman goshin Hurriya & tureta tayi da sauran karfin daya rage mata tace How dare you touch my Royal Body maganar na fita da karkarwa saboda kyarmar da takeyi Bintu tace kiyi hakuri don Allah hankalina ne ya tashi dana ganki haka Bintu tasan cewar Hurriya na bala’in sonta duk da cewar bata nunawa amman idan Bintu na mata labari hankalin ta duka take bata ko Daga yanayinta zakasan tanajin dadin ko wani irin labari Bintu ta bata kuma tasan har abada bazata samu kawa irin Hurriya ba don ako da wani lokaci itace Mai tsaya mata tsayin daka a rayuwarta ta kwatar mata yanci a wurin kishiyar uwa da shikanshi mahaifinta don ba wanda baisan irin muzgunawar da suke mata saidai Hurriya ba ruwanta haka zatazo tazage su tass kuma tayi masu babban kashedi na idan suka kara matsa mata zata dauko masu hukuma kuma sunsan halinta saboda ta taba dauko ma Larai da baban Bintu yayi magana tace a hada dashi saida Bintu tayi sati daya a wurinta lokacin abinci duk idan zasu ci sai ta tambayi Bintu mizasu siyo kuma duk abinda Bintu ta gani tanaso sai ta siya mata shi wani lokacin da kanta take tambayar Bintu Abu kaza yayi maki idan tace Eh zata sai mata shi kamar batasan darajar kudinta ba kuma idan har Bintu tazo bata kara kwana a katifa sai a kasa saboda Hurriya ba wanda ya isa ya taba koda hannunta don tasan wannan halin nata duk wanda yayi gigin taba ta sai ta sauke mashi mari Bintu ma kafin su saba kusan sau uku tana Marinta saboda yawan kai hannu jikinta daga bayane saidai ta tureta tayi mata kallon kada ta kara.
Kallon Hurriya tayi tace mata sanyi ke shigar ki muje ki kwanta banza tayi da ita Bintu kuka ta fashe dashi tana ma Hurriya magiya ta tashi sanyi Amman ina kusan duka mutanen dakin kallonsu suke Bintu kam da taga Hurriya taki tashi sai ta kwanta kasan siminti tana kuka tace mata don Allah ki tashi idan har baki tashi ba nima anan zan kwana Hurriya kallonta tayi cikin muryarta mai cike da rashin karfi tace Bintu ki shekara a kasa idan kin tashi Bintu da tasan wacece Hurriya tayi mata sanin da ba wanda yayi mata shi don tabbas Hurriya dagaske take ta shekara kwance a siminti itadai batasan mi ya faru a rayuwar Hurriya ba daya maidata haka kamar dutsi
Fashewa da kuka Bintu ta karayi sannan ta tashi tanayi mata magiya kallon yanayin Hurriya tayi wanda banda hakoranta dasuke gabgab ba abinda sukeyi wani kuka ta kara fashewa dashi mai tsuma zuciya ta fara hadata da Allah mutane duka kallonsu sukeyi suna mamakin irin son da Bintu keyi ma Hurriya ita kuma Hurriya ta kafe kamar kafurar farko sa’ade tace kibar shegiyar ta mutu kowa ma ya huta kafura Mai bakin hali Karime tayi caraf tace tun ba aje ko ina ba karshen karuwa yazo namu dai muyi kallo duk jiji da kan mutum dole ya ajiye shi don ubanshi zaici yayi anan.
Hurriya duk tanajinsu duk da ciki ciki sukayi maganar ta yadda bazata iyaji ba ,saidai sunanta fa Hurriya Faisait Hamood. Magana daga nesa komin kasa da murya da mutum zaiyi sai taji ta kamar gizo gizo haka take Allah ya bata kunnuwa kamar ba irin na mutane ba saboda kaifin ji da suke dashi.
A hankali ta fara wani irin tari harda sarkewa salati Bintu ta rinkayi tana kuka da tarin ya tsaya ba abinda take sai karkarwa Bintu a hankali ta rage tsawonta tana kuka tace ki taimakeni Hurriya ba kanki zaki taimaka ba Hurriya tunda nike baki taba musu da duk abinda nace inaso ba sai kinyi mani shi don Allah ki taimakeni ki tashi ba don halina ba Hurriya kallon Bintu tayi da idanunta masu kyau saidai sun rikida sun koma jajawur saboda azaba don har jijiyoyin idonta ana gani
Hurriya tashi tayi a hankali ta fara takawa saidai kafafunta banda kyarma ba abinda sukeyi Bintu ta dafata saboda kada ta fadi tureta tayi da sauran karfin da ya rage mata har Bintu na faduwa kasa tana binta da wani kallon cikin muryar ta da ta shake tace kina hauka ne ,Bintu kuka take tana girgiza kanta tace Aa to sai ta kasa maganar tana Neman faduwa Bintu da sauri tazo ta tarbeta kada tafadi kasa daga Hannunta Hurriya tayi da basu da karfi sosai ta wanka mata mari tana kallon Bintu da sai kuka take sannan ta sake ta
Mutane kallon dramar kawai suke wasu lokaci daya Tsanar Hurriya ta kamasu saboda rashin mutuncinta suna jin tausayin Bintu wasu kuma zaginsu kawai suke suna cewa marar sa mutunci zasu zubda hali daga zuwansu duk munsan ma’anar abinda kukeyi hmm mutane sun iya judging din abinda bashi bane Har sun manta da cewar yau su Hurriya da Bintu suka zo bare suyi irin hallayar da suke magana.
Hurriya da kanta ta taka sukazo har inda Bintu ta samu wurin kwana Bintu kam dadi ta rinka ji don har ta goge hawayen ta.
Habiba kallo daya tayi ma Hurriya ta washe mata baki tace sannu yanmata Hurriya ko kallon inda take batayi ba bare ta sanya ran zatayi mata magana
Bintu kallon Hurriya tayi tace bari tayo alwala, waje ta fita sannan ta dawo ta gyara hijab dinta ta fara rama sallolinta har tagama Hurriya idonta a rumtse yake don ta jinginar da kanta jikin katifa.
Bintu bayan tagama addu’arta ta kalli Hurriya tace in samo maki abinci Hurriya daga mata kai tayi alamar Eh Kallon habiba Bintu tayi tace ina zan samo mata abinci Habiba tace muje in raka ki kitchen ki amso naku abincin to inji Bintu don haka tabi bayan Habiba suna tafiya akan hanya sai habiba ta dan wuce Bintu itakuma Bintu tana ta tunani tana tafiya.
Habiba juyowa tayi baya sai taga Bintu na tafiya kamar wacce zata fadi dawowa tayi ta rike mata hannu gam tace kina tunaninta ko ?kada ki wani damu zaki samu wadanda suka fita komai a masarautar nan wacce zata kula dake kuma ta soki sai ta farayi mata tafiyar tsutaa acikin hannu tace Ko nima idan kika bani dama zan maye maki gurbinta Sai ta tsunkuli Bintu a waist dinta tana kashe mata ido daya itadai Bintu kallon ta kawai takeyi ba tace uffan ba don batasan inda zancen nata ya dosa ba kallon habiba tayi tace muje ko naga lokaci na tafiya Dariya habiba tayi tace gaskiya kinason wannan yar tawalwalar ki nima inason inga ana kula dani haka shiyasa nike kaunar ki don daga gani kinada kulawa ko kukan da kikayi mata kadai ya isa ya nuna hakan
Gaskiya inasonki nagode kawai Bintu tace sannan tace muyi sauri kada tayi bacci murmushi habiba tayi ta rike mata hannu suka fara tafiya da fan dan sauri sauri itadai Bintu tanajin yadda take mata tafiyar tsutsa da hannu har suka kai babban kitchen din da ake dafa ma bayi da kuyangi da masu aiki abinci ba’a wani hantare su ba saboda sanin sune sabbin ma’aikatan da suka zo don suna bukatar Abinci don habiba tayi masu bayani
Plate biyu aka basu cike da tuwo habiba ta amsa ita kuma Bintu tayi tsaye tana kallo ana miko mata plate din Habiba ta kalleta tace ki amsa mana bata fuska Bintu tayi tace ba shinkafa ne? Kallonta mai bada abinci take da mamaki tace ke yar Gidan maysiyata ki amsa idan ba haka in maida ki kwana da yunwa shegiya har MU zakiyi ma iyayi alhalin agidan ku ba lallai kina samun kalar shi ba Habiba ta mintsinota Bintu ba domin ranta ba haka ta amshin abincin saboda tasan ba lalle cewar taci tuwon ba
Suna zuwa suka ga Hurriya ta kara dukunkune wa don ta kara makurewa wuri daya kamar da alama sanyi takeji Bintu tace Hurriya ki tashi ki ci abinci A hankali ta bude fuskarta tana kallon Bintu da take kuka a hankali tace ya akayi kuma?Share Hawayen ta Bintu tayi tace Hurriya don Allah ki ci abinci kada ki ce bazaki ci ba akwai nisa fa inda muka amso kuma kinga baki lafiya tana sakin baki kamar karamar yarinya Dan tsotsar bakinta Hurriya tayi kamar daman sararta ce ta daga mata kai
Cike da jin dadi Bintu ta miko mata tuwon Habiba dai tana kallon ikon Allah kwano ta samu ta debo ruwa sannan taba Hurriya ta wanke Hannunta ta fara cin abincin a hankali ta dan ci ba laifi tanajin ta koshi ta ture plate din ta kalli Bintu ,da sauri ta kara miko mata kwano ta zuba mata ruwa ta wanke hannunta Habiba cike da kaudi da son ta samu shiga tace Hurriya ga magani kisha na ciwon kaine Da zazzabi Hurriya ko kallon inda Habiba take batayi ba don a hankali ta sanya hannuta cikin hijab aljihun wandonta anan ta fito da magungunan da Kumurci ya bata hannun Habiba har lokacin yana tsaye tana bata magani cikin muryar ta da take da alamun rashin lafiya tace Bintu bani Ruwa.
Da sauri Bintu ta bata ruwa ta shanye maganinta kallon habiba Bintu tayi tace kiyi hakuri tana da wuyar sabo ne Amman tana da kirki zaku saba In Sha Allah .Bari in tafi in samo wurin kwana sai Hurriya ta kwanta tare dake,Habiba murmushi tayi cikin yanga tace yi zamanki ki kula da abarki ba mai takura maku nizaje inda nima za’a kula dani,dadi sosai Bintu taji ta farayi mata godiya don tasan idan har Hurriya ta kwanta Habiba ta kwanta kusa da ita kilan za’a iya tashi aga habiba kwance saboda irin dukan da Hurriya zatayi mata kuma itakanta Bintu bazata taba bari ta kwana kasa ba saboda sanyi.
Habiba ta fita tace matsiyata kuma ashe kunsan harka muje zuwa ta nufi dakin Su Hansa’u Aiko tana shigowa sukazo suka zagayeta sukace mata habiba ya bakin nan nagansu tsalatsala guda habiba tayi tace ayiri to ku kwantar da hankalin ku don ba wata wahala da zamusha wannan karan wurin jawo hankalinsu tace ai yan gidan matsiyatan suma duk sun san harka don wadda na bama makwanci ma baki gansu ba kamar zasu cinye juna nan ta kwashe labari ta basu tass dariya suka rinkayi suka ce gobe zasu zo ta nuna masu yan matan suna fata ma Allah ya sanya akawosu dakin Barira duka tana jinsu Amman batace komai ba don shiru tayi.
Bintu kallon Hurriya tayi da ta fara gyangyadi tace ki kwanta ni zan kwanta kasa daga mata kai Hurriya tayi ta kwanta dukun kune cikin hijab dinta bacci ne mai wahala ya dauketa Bintu kam tagumi ta buga tana kallon Hurriya don ta hango wahalar da zatasha a masarautar nan don Hurriya bata durkusa ma wada sadai da alama waddanin sunyi yawa a masarautar kuma wahala zata sha don ko bata durkusa ma ma’aikata ba ai akwai ubannin gidansu da dole suyi masu biyyaya tana fatar dai Allah yasa kada su sha wahala don ganin Hurriya tana wahala tamkar itace take wahalar bazata iya dauka ba.
Murmushi tayi ganin Hurriya ta tsotsi bakinta sai kuma ta turo bakin tana bata fuska alamar shagwaba magana tayi da wani yaren Bintu da take kallonta taji tana magana tana bata fuska da wani yaren da bata taba ji ba
Don tasan yaren dai gaskiya babu kalar shi a Nigeria
Kallon kyaun hallitar fuskarta takeyi yadda tayi ma fuskarta kamar wata baby magana takeyi cike da shagwaba murmushi Bintu tayi tace naga ranar da Hurriya zata daina daure fuskarta tana shagwaba haka tabb akwai ruwa da kankara ranar.
Bintu bacci ta faraji don Haka ta kalli Hurriya ganin ta dukunkune wuri daya kuma ga space nan da yawa don haka ta raba gefenta ta kwanta nesa sosai da ita don kada cikin bacci Hurriya taji ta a kusa da ita ta tureta
Addu’a tayi sannan ta runtse idonta bacci mai cike da gajiya ya dauketa .
Karfe bakwai Bintu ta tashi har lokacin Hurriya bata tashi daga bacci ba ta makara don haka agurguje ta kama ruwa hade da alwala tazo tayi sallah .Tana gama Sallah taje inda taga sauran yan uwanta karime tayi ma magana tayi banza da ita don haka tayi ma uwale magana tace miye akeyi anan uwale tace zamu tafi ne za’a araba mana aiki bata ida magana ba saiga Uwar bayi tazo Kallonsu tayi tace saifa kun kula kubi a hankali kuskure daya a masarautar nan zai iya zamar mutum babban kalubale a rayuwarta, kowa amsa mata yayi sannan suka bi bayanta tafiya sukayi Mai nisa sannan suka iso katon wuri inda mazan dasuka zo duk sunja layi suma layi sukaja suna kallon kyawu da tsarin masarautar da babu wani Abuna more rayuwa da bai wadace ta ba.
Kwance take a lallausar katifa wani Abu dake gefenta kamar wasan yara ya fara kara bude idonta tayi masu cike da bacci kokarin komawa take Amman karar ta hana ta karar wayarta ta hade da karar abunda yaketa wakar yaran tsoki taja tana maganganu da kuma mamakin wani marar sa’a ne ya tada ta daga bacci Amman bari Taga kowaye tana jawo wayar wani call din na kara shigo mata kallon wayar tayi da wani bacin Rai cikin muryar ta maidadi tace oh my God sannan ta ziro dogayen kafafunta wani Abu ta latsa saiga kuyangi guda Biyu sun shigo suna dukar da kansu kasa sannan cike da mugun girmamawa sukace Allah ya taimake ki Allah ya kara maki Nasara Allah yasa wannan Rana tazamar maki Ranar farin ciki da Albarka Batace masu kala ba sai da tagama Shan kamshinta sannan ta kallesu Dukansu ba wanda baisan ma’anar kallon da tayi masu ba don haka da sauri daya daga cikin kuyangar ta shiga toilet dinta ta hada mata ruwa Daidai yadda tasan tana amfani dashi kullum ta zuba mata flowers masu kamshin dadi ta wanke mata brush ta sanya mata macline Mai kamshi ta fito tana durkusawa tace Allah ya taimaki Batatuma Angama
Dayar da take tsaye wacce har ta dauko pink towel dan dora mata towel din tayi sannan ta zame mata rigar tareda rumtse idonta ta yadda kada a samu matsala taga wata siffa ta jikinta cewa tayi ya isa don Haka ta juya Neela ta ida daura towel dinta ta shiga toilet din saida ta farayin brush tadan shafa wasu abubuwa na skin care sannan ta shiga bahon da aka hada mata ruwan wanka lumshe idonta tayi tadan fara wasa da ruwan saida ta dauki mintina kafin tayi applying showe gel dinta mai sanyi dadi ta wanke jikinta tass sannan ta fito
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 13&14
A hankali ta fito daga toilet din tana fitar da wani kamshi har tazo tsakiyar dakin da angyara shi tass kamar ba’a taba kwanciya ba vanity table ta zauna tana kallon kanta olive skin dinta sai glowing takeyi ringing din wayarta ne yayi kara wanda tasan ba kowa bace face kilan mahaifiyarta a hankali ta tashi kamar wadda batasan taka kasa saidai ba kasa bace batason takawa tsantsar sarautar dake yawo a jikinta ne bata fuska tayi ganin Mai kiranta kin dauka tayi har ta tsinke karar wayarta ne ta karayin kara dauka tayi ta kanga a kunnenta muryar mai dadi da sautin amo tana ratsa dakin don da tsiwa take maganarta liya wai lapia kike kirana kamar wadda ta ci maki bashi daga dayan Bangaren liya wadda tagama shiryawa tace I just missed my twin sister i decided to check on her ko nayi laifi ne Neela takirata da karfi tace liya da bacin rai a muryarta dariya liya tayi tace wallahi kiyi sauri ki fito ko In kira basai na fada ba kindai san sauran su idan na kirashi Neela tayi sauri ta dafe zuciyarta tace bansan kalar wasannan dariya liya tayi tace Don’t forget to wear green palazzo and white shirt
Tun jiya na sanya akawo maki kayan so kiyi sauri kinsan mu suke jira tunda Mai Martaba da kanshi yace Aikinmu ne Neela da take saurarenta cike da taikaici tace I know I know go to hell Liya I hate you liya dariya tayi tace I love you Neela kashe wayarta tayi . Twin sister dinta kenan she always gets on her Nerves shiryawa tayi cikin kayan da Liya tace akawo mata tun jiya wandon palazzo ne na prada da wata rigar gucci da takalma da scarf
Inner wears ta sanya sannan ta fesa turaruka masu tsananin tsada ta shirya cikin kayan wadanda elegance dinsu sun fito ko ta ina kayan ba karamin kyau sukayi mata ba don dan karamin scarf ta daura kusan duka rabin gashinta ya zuba a baya sai kamshin mai masu dadi takeyi Kallon kanta tayi A madubi sannan taga yadda tayi kyau murmushi tayi wanda ya fito mata da dimples dinta she’s proud of her beauty don masarautar tasu sai kana da kyau za’a san da existance dinka shiyasa subira tayi masu fintinkau saboda tsanin kyau da mulkinta Tunawa kawai da tayi da ita taji zuciyar ta na tashi bloddy Hell tace saboda tasan ta kusa dawowa ba dadewa Neela tace koda yake da da yanzu ba dayaba ,ba zata iya daukar iskancin subira ba zuciyarta ce tace kullum sai kince da da yanzu ba daya ba Amman kullum dayane saboda ba abinda kuke iyawa a gaban yarinya mai jin kan tsiya.
Tsoki tayi ta fito katon parlon ta wanda yake cike da abubuwan more Rayuwa tunda ga floor din parlon da chandeliers din da suke à sama wanda suke bama ko ina wani irin haske wall bracket din kuma masu wani irin designs na royalty masu bala’in kyau fitilu ne ko ta ina haske kam har zai iyayi ma mutum illa saboda parlon baida wani hayaniya sosai don American parlor ne ko royal chairs babu kujerun l-shape designs masu kyau
Tana fitowa kuyangin Dukansu suka dukar da kai kujerar dining daya daga cikin su ta ja mata ta zauna sai kuma daya daga cikinsu tazo da sauri ta zuba mata Irish da liver sauce sai coffee cewa tayi su ta zataci abinci don duk sunyi mata tsaye da sauri kuyangin suka fita waje suna jiranta tagama cin abinci ta take hankalin kwance saidai wayarta na hannunta tana duba wani abu a Instagram kara taji wadda karar ta kusa firgitata,Neela da tasan ba wanda zaiyi hakan sai liya don waye ya isa bama wanda ya isa liya janye plate din Neela tayi ta faracin chips din tace shey you’re here enjoying your breakfast nikuma banci komai ba haba Neela tana maganar tana dafe zuciyarta sannan tace Baki da kirki kallo daya zakayi Neela kasan ta gaji da halin yar Uwarta wadda kammanin su daya don idan zaka tsaya kana kallon su baka isa ka gane daya acikinsu ba,saboda kamanninsu. liya cin cips din take harda mugunta while Neela kallonta kawai takeyi har ta cinye sannan ta dauki coffee din dake gefenta ta shanye dariya tayi tace yanzu naji Daidai tashi mu tafi Neela hararta tayi tace liya daga yau kada ki kara shigo mani chamber dafe zuciyarta tayi sai ta bata fuska tace haba my twin kin sanya an raba mana chamber yanzu kuma so kike in daina shigowa chamber kwata kwata tana dafata tsoki Neela tayi ta ture ta dariya liya tayi tace muje
Tare suka jero suna tafiya Dukansu kuyangin a bayansu wasu kuma a gabansu olive skin dinsu sai shining yake with the help of the sun don Duk bala’inka baka isa kace ga Neela ba ,ko liya saboda tsananin kammannisu moto ci aka bude ma kowace a cikinsu sannan suka shiga baya Daidai inda su Bintu da sauran mutanen da suka zo dasu suka tsaya Bintu da sun kusa awa uku suna jira Dukansu sun gaji ga yunwar da sukeji kamar mi saidai hankalin ta baki daya yana wurin Hurriya da har yanzu bata ganta a wurin ba.
Kallon princesses guda biyu masu kama daya sukeyi su Dukansu kamar kauyawa maza da matan duka kallonsu sukeyi kyau, siga, gayu ,sa’ar rayuwa da mulki kawai suke gani lahaula wala kuwatta illah Billah kawai Bintu take cewa kamar rana haka suka fito don sun haske ko ina don kowa su yake kallo
Kuyangin a gaba da bayansu sukuma a tsakiya Har sukazo inda aka tanadar masu su kadai don su zauna kujerun kansu abin kallone
Su Bintu natsuwa sukai wurin ya dauki wani irin shiru liya da Neela kallon kowa sukeyi da isa kuma da sarauta da idanunsu masu kaifi
Kuyangin kuma duk sun dukar da kansu a tsaye magana liya tayi da kuyangar dake kusa da ita
Ita kuma ta isar da abinda tace ga uban kuyangu da bayi.
Hurriya tun dazu ta tashi lokacin da ta tashi sai taga ba kowa a dakin don haka ta fito ganin kuyangu tayi duk suna ta hidimar su kowa da abinda yakeyi wanka takeson tayi don jikinta duk yayi tsami bata matsa daga inda take ba tsaye saiga Kumurci yazo da ledar kayanta da mamaki yake kallonta Saboda yaga sauran yan uwanta wurin da suke jiran Gimbiya Batatuma da Gimbiya shawata cike da mamaki yace ya akayi Bakije ba banza tayi dashi,Hurriya kamar bada ita yake magana saida ta jima sannan cikin muryar ta Mai tsanani dadi tace bani kayana ta ida maganar tana tsotsar bakinta kadan
Kumurci kallonta yake yana kara tasbihi aranshi yarinyar Allah yayi mata tsananin kyau ga wani uban kwarjini da take dashi ita kam da tasan yadda daurewar fuska keyi mata kyau data rage daurewa tana dariya kilan mazan masarautar hankalin su bazai dauku da kyawunta ba
Kallon kayan jikinta yayi tun na jiya ne wanda yaganta dasu ba hijab ko dankwali babu don duka gashin yayi baya ya sauka a bayanta tsaki Hurriya tayi tace malam ka samu Tv ne?kumurci da yadan daburce cike da borin kunya yace ga kayanki Hurriya kallon kayan tayi sannan tace ka ajiye zan dauka da mamaki yake kallonta don ba’a taba yi mashi irin haka ba Hurriya kam ta rungume hannunta tana kallonshi ido cikin ido kwarjin tayi mashi sosai don haka ya janye idonshi akwai abinda yakeson gaya mata Amman bai iyawa saboda yadda bakinshi yayi mashi nauyi juyawa yayi ya tafi ita kuma Hurriya tayi tsoki ta kalli wata kuyanga sannan tace ina zata tayi wanki Kuyangar sakin baki tayi tana kallonta don sauran kadan ta ruga saboda kyauwunta da gashinta kallonta kuyangar kawai takeyi Hurriya da ranta ya fara baci don ta tsani kallo itama cike da rainin wayau tace wai Tv na Zamar maki ne hajajju Aa baiwar Allah kinada kyau ina jiye maki tsoro ne ga kuma kina da gashi kuma naga shigar kamar bata musulma ba tsoki Hurriya tayi tace akwai wata doka ta sanya kayane? Girgiza mata kai kuyangar Tayi tace ina guje maki karnunkan masarautar nan ne maza da mata
Hurriya tace kinsan fundamental Human right?girgiza kai tayi Hurriya akwai Right of choice yanzu idan naga dama zanyi yawo yadda nakeso kuma ba wanda ya isa yayi depriving right dina so shiga zanyi wadda nikeso hakajju iyakar ki kallo
Kuyangar tace iyakata kallo kuwa shiga kuma duk wadda kika ga dama kiyi zaki basu labari ne a masarautar Qamar Hurriya dage rigarta tayi ta daureta daga gefe shafafen cikin ta wanda sai daukar ido yake sai kuma wata yar sarka ta gold da take like a cibinta ta fito kallon matar tayi tace kafin In fara bada labari ke ya kamata ki fara basu labari tace munafuka magulmaciya kuyangar mutuwar tsaye tayi tana kallon shafaffen cikin Hurriya ko kyaftawa batayi Hurriya tsoki tayi ta saki rigarta tace sakara munafuka ta barta baki sake don kam taji kunya kuyangar sosai Hurriya tayi gaba abinta tabar ta tsaye tambayar wata tayi aiko ba bata lokaci ta rakata har inda suke wanki bata da sabulu don haka ta kalli wadanda suke wanki a wurin wanda suma suke ta kallonta
Tsoki tayi ta kalli wata da take kallonta kamar zata lasheta sabulu ta gani da ruwa a gefenta don haka Hurriya ta zuba ruwa cikin bokitin dake gefen yarinyar ta dauki kayan da tasan zata sanya yau saboda idan tace zata wanke duka zai dauketa lokaci don haka kala daya da zata sanya yanzu ta sanya wandone palazzo da yar top ta duka ta fara wankewa
Hurriya tanajin ana kallonta a jikinta amman tanason ta gama wanki da takeyi saida ta gama wanke kayanta tass ta juyowa tayi ta kalli yarinyar dake mata wani irin kallo Hurriya ruwan kumfa ta diba ta watsa mata nan take ta juya tana soshe kanta Hurriya ruwan dauraya ta zuba taje ta shanya kayanta inda taga ana shanya ta ajiye mata bokitin yarinyar tace mata ki kawo sauran kayan ki in wanke maki naga ke bakuwace Hurriya banza tayi da ita ta jawo wayarta ta sanya waka ta samu wuri ta zauna tana bin wakar tanajin idanu sosai akanta amman ko a jikinta kallon kafarta tayi har dan kumburi tayi ita ba ma’abociya sanya safa bace amman ya zatayi tsaki tayi
Alamun bushewar kayanta da ta ganin ya sanya ta dauki abunta ta tafi. wanka take Bukatar yi don jikinta duk ya dameta tanayin wanka fin sau biyu a rana jikinta har yanzu bai saki ba don tanajin radadi har yanzu a fatarta a waje ta hadu da Habiba
Amman bata ganeta ba Hurriya sarai taganeta zuwa tayi inda Habibar take tace ki samo man ruwan zafi inyi wanka kallonta Habiba kawai takeyi Hurriya shiru tayi tana mamakin yan masarautar basu da aikin yi ne sai kallon mutane tsoki tayi wanda ya sanya Habiba cewa to bari in samo maki a kitchen mi zakiyi dashi? Shiru Hurriya tayi tana kallon Habiba tanason karantar ta saida tagama kare mata kallo sannan tace Bath shiru Habiba tayi alamar bata gane ba tace mata wanka da sauri habiba tabar wurin da niyyar nemo ma Hurriya Ruwan wanka bata wani bata lokaci ba sai gata da ruwan zafi lokacin har tana wurin Hurriya ta cire safarta habiba na dawowa ta mika mata kayan data wanke da safar alamar ta rike mata jiki na rawa habiba ta amsa sannan Hurriya ta shiga inda take tunanin toilet ne da kyar Hurriya take wanka a wurin saboda shegiyar kazantar dake ciki bata wani jima ba don watsa ruwan tayi ko sabulu babu ta maida kayan jikinta ta fito
A inda tabar Habiba ta amshi kayanta sannan ta shiga katon dakin har inda suka kwana itada Bintu kallon katifar tayi taga an gyara tsaff tsaki tayi jin rashin brush din da batayi ba a hankali ta dauki madubi ta bude bakinta tana kallon hakoranta da suke farare jere yan kanana kallon abinda yake gefe da gefen hakoranta tayi golden wanda sai salki yake kurama abun ido tayi tana kallo sai kuma ta rufe bakinta tare da yin tsoki abubuwa da yawa sun dameta ba abinda tazo dashi na yau da kullum na rayuwa da ace bata siye kayan nanba da batasan yazatayi ba tunawa tayi da sauran kudinta aiko ta bude ledar kallon kayan tayi don tana gani tasan anyi mata bincike bata wani damu ba itadai damuwar ta kawai sarkokinta wadanda suke taimaka mata wurin cigaba da rayuwa a hankali tajawosu taga sai sparkling sukeyi zame rigarta tayi ta kalli tatoo din dake zane a jikinta sannan ta kalli zanen sarkar da akayi design da irin tattoo din jikinta a gefe, sai Stone din dake tsakiyar sarkar dake rubuce da H baro baro kallon dayar sarkar tayi zuciyarta na kuna so take tayi kuka amman tasan ba lallai ta iya kukan ba wani wando ta zaro yana da aljihu can kasa kuma daga ciki sannan ta sanya abinta tare da addu’ar kada a dauke mata kara kallon tatoo dinta tayi wanda yake a gefen bayanta jin motsi mutum ya sanya tayi saurin sakin rigar tareda sauke ajiyar zuciya habiba kallonta tayi tana kallon rabin jikinta da ya fito saboda rigar daman buttones gareta to da ta bude rigar kusan har cleavage dinta ana gani kuma bata maida buttons din ba lumshe ido Hurriya tayi Habiba kam tsaye tayi tana kallon jikinta wanda bata taba ganin fata mai sheki da kyalli irin tata ba tana tunanin ko twins albarka.
Hurriya tanajin idonta a jikinta saidai batada energy na magana don duniyar tunanin takeson fadawa abinda ta tsana kenan rayuwarta don tunanin rayuwarta ta baya pure darkness ne wanda bata fatar wani ya tsinci Kanshi a ciki ,ta iya shutting kuma ta iya controlling emotions dinta abinda tasani shine idan har kaine kake da kanka to zaka iya controlling abubuwa da yawa saidai akwai abinda baka iya controlling saboda we’re human beings kuma Humans are weak.
Please comment share and like
Love you all
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 15&16
Bude idanunta masu kyau tayi sannan ta sauke su à habiba da take binta da wani irin lustful look Hurriya zuba mata idonta masu kaifi da kwarjini tayi da sauri Habiba ta gyara tsayuwarta sannan tace kina bukatar wani Abu a hankali Hurriya tace comb da sauri Habiba ta kawo mata comb kallon dogon gashinta takeyi wanda kwata kwata bai kama dana yan Nigeria shiryawa tayi cikin wani brown palazzo sai red riga gashinta sakwa sakwa ta daureshi Habiba na kallonta kamar zata cinye ta so take ta taba gashin taji idan nata ne Amman tsoro ya hanata takalminta ta sanya ta fita batasan inda wurin yake ba saida ta tambayi wani ya nuna mata hanyar da zata bi duk inda ta wuce kallonta akeyi tanaji a jikinta kuma tasan ana kallonta saidai ta saba ko a garinsu haka akeyi mata irin wannan kallon tafiyar ma taki karewa saboda nisan tafiyar wurin.
Uban bayi ya kirga su Amman ba mutum daya acikin mata kuma ance masu su talatin ne mamaki sosai ya kamashi don haka ya nufi inda twins suke Allah ya taimaki shawata Allah ya kara maki nasara Babu mutum Daya a cikin mata kuma su talatin ne liya da mamaki take kallonshi don ba’a taba samun irin haka ba kallon neela tayi saidai hankalin Neela kwata kwata bai tare da ita yana wani saiti daban don haka ba tare da bata lokaci ba ta kalli saitin da Neela take kallo inda Hurriya take tafiya kamar she own half of the world yadda tafiyarta take cike da izza liya da mamaki take kallon Hurriya kowa a wurin hankalin shi ya koma kanta fuskar ta fayau babu komai amman wani irin tsantsan kyau da annuri ne take fiddawa gashin kanta wanda bata daure ba duk ya zubo mata kowa bude baki yayi yana kallonta da mamaki don karime kasa shiru tayi tace uwale kamar Hurriya nike gani daga mata kai uwale tayi tace itace fa karime sanya hannunta tayi a baki tana cizon yatsa
Hurriya ba inda ta tsaya sai a saitin Bintu banda faduwar gaba ba abinda bintu keji .
Neela kallonta takeyi da wani irin mamakin gaske don tundaga kayan jikinta take kallo sannan tunda ga sama har kasa gashin kanta kam ko subira albarka bare ita daure fuska tayi ta murtuketa kamar Allah ya aikota ta taho kuyangin nabin bayanta cikin jiji da kai da isa da sarauta Neela ke tafiya har tazo inda Hurriya take tsaye kallon Hurriya tayi tundaga saman ta har kasanta gabanta ne ya shiga faduwa don tunda take bata taba ganin Epitome of beauty irinta ba the girl is almost perfect with nothing left for people to criticize not almost perfect ma she’s more than perfect kallon cramel skin dinta wanda yake glowing irin na wanda sukaji hutu. hutun ma anihin hutu ba muna hutu ba tayi wannan yarinya Anya ba cikinsu akaso ayita ba aka samu kuskure shine abinda tace kawai a ranta kallon cikakken gashinta takeyi wanda yake da yawa wanda daureshi sakwa sakwa amman dan ziri biyu na gaban gashinta sun dan sauko irin shigar da tayi bata da bambamci da irin tasu shigar Don bambamcin kayan
nasu are damn expensive while her own is cheap cikin zuciyarta tace she’s beautiful she adjusted her self trying her very best to look normal kara matsowa tayi inda Hurriya take tayi ke tace cikin tsadaddiyar muryarta shiru wurin ya dauka kusan kowa ya juyo wurin domin bama idonshi abinci liya itama kallon ikon Allah takeyi daga inda take tsaye
Neela magana ta karayi ma Hurriya cike da tsantsar mulki kuma da sarauta Hurriya dagowa tayi ta zuba ma Neela idanun ta masu matukar kyau da kwarjini
Subahanallah kawai Neela tace don side view dinta ta gani bataga complète face dinta ba sai yanzu da ta dago tabb she wishes to be her friend because the girl is fucking beautiful saidai matsalar they are not in the same classes she’s far better than her kilan idan har tace tayi friendship da ita it will be a great insult to her a cikin masarautar kamar ta Neela baiwa ta zama friend dinta kai not in this life maybe in the next life
Hurriya itama kallon ta take tana analyzing dinta don taki janye idonta daga cikin na Neela itama Neela hakan take a wurinta a cikin masu aikin da kuyangi da bayi ba wanda ya taba bata irin wannan kallon da Hurriya take bata saboda kwarjinin ta and she’s ahead of them they’re far different so they have to always stared at the flour whenever she’s around them nobody will dared to stared at her but this is a different story because Hurriya is not looking away or bowing her head kutt she’s giving her more like a deadful glared cikin isa da mulki tace Who are you Hurriya ta ta dan cije lebenta wanda kamar daman sararta ce Bintu ta rinka kallonta da pleading eyes dinta tana rokonta ta ido kada ta jawo ma kanta matsala ta taimaka
Cikin muryarta mai zaki da dadin gaske da accent dinta na Ethiopia tace Hurriya Faisait Hamood she wasn’t expecting her answer to be like irin amsar da tabata she was surprised because tasan ma aikatan su basu wani jin turanci maybe kilan tayi ayyuka gidajen masu kudi shiyasa ta tsinci irin kalmomin turanci irin haka harda kayan dake jikinta kila ma kwance ne
Cikin jiji dakai tace waye ya baki izinin wannan shigar da kikayi da gadara Neela ke maganar Liya na daga gefe tana kallon ikon Allah Hurriya shiru tayi tana kallon Kyakyawar fuskar Neela wadda batada bambamci data liya saboda tsantsar kamarsu
Neela ta fara hasala Sosai don taga yarinyar tana Neman raina ma mutane wayau kuyangarta tace ta kira mata shaho aiko da sauri aka kirashi jikinshi na bari yazo yana durkusawa kallonshi tayi ta nuna mashi Hurriya aiko a take ya gane abinda take nufi wanda daman kamar jira yake
Cikin tsantsar mugunta ya zuba mata bulala daya wadda saura kadan ta saki fitsari liya ce tazo da sauri tayi stopping dinshi tace kada ya kara dukanta wurin shiru ya dauka Neela na kallon Liya
Hurriya kam kallo daya idan kayi mata zakasan bulalar ta shigeta saidai kwata babu alamun nadama sai wasu flames ma dake fitowa daga cikin idonta Hurriya ta bama liya tausayi sosai sadai batasan tayi Abu makamancin da zai iya zamowa disgi ga yar uwarta don haka ta janye Neela suka koma inda suke kuyangin su na rufa masu baya.
Rarraba masu aiki aka farayi Har akazo kan Bintu ita Bintu ba komai aka bata ba sai mai aikin sashen Neela bayan angama da Bintu uban bayi ya karkato kan Hurriya girgiza kai yayi kadan sannan ya fara lissafo mata aiyukan da zatayi masu matukar wahala sashe biyu zatayi aiki sai kuma aikin bayi wanda wanda bayi ke irin wannan aikin saboda tsananin wahalar aikin to hadashi aka bata har aka gama lissafo mata aikin batace kala ba aikin ne masu azabar wahala aka jero mata don ko yadda uban bayin ke karanta mata ayyukan kadai ya isa kasan da gayya aka bata aikin
Bayan angama raba ma kowa aiki saida suka jira liya da Neela suka bar wurin sannan suka tafi
Uniform aka basu kusan kowa da kalar nashi uniform din don kusan kowa da matsayin shi itadai Hurriya Green and Red aka bata komawa tayi ta shirya cikin uniform din sannan ta linke kayanta ta maidasu a leda baya taje inda akeyin lodin wankin princes da princess da yaran masarautar mata da mazane a wurin banda tikar wanki ba abinda sukeyi sunayi ana zubo masu wasu kayan sai kara tila masu kayan ake ga alama ba wani Hutu daman tattare dasu Uwar bayi ta kalli Hurriya tace gashinan ki jona shiru Hurriya tayi Uwar bayi da take tsaye tana jiran amsa daga gareta jin shirun da yayi yawa ne ya sanya ta juyowa saidai mi wayam babu Hurriya babu alamunta
Hurriya har ta isa inda akeyin wankin in a polite way tayi masu magana tare da tambayarsu abinda zatayi ba bata lokaci aka nuna mata wasu kallon tsantsar hallitar kyau da gashinta sukeyi don kowa a wurin ma ba kallon musulma yake mata ba andwho cares tunda basu take bauta mawa ba kuma mutane are good in making judgement sai suyi tayi
Wanki takeyi tukuru don tanayin wanki don ta saba tunda ita takeyi ma kanta ma wanki she’s not lazy because life had taught her alot ko a garinsu duk aikin da tasan yana bada kudi to tanayinshi in order for her to make a living don haka ba wata matsala bace sosai a wurin ta don haka ta cigaba da wanki baji ba gani
Tafiya takeyi wadda kallo daya zakayi mata kasan cewar ta gaji don yanayin tafiyar ta ne zai tabbatar maka don tunda suka fara wankin babu wata magana wato a huta don kamar jakkai haka sukayita yin sukola sai yanzu dasuka gama
Cigaba tayi da tafiyar saidai dakin kamar an kara mashi nisa don taki kawo dakin har yanzu saida ta kara doguwar tafiya mai tsawo sannan ta iso dakin
Bata wani bata lokaci ba ta dauko kayanta da ta bari a wurin habiba ta nufi sabon dakin da aka nuna mata dazu a matsayin nasu
Dakin babba ne saidai bai kai wancan girma ba don wannan zai iya cin mutum ashirin saitin katifar ta ajiye kayanta duk da tanajin kiran sallah magrib da akeyi bai hanata kwanciya ba wani dogon Bacci ya dauketa Mai cike da gajiya tanaji cikin bacci uwar bayi tana mata magana akan zuwa dayan shashen da take aiki domin hada ma hakimi abinci tsoki tayi ta juya ta cigaba da baccin ta bata tashi ba sai karfe taran dare
Hurriya hamma tayi tana kara gyara dogon gashinta wanda yadan sauko mata tsoki tayi don ba abinda take bukata irin wanka da ruwan zafi a yanzu saidai batasan inda zata samu ruwan zafi don haka ta fito ko ina tarr kamar ba dare ba tayi alwalar ta cikin dakin ta shigo sannan ta sanya doguwar hijab tayi sallah
Bayan tagama rama sallolinta ta duba cikin kayanta ta zaro riga wadda batada hayaniya yar karama wadda ko cinyoyinta bata rufe ba ta sanya
Kwanciya tayi taja hijab dinta ta rufe jikinta yunwa takeji amman bazata iyacin tuwo ba a takure take sosai don tariga ta saba da abinda takeso shi takeci tanason freedom rayuwarta amman kwata kwata tasan dole zatayi hakuri da wasu abubuwan.
Manya matane su uku sai Hansa’u da barira sune cikon biyu haka suka shigo dakin su biyar suna shakiyanci suna dariya barira ce leader ga dukkan alamu yau zamusha dadi inji Hansa’u akwai sabbin zuwa ga dukkan alamu Barira ta kallesu tace saina fara zaba kafin ku zaba gaskiya Hansa’u tace angama shugaba tana dariya suwaiba ce tace ni kinsan nafison hidimar jakunna kafin dayan abun
biyun ne sukayi dariya sukace muma sai mun fara shan dadi kafin muyi rabon jakkuna dariya suka kyalkyace da ita suka zauna inda ya zamar masu kamar chamber su a dakin Hansa’u ce ta bude leda ta fiddo rake mai zaki tanasha murmushi tayi tace kai kai wannan rake akwai zaki Allah yasa yanmatan dakinan suyi zakin wannan raken dariya suka kwashe da ita
Wasila ce tace kinga nayi nan don haka duk inda taga jakunna indai na sabbin zuwa ne saida tadaukosu
Hansa’u da suwaiba sai Aliya suka tashi sukazo inda su karime suke kwance da saraunsu suna tarkato yanmatan da suke wasu kwance wasu zaune
Dukansu saida suka zaba suka darje acikin yanmatan sannan sukazo tsakiyar dakin
Hansa’u da bata iya jira don haka ta fara zame kaya ba kunya ba tsoron Allah taja mardiyya dariya suka fara suna shewa mardiya kam abinda Hansa’u ta farayi mata bata taba jin irin shi ba don haka ta fasa wani irin kuka manya manya matan da suke tsaye suka gaura mata mari mai shiga jiki ba wadda bata gauwara mata mari acikinsu suna dariya
Banda salâti ba abinda mardiya keyi Don Hansa’u ta fara janye mata suturar ta
Barira wadda take shugaba acikin su ta taso tazo wurin tana kallon yan matan uwale tayi ma alama da tazo uwale banda kyarma ba abinda takeyi nan ta fara ja da baya wata irin muguwar faduwa kasa tayi wadda suwaiba ta sanya kafa ta shureta ta fadi kasa tana dafe goshi kuka uwale takeyi mai taba zuciya tana dafe goshin ta Barira tsoki tayi dallah sakara taso kema ai dadi zakiji bamu kadai zamuj dadin ba kuma da kun saba zakuzo kuna nema dakanku kinzo kina ma mutane kuka
Wasila tayi wata shegiyar dariya sannan tazo ta take ma uwale hannu tace shegiya daga gani ma zaki yi jaraba ta kara halba ta tana tsirta mata miyau Barira tace ku shigo man da ita
Suwaiba da wasila suka kamata suka kaita har makwanci Barira don ita har wani labule gareta wanda baka iya kallon komai dake cikin wurin
Uwale sam taki bamaBarira hadin kai don cizo da tsunkuli ba wanda batayi mata da kyar Barira ta barka mata riga wani irin cizo uwale ta kaimata a cinya mai dan banza zafi aiko barira ta hankadeta uwale kam ta rugo a guje tana hawaye Barira sanya kayanta tayi ta fito itama tana bata fuska alamar taci wuya
Kallonta su Mardiya da suwaiba da wasila sukayi sukace lafiya kallon uwale da take sharbar kuka tayi tace gatanan ta kusa illata ni don haka kuyi maganinta
Dariya sukayi a tare ita kuma ta samu wuri ta zauna
Dukan uwale suka farayi wanda kamar daman abinda ya kawosu duniyar kenan don basu ji basu gani hada halbinta sukeyi cike da mugunta suna wata yar iskar dariya ita kuma uwale kuka takeyi mai ban tausayi da taba zuciya
Mutane na kallo Amman waye ya isa yace zaiyi magana don daurin gindi suka samu wurin manya ma’aikatan masarautar don sai suyi maka dukan tsiya kuma su kira mararsa imanin samarinsu suma su dasa
Su Karime kam kyarma kawai sukeyi suna kallon ikon Allah wasu kam acikin su ma kuka sukeyi
Hurriya baccin gajiya takeyi saida bata da nauyin bacci tun dazu takejin kuka da hayaniya saidai bata maida hankali ba ta koma baccin ta amman hayaniyar da kukan damunta sukeyi don duk sai juye juye takeyi cikin baccin tsoki tayi ta janye hijab din dake jikinta ta tashi takalminta kawai ta sanya ta fito ba inda ta tsaya sai wurin su wasila da su suwaiba wanda banda bugun uwale ba abinda sukeyi
Hannunta duka biyun a bayanta sai gashinta da yayi loosing tie saboda bata daureshi da kyau ba
Kamar hadin baki dukansu suka dago suna kallonta itama kallonsu takeyi wanda da alama idanunta basu gaji da bacci ba
Kallon uwale Hurriya tayi wadda take durkushe tana kuka wasila ce ta kara kai mata mari sannan ta dago tana kallon Hurriya tace ke kuma fa babu wanda tace ma kala
Hurriya Dukansu kallon yadda suke binta da kallo takeyi kamar wasu hungry lions
Barira ce ta taho tana karairaya sannan ta kalli Hurriya a izgilance tace wa kike nema tanabin long slender legs dinta wanda rigar ta ko cinya bata gama rufe mata ba ,her legs shine like a sparkling water don wani salki sukeyi na tsantsar kyau hutu da jin dadi da duk suka bayyyana
Cikin isa da kuma rainin wayau Hurriya tace Are you lesbians sai kuma tayi licking gefen bakinta taciji lebenta tace kuna neman mata ne ?kowa acikin zuciyar shi ba wanda baya muradin ta saboda basu taba ganin lafiyaryar mace mai kyau dinta ba don ko gimbiya subira albarka
Barira ce ta taho cike da iyayi da kaudi tace kina son ki tabbatar ne ?sannan ta daga kai tace ma Hurriya Eh muna neman mata sannan ta lashe bakinta tace bari kingani matsowa tayi inda Hurriya take tsaye wadda kyakyawar fuskarta take blank she looks fierce and scary don da Barira tayi gigin kallon idonta da ta shiga taitayinta
Hurriya kallon Barira takeyi wadda har tazo kusa da ita da alama kuma tabata take so tayi don har ta dora hannunta saman gashinta tana lumshe ido bude idonta tayi tar akan na Hurriya sai a lokacin taga yanayin fuskarta mai firgitawa sharewa tayi tana kokarin kai hannunta a cinyar Hurriya saidai saukar zazzafan tuwo da miyar da taji a fuskar tane ya sanya ta sakin ihun azaba don ta tabbata fuskarta ta kone wani irin kuka takeyi mai ban tausayi da taba zuciya
Kowa kallon Hurriya da ta konata da tuwo a fuskarta yakeyi babu alamun ko tsoro ko nadama a fuskar Hurriya don da alama inda akwai saura to kilan Sai ta watsa mata a ko ina na jikin Barira
Wasila ce ta taso da wani irin zafin nama da alama zata kaima Hurriya mari da sauri Hurriya ta kauce sannan ta kalleta ido cikin ido tace i dare you to slap me with your filthy hand licking lips dinta tayi sannan tace da ni Hurriya faisait Hamood na sanya an yaken yatsunki guda biyar
And duk randa kika kwatanta yin haka I promise this ta nuna mata alamun sai an yanke hannun sannan ta kallesu wanda banda kallonta ba abinda sukeyi don ko daga idonka zai tabbatar maka da duk abinda tace zatayi zata iya
Bintu hannunta rike da bakinta don mamakin yadda Hurriya ta kona Barira da tuwon da ta kawo mata yanzu saboda tasan duk yau bataci komai ba kuma ko a jikinta don yadda take acting kamar ba abinda tayi don ta san Hurriya zata iya yin fin haka indai maganar wani zai taba mata jikine
daman Bintu tunanin Hurriyar bataci abinci ba don haka tace bari ta kawo mata tuwon tare da fatan Allah ya sanya taci sai ga abinda ya faru da tuwon da Kuma Barira
Hurriya zuwa tayi ta kwanta ta mike kafafunta ta lumshe idanunta Bintu tarugo tazo tace Hurriya shiru Hurriya tayi Bintu ta kiranta yafi a kirga Amman shiru karshe ma saidai ganin bacci ya dauke tayi don alamar numfashin ta ya canza ya koma na mai bacci
🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 17&18
Karfe 6:10 goma Hurriya ta tashi
saboda ayyukan da take dasu yau murza idanunta tayi sannan tayi mika ba addu’a abakinta ba komai bata dauki komai ba don haka taje babban toilet dinsu ta kama ruwa sannan tazo tayi Alwala Tayi sallah wanka takeso tayi saboda tsamin jikin da takeji duk batajin dadi saboda Rashin cikakken wanka data sabayi don ta saba kafin tazo masarautar nan sai tayi wanka sau uku a rana kuma da ruwan zafi don batasan ruwan sanyi indai wurin wanka ne saboda ciwonta tsoki taja ba tare da ta cire hijab din sallahrba ta nufi babban kitchen
Aiki akeyi a kitchen din sosai shigowa tayi wata yar babbar mace ta gani a gaban tukunya ruwan sai tafasa yake Daidai saitin matar Hurriya ta tsaya saida tagama kallonta don kamar bazatayi magana ba cikin miskilanci tace ruwa zafi zaki bani
Dagowa inna hanne tayi don ganin isassar don batayi mata sallama ba sannan bata gaisheta ba sai ruwa zaki bani cikin tsiwa ta dago domin tsiyaya rashin mutunci saidai ganin kudin da Hurriya take mika mata datayi ya sanya tayi shiru ta fara washe baki tana toh toh miye zakiyi da ruwa yar albarka kamar don dole tace wanka amshe dari biyun inna hanne tayi tace samo bukiti in zuba maki kinji Hurriya juyawa tayi ba bata lokaci sai gata da bucket nan inna hanne ta fara zuba mata ruwan zafi masu yawan gaske har saida Hurriya tace ya isa sannan ta daina zuba ruwan
Toilet ta shiga tayi lafiyayyen wankan ta wanda tasan zataji dadin jikinta Sosai a hankali ta shafa bayanta inda zanen tatoo ke kwance a bayanta wurin saitin wuyanta lumshe idonta tayi ta cizi lebenta masu kyaun gaske sannan ta fito tana tafiya ne a hankali kuma duk da safiya ce sosai tanajin yadda ake nunata
Tana zuwa ta iske Bintu a zaune kamar bacci ma takeyi Don haka Hurriya ta shirya tsaff cikin uniform dinta wanda ta samu ta wanke jiya da kyar wadanda sukayi mata wani irin kyau na musamman fuskarta sai fidda annuri takeyi sanyi da takeji na safiya wanda yake shiga kanta ya sanya ta bude kayanta domin neman Hula Aiko ba tare data sha wahala ba sai gashi ta samu hula mai kyau ash colour hular irin ta sanyi ce duk a wurin asabe ta siye su
Bata fuska tayi don tana dadewa bata daura ma gashinta wani Abu ba don sai idan abun ya kadota sosai .shine take rufe gashinta don a shekara baifi ta rufe gashinta ba sau hudu akwai lokacin da har shekarar ta kare bata damu da rufe gashinta ba idan ba wurin sallah ba
Cikin kyankyami take rike da hular da sam bata wanke ta ba don duk kayan gwanjon duk hasken su sai ta sanya hannunta ta wanke su tas kafin ta sanya.
Warware gashinta tayi wanda ya zubo mata har bayanta sosai don ma akai akai take rage gashin kanta da batasan yadda zai rinka takura mata ba kuma data rage nan da nan yake fitowa har yafi wanda ta rage din tsawo da cika da yawa
Taba gashin tayi sannan ta dan shinshina ko yana wari kamshin coconut oil din da taji ya sanya ta dan saki ajiyar zuciya
Daure gashinta tayi Sosai yadda duk bala’inka baka iya hango tukar don ta linketa ta sanya ta cikin gashin yadda ba mai iya gane yawan gashin ko tsawonshi ko yawanshi
Bintu da ta bude idonta masu kyau ta kalli Hurriya tace kindawo daga mata kai Hurriya tayi tanabin ko ina na jikinta da kallo alamar rama kuma da yar damuwa tattare da ita
Ganin Hurriya nabin ta da kallon minene matsalar ki ya sanya ta washe baki yan hakoranta suka fito tace Hurriya jiya nazo in ganki na kawo maki abinci Amman Saita kasa ida maganar alamar kamar tana kuka ta hade kafafunta da gwiwarta Hurriya ta duko tace Bintu miye ya faru waye ya taba ki fadamin shi. Daga muryar ta zakaji alamar kulawa duk da yadda take kokarin boye emotions a cikin maganarta ,duk wani mai tsantsar fahimta zai iya fahimtar damuwa a maganar ta Amman a yadda take maganar kadai sai mutum yace bata damu ba
Hurriya kara matsowa tayi kusa da Bintu kamar tanajin tsoronta tana tambayar wai lafiyar ki kuwa ki fadamani manah itama maganar ta kubce mata da alamun shagwaba Wata irin kyakyawar runguma Bintu tayi mata sannan ta fashe da matsinacin kuka Hurriya dan ture ta tayi ta zame jikinta Bintu dagowa tayi ta kalleta da idanun ta da sukayi jajir ta kalli Hurriya da take bata fuska kamar kashi ya tabata kuka ta kara fashewa dashi Hurriya dafe kanta tayi tace ki daina kuka ki fadamin abinda ya faru shiru Bintu tayi kamar daman abinda ta jira ta fada mata kenan don haka tayi shiru kafin a hankali tace cikin muryarta mai rauni tace nayi kewar ummanah Hurriya inajin tsoro tana maganar hawaye na zubo mata shiru tayi sannan ta goge hawayenta tana kallon Hurriya data tsura mata ido tashi tayi zata mike Hurriya tace Bintu yadda ta fadi sunanta saida ya sanya tsigar jikin Bintu ta tashi don da wata irin kulawa ta fadi sunan Bintu kallonta takeyi da mamaki tace Hurriya tana zare ido dan murmushi Hurriya tayi kadan wanda duka dimples dinta saida suka lotsa sakin baki Bintu tayi tana kallonta don tunda take a duniya bata taba ganin wanda murmushi yayi ma kyau ba irin Hurriya itakanta har goosebumps saida taji itada take ma mace kenan inaga ta fito tana murmushi bama dariya ba murmushi kawai tabb akwai matsala don ta tabatta duk inda ta matsa mazane zasu rinka binta kamar sleeves Dogs inaga tayi dariya ita kanta Bintu tunda take bata taba ganin mace mai kyaun Hurriya babu ta inda Allah ya rageta a fuskarta ko jikinta
Gyaran murya Tayi ta kalli Hurriya da kamar tana cikin good mood a hankali Hurriya cikin muryar ta mai dadi da sanyi tace Mai kike tunani Bintu ke nake tunani yar dariya tayi wadda har saida hakoranta saida suka fito shiru Bintu tayi tana kallon ratsin gold din dake tsakankanin hakoranta wanda bata taba lura dasu ba sai yau tunda take da Hurriya idonta har wani sparkling sukeyi dimples dinta kam duk sun lotsa Bintu cewa tayi Hurriya daman kina dariya dan gyara fuskarta Hurriya tayi ta koma yadda take da sannan ta juya ba tare da tace komai ba Bintu kiran sunanta tayi Hurriya tsayawa tayi bata juya ba kuma batayi gaba ba Bintu matsowa tayi cikin rauni da sanyi tace Hurriya ki zama yar uwata wadda zan rinka fuskantar ta da matsala ako dayaushe don Allah kada ki Rabu dani ko ki juya min baya ni ko baza kiyi fira dani ba nizan yi maki fira .
Inajin kadaici sosai wanda kwata kwata banda kwanciyar hankali ke kadai nike gani inji dama dama a raina don ni kallon yar uwa nike maki cikin muryar ta mai dadi Hurriya tace Bintu kin zama kanwata daga yau Bintu bata fuska tayi ta bayan Hurriya tace na girme ki Hurriya shiru tayi batace komai ba ta fita don tasan kilan ta makara dage kafadarta tayi sannan tace who cares
Tana tafiya taji ana nunata saidai ta saba sosai safiya ce ga kuma sanyin da akeyi mai shiga kasusuwa Hurriya idan ka kalleta zakayi tunanin batajin sanyin don ba dankwali A kanta amman akwai hula a hannunta tafiya tayi Mai nisa kafin tazo bangaren daza tayi aiki Ma’aikata ne ta gani tun abakin kofar chamber sunata aikinsu a hankali ta shiga bangaren kallon parlon takeyi wanda komai na ciki ya burgeta tun daga ceiling din dakin har zuwa painting komai fari ne kallon chandeliers din dasuke jere a saman popn tayi wanda yake bada wani irin mahaukacin haske wanda yake neman tarwatse mata idanu kujerun parlon royals ne masu matukar tsada kuma very light saboda at first glance ba Lallai ka kirasu royal ba fa sai ka san furnitures Sosai zaka iya ganewa kallon dogayen labulen da aka jerasu tayi komai na parlon is rich and elegant carpet din wanda ya cinye katon parlon da kusan set of chairs guda hudu kuma dukan su luxury royal chairs ne
Sai dining table dake cin kujeru guda shidda saida ta gama kallon komai magana taji daga bayanta don haka tajuya yar budurwa wadda bazata wuce sa’arta ce tagani sai kallonta takeyi kamar zata cinye ta baiwar Allah Amman ke ba yar najeriya bace shiru Hurriya tayi fuskar ta a hade bata ko amsa mata ba gyara tsayuwarta tayi sannan tayi murmushi tace hala kece sabuwar ma’aikaciya to muje In kaiki wurin mama rabi nan ma Hurriya batace mata komai ba don ganin irin kaudinta ta katon kitchen suka bi wanda Hurriya ke biye da ita har suka zo inda mama RaBI take
Matar yar dattijuwa ce tsaye tana kallon sabbin ma’aikatan da aka kawo
Zubaida tace mama rabi ga sabuwar Mai aikin da aka kawo saitin kunnen mama rabi tazo tayi mata rada tace kinga kyaunta sai tayi dariya tace akwai kallo a masarautar nan Amman fa shegiyat akwai miskilanci kamar jikar Qamar wata dariyar tayi tace itada tazo masarautar Qamar ai komai ta ajiyeshi tana dariya mai cike da zallar munafunci da makirci kuma da mugunta
Duk abinda suke cewa Hurriya tana jinsu saidai basuyi tunanin don babu ko alamar hakan a fuskarta mama rabi tazo Daidai saitin Hurriya saida ta kare mata kallo sannan ta washe baki tace sannu yan mata Hurriya daga mata kai kawai tayi
Mama RaBI abun ya bata haushi Amman da yake yar duniya ce sai ta share ba bata lokaci ta fara lissafo mata dokikin Imad shiru tayi tana saurare har tagama Hurriya batace kala ba Amman ga dukkan alamu ta dauka
Mama RaBI ta kalleta tace ki gwada mata hanyar dakin zubaida tace muje ko tare suka koma itada zubaida har zuwa inda zai sada ka da dayan parlonshi kallon Hurriya zubaida tayi tace ki shiga idan kika wuce parlo na biyu zakiga dakinda yayi hanyar da tayi kasa Tohm sai ki shiga kasa din da kin wuce parlon to dakin dake kallon ki sai daki na hagu da na dama daga mata kai kawai Hurriya tayi sannan ta bude kofa ta shiga parlon wanda yake dauke da set of turkey chairs parlon ya hadu don har batasan wanda yafi kyau tsakanin na farko dana biyu ba
Bata tsaya kallon parlon ba don ganin lokacinta ya tafi don ayyuka ne gareta da yawa don haka ta hau steps din da zasu kaita dakin kasa wanda kamar underground
Parlon da tagani akasa saida kam ta tsaya ta gama kallo da yabonshi saboda komai da aka sanya a parlon zata iya cewa abinda ta fiso kenan kamar ita aka tambaya mi takeso ta fadi aka bi zabinta
Cikin tafiyar ta mai kama da catwalk ta shiga dakin kallon dakin tayi wanda yake da matukar burgewa ba bata lokaci ta shiga gyarawa da sauri take komai bayan tagama ne ta shiga toilet din ta wanke komai tass
Sannan ta fito ta kara shiga dayan dakin shima ta gyara komai da sauri takeyinshi kuma cikin rashin ha’inci don ko ina tayi mashi kalkal
Sannan ta shiga dakin karshe tana bude kofar ta lumshe idonta ta dan tsotsi bakinta bude idonta tayi tana kallon ko ina banda kamshin turaren wuta ba abinda mini falon yakeyi
Shiga tayi ta fara kakabe komai ba wani bata lokaci tagama sannan tayi mopping ta goge ko ina tass
A hankali ta nufi kofar dakin da take kallonta ta bude kallon Komi take na dakin wanda yake fari subahanallah dakin ya hadu kowaye yake da dakin ta jinjina ma fashion sense dinshi Komi is extremely expensive and superb a dakin tun daga wall decors din dake a bango dakin hadaddun paintings ne da canvas masu matukar kyau da tsada wanda ko wani zane is worthing millions ba wani tarkace Sosai a dakin wanda alama ta nuna mata mai dakin bai son hayaniya
Tsarin dakin ya taimaka mata wurin reading personality din young master dinta
Kallon katon gadon tayi wanda bedsheets din da duvet din duka farare ne saidai daga inda take tana hangen irin laushin da Eskimon yake badawa
Lura tayi da Akwai mutum dukunkune cikin duvet din don haka ta shiga toilet dinshi banda kamshi ba abinda yakeyi ta hada komai na wankin ta wankeshi kalkal .
Kallon gadon Hurriya tayi tunanin yadda zata gyara wurin take cikin ranta tace why not ki tadashi idan kingama sai ya cigaba da baccin shi
A hankali ta nufo saman gadon tunani yadda zata tadashi takeyi saboda batasan sunanshi ba vanity table ta kalla wanda ta hango brush na gashi dauko brush din tayi tazo Daidai saitin kanshi ta dan janye bargon inda taci karo da fuskar Imad yana baccin shi peacefully he looks so cute and handsome kallo daya tayi mashi tasan dan gayune don ko sumar kanshi wadda take acike irin ta gayu tasha gyara don banda salki ba abinda takeyi kallon dogon hancin shi tayi zuwa bakinshi wanda yake pink dan lumshe ido tayi sannan ta bude .
brush din dake hannunta ta sanya a saman gashin kanshi tana heyy ka tashi
bata fuska yayi sannan ya kara gyara kwanciya
Hurriya kam da taga alamar ma dadi yakeji don haka ta maida brush din saitin kunnenshi tana mashi kamar tafiyar tsutsa
Imad cikin baccin shi mai dadi yaji alamar Abu na yawo a kunnenshi babu abinda yazo mashi arai irin kyankyaso don shine abinda yafi tsana da tsoro a duniya a mugun firgice ya tashi yana cewa innalillahi wa’ina ilaihi raji’un ya diro yana tsalle yana kallon jikinshi yana dube dube kamar sabon shigar hauka
Hurriya kam saura kadan tayi Dariya Amman ta dake yadda ta saba tayi gyaran murya don kwatakwata bai lura da ita ba zaro fararen idanunshi yayi yana kallonta sannan yace who are you Do you want to die banza tayi dashi tamkar yana magana da dutse
Don har ta fara cire pillows din domin gyara gadon
Ammar da tun dazu ya shigo domin neman tsokana wurin twin brother dinshi Amman wata marar Sa’a ta riga shi he’s enjoying their little drama saidai yana mamakin irin zeal din yarinya how dared she play with a prince dariya ke cinshi Amman yaki barin dariyar tafito saida ya gama kallon komai
Amman ya gama jin tausayin ko wacece don yasan halin Imad Sarai don halinsu su uku to daban yake da subira da Imad kuma da Khalifa Qamar to Khalifa ai ba’a sanya shi ma a layi don nashi abun is too much kuma ya dade baya palace din so he can’t say much about him don he can’t remember when last ya ganshi to daman idan anaso Ayi maka hukunci a palace din to dama either akaika chamber din subira ko kuma Imad chamber su biyu nan suna da matsaloli
Hurriya kam banza tayi dashi ta cigaba da aikinta don a wurin ta baida amsa ita dama she hate useless talks ta gama gyara gadon tass Imad da yake tsaye yana fuming don bacin ran da yake ciki zai iya karyata idan har batai wasa ba ba’a taba yi mashi irin abinda akayi mashi ba yau tun kam daga yarintar shi
Ta shigo mashi daki ba tare da izininshi ba sannan ta tadashi daga baccin da yake mai matukar dadi don ta raina mashi wayau wai kuma da brush ta tadashi sannan bata gaishe shi ba and again yana mata magana tayi banza dashi ko bata iya turanci ba bata iya durkusawa ta fara bashi hakuri tana kuka tana rike mashi kafa
Amman shine takeyin kamar ma batasan dashi a wurin ba gaskiya yarinyar nan must have a dead wish because she’s playing with fire
Wata tsawa ya buga mata yace ke bakiji ana maki magana ba ko kurma ce Hurriya a hankali ta juyo ta zuba mashi idanunta masu matukar kyau da kaifi kallonta yake tundaga gashin kanta da yake a bude har zuwa fuskarta mai matukar kyau da annuri yace Do you want to die sai kuma ya tuna ba Lallai tanajin turanci ba magana yafaryi mata cikin muryarshi mai dadi kuma da dadin sauraro yace wacece ke? Dan tsotsar bakinta tayi sannan tace Hurriya Faisait Hamood sabuwar mai aikin ka
Kin aikata laifuka don haka zaki amshi hukunci da ya kamata yana maganar with arrogance ne and full of himself
Hurriya kallonshi take ba tare da ko kyaftawa ba tunda yake babu mai aikin da taba kallonshi ido cikin ido kowa acikinsu yana shakkar shi Amman banda Hurriya wadda take kallonshi kamar yadda Ammar ke kallonshi cikin muryar ta mai dadi da sanyi sai kuma maganar ta wanda yake nuna cewar tana da wani yare na daban tace babu inda nayi laifi tunda nazo a dokokin ance ba ruwana dakai kuma na kiyaye kuma ance bakasan hayaniya kuma banyi ihu ba ance idan kana Bacci kada in tadaka da magana kuma banyi magana nayi amfani da wancan abune wurin tada ka
Sharrudan da aka gaya mata duka ta fada mashi shiru yayi yana kallon bakinta wanda yake da kyau da bakin lining a kasa wanda kamar ita ta zanashi Amman haka hallitar bakinta yake
Zama yayi saman sofa ita kuma ta fara share wurin da vacum cleaner Ammar ya shigo yana wata irin dariya yana nuna Imad wanda ya rasa miye zaice Hurriya kallonshi tayi taga kamar su daya don suma identical twins ne kamar Neela da liya murmushi yayi mata sannan yayi mata wink bayan tagama komai zata fita tazo wucewa kenan Imad ya tadiyeta ta fadi goshinta da hannunta na buguwa da kyar ta tashi.
🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
19&20
Da kyar ta tashi kallonshi tayi da idanunta masu wani kaifi Dukansu kasa gane expression din fuskarta sukayi she looks fierce and scary ta iya hiding emotion don fuskarta baka iya lura da farin ciki ko sadness ko happiness ta kware wurin hiding emotion dinta don haka fuskarta is neutral saidai idanunta ne suke bashi warning sannan ta sanya kafa ta tafi Because she was done ko mopping din batayi yayi da kanshi.
Ammar dariya ke cinshi Amman ganin zallar bacin rai a fuskar shi ya sanya yace Husain waye ya tabaka banza imad yayi dashi ya tashi yaje ya kwanta saman gado ya runtse idonshi
Ganin mulki da sarautar tashi ta matso ya sanya ammar ya fita idan ya sauko sai ya dawo
Hurriya ranta bace yake Mai mutane suka dauki duniya ne itadai abinda ta sani a rayuwarta da mai kudi da talaka duk Abu dayane da yaro da babba duk Abu dayane da makaho da mai ido duk abu daya ne saboda duka suna amsa sunansu mutane batasan yawan tunani don haka ta nufi dayar chamber din
Chamber zinariya kowa kallonta yake kuma ba wanda tayi ma magana abinda ya kaita shi takeyi don Allah ya taimaketa aikin kitchen ne
Aiki sukeyi sosai don abinci akeyi kala kala wasu suna gyara inda aka bata wasu kuma suna jera fruits a trays
Hurriya kam wanke wanke kawai takeyi tana kifewa
Sun dade suna aiki a wurin kafin a kamalla Hurriya wuri ta samu tadan zauna
Shugabar dake a wurin ta kalli Hurriya tace ku tashi kuje kukai abinci kuma ku tsaya har agama ci saboda idan suna bukatar wani abu
Hurriya kallonta tayi ido cikin ido sannan tace bazanje ba daganan nagama aiki sai kuma abincin dare zanzo Amman ba zan kai abinci ba
Shiru kitchen din ya dauka kowa yana kallonta baki bude
Hurriya ba inda suka tsaya sai inda takeyin wanki tunawa tayi bata wanke kayanta ba don haka ta shiga dakin ta dauko kayan saida ta cire kudinta da sarkokinta da wayarta ta adanasu sannan ta nufi wurin wankin
Wata yar karamar yarinya tazo wurin Hurriya kallon Hurriya tayi tace inason ki tayi dariya yan hakoranta na fitowa yarinyar tace kinsan miyasa nike sonki Hurriya ta girgiza kai tana kallon yarinyar tace Aa yarinyar dariya tayi sannan tace saboda kina da kyau shiru Hurriya tayi tana kallonta yarinyar tace kinsan mi ?kinfi kowa kyau a masarautar Qamar
Sai kuma ta bata fuska alamar tanaso tayi kuka tace amman banason in rasaki kamar yadda na rasa fareedaa shiru Hurriya tayi don bata gane inda zancen yarinyar ya dosa ba Hurriya wadda bata iya lallashi ba tace kiyi shiru ki daina kuka sannan ta matsa daga gefen yarinyar ta fara wankin
Hurriya duk tafi jin dadin aikin wanki kowa hidimar gabanshi yake ba wanda ya damu da wani don haka ba ruwanta da bata miyaun bakinta wurin magana
Kayanta ta fara wankewa sannan ta cigaba da wankin da ake kawo mata wanki take sosai ga sanyi
Duk sanyi bai dameta ba kamar yunwar da ta dameta don duk yau bataci komai ba wata irin yunwa takeji
Imad kallon wayarshi yake wadda banda ringing ba abinda takeyi tun dazu khaleed ke kiranshi non-stop Amman yaki dauka saboda his new Maid has ruined his entire day saidai he made a vowed to ruined her life the way she ruined his mood she really messed with the wrong person wani kiran ne ya kara shigo mashi cikin yanayi na mulki da kuma izza ya dauka shiru yayi batare da yace komai ba
Khaled yace kaifa dan rainin wayau ne kaifa kadai muke jira tun dazu don Allah kayi sauri cikin yanayi na mulki Imad yace please I will be there in the next five minutes
Ya kashe wayar sannan ya tashi ya shiga toilet dinshi ya dade a toilet din kafin ya fito sannan ya shirya cikin hadaddun English wears dinshi wadanda sukayi mashi kyau
Imad na fitowa ya iske Ammar da yake zaune a falon da yake link da bedroom dinshi yana kallon football babu wanda yake da access din shigowa wurin anyhow sai hassan dinshi wato twin brother dinshi
Ammar tasowa yayi ya kalki danuwanshi wanda suke da matukar kama sannan ya bashi side hug
Tunda ya kalleshi yasan cewar mood dinshi ba Daidai bane don haka yace twin mi yake faruwa dakai ne
Don’t tell me har yanzu saboda sabuwar maid dinka kake wannan frowning face din dariya Ammar yayi mai kulewa sannan yace haba young prince kada fa ka bada mu ka saki ranka mana don Allah
Zamuyi maganinta ta isa ta taba min husain dina ta zauna lafiya kada kacwani damu i will punish her myself
Dadin baki Ammar ya rinkayi mashi har ya samu Imad yayi dariyar da bai shirya ba daman dariyar tashi a iyakar ta wurin Ammar din sai kuma kannenshi shi kuma Ammar daman baida matsala yana da fara’a sosai
Fitowa sukayi tare wanda duk bala’en ka baka iya ganesu saboda matukar kamar su don wata irin kama sukeyi ba kadan ba they are identical twins kamarsu har tayi yawa
Duk inda suka wuce durkusawa ake ana cewa Allah ya taimake ku Allah ya kara maku nasara har suka fito inda motoci suke parked iri iri cikin hanzari aka bude masu
bayan wata red Bentley flying spur sannan bakaken convoy suka biyo bayansu
Hurriya kallon kala biyun da idan tagama wankesu to shikenan tagama wankin
tayi kololuwa wurin gajiya don daurewa kawai takeyi ga yunwa da take nukurkusarta
Tsotsar bakinta tayi sannan ta maida hankalita ta cigaba da wanki shanya taje tayi har ta fara tafiya taji ana mai kyau mai kyau mai kyau tana haki har ta iso inda Hurriya take tasha gabanta Hurriya kallonta tayi kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru yar kyakyawar yarinya karama wadda ta zauna kusada Hurriya kafin ta fara wanki dazu tace ina maki magana shine ki kayi shiru Hurriya again batace mata komai ba dariya wasba tayi sannan tace mata sunana wasba kefa ? Hurriya ko kallon inda take batayi ba ta kama gabanta.
Wasba kallon inda Hurriya ta bari tayi sannan tayi murmushi ta nufi gidansu dake cikin masarautar.
Hurriya kam tundaga nesa taga bakin dakin wurin ya cika yayi fam cike da mamaki ta karaso tana kallon mutanen da suka cika famm kamar hadin baki kuma suna ganinta sauran mutanen duka suka juyo suna kallonta
Hurriya kam takawa ta cigabayi a hankali tana karasowa don ita haka Allah yayi ta idanun mutane basu takura mata saidai su kara mata confidence don haka ta tsakiyar su ta ratsa don duk kallon da ake mata ko ajikinta saidai wata fitinanniyar tsawa da aka buga mata wadda ta shiga duk wanda yake wurin Hurriya ita kanta tsawar ta shigeta saidai ta maze ta dago idonta cike da rainin wayau ta zuba ma wanda ya jefeta da tsawar tana zuba mashi idanunta masu masifar kyau.
Kallonta yake tundaga tafukan kafafunta har zuwa kan dogon bakin gashinta kallonta yake yana hadiye miyau da kyar
Hurriya kam lura da irin kallon da yake mata mai cike da zallar iskanci ya sanya tayi tsoki tace dan akuya maye ta nufi inda zai sadata da kofa saidai bata ida karasawa ba taji an kifa mata bulala mai matukar zafi
Juyowa tayi aiko taganshi tsaye yana kallonta da idanunshi wadanda basu da kyaun gani
Kallonta yayi sannan yace ke tsinaniya yar gidan matsiyata da ubanwa kike takama dashi duk masarautar nan da har zaki kona ma barira fuska tsotsar bakinta tayi sannan ta kalleshi ido cikin ido tace da ubanka nike takama a masarautar nan tana kallonshi shima yana kallonta wani irin kwarjini takeyi mashi don kwata kwata taki sauke idonta har lokacin idonshi na cikin nashi
Kowa kallon dramarsu yake ana jiran kaura ya jawota yayi mata dukan da bazata iya gane ko kanta ba bare har ta zagi kaura ko ta kona mashi budurwa
Shikam kaura he was lost in thought because he had never seen a beautiful human being like her she’s beautiful beyond words she’s just beautiful yadda take komai yake sanya mashi ganin kyauwunta gyara tsayuwar shi yayi domin ya bugeta kawai saiga kuyanga daga sashen Imad
Kallonsu tayi tace mi yake faruwa ganin duk sunyi shiru ya sanya ta kalli Hurriya tace muje hakimi na kiranki Hurriya ba wanda ta kalla acikin su tabi kuyangar
Suna zuwa suka shiga chamber hakimin wanda yana can ciki kwance a saman sofa
Abinci ya gama ci sannan ya sanya aka fidda mashi kwanonin abinci wayarshi yake latsawa kafin bacci ya daukeshi mai matukar dadin gaske
Hurriya kam tunda ta sanya aka gaya mashi Amman har lokacin bataji anyi mata iso ba don haka taje balcony ta zauna tayi shiru tana kallon masu wucewa
Duk kuyangin dake wucewa kallonta suke da mamaki irin kujerar prince kika zauna tabb kina ruwa ba wanda ta kula bare tayi mashi magana
Lumshe idonta tayi sannan tayi crossing legs dinta banda yunwa ba abinda takeji don duk wunin ranar bata sanya ma cikinta komai
Baccin gajiya da taji ya fara daukarta ya sanya ta tashi ta koma ciki kitchen din ta shiga wanda tayi sa’a ba kowa kallon kulolin abinci tayi wanda aka jera abinci ne a table din kitchen island ba tare da bata lokaci ba ta shiga budewa abinci ne kala kala ga yankakun fruits wani plate mai kyau ta jawo ta zuba abincin ta faraci ahankali saida taci ta koshi don wanda ta rage baifi ace loma daya ba wanda har ta koshi sosai
Mama RaBI ta shigo kitchen din tare da zubaida dukansu bude baki sukayi da mamaki suna kallon Hurriya da tagama cin abincinta hankali kwance salati mama rabi ta farayi tana kallonta sannan tace waye ya baki izinin cin abincin nan kinsan abinci waye kuwa kallonta Hurriya tayi da idanunta masu haske ba tare da tace komai ba ta dauki ruwan da yake jere a saman tray din ta fita.
Mama RaBI kam ba’a tabayi mata irin abinda Hurriya tayi mata ba
Kallon zubaida tayi wadda har lokacin bakinta bude yake sannan tace wai ina aka samo wannan shegiyar yarinyar ne mama rabi kinga wani kallon banza datayi maki sannan ta juya ta tafi shiru mama rabi tayi sannan ta Sauke ajiyar zuciya tace lallai yaro baisan wuta ba sai ya taka sannan ta kyalkyace da dariya zubaida wata dariyar gefen baki tayi itama sannan suka bar wurin
Mama RaBI taji haushi sosai da hakimi bai basu fuska
Ko kara bai basu damar wani ya kaimashi bare munafunci da tsaegumi
Da wallahi sai tagaya ma Imad kaskantaciyar mai-aikin shi taci mashi abinci kwata tayi sannan tace ajuri zuwa rafi watarana tulu zai fashe
Hurriya tafiyar ta Tayi wanda gari har ya fara duhu magrib ta gabato saida tayi tafiya mai nisan gaske sannan tazo bangarensu ta shiga
Ta gaji sosai don ba abinda take bukata irin tayi wanka tayi bacci kallon bintu da take zaune tana hamma tayi wanda dama ga dukkan alamu Hurriya take jira
Wuri ta samu ta zauna Bintu ta kalleta tace sannu Hurriya kindawo ne kinci abinci ? Daga mata kai Hurriya tayi batace ma Bintu komai ba
Bintu kallonta tayi hamma tayi sannan tace saida safe daman jiran dawowar ki nike bari in tafi har ta juya tajiyo sautin muryar Hurriya daga bayanta tace kinci abinci da wata irin murna Bintu tajuyo tace naci a hankali Hurriya ta zaro naira dari biyu ta mika mata
Bintu amsa tayi tana kallon Hurriya domin jin karin bayani lumshe idonta Hurriya tayi sannan ta tsotsi bakinta saida ta dauki lokaci sannan ta bude idonta masu kyau ta zuba ma bintu su tace idan kina bukatar wani abu ki siya can kasan makoshin tace ki kula da kanki sannan ta kara rufe idonta kamar mai bacci
Bintu murmushi tayi tana kallon Hurriya da zallar kauna a idonta wadda idonta suke rufe dan tsalle Bintu tayi kamar karamar yarinya tace Ina kaunar ki Hurriya sannan ta juya ta tafi dakinsu
Saida Hurriya taji tafiyarta sannan ta mike ta nufi babban kitchen din da ake dafa ko wani irin abinci
Dubawa tayi ko zata ga matar jiya saidai akasin haka baba haule reza tagani don duk tafi kowa zama kusa da ita don haka ta nufi wurinta da bokitin baba haula reza kallo daya zakayi mata kasan cewar masifarfa ce ta ajin karshe
Hurriya bokoti ta ajiye ahankali sannan ta kalleta in a commanding tone tace ruwa zaki zuba min
Baba haule reza ta dago idonta a kankance ta fara surfa mata ashariya Hurriya bata janye idonta daga kallonta ba kuma batace mata kala ba
Har saida tagama kumfar bakinta kowa kallon baba haule reza yayi acikin kitchen din sannan kowa ya cigaba da hidimar shi don inda sabo ta saba
Hurriya saida ta tabattar da cewar baba haule tagama masifarta sannan ta zaro naira dari ta ajiye mata tana kulleta da idonta
Baba haule kam kamar an daure mata baki don dauke darin tayi a inda Hurriya ta ajiye tana saka kudin cikin skirt dinta
Bokitin ta janyo ta zuba ma Hurriya ruwan zafi masu yawan gaske ba tare da Hurriya tace kala ba taja bokitin ta nufi toilet ta gasa jikinta sosai da ruwan zafi.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace
By Khadija (KMU)
Page 21&22
Bata wani dauki lokaci sosai ba ta fito daga toilet din tana mai ya mutsa fuskarta don duk batajin dadi don kayan dake jikinta sune ta maida dalili kam da akwai zanen tatoo a bayanta bata kaunar ko wani dan mutum yaga tatoo din sam she’s not comfortable cikin masarautar Qamar don kwata kwata batada yancin dan adam kuma ita a rayuwarta ba abinda takeso irin yanci don haka ta tashi a rayuwarta tunda ta taso ba wanda ya taba depriving right dinta tanada ko wani irin freedom
Tana da matukar tsafta don kaya basu iya mata 24hrs ajikinta bare kuma ace kuma tayi wanka ta maimaita kaya saidai da ace ta fita da daurin zani wanda duk zanen dake bayyane a bayanta zai bayyana ga idon mutane gwara ta maida kayanta
Don haka da kayan ajikinta ta fito sannan tayi alwala ta shiga dakin
Cikin natsuwa ta Cire kayan jikinta kallon inner wears din da ta siya dazu dasu sabulun wanka da brush tayi har da turare mai sanyi kamshi batasan ana kasa haja ba sai dazu da safe inda har tazo wucewa taga haule reza ta kasa kaya masu kyau har ta wuce ta dawo haule reza ba abinda bata saidawa saida Hurriya ta bata kudi sosai wurin siyen abinda takeso don saida ta tabbatar duk abinda take bukata ta siya sannan ta nufi bangaren Imad
under wears ta sanya masu kyau sannan ta shirya cikin wata blue half gown da iyakarta gwiwar kafarta ta tsaya
doguwar hijab dinta ta sanya sannan ta kabbara sallah rama sallolinta tayi duka bayan tagama sallarh ta kishingida jikin katifar ta lumshe idonta ba bacci take ba Amman dai tayi lamo
Sunanta taji ana kira saidai ko motsawa batayi ba bare tayi tunanin bude idonta saida tayi mintuna Sosai kafin ta bude idonta ta zuba ma zubaida su da take tsaye wanda tagama kulewa don tunda tazo tasan ba bacci take ba Amman don bakin rainin wayau ace tanajinta tayi shiru ta kyaleta
Zubaida ta kalleta tace Lallai ma Hurriya shine zaki zo ki kwanta wakike tunanin kinbar ma aiki sai ki taso tunda ba bayi kika ajiye ba
Don ana bukatar ki a Aikin dare shiru Hurriya tayi batace kala ba don yaddda tayi kamar ma da dutse ake maganar
Hurriya magana fa nike inji zubaida shiru Hurriya tayi saita lumshe idonta
Zubaida kam iya jin haushi takai don cikin zuciyarta banda la’anar Hurriya ba abinda take saidai tayi mata wani irin mugun kwarjinin da bata iya maida mata magana
Gajiya tayi da tsayuwa zubaida taja tsoki tayi tafiyar ta
Hurriya kam shiru tayi don saida tayi kusan minti talatin kwance idonta kuma rufe kamar mai bacci
Tashi tayi ahankali cikin yanayin natsuwarta ta sanya takalminta ta fita
A hankali take tafiya wadda idan ka kalli yadda take tafiyar zaka dauka jinin sarauta ce dogayen kafafunta da suke bude sai salki suke sai tulin bakin sumarta wadda baka iya ganin jelar gashin saidai kwantaccen gashinta wanda ya fara tundaga goshinta farin wata ya haskata wanda ya taimaka wurin fito mata da tsantsar kyau na hallita duk wanda ya kalleta ya kara kallonta yasan mai kyau ce wato mai asalin kyau
Kallonta ake gabas da yamma kudu da arewa duk da kasancewar darene
Daidai saitin su barira da suke zaune a tabarma suna shan rake tazo zata wuce tanajin duka idanunsu dake yawo a kanta Amman ko a kwalar rigarta ta cigaba da tafiya tayi abunta
Muryar Hansa’u ce ta doki kunnenta wadda take cewa barira gafa mutuniyar
Barira shiru tayi tana kallon bayan Hurriya da dogayen kafafunta lashe baki tayi ta gyara zamanta batace komai ba
Wasila ce tace har yanzu bamu dauki fansar abinda tayi maki barira ba Amman na rantse bataci banza ba
Don ko yadda ta bata mana suna sai mun gyara mata zama sai na wulakanta yar matsiyaciyar can wulakanci mai muni sai kuma na hada mata tuggun da bazata iya warwareshi ba duka rayuwarta a masarautar nan sai na wulakantata wulakanci mafi wulakanci sannan in kaskantata kaskanci mafi kaskanci
Sannan tazo har gadon baccinki barira sai yadda kikayi da ita
Dukansu dariya suka sheke da ita tare dayin na’am da alkawarin da tayi kuma Dukansu sunce zasu tayata
Hurriya duk tanajin abinda suke cewa duk da kam tafiya takeyi kuma tayi masu nisa kallon sakarkaru marar sa aikinyi tayi masu ta cigaba da tafiyarta
Saida tayi tafiya mai nisan gaske kafin ta kawo chamber Imad
Ahankali ta shiga kitchen din wanda tana shiga kamar hadin baki duka ma’ikatan da suke aiki a kitchen din suka jiyo suka kalleta acikin su ba wanda bai bude baki ba yana kallonta ba tunda daga sama har kasa
Amman Hurriya shin ita ko ajikinta don idanun mutane basu daureta kwata kwata ko alama itadai Allah ya bata wani irin confindence wanda ba ko wani dan mutum yake da irinshi ba
Hurriya bata fasa tafiya ba don tsakiyar kitchen din tazo sannan sai taga tukunyar da ake shredded beef din don haka cikin natsuwa taje ta fara motsa tukunyar
Zubaida ce wadda ta kasa yin shiru cike da rashin kunya da wulakanci tace wai casu zaki ko coci Hurriya dagowa tayi ta zubama zubaida idonta masu kama da zaiba sannan ta tsotsi bakinta a hankali tace casu zamuje nida tsohuwarki da tsohonki idan mugama sheke aya sai mu tsaya ta coci muyi ibada
Tayi maganar hankali kwance tana kallon kowa acikinsu wanda fuskarsu take dauke da mamaki
Dukansu ba wanda bai saka wani abu acikin ranshi ba
Wasu kuma cewa suke daman tana magana?
Hurriya bayan ta tabbatar da shredded beef din yayi ta juyeshi a cikin food flask sannan ta dauki tukunya ba abinda ba’a nuna mata ba a bayani don haka tasan inda komai yake
Ruwa ta zuba a tukunya sannan ta shiga store ta debo basmati ta kunna gas ta daura tukunya hadaddiyar biryani tayi masu don tana abincin tana rera waka nike gani tanayi tana dan juya kugunta har ta gama don kamar abincin na tura mata memories don tana enjoying
Tazo ta kwaba pancake dinta ta soyashi mini sannan ta dauko chocolaté tayi dizzling dashi
Tana aikinta tana wakarta tanajin idanunsu a kanta Amman kamar babu kowa a wurin
Saida tagama yin komai ta dauko kula ta juye don abinci bai dauki wani lokaci ba tagama saboda karfin gas din dake da ci sosai
Hadawa tayi a tray don dakanta ta jera
hada wanda mama rabi tayi da wanda tayi don abinci suna da matukar yawa mutum ashirin zasu iyacin abinci don different varieties of food ne a wurin
Bayan tagama sai ta nufi hanyar fita mama RaBI kamar tasan niyyarta don haka tace Hurriya kune zaku tsaya har su hakimi sugama cin abinci koda suna bukatar wani abu sai ku mika masu
Bata matsa ba kuma bata dawo ba Amman ga dukkan alamu maganar ta shigeta zubaida da mama rabi da wasu kuyangu guda ukku suka fara fitar da tray din abincin da drinks da wasu manya manya non alcoholic wines
Hurriya zuwa tayi ta dauki trays din wanda yake cike da wasu matsiyatan plate ta shiga parlon saida ba kowa a parlon it looks like Dukansu suna parlon gaba don haka Bata wani Bata lokacin ba ta shiga ba excuse ba sallama kallon mutanen dake zaune a tsakiyar parlon tayi duk twins ne kusan set uku masu matukar kama da juna.
Liya wadda ta daura kafafunta saman jikin Neela in an annoying way itace ta fara lura da Hurriya kallonta take from head to toe shiru tayi batace komai ba duka sauran hankalin su yana akan abinda sukeyi Neela hankalinta duka yana Akan wayarta sai Amrah da imran da suke playing ps 5game duka hankalisu yana a wurin game din
Liya kam satar kallon Hurriya kawai take wadda take jera abinda ta shigo dasu a dining kutt The girl is unparalleled beauty su zubaida duk sun dukar da kansu da kuyangin da suka shigo tare
Kallon kafafunta wanda suke bude tayi tana kallon sumarta da take bude fuskar nan a hade take kamar an aiko mata da sakon mutuwa tanayi tana cije lebe wanda ga dukkan alamu sararta ce Liya kasa janye idonta tayi daga kallon Hurriya don tunda take masarautar Qamar bata taba ganin halitta mai kyaun Hurriya ba saidai gabanta ne yayi mugun faduwa tunawa da tayi ana jita jitar cewar masu kyaun masarautar su mutuwa sukeyi don ko a ma’aikata indai matane to ba’a cika kawo marar sa kyaun hallita ba saidai tunda take bata taba ganin Mai kyaun da ta kama kafar Hurriya ba wane subira an dade acikin masarautar Qamar ana bama subira sarauniyar kyau Amman wannan yarinyar tayi ma subira fintinkau don indai za’a hada kyaun subira da Hurriya to subira zata iya samun 30percent ita kuma Hurriya 70percent
Babu abinda Allah ya rageta dashi don ita jikinta irin na models ne wanda turawa suke iya barnar da ko nawa ne garesu saboda su mallaki irin jikinta
Sauke ajiyar zuciya tayi farar daya tausayin yarinyar yana kamata don tana da kyaun da ba kowani namiji bane zai iya dauke ido akanta ba sai kuma babban kalubalen dake masarautar duk da jita jita ne Amman ta dade tana tunanin anya abun ba gaskiya bane don itama ta rasa ma’aikantata Sosai wanda suka shaku kuma ta saba dasu saidai duk idan hakan ta faru akwai abinda jakadiya take fada mata saidai tun tana yadda har tazo tana putting Question mark.
Imad ne ya shigo kallonsu yayi Dukansu sannan yace guys let’s eat dinner ku tafi kubar min part dina don duk kun cikamin part dina Ammar ne ya ajiye wayarshi wadda take hannunshi sannan yazo Daidai inda Imad yake ya dafa shi yace ya akayi ka kosa MU tafi kodai kodai sannan ya fashe da dariya Imad daure fuska yayi dagajin maganar Hurriya don yarinya ta bata mashi rai kuma ta rainashi shida ma’aikatan masarautar Qamar ke shakkar shi Amman yarinya yar Qarama tana Neman rainashi har sanyawa fa yayi a kira mashi ita kuma dagagan ya shanyata so yayi sai tayi awa goma tana jiranshi amman tayi tafiyarta idonshi idon Hurriya Amman sai yayi mata wukanci
Dariya ammar ya cigaba dayi yace kodai har ka folla ne? Naga yarinya is beautiful ya ida da maganar da wata irin dariya
Neela itama dariya tayi tazo saitin ammar tace who’s the girl dan dungurinta ammar yayi sannan yace magulmaciya yace ban fadi sannan yayi mata gwalo
Dariya Liya tayi sannan tazo saitin ammar itama tace who’s the girl bro please tell me kasan ba ajin kanmu dariya yayi sannan itama ya dungureta yace magulmata bazan fada ba
Dukansu tare suka jero sai yan kananun kannansu wadanda suke uwa daya uba daya masu bala’en kyau Amrah da hamdan kenan miskilai ne na karshe kuma yaran da basuyi ma kowa magana don duk da irin tsantsar kauna da take zagaye dasu wurin yayyayensu wadanda suke jinsu kamar kwai to idan ba yayyensu ba wanda sukeyi ma magana sun shaku da yayyansu Sosai saidai sarauta ajinisu take don wata sa’in miskilancin su harga yayyansu don tunda sukazo dinner a chamber imad wadda ta kasance duk sati sukeyinta saboda kowa yanada sashen shi to suna dadewa basu hadu ba sai Ammar ya kawo shawarar every Friday night suyi arranging cin abincin dare tare tohm haka sukeyi dukk satin duniya sai kuka suji damuwar junansu
Tare suka iso katon dining din wanda yake cike da abinci kala kala zubaida kansu a kasa suka farayi masu kirari Allah ya taimake ku Allah ya kara maku nasara sunata yi masu kirari
Duk acikinsu ba wanda ya amsa masu don ko kallon inda su zubaida suke basuyi ba
zama dukansu sukayi ta Liya ce ta juyo tace masu we will serve ourself
Hurriya tana tsaye tana kallonsu ita ba wanda tayi ma magana Liya dai na kula da ita su Imad hankalisu ma bai kai kan ma’aikatan ba bare suga Hurriya don su ma’aikatansu ko kallo basu ishesu ba.
Hurriya tsaye tayi tana kallon kowane acikinsu ba tare da ta dukar da kanta ba
Hamdan ne ya dago idanunshi daga kan iPad din dake rike a hannunshi cikin sa’a kam ya saukesu akan Hurriya da take tsaye fuskarta babu annuri kallonta yake Ko kyaftawa bayayi itama kallonshi take cikin idanu
Neela ce ta kalli Amrah tace ki ajiye iPad dinan muci abinci turo baki Amrah tayi sannan ta ajiye iPad din muryar hamdan ce ta doki dining din dasuke yace you alamar yana kiran wata Dukansu yayyanshi dagowa sukayi suna kallon wadda yake kira kasancewar shi ba mai yawan magana ba don sukansu hardly ne su ji maganar shi saboda miskilancin shi
Hurriya da take tsaye tasan da ita yake kallonta yayi sannan ya kara nunata da yatsa still banza tayi ta kyaleshi tana zuba mashi idanunta
Imad wanda shima hankalin shi nakan wayarshi ya dago ya kalleta saida ya kalleta tundaga farko har karshenta aranshi yace Lallai ma yarinyar nan waye zata burge tazo masu a haka kamar zata club saidai bai iya yaudarer zuciyar shi ba Amman yarinyar gaskiya tana da kyau toh kila shiyasa take raina ma mutane wayau amman bari zaiyi maganinta aiko nan take ya bata rai ya hade fuska yana kallonta
Ammar wanda shima kallonta yake bai ko kyaftawa saida ya tabbatar ya saisaita kanshi sannan ya kalli Imad da yake ta cin magani ya kwashe da dariya
Hamdan ahankali ya karayi mata magana yace please come and join us banza ta karayi dashi
Imad ne ya tashi ranshi bace Ammar yayi saurin rikeshi yana dannah dariyar shi
Amrah ce ta taso tazo saitin Huriya cikin muryarta ta yarinta tace kizo muci abinci tare don Allah tana pleading dinta da hannu in a cute way Hurriya kallon yarinyar tayi mai bala’en kyau amman kallo daya zakayi mata kasan akwai kadaici tattare da ita shiru Hurriya tayi tana kallon hamdan da amrah wanda shima ita yake kallo da alamar tazo tayi joining dinsu Neela ce ta kallesu ta bata fuska sannan tace what are you doing Amrah
Amrah bata fuska tayi haka zalika hamdan Liya ce ta taso tazo saitin Hurriya sannan tace please join the poor babys they love you
Hurriya daga mata kawai tayi ta zauna family dinner din
Zubaida kam kamar ta mutu saboda bakin ciki yarannan da basu tabayi mata magana ba don yaran Allah ya zuba masu mulki da sarauta basu kula kowa gashi yayyansu kamar su cinyesu haka sukejin su aransu idan sun soka tohm tohm yayyen sun soka idan sunki ka tohm suma sunki ka
Hamdan ne ya kalleta cikin mulki da sarauta don kusa da kujerar da yake tazauna ahankali yace mata you’re beautiful shiru wurin ya dauka kowa yana saka Abu aranshi Imad kam zuciyarshi banda bugawa ba abinda takeyi saboda tsanin bacin rai
Imad magana zaiyi Amrah ta rigashi ta hanyar dawowa saitin Hurriya tace ya sunanki please?hurriya kallonta tayi da idanunta masu kwarjini Amrah dafe zuciyar ta tayi ta hanyar cewa please stop looking at me like that way,you look intimidated .i know you’re more beautiful when you smile ok can you smile for me just once tana mata wink
Hamdan dariya yayi wadda ta fito tundaga zuciyar shi sakin baki su Ammar sukayi suna kallon kannansu
yare Hamdan yayi ma Hurriya ta hanyar cewa zaki bani diyarki idan kika haihu you’re beautiful but you’re lonely ta ko ina
gaban Hurriya ne ya shiga faduwa tana kallon hamdan da ya tsare ta da idanunshi yana jiran amsarta
Rabon da taji kalar yarenan har ta manta innallilahi wa’ina ilahi raji’un ta shiga furtawa cikin zuciyarta wadda take duka kamar ganga rabon da ta ambaci sunan Allah rayuwarta ta manta saidai acikin Sallah wadda batada tabbacin tana amsuwa ko bata amsuwa
Hamdan ya saki wani killer smile wanda idan ka kalleshi zaka iya cewa babba ne wanda dudu shekararshi sha biyu a duniya shida twin sister shi
Saidai Allah yayi mashi baiwa wadda ake kira wato smartness
Shiru duka wurin ya dauko suna kallon Hurriya da Hamdan murmushi Hamdan yayi yace mata you look like princess Layla Al-Khasheem she’s my role model because speech dinta yana matukar taimakona did you know her ?dan murmushi yayi sannan yace i know you will not know her saboda celebrity ce a duniya baki daya duk wanda ya kalli Hurriya alokacin zaisan a tsoroce take don sam takasa boye firgicin dake fuskarta salati take Sosai acikin ranta
Amrah ce tace she really look like Layla Al- khasheem sai yanzu da ka fada na lura
Ammar ne ya kalli Hurriya yace sunyi kama Sosai ya sakar mata murmushi tare da cewa you look like Layla Khasheem daga yadda yayi maganar zakasan cewar Dukansu suna kaunarta don liya itama washe baki tayi
Hurriya kam duk ranta ya jagule don kamar tana zaune saman kaya ko garwashin wuta haka takeji tsoro da fargaba suna kara cikata
tanajin saukar idanunwan kowa akanta
Amrah ce tazo saitin Hurriya tareda dafa mata kafada tace mata can you be my friend da wani irin karfi Hurriya ta ture ta ta fadi kasa fuskarta na nuna zallar bacin rai tace wa ya baki damar taba ni tana binta da idanun masu nuna zallar bacin rai saidai tana kokarin saita kanta saboda batasan yanayi fuskarta ya canza saboda da wuya Hurriya ta canza yanayin fuskarta zuwa damuwa ko farin ciki ko firgice ko kuma gazawa ko gajiyawa da rayuwa fuskarta akoda yaushe a yanayi daya take wato ta daurewa wadda za’a iya kiranta bata da mutunci
Imad ne ya tashi yazo Daidai saitin Hurriya wadda take idonta har wani jaa yake kawowa
Shima imad din rannshi a matukar bace shida neela zuwa yayi zai dauke ta da mari Ammar yayi saurin rikeshi Imad please don’t touch her ba tarbiyya bane dukan mace.
Hurriya Dukansu kallonsu tayi ba tare da tace masu komai ba ta fita daga dakin Hamdan ne ya ruga zaibita Liya ta rikeshi
Amrah kam kuka takeyi sosai wanda yasanya duka hankalin su ya dawo kanta
Neela ta rungumota tana lallashinta Ammar shima lallashin yakeyi Imad tashi yayi ya shige daki zuciyarshi na tafarfasa sannan ya barsu a parlon
Hurriya har bata ganin gabanta da kyar take tafiya ga dare da yayi ga sanyi ga fargaba abubuwa duk sun hade mata
Da kyar ta kawo kanta dakinsu tsitt kakejin ko ina adakin wani irin shiru wurin ya dauka don da yawansu sunyi bacci .
Ahankali ta kwanta tare da lumshe idonta tana fadawa duniyar tunani tambayoyi take ma kanta ina wannan yaron ya iya yaren Amarich sannan yace suna kama da Princess Layla Al-Khasheem shin har yanzu kamarsu a bayyane take itada Layla
Zuciyar tace ta buga don tana tsoron kalubalen da zata iya fuskanta nan gaba idan har identity dinta ya fito fargaba tsoro kadaici duk sune suka suka cikata
Bacci ne ya fara fizgarta Mai cike da gajiya ahankali baccin ya fara nauyi saidai saukar Ruwa mai matukar sanyi ajikinta ne ya sanya ta farkawa da sauri kuma a firgice bata Ida warwarewa ba taji an kara zuba mata ruwan mai matukar sanyi ga yanayin sanyi irin na farkon January
Rungume jikinta tayi idanun ta da hakoranta na gab gab wani ruwan taji ankara zuba mata mai matukar sanyi numfashinta ne ya fara ja yana dawowa kirjinta yana wani irin duka gab gab kankame jikinta ta karayi numfashinta na rage sauri dariya suke a kunnenta suna ihu suna kashewa
Tafiya su barira sukayi suka barta tana kokarin saisaita numfashin ta saidai mi ba abinda take gani irin past dinta rayuwarta ta tabaya yadda kawunta yake zuba mata ruwan kankara yana dukanta ne ya dawo mata kanta ne ya farayi mata wani irin nauyi sai wani irin duhu da ta fara gani sannan numfashinta ya dauke.
Hello readers ya kuke tunanin salon labarin namu
Ya akayi Hamdan yayi wani yare wanda Hurriya kadai takejin yaren
Miye tsakanin Layla Al -Khasheem da Hurriya Faisait Hamood
Ga Amrah da Hamdan da suke tsanin son Hurriya mi yasa suke sonta?
Ga Barira da suke barazanar tsoma kansu a rayuwar Hurriya anya basu debo ruwan dafa kansu ba
Ga wasba yar yarinya Karama da Hurriya ke burgeta
Miye yake faruwa ne da kyauwawan masarautar Qamar wanda ya sanya ake kiran masarautar da mysterious palace
Wacece Hurriya?
Ku biyoni cikin labarin masarautar Qamar a hankali komai zai warware.
Waye star dinmu a maza?
Shaho,Kumurci,imad ko Ammar kuma Hamdan
Muje zuwa kawai don salon labarin namu ya bambamta da kowani irin labari.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace
By Khadija (KMU)
23&24
Kwance take male male cikin ruwa mai matukar sanyi wanda kwata kwata bata ko numfashi ba wanda ya lura bare ya ankara
Da kyar suka lallashi amrah aka sanya kuyangu suka tafi da ita chamber dinta Mai matukar kyau da daukar ido
ruwan wanka Neela tazo ta hada mata ta fito mata da kayan bacci sannan tayi mata addu’a tare da kashe mata wuta
Liya kam tare suka tafi itada Hamdan don ba wanda yace ma dan uwanshi komai har suka isa chamber dinshi
Ammar shima chamber dinshi ya nufa ya haye saman gado tare da lumshe ido yana tunanin duka abinda ya faru yau so yake ya hada komai wuri daya don samun ma’anar abun saidai ya kasa hada komai
Amman yarinyar tayi matukar bata mashi rai donmi zata ture Amrah shiru yayi yana tunanin kilan tana da uziri don kowa da uzirinshi.
Karfe 5:44 Allah ya kawo Bintu domin tada Hurriya sallah asuba saidai ganinta kwance ya sanya ta fasa ihu agigice tazo tarinka tadata tana Hurriya Hurriya ki tashi don Allah ki tashi ki daina bani tsoro inna lillah wa’inna ilaihi raji’un Bintu ta shiga furtawa tana bude ma Hurriya ido Amman shiru
Ruwa ta debo da sauri ta yayyafa mata tare da shafa mata a fuskarta bude idonta Hurriya tayi wanda sukayi matukar jaa wani seizure numfashin ta ya fara tana tari mai sarkewa don kamar zata mutu haka numfashin yakeyi ga kuma tarin yaki sassauta mata Bintu banda hawaye babu abinda yake kwarara daga idonta don ta rasa mi zatayi wanda zai taimaka ma Hurriya saidai kukan
Kirjin Hurriya taga yana sama yana kasa numfashinta yazama abnormal don abinda take yafi nada bintu sakinta tayi ta ruga ta fita aguje ta rasa ma inda zataje watar yar matashiyar budurwa tagani tace mata don Allah akwai likita anan yar budurwa tace Akwai inna hanne mai bada taimakon gargajiya idan ansamu mararsa lafiya godiya kawai tayi mata batasan ya akayi ba sai ganin ta tayi a kitchen. ganin kanta a kitchen datayi ya sanya ta fashe da wani irin kuka inna hanne ce ta kalleta tace ke kuma lafiya kike mana sintiri kina kuka
Bintu zuwa tayi ta rike mata kafafunta tace ki taimaka mani ki ceci rayuwar Hurriya ta kusa mutuwa ki taimkeni yatsine fuska hanne tayi sannan tace wacece kuma haka Hurriya yar doguwa mai kyau tureta hanne tayi tace ni likita ce da zaki zo ki tsareni da magiya
Ki taimake ni don Allah ko nawane nayi maki alkawarin idan ta warke zan baki shiru hanne tayi tana tunani kafin ahankali tace muje.
Barira dasu wasila ne sukaje wurin da Hurriya take yashe kwance Hansa’u ce ta ture mata dogayen kafafunta ahankali Hurriya ta bude idonta wanda suke rufe hakoranta suna gab gab kirjinta na sama na kasa binsu take kawai da kallo dariya suwaiba tazo tayi tana take mata yatsun hannunta ita kuma barira ta take dayan hannun da nuna itadin watace tayi dariya tace yau zan kwanta da wannan kaskantaciyar baiwar sannan na sanya a farfasa mata jikinta sai inbi tada gishiri a ko ina kuma kullum kowa da kowa acikinku zai kwanta da ita sannan zansa bawa mafi muni da kaskanci ya kwanta da ita ta fasa wata dariya su Hansa’u suma sukayi dariya Hansa’u ce ta kalli barira sannan tace ina fatar a aske mani gashi kanta murmushi barira tayi sannan tace angama
Wasila ce ta fashe da dariya tazo ta haye Hurriya tare da kama hannun rigarta zata farka mata riga
Hurriya kam ta kanta takeyi don numfashinta kiris ya rage ya kara daukewa Amman tana cikin tsananin tsoro don tabbas idan har ta bude mata baya dolene taga zanen tatoo din dake da tambarin daga inda ta fito nobody is allowed to see the tatoo idan ba haka ba rayuwarta will be at more risk don tatoo din shine yake rike da sirrin ko ita wacece miye zai faru da ita idan wani yaga sirrin dake Zane abayanta
Shiru tayi zuciyarta da kirjinta na wani irin bugawa hannun rigar aka farke wanda hakan ya kasance daidai da daukewar numfashinta.
Bintu da inna hanne da suka shigo yanzu wanda yayi Daidai da daukewar numfashin Hurriya da kuma ida farkewar hannun rigarta
Wani irin kyakyawan mari inna hanne ta dauke wasila dashi tana binsu da wani irin matsiyacin kallo rike kuncinta wasila tayi ta fita daga wurin a hankali Hansa’u ta bita a baya sauran ma Dukansu suka bita a baya duk a masarautar nan ba wanda Suke tsoro irin inna hanne da reza dan daya hatsabibiyace daya kuma fitinaniya ga uban karfi
Bintu kam rungume Hurriya tayi tana kuka inna hanne ta kalleta tace ta fita ta debo masu ruwan zafi Bintu ta tafi don samo ruwan zafin
Taba Hurriya inna hanne tayi saidai abinda tagani saida ya girgiza ta daman har yanzu tanada aljanun da suka so bude mata ido kenan to mi ya kawosu miyasa suka karantar da ita bayanin Hurriya abinda rabon da tasan wani abu game da rayuwar wani andade
Inna hanne kallon Hurriya take tana tunanin abinda tagani tattare da rayuwar yarinyar lallai Hurriya tana cikin hadari acikin masarautar nan don irin duhun da tagani da kalubalen dake lullube da ita sunan Allah kawai inna hanne take fada don ta dade bata ga Abu irin haka ba
Don kwata kwata aljanun da suke son bude mata ido sun tafi tare da karfin ikon Addu’a da azkar don bata ganin komai tafi shekara goma rabonta da budewar idon jinnu sai wannan karon mi hakan yake nufi Akwai matsala babbar matsala tattare da rayuwar yarinyar nan
A hankali ta daga rigar Hurriya a firgice tace masarautar Heral Inna lillah wa’ina ilahi raji’un ta ambata tana kallon zanen tatoo din Hurriya dake kwance agadon kafadarta ta baya kenan itace yarinyar da kusan shekara biyar dasu ka wuce akazo ana nema don kusan ko wace babbar masarautar dake duniya anje don harda masarautar Qamar akazo tare da alkawarin duk wanda ya samota akwai gagarumar kyautar da za’ayi mashi don dashi da zuri’ar shi hatta tattaba kunnenshi sun gama talauci saboda irin zunzurutun abinda aka alkawarta sannan kuma idan nameji ne zai aureta tare da nadashi sarautar kasar baki daya
Shiru tayi tana hasko Labarin irin masarautar Heral da ake basu irin mulkin da akeyi da irin tarin arziki da daular dake shimfide a cikin kasar don masarautar na daya daga cikin jerin masarautar duniya da ake ji dasu
Shiru tayi tana tunanin duhun da tagani tattare da Hurriya wanda ba’a masarautar Qamar kadai ya kare ba hatta masarautar Heral din idan ta koma zata fuskanci kalubalen da kilan zai iya sanadin rayuwarta don ko masarautar Qamar din Qalubalene da zai iya sanadin rayuwarta ko kuma ya tarwatsa mata duk wani farin ciki na rayuwarta wanda yarinyar ga dukkan alama ta dade ba farin ciki rayuwarta
Inna hanne ta sauke ajiyar zuciya tana kallon kyakyawar fuskarta tana nazarin dalilin da aljanunta sukayi nuna mata bayanin Hurriya yarinyar abar tausayi ce saboda zagaye take da makiya Amman In Sha Allah zata taimaketa da addu’oi Sosai da azkar masu matukar muhimmanci saboda tasan tsafin da akeyi a masarautar Qamar
Bintu ce ta shigo aguje da ruwan zafi sannan ta ruga aiken da inna hanne tayi mata don amso mata magungunan hausa Bintu bata wani dauki lokaci ba sai gata da magungunan
Kallon Bintu baba hanne tayi tace ta dan fita Bintu batayi musu ba ta basu wuri
Maganin ta hada mata na lamoniya hade da sanyi sannan ta bude bakinta ahankali ta shiga bata don ko motsi batayi rabin maganin na shiga rabi na fita baba hanne kallonta take cike da tausayinta don itadai tunda ta taso rayuwarta A daji kuma babansu magani yake badawa itama har ta gaje shi to bata taba cin karo da makamanciyar lamoniya irin wannan ba
Bayan tagama bata magani ta samu farin tsumma mai kyau sannan ta shiga gasa Hurriya da ruwan zafin
Tana dora hannnunta ajikin Hurriya ta zabura
Haka ta rinkayi da ta taba mata jiki sai ta zabura saida ta taimaka mata sosai wurin ganin gasa jikinta da magungunan gargajiya
Wasba ce zaune à inda Hurriya tazauna jiya tayi wanki tana wasa da karamin icce wanda ke nuni da kamar Hurriya take jira
Kallon hanyar da ta biyo jiya tayi saidai bata ga ko mai kama da ita ba
Bata rai tayi tana turo baki ta tashi ta koma cikin gidansu
Hurriya shiru shiru bata tashi ba saaidai Bintu na zagaye da ita kamar wacce zata gudu don har tayo aikinta ta dawo
Inna hanne ta dade a wurin tana kula da ita kafin ta koma kitchen domin ayyukanta saida Inna hanne tagama ayyukanta sannan ta dawo inda Hurriya take kwance hannunta rike da kofin shayi cikin hikima ta shiga zuba ma Hurriya ruwan shayin duk da rabi ya shiga rabi ya fito haka abun yake
Bayan tagama bata shayin tayi tagumi tana tunanin ikon Allah tunda take bata taba tunanin ko a rayuwarta zata iya zuwa masarautar Heral ba saboda sai an ketare kasashe shin bama wannan ba itadin wacece ba kowa bace face ma’aikaciya a masarautar Qamar sai kuma Qaddara da ta hadata da long lost princess din Qasar
Saidai Tana Addu’a Allah yabata ikon taimokon yar marainiyar yarinyar nan Allah kada ya sanya san zuciya ya debeta ta tona mata asiri
Su kuma su barira zatayi maganinsu Lallai da ace sun san wacece ita da ko hanya daya basu isa su hada ba
Don duk yan masarautar Qamar tafi karfinsu hatta sarkin idan tagadama tace a sauke shi daga kan mulki to tabbas babu tantama za’a sauke shi don masarautar su tana mulkin masarautoci da yawa a afirca so masarautar Qamar na ciki
Ta dade tana tunanin sannan ta tashi ta fita tana fita saiga Bintu na shigowa dan sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace ki kula da ita don Allah.
Abun kamar wasa Amman har yanzu Hurriya bata bude idonta ba har anyi wata daya da sati daya
Su barira suna sane da halin da Hurriya take ciki don har anfara yada jita jita su barira sunyi kisan kai saidai da yake su din suna da power sosai ba wanda ya tarbesu da maganar
Saukin Hurriya daya data samu Inna hanne tayi bake bake ganin taji sauki don lallabata take kamar kwai kowa yana mamakin dalilin don baba hanne bata da irin wannan kirkin da take nuna ma Hurriya don itama ba Ruwanta da kowa
Bintu kam ta zuge ta rame tass kallo daya zakayi mata kasan cewar tana cikin matsinaciyar damuwa .
Imad kam shima ya shiga damuwar rashin ganin mai aikin nan don Hamdan da amrah duk sun gigita su don yanzu a chamber shi suke kwana Neela kam batasan mi zatace ba a al-amarin don tun tana kushe su yanzu ita kanta burinta da fatanta a samo Hurriya
Imad yafi kowa damuwa don kowa kallo yake yasan inda take don yanzu haka suna tare da Ammar ne a balcony Ammar ya kalleshi yace twin Imad kallonshi yayi yana daga mashi kai dafashi Ammar yayi yace nifa na rasa gane mike faruwa wacece wannan yarinyar miye hadinta da Hamdan da Amrah mi yasa suke sonta har haka yaran da basu damu da kowa ba rayuwarsu Amman sun damu da ita fiye da yadda suka damu damu
Shiru Imad yayi yana nazarin maganar saidai baisan yadda zai hada komai ya bashi ma’ana ba don haka ba tare da karayin wani tunanin ba yace Allah yasa lafiya dai
Shiru Ammar yayi sannan yace ka tambayi ma’aikatan ko lafiya? Girgiza kai yayi yace mashi Aa
Shigowar Liya ne ya sanya Dukansu suka juya suna kallonta cikin jumpsuit din Rimowa wanda sukayi mata kyau sosai zuwa tayi gefen imad ta rike mashi hannu tace na samo labarin maid dinka ka kwantar da hankalin ka
Ammar ne ya zagayo ya rike ma Liya hannu yace lafiya miye ya faru shima rike mashi hannu tayi , murmushi tayi sannan ta gyara zama tace kwantar da hankalin ka tana cikin masarautar Qamar
A hankali ta zayyane masu duk abinda aka gaya mata ance bata lafiya har yanzu batasan inda kanta yake ba tundaga ranar da ta ture Amrah
Shiru sukayi suna kallon yadda takeyi masu bayani har takai karshe ba wanda yace kala Ammar ne yace wani irin ciwo take Liya tace bansaniba Imad baice komai ba ya tashi ya bar masu wurin ba wanda ya damu da tashin da yayi saboda susan halinshi na miskilanci
Hamdan kam ko da yagama jin bayanin da Neela da Liya suka gama mashi sai ya fara sauke ajiyar zuciya kallonshi suka rinkayi da mamaki don abinda basu taba gani bane
Amrah ce ta shigo jikinta sanye da wani crazy jeans sai yar top kunnenta sakale da AirPod Dukansu kallon yar autarsu da damuwa ta bayyana a fuskarta sukayi Hamdan ne ya tashi yaje saitin da take sannan ya zare AirPod din kallon shi tayi ta dage mashi gira guda daya alamun lafiya
Cikin muryar shi mai dadi yace I found her Amrah kallonshi take da alamar bata gane nufinshi ba murmushi yayi mata sannan yace the beautiful young lady bude hakoranta tayi tana kallon hakimi tace like seriously daga mata kai kawai yayi Amrah zuwa tayi ta rungume Hamdan tana mai tsananin murna
Inna Hanne zaune tayi tana kallon Hurriya wadda fuskarta tayi fayau gashin kanta da girarta kwance sai bakinta da yayi pink ta riga ta gama sawa a ranta idan har Hurriya ta cike wata biyu bata samu sauki ba to zataje kauyensu ta taho da yayanta domin ya dubata
Tausayin yarinyar takeji sosai don yarinya mai gata kamarta yaushe ne Zata jira wani maganin gargajiya saidai da yanzu tana asibiti kasar waje Maganar Bintu da taji ya sanya ta dawo daga dogon tunanin da ta shiga ta kalleta sannan tace kindai ci abinci ko? Daga mata kai tayi
Wasba kije innani na kira wani karamin yaro ya gaya mata dauke kanta tayi daga kallonshi hawaye na zuba a idonta yau tasan dukan tsiya zataci bare tun dazu innani take kiranta Amman taki zuwa ta tsaya tana duba hanya ko zataga inda Hurriya zata bullo
Tashi tayi tana kuka tana share majina har tazo dan karamin gidansu dake cikin masarautar Qamar
Aiko tana shigowa innani ta rufeta da duka tana zaginta shegiya daga gidan ubanwa kike yar iska matsiyaciya tsintarciyar mage kin raina mutane ko ta cigaba da dukanta ba tausayi bare tausayawa har saida taga tana Neman daina numfashi ta daina dukanta.
Hurriya a hankali ta fara motsa yatsunta kafin ta bude idanunta Bintu dake zaune ta saki tagumi jin motsin da tayi daga Hurriya ya sanya ta kalleta cikin mamaki taga idon Hurriya bude suna kallonta da wani irin jin dadi da murna Bintu ta nufota girgiza mata kai Hurriya tayi tana mata kallon kada ki sake ki tabani
Daga mata kai Bintu tayi tana ta hamdala Hurriya kuma kallonta kawai take yadda take murna
Shiru Hurriya tayi tana tunanin wadanda suka sanyata jinya inda ace a masarautar Heral ne to babu abinda zai hana su bakunci lahira don abinda suka aikata hukuncinshi kisa ne how dare they messed with Princess wani evil smirk tayi don ita she’s someone that doesn’t take nonsense from anybody whether she’s princess or slave tasan sai tayi maganinsu ita batajira wani ya kwatar mata yanci da kanta da hannunta zata kwatar ma kanta yanci
Hurriya bata da dadi ko kadan idan ka tabata zatayi masu salon azabar da ko a masarautar Qamar ba’a tabayi ma waninsu irinta ba because they almost killed her lamoniyar dake gareta is not an ordinary lamoniya ciwo ne mai hade da poison wanda yake babbar barazana ga rayuwarta all this while tasan Allah ke tsareta and nobody knows about her health condition don ko a masarautar Heral ciwonta is a secret duk wanda yasan da ciwonta sai yabar masarautar tare dayin nesa sosai da masarautar zatayi masu abinda idan akace gobe su kara bazasu kara ba tayi alkawarin sai sun biyata with bigger price Dukansu sai sunyi jinyar da tafi tata tayi wani evil smirk tare da rufe idonta masu kyau tana taune lebanta.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace
By Khadija (KMU)
25&26
Bintu kallom Hurriya kawai take with pure love Hurriya lumshe ido tayi tana yamutsa fuska alamar jikinta na damunta Bintu tace bari in kira maki baba hanne ta kara dubaki
Bintu aguje taje kitchen ta kira Baba hanne wadda take tuka tuwo ai tanajin ance Hurriya ta farfado ta saki muciyar ta rugo aguje sai dakinsu Bintu murmushi tayi tana biyota a baya
A kwance suka iske Hurriya tadan tada kanta da bango ta lumshe idanunta dogayen lashes dinta kwance sai kyalli suke sai pink lips dinta da take dan cijewa Inna hanne kara kallon Hurriya tayi don ba karya tanada kyau kallonta ta karayi ganin irin kwarjini da kuma tsantsar mulki da yake bayyane ajikinta dama saidai idan baka gani Amman kallo daya zakayi ma Hurriya kasan jini sarauta ce bude idonta Hurriya tayi aiko da sauri inna Hanne ta sadda kanta kasa duk tasha jinin jikinta ta kasa motsi Hurriya kallo daya tayi mata ta kauda kanta
Hurriya Bintu ta kalla tace Bintu ki samo man ruwan zafi inyi wanka da sauri Bintu tace to inna hanne ce tace kije kitchen kice nice na aiko ki a zuba maki ruwan zafi Bintu juyawa tayi ta fita domin amso ma Hurriya ruwan wanka
Inna Hanne kam kanta duke a kasa Hurriya batasan ma Allah yayi wata hallita a wurin ba har Bintu ta kawo mata ruwan a hankali ta sauko kafarta wadda tayi mata nauyi da sanyi
Bintu har tazo zata taimaka mata girgiza mata kai Hurriya tayi alamar bataso da kyar ta iya tashi ta fara tafiya a hankali Bintu ta shiga ta ajiye mata ruwan sannan ta bata brush da macline sai sabulun wanka
Saida tayi brush sannan ta mika ma Bintu brush din ita kuma ta shiga toilet domin yin wanka
Ta dade cikin toilette tana wanke jikinta saboda kyankyamin da takeji saida tayi kamar zataji ma kanta ciwo saboda yadda take dirzar jikin sannan ta dauraye jikinta ta fito tana mai jin matukar kyankyamin kayan da ta maida
Hurriya dakinsu ta shigo inda tayi sa’a Bintu da inna hanne basu nan don inna hanne ce tacema Bintu suje kitchen tare domin dafa ma Hurriya abinci dajin haka Bintu taita murna sannan tabi inna hanne kitchen din kallon Bintu tayi sannan tace mi Hurriya tafiso acikin abinci shiru Bintu tayi sannan ta girgiza ma inna hanne kai alamar batasani ba don bata taba ganin Hurriya na cin abi da farin ciki ba don kullum cikin dacin rai take cin abinci kamar dole
Inna hanne murmushi tayi ta debo dankali wanda bai kai goma ba sannan ta fere.
Hurriya kallon ko ina tayi da yayi datti cikin yanayin natsuwarta ta amso tsintsiya wurin uwale da murna uwale ta farayi mata ya jiki daga mata kai Hurriya kawai tayi tazo ta gyara dan wurin ta share wurin tass
Sannan ta cire kayan jikinta vaseline ta shafa ta bude ledar kayanta ta zaro jeans dark blue sai farar top mai shara shara saida ta sanya inner wears hade da vest sannan ta sanya rigar
Kwanciya tayi ta mike kafafunta ta lumshe idonta tunani take neman ta farayi wanda sam babu lisaafin tunani a rayuwarta bude idonta tayi sai kam ga giftawar su barira kallonsu tayi Dukansu tana karantar su
Inna hanne ce ta shigo itada Bintu inna hanne rike da yar karamar kula mai kyau Bintu kuma hannunta rike da ruwa da plate
Da sallama suka shigo kallo daya Hurriya tayi mata tagane ta don itace matar da ta fara bata ruwan zafi. acikin zuciyar ta take tambayar kanta mi takeyi anan Shiru tayi tana kallon matar sai sadda kai take kamar munafuka tana durkusa mata alhalin ranar farko ba haka tayi mata ba
Inna hanne ta zuba mata faten dankalin da tayi mata wanda yaji kayan miya ta mika mata Hurriya kallonta tayi ba tare da ta amsa ba don haka Bintu da sauri ta amsa tazo ta mika mata amsa Hurriya tayi sannan tace Bintu ta miko mata ledar kayanta ba musu Bintu ta miko mata ledar kayanta spoon ta dauka cikin kayanta saida ta daurayeshi sannan ta faraci lumshe ido tayi ta cigaba daci wanda alama ke nuni da tana enjoying abinci
Dukansu kallonta suke inna hanne kanta a kasa saida taci Sosai sannan ta ture plate din Bintu ta kalleta sannan tace kin koshi daga ma Bintu kai Alamar Eh ta koshi
Pure water inna hanne ta miko mata alamar ta ajiye tayi mata inna hanne ta ajiye mata dauka tayi ta fasa ta shanye
Inna hanne ta miko ma Hurriya magani ba tare da tayi musu ba ta amsa tayi chokali uku ta mika mata murmushi inna hanne tayi tana mai jin dadi ganin Hurriya har tayi acknowledging dinta
Kwanciya Hurriya tayi tareda lumshe idonta tana mai neman fadawa duniyar tunani tana tuna lokacin da idan ciwon ta ya tashi yadda iyayenta ke shiga tashin hankali sosai ganin tana Neman ta fada duniyar tunanin wanda bata cika son haka ba don haka ta tashi wayarta ta dauko wadda ta dade batayi amfani da ita ba ta kunna waka sannan lumshe ido tana bin wakar fire on fire by sam smith a haka har bacci ya dauketa
Inna hanne bayan tagama aikinta ta shigo ta iske Hurriya kwance tana Bacci kamar karamar yarinya duk da bacci take amman zaka iya gane yadda ta hade fuska murmushi tayi sannan tace rigimar Duniya
Hurriya bayan ta warke saida tayi kusan sati biyu bata fara zuwa aiki ba don so take sai sanyi ya gama fita daga jikinta tasss don a lamarinta batasan weakness ko kuma ace wani ya gane weak point dinta shiyasa saida ta tabattar da ta warke tasss sannan zata koma aiki
Bangaren kam inna hanne kam hidima takeyi mata babu kakautawa don abinci masu dadi kala kala takeyi ma Hurriya Ruwan wanka kam kullum ita take tafasa mata ta kai mata toilet hatta kayan Hurriya kwana uku sukeyi sai ta daukesu ta wanke mata
Duk hidimar da take ma Hurriya bata taba ce mata ta gode ba don kamar daman dolen ta ne ita kuma Inna hanne bata taba kallon Rashin kulawar da Hurriyyar take mata ba as wani abu ba
Tana addu’a kullum Allah ya bama Hurriya ikon yadda da ita duk da ta fahimci Hurriyar kamar bata yadda da kowa ba
A bangaren su Imad sun baza ido suna taso suga ko ta ina zata bullo don Liya ta bincika masu ance ta warke don Hamdan da Amrah kullum sai sunce zasu je Amman yan’uwan sunki barinsu saboda zai zama abun fadi a masarautar duk dasu ba ruwansu
Fitowar ta daga wanka kenan daga ita sai zani sai kuma doguwar hijab dai dai zata shiga ciki su kuma suna fitowa Dukansu kallonta sukeyi tundaga dogayen kafafunta har zuwa kyakyawar fuskarta wadda babu fara’a saidai zallah kyau da annurin dake fita kafe su tayi da idanunta masu masifar kyau saidai baka iya jure kallonsu saboda yadda suke imnating danger flames ne kawai ke fita daga idanun acikinsu ba wacce bataji shakkarta ba saboda wani kwarjini da ta karayi masu
Saida ta kare masu kallo tass sannan ta shiga daga ciki inna hanne da Bintu na ganin dawowarta suka tashi inna hanne ta kalli Hurriya sannan tace mi zakiyi yanzu cewa tayi sallah shimfida mata dadduma tayi sannan suka fita domin bata wurin saboda shiryawa don sun san bata sanya kaya wani na kallonta
Wata doguwar riga ta sanya mai kyau saidai tana kama da abaya yau kawai taji tanason dan decent dressing dankwali ta daura ma gashinta wanda yake ta kamshin mai na soulmate don Hurriya na yawan wanke gashinta sai ta jirashi ya bushe ya gama shan iska tukuna ta shafa mai ta sharce shi.
Hijab ta sanya tayi sallah hade da rama sallahr da ake binta don daman yaune karshe idan ta rama la’asar tohm sauran magriba da isha’i
Tana gama sallahr inna hanne ta shigo wadda dama dama yanzu Hurriya na kula ta saboda tana kula da ita duk wani motives nata tana kallo duk da tana nuna halin rashin damuwa gareta ganin batada wani motives shiyasa ta kyaleta ta shigo rayuwarta kuma she knew she’s too smart itadin fa sunanta Hurriya Faisait Hamood she’s her fathers daughter wanda zai iya cutar da ita yanzu ai sai yayi babban shiri beside ba wanda yasan kowacece ita saidai she have to be very cautious duk dama ita din she’s always cautious
Turarenta ta fesa mai saukin kudi sannan ta fito domin samun iska wayarta kirar burin yar garuwa sai a hannunta sai earpieces dake makale a kunnenta wakarta takeji wasba ce tazo inda take tana kuka tana sharbar majina kallo daya Hurriya tayi mata taganeta
wasba yar karamar yarinyar ta dukar da kanta tanata sharbar kuka Hurriya batace mata komai ba har ta gama kukanta
Saida tagama kukan sannan ta kalli Hurriya ta washe mata baki tace kinyi kyau kinfi kyau a haka Hurriya batace mata kala ba Amman tana kallon yarinyar surutai wasba ta farayi mata tace ina kikaje ne kullum sai nazo na jira inga ko zaki zo Amman baki taba zuwa ba sai yau yar dariya wasba tayi tace bari muga kwana nawa nayi banganki ba hannunta ta fara kirgawa kamar wata yar baby har saida ta kirga kwanakin da tayi bataga Hurriya ba tashi tsaye wasba tayi idonta na cika da kwalla sannan tace ki yawaita yin addu’oi Saboda banason na rasaki irin fareedaa you’re beautiful ta sakar mata murmushi sannan ta ruga ta tafi
Kallon bayan yarinyar da take gudu tayi wadda damuwa ta bayyana a duka fuskar yarinyar Hurriya can kasan makoshinta tace what is wrong with the girl aranta tace ina ruwanki
Kallon mutanen da suke wucewa suna kallonta tayi itadai tanajin wakarta tana kallon kowa da kowa
Hurriya ta dade zaune a wurin don har saida taga magrib ta tafi zuwa dakinsu
Sallahr magrib tayi bayan tagama ta nufi part din Imad ganin taji sauki don haka bari yau ta koma bakin aikinta
Kitchen ta shiga ba sallama ba komai zubaida datake bakin kofa sakalau tayi da baki tana kallon Hurriya wadda bazaka ce mata yar aiki bace yadda tayi wani irin kyau kuma sai kamshi takeyi zubaida bakin ciki ne ya turniketa don bata manta yadda uban gidanta da Hamdan suka shiga damuwar rashinta ba
Ta tsani Hurriyar nan don batada mutunci ko kadan gashi duk inda taje ita ake kallo duk sauran mutanen dake zaune sun zama banzaye indai tana wuri haka ko su Hamdan basu tabayi mata magana ba karewa ko maganar Imad bata tabaji ba Amman ga yarinya da tazo jiya jiya tafi ta matsayi abun gaskiya yana matukar bata mata rai Amman zatayi maganinta very soon don ba zata zuba mata ido ba
Duk aranta take wannan sake saken
Baba RaBI ce ta kalli Hurriya tace ya jiki kinsha ciwo ko daga yanayin maganar ta zakasan ba har cikin ranta tayi maganar ba jiran amsar Hurriya take saida tana juyowa taga batanan Dariya suka saki Dukansu yan kitchen din shiru baba rabi tayi sannan ta daure fuska
Store ta shiga ta debo basmati tayi continental rice sai vegetables spaghetti wadda taji namomi sai kamshi take kowa kallonta yake amman ita kamar batasan anayi ba saboda earpiece ne ma makale a kunnenta
Saida ta gama suka jera trays din akace su shiga sukai masu ba musu Hurriya tabi bayansu da nata tray din
Basu tarar dasu a falo na farko ko a parlour na biyu basu nan sai a parlon na uku inda suka shiga kansu duk a kasa
Hurriya kallo daya tayi masu ta dauke kanta suka shiga jera abincin
Saidai tanajin idanun dake binta
Ludo sukeyi Dukansu su shiddan kallo daya zakayi masu kasan suna cikin farin ciki kuma suna enjoying game din Hamdan ne yake kokarin cinye game din Neela kuma kiri kiri taki bashi dama
Tunda Hurriya ta shigo Imad yasan ta shigo don lokacin data juyo ta kallesu with distaste yana kallonta saidai bata lura dashi ba shidai yana mamakin halinta na iko da raini wayau Because he never came across someone like her ba all his entire life komai nata ya bambamta bata tsoron kowa acikinsu abinda takeso shi takeyi yasan tana aiki yanda ya kamata indai ta fannin aiki ne baza a kamata da laifi ko ha’inci ba
Bata gaishe da kowa sannan bata kula kowa he can’t read her duk yanda yaso ya dan fahimce ta ya kasa saboda ta rufe kowace kofa da dan mutum zai iya karantar ta
Saidai akwai abinda har yanzu yake bude wanda ta kasa rufe shi duka she’s lonely saidai kallo daya idan kayi mata baza ka gane kadaicin dake tattare da ita ba saboda yadda ta rufeshi ta ko ina
Liya ce ta kallesu tace please Quit the game for now your food is ready Ammar ne yayi saurin tashi yace daman yunwa nikeji ya nufo din dining su Hamdan da amrah suka biyo baya kowa yaja kujerar shi ya zauna
Neela ce tazo ta zauna sannan Imad ne karshe Ammar ne ya dago zaiyi magana aiko cikin sa’a idonshi akan na Hurriya wadda itama shi take kallo tana karantar shi saidai he looks very familiar to her kamar tasanshi kallon imad tayi wanda ya zauna a wani miskilance ya lumshe ido yanajin saukar idonta masu kaifi shima kallonshi tayi Dukansu tasansu amman A ina?Ganin idan fa tanason tagano inda tasansu sai ta koma duniyar tunani wadda batasan hakan kwata kwata
Ammar dariya yayi yace Hurry ya jiki please come and join us
Hamdan yanajin ance hurry yayi saurin dagowa kamar hadin baki Dukansu suka rinka kallonta Amrah ce ta taso tazo wurin Hurriya wanda ta kasa boye murnarta alamun zata rungume Hurriya tayi saurin ja baya sannan tace kada ki tabani idan ba haka ba marinki zanyi daga mata kai amrah tayi stiill tana farin cikin ganinta
Bude baki kowa yayi don jin furucin Hurriya na zata mari amrah saidai ba wanda yace kala saboda sunsan halin amrah indai akan abun da takeso ne yanzu ko maganar banza idan sukayi ma Hurriya to ba wanda zai kwana lafiya don idan ta farayi masu rigima da kuka to sai Allah
Bude bakinta amrah tayi sannan tace Hurry please grant me a wish tana daga mata hannu alamar don Allah ta taimaka mata shiru Hurriya tayi ganin tayi shiru amrah sai tayi tunanin kilan Hurriya batajin turanci sai tace don Allah kiyiman abu daya
Hurriya frowning brows dinta tayi ta kalleta mockingly tace mi kikeso dariya Amrah tayi tace don Allah muci abinci tare shiru wurin yayi kowa na jiran amsarta Ammar ne yayi breaking silent din ta hanyar cewa haba yar mai kyau please join us yana karya murya hade da kanne mata ido kamar mace trying to look funny Hurriya gyara tsayuwarta tayi sannan tace you Better stop acting that way if not I promise you’ll be a transgender by tomorrow morning saboda ka koma kamar wata amarachi Dariya kowa ya dauka shikanshi Imad duk yanda yaso kada yayi dariya saida ya dara
Neela a ranta take maganar muryar Hurriya ta hadu ba karya don wani accent mai matukar dadi take amfani dashi wurin magana Ammar ba karamin dadi yaji ba yadda tayi mashi magana don bai tsammaci hakan ba don yarinya ya lura bata magana kwata kwata don idan bakayi dagaske ba zakayi tunanin bebiya ce .
Hurriya zagayowa tayi taja kujera ta zauna kowa serving abincin shi yayi
Serving ta farayi ahankali don komai ahankali ta zuba tundaga kan appetize komai nata accordling takeyinshi cikin tsari ba wanda bai kalli yadda ta fara cin abincinta ba don da appetizer ta fara sannan taci kadan shima main dish kadan taci yadda zata ida cin komai don a doka tun suna kanana ake koya masu table manners don shine yake determining they are from royalties kuma not an ordinary royal family
Don haka they’ve to be always mindful of their table manners duk wanda yaga yadda take cin abinci yasan she’s from an elegant family because he the way she held her spoon ba kowa ya iya irinshi ba
Ganin almost all of them are staring at her plate ya sanya a hankali tace bloody hell what am I doing cikin wayau da dabara ta lalata plate din ta canza salon cin Abincin.
They ate in silence tana gamawa tasha ruwa sannan ta tashi kallonta Dukansu sukayi Hamdan ne yazo yasha gabanta sannan yace Hurriya we’re not done talking zaki bani diyarkin?i like you wani irin kallon banza Hurriya tayi mashi Hamdan turo mata baki yayi yace please Hurriya banza tayi dashi ta kama gabanta.
Zubaida da suka gama kallon duka scenes din abinda ya faru bakin ciki kam zuciyar ta har kuna takeyi hmmm kawai take cewa cikin ranta
Hurriya kam tana komawa ana kiran sallahr magrib
Alwala tayi sannan tayi sallah bayan tagama ta nufi babban kitchen tareda crossing hannunta abayanta kallon yadda kowa yake hada hada tayi haule reza naganinta tazo wurinta saida ta kalleta tace yar nan naji ance kinsha ciwo Hurriya daga mata kai tayi
Kallon Haule reza tayi sannan tace aiki zamuyi zan biyaki haule najin kudi ta daga kai Hurriya bayani tayi mata yadda komai zai kasance
Sannan ta koma daki Bintu ta bama kudi ta siyo mata sabuwar reza da omo klin sai lemun tsami da gishiri kallonta Bintu tayi tana mamakin mi zatayi dasu saidai tasan kota tamabaye bata da amsa indai Hurriya ce don haka taje ta siyo mata duka abinda ta aiketa
Isha’i Hurriya tayi sannan ta sanya earpiece a kunnenta tanabin waka Bintu tazo tayi mata saida safe sannan ta nufi makwancin ta
Saida dare yayi sannan haule reza tazo da kularta wadda ta juyo tafasaasun ruwan zafinta
Wurin Hurriya taje inda Hurriya take kwance don kamar ita take jira tanajin nishinta ta tashi
Haule reza ta kalleta tace muje Hurriya daga ita sai hijab ta tashi hannunta rike da abinda ta aiki Bintu suka nufi wurin wasila don da ita takeso afara Hurriya tsayawa tayi tana kallon yadda komai ya fara gudana duk yadda Hurriya ta fada ma haule reza haka ta fara gudanar da ayyukanta don saida ta fara Gangarawa ta daura ma wasila kyale ta dode mata baki wanda tana tabata ta tashi daga Bacci tana zare ido saitin fuskarta wasila tazo ta kalla sannan ta kalli hurriya tace ayi anan? Hurriya girgiza kai tayi
Haka haule reza ta rinka tambayarta saida tazo kan kafafunta sannan Hurriya ta daga mata kai Hurriya matsowa tayi tanuna mata Daidai inda zata yanka wurare biyar ne wanda duk idan aka taba ma mutum shi akafa tohm sai Allah haule reza kallonta ta rinkayi tana kallon rashin tsoro da rashin tausayin dake cikin idonta
Wasila kam ihu ta rinkayi Amman sam baya fita kiyi mana inji Hurriya ba bata lokaci haule reza ta daura sabuwar reza mai matukar kaifi sannan taja wurin da karfin tsiya wani irin azababben ihu ta saki Amman to no avail saboda baya fita baba haule ta riketa
sannan Hurriya ta fasa klin dinta guda daya ta zuba mata shi wani irin uban kara ta saki tana shure shure Hurriya murmushi tayi sannan ta barbada mata gishiri ta hada da matsa lemun tsami a ciwon
Saida ta sanya haule reza tayi mata yanka biyar sannan ta barbada mata ingredients dinta
Tun tana kuka har kukan ya daina fita ba imani kwata kwata tattare da Hurriya ta bude kular nan ta debo tafasassun ruwa ta watsa mata akafafunta duka biyun ai wasila suma tayi
Haule reza kallon irin launin azabar da Hurriya take mata tayi tana mamakin rashin tsoro da rashin imanin yarinyar nan. Ta tabbata zuwa gobe kafarta tayi mummunar konewa .
Haka Hurriya ta rinka binsu saida ta tabbata duka tayi masu azaba iri daya don duk saida haule ta daure masu baki sannan tayi masu yanka biyar biyar Hurriya ta zuba masu omo hade da gishiri da lemun tsami sannan ta kona kafafun da ruwan zafi
Bayan sun gama tace a a aske ma Hansa’u gashin kanta tass ita kuma wasila da Barira har yanzu tana binsu bashi ta wuce ta nufi makwancinta
Haule reza kallon bayanta tayi yadda take tafiya kamar tana tausayin kasa haka take takawa tunda take bata taba ganin mutum marar imanin Hurriya ba
Duk ihun da suke da neman ceton rai da suke ko dar bare gizau haka Hurriya ta rinkayi masu launin azaba don tasan ba wanda bai suma ba acikinsu
Tabb inji haule tace akwai kallo dai wurin nan saidai sune suka ja ma kansu daman ance in kasa wata ba kasan wataba.
Hello fans yanzu zan rinka posting from Monday to Thursday saidai daga Friday zuwa Sunday ba post
Idan kuma kun fiso a rinka skipping rana daya tohm I will be waiting for your opinions
Love xoxo❤️👼🏽
[12/02, 4:54 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace
By Khadija (KMU)
27&28
Kwanciya tayi Hurriya tareda sauke ajiyar zuciya don yanzu ne zata iya Bacci cikin dadi don idan batayi masu hukunci ba gaskiya ba sunanta Hurriya Faisait Hamood ba.
Haule reza kam tana mamakin inda yarinyar nan ta samo kalar launin azabar datayi masu don bata taba ganin hakan ba saidai fa ba karya Hurriya muguwa ce tace sannan ta nufi makwancinta
Yau da safe da aka tashi aka iske duka yan click dinsu Barira suna jinya don kusan ihun wasila ya tadasu don azaba ta ko ina takeji kuka kam yinshi take kawai don a halin da take ciki da za’a cire kafar to da tanaso indai har zata rabu da ciwon da takeji.
Barira kam har garin Allah ya waye itada suwaiba to asume suke saida aka samu da kyar suka farfado irin ciwo daya ne Dukansu suke fama dashi Dukansu saidai kowa na mamakin wanda yayi masu wannan danyan aikin
Hurriya yau ta samu ta tashi da wuri don har sallahr asuba ta samu damar yinta da wuri. Tanajin sai jaje akeyi Bintu ce tazo da gudu tana haki ta kalli Hurriya sannan tace naji abinda ya faru gasu barira Amman don Allah kece?kice bake bace don Allah kice man haka Hurriya kallonta tayi sannan tace nice Bintu And idan suka kara koda hararata abun da zanyi masu sai yafi wannan Bintu kallon Hurriya tayi sannan tace haba Hurriya miyasa zakiyi haka kinga kafafunsu idan kika gani sai sun baki tausayi wallahi dama kin kyalesu sunje da halinsu tunda yanzu suma zasu ce zasu rama kema zaki ce zaki rama kuma ance sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma ma kinsan kaura saurayin barira ne sai ance shaho saurayin Hansa’u ne
Bintu batasan duk maganar da takeyi Hurriya tayi tafiyarta
Juyawar da zatayi taga ba Hurriya saidai ganin inuwar Hurriya tayi
Hurriya tana fitowa saiga hauke reza wadda ta taya danyan aikin jiya
Kallon Hurriya tayi tana washe baki sannan tace Hurriya naga sako nagode kuma don Allah inson kibani dama yadda idon akace gobe su kara to bazasu kara ba
Hurriya shiru tayi mata har tagama babatunta batace komai ba
Kitchen taje inna hanne na kallonta tazo tace Hurriya an tashi naji danyan aikin da kika aikata baki kyauta ba
Hurriya dage girarta tayi tace banzo don inji kyautawa da rashin kyautawa wurin ki ba malama ki zuba min ruwan zafi in kama gabana
Inna Hanne kallonta take kamar statue zata iya cewa tunda Hurriya ta tashi daga rashin lafiya to yaune ta samu jin muryarta mai tsayi har haka inna hanne wadda tayi curr tana kallonta tsarki ya tabbata ga Allah sannan tace lallai kedin gimbiya ce duk aranta take maganar don kwata kwata bataji haushi ba
Inna Hanne daukar bokitin tayi ta zubo mata ruwan zafi suka jero tare inna hanne rike da ruwan Hurriya kuma rike da kayan wankanta har suka zo toilet
Hurriya wanka ta shiga tayi sannan ta fito ta nufi daki
Sai kallonta akeyi don ba inda maganar bataje ba ita tayi masu Hansa’u wannan hukuncin wasu ta burgesu wasu kuma ta basu tausayi wasu kuma zaginta kawai sukeyi but who cares
Shiryawa tayi cikin uniform dinta wadanda sukayi mata kyau Sosai
Comb ta dauka ta tsaga kanta hudu sannan tayi kalaba manya manya guda hudu wanda suka sauka har gadon bayanta nade gashin tayi har saida ya dawo Daidai keyarta sannan ta fesa turarenta ta fita
Sashen imad ta fara zuwa aikam cikin sa’a ta gyara ko ina har dayan dakin shi wanda yake bacci
Tanajin karar ruwa hakan ya tabattar mata da yana toilet don haka tana gama mopping ta fito ta wuce part din zinariya wanda tunda ta fara aiki bata taba gifta kofar data wuce ta kitchen ba
Don haka tana zuwa tayi wanke wanke sannan ta fara hada breakfast tanajinsu suna gulma murya can kasa kasa Amman sautim maganar su radam a kunnen Hurriya wata a cikin kuyangin ce tace hmmm labari da dumi duminsa fa
Kowa cewa yayi munajinki subira ta kusa dawowa fa ance sati mai zuwa zata dawo, wata acikinsu ta fara salati tana jajanta masu subira fa suna cikin matsala ta dade batazo kasar nan ba don haka dayawa kilan sun manta wacece subira AI kuma ba lallai kowa ya iya manta subira ba saboda irin record din da ta bari
Hurriya duk tanajinsu wata acikinsu tace shekara fa ta kusa zagayowa shiru Dukansu sukayi suna zare ido wata acikinsu tace nidai bani da kyaun da za’a rasani a masarautar nan
Jakadiyar zinariya ce ta shigo ta kallesu tace me kukeyi ku wuce ku kai abincin Dukansu daga mata kai sukayi itadai Hurriya na aikinta
Tana gama aikin ta fita ta nufi inda suke wanki tana zuwa ta iske wasba tana wasa da dan icce tana ganin Hurriya wasba ta saki iccen ta rugo wurinta tana dariya tace tun dazu nike jiranki Hurriya bata ko kalleta ba tayi gaba inda ta saba wanki
Kayan ta fara wankewa wasba kam ta samu wuri kusada Hurriya ta zauna tana ta bama Hurriya tatsuniya mai ban dariya duk intayi sai taga Hurriya fuskarta daure sai tace bari in canza haka wasba ta zauna tana bama Hurriya labarai masu ban dariya Amman Hurriya ko murmushi batayi ba bare dariya
Wasba kuma taki tafiya sai can wani yaro yazo ya kirata ance ana kiranta tashi tayi ta ruga tana tsalle ta juyo tayi ma Hurriya alama da hannu Inasonki
Hurriya tsoki tayi ta cigaba da wankinta tana waka
Yunwa ce ta fara galabaitar da Hurriya saboda tun tashinta yau bataci abinci ba don haka tana ida shanya kayan ta nufo dakinsu
Harabar wurin tagani tasan cewar ba lafiya ba don haka ba tare da bata lokaci ba kutso wurin
Kowa ita yake jira a taron mutanen da akayi ta riga tasan da haka bata damu ba taja kai tana niyyar shiga wurin shaho ne ya tare hanyar yana watsa mata idanunshi masu firgita ma mutane lissafi itama kalloshi tayi tare da tsirtar da miyau a kafarshi tace disgusting kaura ne yazo a 360 don ranshi yana matukar tafarfasa da wannan makirar yarinya mai kyau sai kace ita tayi kanta duk masarautar nan waye ya isa ya taba barirarshi ya kwana lafiya babushi
Sai ita ta watsa mata tuwo a fuska gashi kuma tayi masu wani irin salon launin azaba tabbas yau sai ya wulakanta
cikin zafin nama kaura ya daga dorinar shi zai zuba mata Hurriya da yau itama ranta yagama baci don bazata iya tuna when last tayi irin bacin ran nan ba ta rike dorinar da karfi tanayi mashi matsiyacin kallo wanda ke dauke da tsantsar mulki da kuma izza tace the moment you beat me with your filthy hands you’re going to be executed ta matso tana mashi whispering tace kana kuskuren dukana to hukuncika kisa
Ta saki bulalar ta tsotsi bakinta cikin isa da mulki tace duk wanda bai fasa dukana ba acikin ku Amman ku tabbata duk wanda yayi gigin kara tabani a masarautar nan da sunan duka to sai ya amshi laifin shi na taba lafiyar Hurriya Faisait Hamood this is a promise and try me and see ta watsa masu wani wukantacen kallo tace jakuna daku matsiyata ta shige cikin dakin tana barin kowa baki bude
Kaura da shaho kam kamar wasu duwatsu haka sukayi don sungani à idanun yarinyar duk wanda ya kara tabata to kilan lahira zai bakunta yadda ta furta kisa kuma yadda ta nuna hukunci mai tsanani mutum zai amsa saidai tayi matukar kunyata su
Shiru Dukansu sukayi tareda juyawa suka tafi cike da borin kunya
Ikon Allah yan wurin kowa ya rinka fada to miyasa basu daketa ba mi tace masu har haka watsewa akayi kowa da alajabin wannan Hurriyar
Sa’ade da karime suna kallon komai sa’ade ce tace wallahi na tsani waccar shegiyar Hurriyar karime tayi wata dariya tace naki akeji amman ki bari zamu yi maganinta a masarautar nan tunda kowa ya gagara maganin shegiyar
Bintu ce ta gifto matsawa tayi saitin su tace kafin kuyi maganinta ni Zan sanya tayi maganin ku mutanen kawai tana kallon yadda suka zare ido alamun shakka dariya tayi ta shige ciki
Sallah ta iske Hurriya nayi Bintu kallon yadda take sallar kawai tayi ta girgiza kai ta zauna tana jiran tagama sallahr
Bayan ta sallame sallahr ta juyo ta kalli Bintu wadda take gyangyadi murmushi Hurriya tayi wanda batasan tayi shi ba don da sauri ta maidashi sannan tace Bintu Bintu adan firgice Bintu ta tashi Hurriya kallon katifa tayi sannan tayi ma Bintu alamu data kwanta
Ba musu Bintu ta kwanta wani irin bacccin gajiya ya dauketa murmushi Hurriya tayi sannan ta dauki wayarta da ta amso chargy dazu wurin haule reza
Bude wayar tayi wani tunani yazo mata da sauri ta cire tunanin waka ta kunna ta kishingida nesa da Bintu
Inna hanne ce tazo da plate da kula na abinci kallon Hurriya tayi da ta lumshe ido tanajin waka sam batason wakar da Hurriya keji don akwai abubuwa da yawa gabanta karatun AlQur’ani ya kamata ta rinka ji ba waka ba Amman Hurriya is not helping matters
Murmushi tayi ganin yadda take bin wakar
Inna hanne tace Hurriya Hurriya saida inna hanne ta daga murya Sosai Hurriya ta tashi kallonta tayi ta dage mata gira alamun lafiya shigowa tayi tare da ajiye kular sannan tace abinci na kawo maki daga mata kai Hurriya tayi sannan ta koma ta kwanta ta dade bata motsa ba don har inna hanne ta tafi idonta rufe
Saida taji yunwa na damunta Sosai sannan ta bude idonta tare da cizon lebenta ta sauko ta zuba shinkafa da mai da yaji hada maggi mai tauraro
Kamar tanajin tausayin cikinta haka ta fara cin abinci har saida taji ta koshi sannan ta ajiye cokalin tasha Ruwa
Yau ya kama wata daya kenan da kona masu su barira da Hurriya tayi su kuma su shaho da kaura tunda Hurriya tayi masu warning dinan basu kara zuwa ba Amman sun kudirta aransu abinda zasuyi mata mai muni ne
Bintu kam da Hurriya sun zama tamkar yan uwa don Hurriya har ta fara bude mata wasu abubuwan duk da she’s not allowed to do that saboda she’s not to trust anybody in this life saidai mi after all she’s human being too tana amsa sunanta yar adam don haka itama tanada émotions kamar kowa kawai ta iya boye émotions din nata saboda emotions dinta babbar barazana ce a rayuwarta bata yadda ace wani Abu yafi karfinta ba tunda ita har takeda kanta so she have full control of herself don haka she control everything around her herself her maids kowa da kowa saidai yanzu kanta kadai zata iya controlling
Bintu ba karamin son Hurriya take ba don ita kadai take kallo taji sanyi a rayuwarta ko kuma ince a masarautar Qamar bata da kowa sai Allah sai Hurriya
Ita kanta Hurriya idan har kasan mi kakeyi yadda take kallon Bintu kadai zai nuna maka tana matukar tsantsar Qaunarta don idonta har wani gleaming na pure love yakeyi
Yanzu haka ma Bintu ce ta siyo masu awara da rake itada Hurriya
Zaune suke saman wani dakali su biyu Hurriya ba dankwali a kanta gashin kanta duka ya zuba a gadon bayanta don bata daureshi ba
Kallon wurin da wasba ke zama tana wasa da icce Hurriya tayi kafin ta sanya hannu cikin awarar wadda ta tauna sai kuma tayi murmushi wanda duka dimples dinta suka lotsa dan gleam din dake a gefen idonta ya kara fitowa Bintu lahaula wala Quwatta illah billah kawai take ambato Lallai babu karfi da iko sai gurin Allah wanda yayi hallitar nan ba tare da makusa ba ita Hurriya wani irin kyau ne take dashi har haka?
Shin gwara da ya kasance bata dariya da ace tana dariya tabbas da dariyar ta zamar mata babban kalubale a rayuwarta acikin masarautar wani irin kyau take gani kota Ina gaban Bintu banda faduwa ba abinda yakeyi ita mace ma kenan wai tohm inaga namiji
Hurriya ta dage girarta daya ta kalli Bintu sannan tace kallon na miye?
Ba komai inji Bintu kasa rikewa Bintu tayi don da farko batayi niyyar fadar abinda ke cikin ranta ba cewa tayi MashaAllah Hurriya kina da kyau Hurriya batace mata komai ba ta kara sanya a wara a bakinta.
[12/02, 4:54 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace
By Khadija (KMU)
29&30
Saida taci awarar kusan guda hudu sannan tasha raken wanda aka daddatsa guda biyu
Bata Qara cema Bintu komai ba ta sauko Bintu nagani Hurriya ta fara tafiya itama ta sauko tana cewa Hurriya jirani banza Hurriya tayi da ita aiko Bintu ta rugo ta samu suka jera tare tana haki
Tana shiga aka fara kiran Sallahr magriba sallah sukayi sai ga inna hanne ta shigo wadda yanzu Hurriya na bata amsa yanzu idan tayi mata magana kallonsu tayi Dukansu Hurriya nagama sallah ta linke hijab sannan ta dauki wayarta ta makala earpiece inna hanne tace Hurriya kidan rufe kanki don Allah tunda dare yayi kinji
Ko kallon inda take Hurriya batayi bare tasan ran amsa ta fita zuwa part din Imad
Ba inda ta tsaya sai part din Imad wanda zasuyi tafiya gobe kuma yace mata tare zasuyi parking she must come
Ba kowa parlon don haka ba inda ta tsaya sai bedroom dinshi yana zaune ya mike kafafunshi yana amfani da MacBook sai Qamshi dakin yake na turaren wuta mai sanyin dadi
Lumshe ido Hurriya tayi sannan ta bude idonta masu kyau ta tsotsi lebenta
Batace mashi komai ba ta bude duka wadropes dinshi akwai wani wuri dake da jerin tarin designers suitcase, Daya daga ciki ta dauka mai matukar kyau da tsada na Bottega veneta ta ajiyeshi sannan ta fara shirya mashi kaya tunda ta shigo yake kallonta ta karkashin ido don ba karamin kyau tayi mashi ba kallon doguwar sumarta yakeyi sai kafafunta da suke waje don rigar da ta sanya tsaga gareta sosai
A ranshi yake tambayar kanshi who is this mysterious girl wadda take neman dagula mashi lissafi ji wata seductive shiga da tayi wadda duk wanda ya kalleta sai yaji wani abi tunda ga kanshi har zuwa tafukan hannunshi
Don yanzu yafi kowa sanin Hurriya da zai iya cewa dagangan takeyi saboda tayi seducing dinshi ko kuma ta ya kulata
Tunawa yayi ko kallo na biyu batayi mashi bare har ta kasa dauke idonta daga gareshi don ko gaisheshi batayi ba wani dogon conversation din da ya taba shiga tsakaninsu bare harma yace donshi takeyi
she’s so unique and classy may that’s why he started to like her
Hurriya tanajin idonshi akanta murmushi tayi sannan ta cigaba da hada mashi kayanshi
kaya take shiyar mashi masu matukar tsada da kyau kallon yadda take komai yake yi
Hurriya tunanin da batasan tayi saida tayishi dan the more tana kallon su Imad da Ammar take ganin tasansu and the most funniest thing ever shine tagano imad dasu Ammar maternal cousins dinta ne mamansu da babanta uwarsu daya ubansu daya they used to come too their palace lokacin suna yara
Ammar and Imad are her best friends kuma sune favorite cousins dinta ba kamar Imad saboda lokacin they don’t get along but deep down she was his favorite person itama Hurriya haka yake a wurinta she used to annoyed him har sai ta tabbatar da ta sanya shi kuka tukuna saboda zuciya gareshi idan tayi mashi abu saboda bacin rai shi kuka yake Bata iya kirga yadda takesa shi kuka sai kuma ta dawo tana bashi hakuri Ammar yayi ta yi masu dariya
She doesn’t get along with the female twins duk da sune mate dinta Amman basa shiri saboda suna mata kallon mutum mai girman kai da nuna isa Because she’s from Heral palace
Ita kuma Hurriya she doesn’t care at all don ko da ace sun shige mata tohm zalintar su zatayi because alokacin Hurriya muguwa ce duk salon mugunta ta iyata mamansu itace favorite person dinta don tana matukar son Aunty Banafsha saidai tana shekara goma rabonta da su Imad da Aunty banafsha lokacin zataje Mexico akwai fashion school din da zatayi acan tohm kusan kowa saida yazo a yanuwanta sukayi bidding dinta farewell murmushi tayi tana tuna childhood dinta a hankali tace how times flies
Imad yanajin sautin murmushinta shima murmushin yayi daman tana dariya kodai he misheard her ne gaskiya baiji da kyau ba
Duk abinda Hurriya tasanya mashi mai kyau ne da tsada tunda yake bai taba ganin Mai great fashion sense dinta ba how did she know expensive abubuwa irin haka kuma tasan duk yadda kayan zasu bada ma’ana who is she?what is her identity?only God Knows sai kuma Hurriya din da kanta.
Bayan tagama ta zage komai sannan ta gyara komai ta juyo saitin Imad wanda ya kauda kanshi saboda kunyar data kamashi yana kallonta gyara murya yayi sai ya rasa mi zaiyi ita kuma Hurriya taki ta daina kallonshi Dage girarta tayi sannan ta rungume hannayenta tace why are you staring at me kallonshi takeyi da idanunta masu kyau tana tsotsar lebanta imad shima gyara murya yayi yace wake kallonki yana dage gira daya harar shi tayi in an annoying way tace you manah sannan ta fita shiru Imad yayi yace kada fa ace wannan yarinyar ta rainani lallai ma I will Deal with her
Hurriya tana fitowa ta iske amrah da Hamdan sai ammar a balcony suna zazzaune
Ammar ne yace hurry ba gaisuwa banza tayi dashi ta cigaba da tafiya da sauri Hamdan da Amrah suka taso Amrah tayi saurin rike mata hannu Hurriya kallon Amrah tayi alamar ta saketa da sauri Amrah ta saki hannun Hurriya
tana rike kunne alamar tayi hakuri daga mata kai Hurriya tayi
Hamdan ne yace Hurriya Guess what?shiru tayi batace komai ba bata rai Hamdan yayi yace Hurriya you’re not funny at all I won’t share the story with you shrugging kafadarta tayi though tanason taji mi zai fada mata because she’s starting to like the twins saidai mi batada lokacin batawa tafiyarta ta fara da sauri Hamdan yasha gabanta yana bata fuska dariya amrah ta farayi masu
Hamdan kallonta yayi sannan ya kara cewa guess what?ganin tayi banza dashi ya sanya yace tunda bazakiyi guessing ba ni bari na fada maki we’re going to Ethiopia 🇪🇹 tomorrow In Sha Allah Gaban Hurriya ne ya fadi don batasan inda zasuje ba sai yanzu da yake fada mata ta dai san gobe zasuyi tafiya Ahankali batare da tasan maganar ta fito ba tace ethopia daga mata kai yayi sannan yace mata eh manah Do you want to know why I was so happy ? Daga mashi kai tayi alamar ehhh murmushi yayi yace I will get to see Layla Khasheem she’s my cousin all this while bansaniba sai ba’a dade ba fa Ammar yake fadamin suka barni inata hauka ashe yar uwata ce ma it will be my first time to be in Heral palace I can’t wait oo har na kosa naga yanda masarautar take don labarinta da ake bani na kasa yadda akwai masarauta irin haka i will get to see it with my own eyes and zanga my grandparents sannan yayi dariya
Gaban Hurriya banda faduwa ba abinda yakeyi Heral palace can zasuje kenan gobe itafa? Heral palace nan ne fa asalinta nan ne gidanta Amman ta gagareta Because of abubuwan da suka faru
Shiru tayi wanda ta fada duniyar tunani past dinta iyayenta wanda batasan ta tuna komai da ya faru Amman ya zatayi karar hoton da tajine ya sanyata dawowa daga duniyar tunanin da take neman fadawa kallon Hamdan da wayar dake hannunshi kirar iPhone 14proMax tayi inda ya dauki hotonta shida ita Hamdan yace idan mun isa i will tell Layle Khasheem about you sai in nuna mata picture dinki taga yanda kuke kama Da wani irin bacin rai Hurriya ta amshe wayar tareda yadda ta kasa Qarar fashewarta kawai akeji
Idonta har ya canza launi saboda tsananin bacin rai Hamdan shima ranshi ne ya fara baci don shima badai zuciya ba kallonta yayi da muryarshi wadda bata wasa ba yace Hurriya how dare you yana mata wani banza kallo itama kallon takeyi mashi tace And how dared you took a picture of me without my consent kallonta Hamdan yayi wanda yake nuna tsantsar bacin rai yace what did you think of yourself girl you’re nothing here but just a filthy maid me kika dauki kanki bari kiji in fada maki ma if You’re feeling great you’re not great don kinga anayi maki magana ba komai ya sanya ake maki magana ba saboda kinyi man kama da Layla Khasheem isn’t it something great a whole prince took a picture of à fouling smell maid like you bari kiji you stink and you’re disgusting kuma kedin ba komai bace face kaskantaciyar baiwa wadda ta fito daga tsatson kaskantattu mutane shas bai ida fada mata kalmar shasha ba yaji saukar maruka guda biyu a tare bai ida juyowa ba ya karajin ta sakar mashi lafiyayyen maruka biyu kara daga hannunta tayi ta kara sauke mai wani marin tana kallonshi da idanunta da suka kada sukayi jawur kamar an zuba mata barkono muryarta har wani shakewa take saboda bacin rai tace And who are you to say that Hamdan shima muryar shi ba dadi yace how dared you slapped a prince with your stinky hands ya nufota alamar zai mareta Amrah ce tayi saurin rikeshi tace haba Manah Hamdan calm down stop please miye haka Ammar ne yazo wanda tun farkon abun yana kallon abinda ya faru duk da Hurriya ce bata da gaskiya Amman sam Hamdan bai kamata yayi mata irin rashin kunyar nan ba kuma ta wani fannin shima Hamdan baida gaskiya
Kallon Hurriya yayi tare da matsowa inda take da niyyar bata hakuri wata irin tsawa ta daka mashi looking so angry 😡 tace Ammar don’t say a word here it’s between me and Hamdan kuma wallahi sai yaji ajikinshi this is a promise gobe idan akace ya karayi ma wani rashin kunya bazai kara ba ta ida maganar da wani irin bacin rai ta kama gabanta
Hurriya har bata kallon gabanta how dare him take ta cewa how dare him har tazo dakinsu duniyar tana bata haushi
Hamdan kam wata irin ajiyar zuciya ya saki sai kuma ya fashe da kuka tare da rungume Ammar yace inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un Ammar what did i did na kwafsa did i just yell at her wani kukan ya kara saki yace zaginta fa nayi da iyayenta na bani ya zanyi idan Hurriya ta daina kulani i just like her why? Amrah da takejin conversation dinsu ta harareshi in a disgusting way tayi tafiyarta ta barsu
“Ammar patting bayan shi ya rinkayi yace it’s okay kadaina kuka kada ka damu zatayi hakuri” a hankali ammar ya rinka kwantar mashi da hankali tare da yi mashi alkawarin zasu bama hurriya hakuri gobe kafin su tafi daga mashi kai kawai ya rinkayi har ya samu ya lallashe ya rakashi chamber dinshi
Hurriya ba abinda tayi face kwanciya tare da lumshe idonta duka abinda ya faru na dawo mata hakan da tayi shine Daidai idan har ya nuna ma wani ilta acikin Heral tohm tabbas she will be at risk rayuwarta zata kasance cikin hadari
Mutane iri biyu ke nemanta da masoysnt da kuma makiyanta kuma ita kam batasan kowa yaganta a cikinsu she will wander around the world she will be freed from all those fights of powers zata tsaya a masarautar Qamar har taga yadda Allah zaiyi da ita
Yau ta kama su hamdan zasu tafi duka ma’aikatansu da dogarawa da kuyangu ba wanda bai masu rakiya ba zuwa airport ba
Neela kam kallon kowa tayi tanason taga Hurriya ta ina zata bullo?saidai shiru bata ganta ba kallon Liya tayi sannan tace wai ina Hurriya Liya murmushi tayi tace I don’t know
Imad shima sai kallon wurin yake yaga ta inda zata fito Amman bata ba alamar ta
Hamdan kam kamar yayi kuka saboda takaici gashi Amrah ta dauke mashi magana kwata kwata duk yanda yaso yayi magana da ita sai tayi banza dashi
Kallon kowa yayi saidai kwata kwata ba gifcin Hurriya kuka ya fashe dashi tareda rungume Ammar dake kusa da Hamdan Ammar lallashin shi kawai yake tare bashi hakuri yana yayi shiru
Announcement din da suka ji ne ya sanya su tashi wadanda suka yo masu rakiya suna dukar da kai Ammar riko Hamdan yayi sannan suka nufi jirgin
Ma’aikatan Saida suka tsaya suka tashi sannan suka juya.
🌚Masarautar Qamar
Page 31&32
Karfe 3:44 jirginsu yayi landing tun a cikin airport din ake masu wata irin busa da algaita ga wasu mutane tsaye gigantic da wasu kaya da basu taba Ganin wasu irinsu ba
Durkusa masu kawai ake ana gaishesu Dukansu a
They’re from the imperial family kenan inji wasu wadanda sukayi landing tare dasu Imad
Imad frowning fuskar su sukayi hade da takaicin wannan durkusawar da akeyi masu saboda islamically ba kyau Amman basuji ko an fada masu saboda basa practicing musuluncin sosai duk da cewar musulmai ne Amman abinda sukaga dama shi sukeyi ba tare da sanin sun aikata laifi ba
Amrah da Hamdan bude baki sukayi Ganin yadda akayi masu kneeling tare da dukar da kai Ammar tsoki yayi cikin ranshi sannan yace Raise sannan suka tashi tare da ce masu welcome
Wasu mahaukatan bakaken jeep ne akayi masu convoy dasu a kowace bayan motar an rubuta Heral palace motocin kusan guda ashirin sai farar limousine a tsakiya bude masu cikin limousine din akayi ana durkusa masu
Imad ya fara shiga su Hamdan suka biyo baya zama sukayi cikin motar wanda yake kamar wani parlo wani dim light blue da red yana kawowa sai kuma ya dauke Différents varieties of meals da small chops ne a cikin motar Liya ce ta lumshe ido tare da cewa Heral palace is freaking rich wannan motar itace latest limo of 2022 worthing shiru tayi tace gaskiya kudinsu yayi yawa .Neela tabe baki tayi tace aifa mun bani da extravagance life har sai an sanya mutum yaji baisan komawa masarautar Qamar
Imad baice komai ba Hamdan ba wani spirit tattare dashi don rungume da ammar yake kamar wani yaro
Basuci komai ba har suka iso Heral palace Din
Busa da algaitu ne akeyi kota ina Mutane kam basu da adadi kowa da irin abinda yakeyi
Hamdan da Amrah sakin baki sukayi suna kallon komai don All their life basu taba Ganin masarauta mai kyaun wannan ba everything is screaming rich and elegant tun daga kasan masarautar har sama
Daidai inda ake taron aka bude masu mota Dukansu suka fito sannan aka sanya ma kowanne acikinsu alkyabba mai matukar kyau da tsada banda kamshi ba abinda alkyabbar takeyi
Neela da Liya murmushi sukayi ganin yadda duk suka rikice da masarautar masarautar Heral kenan duk idan mutum ya dawo sai yaga canji bare wannan karan canjin da yawa sosai
Duk inda suka gifta durkusawa ake ana masu kirari har suka zo inda ya kamata su zauna ja masu kujera akayi
Basu dade ba aka fara annoucing shigowar sarki da matarshi kowa a wurin natsuwa yayi tare da sadda kai har saida sarki ya shigo tare da zama kallon saitin da suke yayi murmushi sarki Hamood yayi ya tashi ya nufo inda suke hannun Hamdan ya kama tare da shafa kanshi murmushi yayi yana kallon kamanninshi da Banafsha Amrah ya kalla yace mata amarya ta Hamdan da Amrah sukayi sauri suka gaisheshi yadda suka ga yan masarautar nayi
Haka su Neela suka gaishe shi kallonsu yayi tare da yin murmushi a hankali yace Hurain itama yanzu tazama yan mata kamar su ya fada cikin ranshi murmushi yayi yanajin wani Abu aranshi saboda babu rana da zatazo ta wuce baiyi tunanin Hurain ba yana tunanin ko tana raye ko ta mutu Allah shi yabar ma kanshi sani don ba inda baisa a nemeta ba saidai Duk maganar Dayace babu ita babu alamunta
itace favorite jikarshi saboda tsananin mulkinta da izzarta kuma kamanninta shi ta dauko da mahaifiyar Faisait wato bahiyya mikati shiyasa Allah ya jarabce shi da sonta yana fatan duk inda take Allah ya sanya tana lafiya sannan tana cin abinci
Muryar Imad ce ta dawo dashi daga tunanin da ya shiga sakin Hamdan da amrah yayi sannan ya rungume imad da Ammar
Yana tambayar su lafiya Dukansu suka amsa mashi lapia lau mutane wurin ba wanda idonshi ke kansu don kowa ya sadda kanshi matarshi kam kamar ta mutu saboda bakin ciki don ya manta da kowa dake wurin ba wanda yake ganin a wurin sai marayun jikokinshi.
Hurriya ta dade tana bacci yau saboda tasan su Ammar sun tafi dagangan taki rakasu Airpot din tasha baccinta yanzu tagama aikinta ta nufi wurin wanki saidai bata ida kai wurin wankin ba taji ana busa Algaita ana kida hayaniya ake kota ina Khalifa Qamar ake cewa Khalifa Qamar Khalifa Qamar Khalifa Qamar
Totsar bakinta Hurriya tayi tace Nonsense ta nufi wurin wankinta saidai maganar kawai takeji ana Khalifa Qamar ya dawo subira itama ta dawo salati taji anayi ana cewa wai daman Khalifa Qamar har yanzu yana a masarautar Qamar aiko muna cikin matsala don ance Khalifa Qamar makaho ne saidai baida mutunci ko kadan haka itama subira Hurriya tanajinsu saidai wankinta kawai ta cigaba dayi
Tunda tazo take mamakin rashin ganin wasba da ba tayi yau ba duk da batayima yarinyar magana amman tana enjoying company dinta sosai wankinta ta cigaba dayi tare da cire tunanin yarinyar a zuciyarta
Amman wata zuciyar na cewa taje ta dubata saboda hakan bata taba faruwa ba tsoki tayi ta cigaba da wankinta ta jima tana wanki kafin tagama ta koma daki dan ko sallah batayi ba saidai tana zuwa kwanciya tayi saidai hayaniya da kidan da akeyi shine ya hanata baccin da take so tayi kunnuwanta duk an cika matasu ba abinda takeji sai khalifa Qamar tsoki ta karayi tare da runtse idonta
Da wani irin gudun masifa convoy din motocin suke tafiya acikin masarautar kowani mahaluki ya matsa daga inda yasan zasu wuce don ko daga yadda kaga suna tafiya kasan shidin mai zafi ne
Busa da algaita kawai ke tashi wurin hade da sunanshi da ake ambata wato Khalifha Qamar
Motar tsakiya wadda take itace kadai iri daya a convoy din Roll Royce aka bude mashi inda yake zaune idonshi a rufe looking so mighty walking stick dinshi mai masifar kyau da daukar ido tafara saukowa kafin shima ya biyota baya sunanshi kawai ake ambata a wurin
A hankali ya fara tafiya mai dauke da mulki da izza don yadda yake tafiyar ko sarki albarka walking stick dinshi ta Brass cane wadda ta zama encrusted with Swarovski elements don Swarovski element na crystals din ba karamin taimaka ma sandar tayi wurin fiddo da tsantsar kyau da tsadar ta tayi ba the flamboyant design glittering Swarovski element crystal doesn’t stop at the handle don ba a handle din sandar kawai ya tsaya ba don har kasan shaft din dauke take da glittering Swarovski element
Kallo daya zakayi ma handle din sandar da shaft dinta kasan cewar they are made from high quality brass wanda yake lullube da crystals yadda yake tafiya kadai zakasan lallai wannan jinin sarauta ne kuma sarautar a jikin shi take yawo ba haye yayi ba gado yayi ko fuskar shi babu alamun sauki bare rahma he’s not young because he looks 36/37 he’s huge and gigantic don Khalifha Qamar sunanshi Amman inda ya fito anfi saninshi da cobra blind snake saboda shidin kamar ba mutum yake ba saboda yadda yake he exude danger that is susceptible to a lifetime harm that leaves you wondering what is different about him that no other human being has.
He’s intact kamar kowani mutum mai lafiya saidai his aura,peril and danger that always follow him behind wanda ba kowa yake da hakanba. a business world ana kiranshi da cobra blind snake saboda poisonous dinshi da danger dinshi a masarautar su kuma ana kiranshi da Khalifha Qamar
Tafiya yakeyi rike da sandar shi sai glasses din dake a fuskar shi wanda dan mutum bai isa ya hasko idonshi ba saboda makantar dake tattare dasu
Wucewa yake ta mutane kusan kowa yana durkusawa yana gaisheshi amman a wurin tamkar baisan dasu ba don ko kallo basu isheshi ba wani acikin security dinshi yazo wanda da alama kamar hakan dokace a wurin shi a hankali kallonshi yayi sannan ya kalli security’s din yace they’re all fired chief of security din ya sara mashi tara da bowing yace okay sir ya tafi
Chief of security din ya dawo yana kallonshi tareda tunanin hali irin na Khalifha Qamar chief of security yace a zuciyarshi ko miyake expecting daga Khalifha Qamar a reptile without any emotion.
Duk masarautar ta dauka Khalifa Qamar ya dawo Khalifha Qamar lmakaho ya dawo.
Gafa Khalifha Qamar kam ya fans kunajin dadin labarin namu ko kuma dai da sauki tohm gafa wani shi kuma wai Khalifha Qamar shima kamar baida kirki Amman ku biyoni domin muji labarin Khalifha Qamar din.
Anan na kawo karshen free page na wannan
Littafin ya Koma na kudi saboda wani dalili na daban
MASARAUTAR QAMAR NA KUDI NE CIGABANSA
Naira dari uku kacal300
3139107983
Khadija Mustapha first bank
Ko kuma katin mtn ta wannan number 08029520062
Ku tura screenshot ta a wannan number 08029520062
Saimun hade a paid group kasaitattun Mata masu ci da guminsu
🤷🏿♀️🙅🏿♀️