Hausa NovelsKurkukun Kaddara Hausa Novels

Kurkukun Kaddara 3

Sponsored Links

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Boss Bature ✍️*

dedicated to Aunty kubra❤
قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔

*E3*

_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata’ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al’ummar Annabi ba.✍️_

Gargarɗi

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_

 

 

Taj kuwa tuni jikin shi yayi san yi, duk da ba su yi zaman lafiya da benazir ba, hakan bai sauya komai ba na daga son da yake Yi mata, Yana jinta sosai acikin ranshi, kusan tun ranar da ta gudu, kullum sai ya jaraba kira layin ta da daddare ko Allah zaisa ta buɗe shi, Amma kullum a kashe yake samun shi,

Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mashi tunaninshi”Ka sawwaƙe mata kawai, da ta je tayi ta aikata zunubi da auran ka akanta, don nasan ba dawowa zata yi ba,”

Girgiza kai taj yayi “baba bazan Iya ba, zan jira ta ne har ranar da Allah zai dawo mun da ita nasan zata dawo ne duk mun daran daɗewa”

Gyaɗa kai Alhaji ubaid yayi”Abunda nake fata kenan Yanzu ina jikar tawa take ne? Inaso na ganta,’

“Tana hannun Inna kulu, Ƙanwar matar maigadina ce, itace ke shayar da ita”

“Allah sarki Amma naji daɗi sosai, ka ɗauko mun Jikata na ganta kafin na tafi da yake bani kadai nazo ba akwai escorts dina dake awaje suna jirana”

Amsa ma shi ya yi da toh, kafin ya miƙe da sauri Ya nufi corridor ɗin da zata sada shi da ɗakin inna kuluwa Lokacin daya ƙarasa a kwance ya samu inna kuluwa tana bacci angel kuma na kwance gefen ta an sanya mata kayan sanyi ajikinta, sai faman tsotar yatsanta take yi, Murmu shi ya saki tare da kai hannu ya ɗauketa Ya fito da ita,

Ƙarasa wa yayi tare da miƙa ma alhaji ubaid ita Wani irin farin Ciki ne akan fuskar shi “Tabarakallahu ahsanul khalikin Taj kaga ikon Allah, Yarinya ƴar kyakkyawa sai kace rainon turai wannan idan ta girma ae zata iya ciyo mana gasar miss world,

Murmushi taj ya saki yana kallonshi addu’o’i ya shiga karanto wa yana tofa mata Taj na amsa ma shi da ameen ameen har ya kammala yi mata addu’ar, Fira sosai su ka yi da surukin nashi, har lokacin Angel na a hannunshi Sai da ya ta shi tafiya ne tukunna ya miƙa ma Taj ita

“In sha Allah zan dinga zuwa akai akai ina duba jikata, Yanzu ka tura mun account number dinka In sha Allah zakaga saƙona”

“Ngde ssae Allah ya kiyaye hanya, idan Anji wani labari game da benazir dan Allah a sanar min”

“Kada ka damu suriki na, duk inda take nasan tana sane da ƴarta da ta bari, kodan saboda ita zata dawo ne”

Har wajen da su ka yi parking na motocin su guda uku, Taj ya rako shi da sauri wani bodyguard Ya buɗe mashi mota ya shiga A jere motocin suka fuce,

Fitar su ke da Wuya, ba zato ba tsammani Sai ga alert na Miliyan 20 ya shigo wayarshi, Ya yi farin Ciki sosai da kuɗinnan dama yana ta tunanin yadda zai tafiyar da rayuwar shi da kuma rayuwar ƴar shi, ga kuma Iyayen shi da yake taimakama wa ga kuma albashin baba mai gadi, Salary ɗin shi basu isa ya dunga ɗaukar duk wani responsibilities nasu, A ranar yayi kwanan farin Ciki,

Bayan Wani Lokaci

Alamu sun nuna cewa Angel ba ƙaramar fitinanniya bace, don tun bayan wata ɗaya da aka haifeta, Taj ya yi ban kwana da yin Bacci cikin kwanciyar hankali, Saboda tsabar kukan ta, da ya ke a ɗaki ɗaya ya ke kwana da ita saboda tsabar son da ya ke yi mata, Kona seconds baison rabuwa da ita,sai suna bacci Idan ta tsala ihu tamkar wadda za’a zare ranta, har asibiti ya mayar da ita don aduba Lafiyarta, Still binci ke ya nuna tana da ƙoshin Lafiya,

Inna kuluwa kuwa da ke shayar da ita lokacin da ta fara Haƙora biyu agaba, Ba ƙaramar azaba take sha ba gartsa mata Cizo take Yi,baiwar Allah Ba ta ta6a sanar da taj halin da ake ciki ba, kullum sai tayi zazza6i duk da tana samun kulawa a wurinshi, Duk wani nauyi nasu ya ɗauke masu shi, Hatta Abincin da take ci wanda ke gina lafiyar jikinta Aneelarh ce ta rubuta masu komai, taj ya siya mata

Lokacin da baby ta fara rarrafe A wata na shida, Tayi 6arna kamar zata haukata masu gidan, da rarrafe take 6aro da kaya su zube kasa ta kacaccalasu akwai ranar da Ta samu wasu mahimman takaddu na Taj, Ta kekketasu into pieces, Ranar Har zazza6i yayi saboda muhimmancinsu kuma idan tayi 6arna taga ya zabga tagumi Yana kallonta Sai ta 6a6aka dariya kamar babban mutun haka sautin dariyarta yake, a lokacin da takai shekara ɗaya da rabi,

Da kanta ta daina shan nono, hakan yasa inna kuluwa ta yaye ta, a washe garin ranar da ta yaye ta, ta sanar da taj maganar komawarta ƙauyen su, ya yi mamakin jin zata tafi duk da irin rayuwar hutun da take yi agidan, Ba don yaso ba ya sallameta, kuma Yayi mata alheri sosai baiwar Allah ita kanta ba don taso ba, tabar gidan sai don zargin wani abu da take yi, Game da Ƴarshi to fah

Bayan tafiyarta kamar an ƙarama yarinyar rashin ji, har tsoro take ba taj saboda ƙarfin halinta, a kwai wani lokaci da ta addabe shi da 6arna, Sai ya dinga ɗaurata Saman Freezer dake ajiye A falo, sam ba ta so Yana ɗaura ta a sama, tun tana mashi kuka a karshe Sai gashi Idan ya daura ta da zarar Ya bar wurin sai ta faɗo kasa, Taci gaba da 6arna Abun Ya ɗaure mashi kai Yarinya sai kace aljana ranar da ta ƙure shi Keji yasa akayi mashi mai girma hada mukullin rufewa Ya sakata acikin kejin Yasa mukulli Ya rufe A tsakar falo ya ajiyeta, shi kuma Ya koma saman Sofa ya kwanta yana kallonta ranta Ya 6aci sosai tun tana gwarancin ta har takai ga fashe mashi da kuka, tausayinta Ya kamashi har baisan lokacin daya fiddo da ita daga cikin kejin ba, Ya rungumeta yana lallashin ta har ya samu tayi bacci, A daren ranar daga zuwa Yin sallar isha’e, Ya dawo ya taras Ta 6alla mashi Laptop dinshi da yake aiki da ita, idanuwan shi sukayi jawur ga shi bai iya koda yi mata tsawa ne balle aje ga bugu, A fusace ya ɗauke ta ya nufi gidan su aneelerh da ita ya kai ma Su, Yace ya basu kyauta su ruƙe ta awurin su,ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba, hannu biyu suka kar6eta ashe xaune bata ƙare ba A tunanin shi Ya samu hutu Daren Ranar bayan yayi wanka ya zura kayan baccin shi Ya kwanta cike da farin Cikin Yau zaiyi bacci hada minshari,

Wuraren ƙarfe 12:30 na dare, Can Cikin bacci Ya dinga Jin mutsu mutsun mutun ajikinshi, hakan yasa shi farkawa daga bacci, Yakai hannu ya kunna fitilar gefen gadon,

Kamar ance Ya dago karaf idanuwan shi suka sauka akan baby Angel dake kwance ajikin shi ta ƙanƙameshi, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, a firgice Yake kallonta Har wani murmu shi take sakar mashi, yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniya ba, Abun yayi mugun ɗaure mashi kai taya akai har ta yi wayon da zata iya Kamo hanya daga gidan Taj dake a jikin gidan shi ta dawo gida ƙarfe 12 da rabi na dare batare da jin tsoro ba,

Jiki a sanyaye Ya shiga yi mata addu’a yana tofa mata asaman kanta, Wai koda shaidanun aljanune suka shafe ta, sae faman lumshe ido takeyi alamar bacci zata Yi,

Babu yadda ya iya haka ya ƙanƙame ta a kirjinshi Yana shafa sumar kanta, Sae gashi bacci Ya ɗauketa bada jima wa ba shima bacci Yayi awon gaba dashi.

Wuraren Sallar asuba, Uzair da aneelarh suka buga uban sammako, Hankalinsu atashe Yarinya ta 6ace, Duk sun ruɗe Suna shiga falon Gidan Suka ci karo da Taj tare da Angel zaune saman Dining Chairs Hannun shi ruƙe da Kofin tea yana bata abaki tana sha,

A ruɗe suka kalli Juna, saboda tsabar mamaki kafin ma Taj yayi masu bayani Uxair Ya rufe shi da faɗa yana cewa ‘Don me zaije Ya ɗauki yarinya batare daya faɗa masu ba, Yasa duk sun tashi hankalinsu,’sai da ya Kammala zazzaga mashi masifa,
Tukunna Taj yace”Wlh bani na daukota ba,dakanta ta dawo,
A sukwane Aneelarh tace”Wai dagske ita tadawo da kanta”?
Kafin taj ya basu amsa angel tariga shi cewa”Eh da ƙafafuna na dawo, kuma ma baba maigadi bashi ya buɗe mun ƙopa ba, ni na buɗe dakaina” tana magana tana cije le6e kamar ƴar daba,
Tashin hankalin da ba’a sama shi date! cike da tsantsar mamaki suke kallonta, Taya akai har ta iya buɗe ƙopar da ake rufewa da key?

Girgiza kai Taj yay “Lamarin Baby sai addu’a, Ina kwance jiya wuraren karfe sha biyu da rabi na dare naji motsin mutun ajikina a she itace ta dawo Ba ƙaramin tsorata Nayi ba”

Tabbas sun fara zargin Yarinyar tana da aljanu shiru kawai sukayi batare da sun sanar ma Taj abunda suke hasashe ba,

A daren Ranar Alhaji Ubaid Ya ƙara kawo masu ziraya, Kamar yadda ya saba duk in yana ƙasar sai ya zo, kuma duk in yazo sai ya kashe ma angel kuɗi kamar hauka kafin ya tafi,

A washe garin ranar da safe Ba zato ba tsammani Sai ga text message an tura mashi da baƙuwar Number, Benazir ce tayi saƙon Bakomai ta rubuta ba face Tana neman Saki a wurin Taj, kuma kada yayi tunanin zata dawo ta tafi kenan har abada abunda yasa ya yi farin Ciki da saƙon sanin cewa tana araye, Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba, Har bibiyar Number da ta tura saƙon yayi amma a kashe ya sameta, Yaji takaici sosai tun yana sa ran dawowar benazir cikin rayuwar shi harya fidda rai, ba don yaso ba ya tura mata da text ta number yasan wata rana dole ta buɗe ta gani, Saki ɗaya yayi mata acikin saƙon daya rubuta mata….,……

A ranar Uncle abdallah ya dawo Nigeria, Uzair ne da kan shi ya ɗaukosu a Airport zuwa gidansu, tsabar farin Ciki a wurinsu bakinsu kasa rufuwa ya yi musamman Taj, hajiya adama tayi murnar ganin su Cikin ƙoshin lafiya Ranar yini tayi da angel awurinta, tun dawowar su Angel awurun su take kwana, Bakomai yafi ba Taj mamaki ba face irin yadda yarinyar take natsuwa agaban mutane, Amma idan shi da itane tadinga 6arna kenan kamar 6eran gida,

****Boss Bature******

A kwana atashi. Yau angel Takai shekara 5 cuf aduniya, a wannan Lokacin Uncle Abdalla Ya kuma tafiya zuwa South Korea, Hajiya adama taso yabar masu Angel su tafi da ita can tayi karatunta amma Taj yaƙiya, duk irin alkunyarshi amma ya gaza jure rabuwa da ita, Babu yadda suka Iya haka su ka tafi suka bar mashi ƴarshi, Aneelerh kuwa Shiru har wannan Lokacin ba Ciki, ko 6ari bata ta6a yi ba a bun ya dame ta sosai, Shi kan shi Uzair ya shiga matsananciyar damuwa, har dai suka yanke shawarar Zuwa asibiti don a bincika lafiyarsu, Amma wani abun mamaki Lafiyarsu ƙalau daga ita har shi, Lokacine baiyi ba ganin sun damune yasa taj zaunar dasu Yana kwantar masu da hankalin su harya basu Labarin Iyayen shi da suka ɗauki shekaru da yin aure kafin Allah yabasu haihuwa, Tunda suka ji hakan sai hankalinsu ya kwanta har suka daina sa damuwa aransu,

A 6agaren baby angel kuwa A tunaninsu idan ta fara Girma zata rage 6anna da rashin Ji, Ashe Yanzu wasan Ya fara,

Tun tana da shekara Uku Ya sanyata nursery, hada islamiyya saboda Bakin da Allah yai mata, rana ta farko da ta fara zuwa makaranta, ta samu ƴa’ƴan mutane ta dinga gartsa masu Cizo, Itafa Ko kallonta kayi to ka Shiga huruminta, saboda jarabarta kusan makaranta Biyar ana sallamarta Saboda baza su Iya Control ɗinta ba, ga shi ya hana a dukar mashi ƴa ko tsawa Baiso Ayi mata sai dai bayan idonshi.

Daƙyar aka samu Angel Ta daina Cizon ƴa’ƴan mutane, tun da yayi mata faɗa abunda bai ta6a Yi mata ba a ranar har fushi tayi taƙi cin abinci, daƙyar Ya lallashe ta ya samu suka shirya da ita,

Wata rana zai tafi Wurin aiki da marece, tana bacci Ya tafi yabarta saman Gado, a tunaninshi Harya dawo bata tashi daga Bacci ba, bayan fitarshi Da rabin awa ta farka tana Jin yunwa gashi Sam bata da juriyar Yunwa,

Kaitsaye Ta Nufi kitchen Tana kiciniyar Ɗaura girki, Ta sanya kujera agaban gass Ta samu ta haye sama har takai yadda zata Iya ganin saman gass cooker din, Dama tasan Yadda yake kunneshi Saboda wasu lokuttan a tare da ita Yake shiga kitchen Yayi girki, To yau dai ga angel zata Yi practicing abunda Ubanta ke Yi agabanta.

Yana Wurin aiki Aka kira shi awaya ana sanar dashi cewa Gobara Ta kama agidanshi, Hankali amatuƙar tashe Ya shiga Mota Ya nufi gidan.

Yana zuwa unguwar ya hango motar ƴan kwana kwana a ƙofar gidanshi, Duk yabi ya ruɗe babban tashin hankalin shi Ina angel ɗinshi kada ace wuta taci ta, da gudun gaske Ya fada Ciki gidan, Su uzair suka bi bayan shi dama sunzo hada aneelarh, A rude ya shiga kwalamata Kira Angel Angel!!kamar makoshinshi xai 6allo, Tunda suka Ji cewa Yarinyar tana agidan wutar ta kama nan fa hankalin kowa Ya tashi,

Sai da suka gama shan wahalar nemanta, Ba zato ba tsammani suka same ta a cikin bedroom dinshi, tsakiyar Gado hannunta ruke da robar yogurt me sanyi tanasha.

Da gudu suka nufe ta gaba ɗaya suka rungumeta, kowa ya na faman sauke ajiyar Zuciya,

Abunda Ya faru a she bayan ta kunna gass, ta sauko daga saman Chair ɗin, Sai ta tuna akwai yogurt da ice cream acikin frigde shine taje ta dauko Ta shige daki tana sha, Sam ta manta da tabar gass a kunne, duk wannan budurin da akeyi na gobara ta kama ita ba ta ji ba, Baba maigadi ne Ya ga hayaki na fitowa ta cikin gidan,a hanzarce Ya shigo Ciki don yaga me ke faruwa, koda ganin Hayaƙin ta kitchen yake fitowa Jiki na rawa Ya nufe shi, Nan yaga wuta ta kama Jawur tana Ci,jiki na rawa Ya watso da gudu waje Yana neman a gaji,

Angel tasha fada awurin Taj kuma duk da laifin da tayi ma shi ko dungurin ta bai yi ba, kadan daga Cikin munanan halin angel shine, Bata barinbshi yayi bacci muddin ta farka, to shima dole ya farka baccinshi Ya qare, Idan suka fita Yawan shakatawa komai ta gani tana so, koda a hannun wani yake to dole A mallaka mata shi idan ba haka ba hmmm xa’aga tashin Hankali, Bayan wannan Ta iya jan faɗa idan suka Je anguwa, komai ta gani saita dauka ta jefar, Ayita nema tana ji bata faɗin ita ta dauka.

duk duniya babu wanda bata Jin tausayin shi Irin mahaifinta, azabtar da shi take Yi, Shi kuma Ya mutu akan sonta Bai iya rabuwa da ita ga shi ta tsani taga yana karatul Alqur’ani, da zarar Ya fara saita 6allo mashi aikin da zaisa ya ajiye karatun, kuma bai isa Yayi salla acikin gidan ba idan uziri ya hana shi zuwa masallaci, Kamar shaiɗaniya haka take, har malami aka dauko yayi mata addu’a Don a fidda aljanun da ake hasashen tana dasu, tun malamin na cikin yi mata rukiya ya dafa kanta, ta dinga buge mashi hannu tana faɗin dama ya daina wahalar dakanshi, Ita lafiyarta qalou

Bayan malamin ya kammala Yi mata ruƙiya, Ta sace takalmanshi ƴan madina, sai da ya tashi tafiya aka nemi takalma wayam an ɗauke su, su ka yi ta nema kasa ko sama babu su, bayan tafiyarshi ta fiddo takalman da ta 6oye a ƙarƙashin gadonsu taba Taj, wai gashi A maida mata su na yara daidai kafarta, haushi kamar Ya rufeta da bugu, yaji kunyar abun nan haka ya kwashi takalman yaje har gidan malamin Ya mayar mashi da abun sa,

Babban abunda zai baka mamaki da ita sam bata da tsoro, yasha farkawa tsakar dare Ya sameta zaune a falo tana kallon cartoon har ta Iya kunna kallo, tun abun na damunshi harya hakura ya kyaleta,

Akwai ranar da zaije gabatar da wani programme agidan radion su, Sai daya kammala shiri Yaji ƙopa a rufe, Tasa key ta rufeshi, dalilin da ya sa Ta yi ma shi haka shi ne, Kullum In zai tafi Evening duty, a mota yake ɗaukarta yakaita Gidan Amininsa Uzair, Ita kuma bata son zuwa gidan tafi son duk inda zai je ya tafi da ita, Wannan ne yasa a ranar Ta saci keyi din ɗakin shi bayan ya shiga wanka, Ta ɗauko kujera ta sanya Yadda tsawonta zai kai, Ta murɗa mashi key ta datse ɗakin Ƙarfin Hali,

Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar mai yin magana da babban mutun, Ya zazzageta Da masifa duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba, har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki, ya kawo mashi taimakon gaggawa batare da 6ata lokaci ba sai ga uzair Yazo gidan, A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo, aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe ma shi ƙofa, koda ya fito baibi ta kanta ba Ya fuce daga falon yana huci, Uzair dai yaci dariya, shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu,

Saboda bala’in angel Saida yakai ga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayin shi, bawan Allah duk yayi duhu ya rame, ita kuwa Babyn tashi har kumatu ta yi saboda rayuwar Jin daɗi, yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita, gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yarda, saboda kowa Mamakin shekarunta ya ke yi Just 5 years fa,

Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani Shine girka mata abinci Yayi mata wanka ya wanke mata gashi Yayi mata kitson kalaba, har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi, Amma yarinyar nan Idonta sun makance idan kana son Ganin Dariyar ta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne,

Lokacin da takai Shekara 7 a duniya, Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi, mai suna Muhsin lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba, musamman da yazo masu da angel, yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta, Allah yayita da farin Jini,

Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe, Taƙi ci da suka tambaye ta meyasa baza ta ci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane, a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba, ƙiri ƙiri ta yi mashi ƙarya, Muhsin ya roke shi akan yayi mata magana taci abincin, Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci, da buɗar bakin ta sai cewa tayi “Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi,”

Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki, Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗin shi akan maganar angel, har suka ta shi tafiya Bata Ci komai ba, tun lokacin yaci alwashin saiya yi mata fada in suka je gida, Ashe da zasu Baro gidan, Ta sace warin Takalmin matar gidan mai tsadar gaske, Babu wanda Ya lura sai bayan Da sukayi nisa da tafiya saman titi, Ta ɗago takalmin tana nuna mashi Wai yakai amayar mata dasu Na yara, Sun burgeta, hankali atashe Yayi parking ɗin motar, dama a ƙule Yake da ita wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, a karshe yace”Bana sonki kin fita araina, Ke ni ba mahaifin ki bane, bansanki ba ki fita arayuwata” Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi, buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje”Kije ki nemi wani uban”

Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri, Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama’a, fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta, yana faman ƙwala mata kira Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin “Wayyo Allah taimako wani mutun zai sace ta, ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta, kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu, Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora, Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba, Ya soma bleeding duk don mutane su ɗauki abun serious sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa”Ba mahaifinta bane sace ta ya yi yana gana mata azaba, Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta, dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi, Jin wannan maganar yasa ran mutane Ya 6aci, Musamman ƴan ƙato da gorar nan sun fusata sosai, Kamar jira su ke yi dama a harzuƙe suke, Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki ita kuwa ko ajikinta, har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba, Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba, tafi kama da ƴa’yan larabawa da turawa, shi kuma yana da ɗan duhun fata ga kuma Launin idonta ba kalar nashi ba

Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba.

Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai,

A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya,
Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaɗai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya’yan mutane,

A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector ɗin ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,

Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance.

Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi,

Har kiran Angel a kayi daga office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne.

 

Shin me ku ke tunani game da angel?

_Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne Kacal, Ban tsawwala ba,mutane Dayawa Suna tambayata Shin wannan book din zai kai father of soldiers daɗi? Lokacin dana fara abban sojoji bansan zaiyi daɗi ba, Allah ne ya nufi hakan,To ba lallai bane Kurkukun kaddara yakai shi dadi ba, zai iyayiyuwa kurkukun ƙaddara yafi Abban sojoji daɗi ko akasin hakan, Allah shi ne mafi sanin dai dai👏Bani da tabbacin akan haka, Saboda Salon Labarin Ba iri ɗaya bane, sunsha banban sosai shima wannan wani salon ne na musamman, murɗaɗdiyar cakwakiya ce acikinsa, Sannan banyi maku alƙawarin cewa wannan Littafin Short story bane Zai iya Kasancewa Yana da yawa labarin! na yi maganar nan ne saboda masu ƙorafi akan Story ya yi tsayi, Shiyasa na faɗa masu tun yanzu Su sani 🤣Tun da ku kaji Ance kurkukun ƙaddara, Kunsan inda ma’anar ta dosa ko ban fayyace maku ba,Kowa yasan ma’anar kurkuku da kuma ƙaddara Dan haka kada mutun yazo yana yi mun complain akan waɗannan abubuwan dana lissafa👏then banyi alƙawarin kullun zanyi posting ba, 4 days ne a week, litinin, talata, laraba, Alhamis, after na kammala free pages, wadanda su ka yi payment zan Canza musu salon Posting🤗_
_Abu ɗaya ne zan Yi maku alƙawari🥳 da yardar Allah ba zaku ta6a danasanin siyan Littafina ba in sha Allah🤗🤣tsakani na daku fatan alkhairi ne Allah yabar zumunci daga nan har gidan aljanna😍_

_Ga waɗanda Suka shirya Yin payment Ga details nan👇_

*3196407426*

*First bank*

*Bature hafsat Muhammad,idan mutun baida acct no pls Ya tura ta Pos,saboda bana amfani da Kati,Ƴan uwa ƴan niger,Suyi mun magana ta numberta,wadanda su kayi payment zasu bada shaidar biya ta screenshot kafin a sanya su paid group*

*08103884440*

*08169856268*

_*Boss Bature💋 ✍️*_

Leave a Reply

Back to top button