Hausa NovelsMasarautar Ulwa Hausa Novel

Masarautar Ulwa Hausa Novel

Sponsored Links

MASARAUTAR ULWA
Na
A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Bismillahir rahmanirrahim!!

   Page 1&2

_______
“”A  Masarautar ulwa kuke tunanin zaku iya tsere ma  ganin mu,  lallai azaba ta tabbata a gareku mai tsanani,  kuna kaskantattu daku amma kuke ganin zaku iya jada SARKI ABUL UWAIS! mai ji da ƙasaita. Lallai ina tausaya ma kalan azabar da zaku sha a hannun sa” …….

Cikin tashin  hankali ɗaya daga cikin waɗannan bayin da aka kamo, ya ƙara kwanciya yana cewa “Yakai wannan Bafade kayi haƙuri ka dubi Girman Allah ka yafe mana tabbas munyi kuskure amma bazamu sake ba ina bada haƙuri amadadin mahaifiyata da Ƙannaina”
A wulakance ya dube su yace “lallai maitama wato kaine kafisu baki da har kake iya magana tabbas ka kama bakinka kafin ku isa gaban Sarki ..

Fadar Sarki Abul Uwais suka nufa, ana gana masu azaba tun kafin isarsu. “”An gaishe da Sarkin sarakuna Uban Yarima Uwais da Ubaid Baban Gimbiya Kalba, Allah ya ƙara maka mulki ya shugabana!  Allah ya taimakeka mun kama mahaifiyar maitama da sauran yaranta zasu gudu, ba bisa doka ba sunbi ta barauniyar kofa mafi sirri , hakan yasa muka gurfanar dasu gareka shugaba”.

Sarki Abul Uwais da ranshi ya baci ya ɗaga kai kallesu a wulakance ya ɗauke kai, kusan minti talatin yayi kafin ya bada umarnin cewa “A tafi dasu dakin durhun a gana masu azabar da ba’a taɓa ma wani mahaluki ita ba, sannan a hana masu ruwa, a basu abinci me barkono da yawa domin zunubin su mafi girman zunubai ne”.

Rufe bakin Sarki Abul Uwais keda wuya aka tafi dasu durhun domin cika umarnin shugaba. Ana shigar dasu aka ware babbar cikin su wato  Ammi gefe aka kulleta gaba daya da igiya, aka rufe idanunta da bakinta ana dukanta da bulali ana sheka mata ruwan zafi me hade da gishri a cikinsa.
Yayinda aka kulle Zeenat irin ƙullin goro ana bugunta ana sheka mata ruwan gishiri gefe kuma ana fisgar gashin kanta …..

Maitama da ƙaninsa Abdallah wanda a a kallaha bai wuce shekara 8 a duniya ba,  suna wani daki aka kaisu aka sargafe su kamar za’a jefe su, ana bugunsu da karfe wanda ake zaro shi cikin wuta, idan aka  bige su iya bugu sai a sheka masu ruwan barkono da gishri sai a cigaba da dukansu.

Kuka suke sosai tun sunayi har zuciyarsu ta bushe, a lkcn aka zo kawo masu wannan abinci me tsananin azabar barkono , a haka aka saka suci dole sunaci kamar zasu shide saboda azaba . Wani bafade  ne me tsananin muni ya bushe da dariya yana me jin dadin ganin irin azabar da su Ammi kesha yanayi yana kallon su ” Tabbas zaku sha azaba a hannuna domin ni kaina ban kaunaar kaina balle kuyi tunanin zan so wani har naji tausayin shi a haka zanta gana maku azaba har sai kun tabbatar da cewa kun saɓa ma Abul Uwais “.

A wahalce Abdallah yace Ammi ruwa zan mutu, Hamma Maitama ka taimaka min kar na mutu! Adda zeenat ku bani ruwa , gaba dayansu wani irin kuka ne ya kubce masu me tsananin azaba da cin rai, domin sunsan babu ta yadda zasu taimake shi . A hankali Adda Zeenat tace “kayi hakuri Ƙanina duk tsanani yana tare da sauki insha Allah! wata rana sai labari . Kara fashewa da kuka sukayi  “Adda Zeenah nasan ni mutuwa zanyi bazan kai lokacin da saukin nan zaizo ba sai dai ku kaďai, amma ku kula mana da Ammin mu karsu kashe mana ita kunji….

Kukan suka kara saki a tare Maitama ne yayi dauriyar tsayar d kukan shi yace” Haba Auta kadaina irin wannan maganar bana hanaka ba uhum, kabari kaji! zamuyi rayuwar farin ciki insha Allah kaji”.
“yaya AA ni nasan mutuwa zanyi nabi Abbun mu kasan banda cikakkar lapiya kuma ga azaba ana gana mana kaga ai barinku zanyi kasan yanayin lapiya ta.
Ammi ki ƙara haƙuri kinji jarabawa ce daga ubangiji Allah ya kawo mana sauki a ciki”.murmushi Ammi tayi cikin jin tausayin kansu tace.
“”Toh Auta nah! Ameen Allah ya amsa, amma ka daina faďar irin maganganun nan kaji muna tare insha sai na aurar dakai Autah , dariya suka saki gaba ďaya tare da kuka “”. Yayinda aka daka masu wata razananniyar tsawa data saka su gigicewa suka Mike tsaye

“Allahumma ajirni fi musibatun wa’aklifni khairan minha” Abinda Ammi tafada masu kenan sun sani, tunda tarbiyarta ne nan take suka shiga maimaitawa cikin ikon ubangiji da kudrarsa sai Allah ya dubi kukansu nan inda suke, Allah y saka ma wannan bafade ciwon ciki me tsanani wanda nan da nan y kwanta ciwo, Allah kenan maji rokon bawansa …….

MASARAUTAR ULWA
Na
A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 3&4

Bismillahir Rahmanir Rahim.
__________
Cikin kwanaki  biyu da faruwar wannan al’ama,  idan kaga Ammi da yaranta saika zubar masu da hawaye saboda tsananin azabar da suka sha  amma duk da hakan bakinsu bai gaza ba wajen neman sauki wajen ubangiji domin basu fasa addua da suke ba akowane lokaci Allah kenan ana cikin hakan Aka fara shirye shiryen tarar wani hamshakin sarki dake zaune a kasar Nigerian. Inda sarki ya cika da farin cikin zuwan   wannan sarki . Wannan ne karo na biyu da Aminin shi ya taka kasar MALI domin ziyartar sa ,Aminin Sarki Abul uwais ne domin tare sukayi karatu a kasar Egypt  kasancewar yayan sarakuna ne a wancan lokacin sai yazama sun dinke sun koma abokai saboda kowa naji da takama da izza ga kuma kyau da dukiya.

Kasancewar su abokai ko ince aminai hakan bai hana  a gane banbancin  dake tsakanin su ba domin halayyarsu akwai banbanci, sarki  Abdulgafar mai lafiya ya kasance me hakuri da son talakawa da dajara dan Adam ,yayinda sarki Abul uwais ya kasance me tsananin kyamar talaka da son mulki da izza ko kadan bai dauki talaka da daraja ba .  A yanzu haka wannan ziyara da sarki Abdulgafar ya kawowa sarki abul uwais yazo ne domin sun dauki shekara wajen biyar kenan basu hadu ba saboda tazarar dake tsakanin su.

Anata hidimar tarar Wannan adalin sarki a lokacin ne su ammi suka samu sauki daga wannan azaba suna zaune sarki ya bada umarmin a sake su albarkacin zuwan aminin sa farinciki ne ya bayyana a fuskar adda zeenat ta Mike ta kama Ammi da autah dake kwance ba lafiya domin take bangaren bayi inda anan suke rayuwar su .

Suna zuwa dakin da yake nasu suka zauna suna maida numfashi ahankali autah yace ammi na inajin yunwa ga kishin ruwa ina ji ki bani nasha sai ki bani magani nasha ko naji sauki kinji ammi . Hawaye ta share tace mashi toh autah bari na nemo maka kaji ka jirani nadawo ina zuwa   mikewa tayi ya rike mata hannu yace Ammi ki yafe min ni nasan mutuwa zanyi na barku keda su yaya Ammi meyasa har yanzu bazaki gaya min asalin labarin muba ,? Meyasa kika zabi daki boye mana ki gaya min koda sunan mahaifina ne nasani kafin na mutu dan Allah  Ammi .

Kuka ta fashe dashi domin bata son taji yaran na son jin wani abu daya shafe su tafi son su bar komai su dauka basu da kowa sai ita . Amma ya ta iya dole watarana su sani , kallon shi tayi tace auta bari na nemo maka abinda zakaci kaji . Ficewa tayi d sauri saboda kukan daya taho mata na tausayin yaran nata tabbas suna cikin kuncin rayuwa Allah ka kawo mana dauki abinda tace kenan ta kama hanya zuwa madafar abinci domin karbo masu abinci suci .

Tana fita daga dakin adda zeenah ta share  hawaye ta kalli yan uwanta tace ” har zuwa yaushe Ammi zata daina boye mana asalin mu da kuma labarin mu bansan meyasa ba amma nasan ba karamin abu bane ammi take boye mana ba koma dai menene ni kaina ina son nasani gaskiya” Maitama ne ya budi baki yace gaskiya  ne sister ni kaina nasani akwai wani abu a kasa amma koma menene mu kara bata lokaci ina da tabbacin insha Allah  watarana zata gaya mana indai muna da rai da rayuwar kaiwa lokacin mu cigaba da addua kawai  .

Amma yaya ka duba fa kagani daka taji kishin kishin din zuwan sarkin nan na Nigeria fa shikenan ta tada hankalinta akan mu gudu zuwa wata kasar sai dai bata samu nasarar hakan ba aka kamo mu bansan meyasa ta tana hankali ; ka duba maganar anya babu wani abu data sani game da Nigeria da har take gudu saboda bata son suzo su same su a wannan masarauta !

Ajiyar zuciya ya sauke tabbas na gamsu da abinda kika fada sis amma kina ganin wannan Dalilin  ne zaisa Ammi tace mu gudu mubar Mali batare da wani abu ba ace lokaci daya ta fada hakan kuma ba bata lokaci ta aiwatar gaskiya ni a ganina wannan ba shine dalilinta ba akwai dai wani abu amma koma menene mu jirata mugani zuwa wani lokaci .

Sallamarta ta hana zeenah cewa komai suka amsa mata ta shigo dauke da wata kwarya an zibo masu abincin a ciki . Zama tayi tace masu kowa yaje ya wanke hannu sai kuzo muci gaba daya,  kamar yadda tace haka sukayi domin basuyi ma mahaifiyar su musu komai ta fada indai bai saba ma addini ba suna mata shi . Adduan cin abinci suka karanta kamar yadda manzon Allah (SAW) ya koyar damu suka faraci .

Ba dabiar su bace cin abinci ana magana hakan yasa tunda suka fara babu wanda yace wani abu harsuka gama suka sha ruwa sannan suka wanko hannuwan su suka dawo daki . Maganin autah ta dauka ta bashi yasha ya kwanta ita kuma ta Mike ta tafi bangaren gimbiya maryama uwar gidan sarki Abul uwais ita kuma zeenah ta tafi bangaren gimbiya kalba domin aikinta acan yake.

Tafiya take amma tana tunanin wannan wace irin masarauta ce ?  kuma ko ina haka masarautun su suke ne ? Anya ana samun masarauta me rangwame kuwa? kowane bawa da kalan kaddarar sa mu kuma irin tamu kenan Allah ka bamu ikon cinyewa.  Tana isa bakin kofar taji an daka mata wata irin tsawa me ban  tsoro nan take jikinta ya ďauki rawa  ta rasa ina zata fuskanta saboda razana a kiďime ta zube kasa bakinta na furta “Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un”  …..

Comments
Share.

MASARAUTAR ULWA
Na
A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association

Page 5&6

Bismillahir Rahmanir Rahim.

____”Keeee! wace irin dabba ce sakara mara tunani, kina mace kina tafiya baki kallon gabanki kamar wata gunki”.
ya faɗa cikin daka tsawa , cikin rawar jiki zeenat ta durƙusa tana cewa ” kayi haƙuri yarima Uwais wlh ban zaton samun ka a hanya ba da ko kaɗan ban isa bin hanyar ba saboda ba hanyar mu bace mu talaka”
“Dallah can jaka matsa kiban guri na wuce kinci arzikin me martaba ke kirana da saina ɗan ɗana maki baƙar azabar da sai kinji dama baki zo duniya ba ƙazama kawai  kucaka tashi ban waje nace”””.
Kuka take kamar ranta zai fita saboda bata taba cin karo da kaskanci kamar na yau ba tashi tayi da sauri ta bashi guri ya wuce fuuuuuuu harta juya da nufin komawa wata baiwa ta kirata gimbiya kalba na nemanta .

“”Allah ya ƙara maki lapiya da nisan kwana ranki ya dade nasamu sakon kiranki”.  kallon banza gimbiya kalba ta watsa mata, zuwan can tace mata “ubanwa kika bar ma girki na  yayi min, ko saboda kinga na ɗaga maki ƙafa saboda hukuncin Abbuna?  toh kisani ni nasaka aka yafe maku kuma badan komai ba sai don kula da abinci na, kina jina” ta fada da daka mata tsawa wanda hakan na nufin abin ya bata haushi kenan.
“” Kiyi haƙuri ranki ya dade yanzu zan shiga na shirya maki abinci insha Allah”. Sallamar yarima ubaid ya katse ma gimbiya kalba  abinda take son fada sai dai tayi kwafa kawai..

Mikewa tayi da nufin ta tafi madafa, domin haɗo masu abinci,  sai taji wata tsawa kamar kanta zai rabu , “”ke yar gidan ubanwa cece da zaki rabani ki wuce, baki ganni ba ko kuwa ni sa’anki ne? ko kayan bayi kika gani jikina? toh kisani ni yarima ubaid ba matsiyaci bane na gaji arziki kuma nidin me daraja ne wanda kaskantattu irin ku basu isa nako kalle suba’;

“Kayi haƙuri dan Allah ranka ya dade banji shigowar ka ba ina amsa umarnin gimbiya kalba ne shiyasa amma ina neman afuwa awajen shugaba”; Yadda tayi maganar ne yasa gabansa faduwa yace mata ” tashi kije” da saurinta tabar wajen yayinda shi kuma ya karasa zama yana kallon gimbiya.

“Barka da shigowa brother ubaid an yini lapiya”. ta fada tare da yin shiru Murmushi ya saki saboda har ga Allah yana ƙaunar ƙanwar tasu, sai dai wani abu dake masu shamaki da juna wanda abin na damunsa, yana son su hada kansu amma abin ya faskara . Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace”” barka dai sister ya ƙarfin jikin naki ina fatan kin samu sauki ?”” Eh naji sauki dazu doctor yazo ya dubani yarima ma ya kira shi bai dade da fita ba Abbu ya kirasa”….

“Allah sarki toh shikenan Allah ya kara lafiya kinji bari naje shan iska kinji kanwa sai na kara dawowa bye” 👋. Murmushi tayi itama tana mai bye, ita kanta tana son dan uwanta saboda yana nuna mata ƙauna sosai sai dai bata san meyasa ake son aga kansu a rabu ba .

Allah ya taimake ki na gama haɗa abincin ki yana sama na aje maki inda kika saba ci sai dai bansani ba koda abinda kike bukata nayi maki ? Babu komai tace a takaice  mikewa tayi ta isa ta zauna akayi saving ɗinta ta fara cin abincin ajiyar zuciya ta sauke saboda yadda abincin ya ratsa mata kwalwa kai gaskiya wannan yarinya ba dai iya girki ba ta faɗa a zuciyar ta.

Mikewa tayi ta fita zuwa ɓangaren su domin hutawa kafin ta dawo tayi na dare kuma.
A hankali take tafiya harta ita sassan su ta kwanta tana tunanin irin cin mutun cin da akayi mata ɗazu hawaye take sosai tana cewa” wannan wace irin rayuwa ce muke fuskanta duk inda muka dafa babu wani daɗi kowa kyamar mu yake yana nuna mana tsana Astagfirullahh Allah mun tuba ka yafe mana laifin ka kawo mana jin  dadi ko ya yake muma,  rayuwar da mukayi a baya tafi wannan muni muna jin daɗin samun sauƙi to ga wannan itama tana neman zaman mana mafi munin waccan da muka baro “

Kuka take sosai tana tausayin kansu a haka har bacci ya ɗauke ta. Sai farkawa tayi taga har anyi sallahr la’asar, da sauri ta Mike taje ta yi alwala ta saka abayar sallar su tayi .tana gama wa ta fice domin zuwa ɓangaren gimbiya domin aiki zatayi sosai acan .

Ammi kuwa bata samu dawowa ba domin aiki ake sosai bangaren gimbiya maryama domin anan zata sauki matan sarki Abdulgafar mai lafiya hakan yasa duk wanda yake aiki a ɓangaren ta baida hutu in ba dare ne yayi ba .

Dakatawa tayi daga kokarin shiga da take domin gaya mata sun gama aikin da tasaka su sun gama sai dai abinda taji ana magana ya matukar razanata…

Comments
Share

MASARAUTAR ULWA
Na
A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association

Page 7&8

Bismillahir Rahmanir Rahim.

_____________Dakatawa tayi daga ƙoƙarin shiga da take domin ta gaya ma gimbiya maryama  sun gama aikin da ta saka su, sai dai abinda taji ya matuƙar razana ta.

“Ummi bari kiji na faɗa maki in ita ta ƙamarsu tsafi zamu nuna mata ƙaryarta dan na rantse babu me hawa wannan kujerar wlh sai ɗana Uwais.  tabbas na ɗauka wannan alkawarin indai ina numfashi to saina nuna mata muba kanwan lasa bane, dodo na yafi ƙarfin tsafinta . Daga can bangaren akace “Ki saurareni kiji maryama kinata ɗaga murya kuma kin saka waya handsfree  ki sani dole sai munbi a hankali kar wani ya zarge mu akan abinda muke son muyima Mufida da ɗanta shiyasa nake ce maki ki kwantar da hankalinki ki natsu”.

“Toh ummi amma kisani wannan karon koda kisa ne sai nayi akan wannan lamarin . Idan har abin zai kawo matsala dole ne mu kawar da duk mai son kawo mana matsala”.
“Eh nagane ummi amma kinsan na tsani duk wani abu daya shafi gimbiya mufida  ke har ɗayar shegiyar ma na tsane su tsana mafi muni kuma indai ina numfashi bazan taɓa bari kan yaran mu su haɗu ba kowa yayi ta kansa .  bari naje na sallami bayi nasaka su aiki tun safe ina tunanin sun gama”.

Ajiye wayar tayi ta nufo ƙofa Ammi dake tsaye da sauri ta boye inda babu me ganin ta harta zo ta wuce sannan tabi ta wata hanyar ta rigata isa wajen da suke aikin .

Tana shigowa ta shiga kallon wajen a wulakance cikin kyama ta sallame su, da sauri suka watse koya na ɗari ɗari yabar gurin kar yayi wani laifi a wajenta saboda sunsan ba imani ke gareta ba  ikon Allah yakai Ammi ɗakinsu ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya me ƙarfi.
Sannu da zuwa yaranta  suka mata kowa na kallon yanayin data shigo dashi wanda ba haka ta saba ba , Auta ne yace “”Ammi lapiya kike kuwa? ko kema baki da lafiya ne naganki haka?”. ya ƙarashe maganar cikin yanayin tausayi da kulawa.

Murmushi tayi masa tace “lapiya lau nake Autah aiki mukayi ne ba hutu toh nagaji ne shiyasa ka ganni hakan”.
“Toh Ammi kici abinci sai kisha maganin da kika jiƙa ki kwanta ki huta kinji Ammi na”,
“Toh Autah bari na watsa ruwa kaji”, ta faɗa tare d Miƙe wa ta ɗiba ruwa ta shiga banɗaki .

Ta shiga bada daɗewa ba maitama da zeenat suka shigo kusan a tare zama sukayi suna fira cikin farin ciki da kaunar juna. Duk ƙuncin da suke shiga hakan bai hana su fira cikin farin ciki ,suna cikin fira Ammi ta fito ta canza kaya ta zauna sukaci abinci kowa yasha maganin data jika musu domin ciwon jiki  sannan tace “toh kowa ya kwanta kunsan jibi ne isowar baki kunga gobe akwai hidima sosai a gidannan  ba kaɗan ba”.

“Toh Ammi” suka faɗa kowa ya nemi makwancinsa ya kwanta maitama kuma ya koma ɓangaren maza yayi addua ya kwanta yana mai tunawa da ƙaunarsa wadda dai-dai da second ɗaya bai taɓa mantawa da itaba a ko yaushe cikin tunanin ta yake A hankali ya furta” ya Allah ka
Ka tsare min Arwah tah a duk inda take ina kaunarki Arwah koda yaushe kece bugun numfashi nah ina sonki Rayuwata”

(Toh fah jama’a wacece kuma Arwa? a ina kuma take   yake ta sambatu akanta ne ?koma dai menene zamu gano ehe😛😀😀)

Ɓangaren Ammi kuwa abinda ta jiyo ɓangaren gimbiya maryama ne ya tsaya mata a rai sosai, domin kuwa tasan ba abinda bazata iya ba tunda ta furta. A hankali ta furta “taya zan taimake su ne dole na shiga jikin gimbiya mufida domin Ankarar da ita abinda ke faruwa don bana tunanin zata iya tsafi balle bin boka ko malamai saboda kamalarta da daraja mutane ba kamar gimbiya sakina ba da gimbiya maryama ba taya zan yi abinda zaisa na koma ɓangaren gimbiya mufida”. A haka bacci yayi awon gaba da Ammi batare d tasamu mafita ba .

Kwance take tsirara haihuwar uwarta gaban bokanyar ta yayinda bokanyar ke zuba mata wani abu kamar jini ita kuma tana wasu maganganu wanda baka gane abinda take cewa . Wata irin razananniyar tsawa da bokanyar tayi saida dajin ya girgiza hatta da tsaunin da suke cikin sa saida ya girgiza sosai yana tsagewa bishiyu na faduwa kasa zuwan wasu halittu gabanta sai tayi dariya tace ” mufii ki gaya masu munfi karfin su  ba’a ja damu in kuma aka ja damu mutuwa za’ayi. Na rantse maku da ƙashin kafar iftul makul marwus ɗanta bazai taɓa hawan wannan mulkin ba idan kuma ta matsa zai mutuuuuuuu” ta fada tana wata irin dariya mai ban tsoro da firgitar wa sannan ta tsaya ta fara magana ” ki tashi ki koma gida ki cigaba da nuna masu fuskarki ta masu mutunci sannan ɗanki in kinga bai hau mulki ba toh niba jikar tsabul kurnajul intawuljunaina bace” !!!!!

Tashi tsaye tayi tana ma bokanyar kirari
“Godiya nake shugaba ta diya ga zukul makut tsabul kurnajul intawuljanaina uwaga tsuntun magnun dabiyanul ashiķul nur ” wata irin dariya bokanyar tayi ta jin daɗi sannan ta sheƙa mata wannan jinin, ta kuma bata wani tasha sannan ta bata wani abu ta shafa batt ta bace sai ganin kanta tayi a bayinta .

Wanka tayi ta fito ta shirya ta kwanta agogo ta kalla 3:57pm na dare wata irin dariya ta saki ta farin cikin zuwan da tayi wajen bokanya sai kuma ta daure fuska tana magana” Ni mufida nafi karfinki maryama mu zuba mugani dan halas ka fasa ” murmushin jin daɗi tayi ta gyara kwanciya sai bacci ba addua ba komai .

(NI KUWA NACE WANNAN WACE IRIN MASARAUTA CE HAKA KU BIYO NI DAN JIN WANNAN LABARI SHIN WACE MASARAUTA CE WANNAN HAKA ME CIKE DA ABUBUWA NA BAN MAMAKI HAKA)

comment
Share.

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 9&10

Bismillahir Rahmanir Rahim.
_________
A yau ne sarki Abdulgafar mai lafiya ya iso kasar mali tare da tawagar iyalan shi tundaga kasar Nigerian domin kawo ma Aminin shi ziyara kasancewar sun dauki tsawon shekaru basu hadu hakan yasa kowa ne daga cikin cikin su yake murna. Shigowar su cikin Masarautar kenan ko ina kagani an kawata shi da furanni me ban sha’awa an gyara ko ina kuma anata shagalin kide  kide kowa kagani yana farinciki  da wannan rana domin ranar yanci ta zamar masu kowa yana yadda yaso yana cin abinda yaso albarkacin zuwan wannan sarki .

Bangaren me martaba sarki Abul uwais aka fara sauke su suka gaggaisa sannan aka shiga fira sosai tsakanin abokan.
Kiran sallah azahar ya tayar dasu suka tafi masallaci dake cikin Masarautar ana idar da sallah suka dawo gida domin cin abinci su dan huta .

    Kasancewar sarki Abdulgafar da yaran shi kawai ya taho duka hakan yasa gimbiya maryama ta cika da jin haushi saboda an gyara ko ina an kuma canza komai dake  na sashenta domin kece raini da matan sarki Abdulgafar sai kuma taga yaranshi ne mata guda ukku , khadija da hafsat da kuma  Zainab  sai kuma danshi daya tilo  wato ALIYU HAIDAR  haka nan ta daure suka tafi cin abincin da aka shirya gaba daya family din .

       Gaba daya kowa ya hallara a wajen gimbiya maryama kawai ake jira da bakinta sallamar su ta saka gaba daya babban falon akayi shiru ana kallon shigowar su.

    A hankali suke takowa cikin falon cike da izza da jin kai hakan yasa gimbiya mufida da gimbiya sakina jin bacin rai ganin q sashen gimbiya maryama aka sauke bakin kowace  taso wajenta aka sauke su .
Samun  guri sukayi suka zauna sannan aka hau gaisawa cikin mutunci da girmama wa a hankali gimbiya maryama ta kalli kalba tace ina sauran abubuwan dana me kula da girkin ki ta hado? Sunkuyar da kai tayi cikin girmamawa tace Allah ya  taimake ki  nasan tana hanya zuwa yanzu ta gama hada komai .

Sallamarta tahana ta kara magana karasowa zeenat tayi cikin ladabi ta duka tana kwasar gaisuwa kafin daga nan ita da dayar baiwar suka  fara zuzzuba masu abinci

Tunda ta shigo gaba dayan samarin ukku  ALIYU HAIDAR,  UBAID, DA UWAIS  saida gabansu ya fadi kowa da abinda yake ji a ranshi.
tana zuwa kan ubaida zata zuba mai abinci yace mata no barshi kawai na koshi hada min lipton kawai , toh ranka ya dade tace tare da hada mai ta ajiye mashi ta Mike tare da isa gaban uwais da yake ta cika yana batsewa ta hada mashi abinda yace sannan ta matsa wajen HAIDAR dake dan gefe yanata aikin kallonta

Cikin girmamawa ta kara gaida shi domin ita kanta ya burgeta saboda yana da kyau sosai kamar shi yayi kanshi . Tambayar shi abinda zata hada mai tayi kanta a kasa domin ta kasa dago ido ta kalleshi tun kallon farko da tayi mashi taji gabanta na faduwa sosai hakan yasa ta gagara kallon ko inda yake zaune .
.
Ki saka min duk Abinda ranki ya kwanta dashi domin zabinki nake son naci ya fada tare da shafa kanshi yana wani kawataccen murmushi.  Saurin dagowa tayi tana kallon shi saboda tabbatar da shine ke magana ko aljanune suke magana gani tayi yana mata murmushi  me kayatar wa hakan yasa tayi saurin waigawa taga ko ana kallon su sai taga kowa harkar gabanshi yake nacin abinci  sai a lokacin taji yar natsuwa tazo mata .

A haka tabi umarnin shi ta zuba mai komai ta aje mashi ta Mike tayi tafiyarta, tana tafe tana murmushi domin hakan da yayi mata taji dadi sosai koba komai bai wulakanta taba balle kuma kallon banza abin yasata farinciki tana tafiya tana murmushi tana tunanin su kuma yan Nigeria haka suke da kirki da daraja mutane kenan basu da kyama ko wulakanci irin na yan Masarautar mali .

Tun bayan fitarta ya aje abincin data zuba mashi yanata murmushi shi kadai domin wannan ne karo na farko a rayuwar shi da yaga mace a kallo daya yaji ta burgesa  har yaji natsuwa da ita a hankali yace tabbas irinta nake nema irinta na kasa samu a rayuwata ya Allah kasa ta zama alkhaeri a gareni da rayuwata ina sonki kyakkyawa. Ni HAIDAR nayi alkawarin duk wuya duk dadi  ruwa ko iska bazan taba barinki ba wahalar ki tazo karshe da iznin ubangiji.

Mikewa sukayi kowa ya tafi falo domin akwai maganar da Abul Uwais zai gabatar .
Kowa ya natsu haidar ne ya fara bude taro da addua  sannan ya Maimartaba Sarki Abul uwais  ya fara magana kamar haka” ina godiya ga Allah daya nuna mun wannan rana ta farinciki a garemu badon komai sai dan karfafa zumuncin mu ina maka barka da zuwa kasata Aminina .
Kamar yadda kasani inada mata ukku da yara goma  sai….. Kiran sallah da aka fara yasa sarki abul uwais shiru saida aka gama Kiran sallah sannan yace kowa yaje yayi sallah zuwa wani lokacin an kara zaman sanin juna kafin nan sun huta suma da gajiyar tafiya.

Kowa tafiya yayi masu zuwa masallaci suka tafi su kuma matan kowa t wuce sashenta domin gabatar da sallahr la’asar.

   Uwais ne kwance ya rasa meke mai dadi ko ina kwanta fuskarta yake kallon cikin yanayin tsoro  da kuka a lokacin da yake mata cin mutunci .
mtswwwww tsaki yaja sai kuma ya tashi zaune yana magana ” shin meye hadina da ita da zata dinga min gizo  ne bayan ita din kaskantacciya ce kuma baiwa me zanyi da ita ne da  zuciyata ta damu da tunanin ta bayan ko kyautar ta aka min bazan iya ko kallon taba balle na iya rike koda hannunta ne gaskiya idan har zuciya ta tace wannan baiwar zata so bata min adalci ba duk ga kyawawan yan mata nan masu kudi da mulki . Yana ta sambatu a haka bacci ya dauke shi .

Bangaren zeenat kuwa tana shiga dakinsu ta iske su ammi sunata fira ta shiga ta zauna anata fira da ita lokaci zuwa lokaci tana sakin murmushi ita kadai domin ko yaya ta rufe ido toh shi take gani yana mata murmushi har dai Maitama ya kalleta kai sis kodai kyauta aka baki ne baki bamu labari ba kike ta farinciki ke kadai .
Murmushi tayi tace ” hmmmm yaya wallahi wani abu ne ya faru nan dai ta kwashe komai ta gaya masu dariya suka sanya mata sai Ammi tace dole kiji dadi kinsan ance shimfidar fuska tafi ta tabarma duk Masarautar nan babu wanda kike samun magana me dadi daga bakinsa inba muba shiyasa abin yayi maki dadi sosai ni kaina naji dadi .

  “Hmmm Ammi wlh hakane kinsan rannan abinda marasa mutuncin nan su yarima.suka min wlh na tsane su ba karamin tsana ba bana ko kaunar ganin su ko jin sunan su saboda basu da kirki wallah”.
“Kul karna sake jin haka daga bakin ki ki fada Alkhairi akansu ko kiyi shiru domin su din sune shuwagaban ninmu nan gaba”.
“Toh Ammi nadaina insha Allah”.

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 11&12

Bismillahir Rahmanir Rahim.

            MASARAUTAR ULWA

Ta kasance masarauta me faďa aji a kasar mali, tana da tarihi naban mamaki babu wata masarauta data kaita girma da mulki a kasar, hakan yasa duk wanda yake cikinta yanada tsananin izza da mulki tare da jin kai .
Sarki ABDULRAHMAN  ABDULLAHI shine sarki adali na farko a wannan zamanin a Masarautar ulwa,  ya kasance Adali me tausayin talakawa da daraja dan Adam.

Yanada mata biyu
GIMBIYA BILKISU DA  GIMBIYA MARIYA

Gimbiya bilkisu wadda suke kira da (ummy) itace ta farko tana da yara ukku duka maza AHMAD SULAIMAN KABEER  sune yaranta sai dukkan su sunyi aure.

AHMAD:
yana da mata ukku ta farkon ba yar kasar mali bace yar Nigeria  ce acan yaganta yaje yin wani course yace lallai saiya aureta saboda Allah ya dora mashi tsananin kaunar Aisha
kasancewar mahaifinshi yana sonshi duk cikin yayan shi yasa ya goya masa baya yanada sarkin katsina a matsayin wakilin shi aka nema mashi auren Aisha baa bata lokaci ba aka daura masu bayan shekara hudu zaiyi ya koma kasar mali …..

Aisha yar garin Abuja ce a maitama anan unguwar ya ganta yaji yana sonta sunsha soyayya sosai . Aurensu bada dadewa ba ta samu ciki murna wajen su baa magana a haka suka raini cikin harta haihu ta samu da namiji aka saka mai ABDULRAHMAN. Tana yaye shi ta kara samun ciki ta kuma kara namiji UMAR bayan nan kuma ta kara mace khadija tana da cikin na hudu ne AHMAD  ya koma kasar sa domin dibo iyayensa.
Duk da dama wannan yagama abinda ya kawo shi kasar Nigeria .
Babu yadda baiyi ba da Aisha akanta shirya su tafi taki zuwa tace ya barta cikin yan uwanta ta haihu inta haihu sai yazo ya sauke su gaba daya babu yadda ya iya dole ya tafi ya barsu cike sa kewa marar iyaka

Sai bayan koma warsa mahaifanshi suka aura mashi mata biyu akan cewa bazai koma Nigeria ba sai dai ya tura a dauko mai iyalanshi ya gama zaman wata kasa sai tasa babu yadda baiyi ba akan su hakura yaje da kansa amma suka hana haka ya zauna ko yaushe babu lapiya saboda tunanin halin da matar shi zata shiga idan taji cewar bazai zo daukar su ba

Bayan wani lokaci akaje aka neme su baa samu ba sunyi gobara baa san inda suka koma ba babu su sama ko kasa sai dai ya hakura yana addua ya rungumi matansa masu nuna mai kauna.

   Maryam itace matar sa ta biyu tanada yara biyu yaseer da salma

Saita ukku itace karimatu tana da yaro daya

SULAIMAN: yana da mata daya da yara ukku Zahra da kausar sai Ahmed

KABEER: Yanada mata ukku yara biyar

Gimbiya Mariya (mom) tana da yara shidda dukka mata babu namiji akwai BAHIJJA , ZAINAB , RAHMA , HADIZA, FIDDAUSI, FATIMA  ta aurar da yara hudu saura biyu fatima da fiddausi

Zaman lapiya ne sosai ke gudana a wannan masarauta babu cuta ba cutarwa saboda hadin kai irin na wannan family

Ana cikin haka kwatsam sai tashi sukayi da rasuwar wannan adalin sarki wanda mutuwar ta girgiza mutane sosai anyi kuka ba karami ba na rashin sarki ABDULRAHMAN  kowa kagani yana cikin damuwa sai dai tunawa da wanda zai hau mulki sai hankalin ya kwanta .

Yau kwana arba’in kenan da rasuwar sarki a kuma yaune za’a naďa AHMAD a matsayin sarki ….

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 13&14

Bismillahir Rahmanir Rahim.

___________
Nad’in sarki ya kara kawo kwanciyar hankali da natsuwa sosai a wannan masarauta. An samu cigaba sosai cikin shekara ukku da yayi akan mulki, sai dai hakan bai hana shi tunanawa da iyalanshi ba dake zaune a nigeria daya bari, hakan na damunshi don wani lokacin yakan kwanta ciwo in yasaka ma kanshi tunanin da yawa nan da nan sai hawan jinin shi ya tashi…..

     Kasancewar ciwon shi na yawan tashi a lokacin,  sai ya kasance wazirin shi ke gudanar da ragamar fada. Ya yadda da waziri sosai hakan  yasa yakan kwana biyu bai fita fada ba saboda jinyar da yake yi …

Yan uwan Maimartaba Sarki AHMAD ne suka yanke hukuncin fita dashi saudiya domin nema mashi lafiya domin ciwon nashi gaba yake.. sun sanar da fada abinda suka shirya yi sai kuma akasamu su waziri sun bada hadin kai wajen shirya tafiya .
Gaba daya suka shirya domin tafiya aikin hajji daga nan sai su tsaya jinyar dan uwansu . Basu bar kowa ba a cikin wannan family haka suka suka shirya domin tafiya saudiya ..

A hanyar su ta  zuwa Airport aka bude masu wuta  nan da nan aka zagaye su zuwa can saiga wata mota ta tsaya daga gefe. Wani mutum ne ya fito daga motar fuskarsa a rufe gaba daya baka ganin komai a fuskar sa, wata irin dariya yayi yace” Nadauki tsawon shekaru ina rokon Allah ya kawo min irin wannan damar domin aiwatar da k’udirina akan wannan zuri’ar taku, sai yau ne Allah ya nuna mani ita ashe ina da rabon ganin ta ban mutu ba! Kusani daga wannan ranar mulkin ku ya kare domin anan babu wanda zai kara numfashi me tsayi kujerar mulki ta dawo hannuna kuma da dana ya dawo zan daura shi akai “.

wani tashin hankali ne ya ziyarce su domin ko ina suka juya basu da hanyar tsira hakan yasa kowa a cikin in banda addua babu abinda yake domin basu da abinda zasuyi in banda ita . Gashi wurin da suke yana da matsalan network masu waya sai gwada kira suke domin a kawo masu dauki amma abin ya gagara dole sai hakura sukayi suka zuba ma sarautar Allah ido…

       ” Ina son kusani babu wani abu da aha ahalinku ya taba yi mani sai dai ina bakin cikin ganin cewa kunfini, hakan na sakani jin tsanar duk wani abu daya shafe ku, amma kusani zan kashe kune, domin na dandana yadda kuke ji akan mulkin badan kun mani komi ba” . Cewar wannan mutumin daya kulle fuskar sa .

Nan take ya bada umarni aka fara halbin su baibar gurin ba sai daya tabbatar kowa ya mutu sannan suka juya suka bar gurin .Waziri ne dake numfashi sama sama ya zaro wayar shi domin ya kira a kawo masu taimako cikin ikon Allah aka kawo nan da nan mutuwar wadannan adalan mutane ta karade  ko ina .

Mutuwar su ta girgiza mutane sosai  anyi kuka ba karami ba a wannan masarauta sai dai babu yadda suka iya da wannan abu, domin lokacin mutuwar ne yazo koda ba’a kashe suba toh sai sun mutum .

           Bada jimawa ba aka nada sabon sarki
Sai dai wannan sarki yazo da wani sabon salo a mulkin shi wanda hakan ya azaftar da mutane kafin su saba da wannan mulki . Mulki ne ake zubawa na tsantsar izza da rashin imani hakan yasa cikin kankanin lokaci kowa ya gane cewa wannan sarki baida imani ko kadan baisan daraja d’an Adam ba…

Cikin shekara biyar da nad’a sarki ZAINUL ABEEDDEN ,Ba kamar uk’uba wannan masarauta ta ulwa suka shiga ba domin suna amsar azaba ga tarin haraji me yawan gaske inda mutane da yawa suke ta guduwa saboda tsananin bala’i  ..

       A yau ne d’a daya tilo ga sarki zainul Abeedden zai iso an kawata ko ina domin tarar wannan yarima..

Bayi ne ta ko ina suke ma yarima sannu da zuwa “Barka da isowa yarima takawarka lafiya dan sarki jikan sarki , Allah yaja zamaninka ka tashi lafiya ka iso lafiya.  Allah ya kara maka lafiya yarima”. Hannu kawai ya iya daga masu dakyar kafin ya wuce zuwa wajen mahaifinshi da yake tare da mahaifiyarsa da sauran yan uwansa .

“Ina maka barka da zuwa sarkin gobe  insha Allah a gobe zan sauka na nada ka amatsayin da ka dade kana buri gobe kamar yanzu na cika maka wannan buri naka .cewar sarki ZAINUL ABEEDDEN ”  Hmmmm!!Godiya nake my heart Shiyasa nake sonka da yawa babanah momy ke kuma me kika tanadar min ya fada yana murmushi. Dariya tayi tace “ZAID ZAINUL ABEEDDEN kenan  d’ana namiji daya dana mallaka a duniya duk abinda kake da bukata ka fada mani zanyi maka shi ba bata lokaci “.

Dariyar jin dadi yayi yace ” momy ina son na auri  mata biyu a rana daya sai na kara ta ukku bayan sati daya dan haka ki nemo su domin a hada daurin aure da shagalin nadi ” dariya suka sanya mashi tare da cewa lallai akwai zalamammen sarki wajen nan .

Kamar yadda ya fada haka akayi a ranar da aka nada mai rawanin sarki, a ranar aka daura amshi aure da mata biyu . Ta farko itace gimbiya maryama , sai ta biyu itace gimbiya mufida . Bayan sati daya kuma aka sake daura mashi aure da gimbiya sakina ……

Bayan wasu shekaru, gimbiya  maryama ta haifi namiji mai suna uwais tun daga lokacin sarki ya maida ma kanshi suna ABUL UWAIS .. Bayan kwana biyu da suna gimbiya mufida ta haihu ita ma namiji aka saka mai suna ubaid . Daga nan kuma basu kara ba sai bayan shekara daya suka kara haihuwan mata a kusan lokaci daya ,Gimbiya maryama ta samu khadija suna kiranta da (kalba) . Sai gimbiya mufida ta haifi Amira . A sannan kuma gimbiya sakina ta haihu duka mata twins  ta samu asma’u da zainab  .
Bayan nan babu wanda ya kara haihuwa sai gimbiya maryama ta kara mata biyu , jamila da nusaiba . Daga nan haihuwar ta tsaya masu kuma kamar an dauke  ruwa ………..

            _____  MUN DAWO LABARI _____

Dan Allah zeenat ki taimake ni ki yafe min, ki amshi soyayya ta wallahi na rasaki mutuwa zanyi  ina matukar kaunarki, bazan iya rayuwa ba tare dake ba kiji tausayina kinji baby nah .” Allah ya kiyaye kaso wadda ka kira jahila kwaila kidahuma ko kamanta irin tsanar daka min wadda baka ita boye amma kake cewa ni zeenat ni kake so, to karya kake wallahi ni bazan taba sonka ba zuciyata akwai wanda take matukar kauna ban tunanin zan iya rayuwa da wani namiji in ba shiba ” .

” Ki taimaka  min kinji wani tari ne ya sarke shi .; Agigice ya farka yanata uban gumi , tare da dafe kanshi . wai meke damuna ne ni….
MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 15&16

Bismillahir Rahmanir Rahim.

_________
Zaune yake cikin lambu idanuwansa a kulle alamar akwai abinda ke damunsa , a tsanake na kare masa kallo . Fari ne sosai  , yana da dogon hanci , bakinsa ya kasance pink  karami wanda yayi daidai da tsayin fuskarsa . Yana da kwantacciyar suma baka sidik  da ita , yanada kasumba mai kyau hade da gemun sa  wanda ya dace da kyakkyawar doguwar fuskarsa . Dogo  ne yana da faffad’an k’irji yana manyan damatsa. Hakan ya nuna da ganinsa yana gym, ya hadu iya haduwa kyawunsa yana tare da wani irin kwarjini na musamman  .

    A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da fesar da iska , budewa idanuwansa yayi  sannan ya kura ma apple din hannunsa ido kamar yana neman wani abu a jikin sa. Dagowa yayi tare da sakin Murmushi wanda har dimple dinsa suka lotsa
( ni kuwa suman tsaye nayi domin bantaba ganin me kyau irin nashi ba ko a mafarki, sai naga duk kyan dana gani ashe banga kyau ba sai yanzu nake ganin madarar kyau. )

Mikewa yayi tare da fara zagaya gidan domin ji yake yau in bai saka ta a idon shiba wani abu zai iya faruwa dashi .   Yakai awa biyu yana yawo amma ko mai kama da ita bai gani ba, hakan yasa ya tsaya jikin wata bishiya yana sauke numfashi

Ya salam ” ni HAIDAR yanzu ina zan ganki naji dadi a rayuwata zuciyata ciwo take min idanuwana radadi suke min na rashin ganinki meyasa kika zabi boye min kanki kyakkyawa tah. Ya Allah ka bayyana min ita “…….

Tafiya take amma ta rasa meke mata dadi duk wani motsi da zatayi saiya fado mata arai da wannan Murmushin nasa me kyau ahankali  ta furta” ooh ni zeenat meke shirin faruwa dani ne ? Meyasa ko da yaushe nake tunaninsa bayan ko ganinsa ban karayi ba ? Uhmmmm koma dai menene gaskiya kilan aljani ne yake bibiyata bari na isa gida na gaya ma ammi abinda ke damuna.”

Daga kan da zatayi ta hango shi jikin bishiya a tsaye kamar me tunani, da sauri ta boye wani dan lungu  tana hangensa zuciyarta na bugawa sosai . A hankali ta sulale ta lungun ta canza hanya ba tare data bari ya hangota taba ta isa gida tana tunane tunane .

Haka haidar ya gaji ya koma bangaren da aka sauke su ya watsa ruwa ya kwanta yanata tunaninta . ” kina da natsuwa da hankali gashi kina da kyan sura , saina mallakeki insha Allah kyakkyawa tah ” haidar ke wannan magana a haka bacci ya dauke shi me cike da  mafarkanta……

          Bangaren UWAIS kuwa daidai da second daya tunaninta ya kasa barin ranshi daya juya saita fado mashi a rai. Idan kuma ya rintse ido to kamanninta yake gani ya rasa gane kansa kwata kwata .

Yanzu haka bangaren gimbiya kalba ya nufa haka nan domin zuciyarsa take ta azalzalar sa dayaje can ko zai sameta .

Yana zuwa ya tarar gimbiya kalba ta sallami bayinta masu dafa abinci sai kuma gobe bai ida shiga ba ya juya ya koma da niyar gobe anan zaiyi kalacin sa na safe ……………

              ****************
Ammi! Ammi!  Ke wai lafiya kika shigo mana kina kwala min kira kamar zan gudu . Dariya zeenat tayi tace” ammi kenan na kosa na ganki ne ammi shiyasa na shigo inata kiranki ” . Toh zauna sai ki gayan menene da ganin bakin ki akwai magana.

Hmmmm ammi bari na gaya maki abinda ke damuna kuwa” kinsan ai na baki labarin abinda wannan d’an
Sarki nan yayi mani wanda suka zo . Toh shine ko yaushe inta tunanin shi ammi ko in na rintse ido na dinga ganinsa, wallahi ni bansan meke damuna ba ammi “. Ajiyar zuciya ammin ta sauke sannan tace mata” kada kisa ma ranki abinda kika san yafi karfinki, ki tsaya iya matsayin ki banason abinda zai jawo mana damuwa ko tashin hankali kinsan halin da muke ciki dan haka ki cire abin a ranki tun wuri nagaya maki. Ruwa ba sa’an kwando bane , kwarya tabi kwarya inji yan magana”…….

Toh shikenan insha Allah zan kiyaye ammi bari na kwanta sai da safe . Allah ya tashe mu lapiya zeenat…..

                *************
Ubaid ne kwance duk tsawon daren nan amma ya kasa runtsawa ya kasa gane kanshi tun ranar da yafara ganin ta gaba daya ya canza hakan yasa yake zuwa bangaren gimbiya kalba domin ganin ta ko ranar da yayi mata wannan cin mutuncin yayi ne domin ta fita a zuciyar sa amma kashh, hakan bai faru ba saima abinda yayi gaba….

Yau kimanin shekara ukku kenan da zuwansu Masarautar tun ranar Allah ya dora masa kaunar ta amma ya rasa taya zai cireta a zuciyar sa domin yasan yanayin su ba irin nasu bane balle yace zai iya tunkarar ta da wata magana .

Iska ya furzar me zafi tare da furta
” taya zan cireki a zuciya ta bayan shekara ukku kenan ina fama da sonki waye zai taimake ni ya gaya min hanyanr da zanbi na cire ta don nasan bazan sameta ba . Mahaifana bazasu bari na auri baiwa ba “

Wannan dare yazo masu da wani irin al’ajabi babu wanda ya runtsa cikin su hudun….

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 17&18

Bismillahir Rahmanir Rahim.

__________
Gaba daya ahalin Masarautar ulwa ne zaune tare da bakin su wajen cin abinci ,  kasancewar yau Abul uwais da kanshi ya bada umarnin a hada liyafan cin abinci tun daga safe har dare . Kasancewar safiyace hakan yasa babu wanda bai cikin babban falon an kawo masu abinci kala kala…..
Kowa kagani a wannan waje da abinda ya dame shi . Gimbiya maryama ce hakimce a  gefe daya ta kare ma kowa kallo cikin tsantsar tsana take kallon gimbiya mufida .
A ranta take fadin” indai ni maryama ina
numfashi saina ga bayanki da zuri’ar ki mufida, kinyi gangancin shigowa rayuwata da kinsan wacece ni da baki fara wannan giving ba na tsane ki fiye da yadda na tsani mutuwa ta kuma saina nuna maki , dodona yafi karfin tsafin ki mu da kike gani ba haye mukai ba gado ne. Kwarai kuwa NAMU BA IRIN NASU BANE.  In kinji ana fadin haka to tabbas hakan yake ba karya”……..

Yayinda itama gimbiya mufida a fakaice take aika mata da nata kallon tare da harara .tana wani irin wahalallen murmushi mai dauke da abubuwa da yawa ita kadai tasan me take kissimawa a ranta.

Sai dai kuma abinda basu sani ita kanta gimbiya sakina da basu dauke ta a bakin komai ba kasancewar bata haifi namiji  ba hakan bai hana ta jin tsanar suba duka ita fatan ta uban kowa ya mutu ciki kuwa harda sarkin tunda akan dai namiji ake wannan banzan kishin ita ta tsani ubaid da uwais saboda akansu ake neman hanata jin dadin rayuwa….

***
Haidar  ne ya fara kokarin mikewa zai tafi ya kwanta saboda jiya bai isasshen bacci ba saboda tunani da damuwa. Ubaid ne ya Mike da niyyar binshi saboda gaba daya ya kasa cin komai a wajen , tare suka fita suna dan taba fira.  domin sun dan saba da juna sabanin uwais da bai shiga cikinsu a cewarsa ya girmi ya tsaya da yara ……

___Tafiya haidar yake amma gaba daya zazzabi ke neman rufe shi tun basu kai isa masaukin suba, saboda yadda ya damu dason ganinta, ya rasa ta wace hanya zaibi don ya gano inda take amma ba wata hanya
a haka ya daure y isa bangaren su ya kwanta.
Bai dade da kwanciya ba bacci ya dauke shi mai nauyin gaske …

Ubaid kuwa maimakon ya tafi nasu bangaren sai yayi kwana ya nufa lambu ya kwanta yanata tunane tunane akan masoyiyarsa da ya kasa cire sonta a ransa , don ba karamin kamu tayi mai ba😜..

**
Gimbiya kalba ce ke yawon Mike kafa, cikin masarauta tare da bayi tafiya take cikin nishadi da farin ciki , yau ba kamar kullum ba da sassauci a yanayin fuskarta . Gefenta hafsat ce da khadija ‘yayan sarki Abdulgafar da suka zo daga Nigeria.  Tafiya suke kowa kagani da farin ciki a fuskarsa saboda ‘yar shakuwar da suka samu daga zuwansu sai kace dama sunsan juna can zainab ce bata cika biye masu ba, kasancewar ta ba mai yawan surutu ba .

     Suna cikin yawan ne har suka iso bangaren bayi maza anan suka iske ana wasan kokowa ….
Maitama! Maitama! Maitama! Abinda kawai ke tashi a wajen kenan kasancewar shine wanda yaci wasan . Isowarsu wajen yasa kowa yayi tsit ana kallon kallo , dagowa gimbiya kalba tayi taga wanene ake ta kiran  sunan shi. Sai dai tana ganin shi gabanta ne ya fadi domin bata taba ganin kirar namiji haka ba , ba ita kadai ba hatta dasu hafsat  da khady saida gabansu ya fadi suma,  domin ganin halitta iya halitta sai dai ta bangaren bayi ya fito amma duk da hakan kyawun shi bai boye ba.

__ Maitama ya kasance karfaffen namiji mai jini a jika , yana da buďaďďen kirji mai yalwar gashi,  farine amma wahala tasa baka gane hakan saika lura da kyau . Yana da gashi me kyau da kaganshi kaga asalin shuwa Arab.  Yana da tsawo amma ba cancan ba , sai dai baida kiba sosai ,jikin sa daidai da daidai . Fuskar sa tanada tsawo hade da dan fadi , sai gemunsa daya kawata fuskar.

Sai da suka kare mai kallo sannan gimbiya kalba tayi kokarin saita kanta ta fara magana
….” kuna kaskantattu amma kuke iya tsayawa kuma kallon mu , toh bari na tuna  maku in kun manta. Kudin bayi ne , marasa daraja ,wanda basu dagata, kaskantattu , kuna tunanin ku wasu abu ne da har zamu zo wucewa amma ku gagara bamu hanya saboda wani wasan banza naku . Dole hukunci ya hau kanku”
ta karashe maganar cikin bacin rai domin a ganinta an muzanta ta tane gaban baki . Hafsat ce fara lallashinta tana cewa “” haba sis kiyi hakuri kiyi masu uziri kinji kada wannan dan abun ya bata ranki kinji kinga dai muna cikin mood me dadi pls ” ta fada da alamar roko .

“”Toh shikenan na hakura sunci albarkacinki sis muje ” har sun juya sun fara tafiya sukaji ana magana cikin wata irin murya mai Amo da kuma zaki ga dadin saurare duk juyowa sukai suga wake da  irin wannan murya haka .
“”” Ina son kisani ko kusani shi ďan Adam Allah ya daraja  shi, rashin daraja dan Adam wannan sai marar daraja . Kusani mu dukkan mu bayi ne wajen ubangiji  babu wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda yafi jin tsoron sa . Wulakanta mutum ko cin zarafin sa hakan ba abu bane me kyau  a addinin mu amma wasun mu sun dauke shi kamar ado .
Idan mutum takamar sa mulki ko wata izza shin bai tunanin cewa akwai ranar da zai barsu . Akwai ranar da daga shi sai farin likafani za’aje a binne shi , zai kasance daga shi sai abinda ya aikata na Alkhairi kona sharri . A shirye nake da duk hukuncin da zaku yanke min amma kusani shi ubangiji Allah ba azzalumin bawansa bane dan haka ina maraba da dukkun hukunci akan fadar gaskiya danayi”””””””

Maitama ne ke wannan magana hankali kwance inba da dan ana ganin motsin bakinsa ba, babu yadda za’ayi kasan cewa shike wannan magana, saboda babu wata damuwa a tattare dashi ko kadan .

Ajiyar zuciya suka sauke gaba dayansu  saboda ko wace magana da yayi ta ratsa su komai ya fada gaskiya ya fada hakan yasa khady da hafsa suka kama hannun gimbiya kalba suka tafi ba tare da sunce komai ba …….

* **
Bangaren zeenat kuwa duk wata hanya da zata hada ta da dasu yarima ta kulle ta kamar tasan abimda ke faruwa a zukatan su . Yanzu haka ma sauri take ta ida hadama gimbiya kalba abincin darenta ta tafi bangaren su , sai dai abinda bata sani yau zakunan sun fito farauta. Neman abincin zuciyar su .

“Alhamdulillah”, ta fada lokacin da take fitowa sashen gimbiya kalba, tafiya take kanta a kasa, sai gani tayi ansha gabanta . Da sauri ta dago kanta domin ganin wanene wannan sai da gabanta ya fadi domin batayi tunanin zata kara ganin shiba . Kallon juna suke kamar masoyan da suka azabtu da kaunar juna,  an dade ba’a hadu ba . Yarima Haidar ne ya katse shirun ta hanyar fara magana domin zuciyarsa ta kosa taji muryar sahibarta….

“” Amincin Allah ya tabbata a gareki sahibar ruhina , Hakika kin azabtar da zuciyar da ta kamu da kaunar ki a kallo daya . Bansan wace irin kauna zuciyar ALIYU HAIDAR  ke maki ba, abinda kawai nasani shine bazan taba iya rayuwa batare dake ba . Ina me rokon ki daki amshe ni a matsayin abokin rayuwa , ni kuma nayi maki alkawarin duk dadi ko wuya,  bazan taba barinki ba zan zame maki farinciki na har abada .
Ki kalle ni naji dadi, kinji kyakkyawa uwar kyawawa, kinfi kyau , kyau ,saboda kyanki ,kyau yazo gunki don barar kyau tauraruwar taurari”.

Suman tsaye zeenat tayi domin ko a mafarki bata taba kawo ma ranta akwai, wanda zai iya cewa yana sonta . Amma saboda ta gasgata hakan yasa ta dago tana kallon sa . Abinda  ta gani ne ya tada mata hankali  . Ba komai bane face hawaye da taga yana xuba a idanunsa  gashi a durkushe a gabanta ……..

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 19&20

Bismillahir Rahmanir Rahim.

______
Gabanta na tsananta faduwa ta zube, gabanshi tare da fashe wa da kuka , waigawa tayi taga ko akwai mai kallon su ,cikin ikon Allah babu kowa a wajen hakan yasa ta fara magana ..
“” Dan girman Allah ka rufa mani asiri yarima , nidin ba kowa bace face baiwai , marar gata , mudin talakawa ne kamar yadda kuke kiran mu da kaskantattu marasa galihu to haka muke. Ka taimaki rayuwata dan Allah kada ka kara mani magana bani da kowa bani da komai, daga Allah,  sai Ammi nah da yaya AA sai autah su kadai nake gani naji dadi”” . Da gudu ta tashi tana kuka tana tafiya kamar zata kifa kasa.

Tana isa dakinsu, ta tarar da ammi da maitama suna ta fira cikin farin ciki,  fadawa jikin ammin su tayi  tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk mai sauraro.  Hankali a tashe suka fara tambayar ta me aka mata, kukanta ne ya kara tsananta, hakan da suka gani yasa jikinsu kara yin sanyi domin ko wane abu yasa ta kuka, toh ba karamin abu bane , domin tana da juriya d hakuri sosai da  wuya kaga rauninta .

Ammi ce ta fara magana cikin lallashi da tausasa murya,  “” kiyi hakuri mamana, kisani duk tsanani yana tare da sauki insha Allah,  babu wani abu da zai dore , inhar mutum zai kai ma ubangiji kukansa . Kisani ubangiji yana halittar bayinsa ne yadda yaso kuma ya kaddara masu rayuwa , sannan yana jaraba bawansa ta kowace hanya domin gwada imanin sa. Ubangijin daya halicce mu ya kuma kaddara mana rayuwa a haka , bawai ya manta damu bane yana sane damu kuma insha Allahu shine zai fidda mu .

Ubangiji yakan kawo hanya ko sila ta samun sauki ga bayinsa . Bazamu gaza rokon shi daya kawo mana dauki a cikin lamuran mu, Idan abu yasa mu bawa, bawai kuka yakamata yayi ba ISTIGFARI yakamata ya yawaita yi domin tuba ga Allah . Sannan ya yawaita TASBIHI ga ubangiji, toh insha Allah mutum zaiga sassauci a cikin rayuwarsa””.

Ajiyar zuciya suka sauke gaba dayansu, ita da maitama domin sukan gode ma ubangiji daya azurtasu da mahaifiya tagari.

( Dan Allah iyaye mu tsaya sosai akan lamuran yaran mu, domin suyi alfahari da samun mu a matsayin iyaye nagari a garesu, saimun dage mun kuma daure sosai , Allahu ya wadatar damu duniya da lahira.)

“”” insha Allah ammi zamuyi amfani da dukkan abinda kika fada mana, muna alfahari dake Ammi.” Suka fada gaba dayansu suna murmushi , sai lokacin Zeenat tasamu natsuwa ta gaya masu dukkan abinda ya faru tsakanin ta da yarima HAIDAR.  babu wanda ya iya magana cikin su domin abin ya basu mamakin da basuyi zato ba . Ammi ce dai ta bata shawarar kaucewa duk inda tasan zasu hadu domin gujema matsala…

***
Bangaren yarima Haidar kuwa direct wajen mahaifinshi ya nufa , bai tsaya neman iso ba saboda abinda yake damunsa , yarasa farinciki zaiyi ko akasin hakan , da sallama ya shiga babban falon, sai dai bai samu mahaifinshi anan ba , kai tsaye ya nufi bedroom din yayi sallama tare da tura kofar ya shiga.

Gabansa yaje ya duka yana gaishe shi cikin girmamawa kamar yadda ya saba.”” Meke tafe da yarima da daren nan aka kasa hakurin safiya .” Cewar me martaba sarki Abdulgafar yana murmushi,  sosa kai ya fara, domin mahaifinshi shine abokin shi dashi yake duk wata shawara , baida tarin abokai sosai abokinsa daya tal ABUBAKAR  yana kiransa da sadeeq.  Sannan ya daure dai ya fara magana.
“” Abba dama wata magana ce mai mahimmanci sosai nake son fada maka !!” “Uhumm ina jinka fada min kayi shiru kuma kodai yau ranar da zanyi rawa ne? Maganar sirikata kuma  diyata zaka fada min? ”
“” Abba wata yarinya nagani a wannan masarauta amma baiwa ce sai dai tana da natsuwa sosai da hankali  kuma ina kaunarta sosai tunda na fara ganinta”.
Kasancewar ba boye boye tsakanin su nan ya fada ma mahaifinshi komai da komai akan lamarin soyayyar shi.

“” Tunda har ka aminta da ita nima na Aminta da ita domin nasan bazaka taba zaban abinda baida nasababa , kaje ka cigaba da neman soyayyar ta, kafin lokacin tafiyar mu , idan ta Amince sai mu tafi da ita da iyayen nata can ayi bikin acan kasar mu . Amma ina son kada ka gaya ma kowa wannan magana , kaji Allah ya taimaka zan maka ISTHIKHARA akan lamarin  , kaima kayi duk da nasan bazaka tunkareta ba tare da kayi ba . Amma ka karayi domin neman zabin Allah.

( yakamata komai zamuyi mu rika neman zabin Allah akan lamuran mu , Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi . Yana koyar damu yin ISTHIKHARA domin neman zabin Allah a cikin dukkan al’amuran mu . Idan mutum yayi niyyar yin wani abu kowane iri ne toh yayi isthikhara domin neman haske wajen ubangiji. )

” Insha Allah zan cigaba da Addua kamar yadda ka fada min nagode sosai Abba nah”
Cewar haidar yana mikewa tare da kara yi ma mahaifinshi sai da safe yabar dakin cikin farinciki marar misultuwa.

****
Bangaren yarima ubaid kuwa ya yanke shawarar tunkarar zeenat da maganar soyayyar shi , domin yayi iya yinshi akan ya cire sonta a ransa amma ya kasa, amma yau dai ya yanke hukuncin fita neman ta domin gaya mata abinda ke ranshi. Sai dai zuciyar shi na hana shi ” tayaya kana dan sarki amma kaje wajen wata baiwa, talaka da ita kace kana sonta! ai kasan ka zubda ma kanka daraja a idon mutane dama iyayenka , ka cireta kota halin kaka ka nemi daidai da tsarin ka “.
Haka dai ya kwanta da ne tare da bin shawarar zuciyar sa.

_________ uwais ________

       Shiko uwais ya tanadi rashin mutunci tare da azaba kala da zaiyi ma zeenat akan ta fita daga tunanin shi, domin shi a ganin sa tana sane take zuwan mai a tunanin hakan yasa ya yanke hukuncin azabtar da ita ta hanya da dama harsai ta daina zuwan mai a tunani .

( Toh jama’a kunji wani salon soyayya ta bangaren uwais 😜😃😃😃.)

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 21&22

Bismillahir Rahmanir Rahim.

____________
A lokacin da wasu ke bacci don hutawa, a lokacin ne wasu ke neman duniyar su , a kuma sannan wasu ke neman dacewa da gafarar ubangiji.

Karfe 3:00am  zeenat ta tashi , ta tayar da Ammin su domin gabatar nafila domin samun sauki a cikin lamuran su , hakan ya rigada ya zame masu jiki, duk dare sai sun tashi sunyi salloli tare da addua har zuwa sallar asuba sannan suke dan rintsawa , shiyasa sun saba da kwanciya da wuri saboda tashin da sukeyi . Kamar yau ma haka ta kasance sun gama sallolin su na nafila sun dukufa akan adduan Allah yayi masu zabi na Alkhairi.

“” ya ubangiji Allah kaine ka halicce mu , kaine ka kaddara mana wannan rayuwar da muke ciki , ya Allah ka kawo mana sauki , ya Allah ina rokonka da sunayenka kyawawa Allah kayi mani zabin miji nagari, Allah ka sanya mana farinciki a zuciyar mu , Ya ubangiji ina rokon ka ka azurtani da miji me tsananin kauna ta , ya ubangiji Allah ka tabbatar min da duk wanda yake alkhaeri a gareni a duk inda yake ko yaya yake indai shine Alkhairi na, Allah ka kara mana hakuri da juriya akan dukkan abinda zaizo garemu na Alkhairi kona sharri Alfarmar Annabi Muhammad ( SAW) “. Zeenat ta shafa adduan tana fashewa da kukan tausayin rayuwar su.

Ammi ce ta dafa kafadar Zeenat tana cewa “Kiyi hakuri, mai hakuri yakan dafa dutse har yasha romansa,  ina me kara baki hakuri ‘yata ki kasance me juriya kinji, Allah yana tare dake kuma insha inaji a jikina farin cikinku zaizo indai munada rai da rayuwa “.

*********
Bangaren yarima Haidar kuwa saboda farin cikin da yake ciki, kasa bacci yayi salloli yake ta jerowa yana ma Allah godiya bisa ga ni’imar da yayi masa ,  kamar yadda mahaifinshi yace masa,  yayi isthikhara aikuwa ya yayi duk da dama saida ya nemi zabin Allah akan lamarin kafin yaje gurin zeenat , saida yaji natsuwa sosai akanta kafin ya tunkareta da maganar soyayyar sa,

Addua ya daga hannu yana zuba ma ubangiji kirari
“” Ya ubangijin sammai da kassai,  Ya ubangijin da baya bacci ko gyangyadi , Ya ubangiji Kaine me kyauta me kari , ya Allah  ina rokonka da sunayenka kyawawa,  ya Hayyu ya qayyum , ya zaljalalu wal’ikhram , ya Ar rahmar rahimin,  ubangiji Allah idan har wannan baiwa taka Alkhairi ce a gareni rayuwata, da kuma addinina ,  Allah ka mallaka min ita , Allah kasa na zamar mata dukkan farin ciki, Allah kasa na zama silar yaye dukkan wani tabo ko damuwa dake tattare da ita, Allah kasa na zama haske a cikin rayuwarta ,
Ya Allah kada kabani ikon musguna ma rayuwar bawanka , ya Allah kada kasa na zama silar zuban hawayen dukkan wanda ya rabeni ,  Allah kada ka bani ikon saka damuwa a zuciyar kowa maimakon farin ciki,  ya ubangiji Allah ka bani ikon taimakon duk wanda yake da bukatar taimakawa””……….

________ UBAID ________

          A lokacin da bacci ya kaurace ma idanuwansa maimakon yayi tunanin mika ma Allah lamarinsa,  sai yayi tunanin tafiya club domin wannan dabi’ar sace ta badda kama ya fice ta kofar sirri sai da safe yake dawowa .

Koda ya fita sai yayi kiran abokansa da suke tafiya tare , bada jimawa ba suka iso da mota suka dauke shi , sunata tafiya suna fira dukkansu da kagansu kasan ‘yayan manya ne masu fada aji a kasar mali,  hakan ya zame masu kamar dole ne wannan fita yawon su debo yan mata su tafi gidan nazeer daya daga cikinsu , anan suke baje kolinsu .

Yau kam wasu yan mata suka gani sun dawo talla wani gari dare yayi masu ga mai mota yanata aikin gyara , motar taki tashi harun tsaya da niyyar kwasar su sai kuma junaid yace” guys  wannan fa kazamai ne ku kalle su da kyau ba ko nonon kirki babu,  kuma in ma sunyi maku ai kunga su ukku ne mu kuma mu biyar ne dan haka ku mayar da maitar ku mu tafi wajen mata masu aji “”.
” kumafa hakane gaskiya kawai sagir ja motar mu wuce ” cewar kamal , ubaid ne kawai baice komai ba cikinsu domin shisha yake zuka abinsa , kamar ba shine wannan salihin nan ba shiru shiru ,  haka suka wuce club acan suka kwana suna sheke ayarsu.

( wa iya zubillah  Allah ya shirya mamu zuria ).

*****
Uwais da momynsa kuwa suna gurfane gaban dodon su, domin a ganin su lokaci ya kusa da uwais zai hau kujerar mulki.
sai dai shi a kagare yake gari ya waye domin a nemo masa zeenat  a kai mashi ita dakin horo a gabansa yake so ayi mata horo mafi tsananin gaske domin tasan shiba sa’an ta bane . Tsawar da aka daka masa ce ta maido dashi cikin hayyacin sa.
“” Ina son kasani akwai wata baiwa da take cikin bayinku dole sai kun nemota  domin  itace makamin dukkan wata nasara taku, banganin fuskarta domin tana da tsari sosai jikinta bamu iya ganinta anan , amma tana cikin Masarautar ku dole ku nemota, idan har kuna son mulkin ku ya zamto naku ,  yazo kuma  hannun ku yadda kuke so,  toh lallai saida wannan yarinya, saika aure ta sannan! Dan haka kuje ku nemota “….

” karya ne nafi karfin na auri baiwa gaskiya dan haka ka canza magana dan abinda bazai yiwu bane ehe”” uwais ya fada tare da mike tsaye yayi tafiyar sa yabarsu nan .

Momy ce tayi saurin fara magana ” kayi hakuri dodon tsafi bazai kara maimaita hakan ba kuskure ne, ayi mana rai a gafarce mu , zamu nemota kamar yadda ka fada “.. wata irin dariya me ban tsoro dodon yayi, sannan ya daka wata irin tsawa dayasa momy sakin fitsari anan,  “””  idan kunyi ruwanku in ma bakuyi ba ruwanku dan haka tashi ki bamu waje “””. Ya fada cikin kaushin murya . Da sauri tabar wajen ta koma ta inda ta biyo ta dawo gida batare da anganta ba .

______
Gimbiya kalba kuwa haka take ta juye juye akan gadonta bacci ya kaurace ma idanuwanta, babu abinda take gani data rufe idanunta sai fuskarsa,  kunnuwanta muryarsa kawai ke amma kuwwa a ciki .

” wai meke shirin faruwa dani ne ni kalba?  komai zanyi sai najishi a jikina , ya hana min nayi sukuni naji dadi , idan kuwa soyayyar shi ce zata shiga zuciyata  toh tabbas  bata min adalci ba , taya zata so abinda bai dace da matsayin taba ? Kai gaskiya bazai taba faruwa ba ni kalba naso bawa,  da sake  gaskiya dole a nemo minshi goben nan “”.  Haka gimbiya kalba keta maganganu ita kadai kamar zararra cikin dare .

( ni kuwa nace adai kira shi ki ganshi zuciya taji dadi.😜🤐🏃‍♀️)

Gimbiya mufida kuwa baccinta tasha hankali kwance domin bata da wata damuwa saboda ta dogara da tsafinta .
Asuba tagari gimbiya 👍

**** ******
Bangaren maitama kuwa yana gama sallolin da zaiyi ya koma ya kwanta sai dai ya kasa bacci , daidai da gyangyadi yaki zuwar mai babu abinda yake tunani sai, masoyiyarsa wato Arwah, Yana mata kauna sosai mai tsananin gaske . ” Ina son nazo na ganki Arwah tah na kusa zuwa gareki insha Allah ki zama mallakina “.

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 23&24

Bismillahir Rahmanir Rahim.

___________
*** KAUYEN KYAUTA ***
Kauyen kyauta wani dan karamin garine na asalin shuwa Arab da suke zaune a wajen kasancewar duk yawancin su, shuwa  ne hakan yasa komai nasu yakasance daban dana sauran kauyukan ,
Gidan malam. Abubakar Adamu  gida ne  daya kasance mafi girma da yawa a kauyen , matan sa biyu da yara biyar uwar gidansa Halimatu ( yayye)  tana da yara biyu mace  Aminatu da namiji Abubakar suna kiranshi (kukku) sai amaryar hindatu ( Nannah)  nada ukku dukka mata, Muhsina da Na’ima sai maijidda,
mutane da yawa sun nanu son auren aminatu  saboda tsananin kyau da ubangiji ya bata kamar ita tayi kanta tana da wani irin kyau me daukar hankali da kwarjini  kallo daya zata maka karasa meke dawainiya dakai , tsoronta ko kwarjini ta maka, ko kuwa soyayyar ta , haka Allah ya halicce ta. Tana da sanyin hali sosai kuma tana da saukin kai saidai batayi karatun boko ba kasancewar duka basuyi amma suna na islamiyya.

Ana tsaka da rikicin da ake akan wanda zai aure tah sai Allah ya kawo wani, Me suna Usman anan kusa da kauyen su , kasancewar yana da ilmin sosai, domin shike koyar da yan garin maza karatun addini, sai mahaifin aminatu wato malam Abubakar ya bashi aurenta , bayan wani lokaci soyayya me tsafta ta kullu tsakanin su , basu dade ba aka daura auren su , dama sai  an shirya kayan aure sannan ake tsayar da miji a kauyen . Bayan auren bada dadewa ba Allah ya azurtasu da samun ciki , sunyi murna sosai da farin cikin wannan ciki ,bayan wata tara ta haifi yarta me kama da ita sak kamar tayi kaki ta zubar, Ranar suna yarinya taci sunan AISHATU ana kiran ta da ARWA kasancewar sunan mahaifiyar malam usman ce wato sirikar Aminatu.  An haifi ARWAH  da wata biyar
Kukku ya tafi karatu nan cikin bamako babban birnin mali.

A haka dai rayuwar su malam usman da ‘yarsu  Arwah tayi ta tafiya cikin farin ciki da kulawa , Arwah na cika shekara biyu mahaifiyar ta takara samun wani cikin , sunyi murna sosai da hakan sunata rainon cikin har ya isa watan haihuwa , Ranar wata asabar Aminatu ta tashi da nakuda gadan gadan , kasancewar sunfi haihuwa a gida hakan yasa basuyi tunanin kaita asibiti har gari ya waye tana abu daya , koda aka kara yini guda bata haihu ba mahaifanta suka dauke ta domin kaita asibiti sai dai a hanyar su ta zuwa asibitin Allah yayi mata rasuwa ita da abinda ke cikinta.

Kwana arba’in kenan  da rasuwar Aminatu Aka daura mai aure da kanwarta Muhsina wadda suke uba daya da marigayiya,  domin ta rike AISHATU , da farko Arwah na samun kulawa sosai a wajen muhsina, sai dai bayan tafiyar malam usman bamako domin anso shedar bude makarantun da akayi a kauyen na boko dana addini, a lokacin ta canza ta fara kyarar ta , duk wata kulawa ta daina samunta sai bakar azaba kala kala , idan yunwa ta is ishe ta sai dai ta tafi gidan kakarta wato mamar mahaifiyar ta  wadda take kira da Amma, taci abinci ayi mata wanka sai ta koma gida duk da hakan kuma sai ta samun hukunci wajen muhsina wadda take cewa mama. A haka dai har babanta ya dawo sannan ta samu salama wajen mama sai dai duk da haka ba kamar yadda take mata da ba , saboda an riga an mata huduba ta kuma dauka..

Ana bude makaranta ya saka Arwah saboda yana son tayi karatu sosai domin inganta rayuwarta , zuwanta makaranta yasa ta samu salama domin bata da lokacin zaman gidan data dawo makarantar boko ita da babanta zasuci abinci yayi mata wanka su tafi islamiyya, kasancewar ko wane fanni yana koyarwa boko da Arabic . Tashin hankalin da muhsina ta bijiro dashi na sai ya mayar da Arwah wajen kakarta yasa sukayi fada sosai saboda ya nuna mata shi namiji ne kuma a tsaye yake , hakan yasa tace bata iya zama da ita sai dai ya zaba ko ita ko Arwah  , baida zabin daya wuce ya zaba ‘yarshi domin yafi kaunarta fiye da komai a rayuwarsa , kaunar da yake ma mahaifiyar Arwah ta karu akan ‘yarta sosai saboda kamanninta da dauka gaba daya .
Muhsina tayi kuka saboda ta dauka zai zabe tane akan Arwah  gashi a yanzu tana son mijinta saidai ta jawo ma kanta da kanta ya sake tah. Saidai dayake kowa yasan laifinta ne babu wanda ya daga  maganar , ko mahaifiyar ta da yan uwanta babu wanda yayi zaton zatayi haka domin kansu a hade yake zugar kawayen banza muhsina ke dauka sai gashi sunkai ta sun baro.

A haka ya cigaba da kulawa da ‘yarsa tare da taimakon Amma data maida ita ‘ya ba jika ba , anan gidan take kwana saita yini a gidan babanta domin tsaftace masa shi .
A yanzu haka js3 su Arwah suke tana da matukar kokari sosai domin babu wanda yakaita kokari duk makarantar itace tafi kowa , a yanzu dai tana da shekara 15 amma har yanzu mahaifinta bai kuma aure ba saboda yana son saiya aurar da ‘yarshi  sannan ya duba yagani ya samu wata ya aura ….

Yau dai suna hanyar dawowa makaranta ita da mahaifinta suka gamu da wasu mutane sunsha bakar wuya , a galabaice suke sosai duk sun kwanta su ukku babu me motsin kirki da sauri suka karasa kusa dasu , taimaka masu sukayi har suka isa gidansu dasu anan suka basu ruwa ta ruga ta amso masu abinci gidan Amma ta kawo masu sukaci suka kwanta , daki suka basu guda daya wanda yake matsayin na Arwah,  shi kuma namijin aka kaishi dakin Abbun tah ya kwanta

Bayan tashin su wajen karfe 11:26  suna zaune anan suka bama Abbu labarin rayuwarsu , ya tausaya masu anan kuma yace su zaune a gidan shi kafin lokacin da zasu tafi ,  washe gari yaje yasamu kakannin Arwah ya fada masu komai suma sunyi na’am da bakin su zauna har zuwa lokacin da zasu tafi , haka ma iyayen Abbun sun yarda da zaman bakin ,

Zaman mutunci ne ya wanzu tsakanin su Ammi da yan kauyen baki daya domin sun nuna masu karamci sosai , shakuwa sosai ta shiga tsakanin zeenat da Arwah duk da zeenat zata girme ma Arwah amma a haka suka kulle kamar dama sun san juna , kayanta ta dauko ta dawo gidansu kasancewar ta samu su Ammi , sai dai kuma dawowarta gidan suka dinke da maitama a haka dai har soyayya ta shiga tsakanin su sosai batare dasu kansu sun farga ba, tun suna boyewa har ta fito kowa yasani, tare suke zuwa makaranta kasancewar an dauke shi aiki saboda yayi karatu shima kuma da takardunsa yake tafe . Akwana a tashi harsu Arwah sun shiga ss2 sunata soyayya da maitama , tafiyar su ta tashi badon sunso ba haka suka tafi suka bar kauyen da mutanen cikinsa masu karamci saidai mahaifin Arwah yayi ma maitama alkawarin bashi auren ta koda bai numfashi a doron kasa

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 25&26

Bismillahir Rahmanir Rahim.

____________
Zeenat ce ke tafiya a hankali cikin natsuwa,  tana ta ISTIGFARI  a cikin zuciyarta
Hankali kwance domin ba damuwar komai tattare da ita, “” Amincin Allah ya tabbata a gareki hasken idaniyata , farin ciki , Albarka da tarin natsuwa su kara tabbata ga ma’abociyar su .””  Saurin juyawa tayi domin bata manta muryarsa ba , kasa magana tayi domin bata da abinda zatace , saurin  dukawa tayi tare da cewa “”” Barka da safiya ranka ya dade fatan an tashi lafiya “”” iyakar abinda ta iya fada kenan domin jikinta rawa yake ko ina , “” Lafiya lau Alhamdulillah  ina fatan kema hakan ” da sauri ta gyada mashi kai domin ta kasa magana kuma ta kosa ya sallameta, “” Hmmmm kiyi hakuri dani fa na tsare ki da magana ke gashi ma maganar kin kasa , ina son isar da sakon da yake raina ne ko zan samu salama , kinga bansan kiba bansan ina kike ba, ko sunan  ki bansani ba amma zuciyata ta kamu da matsanancin kaunarki dan Allah ki tausaya ma zuciyar ALIYU HAIDAR “””. Ajiyar zuciya ta sauke amma ta kasa magana sai hawaye da take yi domin bata da bakin magana .

Magana yarima haidar zaiyi sai kuma ya dakata domin ganin yarima uwais na tunkaro su , jin yayi shiru ita kuma ta dauka ya gama ne ta Mike da niyyar tafiya taci karo da yarima uwais , tassss tasss  yarima uwais ya dauke zeenat da lafiyayyun maruka har biyu ” keee dabbar ina ce wai meyasa komai zakiyi sai kin nuna dakikanci ne eyey ? Amma zan nuna maki niba sa’an wasanki bane bari na dawo jikinki zai gaya maki “”” Rufe bakin sa keda wuya yarima Haidar ya sauke mashi lafiyayyun Marika har ukku domin ranshi yakai  kololuwar baci  magana ya fara cikin bacin rai kamar mayunwacin zaki “”” kai wane irin kalan mutum ne ? Mace zaka daga hannu ka mara ? Kasan darajar mace kuwa da har zaka iya daga hannu ka duketa , toh vari na gaya maka idan baka sani ba , mace da kake gani ubangiji ya karrama ta ya bata abubuwa masu daraja wanda ba kowace halitta yake bamawa ba , kasani macece ta raini cikin ka daga wata daya har zuwa wata tara tasha wuyan nakudan ka sannan ta haife ka, ta raine ka ta baka kulawa har kakai matakin da kake kai, Amma yanzu mace kake daga hannu ka mara macen ma marar gata , kasan irin bakin dake gareta ne ? Idan tayi maka addua wallahi sai ubangiji ya hukuntaka saboda kaci zalinta ne , laifi tayi min amma kasancewar ta mace yasa naji tausayin ta na kyale ta amma kai daga ta bige ka bata sani ba shine tayi laifin mari dan Allah ku dinga sanin yadda ake hukunci da kuma laifin da ake ma hukuncin  “”.

Daga zeenat har yarima uwais sandarewa sukayi suna kallon yarima Haidar lokaci guda ya koma kamar wani zaki , yarima uwais ne yayi murmushin takaici ya kalli yarima Haidar y fara magana”” Ni Uwais zaka daga hannu ka mara akan wannan banzan marar tunani , toh kasani wallahi kaci Albarkacin mahaifinka ina sonsa ina kuma girmama shi , amma da wallahi sai dai wani bakai ba, kaje ka tambayi wanene yarima uwais  a gaya maka , akan rashin sanin wanene ni shiyasa harka iya daga hannu ka mareni , keeee kuma wallahi saina lahira yafiki jin dadi ya jawo maki bala’in da sai kin gwanmaci mutuwa dashi”””…
Fuuuuuu haka ya wuce su kamar zai tashi sama  saboda yadda ranshi ke tafarfasa, zeenat ce tayi kokarin juyawa itama ta koma gida domin gaya ma Ammi abinda ya faru, yarima Haidar ya tsayar d ita ta hanyar shan gabanta yace”” kiyi hakuri kinji habibtiy  nah kada wannan maganar tasa ki damu ni zan shawo kan matsalar insha Allah , indai ina numfashi toh kinbar shan wata wahala ko damuwa ki yadda dani kinji kaunatah , wallahi sonki ne ya rufe min ido bansan ma na wanke shi da mari ba , amma kada ki damu zanje na lallashe shi kinji , dan Allah kisoni kodan kwatan wanda nake maki ne inba so kike na kama haukan da ban shirya ba akanki sarauniyar kyawawa , Amma dai dangin ku larabawa ne ko indiyawa?” Ya karashe maganar yana murmushi domin Allah yayi mata wani irin madarar kyau wanda ba kowa ke lura dashi ba sai mai rabo. “” Nagode sosai Allah yasaka da Alkhairi Amma dan Allah kadaina saka kanka damuwa akaina , indai irin wannan ne mun saba dashi ka kyale ni kawai ka fita rayuwata kada hakan ya janyo maka matsala nagode “” ta fada da juyawa zata wuce da sauri yace mata “” Dan Allah ki daina wahalar min da bakinki wajen fadin abinda bazan iya ba akanki , ki daure ki gaya min koda sunan ki ne”””. Zeenat ” ta fada a takaice ta wuce tabarshi tsaye yana kwallonta yana murmushi………….

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 27&28

Bismillahir Rahmanir Rahim.

*******

        “””Ya ubangijin sammai da kassai, Allah ka bani ikon taimakon waďanan bayin naka , hakika ina matukar kaunarki zeenah in sha Allah saina mallakeki,  saina maida rayuwarku rayuwar farin ciki “”.  Juyawa yayi ya tafi domin ya kwanta ya huta tunda yaga masoyiyarsa kuma yayi magana da ita. Bai kaiga isa sashen da yake ba yasamu sakon kira daga mahaifinshi,  bai kasa a gwiwa ba ya juya domin amsa kiran Abban nashi ,

Da sallama ya shiga ya tarar da mahaifinshi a kwance yana hutawa “” barka da safiya ranka ya dade fatan an tashi lafiya ” amsa masa yayi yana ya nuna mashi waje ya zauna ya fara magana
“” Dama na kiraka ne akan maganar da mukayi dakai toh kaga daga nan kasar ina son na shiga Cameron daga can na koma gida dan haka nan da sati daya ne tafiyar mu ka kokarta kasamu amincewarta zuwa lokacin,  saimu tafi da iyalansu amma ina bukatar naganta ita da ahalinta gaba daya domin yin magana dasu akan lamarin, da naso cikin yaran Abul uwais kasamu daya saidai da nayi mashi maganar,  nuna mani yayi bazai iya aurar da yaranshi wata kasa ba, so shiyasa na Aminta da zancenka , kuma ina mai adduan Allah yasa ta zama alkhaeri a garemu baki daya”.
“”Insha Allah muna fatan hakan Abba,  zan  k`ok`arta don ganin komai yayi da yardar Allah”.
Tattaunawa suka cigaba dayi akan lamarin har aka kira sallahr Azahar suka tafi masallaci tare. Bayan gama sallar , sashen su ya wuce yadan kwanta bai dade ba bacci ya dauke shi dama a gajiye yake.

*****
Bangaren uwais kuwa yana tafiya amma ranshi a mugun bace yake , wajen mahaifiyar shi zaije , koda isar sa ya gama tsara yadda zai azabtar da zeenat da yarima Haidar domin sun shiga gonar daba tasu ba . Ko sallama baiyi ba haka ya shiga tare da zama kusa da ita yana huci , momy kallonsa take kamar tasamu television a gabanta bata ce masa komai ba sai ruwa data dauka mai sanyi ta bashi don tasan abinda zaiyi saurin sauko dashi kenan.                        “” Meya faru dakai son naga ranka a bace ? Ko wani abu akai maka ne daya bata ranka? Gaya min ko menene inji””
Ranshi ne yaji ya kara  baci sosai nan take ya kwashe komai daya faru ya gaya mata , itama ranta ne yayi mugun baci ta Mike cikin tsananin bala’i ta fara sassafa masifa”” kamar kai wani sakaran ďan sarki zai mara , baisan yadda mulkin Masarautar ulwa yake bane dazai mareka gaban kaskantacciyar baiwa , lallai yaja mata bala’in da bai tunani , maza tashi kasa a kamo min ita a gabana nake bukatar a mata hukunci mafi muni””.
“”Momy  duk irin abinda na tanada nasan naki mai sauki ne kwantar da hankalinki basu san wanene UWAIS ba ki jira zakiji anzo maki da labari “” .  yarima uwais ya fada cikin huci da hargagi , komawa sukayi suka zaune su duka,  sai lokacin momy ta tuna da abinda yasa ta kira shi a hankali cikin lallashi ta fara mai magana..
“”””” Son dan Allah inason ka daure ka natsu akan maganar da mukayi da dodon tsafi kaji dai abinda ya fada muddin kana son hawa kujerar mahaifinka dole kayi abinda yace inba haka ba kanaji kana gani ďan uwanka UBAID zai haye ya barka a yariman ka “” …

Wani matsiyacin kallo yake bin mahaifiyar tashi dashi domin tasan babu abinda ya tsana kamar tace ubaid zai hau mulki bashi ba , nan take bacin rai ya kara bayyana akan fuskar shi , Itama momy kallon shi take don tasan inba ta haka ta biyo mashi ba bazai dauki abin da mahimmanci ba .
“”” Momy babu yadda za’ayi dan zan hau mulki ace saina auri baiwa , kema kinsan abinda bazai yiwu bane da kun canza shawara da yafi,  kuma ma ta ina kike tunanin zamu gane baiwar balle har hakan tafaru ?  Kubar zancen kawai don bazai taba faruwa ba “”. Kallon shi take cikin bacin rai domin ya fara bata mata rai akan taurin kansa , “”” To shikenan tunda haka ka zaba nabar wahalar dakaina akanka kaje kayi duk abinda kaga dama tunda kai sakarai ne marar tunani sai kaje ai amma kasani wannan karo zan cire hannuna akanka ne “”  tana gama fada ta tashi tabashi waje , anan ya zauna yana ta tunani , abin ya hade mashi biyu . Mikewa yayi ya fita shima aransa yana ta tunanin ina zaisa a nemo mashi ita nan ya tuna bangaren gimbiya kalba yafi ganin ta , can ya nufa a ganinsa gara ya sauke nauyi daya .

Gimbiya kalba tana zaune tana tunanin maitama,  ta rasa meke mata dadi a rayuwarta , yau tunda ta tashi takasa cin komai tunanin sa take yi , a yau ji take idan bata ganshi ba zuciyarta tana iya samun matsala , shiryawa tayi domin fita neman sa a hanyar fita sukaci karo da yarima uwais ya shigo, tsayawa tayi suka gaisa anan domin kowa d uzurinsa , harta wuce yace mata “” sister ina wannan  baiwar taki ne wadda rannan ta bige ni ? Ita nazo nema ina fatan tana nan “”. Kallonsa take juyo tanayi sai a sannan ta fara tunanin yau bata ganta ba dayar me kula da abincinta kawai ta gani , “” yarima nima ban ganta ba yau amma ina tunanin bata lafiya can zanje dubata domin idan karya ne saina mata hukunci ma tsanani”” haka kawai gimbiya kalba ta tsinci kanta da fada domin kawai bata son kowa yasan halin da take ciki .
“”Muje tare ya fada tare da fara tafiya ”
Don dole tasa aka kira baiwar da tasan wajen da zeenat take suka tafi .

Zeenat kuwa tana komawa gida ta fada ma ammin ta abinda ya faru,  addua kawai sukaci gaba dayi da kuma jiran tsammani , maitama na nan don haka gaba dayansu suna dakin harda auta , maitama ne yake ma auta karin hadith da Qur’ani , dama shike kowa mashi hada na boko domin har turanci auta naji indai akayi , itama zeenat azkhar ne hannunta tana karantawa .
Sallama sukaji anyi sai dai sanin hakan zata iya faruwa kowane lokaci abin sai baisa gabansu faduwa ba addua kawai suka cigaba dayi a lokacin,  izinin shigowa suka bada sai dai  yarima yace bazai shiga dakin bayi ba sai dai su fito waje ..

Fitowa suka suka dan duka suna gaishe su sai dai maitama ko kallon inda suke baiyi ba balle a kaiga batun wata gaisawa,  wani irin izza da jin kai ya saukar mashi a lokacin dan haka a tsaye yake kare masu kallo a wulakance.
Gimbiya kalba kuwa gabanta faduwa yake sosai domin wanda ta fito nema gashi nan tana gani harda mahaifiyar shi da k`annan sa ,”” dama wannan baiwar kanwarsa ce  gaskiya dole suke kyawawa ashe bashi kadai bane kyakkyawa su dukan sun biyo kyau ne wajen mahaifiyar su”” haka take ta sambatu a ranta tana ta kallonsa kamar tasamu television.

Yarima uwais shi kansa saida gabanshi ya fadi don sunyi mashi kwarjini sosai haka kawai ya tsinci kansa da jin nauyin Ammi da kuma ganin girman ta , ya rasa ma me zai ce domin yakasa yin komai akan abinda ya shirya yi , da sauri yabar wajen gabansa na tsananta faduwa,  koda ya tafi haka gimbiya kalba ta kalli zeenat tace “” an fada min baki lafiya ya jikin Allah ya kara sauki””” iya abinda ta fada kenan ta juya domin itama a rikice take ta rasa meke dawainiya da ita a lokacin……..

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 29&30

Bismillahir Rahmanir Rahim.

         Tafiya gimbiya kalba keyi amma gabanta na faduwa sosai, babu abinda ke mata yawo a idanunta sai fuskarsa da ko kallonta baiyi ba , haka nan take jin matukar tsoron sa tunda ta kalle shi a yanayin data ganshi ciki, ko kadan batai tunanin yana da jin kai haka ba sai gashi ko kallo basu ishesa ba, a haka harta isa sashenta tana  tunani batare data sani ba ….

Yarima uwais kuwa kasa motsin kirki yayi har gimbiya kalba tazo ta wuce shi anan tsaye yanata tunanin yadda zai hukunta su akan abinda sukayi mashi ita da yarima Haidar domin sun shiga gonar daba tasu ba inji shi😜
Haka ya juya ya nufi sashen da yarima Haidar yake domin suyita acan tunda bai samu damar hukunta zeenat ba a yanzu , yana tafiya yana mamakin yadda yakasa yin komai a gaban zeenat dasu Ammi , sai dai yadauki alwashin sai yayi ma zeenat hukuncin da batayi zato ba….

Kafin ya isa bangaren ne suka hadu da yarima ubaid ya taho hanyar da yarima uwais ya biyo , ya dawo shikuma zaije , tsayawa sukayi suna kallon kallo tsakanin su domin kowane da abinda ya k`unsa akan dan uwansa . Tsaki yarima ubaid yayi zai wuce  , sai yarima uwais ya fisgo hannunsa ya dawo dashi kafin yayi wata magana ya dauke shi da mari , ďagowar da yarima ubaid zaiyi sai yarima uwais ya kara masa wani marin , ya fara magana cikin bacin rai,
“””””” Kai harka isa kayi min tsaki ? Ko dan kaga ina raga maka ? Toh kasani ruwa ba sa’an kwando bane , idan ba haka ba wallahi sai nayi maganinka a wannan masarauta,  mtsewww sakarai kawai wanda baisan inda kansa ke masa ciwo ba , ka fita harka ta idan ba haka ba saina batar dakai “”””….
A furnace ya juya da niyyar tafiya sai dai  saukar lafiyayyun maruka da yarima ubaid ya watsa ma masa yasa ya daskare a wajen ya kasa ko matsin kirki saboda zallar mamaki “” Nika ďaga hannu ka mara ubaidullah? Kana cin hankalin ka kuwa ? In mareka ka daga hannu ka rama ? Tabbb aikuwa ka debo ruwan dafa kanka ubaid,  wallahi sai kayi nadamar daga hannun dakayi ka taba fuskata . Zan baka mamaki yadda bakayi zato ba , zan kuma nuna maka wutsiyar rak`umi tayi nisa da kasa ka jira lokacin yana zuwa”””…….

“””” Idan kai wawa ne toh niba wawa bane , taya zaka daga hannu ka mareni kayi tunanin ka mari banza ? Toh kasani ubaid ba sakarai bane da zakace zaka raina kamar kowa , ni nafi karfinka wallahi,  ina mai sheda maka zan baka mamaki niba kalan sakarkarin mutanen da zaka ma yadda kake so  bane nafika iskanci wallahi mu zuba, shege ka fasa , banza kawai babu abinda yasani sai dabbanci  da ubaid kake yi mtswwwwww””””…
Yarima ubaid ke wannan magana data razana yarima uwais nan da nan hankalin shi ya tashi,  baisan lokacin da ya juya da niyyar shak`o yarima ubaid sai dai yaga wayam domin shi yayi tafiyar sa, nan ya tsaya ya rasa ma me zaiyi kan wa zai sauke haushinsa , karasawa yayi sashen da yarima Haidar yake yayi domin ya fara takansa kafin sauran su biyo baya…

Yana shiga ko sallama bai tsaya yiba ya kutsa kai cikin falon , sai dai bai iske kowa ba a ciki sai tv da ac dake kunne suna aiki ,  hakan yasa bai tsaya neman izini ba ya shiga cikin bedroom din kai tsaye .
“”  kai wane irin mutum ne da zaka shigo ma mutane batare da sallama ba ? ” yarima Haidar ya fada ransa a bace ..
“” Sallama ! Wannan kaika Santa don haka gargadi nazo in maka na karshe , wallahi akuyar ka ta kiyayi ramata idan ba haka ba wallahi sai dai wani ya koma kasar ku amma badai kai ba. Ina gaya maka da babbar murya ni yarima uwais ba sa’an yinka bane don haka ka fita a harkata idan kak`i ji ai bazaka k`i gani ba “”…

Wani irin murmushi yarima Haidar yayi, yana k`are masa kallo  “”””Amma  tunda nake ban taba ganin jahilin mutum irinka ba,  marar tunani da sanin darajar dan Adam , abinda nake son kasani niba irinka bane banda lokacin batawa akanka, don ina da abinda ya fika mahimmanci da nakeyi  don haka zaka iya tafiya”””…
Rasa abinda zaice yayi dole haka ya juya yabar dakin zuciyar sa na tafarfasa . Bangaren sa ya wuce fuuuuuuu kamar zai tashi sama saboda yadda ranshi ke tafarfasa baiko ganin gabansa sosai haka ya isa , yana shiga ya fada kan gadon sa kwanta yana ta tunanin yadda zai maganin UBAID,  ZEENAT,  DA YARIMA HAIDAR……

*****
Bangaren su zeenat kuwa koda sukaga duk sun fita mikewa sukayi suka koma daki suka zauna , zeenat na kwance ta daura kanta a cinyar Ammi tana ta Hamdala da tasbihi da zuciyar ta duk da bata saka ma ranta cewar yarima Haidar ya kyaleta bane amma taji hankalinta ya kwanta da ganin ya kasa komai a gaban Ammi da yan uwanta..
Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tare da fadin “””” Alhamdulillah ya Allah , babu Abin bautawa da gaskiya sai kai , ya ubangiji Allah kaine mafi sanin dai-dai Allah, ubangiji Allah ka tsare mu da dukkan sharri ka sada mu da dukkan Alkhairin ka , ZEENAT  kiyi hakuri ki kuma k`ara akan wanda kikeyi, sannan ki kara dagewa da addua  domin itace makamin mumini, insha Allah komai mai wucewa ne wata rana sai labari.  Hakika muna cikin jarabawar ubangiji,  Amma ina son kusani babu wanda ya isa ya canza Abinda Allah ya kaddara a rayuwar mu  sai shi daya daura mana , dan haka ku kara rike addua sosai “”……..

     ( Hakika addua bata bar komai ba dan haka  mu rike addua domin samun sauki da salama a rayuwar mu.)

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 31&32

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Zaune take a falo tana jiran isowar yariman tah  domin ta kosa ta ganshi kota ji dadi a ranta . Tunani take irin yadda yake gwada mata soyayya kamar babu sauran wata mace a duniya , wani irin sanyayyan kiss taji an sakar mata ya dawo d ita hayyacin ta, da sauri ta fada jikinsa tana bubbuga kafa cikin shagwaba tare da ďan kukanta da bai kai ciki ba ta fara mai magana cikin sangarta”” Habibi shine kabarni ni kadai ko inata jiranka .”” Kiyi hakuri Habibti wallahi na biya ta masarauta ne me martaba ne ya kirani amma kiyi shiru aina dawo babu inda zan kara zuwa kinji habibti nah”” uhm uhum nidai gaskiya saika goya ni zan hakura “;  aikuwa kamar yana jira ya goya ta suka wuce sama.
Babu wani daďewa suka sauko kasa dinning suka nufa ta bashi abinci yaci ya koshi itama ta bashi yaci ya koshi , suna gamawa suka koma garden domin su dan huta a can .  Babban garden ne akwai bangaren swimming pool a ciki akwai bangaren tsintsaye kala kala masu kyau da daukar hankali sai kuma bangaren shuke shuke iri iri suma . Bangaren flowers suka nufa suka zauna akan wasu kujeru masu kyau gefe kuma wani dan lilo ne .
Rungumeta yayi a jikinsa tare da sauke ajiyar zuciya “”” Habibti nah da zuciya tana buďewa ki gane ma idonki son da nake maki na tabbatar da zakiji tasauyina Habibti.  Ina matukar kaunarki ! Bansan wane irin so nake maki ba , kawai dai abinda nasani bazan iya rayuwa babu ke a tare dani ba . Kullum Addua ta Allah ya barmu tare har karshen rayuwarmu ya bamu zuri’a tagari. Ke kadai ce farinciki nah Habibti. “””
Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un!  Abinda zeenat ta fada kenan lokacin data farka daga nannauyan barcin daya dauke ta.

A duk lokacin da bawa ya tsinci kansa cikin wani hali toh bashi da wata mafita face ya mik`a lamarinsa ga ubangiji domin samun mafita, Haka ya kasance ga zeenat domin ta mik`a ma Allah dukkan lamuran ta . Koda yaushe addua take akan Allah yayi mata zabi nagari , kwance take tana tunanin wannan daddad’an mafarki da tayi . Murmushi tayi tare da mikewa don yin sallah .

Bangaren yarima Haidar kuwa shiri yake na musamman domin zuwa sashen dasu zeenat suke , dakakkiyar shaddarsa ya saka royal blue sai yayi ado da takalma golden, agogo ma ya saka na gold shima kalar golden,   hular kansa me tsadar gaske wadda ta dace da kalar shaddar yasaka , Alkyabbar daya saka kalar golden ta kara fito da ainahin kyansa . Gaban madubi ya koma ya kara kallon kansa . “Alhamdulillah” itace abinda ya furta domin shi kansa yasan yayi kyau , kara turaruka yayi sosai a jikinsa sai ya kara gyara sajensa . Kasancewar sa fari ne sosai hakan yasa ba karamin kyau yayi ba.
Yana da wani irin kyau na daukar hankali, sai dai tafiyar sa me cike da natsuwa kawai zaka kalla kasan jinin sarauta ne shi.  Shiga ta Alfarma yayi ,ya fito tare da bayi a bayansa wanda zasu masa rakiya.

Tunda ta gama sallah take jin gabanta na faduwa sai dai bata gaya ma kowa ba kawai ta cigaba da addua a zuciyar ta . Fira suke sosai kasancewar da yamma ne anyi sallar  la’asar yasa dukka sun dawo gida saboda  ranar juma’a ce , tana kwance kan cinyar Ammi , Autah kuma yana kwance kan cinyar maitama sunata fira gwanin burgewa . Sallama akayi daga waje hakan yasa maitama ya Mike don ganin wanene saboda bangaren mata ne maza basu shiga kai tsaye saida izini .

    “Bismillah ranka ya dade ka shigo ”  cewar maitama yana gaba yarima Haidar na biye dashi a baya . Sallama sukayi gaba daya suna shiga cikin ďakin, kasa mikewa zaune zeenat tayi domin yadda gabanta ya tsananta faduwa kamar zai faďo waje . Har kasa yarima Haidar ya duk’a ya gaida Ammi ta amsa masa cikin farinciki da jin dadi nan take taji kaunar yarima har k’asan zuciyar ta . Zama yayi kafin ya fara masu magana akan abinda ya kawo shi.
“”” Ammi Akwai magana me mahimmanci data kawo ni wajenku dan Allah ina rok’on ku kuyi hakuri da abinda zan fada saboda bansan yadda zaku dauki maganar ba . Ammi gaskiya naga zeenat kuma ina kaunarta sosai ! Aurenta kuma zanyi insha Allah,  tun ranar dana fara ganinta saida na fada ma mahaifina maganar  kasancewar mahaifina shine kamar abokina na ban boye masa damuwata , shiyasa banyi k’asa a gwiwa ba naje na same shi da maganar kuma ya amince min ,  ya kuma  bani goyan baya 100%. Dan haka ne ma ya nemi dana zo na gabatar da kaina , kuma na rokan masa Alfarmar ganinku domin kuyi magana dashi .””””

Gaba dayansu wata irin ajiyar zuciya suka sauke a tare, suka bishi da idanuwa kamar an dasa su a wajen ko motsin kirki sun kasa domin kamar a mafarki suke jin maganganun nasa. Saidai sabanin zeenat da tayi suman wucen gadi anan kwance .
Maitama ne yayi gyaran murya ganin Ammi bazata ce komai ba, yanayinta ma ya nuna kunya take ji ga kuma wani k’warjini da yayi masu , “”” Ba komai Ranka ya dade ka cigaba da addua in sha Allah babu matsala indai sister rabon kace zaka aure ta amma maganar gaskiya bazamu mata auren dole ba sai in tana sonka kuma ta Amince dakai a matsayin abokin rayuwa sannan auren zai tabbata . Maimartaba kuma basai yazo ba zamuje mu same shi insha Allah sai ku fidda ranar da yake son ganin namu.”””””

” Nagode Nagode sosai in sha Allah babu damuwa zan mashi magana saina dawo na fada maku . Da yardar ubangiji bazakuyi dana sanin aura min zeenat ba zan rike ta bisa amana da Aminci insha Allah na maku wannan Alkawarin “”……

Godiy ya kara masu sannan ya aje masu kudi masu yawan gaske ya mik’e yana satar kallon zeenat dake kwance kamar ruwa ya cinye ta. Rakiya maitama yayi masa yana kara yi masa godiya akan karamcin daya nuna masu.
Koda ya dawo sai ya cema zeenat taje yana jiranta a  waje , kasa tashi tayi daga inda take har yanzu gani take kamar mafarki ne take . Saida Ammi ta kara mata magana sannan ta Mike ta dauka hijab dinta ta saka ta fita . Koda ta tafi tattaunawa su Ammi suka cigaba dayi akan lamarin …

Koda ta fita a zaune ta iske shi akan wani dan damali dake dan lungun dazai sadaka d inda su zeenat suke. Sallama tayi mashi tare da gaishe shi , Amsawa yayi yana murmushi dajin wani irin shauk’i mai dauke da farin ciki na musamman.  ” Amincin Allah ya tabbata a gareki Habibtiy ” wata irin bugawa k’irjin zeenat yayi kamar zai wuntsulo waje da sauri ta daga kai tana kallonsa da  dararan idanuwanta. Shi kansa saida gabansa ya fadi data sauke masa waďannan idanuwan nata . Baisan lokacin daya furta”” masha Allah gaskiya komai naki ba irin na kowa bane Habibtiy kina da wani irin kyau na musamman Allah na gode maka Ubangiji ka mallaka min wannan baiwa takaaa”;
Kasa cewa komai tayi sai dai ta mayar da kanta kasa tana wasa da yatsunta. Ganin bazata ce komai ba sai ya hakura ya kyale ta yayi mata sallama ya tafi akan gobe ta daure taje lambu su haďu . Gida ta shige abinta shi kuma ya nufi bangaren da mahaifinshi yake..

Koda ya isa mahaifinshi kawai ya iske a falo yana hutawa bai dade da shigowa ba, saboda fitar da sukayi zuwa wani waje shiyasa a gajiye yake baiko shiga bedroom dinsa ba iyakarsa falo bayi nayi masa tausa,
Duk abinda suka tattauna a gidan su zeenat ya kwashe ya fada ma mahaifinshi.  Mai martaba ya fidda rana akan gobe suzo babu inda zai fita sai suyi maganar da zasuyi . Sunyi maganganu sosai ,  kafin kuma suyi shirin zuwa sallar magriba Koda suka gama basu dawo ba sai bayan sallar is isha’i  daga nan kowa ya tafi domin hutawa …

    Koda yarima Haidar  kwanta murmushi kawai yake domin komai ya tuna sai yaji farinciki sosai .
Haka bangaren zeenat ta rasa me takeji farinciki ko akasin hakan .
Da haka dai bacci yayi gaba da ita …
Asuba tagari zeenat……

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 33&34

Bismillahir Rahmanir Rahim.

__________
washe gari tun wajen karfe goma na safe su  Ammi suka sami iso cikin falon me martaba sarki ABDUL GAFAR. yana zaune cikin shiga ta Alfarma, cikakken adalin sarki wanda bai ɗauki rayuwar duniya da zafi ba. AMMI na zaune daga gefe ɗaya cikin hijab dinta da ƴar atamfar ta wadda kallo daya zakayi ma atamfar kasan taji jiki duk da kasancewar atamfar me tsada . tayi kyau sosai duk wahalar da suke sha hakan bai hana kyawunsu fitowa , daga daman ta kuwa maitama ne shima cikin yadi mafi soyuwa a wajensa .
yayi masa mugun kyau duk da bai niyyar saka shi ba Ammi ce ta umarce shi daya daka shiyasa ma ya saka , ya aje sane da niyyar sai zaije wajen Arwah.  Sannan ya saka yayi mata kwalliya ta musamman dashi domin yana son yadin ta dalilin ta yasame shi shiyasa ya dauke shi da muhimmanci sosai .

Gyaran murya me martaba yayi ya kalle su, akwai inda yasan me kama da waɗannan mutane amma ya rasa a ina ne kanshi ya ƙulle sosai . Kauda tunanin yayi sannan ya fara magana .

      “””” Alhamdulillah!  Alhamdulillah! Muna  ma Allah godiya daya tara mu anan domin ƙulla Alkhairi ko ince zumunci.  muna maku barka da zuwa da  fatan Aminci a gareku.
Maƙasudin zaman mu anan dai game da ALIYU ne. Yazo yasa me mu da maganar yarinyar ku , cewar yana sonta da aure! Toh fatan mu kenan dama yaga wadda hankalin sa ya kwanta da ita , munfi son zabinsa ya kasance na farko . Toh mudai ýan Nigerian  ne muna rokonku idan kun amince da batun mu , muna son mu tafi daku gaba daya can domin yin hidimar auren acan . Amma fa sai da amincewar ku , idan baku amince ba zamu iya hakura sai a daura auren daga nan mu tafi da yarinyar can . Idan hakan shima bamai yiwuwa bane zaku iya fada ba matsala bane sai ya hakura da ita yarinyar . Duk da ya kamu da kaunar ta sosai “””……….

Maitama ne ya fara magana kansa tsaye don yasan Ammi bazatayi magana ba.

” Allah ya taimakeka ina ganin a bamu lokaci domin zuwa muyi shawara abinda muka yanke saimu sanar maka in shaa Allah “”…

Wani irin murmushi me martaba yayi irin nasu na manya kafin nan kuma yace masa,

“” Babu matsala Allah yasa mudace “.

Kallon juna Ammi da maitama sukayi kowa da irin Abinda yake tunani da kyar Ammi ta bude baki tace …

” Ameeen ya Allah godiya muke Allah ya kara maka lafiya da tsawon rai mai Amfani””…

“Ameen ya Rabbil Alamin “.

“Amma zanso naji daga ina kuke in babu damuwa?.”

Da sauri Ammi ta daga kai gabanta na tsananta faduwa tace masa.

“” Ranka ya dade basai kasani ba yanzu tunda ba Amincewa mukayi ba tukunna kabari abinda muka yanke zakaji daga garemu . A gafarce ni idan na fadi ba daidai ba “…..

Kallonta sosai me martaba yake yana nazarin ta sai dai baice komai ba illah kallo kawai da yake binsu dasu kasancewar kansu a kasa yake hakan yasa basu ga irin kallon da yake masu ba. Sai dai suna ji a jikinsu ana kallon su amma babu wanda ya iya ďagowa ya kalle shi..

“” shikenan Allah ya kaimu zaku iya tafiya mun gode”….

Da sauri suka Mike suka kara mashi sallama suka fito . Suna cikin tafiya ne maitama ya kasa shiru yace ……

    “”” Ammi  wai meyasa baki son kowa yasan tarihin mu ? Mu kanmu kinki gaya mana Asalin mu meyasa? “….

“” idan lokacin sanin yayi ko baku tambaya ba zaku sani  da sauran lokaci “”.

    Iyakar abinda ta fada masa kenan ta wuce tabarsa tsaye anan , tunani ya shiga amma ya kasa kamo bakin zaren domin taki basu kofa ko ya take .

Tafiya ya cigaba dayi zuwa sashen su , yana hanya ne aka aiko kiransa zuwa bangaren gimbiya kalba. Bai kawo komai a ransa ba ya tafi batare daya juya zuwa kiran ba , sai ya nufa sashen su domin kar a gansa da kayan jikinsa .
Yana shiga ya canza kayan zuwa na bayi ya fito ya nufi bangaren gimbiya kalba kai tsaye .

Zaune ya iske ta cikin kaya na Alfarma.
Lace ne tasaka kalar black da red yana da matukar tsada sosai. Kallo daya zakayi masa kasan an kashe kudi wajen siyanshi
Ta saka sarkar gold dinta da zoben ta sai abin hannu suma na gold tare da wasu zabban duk na gold ..
Kayan sunyi mata kyau sosai don ba karamin kyau tayi ba . Bata saka Alkyabba ba sai mayafi red data yafa a kanta wanda ya kara fito da kyawun kwalliyar ..

kallo daya yayi mata ya dauke kansa don ko kadan batai masa ba hasali ma haushin ta yake ji sosai ..

“Ranki ya dade naji sakon kiranki a gafarce ni sai yanzu na samu isowa”…

Kallon shi take kamar ta samu tv ji take kamar ta maida shi cikin jikinta kota huta da azabtuwar da zuciyar ta ke mata akan sonsa . Amma da yake tana ji da kanta ko a fuska baka taba gane yanayinta.

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 35&36

Bismillahir Rahmanir Rahim.

_______
Ta ɗauki tsawon minti talatin tana kallonsa,   ta manta waye a gabanta ta zuba ma idanuwa tana kallo . Wani irin farinciki take ji har ƙasan ranta, a lokacin ji take bata da sauran wata damuwa a duniya idan har zata kasance tare dashi a haka, wani irin sonsa take ji tun daga ƙarƙashin zuciyarta , tana jin kamar mutuwa zatayi idan tarasa shi a matsayin abokin rayuwa.
Wani irin haushi da tsanarta yake ji cikin zuciyarsa , ko kaɗan baisan rainin wayau da wulakanci, akan mi zata kira shi tayi banza dashi . Kasancewar kansa a kasa yake bai san ma kallonsa take ba , yanaji a jikinsa ana kallon sa amma bai kawo ita bace . Hakan yasa idanuwansa yin jajur saboda bacin rai , yana ďagowa suka hada ido dashi
Gabanta sai da ya faďi ganin yanayin da yake ciki , kasa jure kallon nasa tayi dole tayi kasa da nata idon .

“”” Ranki ya daɗe kinsa an kirani amma baki ce komai ba”. Maitama ya faɗa ransa duk ba daɗi don ji yake idan batayi gaggawar sallamar sa ba zai iya gaya mata magana marar daɗi.
” Dama na kiraka ne naji yaya jikin wannan yarinyar duk da bansan ya kuke da ita ba amma tunda naganka ɓangaren su nasan da wani abu a tsakanin ku”.
Haka kawai gimbiya kalba ta tsinci kanta da faɗa masa batare data shirya hakan ba.

” Taji sauki Alhamdulillah “.
Iya abinda ya iya fada mata kenan a ƙufule .

   Ji tayi muryarsa ta mata daďin saurara kamar tayi tajin ta koda wane lokaci .

Kasa jurewa yayi yace mata “” shikenan zan iya tafiya?” .

Rasa abin cewa tayi sai dai ta gyaɗa mashi kai,  har yakai kofa kuma ya tsinkayi muryarta tana cewa.
” kana da mata ne ? ”
Juyowa yayi yana kallon ta batare da shayin komai ba a tattare dashi yace mata.
” ina da mata wadda nake ƙauna da dukkan zuciyata , wadda zan iya bata numfashi na don ita ta rayu” …..

Wata irin muguwar ƙwarewa gimbiya kalba tayi take taji duniyar na juya mata amma saboda dakewa ruwa ta dauka takai bakinta don jin sassauci. kasa jurewa tayi ta kara ce masa.
“” kana nufin itace rayuwar ka kenan? Toh ita kuma wannan baiwar dana ganka a ɓangaren su miye alaƙar ku ?”””……

Haka nan  yaji wata izza na shigar shi sai dai kuma komi ya tuna kawai yayi murmushi yace mata.
“”‘ Idan da akwai abinda yafi rayuwa toh ita ɗin ta wuce wannan abin itace komai na kamar yadda nasan nine komai nata “”….

Harya juya yafara tafiya sai kuma  ya dawo yace mata “” Ita kuma baiwar da kike magana akanta jinina ce. In kika cire mahaifiyar mu babu mahalukin da nake so sama dasu,  ita da autan mu sai kuma matata.  na barki lafiya”””””….

Haka ya tafi yabar gimbiya kalba a zaune kamar an dasa ta . Komai ya kwance mata ta rasa meke mata da daďi a rayuwarta , wani irin mugun kishinsa take ji kamar tayi hauka . Da gudu ta Mike ta shige bedroom dinta ta faďa kan gado sai a lokacin taji wasu hawaye masu azaba na sauko mata.

“” Wai wace irin rayuwa ce wannan ? Zuciya ta baki min adalci ba , taya zaki so wanda bai dace dake ba ? Meye haka ne da zaki kaini inda zan ƙasƙantu?  Ina matsayin gimbiya amma na fada son wani banzan bawa , wanda bai ma san inayi ba . Yana da wadda yake so fiye da yadda yake son kansa . Yanzu ni meye makoma ta ? Wallahi saika so ni dole!!!!”…..

Kukan da take ya tsananta maganar ta daina fita  dole tayi shiru ta cigaba da kukanta sai dai taci alwashi kala kala…..

*********
Yarima uwais ne kwance ya rasa abinda masa daɗi,  ya rasa me yakamata yayi akan abinda yarima ubaid yayi masa . Sai dai wani gefen na zuciyar sa yana gaya masa akan yasa a kamo mai zeenat , hukunci ya fara hawa kanta amma ya rasa dalilin da yasa yake jin faɗuwar gaba sosai a duk lokacin da yayi wani yunƙuri don aikata wani akanta .
Turawa yayi aje azo  masa da zeenat daga nan a tafi da ita ɗakin horo . Idan ya gama abinda yake sai yaje  yasa ayi mata kalar hukuncin da yayi niyya.

Tafiya zeenat take cikin natsuwa domin zuwa ɓangaren gimbiya kalba,  sai dai tana zuwa tsakanin part din ɓangaren su dana su gimbiya kalba aka tare ta anan . Ko kadan bata daga ma kanta hankali ba domin bata cire rai da jiran hukuncin yarima uwais ba dama , hakan yasa ba gardama ta juya da nufin binsu.

        “”””” Kai ina zakuje da ita a haka ? “..
Maganar yarima ubaid ta daki kunnuwan bayin da aka saka su kamo zeenat  . Fitowar sa kenan zai tafi shan iska cikin gari yaci karo dasu . Sai dai a lokacin daya ganta ya tuna masa da soyayyar sa , saboda tunda ya hadu da wata shaiďaniyar yarinya ta canza mai tunani koda yaushe tana naniƙe dashi hakan yasa ya fara mantawa da zeenat a zuciyar sa .
Cikin wata irin tsawa ya kara masu magana ganin sai kame kame suke . “” Nace gidan ubanwa zaku kaita ?””” ……

   “”””‘ Allah yaja da ran yarima!  dama yarima uwais ne yasa mu kamo ta mukai masa ita ďakin horo “”…

Wani shu’umin murmushi ya saki tare da ce masu “” toh ku kaita ina zuwa “..

Babu musu suka juya domin cika umarnin sa.
Yarima ubaid komawa yayi part ɗinsa ya canza kaya ya fito ya nufi ɗakin horo….

Koda isar yarima ubaid, shi kuma yarima uwais yazo har an kawo mai  kujera ya zaune .

“”” Nifa jahilci da duhun kan wasu na bani mamaki  , in ba rashin tunani ba me mutum zaiji idan ya huce haushin sa akan macee . Uhum Allah wadaran naka ya lalace dai”””…

Wani irin baƙin ciki ne ya ziyarci yarima uwais domin yasan sarai dashi yarima ubaid  yake. Sai dai yau ya ɗauki alwashin saiya koya masa hankali.
Mikewa yayi yace ma bayin su basu waje saboda baisan ayi abinda wani bawa zai gani har ya samu abin bada labari . Ganin sun fita daga shi sai yarima sai zeenat da aka daure ma kafa da hannuwa jikin icce yace masa….

   “”” Daɗina da gobe saurin zuwa! Meye naka na sauri hukunci?naka na nan zuwa kanka. don babu wani mahaluki da zai hanani naci ubanka ubaidullah “”””…

Wata irin dariya yarima ubaid ya fara harda ďukawa . Zuwa can ya Mike ya haďe fuska kamar bai taba dariya ba tunda yake a duniya , kai kace sakon mutuwar mahaifiyar shi aka sanar masa .

    “”” Cikakken jarumi faďa da cikawa aka sanshi dashi . bawai iya bakinsa ba, idan kai ďin kana jin kanka namiji ne ,  a filin daga ya kamata a ganka bawai ka bige ga hukunta mace ba sakarai kawai “””..

Takaici ya ishi yarima uwais hakan yasa cikin zafin nama ya ďaga hannu da nufin ya mari yarima ubaid.  Sai dai kafin ya sauka a fuskarsa ya rike hannun nasa, yana wani irin huci .

“” Uwais kasani ni ba kanwar lasa  bane balle kace zaka ďanďani idan kuwa kayi wannan kuskuren to ka tabbata saina nuna maka banbancin dake tsakanin aya da tsakuwa””…

“”” Iyyye ni yarima uwais kake gaya ma magana son ranka  to wallahi sai kayi nadama kuma yanzu zan gwada maka karfin ikona fiye da naka a cikin wannan masarauta “””..

Wata irin dariya yarima ubaid ya tinstire da Ita . “” Toh ni Wane irin iko ne Kake dashi da Bandashi a Masarautar nan?”..

Wasu bayi yarima uwais ya kira.  Da sauri suka isa gabansa suka ďuka , umarni ya basu akan su cigaba da bugun zeenat har sai ya basu umarnin dainawa .

Allah sarki zeenat tunda suka fara wannan musayar yawu babu abinda takeyi sai addua domin Allah ne kawai zai cece ta a yau. Rintse idanuwanta tayi tana cigaba da addua da jiran saukar bulali.  Sai dai maganar da yarima ubaid yayi tasa ta saurin buɗe ido.

   “” Wallahi duk wanda ya sake ya taɓa ta,  saina masa hukuncin da sai ya gwanmaci mutuwa akan rayuwar sa””…

Babu wanda yayi yunkurin sauke bulalar akan jikin zeenat, domin sun razana da furucin yarima ubaid.

Nan take rigima ta ɓarke tsakanin yarima uwais da yarima ubaid.  Rigima sosai suke anan wajen.  Bayin sun cirko-cirko domin kowane tsoro yake basu . Hakan da suke ne yasa zeenat fashewa da kuka ta fara masu magana cikin kuka…

“””” Dan girman Allah mene na tsare maku ne a rayuwa? Duk kun ɗauki tsana kun ɗaura min saboda kawai kunaji da mulki ? To ku kasheni ku huta kawai. dan Allah nima na huta ma rayuwata .  Amma ina son kusani, babu wani mulki ko jin daďi da zai ďore , zamu mutu. wannann rayuwar ba tabbatatta bace ba , dole zan mutu! zaku mutu , kowa da kuke gani dole yabar duniyar nan. Wanda akayi duniyar ma dominsa ( SAW )  yabarta bai cikin ta . Balle mu daba kowan kowa ba dan haka kuyi min dukkan hukuncin da zakuyi min  a shirye nake dana mutuuuuu””…….
Dukkansu mutuwar tsaye sukayi domin basuyi tsammanin waďannan maganganun  daga bakinta ba .
Yarima ubaid baice komai ba,  haka ya juya ya tafi jikinsa a sanyaye .
Shi kansa uban gayyar yarima uwais rasa abinyi yayi sai dai ya saka a kwance zeenat ta tafi. Shi kuma ya nufi ɓangaren mahaifiyar shi…
Haka zeenat ta tashi ta tafi jikinta a sanyaye tana ta kuka.  ta nufi ɓangaren su a hanya taci karo da yarima Haidar..

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 37&38

Bismillahir Rahmanir Rahim.

  Tafiya take cikin sauri, duk da ta gansa ya ganta amma bata son ya ganta cikin yanayin da take hakan yasa ta kara sauri sosai . Ganin yana niyyar cimmata yasa ala dolenta  ta tsaya bata shiga sashin nasu ba . Kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta ya iso inda take bata yarda ta daga kai ta kalle shiba saima kara kasa da tayi da  kanta . “”Amincin Allah ya tabbata a gareki Habibtiy nah ina fatan kina lafiya ?”. Ya tambayeta amma yana kara nazarin fuskarta don yaga tayi alamun tayi kuka kuma da abinda ke damunta. “” Lafiya lau Alhamdulillah yarimaaa fatan kuna lafiya?”””. Abinda ta fada kenan da ya kara bayyanar da rauninta sam hankalinsa bai kwanta da ganinta da yayi a cikin wannan yanayi ba,  amma koma menene zai sani . “” Lafiya lau muke Habibti nah,  daga ina kike a haka naga alamun kinyi kuka meke damunki?”” Rasa abinda zatace masa tayi sai dai tayi kasa da kanta, tana tunanin yaushe har yasanta da zaisan tana cikin damuwa ? Meyasa shi yakasa fahimta ne tsakanina dashi akwai banbanci,  bamu dace da juna ba yafi karfi na.  Amma dayake bai gani yarasa wa zaiso saini zeenat gaskiya da abinda ya samu wannan yariman dan inba wani abu ke damun sa ba ina ni ina shi wutsiyar rakumi tai nisa da kasa ai . Tazarar da nisa , gaskiya dole ya kyale ni don bansan inda zan kaisa ba ni yafi karfina .

Shirun da yaji yayi yawa yasa ya kalleta, ganin taunani ma take hankalin ta ba akansa yake ba. Shima sai ya zuba mata idanu yana kallo . Wata irin kaunarta yake ji har kasan zuciya, ji yake kamar ya tsaga jikinsa yasaka ta ya kulle , idan yace zai iya rayuwa babu zeenat to lallai sai dai wani Aliyu haidar din amma bashi ba . Zuciyar sa har wata bugawa take a duk sanda kaunar ta ta motsa masa shi karan kansa bazaice ga irin azabtuwar da yake ji akan son zeenat ba . ” ya ubangiji Allah ka bani ikon rike zeenat da gaskiya,  ubangiji kasa mata soyayya ta a zuciyar ta , ta kaunace ni koda kwatan wanda nake mata ne .”” Abinda yake fada kenan a zuciyar sa amma idanuwansa akanta suke .

“” Ranki ya dade kinyi shiru kin barni inata jira ki gaya min abinda ke damunki “”. Ajiyar zuciya me karfi ta sauke ta ďan dago domin ta saci kallonsa sai tayi rashin sa’a domin idanunta acikin nasa suka fada. Da sauri ta mayar da kanta kasa sannan tace masa”” Babu abinda ke damuna wani abu ne ya fada min ido shine zanje Ammi ta cire min idan bata fita ba””….                     ISTIGFARI take a zuciyar ta domin basu saba karya ba , ko kadan karya ba ďabi’ar su bace amma sai gashi yau tayi ta.
Kamar yasan abinda take fada a zuciyar ta yace mata “” Amma dai kinsan karya ba ďabi’ar ku bace ko ? Bakiyi kyau ba da kika yi ma a yanzu dan nasan ISTIGFARI kike a zuciyar ki idan kuma ba haka bane ki musa min . Ina gane mutum me karya fa dan haka fada min gaskiya “…
“” Allah yarima babu wani abu karka damu kanka a kaina domin nidin ba kowa bace bamu da wani gata sai Allah , duk wata wahala sun saba mata dan haka wannan ba abin damuwa bane , kayi tafiyar ka inda zaka nagode .””
Wani iri yaji da tayi magana irin haka, da tasan yadda ya daukesu da bata fara irin wannan furucin ba amma yau zai nuna mata matsayin ta a wajensa.                                                                        “”” Hmmm kina bani mamaki idan kikayi irin wannan maganar, shin kin manta Allah shine ya halicce mu, kuma shine yayi talaka da mai kudi. Sannan ya zabi shugaban ni a cikin mu sannan yasa wasu akasan su , toh ina son kisani babu wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda yafi tsoron sa . Kowa da kike gani ba kowan kowa bane a wajen ubangiji,  babu ta yarda bai iya juya lamarinsa,  shine yake halittar matacce cikin rayayye sannan ya halicci rayayye cikin matacce. Allah ne mafi sanin daidai amma bakisan kedin me zaki zama ba nan gaba, dan haka komai zaki ki dinga tunawa da Allah shike yi””…..
Ajiyar zuciya ta sauke dan gaskiya ya fada komai daga Allah ne, amma ita tana mamakin ta yadda yake gwada mata soyayya kamar ba  ďan sarki ba .
“” Nagode yarima kuma insha Allahu zanyi amfani da dukkan abinda ka fada min Allah ya biyaka da jannatul firdausi.””
“”” Ameeen Habibtiy nah Amma addua da yakamata kimin shine Allah ya mallaka min ke a matsayin abokiyar rayuwa  , sannan kice kina sona kin aminta dani””   wani irin murmushi yarima Haidar yake da yake  nuna tsantsar farin cikin da tsayuwar tasu koba komai ya ganta kuma yana jin muryarta …
Kasa fadan abinda yace zeenat tayi domin ya bata kunya sosai ba kadan ba, kasa ta kara dukar da kanta don ita mamaki ma yake bata da har yake iya faɗa mata irin waďanan kalamai.
“” uhum uhum Habibtiy kiyi min magana mana inji ďadi, kinsan yadda nake kaunar ki kuwa? Ina maki son da zan iya baki numfashi na donke ki rayu , ina matukar kaunarki Habibtiy nah  . Ina maki so irin wanda uwa keyi ma ďanta , kinsan dai uwa komai ya ďan ta zai koma bata iya rabuwa dashi toh haka nake sonki. Bari ma in tambayeki kinsan yadda ake gane so na gaskiya?”…..
Murmushi kawai zeenat keyi da yar dariya kasa kasa ita mamaki yake bata bil hakki. Amsa masa tayi da “A’a ” tana jiran ya cigaba domin wani irin farinciki take ji har kasan zuciyar ta  bata son yayi domin kalamansa suna mata daďi ne sosai tare da amsa kuwwa ….

“”” Ana gane sona gaskiya ta yadda uwa ke gane ďan ta da ido ko babu. Sannan sona gaskiya baya boyuwa , kuma anayinsa ne tsakani da Allah badan wani abuba na jikin wannan wanda ake so . So na gaskiya baya tsufa “”…..
Murmushi tayi wanda harya bayyana fararen hakoranta . Rasa abinda zata masa tayi sai kuma can kamar an fisgo maganar daga bakinta tace masa “””” Meye banbancin so da kuma kauna ?”””” …
Sai da ta furta sannan taji wata irin kunya ta kamata amma kuma zuciyar ta ta kwaďaitu dason jin muryarsa da kuma jin amsar tambayar da tayi masa..

Shi kansa yarima Haidar sai da ta bashi dariya sosai akan tambayar tata, sannan yayi mamaki da harta tsaya sunata fira dashi haka . Abin ba karamin daďi yayi mashi ba sai kawai yace mata “” ke yakamata ki bamu wannan amsar malama kin mani wayau inata suba kamar parrot ( Aku) , dan haka ki samu mana amsar nan a yanzu in kuma baki sani ba ki nemo mana gobe nazo na amsa “”…

“”” Uhumm Uhumm nidai kai na tambaya fa zakace haka, nida ban taba soyayya ba ta ina zan sani, amma kai da ganinka kanayi tunda gashi ka iya sosai nidai ka fada min kawai”…..
Cikin shagwaba zeenat tayi maganar batare da tasan abinda tayi ba, don wani irin shauk’i takeji a tattare da ita na musamman.
Shi karan kansa sai da gabansa ya faďi yadda take shagwabar ba tare da tasan ma tanayi ba ita a tunanin ta magana kawai take lafiya lau amma shagwabar ba karamin kyau tayi mata ba . Yarima ji yake kamar ya maida ta ciki don so harga Allah yana jin kaunar ta marar iyaka.

“”” A’a Nike naba ma wannan aikin dan haka ki nemo mana amsa ina nan zuwa gobe na amsa in kuma zuciyata takasa hakuri zaki ganni da daddare nazo, yanzu bari na barki kiyi aikin da zakiyi, sannan ki nemo mana amsa ehe ni zuwa zanyi na kwanta ko in tsaya ne dan ban gajiya da kallon ki fa””…

Bataji dadin tafiyar da yace zaiyi ba amma haka nan ta daure tace masa “” To shikenan Allah ya tsare ka a huta lafiya “…

Murmushi yayi mata me kayatar wa  sannan yace mata “” Ameeen Habibtiy nah, ina kaunarki sosai ki kula min da kanki dan Allah kinji kiyi tunani nah na barki lafiya gimbiyar mata I LOVE YOU SO MUCH “….

Dariya tayi , ta ruga da gudu cikin gida tana jin kamar bata da wata sauran damuwa a duniya , farin cikin da take ciki ne yasa ta manta da abinda ya kawo ta gida dan haka kwanciya kawai tayi tanata tunanin nasa . A haka bacci yayi awon gaba da ita……….

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 39&40

Bismillahir Rahmanir Rahim.

_____________
Yau sauran kwana hudu, su yarima Haidar su koma kasar su , a yau me martaba sarki ABDUL GAFAR  ya kira yarima Haidar domin jin ina suka kwana akan maganar su. Domin har yanzu baiji komai daga bangaren su Ammi ba,  hakan yasa ya fara tunanin akwai matsala domin yakamata ace ko basu amince ba sunce wani abu game da maganar ….

Bangaren su Ammi kuwa! sun tattauna sosai akan maganar, sai dai Ammi tace sam lokacin bayyanar komai baiba don haka idan har sai me martaba yasan kosu suwaye sannan ďansu zai auri zeenat to ba kuwa zata amince ba . Dan haka ta tattara maganar ta watsar , ta cigaba da harkokin gabanta domin tasan abin bamai yiwuwa bane idan har sun nace dole sai komai ya fasu …

Koda me martaba ya aiko kiransu Ammi, bata samu zuwa ba, domin ita tace idan sai sun sani ko su suwaye to saidai su fasa dan bazata fada ba . Maitama ne kawai yaje ya samu me martaba sarki ABDUL GAFAR kai tsaye , bayan sun gaisa anan yake shaida  masa abinda Ammi ta fada dan haka basu da wani zabi illah bin umarni . Dan haka me martaba yace ma maitama “” idan har kun amince wannan  ba damuwar mu bane domin ina ji ajikina kudin daga babban gida kuka fito, dan haka ina me nema ma ďana  auren zeenat idan kun yarda “”” .

Maitama ya cika da mamaki sosai, don bai taba ganin mutum me dattako irin wannan sarki ba. Yana da karamci sosai , sannan yasan darajar dan Adam.  Haka kawai yaji zuciyar sa ta aminta da dashi dan haka bai tunanin komai ba yace masa,  “”‘ Na Amince kuma na baka auren zeenat Allah yasa haka shine mafi alkhairi a garemu baki daya “”…..

Yarima Haidar da shigowar sa kenan, yaji wannan furucin daga maitama baisan lokacin daya isa garesa ba ya rungume sa yana jin farinciki marar misultuwa a zuciyar sa. Yau ta zamar masa rana wadda bazai taba mantawa da ita ba har abada ……

“””” Nagode Nagode sosai da karamcin ku garemu , munji dadi matuka kuma insha Allahu zaku same mu da rike amana ďari bisa ďari. Abba ka tayani gode masu bansan da wace kalma zan nuna godiyata a garesu ba , UMMI na kawai zan raba wannan farin cikin da ita domin tafini son zeenat din ma tun kafin ta ganta “”….

Sujjada yayi yana gode ma ubangiji,  yadda kasan an bashi Aljannah haka yake ta jin dadi !.
*Me martaba ma kansa farinciki yake ganin ďansa a cikin wannan farinciki hakan ba karamin ďadi yayi masa ba , dan yasan ba karamin so yarima yake ma zeenat ba , hakan yasa shima sai hamdala yake yana ma ubangiji kirari da tasbihi a zuciyar sa . Koda gama wannan murna tasu sai dai ganin babu maitama sukayi domin tafiya yayi abinsa …

Koda maitama ya koma bangaren su Ammi, zaune ya tarar dasu ita da zeenat suna fira , zama yayi ya fada ma Ammi duk yadda abin ya faru . Ita kanta taji ďadi domin tasan zeenat zata samu kwanciyar hankali sosai a wajensu hakan yasa ko kadan bata da damuwa akan auren . Zeenat ce ta share hawaye ta kalli Ammi sannan tace “”” Ammi yanzu aurar dani zakuyi batare da nasan komu suwaye ba? Taya kuke tunanin zan samu kwanciyar hankali da natsuwa bayan bansan koni wacece ba? bansan ina mahaifina yake? Dan Allah kada bayar dani batare da nasan komai game da kaina ba kodan kare kaina daga gori “”……

Gaba ďayansu shiru sukayi, domin duk Abinda ta fada gaskiya ne . Maitama ne yace “” gaskiya kika fada sister dole ne kisan ko wacece ke kafin a aurar dake dan duk abinda kika fada to babu karya a ciki dan haka Ammi dan girman Allah ki daure ki gaya mata , karki bari ta tafi batare da tasan asalin ta ba “”…..

“”” In sha Allah zan fada maku komai Amma kafin lokacin auren akwai abinda nake son sani dan haka idan nasamo zaku san ko kuďin suwaye da yardar ubangiji nayi maku wannan Alkawarin “”.
Farinciki ne sosai akan fuskokin su zeenat don ba karamin daďi maganar tayi masu ba musamman zeenat da farin cikin ya kara kamata tunawa da yarima Haidar yace zasu hadu ta bashi amsa yau ko gobe dan haka take jin farinciki sosai a ranta .

********
Yarima uwais ne kwance kusa da mahaifiyarsa,  tana shafa kansa idanuwansa a rufe amma ba barci yake ba , tunanin zeenat ne kwance a ransa maganar ta na masa amsa kuwwa . Gimbiya maryama ta gaji da tambayar sa abinda yake damunsa , dan haka tace masa “”” Ni kuwa yarima ina kake ganin zamu samu wannan baiwa da dodon tsafi ke magana akanta ? Lokaci na kurewa fa , yakamata ace munyi wani akai bai kamata mu zuba ido ba “..

Ransa ne yaji ya baci, taya zai auri baiwa yana matsayin yarima me jiran gado , ina Sam hakan ba me yiwuwa bane,  idan wasu ma sukaji ai dariya zasu masa ace kamar sa ya rasa wadda zai aura sai baiwa, kai bazai taba faruwa bama.
“” Da kinbar wannan maganar momy dan Abinda bazai taba yiwuwa bane wallahi ace kamata na auri baiwa kema kinsan hakan ba daidai bane , ki canza tunani ko ince ku canza tunani keda dodon  naki , ni nasan dole nine zan hau kujerar mulki. Koda tsafin ku ko babu dan haka ku canza shawara hakan zaifi “….

*Ran gimbiya maryama ba karamin baci yayi ba , wani tunani tayi a zuciyar ta . Tayaya ma za’ai ace ta zuba ido wasu su gaji mulkin nan ba ďanta ba, gashi kuma ďan nata ke neman ya bata komai don idan har ba umarnin dodon tsafi suka bi ba, to komai zai iya lalacewa dan haka dole ta Mike akan uwais..
“” Haba ďana yarima, kasani bani da kowa sai kai yanzu idanu kake son na zuba , akan mulkin nan ? Bayan kasan su ba zaune suke ba akan ganin ubaid ya ture ka yahau mulki . Kayi hakuri kabi umarnin dodon tsafi, na tabbata gaba zaka ga ribar hakan, don yana mana kokari sosai akan hidimar nan , kaji mu daure mu nemi baiwar daka aureta bayan ka hau mulkin ai sakinta zakayi , tunda ai ita hanyace ta hawa mulkin dole saida ita . “””

( Gaba ďaya sun manta cewa  Allah shike badawa a sanda yaso ga kuma wanda yaso. Allah ya kara tsare mana imanin mu.)

“” Toh shikenan zanyi tunani akai momy Amma yanzu ta ina ma zamu fara neman wannan baiwa , dan ni kinsan ban shiga hidimar bayi “”..
Wani irin daďi gimbiya maryama taji, domin ta fara samo kan yarima dan haka tace mai “” karka damu kabar komai a hannuna zansa a bincika min sannan nima zan zuba idanu sosai akan duk wani motsi na bayin Masarautar nan “…
Mikewa yarima yayi ya tafi bangaren sa, domin ya kwanta yaďan huta , sai dai yana kwanciya kamar ya kwanta da tunanin ta . Ya rasa ma meke masa daďi a rayuwar sa, komai bai masa daďi , da kyar bacci yayi awon gaba dashi…

_______
Yarima ubaid kuwa, sharholiyarsa kawai yake batare da sanin kowa ba , duk wani club da party zaka same su acan . A yanzu ma ba sosai yake zaman masarauta ba , yafi maida hankali akan yawon da suke , Gidansa daya saya inda suke sheke ayar su , anan yafi zama yanzu.
Ita kanta mahaifiyarsa bata san abinda yake aikatawa ba, duk a tunanin ta yana cikin Masarautar domin yana shiga duk safiya gaishe ta sannan ya shiga fada gaishe da Sarki Abul uwais.  Tsafinta ya dauke hankalinta sosai akan lamarin ďanta , don sosai take so taga ďanta shine akan mulki bataki uban kowa ya mutu ba idan har yarima ubaid zai hau kujerar mulki…

A yanzu haka, wani aiki bokanyar tsafinta ta bata, na samo mata kananan yara guda biyu wanda da jinin su zatayi amfani wajen tsafin . Haka ta fiya wasu gardawa suka je suka kawo mata su cikin dare , babu wanda yagansu haka ta kaiwa bokanyar yaran aka shanye jinin su …..

( wa’iyazubillah ubangiji Allah ka tsare mana zuri’ar mu ka kare mana su daga sharrin mutum dana aljan.)

***************
Gimbiya kalba ce zaune, tana aikin tunanin nata data saba akan  wanda baima san tanayi ba. Ta fada cikin kaunar maitama sosai ta yadda bazata iya fita ba sai dai hukuncin ubangiji….

Aikawa tayi a kira mata zeenat,  babu dadewa sai gasu sun dawo hada zeenat din.
“”” Ranki ya dade barka da hutawa , nasamu sakon kiranki a gafarce ni idan nayi wani laifi. “

Haka kawai, gimbiya kalba ta tsinci kanta da jin son zeenat har k’asan ranta! Domin a lokacin ji tayi duk wani abu da yake so tana sonsa abu daya ne bazata taba so ba wato wannan matar tashi dayace yanada ita. Amma tana jin son yan uwansa, a ranta dan haka tace ma zeenat.
” Ina ďan uwanki yake yanzu”.

“” Ranki ya dade bai dade da tafiya unguwa ba, amma gobe zai dawo, Allah yasa ba wani laifi ya aikata ba “””…..

Gaban gimbiya kalba babu abinda yake sai luguden duka , bata taba tsintar kanta a tashin hankali ba irin na yanzu, gani take gashi can tare da matarsa . Gabanta sai faďuwa yake kamar zai faďo! , Allah yasani idan ta rasa wannan mutum mutuwa zatayi ita kam….

Ganin halin da gimbiya ta shiga, yasa da sauri zeenat ta Mike ta dauko mata ruwa masu sanyi ta kawo mata a gabanta .

Ita kanta zeenat gabanta faďuwa yake domin ita a tunanin ta wani laifi maitama yayi ma gimbiya da har yasata a wannan halin shiyasa taji hankalinta ya tashi. Kasa hakuri tayi tace ma gimbiya kalba.
“” Ranki ya dade  Allah yasa ba laifi yayi maki ba””…

“” Karki damu babu abinda yayi min,  kawai dai kama yayi min da mijin da zan aura shiyasa na tambaye ki”””…

Sa a lokacin Zeenat hankalinta ya kwanta , taji natsuwa tazo mata sosai .
“”” Allah sarki shima wajen matar shi yaje domin ganin lafiyar ta gobe zai dawo yace mana! kawai yayi kewarta ne shine yaje””….

Kasa magana gimbiya tayi, domin wani irin azaba takeji a zuciyar ta . Wanda take so baisan da zamanta ba hasalima yanada mata ita kanta tausayin kanta takeyi!!!!

Cikin bacin rai gimbiya tace ma , zeenat
“”” ya isa haka!! Tashi kije kawai “””..
Da sauri zeenat ta fita , ta barta nan zaune ..

Koda ganin zeenat ta fita , kuka ta fashe dashi.
“Zuciyata baki min adalci ba wallahi, dole sai ya rabu da ita nidin dai zai aurahhhhhh”

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 41&42

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Kwance suke a falo saman doguwar kujera suna kallo, nanike yake da ita kamar zai maidata  cikin shagwaba daya saba zuba mata yace mata “” Habibti ina jin yunwa fa kibani wani abu naďan ci””..
“” Angama ranka ya daďe bani yan mintuna ina zuwa””.
Kitchen ta shiga ta tsaya tana tunanin me zata dafa ma habibin nata me sauki wanda zata gama babu bata lokaci. Indomitable  ta daura wadda taji kifi da vegetables nan da nan gidan yaďau kamshi , ta hada banana juice da fruit salad. Tana cikin aikin ne tajiyo maganar sa.
“”Habibti nah Dan Allah ki fito kitchen din nan haka, idan kuma kinki yanzu nazo na fiddo dake, ni wallahi dama kin barshi bana son kina wahalar min da kanki kibari kawai muyi order abincin basai kinyi komai ba ki huta indan nine na hakura na yafe kizo kawai inji ďuminki yafi min ni wallahi””.
” kayi hakuri Habibi na kusa gamawa fa sauran kaďan na ida fa sai in zo gareka Abin kaunatah”.
“” uhum uhum nidai dan Allah ki fito in ganki Habibti kina azaftar da idanuwa na fa ya kike so inyi da raina na yafe dan Allah ki barshi haka kinji “”.
” gani nan sarkin hakuri nagama ai anan zan kawo maka ko a dining table zaka ci?”.
” Nidai ki kawo nan muci kawai basai munje ko ina inba dai ďaki zamu ba ko””.
“” lallai ma naki wayon aci anan kawai basai anje ko ina ba”.
Dariya ya sanya mata dama yasan ba yarda zatayi ba kawai tsokanan fada ne . Anan suka zauna suna cin abincin cikin shauk’i da soyayya kamar zasu maida juna ciki . Ganin dare ya fara ne suka tattara kayan su suka nufi ďaki don shirin kwanciya.

Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un abinda ya faďa kenan lokacin da aka kara bubbuga kofar baiso yanke masa bacci da akayi ba yana cikin mafarki me daďin gaske . Cikin bacin rai yarima Haidar yace ” wai waye yake ma mutane bugun kofa haka ?”
” kayi hakuri brother nice Hafsat Abba ne yace nazo na kiraka”. Hafsat ce kanwar yarima Haidar.
Dole ya Mike ya shiga bayi yayi wanka tare alwala sannan ya shirya ya fita zuwa wajen Abban nashi..

***
SARKI ABUL UWAIS ne zaune a falonsa tare da Aminin shi sarki ABDUL GAFAR  suna magana , kai da ganin irin maganar kasan me mahimmanci ce sai dai baka jinsu suna maganar ne kamar ta sirri.

Sallama yarima Haidar yayi ya shigo tare da dukawa yana gaishe da iyayen nasa .
Ganin kowa da kowa na wajen yasan abu me muhimmanci ne yasa aka taru anan din.
Cikin farinciki suka amsa gaisuwar tasa . Natsuwa yayi sosai domin yana ganin su yasan da magana me mahimmanci a wajensu .

  Me martaba ne yayi gyaran murya tare da fara magana cikin natsuwa.
“””” Alhamdulillah muna godiya ga Allah daya tara mu anan Allah ya sada mu da  Alkhairin dake cikin wannan zama””..
Da Ameeen suka amsa gaba daya . Sai da ya numfasa sannan ya cigaba da magana.
“” Dalilin wannan zama shine ina son zanyi mana tuni akan zumunci . Zumunci wata hanya ce ta Alkhairi da zata kai mutum Aljannah,  Idan har muka rike zumunci kuma mukayi shi don Allah to zamu samu rabauta wajen ubangiji. Shi zumunci yana kara kusanci , zumunci yana kara soyayyar . Shi zumunci basai yan uwa na jini ba musulunci ya koya mana son juna. Me zumunci Allah yayi masa tanadi Ladan sa wajen Allah adadi .in ka yanke zumunci ba wani sanadi to kamar ka yanke wata kauna ce dake tsakanin mutane . Fatana mu kara karfafa zumuncin mu””……

Shiru yayi domin numfasawa , Abul uwais ne yayi gyaran murya ya dora da cewa “”” gaskiya ka fada Abokina ubangiji Allah ya bamu ikon karfafa zumunci da kuma yinsa. Gaskiya naji dadin maganar ka sosai Allah ya barmu tare “”..

“Ameen ya Allah” suka amsa dukan su sannan Maimartaba ya cigaba da cewa.
“” Abul uwais ina fatan baka manta da tafiyar mu nan da kwana ukku ba ? To in sha Allah zamu tafi kamar yadda muka zo sai dai ina neman mana Alfarmar kabani bayinka mutum hudu ko biyar na tafi dasu kasata domin na dinga ganin bayin Masarautar ulwa, da fatan ban maka ba daidai ba?”.. ya karashe maganar cikin zolaya don yasan wane abokin  nasa sai ya biyo masa ta bayan gida idan ba haka ba tsarin su bazai tafi yadda suke so ba.

“” Haba Abokina ai kunfi karfin komai a wajen idan ma fiye da haka kuke bukata kawai zaku diba ne basai ka gaya min ba . Karka damu yanzu zansa a tattara dukka bayin gidan nan saika zaba wanda kake so kaji”..

Godiya sukayi masa, sannan aka kara fira sosai daga anan aka rufe taro da addua  kowa ya kama gabansa .

Abul uwais ne ya bada sanarwar yana bukatar ganin duk wani bawa da yake Masarautar ko bai lafiya yazo haka nan. Babu bata lokaci suka fara haduwa gaban fada .

***
Ammi da iyalanta ne zaune suna fira gwanin ban sha’awa. Kallo daya zakayi masu kasan yau suna cikin farinciki.

Maitama ne zaune gefensa kuma auta ne, sai Arwa da zeenat kwance kowace kanta na kan cinyar Ammi gwanin burgewa.  Ammi ce ta kalle su cikin farinciki bakinta yaki rufuwa tace..

    “”” Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!. Allah nagode maka dakayi mana wannan ni’imar! Hakika babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad (S A W) manzon sa ne. Allah muna tawassali dakai Allah ka Albarkaci rayuwar yaran nan . A gaskiya naji daďi kuma nayi farinciki da wannan auren naku duk da bamuyi shi cikin shiri ba Amma ina mai tabbar maku da za’ayi bikin da babu kamar sa indai muna da rai akwai lokaci yana zuwa “… ta karashe maganar hawaye na wanke mata fuska .

“” Maitama ga Amanar AISHATU nan kamar yadda mahaifinta ya damka amanarta gareka dan Allah karka bashi kunya duk da nasan zaka rike banjin ka amma ina mai kara maka tuni akan girman amana . Yanzu AISHATU bata da wanda yake iko da ita sama dakai haka babu wani gata da take dashi bayan kai sai kuma mu. Ka rike AISHATU tsakani da Allah kaji karka bari tayi kuka dan Allah kayi min alkawarin kula da AISHATU fiye da yadda zaka kula da kanka idan kayi min haka to ka gama faranta min …

“”” Haba Ammi na kamar kin manta kaunar da nake ma Arwah ne! In sha Allah nayi maki alkawarin duk dadi ko wuya bazan taba bari hawaye ko damuwa ko bacin rai a tare da Arwah ba . Nayi maki alkawarin zan kula da rayuwar ta fiye da yadda zan kula da rayuwata Ammi! Farinciki zai maye gurbin dukkan wata damuwa tata . Zan zame mata jigo kuma  uwa uba da dangi na maki wannan Alkawarin indai ina numfashi bazan taba bari tayi kuka ba””…

“” Alhamdulillah naji daďi kuma nagode ďana Allah ya albarkaci rayuwar aurenku ya baku zuri’a tagari “”…

“Ameeen  Ya Allah Ammi baki ji daďin danake jiba wallahi gobe sai muje muyi godiya Aunty Arwah ta zama tamu “..
Zeenat ke magana cikin tsantsar farin ciki. Bakin su yaki rufuwa Auta ne yace mata ” kai Adda zeenat nafiki jin daďi fa kinga yanzu mun kara yawa Hamma yayi aure ke kuma zaki tafi kibar mu , kibar murna ma Nike da murna inkin tafi kinga ina da Aunty Arwah “..

Lokaci guda zeenat ta bata rai , su kuma suka shiga yi mata dariya sosai dan ba karamin son yan uwanta take ba ko yaushe tunanin ta yaya zatayi idan tayi aure tabar yan uwanta.

Arwah ce ta share hawayen farinciki domin irin kaunarta da suke nuna yasata jin hawaye, ina ma mahaifiyar ta na raye! yau taga aurenta sannan taga yadda mijinta da mahaifiyar mijinta da yan uwan sa  masu matukar kaunarta. Sai dai babu ita! Allah ya jikanki mahaifiyata Abinda ya fito bakinta kenan cikin kuka.

Shiru sukayi suna kallonta don sunsan abinda yasata kuka . Ammi ce ta jawota jikinta tana lallashi tare dayi mata nasiha a haka harta daina kuka sannan ta ďago tana kallonsu sannan ta fara magana cikin sanyinta.
“” Ina ma Allah godiya bisa ga ni’imar da yayi mani na zamowa daya daga cikin ahalinki Ammi ina jin daďin samun dangi nagari abin Alfahari ga wanda ya dace da samun ku , in sha Allah zan kasance mace wadda zakuyi Alfahari da samun ta . Zan kasance Mai biyayya a gareku! Da yardar ubangiji baza kuyi dana sanin shigowa rayuwar kuba”.. kuka take a hankali don tarasa da wace kalma zatayi amfani wajen nuna jindaďin yadda suka karbeta . Tasan suďin masu karamci ne.

Yarima Haidar ne yayi sallama daga waje . Maitama ne ya Mike don ganin waye duk da ya gane muryar yana zuwa suka gaisa magan ganu sukayi sannan ya shigo gida .

Sakon sarki ya iso garesu dan haka suka shirya suka fita gaba dayansu zuwa can.

Kowa ya hallara a wajen duk wani bawa dake karkashin Masarautar yana wajen dan haka fitowar sarki kawai ya rage.  Babu dadewa sarki suka fito tare da yarima ubaid da yarima Haidar  da yarima uwais. Sai Maimartaba Sarki Abdulgafar .

Anan Abul uwais yayi ďan jawabinsa sannan ya faďa abinda zai faďa .
Abinda yasa aka taru ya faďa dan haka babu wanda yayi ko tari a cikin bayin.

Abul uwais ne yace ma yarima Haidar daya zabar masu wanda suke son tafiya dasu dan yasan abokinsa bazai zaba ba danshi yace  aba yarima Haidar din zabi .

Cikin girmamawa ya amsa sannan ya fara zaga yawa yana dubawa. Yana zuwa kan auta ya nuna sa, sai kuma daya kara gaba ya nuna maitama, daga nan sai ya koma bangaren mata da Arwah ya fara cin karo duk da baisan ta ba haka kawai yaji a jikinsa tana da alaka dasu zeenat dan haka ya nuna ta mikewa tayi ta koma gefe , sai kuma ya nuna Ammi. Daga nan kuma ya koma bangaren da zeenat take rakube gefe daya . Yana zuwa ya nunata dan haka ta Mike ta koma gefe gabanta na faďuwa.

Yana gamawa aka sallame su . Kowa ya kama gabansa , ba karamin daďi sukaji ba daya nuna Arwah duk da baisan taba ….

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 43&44

Bismillahir Rahmanir Rahim.

__________
Bayan watsewar bayin, sarki Abul Uwais ne yayi gyaran murya ya kalli Amininsa yace “” muje kaga wanda yarima ya zabar maka idan sunyi maka shikenan sai ka tafi dasu. Idan basuyi maka ba kuma sai a kara tara su ka zaba da kanka””.
Gaba ɗaya suka juya zuwa wajen da bayin suke a gefe sai dai suna zuwa  yarima uwais yace “” kai inaaa wallahi sai dai ka canza wasu amma bazaka tafi da wannan yarinyar ba! Ban gama mata hukunci ba dan haka a cireta a lissafi “”..
Wata irin tsawa Abul Uwais yayi ma Yarima uwais badan ya gama maganar ba dole yayi shiru cikin ɓacin rai yace mashi”” Koda dukka bayin Masarautar Ulwa suke so to zan iya basu su. Kasan yadda nake kaunar Aminina kuwa ? Kasan yadda yake da muhimmanci a wajena ? Karka sake na kara jin bakin ka idan ba haka ba Billahil Azim dakai zai tafi Nigeria “”…

Gaban yarima Uwais ne ya yanke ya faɗi bai taba zaton hakan daga bakin mahaifinsa ba, sai dai gashi ya bashi mamaki a cikin mutane.

Ba yarima uwais  kaɗai maganar Sarki Abul uwais ta daka ba harda gimbiya maryama, sai da ta firgita da maganar don ba karamin tsorata tayi  da furucin nasa ba . Bataji daɗin yadda yaba ma ɗanta kunya ba a gaban mutane nan take taji mugun tsanar yarinyar domin gani take a dalilinta Abul uwais yayi ma yarima uwais tsawa.

   Dariya Gimbiya mufida tayi tare da cewa “” Allah na tuba mutum shiba kowan kowa ba amma yace zai nuna isa a inda bai isa ba, taya zai tunanin za’a ga isar tasa bayan bai isan ba hhhhhh a dai bi a sannu idan ba’a ji bari ba anji hoho “””…dariya take tsakanin ta da Allah domin abinda Abul Uwais yayi ya faranta mata Rai sosai da sosai..

  Tsaki gimbiya maryama tayi domin abinda take gudun ya afku sai dai zata nuna mata ruwa ba sa’an kwando bane. Sai dai dole ta taka ma yarima uwais birki domin tasan yadda zuciyar sa taɗau zafi bazai iya shiru ba , ita kuma ta tabbatar idan ya kara maganar to tabbas Abul uwais bazai kaffara ba sai yayi abinda yayi niyya , ita kuwa bata shirya rabuwa da ɗanta ba yanzu yana shirin hayewa mulki..

Maimartaba Sarki Abdulgafar ne yayi murmushi sannan ya juya gasu Ammi da kansu ke kasa suna jiran ikon Allah. Kallonsu yayi sannan yace “” Sunyi Abokina ubangiji Allah yasa su zama Alkhairi a garemu baki ďaya”..
“Ameen ya Allah” sarki Abul uwais ya amsa yana jin farinciki ganin yau yayi ma Amininsa Abinda ya bukata daga wajensa .

Gimbiya kalba ne suka iso tare da ƙannan yarima Haidar Hafsat da Khadija. suna isowa idanuwan gimbiya kalba suka sauka akan Maitama dake duƙe a gefe shida Auta.Gaban ta ne taji ya faɗi sosai batasan lokacin data furta..
“” Waɗannan sune aka zaba innalillahi wa’inna ilaihi raju’un Na shiga ukku ni kalba””.

Gaba ďaya juyawa sukayi suna kallonta kowa da abinda yake sakawa game da furucin nata sai dai kowa ya gaza cewa komai akan maganar tata. Sai idanuwa da suka bita dashi. Ita kuwa hankalin ta gaba daya yana kan maitama ta zuba mai ido tana kallo zuciyar ta kamar zata faso kirjinta ta fito.
Yarima Ubaid ne yayi karfin halin yin magana “” sister bamu gane me kike nufi ba, kina da wata alaƙa ne dashi ? Ko akwai wani abu dake tsakanin ku bamu sani ba da har zaki tada hankalin ki don an zabe su ? “”..

Sai lokacin gimbiya kalba ta farga da ɓaran ɓaramar da tayi a gaban kowa da sauri tace masa “” Lahh wallahi bakomai brother kawai dai  zan missing wannan yarinyar  ne me kula da Abinci na amma bakomai ai Akwai wata wannan mun barma su Abba su tafi dasu “”….

“”Toh shikenan sister naďauka ai ko wani abu ne daban, Amma dai koma menene tunda kin gama magana shikenan ai””.. gimbiya maryama ce ta kalli yarima Ubaid ranta a bace tace mashi.
“”Kai Dallah kayi ma mutane shiru ka ishi mutane da wata sister  me akai ya akai ina ruwanka da lamarinta ? Bansan shishshigi fa,  meye haďin tuwo da latas babu ruwanka da lamarin yarana na gaya maka da fatan kaji””….

“” Duk tsiyar mutum dai bai isa ya canza ma tuwo suna ba! sai nake ganin bashi ya kashe zoman ba rataya aka basa”.. Gimbiya mufida ta faďa ranta fess don tasan duk abinda gimbiya maryama zatayi sai dai tayi borin kunya ..

Kamar daga sama sukaji maganar gimbiya sakina “” Da kai da kaya sai nake ganin kamar duk mallakar wuya ne. Idan kun kwantar da hankalin ku wannan mulki da kuke ta hauka akansa!  ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Daku haďa kan yaran mu da karku haďa dole  dai abu ďaya yayi su don haka ba’a san rabon kan wa yake ba””..

“” Dallah rufe mana baki! Aike mata kika rako, kina mace ki haifi duka mata ai ba sa’ar mu bace, da kinja gefe da yafi maki yakin ba naki bane. ki bari sai kin iya haihuwa sannan! dan yanzu ba cikakkar mace bace”… Gimbiya maryama ta faďa ma gimbiya sakina magana a kausashe .don ba karamin kara bata mata rai tayi ba .

Yarima Haidar ne ya gaji da maganar tasu duk da sarakan ba jinsu suke ba amma su suna ji saboda suna kusa dasu dan haka yace masu .”” Dan girman Allah kuyi hakuri da wadannan magan ganun abarsu haka please “…
Kowace shiru tayi a cikin su amma duk da haka kowace da Alwashin data ďaukar ma ranta .

     Gimbiya kalba ce ta kasa jurewa ta matsa can kusa dasu maitama ta tsaya tana kare masu kallo, sai a lokacin ta lura da Arwah a wajen . Rass gabanta ya faďi magana ta fara cikin gushewar tunani .
“” Dama wannan itace matar taka da kake magana akanta ? Gaskiya kam tana da kyau sosai kamar kai amma sam bata dace dakai ba wallahi, ni….” kasa karasawa tayi wani abu ne ya tokare mata maƙoshi hakan yasa maganar ta gagara fita sai dai ta juya da sauri ta nufi sashen ta.

Babu wanda ya lura da ita sai yarima Haidar da yarima Ubaid.  Ganin yanayinta ya tabbatar masu da akwai wani abu a ranta da take boye wa .

Magana sarki Abul Uwais yayi akan an gama kowa ya tafi,  suma bayin ace masu zasu iya tafiya su fara shiri. Yana juyawa har sun fara tafiya shida Amininsa ya jiyo yarima Uwais yana magana.
“” wallahi bazan taba bari su tafi da ita ba ! Wannan abin akwai wani shiri da akeyi na tabbata . Idan ba shiri bane taya za’a ce duka yan gida daya zasu zaba sannan dan nayi magana akan a cire daya ace ba hakaba! Nifa na tsane su haka kawai ko ganinsu nayi sai naji gabana ya faďi akan me ? Dole hukunci ya hau kansu koda me zan fuskanta dan ban yarda da wannan tsarin ba”…

“” Aikuwa babu wanda ya isa ya canza abinda na zartar wallahi,  Idan kaga wani cikin su bai tafi Nigeria ba to bana numfashi.  Baka isa naja kaja ba! zan iya yafe ka gaba daya, idan har kace zaka ja dani. nafi ka tsageranci. Ko ka manta waye ni? kuma waye mahaifina!!  Ka shiga hankalinka””……
Sarki Abul uwais ke magana cikin bacin rai don yaga ďan nasa na neman bashi kunya a idanun mutane . Harya juya sai kuma yaji yana son yaga mutanen da ake nema ayi tashin hankali akan su.

Yana juyawa idanunsa ya sauka akan Maitama ! Gabanshi ya yanke ya faďi “”innalillahi wa’inna ilaihi raju’un ” shine abinda ya fito daga bakinsa kawai . Idanuwa ya zuba masu yana kare masu kallo baisan meyasa gabansa ke faďuwar ba amma ji yayi gaba ďaya kafafunsa sunyi mai nauyi.
Hannun Amininsa ya kama suka wuce ɓangaren shi . Koda ganin sa kasan ransa a ɓace yake sosai…

*

Gimbiya kalba kuwa kuka take kamar ranta zai fita,  nan da nan wani zazzabi me zafi ya kamata . Ganin halin da take yasa bayinta zuwa su sanar da gimbiya maryama.  Koda suka gaya mata gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake ta nufo ɓangaren gimbiya kalba din .
Ganin halinda take ciki bana zama bane dole aka kira doctor domin yazo ya duba ta anan. Yana zuwa yayi iya yinsa amma ya gagara gane kanta sai yace a kaita nan asibiti cikin Masarautar.
Suna zuwa emergency aka amshe ta aka shiga da ita …..

Bangaren su zeenat kuwa koda suka ga an sallame su gida suka koma. Kowa da abinda yake me yawo a zuciyar sa , musamman Ammi don wani tunani take a ranta . Tarasa meke tsakanin matan sarki da suke wannan yar tsamar . “Kodan yaransu maza ne shiyasa suke haka kowace nason ďanta ya hau mulki?”Ta tambayi kanta
“”Allah dai ya kyauta yayi mana zabi mafi alkhairi a garemu baki daya “”..
Ta fura tare da mikewa don yin Alwala.

Arwah kuwa haka nan taji hankalinta bai kwanta ba da gimbiya kalba.  Sai dai ganin babu wani abu a tare dashi maitama sai itama ta basar amma duk da haka abin nacin ranta na yadda tazo tanayi masu magana, hakan ya nuna akwai abinda take nufi dashi shiyasa harta furta hakan .

Shi kansa maitama abin ya ďaure mai kai sosai ba kaďan ba saboda yasan baida wata alaka da ita kuma babu wani abu dake tsakanin su idan ba wannan kiran data taba yi masa ba sune kawai zaice wata magana ta taba haďa su. Tambaya ta shiga yima kansa a cikin zuciyarsa. ” meyasa tayi wannan maganar a gaban mu ? Hakan ya nuna cewar kamar tana sona kenan ko kuma ta damu dani ne? Kai ina sai dai kodan zeenat tayi maka haka, amma idan har ba sona take ba akan me zata nuna kishi da nuna rashin jin daďin zabar mu? Kai gaskiya akwai dai wani abu”…
( ni kuwa nace malam maitama gimbiya yakamata kayi ma wannan tambayar ba kanka ba don baka da amsar su😜😜🤣🤣🤣)…

Zeenat kam kwance take amma tunanin yarima Haidar take haka kawai take jin kewar sa tana son ta gansa domin suyi maganar da basu karasa ba ran nan….

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 45&46

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Zaune yake cikin lambu, iska na kaďawa tare da kukan tsuntsaye masu daďin saurara lambun kawace yake a koren ciyawu , da furanni masu kyan gaske . Idanuwansa a lumshe suke, babu abinda yake tunani sai Habibtiyn  shi , tunaninta ya hana mai sukuni wata irin zazzafar kaunarta yakeji . Kamar ya bude idanunsa ya ganta a gabanshi . Kasa haƙuri yayi dan haka ya kira bayin da suke tare ya aika domin a kira mashi ita.

A kwance take suna fira ita da Arwah, sai dai gaba ɗaya tunaninta yana wajen yarima so take kawai ta ganshi taji muryarsa.  Sallama suka ji daga waje dan haka dole ta Mike don ganin waye tunda muryar namiji taji , ganin bawan da yake tare da yarima Haidar ne yasa gabanta faďuwa .
Gaisawa sukayi ya gaya mata sakon kira da aka aiko shi ,  amsa ta bashi sannan ta dawo ciki tana murna har abin yaba Arwah mamaki domin fira take mata amma ba magana daga Eh sai Aa . Mayafin ta ďauka tace ma Arwah,
“” To Aunty nah ki kula min da kanki bari naje ba daďewa zanyi ba na dawo”..
Bata jira jin abinda Arwah zata faďa ba tayi waje da saurin ta.

Tunda ďan aikensa ya dawo, ya zuba ma hanyar shigowa lambun ido. Idanuwansa har zafi suke masa na azabtuwar rashin ganinta, yana hango ta yaji hankalin shi ya fara kwanciya. Idanuwa ya zuba mata kamar zai haďiyeta harta karaso gabansa.
“” Assalamu Alaikum! barka da hutawa Ranka ya daďe fatan na same ka lafiya”..
Lumshe idanuwansa yayi yanajin wata irin natsuwa na saukar masa . Jin muryarta ba karamin taɓa mai zuciya yayi ba.
“” Amincin Allah ya tabbata a gareki Habibtiy nah!  ina lafiya ina fatan kema kina cikin koshin lafiya? “.
Wani irin bugawa ƙirjin zeenat yayi. Jin muryar sa ba karamin tasiri tayi ma zuciyar taba.
“” Lafiya lau Alhamdulillah “.
Ta bashi amsa a taƙaice

Murmushi yayi cikin jin daďi. Yace mata
“”” Masha Allah haka nake son ji Amarya tah. Kiyi hakuri fa yau yariman naki amayar da abinda yake zuciyar sa zaiyi dan haka ina fatan bazan takuraki da surutu ba dan naga kema akwai sarauta.””
Dariya sukayi gaba dayan su, saboda yadda ya karashe maganar cikin zolaya dole mutum ya dara .

“”Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya d’ayace babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki”””.
Ajiyar zuciya suka sauke a tare.  Sannan dauki ruwa ya sha kafin ya cigaba da cewa .
“””Zan kasance cikin baki furen soyayya a dukkan lokacin da muka had’u, matu’kar na samu tukuicin murmushinki a kan haka, to fa tilas na gina mana gida cikin da’irar lambu mai cike da tarin furanni masu kyawun launi da dad’in ‘kamshi””.

Murmushi tayi tare da jin wata irin natsuwa ta musamman dashi domin yana da wata irin baiwa ta iya sarrafa kalamai. Dagowa tayi ta saci kallon sa sai akayi rashin sa’a idanunta suka faďa a cikin nashi . Kallon juna suke sosai sun manta a ina suke da kuma abinda suke , kowa da abinda yake ji a cikin zuciyarsa.

Magana ya cigaba dayi idanunsa na cikin nata.
“” Kin zamo ta musamman daga cikin mutane na musamman da na ta6a had’uwa da su a rayuwata, kin shiga zuciyata kin zauna ta yadda ba zan iya mantawa da ke ba har abada. Ina fata da burin kasancewarmu tare a daula mafi tsari da kyawun burgewa wato Aljanna. Cikin nishad’i da yalwatuwar murmushin fuska nake mai furta miki cewa. INA KAUNARKI HABIBTIY NAH””..

Numfasawa yayi sannan ya cigaba da cewa”” Shin wani ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne? Sannan kuma a duk lokacin da kike yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai haske? Ke kyakkyawa ce, hakan ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata wadda ta zamo abar nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni d’aya cikin kad’aici a dare ko safiya. Ke ce abar so na””.

Ruwa ya kara dauka yasha sannan ya cigaba da cewa..
“”A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyata ma ta gaskata hakan, Lokaci na shudewa soyayyarki na karuwa a cikin zuciyata.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.””

Murmushi yayi sannan ya kalleta shi kansa da ya kalleta yasan tana cikin farinciki sosai dan haka ya cigaba da cewa..
“”” Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka?
Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE Habibtiynah.
A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe”””……..

Kallon shi tayi domin taga baisan ma lokaci yana ja ba, dan haka tace masa
” Ranka ya daďe lokaci sallah ya kusa yakamata mubar nan haka . Na gode sosai da kaunarka gareni “”….

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta .
“”” Hakane Habibtiy yanzu zamu tashi in sha Allah,  Amma sai kin bani Amsa daya KINA SONA?”””……

kunya ce ta kamata sosai don batayi zaton wannan tambayar ba a yanzu da haka da sauri ta mike  tare da juyawa zata tafi. Harta fara tafiya ta jiyo muryarsa Cikin ďan ďaga murya yace mata .
“”” Ina son soyayyar mu, da rayuwar Auren mu ta kasance ta daban . Ina son rayuwar mu data yaran mu ta zama abin sha’awar kowa , Ina son komai namu ya kasance na daban . Rayuwa me tsafta da burgewa, farin cikin mu da komai namu ya kasance ďaya Kinga kuwa dole . Sai kin shirya sosai ina son mu zama abin kwantance fiye da romeo and Juliet,  laila da majnon don haka NAMUBAIRINNASUBANE”” ……

Da sauri ta fita cikin lambun maganarsa na mata amsa kuwwa a cikin kunne..

Shima yarima mikewa yayi domin zuwa bangaren shi yayi shirin zuwa  masallaci…

*******
Tafiyar Zeenat bada daďewa ba Maitama ya shigo gidan, bai samu kowa ba matar sa Arwah.
Kwance ya isketa tana ta dariya akan abinda Zeeanat tayi kafin ta fita.

Murmushi yayi mata tare da zama kusa da ita yace “” Gimbiya tah dariyar fa ta mecece akeyi mu ba’a gaya mana mu dara muma””…
Dariya ta kara yi sannan ta bashi labarin abinda ya faru. Shi kansa dariyar yayi don yana zargin Zeenat ma ta faďa son yarima Haidar.

Jawota jikinsa yayi, tare da raďa mata magana a kunne “” Gimbiyata me zan samu ne naga tunda kika zo koďan duban marayan Allah baki yi kamar bake ce masoyiyata ba””.. ya karasa faďa cikin kasalliyar muryar sa . Dagowa tayi suka zuba ma juna ido cikin wani irin maye na soyayya wanda ba kowa ke gane yaren ba sai wanda ya tsinci kansa a irin yanayin.

Kasa magana tayi domin yanayin data tsinci kanta bazata iya furta komai ba .
Lafewa ta karayi sosai  a jikinsa tare da sauke ajiyar zuciya a jajjere.
“” Cutar sonki batada magani agurin likita saidai ke,cancantarki ce tasa hakan Arwah,  ina me tabbatar miki bazan taba jabaya a soyayyar kiba kece farincikin raina, burun zuciyata Arwah tah wai dan Allah wane irin so nake miki haka? “”..

Wata irin mika tayi tare da kara shigewa jikinsa domin salon da yake magana dashi kawai ya isa ya caza ma me lafiya tunani.
Ganin bazata ce komai yasa shi kallonta, yana ganin yanayin da take baisan lokacin da ya kaima bakinta wani irin deep kiss ba. Sun dauki tsawon lokaci a haka , kamar ance mata ta janye jikinta daga nasa sai dai idanuwansa sunyi jajir saboda fitina.

Ita kanta Arwah jikin ta duk ya mutu, ko ina ya amshi sakon mijin nata . Sai dai bazata yadda wani abu ya shiga a tsakanin suba har sai in tarewa sukayi don ba za’a yi abin kunya ba tare da surukai da kannai..

Kara janyo ta yayi jikinsa domin jin sassauci a yanayin da yake ciki . Magana yake a cikin zuciyar sa “” Gaskiya ina bukatarki Arwah , bansan ina da sha’awa ba sai da naga na mallake ki, duk sanda na kalle ki ina jin kamar na haďiye ki don so , Allah ka azurtamu da zaman lafiya tare da zuri’a me Albarka,  Allah ka kara mana kaunar juna””..

“”Ameen ya Allah “” Arwah ta amsa domin maganar zuci ce ta fito fili .

Kallonta yayi da kyau don shi dai yasan a zuciyar sa yake addua amma yaji ta amsa da Amin.

Dariya tayi tace masa “” Hamma duk abinda ka faďa fa a fili ka faďa , nikuma amsawa nayi da Amin kawai “”..

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace mata”” uhum Nidai a zuci nasan nayi amma bakomi tunda wadda nayi don ita ta amsa min. Gaskiya nidai a canza min Hamma nan yanzu fa ni mijinki ne ba yayan kiba “”…

Dariya tayi sosai don indai shagwaba ce tasan da ita yake , don  haka tace masa “”” Hmmmm kawai dai mutum yake baiga nayi shagwaba basai ya wayance va ehe kuma naki nayi 😜😜””…

Ganin ta tashi tanayi mai gwalo  shima sai ya Mike ya bita sunata guje guje a ďakin , cikin farinciki  da shauki na soyayya suke abin gwanin burgewa
Duk wanda zai gansu a lokacin sai sun burgesa sosai don wata irin madarar soyayya suke zubawa kamar su kaďai ne a duniyar..

Sallamar da sukaji ne yasa du dakatawa . Zama sukayi suna hutawa yana rungume  da ita . Sai da tayi masa magana sannan ya sake ta ya fita dan ganin wanda yake sallama a wajen ..
Yana fita gaya wani tsoho tukuf a rakube zaune , gaishe da tsohon yayi sannan yace masa “” baba ban gane kaba kodai cikin Masarautar zaka ka bata hanya ne ??”.

Yadda tsohon ke kallonsa saida gabansa ya faďi. Amma don kada ya ruďa kansa ya kara kallon tsohon da niyyar kara mai magana sai dai yaga tsohon ya daga mai hannu alamar ya mikar dashi zaune .
Bai musa ba ya mikar dashi sannan ya tsaya shima.

“” Nagode yaro Abinda nazo nema ne nasamu shine na bata hanya na biyo ta nan amma yanzu ka kaini hanya na in fita “”…..

“” Toh baba muje na rasa ka ba damuwa ai””..
Tafiya sukayi yana rike da tsohon har fidda shi bakin masarauta sannan ya juyo gida . Koda yadawo Alwala kawai yayi ya tafi masallaci don yin sallah.

Zeenat na dawowa gida Alwala sukayi ita da Arwah sannan suka tada sallah .
Koda suka gama fira suka shiga domin kowa a cikinsu yana cikin farin ciki ne sosai .

Suna nan zaune suna fira Ammi ta dawo itama sallah tayi sannan ta zauna suna ďan taba fira jefi jefi. Koda aka gama sallar asuba maitama da auta nan sukayo suma aka cigaba da fira da tattaunawa akan tafiyar tasu…

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 47&48

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Sosai Sarki Abul Uwais ya shiga tunani da fargaba komai neman kwance masa yake,  babu yadda baiyi ba akan ya daina wannan tunani da yake yi amma abin ya gagara. Haka kawai yake jin matsuwar barinsu kasar Mali sai dai shi karan kanshi bazai ce ga dalilin daya sa haka ba. Zaman fadar yaji ya ishe shi don haka ya mik’e don shiga daga ciki ya kwanta ko zai samu natsuwa..

****
Yarima Uwais ba karamin tashin hankali ya tsinci kansa a ciki ba, tunanin hanyar da zai samu mafita yake nema amma ya gagara samunta. Tunanin yadda zai hana tafiyar su zeenat ke damun sa haka ya wuni ya kwana yana aikin tunani don baisan meyasa ba yake jin kamar da rayuwarsa zasu tafi.
Rashin samun mafita da baiyi ba yasa ya Mike ya shiga bathroom don watsa ruwa ko yaji ďan dama-dama , yana fitowa ya shirya cikin shiga ta Alfarma ya nufi cikin lambu.
Iska me daďi ke kaďa shi tunanin son ganin zeenat ne ya faďo mai a ransa , bai bata lokaci ba wajen tura bayin sa biyu su kira mashi ita. Suna zuwa suka iske zeenat da maitama a waje, koda suka gaya mata sakon tare suka taho ita da yayan ta don haka kawai hankalin sa bai kwanta daya barta taje ita kaďai ba.

Koda suka iso daga bakin lambun ya tsaya ita kuma ta shiga ciki, Yarima Uwais ta gani a kishin giďe  sai kayan marmari a  gabanshi. Dukawa tayi ta gashe shi cikin girmamawa ,
A wulakance ya dube ta da niyyar cimata mutunci sai dai akayi rashin sa’a ta ďago idon ta suka haďa idanuwa.
Gabanshi ne yayi wata mummunar faďuwa nan da nan yaji kanshi ya sara baisan lokacin daya Mike tsaye ba yana kara kallon ta da kyau don zuciyar sa kamar zata faso k’irjin sa ta fito..

Yana niyyar mata magana sai ga yarima Haidar da yarima Ubaid sun shigo lambun a tare suna fira kowane fuskar sa ďauke da dariya. Turus  sukayi suna kallon yarima Uwais don ganin abinda zai aikata , ganin su a cikin wurin yasa shi jin wata izza da jin kai na kara hawa kansa. A yau yana son su gane banbancin dake tsakanin sa dasu sai dai ya rasa ta ina zai fara don zuciyar sa nakan zeenat gaba ďaya  jinshi yake kamar bashi ba wata zuciyar nace masa”” Wannan yarinyar sonta kake dama kabar wahalar da kanka” ..

“” Ina nafi karfin naso wannan yarinyar wallahi baiwa ce fa””. Kamar an fisgo maganar haka ta fito daga cikin bakinsa, don shi kansa bai zaton maganar zata fito ba sai gashi kowa yaji abinda ya fito .

Wata irin dariya yarima Ubaid ya saki don harga Allah yanzu baijin son zeenat saboda babynsa tana kula dashi, amma maganar yarima ta bashi dariya domin asirin zuciya ne ya tonu,  zuciyar ta fallasa sa koda bai shirya hakan ba
“” yaro yaro ne , kace an faďa soyayya kenan ? Ah lallai kam munga zahiri sai dai kuma wannan ďin rabon wani ce don har an ďaura auren ma “..
Cigaba da dariyar sa yayi don so yake ya tabbatar da gaske yarima Uwais son zeenat yake ko ba sonta yake ba.

Cikin zafin rai da rufewar ido yarima Uwais ya shako kwalar yarima Ubaid wani irin zafi da turiri zuciyar sa ke masa.

“‘ karya kake babu wanda ya isa ya aure ta indai ina numfashi,  wallahi ni kaďai zan mallake ta, da soyayyar ta aka halicce ni dan haka babu wani mahaluki daya isa ya aure ta wallahi”….

Fisge jikinsa yayi yana cigaba da dariya domin ya samu abinda yake son yasani ďin, tsayar da dariyar yayi sannan yace masa.
“” Yarima Uwais kabar wahalar da kanka don wallahi ina me tabbatar maka bazaka taba samunta ba, koda ace za’ayi maka rangwame a baka ita wallahi sai nabi duk wata hanya da zanbi don ganin baka mallake taba. Ba irin ka suka dace da ita ba wanda babu abinda yasani sai izza da jin kai mtswww”…

A zuciye yarima uwais yayi kan yarima Ubaid sai shako shi dai dai ganin yarima Haidar a tsakiya yasa shi dakatawa yana kallon sa.

Wani irin miskilin murmushi yarima Haidar yayi don zuciyar sa tafasa kawai take sai dai ganin nuna fushin a bayyane baida wata fa’ida shiyasa ya shanye kayansa. Amma Allah kaďai yasan yadda yake jin kishin Habibtiyn shi a ransa.

Wani banzan kallo ya wurga ma yarima Uwais sannan ya fara magana.
“” Karka yadda ka shiga gonar daba taka ba , karka yadda ka kai kanka inda za’a wulakanta ka , ka iya sarrafa kanka a duk lokacin da ke fushi sannan bayi na kewaye dakai hakan zai iya janyo maka rashin daraja a wajensu. Ita mace da soyayya ake mallakar ta bada karfi ba ko nuna isa, ka nuna jarumtar ka wajen samo soyayyar ta baka zauna kana tada jijiyoyin wuya akanta ba . Ka nemi soyayyar ta daga yau zuwa gobe idan ya wuce haka to ya tabbata har abada babu kai ba ita.”…

Yana gama maganar shi ya juya ya kalli zeenat sannan ya wuce yabar wajen . Bayan shi yarima Ubaid yabi yana dariya sosai.

Kamar an dasa shi haka ya tsaya a wajen maganganun sun tsaya mai ya rasa wane mizani zai ďaura su . Kasa cewa koma yayi don haka jiki a sanyaye shima ya fita aka bar zeenat ita daya a wajen.

Kuka take sosai a wajen, gaba ďaya tunanin ta yana ga yarima Haidar don yadda ya kalleta ya tabbatar mata da ransa a bace yake. Hankalin ta a tashe ta mike ta fita daga wajen itama sai dai tana zuwa bakin wajen taga Maitama wanda yake nan  duk abinda ya faru akan  idon sa akayi…

Kama hannunta yayi suka tafi, koda suka isa Ammi suka iske da Arwah suna haďa kayan da zasu tafi dasu Nigeria. Zama sukayi kowa da abinda yake sakawa a ransa game da abinda ya faru, Ammi ganin sunyi jigum jigum yasa ta kallonsu sannan tace “” Ku kuma lafiya kuka zo kuka zauna mana kunyi shiru, ko wani Abun ne ya faru kuma?”..

Ajiyar zuciya maitama ya sauke sannan ya kwashe duk abinda ya faru ya gaya ma mahaifiyar tasu. Ita kanta abin ya ďaure mata kai sosai ba kaďan ba , sai dai kawai tayi murmushi tace masu ” Dama ita ďin aiba matar yara bace, dole ai hakan ta faru muje zuwa sai ma nan gaba “…
Ammi ta karashe maganar cikin zolaya da son mantar dasu komai don a ganinta ba abin damuwa bane wannan tunda saura kiris subar kasar.

Dariya suka sanya gaba ďayan su,  nan d nan suka shiga wata firar suka manta da wancan maganar . Sunan  har akayi sallah sannan suka mike don gabatar da sallah bayan sun gama ne suka samu kira bangaren me martaba sarki Abul Uwais.

Dukkan su sai da sukaji faďuwar gaba da jin wannan kira amma da yake sun mika lamarin su ga Allah sai suka mike don zuwa suji abinda ke faruwa.

****
Zaune suke gaba ďayansu  yara da matan sarki Abul Uwais sai Amininsa da iyalansa shima .

Tattaunawa suke game da lamarin tafiyar su zeenat, yayinda wasu ke goyan baya akan tafiyar wasu kuma basu goyan baya. Gimbiya Maryama da tafi kowa tada jijiyoyin wuya akan tafiyar domin ita tace zaman su bala’i ne a cikin wannan Masarauta.
Cikin bacin rai ta kalli Abul Uwais da yayi shiru yana jin duk abinda suke faďa tace mashi.
“” Wallahi sai sun bar Masarautar nan taya ma za’a ce kamar Gimbiya kalba ta faďa son wannan kazamin bawan , gashi har tana neman rasa ranta akansa to wallahi bazai taba yuwuwa ba dole su tafi “”..

Cikin fargaba Sosai Gimbiya kalba tace “” momy zaki ida kashe ni da sauran raina wallahi bazan iya rayuwa idan ba tare dashi ba ina sonshi sosai momy””…..
Sakin baki Gimbiya Maryama tayi don batayi tunanin Kalba zata iya faďin haka ba a gaban kowa , bata dawo daga duniyar mamakin Gimbiya Kalba ba taji sautin muryar Yarima Uwais yana cewa..
“” Karya ne wallahi babu wanda ya isa ya tafi dasu suna nan tare damu, momy ba kince na samo baiwa na aura ba saboda cikar burin mu na hawa mulki to nasamu wannan yarinyar ita nake so kuma ita zan aura.””

Cikin gushewar tunani da fita cikin hayyaci yarima Uwais ke wannan magana da ta daki zuciyoyin mutane da dama a ciki. Cikin tashin hankali Gimbiya Maryama ta wanke fuskar sa da mari tana huci don taga baya cikin hayyacin shi , tunaninta ya akai ma har yaga yarinyar yake sonta gashi dalilin ta yana neman tona masu Asiri a bainar jama’a.

Rigima sosai ta barke a cikin wannan babban falo kowa da abinda yake faďi har ana neman buge buge tsakanin yaran .

Sarki Abul Uwais ne ya daka masu tsawa kowa ya natsuwa. Cikin bacin rai da muzanta yace masu.
“” A gabana zaku zubar min da mutunci ku nuna cewar ban isa daku ba , gaban Aminina zaku wulakanta ni . Ganin mu a gabanku baisa kun fasa abinda kukayi niyya ba. Wallahi Allah duk wani ya kara magana a cikin idan har ba izini aka basa ba sai ransa yayi mummunar baci”..

Dafa kafaďar shi Sarki ABDUL GAFAR yayi don yaga sosai Ransa ya baci, shi kansa yaji ba daďin abinda suke yi a gabansu amma bai nuna ba.

Sallamar su Ammi yasa gaba ďaya aka jiyo ana kallon su , ba kowa ya amsa masu sallamar ba dan haka zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa ga shugabanin nasu. Amsawa sukayi daga nan sarki Abul Uwais ya fara magana .
“” Zanyi magana guda ďaya akan abinda ke faruwa ga wannan yarinyar kafin na cigaba da sauran magana. Wacece yarinyar da ake magana akanta? “.
Shiru kowa yayi yarima Ubaid ne ya nuna zeenat dake durkushe gabanta na faďuwa kamar zai faďo kasa.

Gaban sarki Abul Uwais  taje ta duka tace ” Allah ya kara maka lafiya shugaba gani”…

Jinjina kai yayi sannan ya cigaba da magana.
“” Ina son a cikin yaran nan ukku ki zabi ďaya a cikin su idan kuma babu da wani can da kike so to karkiji komai ki gaya min ni kuma nayi maki Alkawarin duk abinda ake ma ýa zanyi maki kuma anan take zan ďaura maki aure da kowa ye matukar kina so kar kiji tsoron kowa a wajen nan faďa kawai”..

Cikin fargaba da tashin hankali ta ďago tana Kallon Ammin ta sai dai ganin murmushi akan fuskar ta tana jinjina mata kai yasa taji kwarin gwiwa ya shige ta sosai sai dai duk da haka a cikin su wa zata nuna.

Juyawa tayi idanunta suka sauka akan yarima Ubaid sai dai bata ga wani abu a tattare dashi ba na nuna kaunwarta ko so dan shi a lokacin ma ya kosa a gama ya tafi wajen babynsa.

Kallonta ta maida kan Yarima Haidar Amma shi Sam bama ita yake kallo ba ransa a mugun bace yake akan abinda yake faruwa a wajen.

Yarima Uwais ta kalla shima dai Kallonta yake sosai dayi mata gargaďi da idanuwan sa .

Tunani ta shiga yi idan harta nuna yarima Haidar to kowa zai zargi wani abu akan zabar su , satar kallon Sarki Abdulgafar tayi sai taga yaďan girgiza mata kai alamar kada ta zaba kowa , dan haka cikin kwarin gwiwa tace .
“” A gafarce ni Ranka ya daďe a cikin su babu wanda nake so ina da wanda nayi ma Alkawarin Aure.””

Murmushi Abul Uwais yayi sannan yace “” Ina son ki gaya min sunan sa saboda na cika Alkawarin dana ďauka akanki . Zan mashi wakilci ke kuma ďan uwanki zai maki wakilci a ďaura auran yanzu domin na raba wannan faďan “…

Sunkuyar da kanta tayi sannan tace mashi. “”  Sunan sa,   ALIYU HAIDAR “”…

Cikin jin daďi maitama ya kalli Ammi dake murmushi kasa kasa wanda ba kowa ke fahimta ba.

Kiran Maitama Sarki Abul  Uwais yayi ba tare da tunanin ba yace.  “” Ku zama shaida zan wakilci yaron da take so a matsayin ďana zan biya masa sadaki dan haka ka wakilci yar uwarka dan kaine babban wants kuma kaine uba a gareta koba anan ba nasan kaine zaka ďaura aurenta , dan haka ina nema wa ďana ALIYU HAIDAR auren ZEENAT akan sadaki 10000cf. cinta, shanta, sutura, lafiya , ilminta, duk mun ďauki wannan nauyin. “…

Anan dai aka kammala ďaurin auren ba tare da binciken me sunan ba sai dai Yarima Haidar da mahaifinshi sun san dashi Aliyun take dan haka wani irin farinciki ya ziyarce su a lokaci ďaya .

Ammi ma farinciki sosai ta tsinci kanta a ciki don batayi tunanin Zeeanat zatayi wannan basirar ba gashi cikin sauki an ďaura aurenta da wanda take so yake sonta.

Wata irin gigitacciyar kara yarima Uwais yayi tare da mikewa tsaya sai dai wani irin tari daya taso mai ya sarke shi nan take yanke jiki ya faďi. Gaba ďaya hankalin su ya tashi don basu tsammanin hakan ba.

Kiran likita akayi yazo aka ďauki yarima aka kai wani ďaki  aka kwantar dashi ko numfashi bayayai da taimakon Allah likitan yaso ya dawo da numfashin nashi ya koma daidai. Allurar bacci akayi masa sannan kowa ya fito aka dawo falon gimbiya Maryama ce kawai aka bari wajen shi tana ta kuka..

Kowa ya natsu sannan Sarki Abul Uwais ya cigaba da magana.”” Alhamdulillah na cika Alkawarin dana ďauka, yanzu kuma zan yanke hukunci ne akan maganar tafiyar ku dan haka babu fashi zaku tafi sannan zaki gaya ma wanda aka ďaura aurenku ya shirya tare dashi zaku tafi, maganar  Gimbiya Kalba da Wannan yaro da take so kuma zuwa gobe zamu yanke hukunci akai.””…..

Maitama ne yayi saurin cew. “” Allah ya taimake ka Ni a ganina bai dace ta auri bawa ba kuma talaka wanda yake da mata dan shi baida ra’ayin sama da mace ďaya a gafarce ni idan na fadi ba daidai ba “”..

Murmushi me ciwo Sarki Abul Uwais yayi don dama yadda yaron yake abu da izza ko maganar sa yasan hakan na iya faruwa , amma ba kowa ya jawo masa ba sai Kalba…

Ya bude baki kenan zaiyi magana sai ji yayi ance…

“” ASSALAMU ALAIKUM “”..

A mugun razane ya mike tsaye domin wanda ya gani ya matukar razana shi…….

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Page 49&50

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Gaba ɗaya wanda suke cikin babban falon na Sarki Abul Uwais suka jiyo suna kallon wannan tsoho daya shigo. Takowa  tsohon yayi har ya iso tsakiyar su, idanuwansa suna kan Sarki Abul Uwais dake tsaye jikinsa ko ina yana rawa.
Yarima Haidar ne ya lura da Abul Uwais dake neman faɗuwa da sauri ya tashi ya isa gareshi ya rike shi ya zaunar dashi inda yake zaune.

Ganin An zaunar da Abul Uwais sai tsohon yayi murmushi sannan ya nemi guri ya zauna yana bin kowa da kallo . Kasa hakuri me martaba sarki Abdulgafar yayi dan haka ya ďago ya kalli tsohon sannan yace masa.
“” Baba tsoho lafiya kake kuwa ka shigo kai tsaye har nan ba tare da fargabar komai ba”…

Wani irin murmushi me ciwo ya bayyana a fuskar wannan tsoho. Sai kawai ganin hawaye sukayi yana zuba akan fuskar sa, sai da yayi kukan sa me isar sa sannan ya ɗago yana ƙara kallon kowa dake wajen sana ya fara magana..
“” Kuyi hakuri da Abinda zakuji daga bakina sai dai a yau,  tulun da aka cika aka binne shekara da shekaru yau zan tono shi kuma da hannu na zan fashe shi. Sai dai ina son kafin na fashe shi a jira isowar Shugaban ƙasar Mali da duk wani mai faďa aji a wannan kasa, sannan abu na gaba kuma da zanso ku sani kowa ya Hallara a cikin duk wanda nake son nagani a wajen nan har da karin wani sarkin ma da iyalansa””…

Kowa yayi shiru yana sauraran wannan tsoho sannan kowa da abinda yake sakawa a ransa game da maganar da yayi yanzu.

Gimbiya Maryama ce ta da baro yarima Uwais ya samu bacci ta samu wannan tsoho na waɗannan maganganun tace masa.”” Kai asuwa da har zaka zauna kana bama mutane umarni akan wasu surutan banza naka, ka tashi ka bar nan kafin ka fuskanci hukunci daga wurina””…..

Murmushi Baba Tsoho yayi sannan yace mata .”‘ Da kin kwantar da hankalinki da yafi maki wannan surutun ki jira nan da wasu awanni kiga yadda rayuwarki zata koma , abinda ya kamace ki kenan zama ki natsu.””…

Gabanta sai da ya faɗi akan maganar ta Baba Tsoho,  Amma dayake tunanin ta bai bata wani abu ba haka ta zauna sannan ta ƙara cewa. “” Waɗannan bayin su zaman me sukeyi anan to ? Ina zaton ai angama dasu ko ? Dan haka kuna iya tashi kuba mutane waje”…

Kowa yasan dasu Ammi suke dan haka suka mike da niyyar barin falon sai dai jin muryar baba tsoho yasa su dakatawa.
“” Ko dawo ku zauna kusan Rabin zaman nan dama  danku za’a yi shi “….

Gabansu  saida ya faɗi amma banda Ammi don wani irin murmushi da tayi ne yasa yaran nata kallonta da kyau, ganin ba wajen tambaya bane suka kama bakinsu sukayi shiru.

Basu kaɗai wannan lamari ya faɗar ma gaba ba, harta da sarki Abul Uwais sai da gabansa ya yanke ya faɗi..

Gimbiya Maryama da Gimbiya Mufida kallon juna sukayi kowa gabansa na faɗuwa sosai , kowane da Abinda yake sakawa a ransa game da lamarin kansu duk ya ɗaure.

Gimbiya Sakina kuwa babu Abinda yake damunta sai dai kawai gabanta da ya bata akwai gagarumin abu dake shirin faruwa yanzu.

Yarima Ubaid kuwa hankalin sa nakan babyn sa , ya kosa a tashi wajen nan saidai kuma gabansa faɗuwa kawai yake jikinsa yana basa akwai abinda yake shirin faruwa dasu.

Jiniyar shigowar me Girma Shugaban ƙasar Mali ne ya dawo dasu daga tunanin da kowannen su ya shiga. Nan da nan Masarautar ta ɗinke da manya manyan mutane masu faɗa aji da jami’an tsaro ta ko ina daga ƙasar Mali.

Bayan komai ya lafa , sannan kayi adduan buɗe taro daga nan kuma hankalin kowa ya koma kan shugaban ƙasa da zai fara magana.

   “””Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya tara mu anan, Ina ma kowa fatan Alkhairi. Dalilin taruwar mu anan ba komai bane illah ta dalilin wannan bawan Allah wato Baba Tsoho, Yazo mana da wani babban Al’amari game da wannan masarauta,  dan haka muke son jin Abinda ke faruwa daga bakinsa.””…..

Tsit babban falon ya kara ďauka kowa ya kosa yaji menene wannan Abu.

Baba tsoho ne ya fara magana kamar haka. “””  Shekara Ashirin da takwas da suka wuce anyi wani Adalin sarki wanda yasan darajar duk wanda yake kasa dashi. Rashin lafiya tasame shi dalilin damuwar iyalinsa daya saka a ransa wanda suna kasar Nigeria acan ya baro su , babu yadda baiyi ba akan abarsa yaje ya taho dasu amma Mahaifinsa ya hana shi saboda shi zai hau kan mulki a lokacin,  babu yadda ya iya dole ya hakura aka  ďauka shi amma koda yaushe tunanin iyalansa yana damunsa domin yayi masu alkawarin zaije ya ďauko su, su dawo kasar sa cikin ahalinsa da zama . Ni ya turo domin zuwa na taho mai dasu a lokacin nine babban Amintaccen sa, koda ya bani adireshin su naje ban same suba ance sun bar wajen sanadiyar gobara ba’a san ina suka koma ba. Na dade ina neman su ban samu ba , har na gaji na dawo na sanar dashi abinda ya faru . Wannan labari ya kara tayar da ciwon sarki  AHMAD ABDULRAHMAN ABDULLAHI. Haka yasa akayi shirin fita dashi kasar waje, ba’a bata lokaci ba aka shirya tafiya a hanya ta zuwa aka buďe mana wuta a kuma nan take aka kashe gaba ďayan ahalin wannan adalin Sarki. Koda ake harbin karkashin mota na shiga hakan yasa babu wanda ya kula dani.””

Numfasawa yayi sannan ya cigaba da magana..
“”” Abin mamakin anan wannan wanda yayi kisan ba kowa bane illah ZAINUL ABEEDDEN kanin GIMBIYA MARIYA matar adalin sarki na farko wato Maimartaba Sarki ABDULRAHMAN ABDULLAHI, Kasancewar bata da namiji ko ďaya a yaranta shiyasa ta shirya duk abinda ya faru . Sai dai kuma motar da take ita da yaranta gaba ďaya suma aka buďe masu wuta nan take kowa ya mutu har ita me shirya makircin.
Koda yaga yayi galaba sai ya juya suka bar wajen shida yaran sa. Ban bari anzo an same ni wajen ba guduwa nayi nafara shirin shiga Nigeria domin nemo iyalan sarki AHMAD ABDULRAHMAN ABDULLAHI.
Nasha wahala sosai kafin nasamu inda iyalansa suke a nigeria saboda bansan yanayin kasar ba saidai na tafi da kuďi sosai hakan ya saukaka min wahalar , Duk yadda naso matar maragayi Sarki AHMAD ta saurare ni ta kuma fahimce ni amma taki hakan yasa na sace mata yaro ďaya UMAR  domin saukaka mata wahalar da take ciki. Nan na maido Umar nasa shi makaranta ya cigaba da karatu, yayi mitar mamansa har ya gaji ya hakura ,  ni kuma na koma Nigeria na cigaba da bibiyar su”””…..

Kuka Ammi ta fashe dashi me tsananin ďaci da cin zuciya. Sannan ta sassauta ta fara magana.
“”” Hakika mun tsinci rayuwar mu cikin wani bahagon yanayi , a yau zan sanar daku asalin ku yarana!. Bayan tafiyar AHMAD  iyayena sun matsa akan guduwa yayi yabarni dan haka bazasu kula da yaransa ba sai dai a tura su kasar su wajen mahaifinsu. Nayi iya yina domin na fahimtar da su amma abin ya gagara, hakan yasa suka cire hannunsu akan lamarina. Anyi ma babana karin girma ya koma Ambassador na Nigeria a kasar London dan haka suka nace akan lallai dani zasu tafi yaran na tura su kasar mahaifin su , ganin na kiya suka kyaleni badan ransu yaso ba suka ban kuďaďe masu yawan gaske suka tafi. Bayan nan nasake  ABDULRAHMAN makaranta wanda muke kiranta da MAITAMA domin mahaifinshi haka yake kiransa a cewarsa bazai taba mantawa da Maitama ba saboda anan ya haďu dani , bayan wani lokaci kawai muka tashi da gobara a gidan da muke ciki wadda bamusan daga ina ta taso ba Abubuwa masu mahimmanci kawai na fidda mukabar gidan daga nan ne rayuwar mu ta shiga garari da kyar na samu gidan haya na kama mana har Maitama ya gama primary dinsa . Hijira mukayi daga Abuja muka koma kano nan rijiyar Zaki nashi makaranta ya fara secondary anan , ita kuma khadija wadda muka boye sunan ta ya koma Zeenat nasata tacigaba lokacin tana ajin karshe a primary.  Anan na haifi Abdallah wato Autah, munsha bakar wuya sai da muka koma abinda zamuci ma yana gagarar mu , har Maitama ya gama secondary ita kuma Zeenat na ajin karshe , suna gama makaranta na saida abin hannuwa na na gold da nake ta boyo saboda tafiya nemo AHMAD kasar mali.
Bayan munzo kasar mali munsha wuya mun tagayyara sosai Haka muka dinga ratsa garuruwa har muka isa wani kauye me suna KAUYEN KYAUTA.  acan muka haďu da wannan yarinyar ARWAH da Mahaifinta sune suka bamu waje, ban boye masa komai ba game damu hakan yasa ya fara mana bincike har ya gano mana wannan masarauta, shine yayi mana hanyar da aka siye mu a matsayin bayi da kuma bama ďana kyautar yarsa wanda har ya ďaura masu Aure yanzu haka””….

Gaba ďaya falon salati suka ďauka domin basu taba cin karo da wannan zalunci ba sai a yanzu da suke sauraron shi.

Baba Tsoho ne ya cigaba da magana .
“”” Bayan na cigaba da bibiyarta har na gano ta iso cikin Masarautar nan , hakan ya bani damar cigaba da bincike na . A yanzu haka Umar yana matakin shugaban babbar University din dake bamako babban birnin kasar mali kuma yasan komai domin yana badda kama yazo yaga yan uwansa da mahaifiyarsa. Wannan shine Umar gashi nan zaune cikin manyan kasar Mali. “….

Cikin sauri Su Ammi suka kalli inda aka nuna masu UMAR,  shima kallonsu yake sai hawaye da yake sharewa.  Kuka suke sosai domin bazasu manta dashi ba ga kamannin su nan bayyane .

Cigaba da magana baba Tsoho yayi .
“”” Ni nasamu SARKI ABDUL GAFAR  da maganar halin da wannan masarauta take ciki saboda a bincike na Aminin ZAID ZAINUL ABEEDDEN ne wato Sarki Abul Uwais, shi ya bani goyan baya sosai akan abinda nayi sannan ya shaida zuwansa kasar mali .yasan koma dan haka koda isowarsa Bayan ya huta sai da na shigo masarauta muka tattauna ana  ne ďansa yasan abinda ke faruwa ya kuma ďauki alwashin sai ya maye gurbin farin cikin da suka rasa ta hanyar Auren ZEENAT.
Duk abinda yake faruwa sun san komai dan haka komai daya faru a shirye yake . A yanzu haka waďannan yaran da mahaifiyarsu suke da asalin wannan mulki,  suke da gadon shi. Wannan sarki kuma dayake kan mulki mahaifin sa ne ya kashe ahalin wannan masarauta masu mulki da adalci. Sannan ya ďaura ďansa wato ABUL UWAIS  shi kuma Bayan ya hau ganin yadda iyayen sa keso yayi shi kuma ba haka yake so ba yasa ya tura aka kashe su domin ya zama daga shi ya yaransa akan Masarautar Ulwa.””…..

Gaba ďaya kabbara Babban falon ya ďauka, nan da nan hayaniya ta barke bakajin maganar wani saboda tashin hankali abinda kuma basu sani ba gaba ďaya duk wannan labari da ake ana ďaukar shi dan yanzu haka a gidajen radio da television a live suke kallonsa.

Wasu na murna sosai yayin da wasu ke cikin tashin hankali marar misultuwa.

Shugaban kasar Mali ne yayi magan na take wajen yayi tsit. Sannan ya fara magana.

“”” Allahu Akhbar! Allah me girma , babu abinda zamuce sai godiya daya bayyana gaskiya a yau dan haka bamu da lokaci yanzu zamu yanke hukunci sannan zamu fidda rana domin naďin sabon sarki wato ABDULRAHMAN AHMAD ABDULRAHMAN ABDULLAHI ( A A MAITAMA). Dan haka gaba ďaya iyalan Abul Uwais a kamasu  kuma tsare su ayi masu hukunci daidai da laifin su su kuma waďannan a yanzu zamu Mika masu mulkin su a hannun su.”””…..

Kabbara ta hau tashi a wajen Su Ammi kuwa banda kukan farinciki babu abinda suke yi .

Nan take aka Mika ma AA Maitama Abubuwan mulki sannan aka naďa mai rawani aka ďaura shi sai zuwa lokacin da aka yanke za’a yi shagalin naďi.

Alkyabba ta Alfarma aka saka ma Ammi tana hawaye sannan sauran yaranta ma .
Nan take aka bayar da umarnin a fidda komai na masarautar sannan a wanke ta sai ayi zubin wasu kayan .

Su ABUL UWAIS kuwa da zuri’ar sa aka tasa su aka zuba a mota akayi waje dasu .
Shugaban kasa ma iyalansa sun tafo kowa ya watse . Sai su Ammi kawai da iyalanta a falon . Godiya suka kara yi ma Allah anan suka shiga murnar ganin Umar , fira suke cike da murna wadda suka daďe basuyi ba .

Anan Umar yaga khadija ďiyar sarki ABDUL GAFAR  kanwar yarima Haidar yaji yana sonta kuma yayi mata bai bata lokaci ba ya gaya ma Maimartaba anan kuma ya bashi auren ta.

Bayan sati biyu da faruwar komai, hankali ya kwanta komai ya lafa anan kuma aka shiga shirye shiryen Naďin sarki tare da bikin auren.ME GIRMA SARKI ABDULRAHMAN DA GIMBIYA ARWAH.sai kuma
YARIMA HAIDAR DA GIMBIYA ZEENAT.
YARIMA UMAR DA GIMBIYA KHADIJA…..

MASARAUTAR ULWA

          NA

A’ISHATULHUMAIRA

Mikiya writer’s Association.

Bismillahir Rahmanir Rahim.

LAST PAGE

Yau takama Asabar a yaune ake shagalin biki naďin Sarki ABDULRAHMAN AHMAD Ango ga Gimbiya Arwah. Tun safe ake shagali kamar ba gobe yayinda ƙarfe goma na safe yan Nigeria suka samu isowa Masarautar ulwa, nan da nan masarauta ta kara rikicewa da mutane, ta ko ina bullowa ake, ko ina ka shiga abinci da abinsha gasu nan kamar banza.

Karfe Biyu  na rana aka ďaura auren Yarima Umar da Gimbiya Khadija sai na yarima Haidar da zeenat da aka kara jaddada shi ga dunbin jama’a. Sai na Sarki guda da aka kara jaddada shi ga duniya baki ďaya. Daga nan  shagali ya fara ba gajiyawa, masu kiɗin kwarya nata yi, masu na gargajiya nayi, abin gwanin birgewa, har la’asar anata shagali daga nan aka fara shirin kilisa ta anguna da amare.

Gimbiya Arwah ce cikin Alkyabba ja kayan jikinta kalar golden tayi kyau harta gaji, kayan sun matuƙar dacewa da jikinta, sai zuba kamshi take kamar anyi barin turare akanta. Arwah nada kyau sosai asalin kyau, domin kuwa gado tayi ba haye ba a sannan ta fito asalin  Shuwa Arab dinta. fatar nan tata sai daukar ido take ga gashin nan kamar an dasa shi, Abun kam sai masha Allah domin Amarya kuma Gimbiya tasha kyau harta gaji.

Gimbiya Zeenat kuwa Alkyabba ta, ta kasance kalar golden kayanta kuma lace ne golden brown me kyau da laushi kallo ɗaya zaka mai kasan me tsadar gaske ne, ya dace da ita sosai. Sai lokacin na kare ma zeenat kallo sosai, Fara ce me ɗauke da dogon hanci, fuskarta doguwa ce amma ba sosai ba tana da karamin baki wato cute lips, tana da idanuwa masu kyau sosai wanda suka dace da fuskarta, tana da tsawo sosai sannan tana hips wanda suka fidda ainahin shape dinta. Kyakkyawa ce sosai zeenat ta ƙarshe kuma ajin farko sai dai muce ma sha Allah.

Ɓangaren gimbiya khadija kuwa ita ma tasha kyau sosai, lace ɗinta kalar pink ne da touch  din milk sai Alkyabba ta milk colour, tayi kyau sosai da sosai don itama tana da kyanta daidai misali ba fara bace amma tana da haske don bazamu kirata da chocolate ba tana haskenta amma bata kai farare ba..

Angu nah kuwa suna can ansha kyau har an gaji. Kowane ango kalar kayan matarsa ya saka haka suka jero a farfajiyar Masarautar suna jiran a fiddo masu matayen nasu. Kowa ne ka kalli fuskarsa zaka gansa cikin annuri….

Amaren aka fito dasu kowace aka aje ta wajen Angon ta, nan da masu ďaukar hotuna da gidajen tv da yan jaridu suka shiga ďaukar su ba ƙakƙautawa. An ɗauki lokaci ana kiɗe kiɗe da hotuna sannan suka hau dokuna don fita kilisa zagaya gari..

Sosai kilisar ta kayatar don kuwa kamar hawan sallah haka mutane suka fito da yan kallo da yan tawagar kilisar. Sai gab da magriba sannan suka dawo gida kowa ya tafi ya kwanta domin gobe za’a miƙa amare ďakin su.

Washe gari ma ansha shagali sosai kuďi sun magana sosai domin yan wasa aka ďauko daga ƙasashe a wajen walimar da aka shirya. Bayan sallar isha’i aka ƙara shirya Amare kowace aka miƙata ďakinta. Amaryar Yarima Umar aka fara tafiya da ita domin ya ƙyanƙyasa gidan sa yace Sam bazaiyi zaman masarauta ba, tunda yana aiki kuma nesa ne ba kusa ba  dan haka can za’a kaita idan ya aje aiki saisu dawo masarauta.

Bayan an tafi da ita sannan yan uwan Gimbiya Arwah suka miƙata part ɗinta na musamman a cikin Masarautar, bangaren uwargida kenan ya ƙawatu an zuba kudi na tashin hankali a wannan bangaren.sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya gimbiyar Maitama..

Gimbiya Zeenat ce ƙarshe domin ita sai jibi da safe zasu wuce ƙasar Nigeria, Amma duk da haka bangaren yarima Haidar da aka gyara aka ƙawata can aka kaita.

Ƙarfe 11:30 na dare agogon bangon ďakin Zeenat ya buga amma har yanzu bata ji  motsin kowa ba dan haka ta tashi ta murza key a ďakin ta shiga bayi tayi Alwala tayi sallah sanna  tayi addua ta haye gadon ta kwanta tare da sake yin addua sai bacci domin ba karamin gajiya tayi ba..

Yarima Haidar kuwa baisan a ankai  mai Amarya ba yana can ɓangaren sarki ya samu wani ďaki ya shige ya kulle kansa yanata bacci abinsa.

Yarima Umar kuwa yana can yana shan soyayya wajen matarsa duk da tana jin kunyar sa,  taƙi sakin jiki dashi amma a haka yake ta lallabata, harta saki jiki suka ci suka sha sannan sukayi sallah don nuna godiyarsu ga Allah. Bayan ya dafa kanta yayi mata addua sannan yayi mata duk tambayoyin da zai mata Alhamdulillah ta amsa masa kuma ya samu gamsuwa sosai da amsar data bashi hakan ya tabbatar masa da tarbiyar ta. Wanka ya tafi dakinsa yayi sannan yayi  shirin bacci na nufo ďakin amaryarsa. Koda ya shigo itama tayi wanka tayi brush dinta da kayan bacci sai kamshi take amma ta ďora hijab babba akai . Fira ya zauna suka ďanyi ,
Daga nan kuma suka koma bakin gado   a hankali ya jata jikinsa ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya. Daga nan kuma wasan ya canza aka tafi wata tashar.
Mu kwana lafiya Mr and Mrs Umar…

Ɓangaren su Gimbiya Arwah kuwa, sharholiyarsu kawai suke zubawa ta soyayya domin kuwa Maitama yace baisan wata kunya ba raƙashewa zaiyi a wannan daren, duk yadda taso kwantar da hankalin ta a lokacin amma ta kasa. dan yadda yake nuna matan tabbas tasan babu ďaga ƙafa. Duk abinda musulunci yace ayi sun ƙaddamar dashi a wannan dare dan haka  Sarki Maitama angon Arwah ya zaƙe yana ta shagali, wata irin soyayya da tattali yake gwada mata a zahirance hakan ya ɗimauta ƙaramar ƙwalwarta. Duniyar data tsinci kanta yasa numfashin ta daukewa a wannan dare shi kuwa yana can sharholiyarsa baisan abinda ke wakana ba. Baisan abinda ke faruwa ba sai da ya dawo natsuwar sa , hankalin sa ya tashi sosai dan haka ya zage yana bata taimakon gaggawa harta dawo hayyacin ta. Kasancewar tasan yadda ake faďin wannan dare da yadda mutum zai tamaki kansa hakan yasa bata cuci kanta ba ta bari ya gasata sosai. Nan da nan ta fara komawa normal ganin Alhamdulillah jikin ya saki sai ya ďauko ta ya maida bakin gado ya cire bedsheet din ya canza wani, sannan ya kwantar da ita aikuwa kamar tana jira yana kwantar da ita sai bacci. Shima wankan yaje yayi sannan yazo yayi sallah ya kwanta tare da rungumeta a jikinsa yana ajiyar zuciya.  Nan take shima baccin yayi gaba dashi….

Washe gari kuwa yan Nigeria suka fara shiri domin jirgin asuba zasu bi zuwa gida. Dan haka Ammi tasa aka ƙara gyara mata Zeenat gyara na musamman. Ciki da waje Zeenat tasha gyara ba kaďan ba, duk inda ta wulga sai ka ganta kamar walkiya.a yinin ranar basu haďu da Yarima Haidar ba yana can shirye shiryen tafiya itama anata shiryata….

Wajen Amare kuwa, kulawa sosai suka samu daga mazajen su. Tare da wata irin zazzafar ƙauna me cike da shauƙi da tafiya da rai.yini guda suna manne da Amaren su basu san ko motsin kirki suyi..

Da asuba jirgin su zeenat ya tashi zuwa Nigeria. Tayi kuka kamar ranta zai fita yan uwanta ma babu wanda bai zubar mata da kwalla ba. Kowa yana jin tausayinta, tabar ƙasar da yan uwanta suke ta tafi wata. Auren kenan babu inda baikai ďiya mace…

Bayan isar su Nigeria  ba karamin shagalin biki suka tarar anayi ba, sai da aka kwana biyu ana biki a Masarautar Gombe sannan aka bama ango Amaryar sa.

A wannan dare Yarima Haidar ya tabbatar ma Zeenat irin matsanan ciyar kaunar da yake mata . Yayi mata gata wanda ita kanta ta shaida hakan , a ranar ya tabbatar mata da Kalmar da yake faďa NAMU BA IRIN NASU BANE.  Domin yayi kuka share share da idanunsa akan ni’imar daya samu tare da wata irin natsuwa da bai taba samu ba a rayuwar sa, sai yau wajen Habibtiyn shi. Wannan dare ya kasance mafi soyuwar dare da bazasu taba mantawa ba, sun sha soyayya kamar su maida juna ciki.Sun aje tarihin da bazai taba goguwa a zukatan da suka mutu akan juna ba, soyayyar su daga Allah ne, domin shi kaďai yasan yadda suke mahaukacin son juna .

Rayuwar da suke ta kasance rayuwa mafi soyuwa ga dukkan wasu masoya, yadda suke tattalin junan su da yadda suke girmama juna da mutun tawa dole abin ya birgeka. Rayuwa suke me cike da tsafta da sanin darajar Aure. Basu ďauki burin duniya fiye dana lahirar su ba, Komai zasuyi suna duba dacewa da Addinin su fiye da san ransu….

B̸A̸Y̸A̸N̸ S̸H̸E̸K̸A̸R̸A̸ U̸K̸K̸U̸.

Gaba ďaya ahalin Masarautar ulwa ne  da zuri’ar su,  kowa kalli fuskarsa zaka gansa cikin walwala da farin ciki.  Ammi ce na zaune yan jikokin ta duk sun zagaye ta.
Yarima Umar yana yarinya ďaya AISHATU suna kiranta da KHAIRAT. A  yanzu matarsa tana da wani tsohon cikin.
Gimbiya zeenat kuwa tana da santala santalan yaranta maza guda biyu twins. AHMAD DA ABDUL GAFAR. Suna kiranki da Arif da Ahyan.

Gimbiya Arwah da sarki kuma suna da ďa namiji ďaya me suna ABDULRAHMAN, suna kiransa da ASAD.

Gaba ďayansu kowa yana babban falon Ammi suna ta fira abinsu cikin farin ciki,  dama su Zeenat hutu suka hakan yasa lallai matar Yarima Umar ita ta taho hutun suka haďu gaba ďayan su anan.

Kowannen su, suna rayuwa cikin farinciki da kwanciyar hankali, tare da kaunar juna. Babban abin burgewa ga wannan zuri’ar shine haďin kai, suna matukar girmama junan su. Kowa na nuna kaunar yan uwansa a bayyane da baďini.

TAMMAT BIHAMDULILLAH..

ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI UBANGIJI KA  YAFE MANI KUSKUREN DANA RUBUTA.
ALLAH YASA ABINDA YAKE DAIDAI YA ZAMA ALKHAIRI A GAREMU.
DA FATAN ZAMU ĎAUKI ABINDA YAKE DAIDAI WANDA BA DAIDAI BA MUBAR SHI.

INA MAI TALLAH TA MAKU SABON LITTAFI NA DA ZAI FARA ZUWA BADA DAĎE WA BA INSHA ALLAH..
FATAN ZAMU KASANCE TARE A WANCAN TAFIYAR DOMIN DA ZAFINSA  ZAI SAUKA…

Leave a Reply

Back to top button