Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 69

Sponsored Links

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣9️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

Tani data hadu dashi zai shigo asibitin ya tsaya suka kara gaisa nan kwarmaton ta ya debe wurin dadin hira har take labarta mashi abubuwan da suke faruwa kafin tayi mai sallama zataje taron yarane ya biya mata kudin mashin ta dane zuwa gida.

Da sallama ya shigo dakin sai ga su Hannatu suma sun shigo tare da Dije da kanwarshi Aisha dauke da ledan pure water a hannun Aisha din.

Gaida ummah yake jin hakan yasa na juyo ina masa kallon mamaki lokacin hannatu ta gani take fadin masha Allah kintashi matar master ?

Duk suka juyo suna kallona to keyi kwana na rigaki karban jakkan tun dazun ai har na banye na bar maki ragowa jin hakan ya dan sani murmushi kadan ina kokarin juyowa.

Sai ya mike ya nufo bakin gadon yana fadin kin tashi Zahra ya jikin naki yana kokarin taba jikina lokacin Dije ke fadin kai danga ga idon uwarku kana kokarin taba matar ka gaba  mu ?

In bakaji kunyan idona ba aikaji na uwarku ummah ta mike tana fadin mama ki barsu sallah zan tafi yanzu inyi ni to Dije ki bita kada ki zauna ki saka muna ido Aisha kai masu ruwan nan sai suyi alwala dashi.

Babu Faro ne hannatu kuka sayo wanan ga ummah  da ledan Faro kuka dauko ai da sauri ummah tace a a kai wanan din ma ai muna amfani dashi sosai ko a gida.

Bari dai a je a sayo makushi wanan din sai a aje don wani amfani zauna abinka don Allah wanan ya wadatar ai lalurane ya kawo hakan.

Jin hakan ya koma ya zauna yana fadin hannatu ko zaki zuba mata abinci ko zataci wai to Allah yasa tunda kana kusa amma rabon zahra da abinci ni har na manta ta fada tana mikewa da kyat na daga mata hannu alaman ta barshi.

In serious voice yake fadin don me zaki zauna da yunwa a cikin ki haka kina gani  yunwama ai yana iya kara maki ciwon na girgiza kai alaman a a.

Naji yace haba princess ko yunwa na kara maki ciwo ai ki daure ko ba yawa kici ko kadan ne haka nake fada mata amma da takai baki zata dawo dashi.

Wani kallo naga yayiwa hannatu dake bayanin hakan gareshi kun fadawa likitocin haka duk mun fada masu yadda take ji din sun dauki bayani.

Tun kan a kawo abin na kawar da kai ya karba wai ya bani da sauri na rufe bakina kamar wanda yaga mugun abu a lokacin guda yayi yayi na juyo na karba na kasa.

Haka ya hakkura ya mike tsaye ya fita ya dan jima sai gashi ya dawo da leda da kayan sanyi a cikinsa ya samu sun shigo dakin ummah tana min fadan cewa na don me ba zan daure koba dadi inci abincin nan ba.

Ummah ku barta ko zata sha wannan yana kokarin budan ledan ya zaro goran fresh milk ya miko min yana kokarin budewa tare da fadin ki daure ga wanan ki dansha ko kadan ne.

Yadda na karba a hannun shi hakan ya tayar mai da hankalinshi karkareni daya ga yadda na fitar da idannuna waje saida gaban shi ya fadi don tsoro.

Wani iri yake ji lokaci guda kanshi na wani irin juyawa hankalinshi na neman gushewa gare shi Allah ya taimaka yayi dabaran mikewa zuwa wajen dakin da sauri zakace ya tuna da wani abune a lokacin.

Ruwa ya saya ya tsiyayya a kanshi tun wanan lokacin ya koma wani sukuku dashi kamar wanda ke ciwo ko dakin baya son shigowa sai dole in ma ya shigo can kofa zai tsaya yai maganan da zaiyi ya koma.

Ummah ce ta farga da hakan ta farawa dije bayanin amma taga Dijen bata gano komai data gano ba sai bayan sallah magariba ta dawo daga sallah ta sameshi zaune yayi tagumi shi kadai a wurin zaune.

Har zata wuce ta gano shine tace Ahmed ne wai ya dago kai da sauri yana mikewa tare da fadin barka da fitowa ummah Allah ya karba tace amin.

Lafiya dai na ganka haka tun dazun nake lura da sauyi gareka saidai ban san me ya jawo maka hakan ba lokaci daya ta fada tare da tsureshi da idanunta.

Eh wallahi dama ba komai bane saidai ban san ya za a fahinci magana taba yanzu idan na fada don gaskiya na fahinci ciwon nan na zahra kamar dai bana asibiti bane kawai kamar ya dan surku da harkan jinnu haka.

Wani kallo na tsab ta aika mai dashi lokaci guda kafin ta sauke ajiyan zuciya tace eh zai yuyu hakan ne don nima nayi wanan tunanen amma yanzu tunda munzo saimu dakata muji abinda sakamako zai bada kafim mu san abin yi nima dai hankalina bai kwanta ba a yadda nake ganin ta din nan.

To shike nan ya fada tare da dan sunkuyar da kai katsa tace Allah ya kyauta ya amsa da amin ta nufi hanyar shiga dakin da nake kwance.

Sai kuma taja ta tsaya tare da dan juyowa ta kalleshi tace da badon akwai gajiya a tare da kaiba dakayi sakkon zuwa zuwa funtuwa gobe kaje kaga wani kawuna a can da ake kira malam Idi mai rafannan acan.

Da sauri yace ba matsala sai inje din ko yanzu badon dare yayi ba aida zan tafine tace a,a ka bari zuwa gobe din nan tayi mai kwantace yace ya gane insha Allahu kuma zai tafi din in Allah ya kaimu da safe sukai sallama take fada mai tunda jjkin nawa da sauki zata koma gida tunda ga Djje da hannaty har da Aisha.

Tayi waya azo a dauke karfe goma yayi mata godiya ta juya ziwa dakin ya koma ya zauna nan dije tazo suka zauna suna dan tatataunawa kan zancen matsalan nawa.

Cikin bacin rai ta juya tabar dakin ganin ya dauki waya ya fita batun ta ya nuna baida lokacin ta kamar yadda tayi mai itama ke nan da safen.

Saidai bata dauki nata da sunan wullakaci ba sai nasa don haka ta kulla a ranta cewa ai don hjy murja dince yai mata hakan bako sauran zaman lafiya ke nan a tsakanin su a gidan .

Don haka zata kada masu gangan shedan da sai duk sun raina kan su suyi da sun sani da basuyi mata hakan ba a rayuwan su don ba a takata a wanye lafiya a rayuwan ta.

Ita mace ce dake tsaye da kanta da yayanta a ko wani lokaci tayi a mannan cewa boka da malam suna biyawa mutum duk bukatan sa idan ya nemesu.

Da wanan kudirin takai dakinta ta kwanta tana faman saka yadda zata fara bullowa zancen da hjy murja zata fara koda maigidan yanzu nan tunanen ta ya tsaya akan zata yakesu a lokaci dayane don da zafi zafi ake buga karfe.

Mai aikinta ta nema da sunan bata umurni akan ta san ita dai ta daukota aiki a gidan nan ko daga lokacin aikinta zai tsayane akan ita da yayanta da mijjnta kawai a gidan.

Da sauri Asabe ta dago kai ta kalleta don jin umurnin da tabata a lokacin kafin cikin ladabi tace hjy ki gafarceni jiyan nan Alh ya ban umurnin da a hade girki ga baki daya a gidan nan.

Itama din wani kallo ta jefeta dashi a harzuke take fadin Asabe nina daukoki gidan nan ko shi kece hjy Asaben ta fada cikin rawan murya.

Tace don haka nina baki umurni da haka  idan ya tambayeki dalili ki fada masa ninace ai hakan ki tashi ki van wuri Asaben ta mike da sauri zata tafi sai kuma ta dakarta da ita tana kare mata wani mugun kallo tace.

Wai yaushe har kika samu daman yin magana da mijina haka ban sani a gidan nan wani iri Asaben taji sai ta daburce lokaci guda kafin tace da sauri a,a hjy jiyane da ina tsaka da aikin yamma ya shigo kitchen ya fada min.

Wani kallon banza ta bita dashi kafin ta kawar da kanta gefe ta fita batun ta ta dan dade a duke kafin ta mike da sauri ta bar dakin tana watsa mata zagi a zuciya da fadin macuciya karyan ki dai ya kare tunda kishiya ta shigo gida  nan da sunan zama.

Har takai kitchen din tana tunanen yadda zata bullowa zancen Allah da ikonshi taji muryan maigidan waje yana magana yan aikin gidan maza.

Nan ta dauraye hannu ta sameshi ta rusunna daga bayan shi tana gaidashi kafin tace dama Alh hjy ce dai ta kirani dazun nan ta ban umurnin dana daina girki da hjy karama da duk wani aikin daya danganta da  ita a gidan nan.

Ya juya gareta a cikin mamaki sai daga bayan shi kuma yaji mazan na fadin muma dai Alh munsan hakane zai cika damu gun hjyn .

Don yana da wuya ta barmu muyu wani aiki daya shafi hjyn a gidan nan din ko baki akayi mukai masu wani abu zata zagemu tace zamu bar aiki balle wanan da take ganin kishiya a gareta yanzu.

Innalillahi ya ambata kafin yace duk ku saurareni cikin tsawa shin hjy ce ke biyan ku koni to ku sani daku da ita duk a karkashina kuke har wana  din datazo daga baya.

Don haka kowan ku ya tsaya iya matsayin aikin da aka daukeshi a gidan nan wanda bai iya bin umurnina sai nata ya fada min tun yanzu na sallameshi.

Kafin ya bisu da kallo daya bayan daya can kuma ya numfasa tare da fadin bayan hakan tunda aiki ya karu yanzu zanyi doubling din kudin kowa a cikin ku ga wata kai driver mai kai yara school.

Zan kara ma kudin ka ya cike dubu hamsin haka mai wanki daba shuka ruwa kaima kudin ka a yanzu zakai arba,in da wani abu sama ke kuma ga wata nan zakuyi aiki tare zan baku a wata dubu arbain da biyar duk wata maigadi kuma dubu arba in.

Kallon juna sukeyi kafin Bala driver yace Alh ai dama ni sha biyar ake bani duk wata yace what yace kwarai kuwa Alh ga yan uwana nan ka tambayesu kaji maigadi yace goma ko takwas ake bani ba da abinci ba hakama mai wanki da guga.

Wani jiri ne yaji ya dabeshi lokaci daya ya dafa motan shi saida driver shi ya karaso yana fadin Alh abi a sannu sun sha min wanan korafin lokaci lokaci ina basu hakkuri.

Watau shi kadine ake ba kudin shi daidai ke nan a cikkn su shima don kudin basa yana fitowa daga company sune yasa haka da wurintane zata gunce ta basa rabi ke nan ?

Wai me hjy ta dauki daukan alhakine a rayuwan ta ya tambayi kansa lokaci guda kafin ya juya zai shiga mota da sauri driver yazo ya bude masa saida ya zauna ya dago kai ya kallesu yace.

Daga yanzun nan biyan kudin ku zai dawo hannun hassan gashi kowa ya koma bakin aikinsa suka amsa suna godiya suka koma shi kuma suka fita da driver shi.

Duk abinda ke faruwa a gaban idon hjy Yabi dake tsaye a window dakinta tana kallo saidai abinda ta kasa fahinta shin Alh ne ya tara dukka yan aikin har Asabe mai aiki ko kuwa dai Asaben ne ta kai karanta ya kirasu.

Ganin ya fita yasa ta sauko kasa gagauce tana kwalawa asaben kira lokaci guda gabanta ya fadin jin irin kiran da hjy din ke mata a lokacin Asabe uban me kukeyi waje da Alh dukkan ku ?

Hjy shine ya kiramu yana kara muna kashedin aiki a gidan nan shine kika ganmu akan me tace akan dai zuwan hjy karamane dai ya kiramu din yana bamu umurni.

Ashe ko duk zaku bar gidan nan kuwa duk wanda ya ketare dokan dana saka mashi albashin ne hakan ta barta tsungune ta fice daga falon can ma amsa daya ta samu nan ma din tayi masu bara zanan irin wanda taiwa Asabe din a cikin gida.

Shigewan ta maigadi ya kalli mai wanki yace rabu da idan duniya taso basheka haka kake komawa kamar tababe a cikkn mutane mu ai gaba zuwan matan nan ya kaimu don zuwanta ya zama muna alheri a gidan nan yanzu.

Daki ta koma tana daka hannayenta a wuri daya babu abinda take fadi sai watau akwai dan karamin yaki gabanta kwanan nan ita da Alh a gidan na  ke nan kan zuwan wanan kuchakar yar kauyen matar nasa.

Har yaushe murja ta zama mace a wurin sa da har yake wanan rawan kafan akanta yanzu indai hakane ya zama dole itama ta nuna mata cewa bata kaiba kuma bata isa ba don ita bakuwace a wanan harkan.

Zata gwada mata gaba da gabanta ko a wanan harkan na bin bokaye da malamai don meke ga murja da har zata kai masu.

Mamaki da tunane ya hannashi magana ba abinda yake tunane a lokacin sai yadda yai sakaci haka a rayuwanshi har yabi ta shige mashi gaban komai na rayuwan shi daya kamata ace shi namiji shine ke kula da duk wanan abin a gidan sa wayan shi ya dauki kara ya dauko ya duba dansa yasir ke kiranshi a lokacin.

Cikin ajiyan zuciya ya dauki wayan tare da fadin salamu Alaikum sai dan ya amsa da hey dad ya kuke ya yanayi bakaji sallaman danayi ma bane ka amsa min da wanan kallaman uban ya fada rai bace.

Meye a cikin haka kuma dad dama na kiraka ne na tambayeka ko mum ta fadama ina bukatan kudi banji an aiko min dashi ba ya fada a kasalance irin na sagartatun diya.

Bata fada min ba kota fadama yanzu ba zan turo maka da komai ba sai wata ya cika don yau sati biyu ke nan dana saka ma kudi ga accoun din ka.

Why dad kafa san kudi shine rayuwa zan zauna ba kudine a hannuna cikin hasala uban yace idan ban sako maka ba ka mutu can ya kashe wayan nasa yana tsuki tare da fadi a fili malam Sale nayi sakacin da a yanzu nake nadaman shi a rayuwana.

Alhaji hakan ba yin kanka bane duk aikin sihirine ga yadda alama ya nuna yanzu kamar ka kurto daga daurin boyen da akai makane a baya.

Don abin yana da mamaki yau kaine ke tsaye haka kan hjy wanda a baya a gaban kowa kana iya bata hakkuri kan abinda bai taka kara ya karya ba saidai na tare dakai yaji haushin haka.

Wanan gaskiyane nima a yanzu ina wanan tunanen da ada bai taba kawo min ba a zuciyana sai yanzun nake dan gane kuskurena.

Sayayya sukayo kashe rika a wani sabon store dake kusa dasu a can magariba ya samesu don haka yana dawowa sallah ya fara gabatarwa kafin ya fito don yaci abinci karo na farko tun bayan kauracewa cin abincin gidan dayayi na yan makwani a gida.

Babu komai saman dinning din a lokacin hakan yasa daga inda yake tsaye cikin daga murya yake kiran Asabe mai aiki da karfi karo na farko da suka fara jin hakan gareshi don dauka suke baima san sunnanta ba duk zamanta a gidan.

Itama din a gigice ta fito daga kitchen inda take faman wanke kwanonin da tayi amfani dasu da yamma din tazo da sauri tana rusunnawa tare da fadin Alh gani.

Cikin daure fuska yake tambayan ta yau lafiya bai samu abincin shi a falon bane yadda ya saba sai tayi kasa da kai don rasa na fadi a lokacin ya kara maimaita tambayan nasa da fadin yau baki girka abincin dare bane a gidan.

Alh na girka hjy ce tasa na zubar wai ba wanda zaici yau a gidan ta bani umurni da hakan kuma kin zubar din sai tayi kasa da kai can ta dago tace Alh ka gafarceni na zubar amma ba duka ba saura na kitchen na aje.

Kina iya tafiya ya fada a sanyaye kafin ya juya nufi dakin shi ya kira malam sale driver a waya ya bashi umirnin a shigo masu da take awaye na tuwon shinkafa mai kya guda goma.

Motan farko na garin zaria ya bi zai sauka a maraban Funtuwa daga nan motan bata tsaya ko ina ba sai inda yace zai sauka din nan mota ya tsaya ya sauka.

Sunan unguwar ya fadi mai mashin din yace ya hau su tafi a hanyane yake tambayan mai mashin din ko yasan malam idi mai rafannai a unguwar ?

Yace kwarai kuwa duk garin nan waye bai san shi ba aiba bace yake ba da kayi mai inkiya da wanan sunan gidansa zakane muje can din ?

Yace eh bai tsaya ba sai kofan gidan kamar yadda ummah ta kwatatabta mashi gidan haka ya samu wurin daga kofa ya tsaya ya sallami mai mashin din.

Kafin ya tattaro natsuwa yasawa zuciyan shi ya samu yaro yace ai masa sallama da maigidan bakone daga gusau yace ace dashi bako daga wurin salamatu ko ?

Yace eh daga wurintane yake tafe akace ya shigo ya shiga daga zauren gidan ya sameshi zaune a zauren saman wani katon farin buzu na fatan rago ga tulin littatafai daga gefen shi sai goruna dake aje da ruwan rubutu wasu har kura ya hau kansu don dadewa a wurin.

Sallaman Ahmed din yasa shi dago kai tare da dan kura mai do har lokacin da ya kai zaune yana fadin barka da warhaka malam mun sameku lafiya ?

Alhamdullahi ya fada yana kawar da allon dake gabanshi lokacin yace zama tsakanin gusau zuwa nan ya koma kamar tafiya zuwa unguwa dazun da safe nan naga zuwanka nan gashi cikin hukuncin Allah har ka iso.

Eh malam ana fitowa daga sallah na nufo nan din don in samu in koma da wuri insha Allah dama ummah ce ta turoni nan wurin ka don matsalan , , , ,

Hannun daya daga mai yasa yayi shiru lokaci guda yana kalon malam din shi kuma kamar mai sauraren wani abu a lokacin zakace yana magana da wani ko yana sauren abinda ake fada mai a wayan kafin ya daga yace na,am ya kallo Ahmed din yace.

Kayi saurin gano matsalan matarka cikin lokaci don ta riga da ta firgice tun a cikin mafalkinta da tayi a ranan sai kuma aka samu wasu shedanu dake son bata tsakanin ku a gefe wanan yasa harta kai kwance.

Lamarin ai mai sauki ne don daga kai har ita akwai tsari na Allah a tare daku da ba yau ba wanan bakar matan dake bibiyan ku koda yake su biyu ne na gani da suncinwa manufarsu akan yarinyar nan.

Sakaci irin na salamatu yana ban mamaki da yaya aka samu suka sakar mata mahaifanta harta samu rabon diya a duniya don lamari da mai tsafi abune mai wuyan sha,ani tasani.

Yanzun dai ba dogon bincike zan baka wanan kaje yau din nan ku shaka mata zatayi barci sosai kada ku damu ita da kanta zata tashi har ta nemi abinci taci.

Don zasu koma gun wace tayi amfani da damanku ta turo maku abin saboda sakon bana yau bane sun dade suna son kafan da zasu shigeta basu samu ba don irin abubuwan dake kanta ba nawasa bane.

Abubuwan kanku kusan gudane kuma Allah ya gyara fararene ba masu cutarbane su shiya komai naku yake zuwa da sauki ko wani lokaci.

Ga alheri nan babba tafe ma da sunan ka zai amsa sosai za a sanka zakayi suna mai ma,ana nan gaba kadan insha Allahu amma akwai kakubali hakan a kanku.

Ka zama namiji sosai a wanan lokacin kada ka zama cikkn butulai yan adam masu manta halarci kaci gaba da rikon ammana duk yadda yazo maka.

Karbi nan wanan ya isa hakan kaje kuyi amfani dashi ku duka Allah ya tsare ya kare jeka kada rana yai maka ka koma zuwa garesu.

Malam na gode ya fada yana amsan dan goran daya miko mashi din yace ba komai kadai kula da abubuwan dana fada maka din zaifi.

Yaya kakar ka da akuyan ku tana nan dai kuna cigiyar mai ita ko ka hutar da zuciyar ka ba zaka taba ganin wanan dattijon ba don taimakon ka yayi ta wanan tsigar.

Kayi hakkuri da zancen mahaifin ka don duk abinda ya faru bayin kansa bane asirine mai karfi yake aiki a kansa tsawon lokacin nan amma ka godewa Allah don a sanadin ka komai ya karye a yanzu.

Zai nemoka da kansa da taimakon abokanan sa da sukai masa tsaye dakai ancinwa manufa yanzun sai dai sun koma zargin wace bataji bata gani ba kamar yadda abubuwa ke faruwa a gidan sarakan ka a yanzu da nan gaba zasu kokawa hakan.

Jeka a dunkule na baka bayani da sannu kanka zai hasaka ka gane inda zancena ka yanuf dan maganganun a yanzu suna dunkule yasa hannu a aljihu yana ciro kudin don ya bawa dattijon .

Ya ciro kudi  masu dan yawa yana kokarin bashi ya dakatar dashi da fadin ko kusa kai ai jikanane yanzu dole in maka nayiwa banza balle irin ku kadai kula da kanka ka hada kuma da hakkuri da duniya .

Allah ya aauke ka lafiya ka gaida min da ita salamatun kace ta dai dage da yawan addua kamar yadda ta saba da hakan duk da hakan sai da Ahmed din ya kasa wucewa bai basa komai ba sai ya zaro leda daga aljihun shi yace ta malam ga wanan gorone ka karba ya kalli ledan kafin ya mika hannu ya karbi ledan a hannunshi.

Sukai sallama ya mike ya fita bai tsaya ko ina ba sai inda zai samu mota nan ya juyo zuwa gusau zuciyar shi cike da tunanen sarkakiyar maganan tsohon da yai mai.

Leave a Reply

Back to top button