MECECE ƘARYA A MUSULUNCI KASHI NA FARKO
Aslm alaikum
Gabatarwa
Daga naku
musa s zage
MECECE KARYA❓PART ONE
KARYA wata abace damutane suke kirkirarta kamar abu ba ayiba sai mutum yakirkira yafada alhalin bama asason da maganar ba hakika duk wanda yake karya to tabbas duk tsananin gaskiyar sa ba ayarda dashi saboda baya fadar gaskiya sai KARYA.
Da farko dai karya ba kyau Allah ya hana yin Karya Kuma bayasan meyin karya acin alkur’ani me girma Allah ya kira masu Karya da faskan da dama a hadisai da dama Sun nuna irin azabar da Allah zaiwa me Karya a lahira amman Karya ta kasu kashi biyu.
Akwai karyan wacce zakayi Dan gyara akwai Kuma wacce zakayi gin kare kanka sai Kuma din batanci ga mutane Kuma duk Wanda yayi karya din batanci ga muta ne yanada laifi laifin shine gashi ya samu zunubin karya gashi ya samu zunubin bata wani ko wata Allah karemu.
Amma in kayi a kan gyara to balefi ba ne
Amma in kayi soboda San wani abun duniya ko batanci ga mutane kanada laifi saboda Allah yace karya babu kyau Kuma munsani sai mutake sanin.
Kuma Allah yayi alkawarin me Karya bazai. Shiga Aljannah ba har sai ya tuba ga Allah.
In kuwa bai tuba ba toh bazai taba jin kanshin Saba Allah karemu .
Sahabbai sun tambayi manzon Allah (S . A . w) shin me karya shaki zasu shiga Aljannah ya ce musu in suntuba zuwa ga Allah.
Dayake Allah maji rokan bayin sa ne da da kanima tuba gare shi sai ya yafema Allah ka yafe mana da isar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama.
Wasu yaran Kuma in kaji suna karya tun a gida suke koya saboda sungan yanda maman su takeyi ko babansu yakamata in yara su nan duk wani abun da zai bata musu tarbiya ko da kinayi hali haka in su nan ki daina sbd baki san in da zasu fada ba Allah bamu ikoh hk
Ata kaice dai abun da zance yan uwana karya babu kyau mugyara murin ga fadi gaskiya ko da kuwa baza a soba ka fada kai kafita .
*NAUOIN QARYA*
1- YIMA ALLAH QARYA
Shine ka kirkiri wani abu Wanda baka da ilimi akai kace Allah ne ya fada, wannan itace qarya mafi muni kuma mafi hadari, Kuma masu yin haka Allah ya siffantasu da azzalumai, kamar yandda Allah ya fada acikin alqur, ani.
*suratul _Aaraf* Aya ta 37
👇🏽
ﻓَﻤَﻦْ ﺃَﻇْﻠَﻢُ ﻣِﻤَّﻦِ
ﭐﻓْﺘَﺮَﻯٰ ﻋَﻠَﻰ ﭐﻟﻠَّﻪِ ﻛَﺬِﺑًﺎ ﺃَﻭْ ﻛَﺬَّﺏَ ﺑِـَٔﺎﻳَٰﺘِﻪِۦٓ
*Ma, ana*
*Wanene yafi zalunci akan Wanda ya qirqiri qarya ya jingina ta ga Allah, ko kuma ya qaryata ayoyin Allah*
Wannan Aya 👆🏽tana nuna mana hadarin yima Allah qarya, ko ka kirqiri abinda baka da masaniya akai kace Allah ne ya fada.
2- YIMA MANZON ALLAH QARYA
Wannan itama nauin qaryace mafi hadari ka kirkiri qarya ka jingina ta ga manzon Allah (S. A. W).
Akwai HADISI ingantacce Daga manzon Allah S. A. W yace 👇🏽
ﺇﻥ ﻛﺬﺑﺎ
ﻋﻠﻲَّ ﻟﻴﺲ ﻛﻜﺬﺏ ﻋﻠﻰ ﺃﺣﺪ، ﻣﻦ ﻛﺬﺏ ﻋﻠﻲ ﻣﺘﻌﻤﺪﺍ ﻓﻠﻴﺘﺒﻮﺃ
ﻣﻘﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ) ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، ﻭﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
*Lallai yi min qarya ba kamar yima wani qarya bane, duk Wanda ya min qarya da gangan to ya tanadar ma kansa wajan zama a jahannama*
Wannan hadisin yana nuna mana Lalle yima manzon Allah (S. A. W) qarya abune mafi tsananin muni mafi siffa gawanda ya aika ta kuma yana daya Daga cikin manyan zunubai ,
Allah ya tsare mu.
3 -YIMA MUTANE QARYA
Wannan itace qarya mafi saukin hadari saide itama tana cikin manyan zunubai, kuma itama haramun ce.
Anan zamu diga aya cikin wannan topic namu mai albarka, domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan website mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu,
Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.
Allah ya sa mun dace duniya da lahira
gaskiya dai dayace da ka kin bin ta sai bata.
Daga naku musa s Zage