Hausa NovelsMusabbabi Book 2

Musabbabi Book 2 Page 6

Sponsored Links

MUSABBABI BOOK 2

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere)

Page 6

Tambayar ta zo ma Haj Rakiya a bazata, hakan yasa ba ta tanadi amsar da zata ba ta ba, cikin kame kamen magana tace “ wa ko nake kaima idan ba shi ba, domin sanda nake zuwa ba a haka na tadda shi ba, ina ganin cikin ɗan lokacin da ban je ba ne ya koma haka”, Haj kilishi ta watsa mata harara tace “ jiya ko shekaranjiya ya koma haka domin dai na ga ko kwanaki uku da suka wuce na baki kuɗi kin kai masa akan musaddiƙ da Afrah”, shurun da tayi yasa Haj kilishi ƙara gasgata abinda take zargi, ta gyara zamanta daƙer tana cigaba da yi mata wani irin kallo.
Cikin rawar hannu Afrah ta fito da wayarta daga cikin jaka ta maidata silent sannan ta buɗe camera ta ɗora akan su Haj kilishi, daga inda take tana iya ɗaukar komai.
Haj kilishi tace “ Tabbas Haj Rakiya akwai lauje cikin naɗi, duk irin kuɗaɗen da kike amsa a hannuna ke ce ke amfana da su, na ji a jikina tunda na daina zuwa wajen boka da kaina na ɗoraki akan harkar kike cinye duk kuɗin da na ke baki”, Haj Rakiya ta ɓata fuska tace “ Au zargina ki ke yi?”, ta gyaɗa kai tace “ ƙwarai kuwa ina zarginki, domin duk rashin gaskiya ya gama bayyana a fuskarki, sannan sam bana jin shauƙin da nake ji na yarda da ke a cikin zuciyata”. Haj Rakiya ta fahimci dai tuni Haj kilishi ta gama ganota, ta tabbatar babu wani sauran kwana kwana da zata yi mata, don haka ji tayi ba zata iya cigaba da ɗaukar maganganun da Haj kilishi ke soka mata ba, don haka ta ƙara haɗe rai cikin fusata tace “ To ba sai kiyi ta zargin nawa ba, ko an gaya miki ni baiwarki ce, da iya rana iya ruwa zaki kirani ki sani bautarki, na ci kuɗin na ki idan kina da hujja ai sai ki kai ni ƙara”, cikin mugun mamaki Haj kilishi ta fiddo ido waje tace “ lalle tsintacciyar mage bata mage, har kece ki ke iya gaya min wannan maganar, bayan kuɗina da kika ci bayan kinyi min zamba cikin aminci”, Haj Rakiya ta saki tsaki tace “ ke har za kiyi maganar zamba cikin aminci, bayan babu wanda ya kaiki yin zamba cikin amincin, ko kin manta zambar da ki kayi ma musaddiƙ ki ka haɗa hannu da yar’uwarki kuka raba shi da dukiyarsa, ko kin manta zambar da ki kayi masa ki ka haɗa aurensa da Hannatu ta hanyar malamai, ko ko kin manta zambar da ki ka yi masa ta raba shi da kyakkyawan halinsa ki ka haɗa shi da shaye shaye, ko kin manta zambar da ki kayi ma Afrah na son rabata da musaddiƙ, ke har kina da bakin magana”.
Gaban Afrah ya cigaba da faɗuwa, hannunta ya cigaba da rawa kamar wayar hannunta zata faɗi, a yayinda Haj kilishi ta yi matuƙar harzuƙa tace “ Duk abinda ki ka lissafa a shawarar wa aka yi, ai ke ki ka ba da shawara, mara mutunci kinibabbiya, barauniya” Haj Rakiya ta miƙe tace “ Ga ki nan babbar ɓarauniya ko kin manta kuɗin musaddiƙ da ki ka sace, ke ni fa na dawo daga rakiyar ki, kuma ki sani tun daga kan Tsiduhu zuwa duk wasu bokaye da na haɗaki da su duk ƙarya ne, kuɗin da ki ke bani ni na ke hidimata da su, don na fita daga cikin sabgarki,”.
A zafafe tace “ Allah ya isa tsakanina da ke, yau da ina da lafiyar ƙafafu da ƙarfin jiki da sai na yi miki dukan tsiya yadda duk kuɗin da kika damfare ni zasu ƙare a wajen neman lafiyarki don saina karairayaki, na tsaneki yar aiken shaiɗan”, Haj Rakiya ta yi shewa ta tafa hannu tace “ Idan ni yar rakiyar shaiɗan ce to ke shaiɗan ɗince, kuma ko lafiyarki ƙalau ya za kiyi da ni, ai sai dai mu buga, Allah ya isan ki kuma ta banza ke Allah ya isa nawa ce a kan ki, ta riga ta ƙare miki amma kin kasa hankalta, halin da mai rakwacam ya ke ciki irinsa zaki shiga idan baki tuba ba, wannan ciwon na ki duk sakayya ce daga Allah, ni dai na cire hannuna, kuɗi kuma na ci asalima har gida na saya, ki haƙura kawai ki kyale musaddiƙ da matarsa domin sun fi ƙarfinki ki sani kadarinki ya karye”.
Wani irin zafi zuciyar Haj kilishi ta ke yi yau ta yi mamakin da bata taɓa yin irinsa ba, Haj Rakiya ta ci amanarta. Ido jajir ta dubeta tace “ ki je duk abinda ki ka ci min ban yafe miki ba”, ta miƙe tana harare harare ta tsaya a gabanta tace “ kada Allah yasa ki yafe, kema ai na Allah ya isan ne, kuma ka da ki manta da asirin da muka binne a ƙasan kuka wanda yasa musaddiƙ shaye shaye, ina son kisa a ranki cikin ko wane lokaci ina iya zuwa na tone ko don na kawo karshen zaluncin da kike yi ma musaddiƙ”, tana gama faɗin haka ta buga tsaki ta juya zata fita, dai dai lokacin Afrah ta yi gaggawar ɓoyewa ta bayan falon, hakan yasa har Haj Rakiya ta fice daga gidan cike da fusata ba ta ga Afrah ba.
Kamar yadda tabar Haj kilishi cikin tsananin tashin hankali da alhini gami da damuwa, yau komai ya kwakkwafe tsoro ya ƙara kamata data tuna furucin Haj Rakiya agame da abinda suka binne a ƙasan kuka, ita kanta tana jin wani abu mai kama da nadama sai dai tana jin tsoron a tono asirin don rashin sanin abinda zai iya biyo bayan tonewar wanda batq sani ba. Gabanta ya ƙara faɗuwa babu yarda tsakaninta da Haj Rakiya don haka tasan zata iya tonewa ko don taga bayanta, wannan wace irin masifa ce, hawaye masu zafi suka shiga sauka mata, ta faɗa cikin wani irin mugun yanayi, tuni ƙirjinta ya ɗauki zafi kamar ana soya shi da wuta, damuwa mai tsanani da nadama ta ƙara rufeta, halinda mai Rakwacam yake ciki ya taimaka wajen sanya nadama a tare da ita, ita kanta tana jin zata iya tone sihirin da ta yi ma musaddiƙ amma tsoro take ji matuƙa bata san me zai faru da ita ba, hakan yasa saboda tsabar son kai ta gwammace asirin ya cigaba da zama a inda yake, wanda hakan na nufin musaddiƙ ya ƙare rayuwarsa bai zama cikakken mutum ba.
To amma ya zata yi da Haj Rakiya, ya zata yi ta rufe bakinta daga tona mata asiri?, lalle tana cikin tsaka mai wuya.

A sukwane cikin tsumar jiki Afrah ta fito daga inda ta ɓoye bata saurari komai ba ta yi waje, ganinta a kiɗime yasa Baba maigadi tasowa ya tareta, a gaggauce yace “ Afrah ya ya lafiya kuwa? Ko jikin Haj ne, gama naga itama Haj Rakiya ta fito a kiɗime”, Afrah ta girgiza kai tana ƙoƙarin share hawayen da ta kasa riƙewa, tace “ Baba ina cikin ruɗani ƙwarai da gaske, akwai damuwa”, ya ƙara matsowa kusa da ita, duk da baisan matsalar ba shi ma sai ya ji damuwa sosai, yace “ki gaya min menene?”, ta ɗaga kai tana kallon saman ɗakin Haj kilishi sannan a hankali tace “ mu je”, da sauri ya bita cikin ɓangarenta.
Har cikin falonta suka shiga, har zuwa lokacin kuma a kiɗime take , haƙurin Baba maigadi fa ya fara gazawa ya dubeta a ƙagauce yace “ ki gaya min menene ke faruwa”,
Afrah ta gpge hawayenta sannan sannu a hankali ta sanar da shi komai tana hawaye ta ƙara da cewa “ Batun yau na ke zargin Haj ba akan duk abinda ke faruwa da yaya musaddiƙ, sai dai rashin shaida yasa ban tada maganar ba, amma yau komai ya fito, yanzu Baba ashe har akwai ƙeƙasasshiyar zuciyar da zata iya cutar da mutumin da baiyi mata komai ba, meye laifin yaya musaddiƙ don ya fito a matsayin ɗan kishiya, wace irin al’umma mu ke ciki ne da son kai da son zuciya ya yi mana yawa, wannan wane irin zalunci ne”.
Hankalin Baba maigadi ya ƙara dugunzuma ya sauke ajiyar zuciya yace “ Duk abinda akace Haj zata yi to zata iya, don na rayu da ita a gidan nan tun kafin a haifi musaddiƙ nasan wacece ita nasan irin mugun zaman da tayi da mahaifiyar musaddiƙ, don haka ƙiyayyar musaddiƙ ya zama tamkar wani ɓangare ne na rayuwarta, don haka ko kaɗan banyi mamakin jin hakan ba, kawai dai ina mamakin yadda duk da tsanar da ta yi masa amma babu wanda ya taɓa jefa mata zargin sa hannunta a cikin lalacewar nagartaccen mutum irin musaddiƙ”.
Kuka Afrah take sosai, tausayin mijinta ta ke ji, Baba maigadi yace “ ki yi haƙuri in sha Allah komai ya zo ƙarshe, ki natsu ki tashi ki tafi gida ki sami mahaifinki ki sanar da shi komai”.
Dama abinda take tunani kenan, don haka Baba maigadi yana fita ta tashi ta wanke fuskarta ta gyara kanta.
Sannan ta ɗakko waya ta kira musaddiƙ bugu ɗaya ya ɗauka, yana tambayarta lafiyarta da makaranta, ta yi ɗan murmushi tace “ komai lafiya yaya, ina son ka yi min izinin zuwa gidan mu ne”, yace “ Bakomai Allah ya tsare hanya”, sai bayan da suka aje wayar ne sannan musaddik ya tsinci alamun damuwa a cikin muryarta, sai dai bai ƙarfafa hakan ba.
Cikin sauri da zafin rai Afrah ta nufi gidansu, cike da tsana da ƙyamatar Haj kilishi, tun kafin ta isa gidan ta kira mallam mahmud domin tabbatar da yana gida, ya yi shirin fita amma wayar Afrah ya dakatar da shi daga fitan, duk da daga Mama Hauwan har Na’ima basa san ota mama Hauwa ta tafi dubiya cikin unguwa, ita kuma Na’ima ta tafi gyaran gashi.
Hakanan ya ji ya ƙosa Afrah ta ƙaraso domin ya fahimci damuwa a cikin maganarta, musamman yadda ta ƙara kiransa ta sanar da shi ya kira Inna Halima zuwa nan gidan nasa, ananne ya kasa jurewa yace “ Afrah wai lafiya kuwa”, tace “ Baba ka dai kirata sannan kayi haƙurin jin komai har na ƙaraso”.
Bai ja maganar ba, yana kashe wayar ya kira Inna Halima ya tabbatar mata ta nemi izinin maigidanta ta taho gidansa yanzu, itama ta so sanin dalilin kiranta amma bai tsaya yi mata wani bayani ba ya dai gaya mata ta taho yanzu.
A waya ta kira maigidanta ta nemi izini sannan ta taho, tayi sa’a yaronta Abdullahi tsayawarsa kenan da mashin ɗinsa a ƙofar gidan ya zo gaisheta, babu ɓata lokaci ta haye mashin ɗin tace ya kaita gidan kawunsa mahmud.

Abdullahi bai shiga gidan ba saboda wani uzuri yana ajeta ya juya.
Inna Halima ta tadda Mallam mahmud da Afrah zaune a kan tabarma a ƙofar ɗaki jugum jugum fuskar Afrah sharkaf da hawaye, mallam mahmud kuwa tagumi ya zuba hannu biyu. Cike da firgita ta ƙaraso tana maimaita tambayar da tun da ta shigo gidan take yinta, “ Meya faru?”.
Mallam Mahmud ya zame tagumin da ya yi yana kallonta yace “Halima yau dai gaskiya ta bayyana, dama ance kwanaki casa’in da tara na ɓarawo kwana ɗaya tak na me kaya”, ta ƙara shiga wasi wasi, tace “ yaya bangane maganar ka ba”, mallam Mahmud ya dubi Afrah yace “ kiyi shuru, ki sa ma Halima video ta gani”. Afrah ta buɗe wayarta ta fito da vedio itama ta sa mata kamar yadda ta sa ma mallam mahmud.Tun Inna Halima na tsugune sai ga ta ta yi zaman dirshan tana share zufar da ke keto mata ko ta ko’ina.
“ Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, amma kilishi ta gama da asara, Afrah sannu da ƙoƙari lalle yau kin samo shaidar da zata gamsar da kowa, da kuma wannan shaidar babu inda ba zamu je ba domin ƙwatoma musaddiƙ haƙƙinsa”, mallam Mahmud ya jinjina kai yace “ kwarai kuwa Halima, duk yadda za’ayi ya zama dole kilishi ta tone asirin da ta yi ma marayan Allah, ni na rasa abinda ma zance tun da na ga wannan vedio na rasa a duniyar da na ke”, cikin kuka Afrah tace “ wannan wane irin mugunta ne, wane irin zalunci ne”, Inna Halima ta janyota ta rungume tana faɗin “ komai ya zo ƙarshe da ikon Allah”.

Nan da nan suka fara shawarar yadda zasu ɓullowa lamarin, Sai dai shawarar da mallam Mahmud ya ba da duk ita suka bi, wato ba zasu tunkari Haj kilishi kai tsaye ba har sai sun fara danganawa da ofishin jami’an tsaro, dalilin hakan yasa Afrah ta kira Murtala ta sanar da shi komai da kuma taimakonsa da take nema na shige musu gaba wajen shigar da matsalar wajen yansanda. Duk inda hankalin Murtala yake sai da ya tashi, tabbas shi ma batun yau yake tunanin akwai sa hannu a cikin lamarin musaddiƙ ba sai dai bai taɓa kawowa a ransa Haj kilishi ke da hannu a faruwar komai ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci Murtala ya iso gidan Mallam Mahmud, haka zalika babu ɓata lokaci suka ɗunguma zuwa police station ɗin gangare inda murtala yake da tabbacin zai sami taimako, kasancewar akwai ƙaninsa a wajen da bai daɗe da fara aiki ba.
Shi yasa babu wani ɓata lokaci aka karɓi ƙararsu haka zalika aka haɗasu da motar yansanda domin zuwa a kamo Haj Kilishi da Haj Rakiya, saboda case ɗin criminal case ne.

Tun komawar Haj Rakiya gida take ƙoƙarin kiran wayar Dillali Babaye amma wayarsa tana kashe, hakanan ta fara jin wata irin damuwa a zuciyarta, anya bata zura jiki da yawa ba kuwa, bata ba Babaye yarda da yawa ba kuwa? Idan ta tuna da yawan kuɗinta da ke hannunsa sai ta ji gabanta na faɗuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, haka ta ƙara figar gyale ta tafi neman babaye a gidansa, da ta saba zuwa akan maganar sayen gidan. Cikin sanyun jiki take tafiya ko kaɗan babu ƙarfi a jikinta.
Tun bayan tafiyar Haj Rakiya, ciwon Haj kilishi ya tashi sosai, ga wani irin mugun zazzaɓi da ya yi awon gaba da ita, bata jin daɗin komai a rayuwarta, hatta bakinta ba ya yi mata daɗi, ɗaci yake mata, ga babu kowa a gida don masu aikinta ɗaya bata da lafiya ɗaya kuma jiya ta fara jinyar mahaifiyarta, tunda ta fara jin jikin nata haka kuma take ta ƙoƙarin kiran Hassana amma ta rasa dalilin da yasa wayarta ke kashe. Tana cikin wannan yanayin ne, Baba maigadi ya shigo fuska a tamke tsanarta ce shimfiɗe akan fuskarsa, ya sanar da ita yansanda sun zo suna son ganinta, ta yunƙura a daburce tace “ yan sanda kuma” , ya jinjina kai yace “ Eh suna waje”. Wani tunani ne ya faɗo a ranta, ta dubi Baba maigadi da yake shirin fita tace , “ Yaushe rabon musaddiƙ da gida?”, ya yi mata wani sakaran kallo yace “ Tun safe da ya tafi wajen aikinsa”, ta ɗan yi ajiyar zuciya sannan tace “ To Allah yasa ba shi ba ne ya tattago wani aikin”,
Ba tare da ya tanka ba ya juya ya yi ficewarsa, a ransa yana faɗin, yau ba musaddiƙ ba ne ke ce ki ka ɗakkoma kan ki masifa”.
Haka ta rarrafa ta tashi ta janyo gyale ta rufe jikinta, daƙer take dafa bango take ɗaga ƙafarta har zuwa bakin get ɗin gidan.
Tun daga nesa ta yi turus, tsoro ya fito ƙarara a cikin idanunta, a sanadiyyar ganin Mallam Mahmud da Inna Halima, Afrah da kuma abokin musaddiƙ Murtala, shin meke faruwa ne?, sai dai nan da nan ta kori tsoron nata, ta kuma ƙara ƙarfafama kanta guiwar cewa lalle musaddiƙ ne ya ɗakko wata fitinar, don idan ba haka ba me zai kawo su mallam Mahmud gidanta da yansanda.
Tana ƙarasawa ta dubi yansandan ta kuma dubi su mallam Mahmud tace “ lafiya me ke faruwa kuma”.
Gaba ɗayan su kallonta su kayi suka watsar, musamman Inna Halima da take jin tamkar ta janyota ta matse.
Ɗaya daga cikin yansandan mace ta yo kanta cikin fusata tace “ muna gayyatarki zuwa ofishin mu, domin amsa wasu tambayoyi, ki na da damar da zaki rufe bakinki da ga nan har zuwa lokacin da zamu isa police station”.
Nan da nan tsoro da firgicinta ya dawo sabo jikinta ya shiga tsuma, ɗaya ɗansandan ya daka mata tsawa yace “ ki wuce mu tafi”, ta ƙara daburcewa tace “ Babu kowa a cikin gidan, zan je na kulle gidan”, ya girgiza kai yace “ A’a ga maigadunki nan, zai iya kula da komai, tunda dama aikinsa ne, wuce mu tafi kawai”. Haj kilishi ta dubi maigadin tace “ Ka kula da gidan”, bai amsa ba illa kai da ya juyar gefe, ta ƙara kallon su Mallam mahmud da babu alamar sassauci a tare da su, haka ta wuce su ka tafi ba tare da magana ta haɗa ta da su Inna Halima ba.

Hankalinta bai ƙara tashi ba, ta kuma fara tunanin shin ko asirinta ya tonu ne a wajensu mallam Mahmud, sai da yansandan su ka buƙaci ta yi musu jagora zuwa gidan aminiyarta Haj Rakiya. Haka ta nuna musu hanya har zuwa gidan na ta. Wanda dawowarta kenan daga gidan Babaye cikin tashin hankali domin bata tadda shi ba asalima a kulle gidan ya ke. Yar sanda mace ce ta shiga cikin gidan na ta, ta fito da ita cikin gigita, ganin su Afrah kuma da Haj kilishi ya ƙara dagula dukkan lissafinta, babu abinda ya zo ranta face asirinsu ya tonu, to amma ta ya ya asirin na su ya tonu?.
Wani irin mugun kallo su ke sakar ma da junansu tsakanin Haj kilishi da Haj Rakiya, domin yanzu Haj kilishi Haj Rakiya ta ke zargi a bisa duk abinda ke faruwa. Tana tunanin itace ta tona asirinta. Haka dai suka kasance cikin ɗimbin tashin hankali da saƙe saƙe, har zuwa lokacin da suka isa police station ɗin, wanda kafin komai cikin cell aka watsa su kafin a buƙace su………..

Yar gidan Imam✍️

Leave a Reply

Back to top button