Musabbabi Book 2 Page 9
MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu Mayere )
Page 9
Kofur Lawal ya na ƙoƙarin buɗe cell ɗin Haj Rakiya na ƙara sakin wani irin ihu, taga mutuwa ƙiri ƙiri duk idanunta sun firfito, ko da ya buɗe cell ɗin daƙer suka ɓamɓare hannun Haj kilishi a wuyan Haj Rakiya, aka fito da Haj Rakiya da sauri suka ƙara kulle Haj Kilishi.
Haj Rakiya na nurfarfashi tana ƙara jaddada musu cewa Haj kilishi fa ta haukace, ɗaya cell ɗin me mutane da yawa aka maida Haj Rakiya.
Insifekta da kofur Lawal da sauran yansanda haka suka tsaya cike da kaɗuwa suna tunanin yadda za suyi da Haj kilishi wacce ta cigaba da buge buge da sambatun maganganu wanda abin takaici duk irin mugun abun da ta yi ne take ta faɗa, kai Allah ka rufa mana asiri duniya da lahira, duk wanda ke cikin cell ɗin Allah wadai yake yi da halin Haj kilishi. Haka zalika babu wanda ya yi mamakin halub da ta tsinci kanta a ciki domin dai hauka itace ta dace da ita.
Duk sunyi jungum jugum suna tunanin yadda zasu karɓi wayar hannunta domin kiran yan’uwanta burinsu ɗaya ko babu kuɗin beli su zo su ɗauke musu Haj kilishi a police station. Kofur lawal ne ya koma wajen Haj Rakiya yana tambayarta ko tana da nambar wanin Haj kilishi da zasu kira, har zuwa lokacin Haj Rakiya ba ta dawo dai dai ba, ta dai gaya musu su jira ta riga ta kira yarta tasan tana hanyar zuwa.
Ba a ɗauki wani dogon lokaci ba bayan hakan, Hassana ta iso police station a cikin motarta, ta tadda tashin hankalin da ya fi wanda take ciki, dama ƙarya ta yi ma maigidanta ta taho, ta ce masa jikin Haj kilishi ne ya tashi shi yasa zata je gida cikin daren, to yanzu kuma ta zo ta tadda Haj kilishi cikin mugun hali na hauka tuburan, domin dai daƙer da taimakon sauran yansanda aka samu aka sanya Haj kilishi a cikin mota Hassanar ta ja motar cike da tsoro da fargaba. Har ta kai gida idanunta ba su tsagaita wajen fitar da hawaye ba, a gidan ma sai da taimakon baba maigadi aka samu aka shiga da ita cikin gidan, haka zalika baba maigadinnne ya bada shawarar a ɗaureta kafin gari ya waye asan abin yi da ita. Shi da kansa ya ɗaureta, sannan su ka yi zaman jugum a falon ko wannen su ya kafeta da idanu Hassana na kuka shi kuwa tunanin duniya ne ya cika zuciyarsa fal, lalle babu masifa irin ɗaukar hakkin wani, yau ku dubi yadda Haj kilishi ta koma mahaukaciya sai kace ba ita bace me izza da ji da kuɗi da take jin zata iya yin komai domin ta mallaki komai, yau ina ranar duk abinda ta tara, da ba za su iya yi mata amfanin komai ba. Duk yadda hankalin Hassana yake ya tashi ta rasa ta inda zata fara, ta san mahaufiyarta da son rai da son zuciya sai dai bata taɓa zaton zata iya lalata rayuwar musaddiƙ ba haka, duk da tasan bata ƙaunarsa, domin irin mugayen maganganun da Haj kilishi ke faɗa da bakinta na irin abinda ta aikatama musaddiƙ harda mahaifinsu, haka zalika tayi tayi ta hanata maganar amma hakan ya faskara, ga bacci ya ƙauracewa idanunta, haka Hassana tayi ta kuka har ta ba uku lada.
Baba Magadi ya cigaba da zama tare da su, domin ya na tsoron tashi yabar Hassana ita kaɗai da Haj kilishi, duk da dai tana ɗaure.
Ƙarfe ɗaya saura minti biyar na dare Afrah na zaune a tsakiyar gadon Inna Halima ta haɗe kai da guiwa, tunanin inda musaddiƙ ya shiga ya tsaya mata arai, tun tana kuka har hawayenta suka ƙafe, Inna Halima ta dafa kafaɗarta cike da tashin hankali tace, “ Afrah ki samu ki sami bacci ko ya ya ne, zuwa gobe ba zamu cigaba da rungume hannu ba, zamu nemi gidan Haj Hudah zamu je don sanin inda musaddiƙ ya ke”, ta saki ajiyar zuciya tace “ Inna bazan iya bacci ba ba tare da nasan halin da yaya musaddiƙ yake ciki ba”.Inna Halima tace “Haba Afrah, ki sassautama kanki wannan tunani da damuwar, in sha Allah babu abinda ya sami musaddiƙ”, Afrah ta yi saurin janyo waya ta kira Baba maigadi yana ɗauka kafin yace komai ta shiga tambayarsa ko Musaddiƙ ya dawo gida, yace “ Bai dawo ba Afrah, sai dai mu nan muna cikin tashin hankali”. Ta yi gaggawar cewa “ Me ya faru?”, sannu a hankali ya sanar da ita komai, fargaba da mamaki ya yi mugun kamata ta yi ƙasa da wayar, Inna Halima na tambayarta abinda ya faru, ita kuwa sunan Musaddiƙ kawai take ambata tunaninta ya ƙara tsananta akan halin da yake ciki, domin bata raba ɗaya biyu haukar Haj kilishi tana da nasaba da karyewar asirin, to idan hakane kuwa shi musaddiƙ ɗin me yake faruwa da shi a yanzu. Daƙer ta sami natsuwar gayama Inna Halima abinda yafaru da Haj kilishi.
Inna Halima itama ta firgita da jin hakan, wato yanzu tun a duniya Allah yake yin hisabi, ya Allah kasa mu gama lafiya, Allah yasa mu fi ƙarfin zuciyar mu ya ba mu ikon aikata alheri.Tun a wannan daren suka sanar da mallam Mahmud halin da Haj kilishi take ciki, yadda yace a wajen Allah su ke neman sakayya to ga shi nan Allah ya yi nasa sakayyar, duk da zafi da ƙiyayyar da yake ji na Haj kilishi bai hana shi yi mata addu’ar samun lafiya ba.
Haj Hudah tana gefen musaddiƙ har yanzu da agogo ya nuna ƙarfe biyu na dare bai dawo hayyacinsa ba, ta kasa tafiya ko’ina duk da akwai masu kula da marasa lafiya, ta ƙi tafiya ita kaɗaice ke zaune da shi. Ta ɗora kanta akan hannunsa wanda babu ƙarin ruwa tana jin ɗumin jikinsa, duk da ta ƙosa ya dawo hayyacinsa amma tana jin ina ma rayuwarta ta cigaba da kasancewa a haka tare da musaddiƙ. Lokaci ɗaya ta ji wani takaici ya rufeta alokacin da ta tuna musaddiƙ yana farfaɗowa to fa ya zama dole ta kira matarsa domin ta sanar da ita halin da mijinta yake ciki, ko a yanzu rashin sanin makullin sirrin da ya sa ma wayarsa ya hana mata kira duk da ba haka ranta ya ke so ba.
Sosai take ƙara jin ƙaunar musaddiƙ mai tsanani a cikin zuciyarta,
Tana jin tamkar ba zata iya cigaba da jure ɓoye soyayyarsa ba a cikin ranta.
Bacci ya fara kwasheta kenan wajen goshin asuba, kanta na kan hannunsa har zuwa lokacin, musaddiƙ ya saki wani dogon numfashi gami da yin salati wanda ya yi sanadiyyar farkawar Haj Hudah da sauri ta tashi tana cewa “ Alhamdulillah, musaddiƙ ka farka, sannu”, ya yi zumbur ya tashi ya zauna gami da zare oxcigine ɗin da ke fuskarsa ya na yi mata kallon mamaki ta ƙara matsowa kusa da shi sosai, irin kallon da yake mata yasa ta ji tana da buƙatar sanar da shi abinda ya faru da shi. Hakan yasa sannu a hankali ta warware masa dalilin kawo shi asibitin, da sauri ya shiga waige waigen neman wayarsa, ta tura hannu cikin jakarta ta fito da wayar ta miƙa masa.
A gaggauce ya kunna bayan ta kunnu ya ya cire makullan sirrin wayarsa, Afrah kawai yake ƙoƙarin kira, amma kafin ya sami damar kiran ,sakonnin Afrah ne ke ta kokawar shigowa cikin wayar tasa, hannu kawai Haj Hudah ta harɗe tana kallon yadda bai damu da halin da yake ciki ba fiye da kiran Afrah, bata ji zafi a ranta ba, har sai da ta ji yadda musaddiƙ da Afrah ke faɗama juna kalamai masu ratsa zuciya, tana jin yadda Afrah ke rusar kuka a waya tana faɗin zata taho Abuja.
Sun ɗauki tsawon lokaci a waya kafin su iya aje wayar, kawai Haj Hudah ji tayi hawaye na neman ɓalle mata saboda tsabar kishi, kishin da bata taɓa jin irinsa ba ko da akan mijinta ne.
Ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta iya cewa uffan ba.
Mallam Mahmud Inna Halima ta fara gayama halin da musaddiƙ yake ciki, tare da gaya masa idan gari ya ƙara haske zasu tafi Abujan domin ganin halin da yake ciki. Hakan yasa tun bayan idar da sallar asubah, mallam mahmud ya yi ma Liman bayanin halin da Musaddiƙ yake ciki. Mallam Liman ya nuna masa kada ya damu, domin ga dukkan alamu , aman da ya yi aman irin abubuwan shaye- shayen da ya yi ne, aman kuma shaida ne, na cewa Musaddiƙ ya dawo cikin nutsuwarsa, ya dawo mutum kamar yadda ya ke da, haka zalika duk wani sihiri da ke jikinsa ya karye. Amma duk da haka Liman ya yi rubutu, an wanke an ɗura a cikin roba, ya kuma tabbatar ma Mallam Mahmud da sun je wajen musaddiƙ ɗin ya ba shi rubutun ya sha, ya kuma shafe jikinsa, Mallam Mahmud ya amsa cike da godiya me yawa.
Murtala Afrah ta kira ta sanar da shi halin da musaddiƙ ya ke ciki a Abuja, Murtala ya tabbatar mata da cewa zai taho yanzu su tafi Abujan.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa Murtala ya iso, ya kwashi Afrah da Inna Halima sannan suka wuce su ka ɗauki Mallam Mahmud suka yi ma Abuja tsinke. Suka bar Mama Hauwa cikin damuwa da daburcewa, danasaninta ya ƙara yawa, tabbas Afrah ta yi dacen miji matuƙar ya dawo musaddiƙ ɗinsa na da, shin ina Na’ima zata sami miji kamarsa, ji take ta kasa samun natsuwa.
Musaddiƙ jinsa yake kamar wata sabuwar halitta ji yake kamar wanda ya farka da ga bacci, ita kanta Haj Hudan wani irin kallo yake mata tamkar wanda bai yarda da ita ba. Har su Afrah su ka iso asibitin bai dawo dai dai ba. Afrah ta ga yadda nan da nan ya rame, tamkar ya daɗe yana jinya. Idanunta cika su kayi da hawaye, idon Musaddiƙ na kanta yana jin soyayyarta ta na ƙara cika zuciyarsa, ya kirata da hannunsa, ya nuna mata kusa da shi, alamar ta zauna, cikin hawaye ta wuce ta je ta zauna, ya ƙura mata idanu na tsawon lokaci, idanunsa babu komai a ciki face tsananin ƙaunarta, “ sannu yaya Musaddiƙ” ta ƙarasa magana ta na goge hawaye, ya girgiza kai ba don idanun su Inna Halima ba tabbas da ya rungume Afrah a ƙirjinsa, yace “ ki daina kuka, ba ki ga na ji sauƙi ba, babu abinda yake damuna sai rashin ƙarfin jikina”, ita kam Haj Hudah tana gefe kan kujera ta kasa jurar irin kallon da su ke ma juna da irin saƙonnin da ke cikin idanun nasu na soyayya. Ƙasa kawai tayi da kanta, tana son ta mallaki natsuwarta.
Murtala ya matsa kusa da shi yana yi masa sannu, su ma duka su Mallam mahmud ɗin suka gaishe shi, daga bisani suka juya kan Haj Hudah su na yi mata godiyar ɗawainiya da Musaddiƙ, inda ta nuna musu duk abinda ta yi masa haƙƙinta ne ta yi masa don haka ba sai sunyi mata godiya ba. Ta ƙara duban Inna Halima sosai tace “ Amma wai dama ya saba yin irin wannan aman ne na ban tsoro?”,
Ta girgiza kai tace “ Bai taɓa ba Haj wannan ɗin ma, bana tashin hankali ba ne, abin ayi ma Allah godiya ne, domin aman nasa silar abubuwa ne na alheri da yawa a rayuwarsa”.
Cike da mamaki Haj Hudah tace “ Ban fahimceki ba, kamar ya ya , bayan irin wahalar da ya sha me tsanani”,
Mallam Mahmud ya muskuta ya gyara zamansa yace “ Halima ai Haj ta zama wani ɓangare na zuri’ armu , domin duk me ƙaunar na ka, ai kai yake ƙauna, a yanzu dai babu abinda zamu ɓoye mata, don haka ki yi mata bayanin komai”. Ya waiwayo ya dubi Musaddiƙ yace “ Shi kansa Musaddiƙ ɗin yana da buƙatar sanin abinda ya yi sanadiyyar shigarsa wannan halin, domin nasan yanzu yana jin sa ne kamar wanda ya yi bacci ya farka, don haka ki yi musu bayani dukkan su”.
Musaddiƙ ya yi shuru yana kallon Inna Halima, ya ƙosa ya ji abinda ke faruwa, domin tabbas abinda Mallam Mahmud ya faɗa gaskiya ne, ji yake kamar ba shi ba, yana jin kamar ya manta da wasu abubuwa da yawa a rayuwarsa, haka zalika a yau ya ji daɗin jikinsa sosai tamkar wanda aka sauke masa wani kaya. Murtala ya ƙara matsowa kusa da shi cikin nuna kulawa yace “ ka natsu naga kamar kasa ma kanka fargaba, ba wani abu ba ne”, kai kawai ya gyaɗa ba tare da ya ce komai ba. Sannu a hankali Inna Halima ta fara yi musu bayanin duk abinda ya faru, tun kafin ta gama idanun Musaddiƙ su ke zubar da hawaye, haka ma Afrah sai kuka take, ta yi dabarar zura hannunta a cikin nasa ba tare da kowa ya gani ba, ta damƙe hannunsa sosai, har sai da ya ɗago ya zuba mata ido duk yadda ya so da ya tsaida hawayensa ya kasa.
Har Inna Halima ta gama faɗan komai Haj Hudah ta kaɗu kwarai da jin wannan labari mai cike da ban tausayi, tsananin tausayinsa ya ƙara jefa ƙaunar musaddiƙ a cikin zuciyarta, ta dubi musaddiƙ tace “ Amma wannan wace irin muguwar macece, ai da an kaita kotu bai kamata kuce an haƙura ba, ta ci banza kenan fa, ki raba mutum da dukiyarsa, ki raba shi da natsuwa da kwanciyar hankali, gaskiya ni bazan bar wannan maganar ba sai na wulaƙantata kamar yadda ta wulaƙanta musaddiƙ”, kawai yadda ta haƙiƙance damuwarta akan lamarin ya yi yawa, hakan yasa Afrah ƙura mata ido, bata jin zargi ko shakka akanta, amma me yasa ta damu haka da yawa, kwatankwacin irin damuwar da ta yi.
Kalaman Mallam Mahmud ya yi sanaduyyar korar tambayoyin da Afrah ta fara yi ma kanta.
Inda ya dubi Haj Hudah yace “Ka da ki damu Haj, Allah muka roƙa ya yi mata hukunci irin nasa da gaggawa, Alhamdulillah kuma ya amshi addu’ar mu, domin ya hukuntata da mafi munin hukunci, don duk wanda aka raba shi da hankalinsa, aka kuma sa shi ya gayama duniya duk irin mugun aikin da ya aikata da kansa da bakinsa ai an gama yi masa hukunci”.
Inna Halima ta karɓe maganar tace “ Ta yi hauka tuburan, sai ɗaureta aka yi to ko kinga ai ba’a yi ƙarshe mai kyau ba”. Da sauri musaddiƙ ya yunƙuro ya daidaita zamansa cike da damuwa da tashin hankali yace “ Hauka, Hajiyar?” Murtala yace “ ƙwarai kuwa ai tabbatar Allah baya zalunci kenan, shi yasa ya yi maka sakayya tun a duniya”.
Ya runtse idonsa ya buɗe yace “ Na san ta zalunce ni, don a duniya babu abinda na fi so sama da mutuncina, gashi kuma ta watsar min da shi, amma duk da haka ban ƙullaceta da komai ba, domin duk abinda ta yi min kanta ta yi ma, haka zalika ko don takabar da ta yi ma mahaifina bazan wofintar da ita ba, don haka ina yi mata addu’ar samun lafiya cikin gaggawa, dukiya kuma da ta ƙwace min a cikin irin son ranta da ta tambaye ni zan iya mallaka mata ba tare da ta naƙasa min rayuwa ba, domin ni na fi son mahaifina akan dukiyar da ya bar min, a kullum kuma na fi son na tara tawa dukiyar da gumi na, hakan ne yasa bazan taɓa ɗaga maganar ba, na karɓi komai a matsayin ƙaddarar rayuwata”.
Maganganun Musaddiƙ sun ƙara da sa ma Afrah ƙaunarsa, domin cikakken mutum kenan, wanda ya ke yin afuwa ga wanda ya zalunce shi , lalle yana ƙaunar irin waɗannan bayin nasa , shi ma kuma yana yi musu afuwar dukkan zunubansu tare da ba su kyakkyawar makoma. Ita kanta Haj Hudah ji ta yi musaddiƙ ya ƙara mallakar dukkan zuciyarta, a kullum tana ganin babu wani namiji irin musaddiƙ to a yanzu ma ta ƙara tabbatar da hakan, samun mutum irinsa yana da wahala.
Musaddiƙ ya ƙara gyara muryarsa yace “ Abu dai mafi dasa farinciki a gare ni shine da zan koma mutumin ƙwarai da zan dawo da ɗabi’u da halayyata irin wanda na bari, sannan na yi sallama da mummunar rayuwar da take sani zubar da hawaye kullum kwanan duniya( ya juya ya dubi Afrah) duk wannan kuma ya faru a dalilin ki ne Afrah Allah ya saka miki da alheri, ke ɗin samun ki a cikin rayuwata babban alheri ne da Allah ya yi min”, wani irin abu ne ya shiga yawo a cikin ƙwaƙwalwar Haj Hudah.
Irin murmushin da Suke ma juna ya isa ya ƙarasa narkar da zuciyar Haj Hudah.
Ya dawo da kallonsa ga Mallam Mahmud da Inna Halima yace “ kuma Allah ya saka muku da alheri da kuka zama silar mallaka min Afrah, nagode” mallam Mahmud ya matso yana murmushi yace “ Allah ya yi maka albarka ya rabaka da dukkan sharri”, yana magana ya na buɗe robar rubutun da ya zo da ita ya miƙama Afrah yace “ ki bashi ya sha, ya kuma shafe fuskarsa da jikinsa”. Ta karɓa da kanta ta buɗe ta bashi yasha sannan ta zuba a tafin hannunta ta shafe masa fuskarsa, ta rage wanda zata shafe masa a jiki idan jama’ar ɗakin sun bar ɗakin.
Sai bayan la’asar sannan Murtala ya koma da su Mallam Mahmud, bayan musaddiƙ ɗin shi ma ya yi masa godiya mai yawa, a yayinda suka bar Afrah a gunsa, ita kanta Haj Hudar dole yasa ta tattara ta koma gidanta na nan Abujan tabar Afrah tare da shi, a dalilin ba zata iya jurar cigaba da ganin irin soyayyar da suke nunawa juna ba wacce tun bayan tafiyar su Inna Halima suka kasa ɓoyewa juna ba, ita kuma ji take kamar zuciyarta zata fashe a duk lokacin da ta ga irin soyayyar da musaddiƙ ya ke ma Afrah a cikin ƙwayar idonsa.
Tunda Haj Hudah ta shiga gidanta ta ji ta kasa samun kwanciyar hankali, damuwa ne fal a cikin zuciyarta na yadda ta ke neman ja ma kanta fitina, domin dai tana jin tamkar soyayyar musaddiƙ ta zo gaɓar da zata fallasa ta, amma ta ya ya?, bayan tana matar aure, musaddiƙ kuma yana mijin aure, shin wace irin alaƙa ta ke son ƙullawa tsakaninta da shi?,
Wata zuciyar ta ce mata ko da aurenki zaki iya ƙulla alaƙa ta sirri tsakaninki da shi. Ta yi saurin dafe ƙirjinta, tana aje ajiyar zuciya, bata zina amma me yasa soyayya zata rufe mata ido ta fara akan musaddiƙ, ta lumshe idanunta tana tuna lallausan jikin musaddiƙ da hannunta ya taɓa, ba taƙi ta rayu tana taɓa jikinsa ba, kamar yadda take jin zata iya ɓarin mutuncinta don kawai ta kasance tare da musaddiƙ.
Har ta gama shirin kwanciya ta kwanta ƙarfe sha ɗayan dare ba ta sami sassauci ba, ba ta jin kuma zata iya runtsawa, domin tunaninta na ga musaddiƙ da Afrah shin wace wainar suke toyawa a inda suka kasance su kaɗai. Dai dai lokacin wayarta ta ɗauki ƙara, ta na dubawa ta ga nambar Alh yusuf sanda ce ta ƙasar italy, ta ɗan saki ƙaramin tsaki ba ta ɗauka ba harta kartse, sai dai tana katsewar ya ƙara kira, tasan idan ba ta ɗauka ba ya dinga kira kenan, hakan yasa ta fisgo wayar cikin ɓacin rai ta ɗauka.
Ta daidaita muryarta tace “ Ranka ya daɗe”, daga can ɗaya ɓangaren Alh yusuf sanda ya kurɓi lemo ya aje kofin kan ƙaramin tebur ɗin da ke gabansa sannan yace “ Tare da na ki, kina lafiya?”, tace “ Lafiya lau, har an sauka a italy ɗinne?”, ya yi ɗan murmushi yace “ Ai na daɗe da sauka, na kiraki a lokacin ba ki ɗaga ba, na kuma yi mamakin yadda ba ki biyo kiran ba, yanzu kuma na yi ta kira ba ki ɗaga ba na yi zaton ma ko kinyi bacci ne, nace to yau kuma yan mulkin ne suka motsa”, ta gyatsine fuska tace “ Banga kiranka ba, kaima kasan da na ga ni ai da na kiraka,” ya ƙara murmusawa yace “ Babu damuwa, kada ki damu”, ta gyara kwanciyarta tace “ To ka binciki kayanne ka ji farashin su” ya girgiza kai yace “ Haba yaushe na iso da har zan sami damar yin hakan, sai na huta gaskiya sai zuwa gobe zan je kamfanin na bincika komai”, cikin ƙosawa da hirar tace “ Allah ya kaimu”, sai da ya ja numfashi ya saki sannan yace “ kina ina ne?”. Ta yi ɗan jim sannan tace “ wace irin tambaya ce wannan, ina yakamata na kasance a dai dai wannan lokacin da dare ya yi”, cikin murmushinsa yace “ Gida”, tace “ To idan kasan hakane me yasa ka tambaya, ina gida Minna ina kan gadona zanyi bacci”,
Ya zame ya kwanta sosai akan kujerar yana cigaba da murnushi lokaci ɗaya kuma ya kashe wayar ba tare da sunyi sallama ba, a fili yace “ dama haka nasa ran zanji kin faɗa, amma me yasa ba zaki gaya min gaskiyar cewa kina Abuja kina jinyar musaddiƙ ba, yanzu kuma kin dawo gidan ki kin kwanta ne a dalilin zuwar matarsa asibitin………………
Yar gidan Imam✍️