ILIMIN HADISI A SAUKAKE KASHI NA GOMA
بسم الله الرحمن الرحيم
(29) MENENE HADISI MUKTALAFI?
Shine hadisin da suka zamo sun daidaita a wajen rubutu amma suka saba ta wajen lafazi.
{29} MENENE HUKUNCINSA?
Hukuncinsa shine zai iya zama sahihi ko hasani ko kuma ra’ifi.
مؤتلف متفق الخط فقط
وصد مختلف فاخش الغلط
{30} MENENE HADISI MUNKARI?
Hadisin munkari shine hadisin da ra’ifi ne ya rawaito shi.
{30} MENENE HUKUNCINSA.?
Hukuncinsa shine ba za yi aiki da shi ba kuma ba za a karbe shi ba.
والمنكر الفرد به راو غدا
تعديلهُ لا يحمل التفردا
(31) MENENE HADISI MUTRUKI?
Shine hadisin da mallaman hadisi masu yawa suka ruwaitoshi daga ra’ifi.
(31) MENENE HUKUNCINSA?
Hukuncinsa shine ya fi ra’ifi rauni.
متروكه ما واحدا به انفرد
واحمعوا لضعفه فهو كرد
(32) MENENE HADISI MAURU’I?
Shine hadisin karya da aka kirkira aka dangatashi ga Annabi ko zuwa sahabi ko tabi’i.
(32) MENENE HUKUNCINSA ?
Ruwaito shi ma haramun ne.
وكذب المحتلق المصنوع
على النبي فالك الموصوع
. الحمد الله الصلاة والسلام على رسول الله صلى الله عليه وسلم.
{ WANENE SAHABI? }
Sahabi shine wanda ya hadu da Annabi yana mai imani da shi ya mutu akan haka
Place ( MENENE HUKUNCINSU?)
To, shabai dukkaninsu Adalai ne manyansu da ya ransu, ko da ya halacci yakin da akayi سيدنا Ali da سيدنا da Mu’awuya dalili kuwa shine Allah yace MUHAMMADU MANZON ALLAH NE WANDA YAKE TARE DA SHI (wato sahabai) masu matsawa kafirai ne, masu tausayi a tsakanin su.? suratul fatahi aya 29: