Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 11

Sponsored Links

 

📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

 

*SAKAYYAH*

_Page 11_

 

_NA_

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

*FREE PAGE fa ya kusa ƙarewa*

 

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine wannan Free page ne ƴar uwa 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin.*

 

 

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

 

_Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

 

 

 

🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

 

Cikin lumshe Ido Mommy ke cin perpesoup ɗin yayin da daɗinsa ke ratsa ilahirin jikinta,

kallonta Hajiya Bunayya dake murmushi tayi tare da ɗiban romon da cokali takai bakinta kana ta buɗe Idanunta dake lumshe.

Tace.

“Gaskiya Yaya Nagode wallahi bakiji yanda naji daɗin Perpesoup ɗin nan ba, dama sai tunanin a binda zanci nake tuntuni sai kuma gashi Allah ya kawo ki”.

Murmushi mai cike da Ma’anoni Hajiya Bunayya tayi kana ta muskuta tare da gyara zamanta tace.

“Lallai de kam aidama sanyin nan saida abu mai ɗumi da ɗan yaji-yaji”.

Yayin da aƙasan ranta wani irin farin cikine mara misaltuwa wanda har yakasa ɓoyuwa asaman fuskanta.

Ita kuwa Mommy Sosai take cin perpesoup ɗin tana mai lumshe Idanunta yayin da daɗin sa ke ratsa har ƙwaƙwalwar kanta tace.

“Yaya perpesoup ɗin nan yaji kayan yaji”.

Dariya Hajiya Bunayya tayi tace.

“Dama Alhaji nayiwa nace bari na zubo miki dan nasan zaki ji daɗin sa”.

Kai Mommy ta gyaɗa da faɗin.

“Aikam gashi yamin daɗi sosai”.

 

Acan ɗaki kuwa miƙewa tsaye Khausar tayi daga kan stool tare da riƙe ƙugunta ta bayan ta gama nin ke kayan asaman laɓɓannta ta furta.

“Wash Allah!, Gashi yanzu na gama gyara kayan nan, amma Raudat na zuwa ɗaukan abu ɗaya zata wargaza shi kab, ya zama kamar ba’a taɓa gyarashi,  amma Insha Allah next time, Idan ta ƙara har gitsashi, sama Zan mayar dan kayanta, ta yanda idan tazo baza ta iya ɗauka ba sai ta kirani in bata yafiye min sauƙi”.

Ta Ida maganar tare da fitowa falon tana riƙe da ƙugunta da hannu ɗaya yayin da ɗaya hannun ke dafe asaman wuyanta.

Cike da mamaki take kallon Hajiya Bunayya dake zaune yayin da Mommy ta ke shan perpesoup ɗin da kaɗan ya rage asaman Plate ɗin.

 

Cikin yanayin tashin hankali da razana Khausar ta ɗaga Muryanta tace.

“Mommy me kike ci?”.

Anitse Mommy ta ɗago kanta dan sam batasan ta fito ba sai da taji muryanta, gyara rikon Plate din Mommy tayi kafin tace.

“Perpersoup ne ko zaki cine?”.

Ita kuwa Khausar kai ta girgiza cikin rawan murya tace.

“A’a nikam bazan ciba Mommy kekam Komai kika samu sai kinci, ba zaki tsaya ki duba ingancin sa da kuma rashin ingancin saba”.

Baki Mommy ta sake tana kallon Khausar da Mamaki.

 

Ita kuwa Hajiya Bunayya wani mugun Harara ta galla mata cike da tsanarta tace.

“Komai ta samu saita ci ke kin isa ki hanata cine?, Khausar!, Khausar!!, Khausar!!! ki kiyayeni fa”.

Ta Ida maganar tana dariya irin abin awasa takeyin sa, yayin da kuwa azuciyarta ba haka bane.

Ita kuwa Mommy taɓe Baki tayi tace.

“Yaya rabu da ita itama kanta kwaɗayin ya kawota ƙilan so take in bata”.

 

Fuska Khausar ta ɓata cike da damuwa tace.

“Wallahi nikam ba zanci ba Mommy kema Meyesa zakici, kema daga ganin abu saiki hau ci, batare da kin duba ingancin sa ba Allah ma dai yasa kinyi Bismillah”.

Dafe kai Mommy tayi tace.

“Aikuwa de Wallahi kwaɗayin sa yasa na shafa banyi Bismillah ba, Anma bari nayi.

Bismillahi feh Auwalihi Wa’ahirihi”.

Ta faɗa tare da cigaba da shan perpesoup ɗin.

Wani banzan kallo me cike da tsana Hajiya Bunayya ta watsa wa Khausar aranta tace, shegiyar yarinya, wannan yarinyar saina bi takan ta tukunna zata gane kurenta, bari dai ingama da matsalolin dake gabana”.

Ita kuwa Khausar kallon mahaifiyarta da har zuwa yanzu take shan perpesoup ɗin tayi tace.

“Wai Mommy ba zaki haƙura dasha haka ba?”.

Girgiza Kai Mommy tayi kana tace.

“Kema Idan zaki ci ga shican akula Khausar ban hana kiba, amma wannan tambayoyin naki sun fara isata”.

 

Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi tace.

“Ƙyaleta bare ma ni bazan bar mata ba ina kedai ya isheki?”.

Cikin sakin fuska Mommy ta gyaɗa kai tare da faɗin.

“Eh Alhamdulillah ya isheni”.

 

“Aiko buƙatar maje haji salla, ba zan bar matashi ba, tunda dai ke kinsha ai hikenan, idan tanaso ta biyoni ɗakina”.

Ta ida maganar tare da ɗaukan kularta ta fice bayan ta yiwa Mommy sai anjima.

 

Zama Khausar tayi agaban mahaifiyarta cikin raunin murya da yanayin damuwa tace.

“Mommy meyesa!?, Rayuwar nan fa ba yanda kika ɗauke ta da yanda zuciyarki take ace haka na kowa yake  da munji daɗin duniyar nan fa, amma Mommy meyesa daga kawo miki abu zaki ɗauka kici yanzu kuma idan abin cutarwa ne fa?”.

 

Kallonta Mommy tayi cikin tsukr fuska kana cikin fushi tace.

“Khausar ki kiyayeni fa, bana son wannan baƙin halin da kike ɗaurawa rayuwarki fa. Ni bakiga ina nunawa matar nan baƙin hali ba haka zalika itama da zuciya ɗaya take zaune damu,  zaman lafiya mukeyi babu kishi bare tsangoma ko hassada, amma meyesa zaki sawa ranki rashin yarda akan n

Me kike zaton zata cutar dani, babu abinda zata yimin dan haka ki kiyaye”.

Ita kuwa khausar hawaye da ya cika mata Idanunta  tashiga ƙoƙarin mayarwa  sabida takaici, mahaifiyarta ta ɗauki duk kan yarda da amana ta basu, amma sukuma da wannan damar suke amfani ganin sun cutar da rayuwarta.

Ƙasa Tayi da kanta kana tace.

“Shikenan Mommy Komai na faɗa miki ba zaki yarda dani ba, amma babu komai Ubangiji Allah yatsareki ya kuma kareki”.

“Ameen”Mommy ta amsa a kufule.

Ita kuwa Khausar cikin mutuwar jiki ta miƙe tare da wucewa Bedroom ɗinta tana maijin wani irin zafi azuciyarta.

Da kallo Mommy tabi bayanta tana ayyana abubuwa da yawa akanta, tarasa ina Khausar ta ɗauko wannan halin baki ɗaya bata da yarda muddin Hajiya Bunayya zata kawo mata abu ko Haiydar saita tsaya tana musu tambayoyi akai, da faɗin kada suci kada suyi kaza da kaza.

Jin ƙiran sallah magriba yasa ta miƙe tashiga Bedroom ɗin ta dan gabatar da Sallah.

 

Aɓangaren Khausar kuwa tana shiga ɗaki ta lumshe Idanunta tare da manna bayanta da jikin ƙofa.

Hawaye masu ɗumi suka zubo mata jikinta na bata da wani makircin da Hajiya Bunayya ta shiryawa mahaifiyarta sam bata yarda da wannan perpesoup ɗin da takowo mata ba,

shin wai ma ta wani hanya zatabi ta fahimtar da mahaifiyar?.

Sosai ta zurfafa acikin tunanin da take har aka shiga Masallaci sai, asannan ta sauƙe gauron numfashi tare da nufar toilet cikin nutsuwa ta ɗaura alwala kana ta fito,   tare da shimfiɗa darduma duk da yanayin zullumi da take ciki bai hanata tattara nutsuwarta zuwa ga Ubangiji mabuwayi gagara Misali ba,

bayan ta sallame ta ɗaga hannayenta biyu zuwa sama kana tace.

“Ya Allah baka zalinci sannan kai ka hana zalunci atsakaninmu ya Allah baka gyan-gyaɗi bare bacci ya Allah kada ka bawa wannan baiwar taka daman cutar damu ya Allah ka  kare  mahaifiyata al’farma Annabi da al’ƙur’ani”.

Kana ta shafa addu’ar tana mai zubar da hawaye har aka idar da Isha’i bata fita ba saima miƙewa da tayi ta kwanta agado lamo cike da tunanin rayuwa da haka bacci mara daɗi ya ɗauke ta.

 

Cikin ikon Allah haka Mommy ta kwana lafiya lau batare da wani mugun abu ba, tun Khausar na jira taji Mommy tace wani wajen nayi mata ciwo ko kuma taga zubewan cikin Mommy kamar yanda Hajiya Bunayya ta faɗa taji shiru,

hakan yasa ta watsar da abin aranta yayin da Aɓangaren Hajiya Bunayya baki ɗaya kunnenta ke sauraron jin wani labari daga bakin Mommy sai dai shiru amma tace bari ta kara jira kaɗan ta gani.

 

Yau kwanan Mommy uku da cin perpesoup ɗin da Hajiya Bunayya ta kawo mata tana zaune a Bedroom ɗin ta cike da kasala.

Cikin rumtse idonta ta zabura tare da dafe ƙasan maranta da yayi wani masifan murɗawa ahankali ta furta.

“Wash! Allah na”.

Sai kuma ta koma ta zauna tare da lumshe Idanunta yayin da hannunta na dama ke dafe asaman maranta sai ka ta miƙe  tare da fitowa falon tana takawa ahankali.

Khausar dake zaune a asaman 3sitter Jikinta sanye da half gownt na bacci  yayin da ta tura tulin sumar kanta acikin hular Net Idanunta na kan takardan Geography dake riƙe ahannunta yayin da Nahawu ke ajiye gefe ta ɗago manyan Idanunta ta zubasu akan Mommy dake ya mutse fuska alamar bata jin daɗin jikinta, zama tayi akan 1 sitter kana a hankali tace.

“Khausar har yanzu baki shiga ba?”.

ta ida mgnar tana mai cije lips ɗinta.

 

Ita kuwa Khausar kai ta gyaɗa mata tace.

“Eh Mommy karatu nakeyi,  gobe Idan Allah ya kaimu zamu fara Exam ɗin First term, lokacin ai ya tafi amma Mommy lafiya na ganki haka?”.

Ta ƙare mgnar tana kafe mata ido.

Ya mutse fuska Mommy tayi tare da lumshe Idanunta still cikin na damƙarta tace.

“Wallahi cikina ke ɗan min ciwo Khausar”.

 

Cike da tausayawa Khausar tace.

“Cikin ki kuma Mommy?”.

Kai Mommy ta gyaɗa tace”.

“Eh”.

Ita kuwa Khausar ajiye takardan hannunta tayi tare da tsirawa mahaifiyarta ta Ido cikin tausayawa tace.

“Mommy kodai in faɗawa Abba Azo atafi Asibiti ne?”.

Kai Mommy ta girgiza kana tace.

“A’a ai beyi tsanani har haka ba”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da sauƙe numfashi tace.

“Toh Allah ya sawwaƙe”.

Mommy da hannunta ke dafe asaman cikinta still Idanunta na lumshe tace.

“Ameen”

Miƙewa Mommy tayi ta koma kan 3sitter ta kwanta kamar minti biyu da kwanciyarta ta sai kuma sake miƙewa ta zauna tana yamutse fuska.

 

Ita kuwa khausar cikin yanayin damuwa tace.

“Sannu Mommy kode in Kira Abba ne?”.

Girgiza kai Mommy ta kumayi sannan tace.

“A’a tashi ki koma ɗaki nima yanzu zan shiga na kwanta”.

Girgiza kai Khausar tayi tace.

“A’a Mommy Zan zauna dake”.

Lumshe idanu tayi tare da cije laɓɓanta na ƙasa tace.

“Kada ki damu kije ki kwanta na faɗa miki naji sauƙi kuma nima yanzu zan shiga na kwanta”.

 

Cikin sanyin jiki ta mike kana tace.

“Saida safe Allah yaƙara sauki”.

Mommy ta amsa da “Ameen”.

 

Ita kuwa Khausar tana shiga ɗaki ta zube akan gadonta tare da faɗa wa duniyar tunanu, a haka bacci ya ɗauke ta kasancewar dare yaja batayi bacci ba ga kuma gajiya.

 

A ɓangaren Mommy kuwa haka ta kwana cikin mawuyacin hali tare da murƙusoso cikin matsanancin ciwon ciki.

Washe gari.

Da safe bayan Khausar na idar da Sallah tayi Azkhar ta nufi ɗakin Mommy bakinta ɗauke da sallama.

Mommy dake kishingiɗe kan darduma ta ɗago kanta tare da amsa sallamar Khausar.

 

Kusa da ita Khausar ta tsugunna tare da riƙe hannunta tace.

“Mommy ina kwana ya cikin naki?”.

“Murmushin Ƙarfin hali Mommy tayi kana tace.

“Naji sauƙi Khausar kije ki haɗa muku abin Breakfast kada lokaci ya ƙure”.

Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.

“Amma da sauki Mommy kodai daurewa kike yi?”.

Murmushi Mommy tayi tace.

“Eh jeki shirya muku”.

Kai ta gyaɗa sannan ta fice kai tsaye kichen ta nufa.

 

Tana shiga tasa ruwa kadan atukunya yanda zai wadatar mata bayan ya tafasa ta ɗan zuba mai kana ta zuba Couscous kamar minti goma ta buɗe taga ya dahu yayi sar gwanin kyau, amfanin ɗiga man kenan.

Sauƙewa tayi sannan ta buɗe fridge ta ɗauko miyan stwe da yaji naman kaza ta ɗumama sai kuma ta dauko lunch box din Raudat, Ramadan da Haiydar da kuma nata ta zuba musu, sai kuma ta koma ɗaki tashiga toilet tayi wanka Agurguje ta fito ɗaure da towel mai ɗan girma sannan ta cirewa Raudat kayanta tayi mata wanka bayan sun fito tashafa mata mai kana ta sanya mata Uniform sannan itama ta shirya cikin Uniform da yayi matukar amsar jikinta hannu Raudat taja suka fita dai-dai lokacin da Haiydar suka fito da Ramadan cikin shiri ko wannensu ya nufi inda lunch box ɗin da yake ya ɗauka kana suka fice harabar gidan suka shiga mota.

 

Kamar ko yaushe motar na parking Khausar ta fito riƙe da hannun Raudat,

Sai da ta kaita ajinsu sannan cikin sauri ta juya ta kama hanyar koma ajinsu daga baya taji ankira sunan ta da faɗin.

“Lelewal ke kullum sai kowa ya riga ki shiga cikin aji ko?”.

Ahankali ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta akan Malam Isa dake tsayi  murmushi tayi da faɗin.

“Ba haka bane Malam na tsaya kai Raudat ajinsu ne shiyasa”.

Kai ya gyaɗa still Idanunsa akanta hakanan yarinyar ke burgesa ahankali yace.

“To ki tafi kar araba musu questions paper ba kyanan”.

Kai ta gyaɗa tare da juyawa cikin sassarfa da sanin darajar kanta take tafiya har ta isa cikin ajin.

 

Aɓangaren Amina kuwa koda M Jameel yashiga class da niyyar raba musu questions paper ƙasa tayi da kanta ta amsa batare data kalli fuskarsa ba domin koda gaishesa ne ta dena tunda ta lura da baya buƙata kallon fuskanta, to shima M Jameel Sosai yaji daɗi da yarinyar ta daina gaishesa, dan ko kaɗan baya ƙaunar kallon fuskarta, bare kuma wata magana ta haɗa su.

 

Acan gida kuwa tun bayan tafiyar su Khausar Makaranta cikin Mommy ya tsananta da ciwo da ƙyar ta yunƙura ta miƙe tana mai rintse Idanunta jini taga yana bin ƙafafunta da sauri ta dafe cikinta da ƙyar ta iya furta.

“Ya Allah wannan ciwon cikin kuma na menene?”.

Da ƙyar taja ƙafanta zuwa jikin beside drawer ta ɗaga wayarta tare da kiran number Hajiya Bunayya, kafin ya katse Hajiya Bunayya tayi picking tare da Sallama.

 

Mommy kuwa cikin azaban ciwon da cikinta ke mata ta rintse Idanunta kana tace.

“Yaya”.

Da sauri Hajiya Bunayya ta katseta da faɗin.

“Ƙanwata lafiya naji muryanki haka?”.

cike da yarda  ta rintse Idanunta cikin yanayin azaban ciwon da cikinta keyi tace.

“Wallahi Yaya cikina ciwo yake tun daren jiya, haka na kwana banyi bacci ba yanzu kuma gashi jini ya ɓalle min!

Dan Allah ki faɗawa Alhj mutafi asibiti”.

 

Hajiya Bunayya kuwa da damuwa amuryanta tace.

“Subhanallahi! bari na faɗa masa yanzu ma kuwa”.

Sannan ta katse wayar ta nufi ɗakin Lamiɗo ranta fari Sol burinta ya cika abakin ƙofa suka haɗu yana shirin fita.

A take ta wani marairaice fuska kana cikin yanayin damuwa tace.

“Yanzu Mommyn Khausar ta kirani.

Wai jiya da ciwon ciki ta kwana yanzu kuma jini ya ɓalle mata”.

Ai bai ma gama sauraron abinda zata faɗa ba ya ratsa ta ya wuce sashen Mommy cike da damuwa.

Hajiya Bunayya kuwa da harara tabi bayansa kafin taja siririn tsaki ta mara masa baya.

Tana shiga Bedroom ɗin ta samu Lamiɗo tsugunne akan Mommy da sauri ta tsugunna daga gefensa ta riƙo hannun Mommy.

 

Cike da tausayawa kamar za tayi kuka tace.

“Sannu Aysha ciwon ciki amma baki yi magana ba, gashi har ya tsananta jini na zuba”.

Ta ida maganar zufa na karyo mata wanda in kagani zakayi zaton na tsananin damuwa ce, nan kuwa na tsananin farin cikin burinta ya cika ne.

 

Lamiɗo kuwa miƙewa yayi tare da naɗe hannun rigarsa zai ɗauke ta Ganin haka ne yasa Hajiya Bunayya tayi saurin miƙewa tare da tallafo Mommy jikinta suka fita,

agidan baya suka zauna Lamiɗo kuma ya shiga gefen mai zaman banza Driver yaja suka tafi Hajiya Bunayya sai faman sannu take yiwa Mommy.

 

Suna isa asibitin aka karɓe su kai tsaye emergency aka nufa da ita ganin cikin ya riga ya zube yasa likitoci suka nufi wani ɗaki da ita tare da yi mata wankin ciki kana suka yi mata allurai nanda nan bacci wahala ya ɗauke ta Lamiɗo kuwa kasa Matsawa daga kusa da ita yayi ya cike da kulawa ya zauna a bakin gadon tare da riƙe tafin hannunta cike da tausayinta.

 

Hajiya Bunayya data shaƙa ta cika kuwa.

Wani lalataccen harara ta watsawa ƙeyansa cikin ranta tace, tabbas sai tayi wani abu akan wannan rawan jikin da yake mata.

A zahiri kuwa dafa kafaɗar sa tayi,  ahankali ya ɗago kansa ya kalleta da idanunsa dake cike da damuwa amma baice komai ba.

Cike da kirsa ta ƙirƙiri murmushin da bai kai zuciba kana tace.

“Dan Allah ka rage damuwar nan, babu yanda zamuyi da ƙaddara haka Ubangiji ya tsara wannan ɗin ma ba rabo bane, ayanzu addu’ar lafiya take da buƙata awajenmu”.

A hankali ya sauƙe nannuyar Ajiyar zuciya tare da mayar da Kallonsa ga Mommy dake bacci tamkar babu abinda ke damunta.

Lumshe idanunsa yayi yace.

“Ina matuƙar tausayawa Aysha tun bayan haihuwar Haiydar take fama da wannan matsalar sannan ko wanne cikin sai ya wahalar da ita kafin ya fita”.

Da sauri Hajiya Bunayya ta katsesa da faɗin.

“Ya zamuyi da rubutacciyar ƙaddara, ai kaga da Ubangiji yaga dama ai cikin Raudat da Ramadan ya zauna”.

Kai ya jinjina amma baice komai ba.

Ita kuwa cikin ɓoye farin cikinta ta sauƙe ajiyar zuciya da faɗin.

“Zan koma gida kafin ‘yan makaranta su dawo, naga lokaci yaja amma Insha Allah anjima zan dawo”.

Kai ya gyaɗa ba tare da yace komai ba still Idanunsa na kan Mommy.

Hajiya Bunayya kuwa ficewa tayi ranta fari fess kana tasa Driver ya maida ta.

 

Acan Makarantar su Khausar kuwa koda suka gama Exam ba abasu damar tafiya ba bayan sunyi sallar la’asar suka shiga haddar Alkur’ani sai ƙarfe biyar aka tashe su, kana suka shigo mota suka nufi gida, motar na parking Raudat ta fice da gudu ta nufi sashen su

Tana shiga falo ta fara  kiran.

“Mommy! Mommy!! na mun dawo”.

Jin shiru yasa ta nufi Bedroom ɗinta da gudu ta buɗe ta shiga tana kiran.

“Mommy!, Mommy!!, Ina kika shiga”.

Still Bata ganta ba da gudu ta juya ta fito falon dai-dai lokacin Khausar kuma ta shigo ƙara sawa kusa da Khausar tayi ta riƙe hannunta kana tace.

“Addah Khausy Ina Mommy?”.

Kallonta Khausar tayi kafin tace.

“Bata ɗaki ne?”.

 

Kai Raudat ta gyaɗa mata alamar Eh,

Sake hannunta Khausar tayi kana ta nufi kichen ta buɗe wayam tagani alamar bata nan komawa tayi ta shiga Bedroom din ta ɓude still ba tanan jikin toilet ta nufa ta manna kunnenta ajiki tare da faɗin.

“Mommy Mommy kina ciki kuwa?”.

Jin shiru yasa ta tura ƙofar toilet din still bata nan fitowa tsakiyar falon Khausar tayi tare dasa hannun damanta ta riƙe ƙugunta tana tunanin ina Mommy ta shiga haka, bayan tasan bata fiye fitar yamma ba kuma koda zata fita tun safe kafin su tafi makaranta zata faɗa musu bare kuma yau da suka barta bata jin daɗi.

 

Da sauri ta kalli Raudat sai kuma tace.

“Jirani anan ina zuwa”.

ta faɗa tare da ficewa kai tsaye sashen Hajiya Bunayya ta nufa bakinta ɗauke da sallama tana faɗin.

“Ummah”.

Shigar ta yayi dai-dai da lokacin da Hajiya Bunayya ke riƙe da waya tana cewa.

“Kedai Hajiya Lami bari buƙata ɗaya ta biya saura ɗaya, tana can kwance a asibiti cikin ya zube yabi makwarari, saura ɗayan daman  jira nake inga ya zata kaya ne ki shirya jibi zamu koma”.

Komai Hajiya Lami ta faɗa ohon musu, ita dai Hajiya Bunayya  cikin jin dadi ta kece da wata mahaukaciyar dariya mai nuni da tsantsar farin ciki.

Lokaci ɗaya kuma dariyar nata ya tsaya ganin Khausar tsaye, sai kuma ta katse kiran tare da kallon Khausar.

Kafin tace wani abu Khausar tayi saurin cewa.

“Ummah ina Mommy mu?”.

 

Hajiya Bunayya ta wani langwaɓar da kai kana tace.

“Ayyah Khausar am Mommy ku tana asibiti bata da lafiya wallahi cikinta ya zube”.

 

Da sauri Khausar da kanta ke ƙasa ta ɗago ta kalli Hajiya Bunayya tana sake maimaita kalmar cikinta ya zube akasan ranta lokacin ɗaya hawaye masu zafin gaske suka cika kwarmin Idanunta.

Sai kuma tayi saurin maida hawayen ta kafin tace.

“Shikenan ɓuƙatar magauta tabiya hankali ya kwanta. Allah ya raya mata wa anda ta haifa. Ubangiji ya tsaresu daga sharrin mai sharrin”.

Ta ida maganar tana ƙoƙarin fita.

Da sauri Hajiya Bunayya tace.

“Ke Khausar zo nan Me kike nufi?”.

 

Anutse Khausar ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta da suka sauya launi zuwa ja ta zubawa Hajiya Bunayya kana tace.

“A’a Ummah babu abinda nake nufi, kawai dai addu’a ce nayi”.

Cikin tsuke fuska Hajiya Bunayya ta watsa mata Harara da faɗin.

“Sannan su waye ne Magautan?”.

 

Ware hannu Khausar tayi tare  da faɗin.

“Nikam ban sansu ba,  amma dai nasan Allah Mabuwayi gagara Misali ya sansu kuma zaiyi maganin su, domin ai bahaushe yace rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya,  suji tsoron ranan da Ubangiji zai musu kamun talala!”.

 

Cike da Mamaki Hajiya Bunayya tace.

“Wai Khausar me kike magana kamar habaici kike min ko kuma hannunka mai sanda!?.”

 

Ware ido Khausar tayi tace.

“Haba Ummah in Miki habaici kuma ayanda kike ƙaunar Mommyn mu kinfi ƙarfin habaici ko hannunka mai sanda kin wuce haka sai dai mgnar ce tazo kamar zaurance”.

 

Ɓoyeyyen Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta saki domin tayi zaton yarinyar ta gano lagonta ne.

Khausar kuwa murmushi tayi tare da faɗin.

“Bari na tafi asibitin kar dare yayi”.

Da sauri Hajiya Bunayya ta gyara zamanta Idanunta akan Khausar tace.

“Toh kibari in ƙara sa abinci mana sai ki tafi dashi”.

Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

“Toh amma bari na shiga gidan Aunty Ruƙayya kafin ki ƙarasa”.

Kai Hajia Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.

“Toh ki gaisheta”.

Kai kawai Khausar ta gyaɗa Sannan ta wuce sashen su.

 

Tana shiga Bedroom direct toilet ta wuce ta cire Uniform ɗin ta sannan ta watsa ruwa bayan ta fito ta dauki dogon rigar material pinch colour ta sanya, kana ta nufi kichen Agurguje ta dafawa su Haiydar jollof ɗin shin kafa da yaji bushesh-shen kifi da kayan ƙamshi nan da nan kichen ɗin ya ɗauki ƙamshi Warmers ta ɗauka ta juye sannan ta tafasa musu tea kana ta ɗura musushi, sannan ta fita falon dai-dai lokacin da Haiydar ya shigo.

 

Kallonsa Khausar tayi tare da kiran sunansa tace.

“Haiydar”.

Ya amsa da.

“Na’am”.

Cikin sanyi tayi ƙasa da muryanta tare da faɗin.

“Dan Allah Haiydar ka kwana anan kai da Ramadan, Raudat kuma zamu tafi da ita asibiti sai mu kwana da Mommy”.

 

Kai ya gyaɗa mata sai kuma yace.

“Nima ai inaso naje na dubata”.

Jinjina kai Khausar tayi tace.

“Ba damuwa kazo mutafi dukan mu amma yanzu zan fara shiga gidan Aunty Ruƙayya in sanar mata, idan yaso kai da Ramadan ku taho tare da Ummah,

In yaso sai ku dawo tare amma kubar min Raudat dan zamu kwana tare”.

 

“Toh shikenan Allah ya bata lafiya”.

 

“Ameen”,

Tace kana ta juya ta tafi har ta kusa fita ta sake juyawa ta kalli Haiydar dake tsaye Ahankali tace.

“Dan Allah Haiydar ka kula, bakomai za’a baka kaci ba, akwai abinci na dafa muku sannan duk wani abu da zaku buƙata akwai”.

Da sauri ya dafe kansa tare da faɗin.

“Ke dai jeki da rashin yardan ki kedai haka Allah ya halicce ki baki da yarda”.

Cikin sanyi ta girgiza kai kana tace.

“Shikenan ni dai ban san sai yaushe zaku yarda dani ba”.

Ta ida maganar tare da ficewa”.

 

Kai tsaye gidan Aunty Ruƙayya ta nufa.

 

Tare da Sallama tashiga Babban falon da yaji kayan alfarma kujerun set biyu aciki Black and Ash sai kuma babban tv plasma dake Manne abango daga ƙasansa kuma horm teater ne ƙasan falon kuma shimfiɗe yake da chanis capet.

 

Aunty Ruƙayya dake bedroom ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tace.

“Khausar kece sannu da zuwa, shigo ciki”.

Da sauri tace.

“A’a Aunty sauri nakeyi ai”.

Cikin kulawa tace.

“Yo yasu Mommy ki?”.

Murmushi Khausar tayi tace.

“Wallahi Aunty Ruƙayya Mommy ce ke asibiti bata da lafiya, shine nace bari nazo na faɗa miki, Ni yanzu ma zan wuce ko za muje tare?”.

 

Cike da tausayawa Aunty Ruƙayya tace.

“Ayyah Allah ya bata lafiya zanje bari ina zuwa mu tafi tare”.

Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

“Toh”.

Aunty Ruƙayya kuwa bedroom ta shiga tare kiran mijinta a waya, bayan ya bata izinine, ta ɗauko key mota da mayafinta suka fita,

suka shiga mota,

jingina kai Khausar tayi da jikin motar kalaman Hajiya Bunayya nayi mata suwwa akunne.

Juyawa Aunty Ruƙayya tayi ganin yanda Khausar ta zurfafa cikin tunani yasa tace.

“Ki riƙa yi mata addu’a”.

Kai kawai Khausar ta iya gyaɗa mata.

Cikin Mintuna kaɗan suka isa Asibitin bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga ɗakin da aka kwantar da Mommy saboda Hajiya Bunayya ta faɗa mata.

 

Kwance akan gado suka tarar da ita yayin da Lamiɗo ke gefenta akan kujera hannunsa riƙe da kofin tea yana miƙa mata da faɗin.

“Ki tashi kisha”.

Yana jin Sallamar Khausar ya juya yana kallonta har ta isa kusa dashi.

Cike da kulawa yace.

“Khausar har kun dawo?”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Eh Abba ya jikin Mommy!?”.

Sai da ya ɗan kalli Mommy dake jingine da pillow sai kuma ya mayar da Kallonsa kan Khausar yace.

“Da sauƙi”.

Sai asannan ya lura da Hajiya Rukayya ya ɗan yi murmushi da faɗin.

“Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa”.

 

Zama tayi akujeran dake kusa da ita tana cewa.

“Yawwa ya Hajiya Aysha da jikin kuma?”.

Ɗan Murmushi yayi kana yace.

“Da sauƙi”.

Tana kallon Mommy tace.

“Ubangiji Allah ya ƙara sauki”.

Ya amsa da.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

 

Khausar kuwa bakin gadon ta ƙarasa ta riƙe hannun Mommy acikin nata.

Cikin raunin murya tare da tausayawa mahaifiyar tata tace.

“Sannu Mommy ya Jikin?”.

Lumshe idanu Mommy tayi kana ta buɗe su a hankali tace.

“Da sauƙi Khausar bana jin komai in dan ta nice ma, da su sallame ni in koma gida mu kwana tare, dan bana jin ciwon cikin yayi sauƙi babu inda yake min ciwo!”.

 

Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da faɗin.

“Masha Allah Mommy Allah yaƙara sauƙi Ubangiji ya ƙara tsarewa ya kare”.

A ranta kuwa cewa tace.

Ayyah da ace duk addu’o’in da takeyiwa Mommynta tun randa taci ferfesun da ace tana haɗa addu’ar da yaron cikin wata ƙil da bai zube ba.

 

Shafa kanta Mommy tayi cike da ƙaunar ta tace.

“Ameen Khausar ki kwantar da hankalin ki ba najin Komai”.

Ta faɗi hakan ganin yanda Khausar tayi zuru-zuru da ita.

Hajiya Ruƙayyance ta kalli Mommy kana tace.

“Hajiya Aysha ya ƙarfin jikin!?”

 

Murmushi Mommy tayi kana tace.

“Dasauƙi Hajiya Ruƙayya ya ‘Yar taki ya kuma rigima a makaranta!?”.

Kallon Khausar Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.

“A’a yanzu ai ta daina ta fara girma!”.

Jin haka yasa Khausar tayi murmushi.

 

Lamiɗo kuwa miƙewa yayi idanunsa akan Mommy yace.

“Toh shikenan bari na tafi dama ganin babu kowa ne yasa nake zaune bari na samu naje nayi wanka dan tunda muka zo ban samu na koma gida ba”.

 

Hajiya Ruƙayya tace.

“Ayyah ai babu komai Alhaji kaje”.

Jinjina kai Mommy tayi tace.

“Allah ya tsare”.

Ya Amsa da.

“Ameen”sannan ya juya ya fice.

Tafiyar Lamiɗo babu daɗewa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka zo Raudat na riƙe da hannunta.

 

Suna shiga Hajiya Bunayya ta zauna daga gefen gadon tare da kallon Mommy tace.

“Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.

Murmushi Mommy tayi kana tace.

“Ai naji sauki Yaya”.

Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi cikin yanayin tausayawa tace.

“Allah ya baki lafiya”.

Hajiya Ruƙayya kuwa kallo ɗaya tayi wa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami taji sam basu kwanta mata arai ba musanman ma Hajiya Bunayya dake wani shish-shugewa Mommy.

Ta dai daure tace.

“Sannunku da zuwa”.

Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka haɗa baki wajen cewa.

“Yawwa ya mai jikin”.

Ataƙaice Hajiya Ruƙayya tace.

“Da sauƙi”.

 

Hajiya Lami kuwa jikin gadon ta matasa Idanunta akan Mommy tace.

“Ayyah Sannu Hajiya Aysha Ashe ga abinda ya faru kuma? Amma wannan abu yayi  yawa ai gwara Alhj yayi ƙoƙari ya fitar dake waje wannan matsalar ko yaushe da ansamu ciki ya zube ai babu daɗi!”.

 

Kafin Mommy tayi magana Hajiya Bunayya tayi saurin cewa.

“Kede bari Hajiya Lami abin nan yana damun mu, gaba ɗaya mun kasa gane menene ainihin matsalar, amma hankalinmu na tashi kullum cikin yanayin nan, abin babu daɗi yanzu ciki takwas kenan yana zubewa abin ai babu daɗi!”.

Taɓe baki Khausar da Hajiya Rukayya sukayi alokaci ɗaya.

 

Ahankali Mommy ta gyara matashin data kishingiɗa akai kana tace.

“Uyummm ya za’ayi da abinda Allah ya tsara, amma ni inaga nin ba wani matsala bane, tun da gashi na haihu bayan haihuwar Haiydar ma haka nata fama da ɓare-ɓaren nan, kuma daga baya da Allah ya kawo Ramadan da Raudat an haifesu ba komai ai”.

 

Cike da kirsa Hajiya Bunayya tayi yaƙe kana tace.

“Hakane kam, toh Allah ya kawo masu albarka”.

Hajiya Lami kuwa harara ta gallawa Mommy tare da taɓe baki aranta tace shegiya me iyayin jaraba keda haihuwa sai dai kiga anayi.

 

Idanun Hajiya Ruƙayya da Khausar na kan Hajiya Lami alokacin data taɓe baki ta harari Mommy,

Juyawa Hajiya Ruƙayya tayi ta kalli Khausar tare da jinjina kai itama Khausar kai ta jinjina.

 

Miƙewa Hajiya Ruƙayya tayi tare da kallon Mommy tace.

“Toh Hajiya Aysha Ubangiji Allah ya ƙara sauki sannan Allah ya tsareki daga sharrin abin ƙi ni zan wuce!”.

A hankali Mommy ta ɗan yunƙura tare da lumshe Idanunta kana tace.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Hajiya Ruƙayya Nagode”.

 

Hajiya Lami da Hajiya Bunayya kuwa baki suka saki suna kallon Hajiya Ruƙayya da Mamaki aransu suka ce kaji shegiyar mata da iyayi uban wa takewa wannan addu’ar.

Miƙewa Raudat tayi tare da riƙe hannun Hajiya Ruƙayya tace.

“Aunty Ruƙayya ni zan biki gidanki, Inje in kwana dasu Salman tun da gobe babu makarata”.

Da sauri Khausar ta kalli Raudat dake riƙe da hannun Aunty Ruƙayya tace.

“Ayyah Raudat am baza mu kwana ba?”.

Girgiza kai Raudat tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.

“ Ni dai Ina tsoro  ni bazan zauna ba”.

Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

“Shikenan kibi Aunty Ruƙayya”.

Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tare da jan hannun Khausar dake cikin nata

 

Har sun kai ƙofa Hajiya Bunayya ta ƙirƙiri murmushi tana kallon bayan Raudat tace.

“Oohhh Raudat ba zaki bini mu tafi gida ba?”.

Kafaɗa Raudat ta maƙale tace.

“A’a ni zanbi Aunty Ruƙayya”.

Aunyty Ruƙayya kuwa jan hannun Raudat tayi suka fice batare data sake jiran jin Abinda Hajiya Bunayya zata ceba.

 

Bayan tafiyar Aunty Ruƙayya babu da ɗewa Hajiya Bunayya ta miƙe tare da kallon Mommy tace.

“Toh ƙanwata  zamu wuce Allah yaƙara sauƙi”.

Murmushi Mommy tayi da faɗin.

“Nagode Yaya ahuta gajiya”.

Hajiya Lami tace.

“Babu Gajiya”.

Sannan suka fice Khausar kuwa jinginar da kai tayi kamar mai bacci.

 

Da daddare Khausar ta miƙe daga kan dogon kujeran asibitin da take kwance ta dubi Mommy da bacci ya fara fisgarta tace.

“Mommy”.

Buɗe idanu Mommy tayi tare da kallon Khausar tace.

“Na’am Khausar ya akayi?”.

 

Ajiyar zuciya Khausar ta saki tana wasa da yatsun hannunta tace.

“Mommy baki zargi perpesoup ɗin nan da kika ci azubewar cikin nan ba!?”.

Sosai Mommy ta tsira mata ido na second uku zuwa biyar sai kuma ta miƙe daga kwanciyar da take Atake fara’ar dake fuskanta ya gushe cikin ɗaure fuska cikin kakkausan Murya tace.

“Khausar!, Khausar!!, Khausar!!!, Ki cigaba Nagode da abinda kike min Khausar, duk irin tarbiyyan da nake baki fatali kike dashi ko, kina ɗaukar rashin yarda kina ɗaurawa mutane ki sani Manzon Allah (S.A.W) Yace.

:Azzana zambu walau kana haƙƙun”.

Khausar kuwa ƙasa da kai tayi hawaye masu zafi suka cika Idanunta shin sai yaushe mahaifiyarta zata amince da gaskiyar da take so ta sani akan Hajiya Bunayya basa ƙaunarta cutar da ita suke sonyi.

Cikin sanyi murya tare da rauni gami da ban haƙuri tace.

“Shikenan Mommy kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki”.

Mommy bata tanka taba ta juya ta gyara kwanciyar, ta itama Khausar juyawa tayi ta kwanta zuciyarta babu daɗi.

 

Washe gari  Alhamis Da safe Dr ya shiga ya basu sallama dan jikinta yayi sauƙi Sosai Lamiɗo da kansa yaje ya maido su gida.

Suna dawowa Hajiya Bunayya ta shigo hannunta riƙe da babban Warmers da tayi Perpesoup ɗin Kaji ta shigo dashi.

Zama tayi akan 2sitter tace.

“Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.

Mommy tayi yar dariya tare da faɗin.

“Jiki yayi sauƙi Yaya sai faman hidima kike dani kamar wacce tayi haihuwar farko?”.

Dariya Hajiya Bunayya tayi da faɗin.

“Ai mai ɓari yafi son akula dashi fiye da mai haihuwa”.

Khausar dake tsaye duk takaici ya gama cikita gashi babu dama ta faɗawa mahaifiyarta gaskiya sai ta hau kanta da faɗa bayan da ta iya daga ƙarshe ma Saboda takaici kawai sai ta koma Bedroom ɗin ta ta fara karatu.

 

Wunin ranan haka Hajiya Bunayya ta yini tare da Mommy ta cigaba da kulawa da ita.

 

Washe gari juma’a dai-dai lokacin da maza suka tafi Juma’a dai-dai lokacin da kowa ya tafi Sallar juma’a Akuma lokacin ne Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka tafi gidan Boka Kar’uzu.

 

Khausar da Mommy ne zaune suna hira sosai jikin Mommy yayi ƙarfi abinka da mai juriya ga kuma kulawa da take samu.

Sallamar Aunty Ruƙayya ya katse musu hirar da suke.

Khausar ta faɗaɗa fara’ar fuskarta kana tace.

“Aunty Ruƙayya sannu da zuwa ina Affan?”.

Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tana zama tace.

“Affan yana lafiya bacci ma yake ya mai jikin”.

Khausar tace.

“Jiki da sauƙi”.

Aunty Ruƙayya tace.

“Masha Allah Ubangiji ya ƙara sauki”.

 

Cikin sakin fuska Mommy ta gyara zaman hular dake kanta tace.

“Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa ya gajiyarki?”.

“Hajiya Ruƙayya tayi murmushi da faɗin.

“Babu gajiya ya jikin naki?”.

 

“Jiki yayi sauƙi ya yara?”.

Alhamdulillah ta bata amsa.

 

Khausar kuwa miƙewa tayi cikin neman izinin tace.

“Ayyah Mommy zanje gidan su Asma’u?”.

Ido Mommy  ta zuma mata, na tsawon second bakwai tana kallonta kana tace.

“Toh yayi kyau”.

 

Khausar kuwa juyawa tayi ta shiga Bedroom Dogon rigar dake jikinta ta cire tare da ɗaura towel tashiga toilet,

shawer ta ɓude ta sakarwa kanta ruwan ɗumi,

ta ɗauki kusan minti shabiyar kafin ta fito ɗaure da towel da tsawon sa bai wuce gwiwar taba yayin da ƙarami ke kanta tana tsane ruwan kanta.

Stool ta janyo ta zaune tare da goge ruwan jikinta ta ɗauki Vassiline lotion ta shafa kana ta ɗauki powder ta shafe sai kuma Kajol ta zizara a idanunta mascara ta ɗauka ta taje gashin Idonta da sukayi tsayi tamkar tasa Eyelashes golb mai sheƙi ta ɗauka ta shafa asaman pinch lips ɗin ta sai yayi kamar jan baki ta shafa kallon fuskarta tayi a mirrow sosai tayi kyau.

Miƙewa tayi ta nufi jikin durowar ta buɗe uban kayan dake ciki ta zubawa ido ahankali Idanunta suka sauka akan wani Less Coffee da aka masa adon cycle da rastin Milk colour ta janyo ta sanya Masha Allah Sosai ɗinkin less ɗin ya mata kyau tare da fitar da shape din jikinta skirt ɗin ya zaune ɗass ajikinta tare da fitar mata da tsarerrenn ƙugunta haka ma rigar ta zauna ɗass ajikinta ɗan kwalin ta ɗauka tayi ɗauri mai kyau sai kuma ta ɗauki glaye medium size milk color kana ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi.

 

Falon ta fita tun kan ta isa Aunty Ruƙayya ta ɗago kanta tare da tsira mata Idanunta jin ƙamshin daya ratsa hancinta ta saki murmushi kana tace.

“Iyeee Masha Allah Khausar irin wannan kyau sai kace preety  ta ƙasar India”.

Hannu Khausar ta sanya ta rufe fuskarta tana dariya sai kuma ta buɗe tace.

“Kai Aunty Ruƙayya Ina Zan samu koda rabin kyawunta ne?”.

Ware ido Aunty Ruƙayya tayi kana tace.

“Allah kuna kama dan da zakije India ma cewa za’ayi ke ƙanwarta ce, har rawan kanki ma irin natane a Film ɗin Chori-Chori Cubke-Cubke ne”.

Mommy Kam murmushi take musu batare da tace komai ba.

 

Khausar kuwa Murmushin jin daɗi tayi tare da tsugunnawa ta ɗauki wayar Mommy tace.

“Mommy zan tafi da wayarki”.

Kai kawai Mommy ta gyaɗa mata sannan ta ɗauƙi wayar tare da faɗin.

“Na tafi”.

ta ida maganar tana gyara zaman Handbag din Hannunta tare da ciro earpiece aciki

Suka haɗa baki wajen faɗin.

“Adawo lafiya”.

Kai ta jinjina tare da ficewa,

Abokin gate ta haɗu da Haiydar riƙe da MP ɗin sa, cikin sauri tace.

“Yauwa Haiydar dan Allah aramin MP ɗinka”.

Cike da mamaki ya zuba mata ido tare da cewa.

“Yau kuma to ke kuma da ba jin kiɗa ya dameki ba, me zakiyi dashi?”.

Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.

“Wallahi yau dai shauƙi nakeji zanje wurin Asma’u mu ɗan rausaya”.

Murmushi yayi yana mamakin wai yau Khausar ce da cewa zata sha ƙiɗa, kawai miƙa mata yayi. Tare da cewa.

“Kuma kikasa gyale ko?”.

Cikin daɗi tace.

“Ngd kai rabani kullum mutum liƙe da hijabi kamar maitakaba” na mgnar  tana fita  ta tari adaidaita sahu ta shiga.

 

Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan an idar da Sallah juma’a ya kalli M Jameel dake Driving yace.

“J yakamaya muje mu gaida Ummi kafin mu koma gida!”.

Kai ya Jinjina  kana yace.

“Dama abinda nake son faɗa kenan ka rigani”.

Gyara zama Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraron ƙira’ar dake tashi amotar kana ya shafa sajensa yace.

“Muje toh”.

Kai M Jameel ya gyaɗa tare da juya akalar motar zuwa unguwar su Ummi.

 

Suna cikin tafiya wayar M Jameel ya hau ruri yana duba screen ɗin wayar yaga Bahrain ba suna sai Number Dariya M Jameel yayi still hankalinsa nakan Driving din yace.

“Jalaludden! Wallahi Jalaludeen!!  nayi mana abinda ransa keso”.

Moddibo da Idanunsa ke lumshe yayi ɗan guntun Murmushi ba tare daya buɗe idanun ba yace.

“Toh ka ɗaga mana kar ya yanke”.

 

Picking M Jameel yayi tare da Sallama.

Amsawa Jalaludeen yayi  da faɗin.

“Idan kun isa ku gaishe da Ummi”.

M  Jameel yayi Murmushi kana yace.

“Kana biye da mu ne?”.

 

“A’a bana biye daku na dai rigaku zuwa na gaisheta”.

Cewar Jalaluddeen

Dariya M Jameel yayi sai kuma ya zare ido yace.

“Wallahi Jalaludeen kada ka razana mana tsohuwa!”.

 

Murmushi Jalaludeen yayi yace.

“A’a bazata ra zanata ba sannan ba zata tsorata ba ai mun taɓa zuwa tare daku baku dai sani bane kuma na bayyana mata ta ganni”.

 

“Wallahi Jalaludeen ka kiyaye mufa”.

 

Dariya Jalaludeen yayi kana yace.

“Tare dai mukayi sallama jumma’a a sahu daya.

Yanzu kuma Na dai hango ku ahanya zakuje yanzu ina katakon nan?”.

Da sauri M Jameel yace.

“Wani katakon?”.

Cike da tsokana Jalaludeen yace.

“Katakon dake gefenka”.

Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Moddibo yace.

“A.J ɗin nawa ne katako?”.

 

“Eh inba katako ba shi menene? ka faɗa masa cewa akwai furen dake ƙoƙarin tsiro a jikinsa tun daga ƙasa har ya isa zuciya ya gab da kanshi tuni ma ya ratsa zuciyarsa amma bai sani ba”.

Murmushi M Jameel yayi  tare da kallon Moddibo da still Idanunsa ke lumshe kamar mai bacci kana yace.

“Wai yace in faɗa maka akwai furen da zai fito tsakiyar kanka yama ratsa zuciyarka”.

Sai asannan Moddibo ya buɗe idanunsa ya kalli M Jameel tare da faɗin.

“Ka ganni karabu dani da kalaman Jalaludeen, shiya sani can yaje yata faman maganganunsa da baza ka gane kansu ba bare gindinsu ya riƙa yi mana maganar damu mutane zamu gane ba sai wanda sai sune masu ganewa ba”.

 

Dariya Jalaludeen yayi yace.

“Zaka gane ne ai lokaci ne yana zuwa”.

Dariya M Jameel yayi tare da hong aƙofar gidan Ummi ganin shiru ba’a buɗe masu bane yasa, M Jameel fitowa ya buɗe, kana ya dawo yaja motar still kafaɗarsa saƙale da wayar

Jalaludeen ne yace.

“Ku gaishe da Ummi idan kun shiga”.

Sannan ya katse wayar kana shi kuma ya kutsa kai cikin gidan.

 

Dai-dai lokacin da a dai-dai-ta ya ajiye Khausar kudinsa ta basa tare da buɗe ƙaramin ƙofar dake maƙale da gate ɗin tashiga,

Batama lura da babban gete ɗin dake ɗan buɗe ba,

ganin mota a fake a harabar gidan yasa ta isa wajen kasancewar glass ɗin tink-tenk ne yasa bata fahimci da mutane aciki ba rawar kanta kuma ya hanata fahimtar alamun yanzu motar ta tsaya.

 

Jikin gefen mai zaman banza ta nufi tare da kallon fuskarta ajikin mirrow sai kuma ta juya manyan Idanunta kalaman Aunty Ruƙayya suka dawo mata kunne tana kama da Preety matsa pinch lips ɗin ta tayi tare da lasa kadan sai kuma ta juya manyan Idanunta.

M Jameel kuwa dake mazaunin Driver  murmushi ya saki domin  ya tabbata bata san da mutane aciki ba.

 

Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa zaune suke gaban boka Kar’uzu  cikin tsananin ɓacin rai da fushi Boka Kar’uzu ya buga musu wata razananniyar tsawa cikin sautin muryarsa mara daɗin sauti

bayan ya gama sauraron Hajiya Bunayya yace.

“Ai seda na faɗa muku aduk lokacin data fara aiki da maganin kada tayi alwala da sallah na tsawon wata ɗaya amma saboda taurin kai kuka bari tayi alwala tayi sallah shiyasa yake kallon fuskar ta kamar na ƙonennen Biri”.

Atsorace Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da itama ɗin Iran take kallo.

Sun kasa hafimtar sharrin boka na wasa da hankali da ƙarya sun kasa tuna sam bai faɗa musu hakanba a lokacin, su kasa aminta mgnar boka dubune babu gsky ko ɗaya sai yaudara da taɓewa.

 

Acan ɓangaren su Moddibo kuwa sake kallon madubi Khausar tayi tare dasa hannu ta gyara man lips ɗin ta sai kuma danna MP ɗin cikin Sa’a kuwa sautin waƙar BUGA ya fara tashi.

A hankali ta gyara tsayuwar ta, tare da fara jujjuya ƙugunta a hankali tana mai rausaya jikinta.

Zuwa tsakiyar waƙar kam fa da abu ya jiƙa, sai ga mayafinta bisa kafaɗarta gefe ɗaya, sosai take jujjuya mazaunenta tare da motsa dukkan jikinta, tana mai kallon kanta a madubi.

Sai kuma ta kalli Glass ɗin tare da ɗaura bakinta akai ta saki zazzafan  kiss muahhhh.

Shi kuwa Moddibo dake zaune idanu ya zuba mata tare da manna kumatunsa adai-dai glass ɗin sai kuma hakan yasa lips ɗinta sauƙa kan….!

 

 

FREE page sun kusa ƙarewa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ki biya 1k dinki ya isheki

 

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button