Labarai

Shin Konsan Abin da ya sa Amurka ke barazanar haramta TikTok a faɗin ƙasar ta Kowa?.

Sponsored Links

 


Shin Kasan Abin da ya sa Amurka ke barazanar haramta TikTok a faɗin ƙasar ta Kowa?. 

Gwamnatin Kasar Amurka ta ce dole ne a sayar da kamfanin TikTok ko kuma ya fuskanci barazanar haramta amfani da shi a faɗin ƙasar.


Ana zargin shafin wanda ake wallafa bidiyo a kansa, mallakin wani kamfanin China mai suna ByteDance, da janyo barazana ga ƙasar bayan tattara bayanai daga miliyoyin mutane masu amfani da shafin.


Manhajar TikTok ya tabbatar wa BBC cewa Amurka ta buƙaci a sayar da shafin ga kamfanin da ta ke so.


Kamfanin ya ce tursasa sayar da shi ba zai sauya yadda mutane ke amfani da shafin ba.


Fadar White House ba ta ce komai ba kan haka bayan da BBC ta nemi jin martanin su.


A tsawon shekaru da suka wuce, jami’an Amurka sun nuna damuwa cewa bayanan masu amfani da shafin ka iya faɗa wa hannun gwamnatin China.


A cewar jaridar Wall Street Journal, gwamnatin shugaba Joe Biden na buƙatar ByteDance ya cire kansa a matsayin mai TikTok domin ya fita daga hannun ƴan China.


Jaridar ta ce kwamitin kula da harkokin zuba jari na ƙasashen waje a ƙasar ta Amurka CFIUS, wadda ke kula da barazana da ƙasa ke fuskanta, shi ya bayar da shawarar cewa kamfanin ByteDance ya sayar da TikTok.


Wani mai magana da yawun kamfanin TikTok ya ce bai ki amincewa da rahoton jaridar ba, inda ya tabbatar da cewa CFIUS ya tuntuɓe shi.


Sai dai mai magana da yawun kamfanin ya ce an yayata rahoton sannan bai gane mene ne Amurka ke nufi da a sayar da shafin ga wani da ba ɗan China ba.


“Idan ana nufin kare barazana da ƙasa ke fuskanta ne, sayar da shafin ba zai magance matsalar ba: canza mamallakin shafin ba zai sa a takaita yadda ake samun bayanan mutane ba,” in ji mai magana da yawun kamfanin.


“Hanyar da ta fi dacewa na shawo barazanar tsaro da ƙasa ke fuskanta shi ne zama mai gaskiya, Amurka ta kare bayanan ƴan ƙasarta da na’urorinta”.

Leave a Reply

Back to top button