Hausa NovelsHausa NovelsTabarmar Kashi Book 2

Tabarmar Kashi Book 2 Page 12

Sponsored Links

TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 12

Gyaran murya ta danyi,idanunta akan
sãahar tana sake takowa kusa da da ita,daga
gefan lallausar sofa bed ta zauna tana
dubanta da kyau
“Maraba da shigowa mahmud JARMA
family,na tayaki murna qwarai bisa samun
wannan nasara da kikayi,sannan kuma ina
miki alhinin cewa….nasararki zata kasance
ta gajeran zango ce,sakamakon toufeeq ba mallakinki bane,dukka tsahon rainon
da nayi masa,na raineshi ne don ya zama
mallakina,wato mallakin ‘vata meenal haseena”
wani dan banzan haushi maganar hajiya
qarama ta saukar a zuciyarta,tayi qoqarin
tsaida hawayenta tana son fahimtar abinda
matar take fadi, idanunta na kallon tafukan
hannayenta ba tare data yaye rufin kanta ba

“Na jinjina miki yadda kika shirya komai ya
kuma tabbata lokaci kadan bayan tafiyata,to
amma ki sani,sauyawarki daga sunan nanny
boyi boyi zuwa ga matar auren toufeeq
babu abinda zai canza daga dokoki da
tsare tsaren gidan nan,fatan da nake miki
ki iya kiyayewa,sannan ki jirayi sakamakon
da zai biyo baya nan da kwanaki bakwai
masu zuwa,batun jikata fadeela,banason
ki fiya zaqewa cikin lamuranta saboda
shine samun lafiyarki,kiji kigi ji ki gani kigi
gani,na barki lafiya,asha amarci lafiya” tana
kaiwa nan ta mige,saidai taku uku kacal
tayi sãahar da zuciyarta ke a dugunzume
ta gaza daurewa kalaman hajiya qaramar,ta
tunzura qwarai,itama irinsa ce kenan? me tarin
Izza taqama da izgili,ashe ga inda ya debo dabi’arsa,lallai akwai wani boyayyen abu cikin taku da rayuwar matar cikin gidan,jikinta da zuciyarta sun gama aminta da hakan,adam ya yiwa rayuwa ruhi zuciya da gangar jikinta mugun horon da yasa nan da nan take iya fahimtar wani abu daga wasu mutane da dama.

“Inda kinsan abinda ke qasan zuciyata da baki bata bakinki kina wannan b’ab’atun ba.don haka na roqeki ki kama girmanki,zan nanata miki tun a daren farko na cikin gidan nan saboda daga ke har shi ba zamanku nazo yi ba” zallar madarar mamaki ya saukar mata.wani abu yayi mata tsawa a kanta,ta waiwayo tana son tabbatar da abinda kunnuwanta suke jiye mata,sai sukayi idanu hudu da saahar data dage hular kanta,wanda hakan ya bawa kyakkyawar fuskarta data sake wani sassanyan kyau saboda gyara data ci kamar babu gobe,da kuma haske da annurin
AMARCI dake sauka a fuska da jikin kowacce diya mace data amsa wannan sunan. Kamar ko yaushe yanzun ma kwarjini tayi mata,amma hakan bai hana hajiya qarama ritsata da ido ba,tana mamakin qarfin halin yarinyar.

Tabbas dole ta shiga cikin mutanen da take
targeting,ta yiwa kanta wannan alqawarin,sai ta gyada kanta ta juya ta fice a hankali daga dakin.

Qaramin tsaki säahar ta sauke bataii
zata zauna matar ta sanya mata wata
damuwa,ita sam bata cikin damuwarta bare
tace zata takura mata,ba ita ba,koda shi kansa
toufeeg din ba zata yarda ya zamar mata
damuwa ba bare wata ganwar mahaifi data
fuskanci zuciyarta akwai ayar tambaya.

Ta jima zaune a gurin tana saga da
warwarar yadda zata tafi da rayuwarta cikin
gidan,zata bawa kowa girma,amma sam ba zata dauki raini cin zarafi ko cin fuska ba. A
yadda taji gidan ya fara shuru ya tabbatar
mata dare ya fara yi,sai ta dubi agogon
dake jikin bangon dakin nata,fitsari takeji
sosai hakanan ta tabbatar wadan nan kayan
jikin nata ba zasu barta sakewa ba,don haka
ta miqe ta zare rigar saman,tanar doguwar
rigar wadda ta fidda shape dinta qwarai da
gaske,tun daga girji zuwa qugunta,ta tattareta ta nufi qofar da take tunani bandaki ce da zummar idan ta fito tasan yadda zatayi ta raba kanta da rigar itama yadda zatafi jin dadin kwanciya.

Ya kusa mintuna talatin zaune
cikin motar tasa bayan fitowarsa daga gurin maji,a yau addu’o’in da yasha a bakinta zai iya cewa bai taba jin makamantasu ba daga bakinta.farincikin da ya gani kwance a fuskarta ya taba zuciyarsa,duk yadda yake zaton ta dauki auren ya wuce nan,ta mashi wani babban matsayi da yayi imanin ba nan kusa ta ajiyeshi ba. Motar na a kunne ac naci gaba da aikinta,hakanan fitilun cikin motar. Sanye yake da wani baqin yadi da aka yiwa dinki tamkar na buzaven qasar nijer,dinkin ya zauna matuqa da gaske a jikinsa, kamar yadda baqin yadda ya kwantawa farar fatarsa ya sake fidda ainihin haske da kyanta tare da bayyana zallar hutu da in dadi hadi da kulawar da take samu,bagar sumarsa ta ainihin halfcast na nannade saman kansa tana bada wani sheqi me kyau da sassanyan gamshi kamar ko yaushe.
Waiwayawa yayi a nutse ya kalli tarin ledojin alfarma dake gefansa,wanda duka maji ce ta bashi tace ya shiga gurin iyalinsa dashi,don shi babu abinda ya riqo a hannunsa,duk da yanajin sanda abokansu ke hadawa sajjad,sunyi la’akari da cewa shi din tsohon aure ne,sunsan zai tanadi abinda ya kamata ba sai an gaya masa ba. Su kansu kayan qarin nauyi ne a wajensa,don ya tabbatar tilas ya sadasu da wadda aka siya saboda ita kodon cika kima da martabar maji.
Sashen nasa ya sake saukewa

idanunsa a karo na barkatai,sam baya gaunar shiga sai don babu yadda zaiyi,a duk sanda ya tuna cewa akwai wata mace a ciki me amsa sunan matarsa duk sai yaji kamar dai an takureshi ne kawai. A karo na gaba da qarfi yaja tsakin hadi da balle murfin motar a zafafe ya fito,jibril dake jingine jikin motar ya qaraso da sauri,kafin yace komai toufeeq din ya rigashi magantuwa

“Ka gayawa Jacob ya shigomin da kayan cikin falo, ka kashe motar na sallameka,sai kuma da safe”

“Sir,da safe kuma? na dauka zakaje hutu ko?, ko don madam” jibril din ya fada zuciya daya yana murmushi,saidai kallon da toufeeq din yayi masa ya tabbatar ya tafka baranbarama,sai yayi saurin jan bakinsa ya tsuke yana yunqurin bude daya side din ya fiddo kayan kamar yadda ya umarta.

Hannayensa zube a aljihun wandonsa yake qarewa falon kallo,ya sake jan qaramin tsaki, komai nashi sajjad ya canza masa,duk da kyawun da sassan ya qara ya kuma zuna favourite colours dinsa,to amma shikam bai shiryawa dukka wadan nan abubuwan ba. Da kansa ya gaji da tsaiwa,ya sunkuya ya kwashe kayan da jacob ya shigo masa da su,ya nufi hallway din da zai sadashi da dakunan baccinsu,ransa yana sake baci,komai a yanzun sai yayi sharing da wani,gurin mallakinsa ne a baya,shi daya yake shiga yayi rayuwarsa,idan zao shekara bai fito ba motsin kowa bazai dameshi ba,amma a yanxun bashi da wannan tabbacin.

Tsaye tayi a gaban madubi bayan fitowarta daga toilet din tana kallon fuskarta data fito sosai saboda qananun kitson da aka zauna aka yarfawa gashinta me santsi,abinda zata iva cewa tsahon rayuwarta ba zatace ga lokacin da irin hakan ta faru ba,hasalima kwata kwata kitsonta baya wuce manyan kalba guda hudu,saboda tsaho da santsin gashinta, amma a yanzun an samu wata gwana jarababbiyar iya kama gashi ta kitse mata kan tsaf,kuma hakan ba qaramin qarawa fuskarta kyau yayi ba,jelolin kitson gaba daya sun kwanta sosai a gadon bayanta har tsakiyar bayan nata. Hannu ta sanya tana qogarin zuge zip din rigarta wanda afifa ce dama ta zuge matan,da qyar hannun nata yakai,ta fara jan zip din ya fara saukowa,har yakai rabi taji an taba qofar,saita tsaya cak tana kallon madubi dake haska mata bakin gofa,tanason tantance qofar dakin nata aka taba ko kuma sauran qofofin dake wajen.

A hankali qofar ta bude,ya bayyana daga bakin qofar da daurarriyar fuskar nan tasa,tashin farko qamshin da dakin ke fiddawa ya marabci hancinsa kafin a sannu idanunsa su suka a bayanta da fara qal don brassiere dinta ta bayyana. Sosai ta razana don batayi tunanin ganinsa ba wannan lokacin,tunawa tayi da zugaggen zip dinta data tabbatar a vadda ya sauka har brassiere dinta za’a iya gani,wanann tunanin ya sanyata juyawa da sauri kamar numfashinta zai dauke ba tare data tuna yadda rigar ta fidda tudun qirjinta ba da kyau.

Kamar daukewar majigin tv,gushewar baya zuwa bayyanar qirjinta ga idanunsa duka sun faru cikin abinda baiyi damanda second uku ba,bazaice ga yadda akay ba ya samu idanunsa dumu dumu suna kallon qirjin nata ba da suke a cike,farar fatar dake lullube ko ta ina ta jikinta ta bayyana daga samansu tana nuna mizanin cika da suke da ita. Wani mugun fusga ya yiwa numfashinsa da idanun nasa ma gaba daya yana sanya qarfin zuciya dana ruhi gurin janye kallonsa daga kanta. Yayin da sãahar din gaba daya ta qarasa rudewa,ta fisgi dankwalinta dake ajjiye saman madubin ta yafa ranta a bace.

Tamkar baiga komai ba ya sanya kansa cikin dakin yana furta sallama can qasa,kanshi tsaye yake takowa dakin tamkar dai mallakinsa bawai nata ba,bai tsaya ba har sai da ya isa kusa da bedside drawer ya zube dukka ledojin a kai ba tare da ya dauki ko daya ba,sannan ya juya abinsa zai fice daga dakin. Kasa jurewa tayi,tadan daga muryarta kadan

“Ba kowanne daki bane mallakinka a yanzu,kafin shiga kowanne daki a gidan nan ya zama dole ka nema izini” tsaiwar mashi maganar tayi masa bisa kansa,har ya rage saurin tafiyar tasa,sai kuma yaci gaba da ficewar,saboda wata kasala dake sauka a kowanne sashe na jikinsa,muddin kuma yace zai tsaya cewa wani abu,a matsayinta na me aure na biyu dole zata fuskanci wani sauyi tattare dashi, wanda hakan mugun abun kunya kasawa da kuma gazawace a tattare dashi but yayi alqawarin zai saita mata bakinta da wasu dabi’u nata,bazai yarda da rashin girmamawa ba,she can live duk yadda taso,amma dole tasan girmansa.

Tsuka tayi ta murguda bakinta saboda baqincikin da ya cikata,batasan tsautsayin da ya sanyata barin qofarta a bude ba,bata taba kawowa wai zai shigo ba wannan shine dalili,amma dole daga wannan karon ta tabbatar bai sake shiga mata daki ba. Har tayi banza da ledojin daya shigo dasu,sai kuma taga duk abinda ta bari ya lalace zai shiga sahu ne na almubazzaranci.

Short note din data gani jikin wata
leda ya bata tabbacin babu abinda ya siya da kansa ko daya,dukka sagon maji ne.
Murmushi ya subuce mata,tana qaunar mata sosai har cikin ranta,sonta majin take da gaske har hakan baya iya boyuwa,ta miqe ta adana komai ta dawo ta rage kayan jikinta ta kwanta.
[15/09, 5:29 pm] Laila Abdulqadir: “HUGUMA*

•_TABARMAR KASHI_*

Leave a Reply

Back to top button