Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 1

Sponsored Links

 

 

  🌱TUMFAFIYA
BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

 

  🌱TUMFAFIYA
SIRIN KI     SAI ALLAH  ,,,,,,,,,,,

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

 

1️⃣

 

YA ALLAHU,,,,,,,,,,

 

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
BA TARE DA HAKKIN KOWA A KANKI BA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI
AIKA 2254380105 KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN ,,,,,,,,

 

YAR UWA DA BAZANKU MUKE RAWA IDAN BA MAKARANTA BABU RUBUTU
GODIYA GAREKU HAR KULLUN DA IRIN GOYON BAYAN DA KUKE BAMU MUKE CI GABA
KULLUN,,,,,,,,

 

    Matashine ke
tafene da sauri a cikin tashin hankali kamar yadda kowama a unguwar yake cikin
sauri dan yanayin da gari ya nuna idan da rabo ruwane zai iya gwaucewa a ko
wani lokaci a garin.

    Saidai shi kana
ganin shi kasan yanayin shi baya cikin walwala
a lokcin don yadda yake tafiyan zaka iya fahintar hakan gareshi .

    Sauri yakeyi a
cikin tafiyan shi irin na mazan dake da karfin kira da zatin karfi inda yake dan
hadawa da sarsarfa don kada hadarin daya game gari yana shirin saukoda ruwa ya
sameshi a hanya lokacin.

  Yayafi akafara dan
sakewa haka yasa ya kara saurinshi a lokacin ba komai yakewa sauri haka ba sai
don abu biyu zuwa ukku na farko don kada yan tufafin dake jikinshi su jike dan
ko a gobe su yake da niyar mayarwa a jikinshi
da kuma yar jakkar shi da yake adana takardun karatunshi a ciki wanda ke
rataye a kafadan shi.

   Sai  abuna biyu tunawa da kakan shi Dije dake gida
ita kadai a wanan lokacin yasan ba kafane gareta ba a yanzu saboda tsufa daya
fara kamata kafan na dan rike mata lokaci lokaci don ko da zai fita da safe ya
barta dashi dan ya taso mata haikan yana mata ciwo a cikin yan kwanakin nan
sosai.

    Da sallama ya fada
gidan idonshi ya fara tozali da Dije dake tsakar dan gidan nasu tsaye tana
tafiya da kyar tana kokarin kama dabbobin dake ta kuka saboda yanayin hadarin
da suka gani suma a lokacin.

   Da sauri ya karasa
inda take ya karbi dabbobin daga hannunta ya nufi dan rumfar  da ake dauresu ya fara turkesu ita kuma tana
kokarin juya zuwa daki take mashi sannu .

    Yana ciki yana
dauresu yaji saukan ruwan da karfi wanda kafin ya fito ruwa ya fado sosai ta
yadda sai ya jika jikinshi dole don karfin ruwan.

    Dakin kwanan dijen
ya nufa da sauri ya fara walwale ledan da suke tare ruwan sama dake diga a
dakin idan ana ruwan sama sai  sukanyi
wanan dabaran a daura leda koda ruwan zai zobo ba zai taba yan kayan dake dakin
ba sai ya tsaya iya leda kawai.

   Bayan ya gama daura
ledan ya dan fara samun natsu a lokacin kafin ya kai hannu saman rigan jikin
shi da ruwan ya riga ya taba ya fara balle bottom din rigan a hankali yana
kallon yadda ruwan saman ke zuba.

   Kallon rigan yayi
ruwan saman ya riga ya taba duk da baiso hakan ba a lokacin saboda ita din yake
da niyar mayarwa idan Allah yakaimu washegari zai fita.

    Duban ruwan yayi
daga inda yake tsaye a cikin dakin   yaga
yadda ruwa da iska ke zuba da karfi lokaci guda irin na tsakiyan damana din nan
mai barna ga mutane da kaddarorinsu.

   Ajiyan zuciya ya
sauke don yasan yau akwai barna idan ba Allah ya gyara ba ke nan dole haka ya
ratsa ruwan ya fito a guje zuwa dan karamin dakin shi da yake kwana a cikin
gidan tsohuwan kakan nasa da ita ke nan masa tillo dake kula da komai nasa .

   Kayan ya sauya tare
da baza wanda ya cire a jikin shi zuwa wani tsohon gajeren wandon shi da wata
riga nasa daya tsufa har ya dan fara cacakewa don tsufa amma haka yake amfani
dashi idan yana cikin gida.

   Komawa yayi ya
rakube a wuri daya kafin ya fara bin dakin da duba na dan lokacin yana sauke
ajiyan zuciya a hankali tare da kara kai kallonshi gun kofa yana kallon yadda
ruwan ke zuba da karfin Allah.

    Wani ajiyan zuciya
ya kara saukewa a hankali tare da lumshe idanuwan shi yana ci gaba da tunanen
kuncin rayuwan da sukeyi a gidan dashi da kakanshi Dije.

   Baida kamar Dije
din yanzu a duniya don da Dije ya bude idanun shi da Dije ya taso a rayuwanshi
yau duk abinda ya zama Dijene silla itace gatanshi a duniyan nan.

    Don itace uwa uba
kaka a gareshi tun tasowan shi bai san kowa na kusa nasa ba idan ka debe Dije
dake bashi kulawa irin na mahaifa don a tare da ita ya taso ya bude idon shi.

    Wani irin tsawa
aka sake lokaci daya tare da walkiyan da yai sanadiyar budewan idonshi da sauri
yana karanto addua a bakin shi subbuhul kudus wal,mala,ikatu walruhu,,,,,,

    Ihun da yaji kamar
a makwabtansu yasashi bude idon da sauri tare da kara dan firgitashi lokaci
guda don yana ji yasan ihun bana lafiya bace.

   Don kusan haka suke
fama duk shekara sai sun samu wanan matsalan ruwan saman kasancewa gidanjen
unguwar duk tsofin ginene ne irin nada can baya.

   Wanan yasa duk
shekara idan ruwan sama ya fado hannunsu a gaba yake don fargaban ruwan sama
yadda zai kasance masu yawancin gidajen basu da sukuni idan ba sunga an dauke
ruwa ba.

   Gashi talauci irin
na yan arewa yayi masu katutu ba zarahin gina wani a garesu sai wanda Allah ya
tallafawa ya samu wani budi zai dan yiwa nasa kwaskwarima ko a fita ciki.

  Wanan yasa ake kiran
unguwan da tsohon gari don mafi yawan gidajen dake unguwar duk gidajen
tallakwane a wurin matasa da masu kudi
sunfi komawa daga bayan gari

 suna ginan su irinna
zamani.

    Kakan wanan
matashin gidanta na daga cikin jerin gidajen dake cikin wanan  unguwar ta tallakawan dake fama da barazanan
ruwan saman a duk shekara.

   Duk da karfin ruwan
saman da iska da akeyi a lokacin bai hana yan unguwan jin kururuwan wasu
mazauna unguwan da iska da ruwan saman yayiwa barna a ranan .

   Haka ya jawo
hankalin sauran yan unguwan suka fara fitowa daga gidajen su don zuwa bada
agaji kamar yadda suka saba bawa junan su lokaci lokaci.

    Dakin kakanshi ya
fara nufa inda ya samu duk da ledan daya daura mata don tare feshin ruwa dake
diga a dakin yau karfin wanan ruwan bai tsaya a iya ledan ba kwarai ga tsohuwar
tsugune tana faman tara yan tsummakara tana tare ruwan  dake dan dinga daga saman dan rufin kwanon
dakin wanda duk kwanon ya riga daya tsufa sosai a lokacin saboda dadewan da
yayi.

    Ihu nake ji a waje
ya fada yana karban abinda take kwasan ruwan dashi dake hannunta bata kai ga
mika mashi ba, take fadin jeka kakai masu agaji saboda Allah.

    Tun ganin yadda
aka hada hsdarin nan nasan yau unguwar nan sai yadda Allah yayi damu don wanan
ruwan da karfi ga iska yake sauka ji
dakin na  duk da wanan dabaran
saka mai ledan da kayi amma sai zuban ruwa yakeyi yau din nan.

   Juyawa yayi da
sauri ya fice ya barta a duke tana magana ita kadai yana fita abinda ya gani ya
kara daga mai hankali don ruwane ko ina a kwance zakace a tsakiyan rafi
gidajensu yake a unguwar.

   Da sauri ya kara
kai kallon shi gefen hagu gidan malam Tanimu mai faskarene yayi flat kamar ba a
taba gina a wurin ba.

   Gasu tsatsaye sai
ihu iyalinshi keyi suna neman taimako ga jama,a da suka fito don kawo masu
agaji ga kururuwan neman agajin da sukeyi.

    Hankali tashe ya
nufi wurin a gigice da alama akwai wani da ginan ya rufta dashi don yadda suke
kururuwan taimako daga jama,a.

    Gashi sai su biyu
yake ganin sun fito don basu agaji don kowa na cikin gidansa a lokacin ya kasa
ya tsare ana duban hukuncin ubangiji.

  Malam suke fadi
kawai don matar gidan daga ita sai zani daura gaba kawai a jikinta sai kai
gwauro da mari takeyi a tsakiyan rubaben gidan nasu.

  Dakin ya nufa
gadangadan ya fara tono kasan dake wurin a cikkn sauri irin na bada agajin
gagawa ga mutum ganin hakan suma suka taimaka mashi har Allah ya taimaka suka
fara hango malam Tanimu din da kasa ya rufeshi a some suka zaroshi baya cikin
hayacin shi.

    Duk sun zuba ido
suna kallon yadda yake bashi taimako a cikin gwanewa da hikima sai gashi ya
fara dan motsi da hannayen shi a daidai lokacin aka kara sake  wani cida mai karfi da walkiya.

    Ruwane masu karfi
suka kara biyowa bayan hakan wanda yasa hankalin kowa kara tashi don dare
sukewa gudu Allah ya taimaka a lokacin yamma ne duhu bai riga dayazo bako.

    Ganin mutane sun
fara watsewa suna komawa gidajen su saisu da abin ya shafa sai Amadi da yake
kan malam din yana bashi taimako.

   Karan ruwan daya
tun karo unguwar daga wani bangare na cikin gari ya kara daukan hankalinsu ya
dago kai yana fadin wani ya taimaka min mu kamashi mubar wurin nan.

   Sai gani yayi daga
shi sai iyalan malam Tanimu din makwacin su kawai a wurin duk saura sun shige
gidajen su a lokacin da taimakon iyalan malam din suka sam u suka kamashi zuwa
dan kangon gidansu.

    Su samu su fake
har ruwa ya dauke asan abinda za ayi saidai suna tun karan cikin gidan kakanshi
Dije ce a waje cikin ruwa yana dukanta hankali tashe tayi tagumi da hannu daya
tana kallon ikon Allah.

    Ganin su yasa ta
nufosu hankali tashe tana fadin Amadi dakin nawa rawa yake yana jijiga kamar
zai tashi sama yasa na fito na  tsaya
nan.

   Duban dakin yayi
hankali a tashe kafin ya juya inda malam tanimu yake tsaye rabin kafadanshi duk
a jikin Amadi din yake bai ajeshi ba saidaya danganashi da dakinshi har kakan
nasa suka kutsu gaba dayan su sun zubawa saurata Allah ido.

    Manyan duwatsu ya
dinga mirginowa zuwa bayan dakin har ya samu ya tangale ginan tsohuwan dashi ya
koma ya zauna daidai ya daina rawa.

   Sai lokacin ya
sauke ajiyan zuciya kafin ya samu shiga dakin tsohuwar ya fake yana sauke
numfashi a hankali wurin zama yaiwa kanshi saman kujera yar tsugunno dake dakin
aje ya fara bin dakin da kallo yana tausayawa halin rayuwa irin nasu.

  

Duk ruwan saman da ake shekewa su sam gidan basu sanma anayi
ba saboda yanayin ginan nasu na zamani da bai nuna hakan idan baka fito wajen
gidanba ba zaka sanda ana wanan irin uban ruwan mai karfi haka ba garin.

   Sai sha,anin su
sukeyi a cikin gidan basu san wani wahala ko tashin hankalin da marasa karfi
suke ciki a garin ba.

   Hjy saude ne
tashigo dakin yar nata tana saye da hijjab a jikinta mai ruwan toka farace mai
dan matsaksicin tsawo mara jiki kallo daya zakai mata zaka gane bata da wani
shekaru mai yawa.

   Idanun ta akan yar
nata dake kwance tana karatu duk rabin jikinta a waje ya kware don yar rigar
zama gidace doguwa a jikinta.

    Haba mamangida ace
tun safe mutum yana kwance haka ko dan lekowa waje ina jin yau bakiyi ba tunda
safe watau ke dai bakya jin magana dai maamah.

    Wace aka kira da
Maamah din ta dago kai tana murmushi tana dan dagowa daga kwancen tare da fadin
wallahi yanzun nake fadin in fita in ganki sai karatun test din nan ya dauke
min hankali.

   Kiyi hakkuri ummah
ta fada tana sauke kafafuwanta daga saman gado uwar tabi fararen kafafuwan yar
nata da kallo tana fadin yau part din maman ku bakije kin gaida ita ba.

   Irin wanan halin
naki take na ko in kula bana son shi kisa ana dauka nice ke rabaki da mutane ko
nake hanaki shiga yan uwa sam bana son irin wanan halim mutum ya dinga baya
baya da kowa.

   Ummah yi hakkuri
yanzun nan zan fita na gaidasu ai karfe nawa kike tsamani yanzu din duban
lokaci tayi ta hanyar daga kai ta kalli agogon dakin daya nuna biyar da rabi na
yamma lokacin.

    Au ashe da sauran
lokaci amma naga wurin yayi duhu haka mana ruwan sama ake yau sosai a wajen
kina nan ciki baki ko san abinda gari ke ciki ba wanan irin rayuwan baida kyai
maamah  ki dinga shiga yan uwa ki daina
nisanta kanki da kikeyi da yan uwan ki bana son haka ummah ta karasa cikin nuna
bacin ranta.

   Ummah kiyi hakkuri
ta juya ta fice daga dakin ban dakin ta shiga ta gyaro fuskanta kafin ta fito
zuwa part din maman nasu sai a lokacin take jin yanayin sanyin ruwan saman da
akeyi yana ratsa jikinta a hankali.

   Tafiya takiyi kamar
bata son taka katsa ta nufi wani dogon corridor daga barin gabas wanda ke
kallon nasu part din kofan falon a bude yake haka ya bata daman sa  kai ta shiga da dan sirierin sallama a bakin.

    Duk suka juyo suna
kallonta bayan sun karba mata direct wurin matar dake zaune saman carpet ta
nufa har kasa takai kafin tace mama ina wuni.

    Da mamaki a fuskan
matar take fadin Maamah kina gidan nan dama ko a can wanan ruwan ya sameki haka
?

    Dan murmushi ta
sake kafin ta kai zaune kusa da matar tana fadin ai yau ban fita ko ina ba ina
ciki ina karatun test da zamuyi gobe idan Allah ya kai mu.

   karatu tun safe
mutum yana kwance a daki wata kila ma ko abinci bakici ba tundazun son
shiririra dazun nan nake maganan ki da ake fadin ruwa yau akeyi sosai garin.

    Wallahi ina gida
mama ban fita ba ta fada tana gyara zama kallon ganyen dake gaban maman tayi
cike a plate daya ya sha kayan hadin gargajiya zogalene da kuli kuli sai su
tumatur da albasa attarudu da aka zuba a sama.

    Zakici ke nan uwar
ta fada ta dan daga kai alaman eh a hankali zubo mata Yasmin matar ta fada wace
aka kira da Yasmin din ta tabe baki tana fadin mama ba yawafa kuma ai kin aika
masu part din su dashi.

   Ina ruwan ki wanan
din dai take son ci don haka ki dauko plate ki zuba mata ko kuma barshi nasan
halin cin  nata,  ta dai saka hannu a nan muci tare kawai.

    Duban hannun nata
tayi kafin muryan maman yace kin san dai ba a cin abinci da cibi sarkin tsabta
tashi ki wanko hannun kizo muci matar ta fada.

  Mikewa tayi zuwa
kitchen din part din bayan tafiyan ta matar ke fadin Yasmin bana son wanan
halin da kuke son nunawa yarinyar nan wanan yasa yanzu take yawan jan baya damu
na sani don ba halinta bane haka.

   To mama ita din
sa,arkice da zata dinga manne maki ko yaushe taje gun uwarta mana amma sai ta
dinga wani shishigewa mutane a daidai lokacin yarinyar ta fito daga kitchen
din.

   zama tayi zuka
zauna da mama din tare sukaci ganyen suna da hira jefi jefi wanda baifi sau
hudu da takai ganyen a bakinta tana fadin ta gode ta koshi ta mike ta koma
kitchen din ta wanke hannu sai gata da wani ruwa a roba ta kawowa matar tana
fadin mama ga ruwa idan kin gama ki wanke hannun ki.

   kai maamah badai
tsabta ba shiyasa nake son ki ai bata zauna ba don ganin magariba ya kawo jiki
tayi masu sai anjima ta koma part din ida nan ma bata zauna ba yan gyare gyare
tayi kafin ta shige daki yin sallah zuwa lokacin sanyin damana ya hade dana
iskan dake kadawa ya kade ko ina yana shiga jikin bawa.

   Bata kara leko
wajen ba sai washegari don tasan tana da exam a ranan don haka ta tashi da wuri
ta shirya a falon su ta samu mahaifiyat ta da mai aikin suna magana yanayin
fuskan mahaifiyan nata ys sauya.

    Ummah ina kwana ta
fada daga bayan ta hakan yasa uwar dan juyowa tana kallonta tare da amsawa take
fadin kin fito ke nan ko me eh ummah ina son na isa da wuri don na dan taba
karatu a can.

    To ki karya don
ba,a fita gida hakana ba, a karya Tani don Allah miko mata ruwan zafi ummah ta
fada cikin rashin walwala a fuskanta har lokaci.

  Ummah wani abune ya
faru  lokacin uwar ta juyo tana fadin
bari maamah ruwan nan najiyane yayi barna a cikjn gari harda rasa rayuka mai
aikin ce ta fito tana fadin hjy inaga ashanan mu ya karefa.

   Haba Tani na hanaki
yin hakkan idan abu zai kare ki fada min don Allah na sayo ummah barin wuce
kawai kada in makara idan naje can zan ci a capterial.

   Akwai kudi a hannun
kine eh wanda Abba ya ban banyi komai dasu ba suna nan ta fada fatan alheri
uwar tabi yar dashi ta fita duban part din mama tayi yana rufe ba a bude ba har
lokacin yasa ta fice daga gidan kai tsaye.

   Komawa ummah tayi
ta zauna bayan fitar yar nata da take bi da adduan fatan alheri akoda yaushe al
rayuwan ta.

   Kasancewan su su
hudu tillo suke a wurin ta auren ta shekara goma sha takwas kafin Allah ya
azurta ta yarta Zarah wace taci suna uwar mijinsu Fatima wace ke raye har har
yanzu da rayuwanta .

    Rashin haihuwan
ummah yasa bayan shekara daya da aurensu aka matsawa mijinta ya kara aure ida
ya auro mama bata take wata ba ta samu ciki a gidan wanan ya jawowa mama dauka
sosai ga kowa.

   Nan soyayyan duniya
ya hau kanta daga mijin har yan uwan miji ta zama abin lele a garesu sai ya
koma kamar itace uwargida a gidan ba ummah ba.

   Sai gashi wasa wasa
har ta haifi yara maza biyu sai mata uku sai kuma maza   da suke sa,an zarah a yanzu wanan yasa ummah
ta sakewa mama duk wani girma dama kuma ita mama ta girmi ummah din don ita
saida ta tsaya ta kare secondary din ta lokacin ana form five afita secondary.

    Lokacin da Ummah
ta gane tana da ciki a jikinta tayi ta boyon cikin jikinta na zarah lokacin don
tana gudun azo daga baya ace marudiyace ya kasance ba cikin bane jikinta har
saida cikin ya fito fili ya nuna kan shi ga jama,a .

   Nan tsegumi ya fara
tasowa wurin mutane har zuwa lokacin haihuwan zarah da wasu ke kiranta da Tuni
don dadewan da akayi ba a sameta ba lokacin.

Leave a Reply

Back to top button