Yankan Karfe 3-4
*💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE ⚔️⛓️💫*
~Written By~
*Hanyluv✍🏻*
*Free page*
Page 3 & 4
Tashi tayi tare da fizge hannun ta a fusace tace “wato da ran Daddyn ka ya ɓaci gwanda nawa ya ɓaci!! Okay fine! Yanzu na fahimci me kake nufi!” da sauri ya tashi yana girgiza mata kai tare da ƙoƙarin riqo hannun ta, dakatar da shi tayi ta hanyar ɗaga mai hannun,
“kar ka matso inda nake,”
“Mami Please!!”
“Saheel!!! Soyayyar da nake nuna maka shi ne lefi na koh? nuna bana son kayi nesa dani shine lefi na koh? Daddyn naka da kake ta magana akan shi ina yake? Kasan da baya garin kuma sam ba nan kusa ze dawo ba! Koh kiran ka yayi ka faɗa mai kana can ina ze sani! Akwai wanda ze kira ya faɗa mai ne? Amma tunda tafiyan kake so kaje Allah ya kiyaye hanya!!! I will never ask for something like that again!!” da sauri ya riƙo hannun ta a firgice,
“Mami dan Allah ki daina magana irin haka! Na fasa tafiyan, koh da koh hakan ze sa Daddy ya fushi dani mafi tsanani! Ni dae bana so ki ƙara magana irin wannan please and please Mami am begging you, ki yafe mun! kinji!,” ƙin juyowa tayi, zagayowa yayi ta gaban ta yasa hannu yana ɗago fuskar ta,
“Mami dan Allah kiyi haƙuri, i can’t bare your anger🙏🏻” shiru tayi na ɗan mintina sanna tace “naji na haqura amma kar ka ƙara yi mun irin haka! duk abun da nake yi saboda ina son ka ne Saheel, Ni fah Mahaifiyar ka ce!” jinjina kai yayi,
“Mami i know! duk duniyan nan babu wanda ya kai ki sona, Insha Allah bazan ƙara yin abun da ze ɓata miki rai ba,” murmushi tayi sannan ta jawo hannun sa suka zauna a gefen gadon na ta…
_______________________________
Tafe suke Ni’imah riƙe da hannun Gidado se zuba musu surutu yake yi, Ni’imah se dariya take yi ita kuwa Nimrah ta haɗe rai se hararan shi take yi,
“kai dalla rufe mana baki! Duk ka bi ka cika mutane da surutu!!,” Nimrah ta faɗa tana zabga mai harara, shagwabe fuska yayi yana kallon Ni’imah,
“Adda Ni’imah kin gan ta koh!”
“rabu da ita Gidadon Daadah ai ba ita kake bawa labarin ba Ni kake bawa kuma ina jin daɗin shi,” Ni’imah ta faɗa tana shafa kan Gidado, haka suka cigaba da tafiya Gidado na ta zuba surutu ita kuma Ni’imah se biye mishi take yi har suka ƙarasa gida, da sallama suka shiga suka samu Daadah a gaban murhu tana hura ice,
“Haba Daadah meyasa baza ko bari mu dawo mu hura ba!” Nimrah ta faɗa a marairaice, ita ma Ni’imah shagwabe fuska tayi tare da cewa
“Ai kam dae Daadah ki daina cewa zaki bawa kanki wahala! Meye amfanin mu toh!” murmushi Daadah tayi tace “toh ai ba komai bane dan nayi dan nasan idan kuna nan bazan yi ba ae, kuma ma yana da kyau na dunga motsa jikin nawa ae!”
“Eh duk da haka dae Daadah gwanda kiyi wani aikin ba na hayaƙi ba,” Nimrah ta faɗa tana fitowa daga ɗaki, ƙarasowa tayi ta amsheta ta cigaba da hura icen, tashi Daadah tayi ta koma kan tabarmar da Ni’imah ta shinfiɗa, zama tayi tare da janyo Gidado tana shafa kanshi,
“Daadah bari na matsa miki ƙafafuwan naki!” Ni’imah ta faɗa tana matsowa tare da riƙo ƙafafun Daadahn ta fara matsa mata,
Nimrah bata jima ba ta gama ɗumama ragowar shinkafan jiya da ta ragu, zubo musu tayi gabaki ɗayan su, dama da safe haka suke haɗuwa su karya harda Abboh se dae idan baya nan, bayan sun kammala ta kwashe kwanukan ta kai wajan wanke² tare da wanke su sanan sannan ta dawo ta zauna suka cigaba da fira,
“Nimrah kuje gidan Gwaggo idan ta tara ƙanzon ta bamu!” nan da nan Nimrah ta canza fuska ta koma kalar damuwa tace “Daadah ni dae da za aji ta tawa da an haƙura da amsan ƙanzon nan wanda ake bamu a wulaƙance, ki ga fah wancan karan da muka je baki ga cin mutuncin da ta yi mana ba, harda ce mana awakai!” ta ƙarashe maganar cike da ɓacin rai, murmushi Daadah tayi wanda ya zama ɗabi’an ta tace “Nimrah! Ita rayuwar duniya haƙuri ake! Ba ka fushi da abunda ba ka dashi, haka zalika duk wulaƙancin da mutum ze yi maka in dae ze ciyar da kai toh ya fiye maka kowa, don haka komai Gwaggo zata yi mana kar ku taɓa bari ma ya zauna a ranku balle har kuji haushin ta wallahi koh kaɗan bana ganin lefin ta!” jinjina kai Nimrah tayi ba tare da tace komai ba, ita kuwa Ni’imah dama irin Daadah ce kwata² bata da zafi kuma ga haƙuri, Nimrah ce mara haƙuri,
Tashi suka yi suka ɗakko hijaban su da ɗan ƙaramin buhu sannan suka fito,
“Daadah nima zan bisu gidan Gwagg..!” Gidado ya faɗa a shagwaɓe ai kuwa be dire ba Nimrah ta tari numfashin shi cike da masifa,
“Ai baka isa ba babu inda zaka bi mu! Mu sa’o’in ka ne? da zaka wani ce zaka bi mu, koh idan riƙe mana buhun kake yi idan ka bimu?”
“Haba mana Nimrah meye dan ya bimu! Ae koh ɗan surutun ma da yake mana shi kanshi aiki ne ba se ya riƙe buhu ba,” Ni’imah ta faɗa tana murmushi Daadah ta cafe,
“Kyale ta dae Ni’imah, ni har tsoro ma nake na mutu na bar Nimrah da Gidado nah don naga alaman baza ta iya haƙuri dashi ba se dae na damƙa shi hannun Ni’imah dan ita zata fi iya kula mun dashi,” nan da nan jikin Nimrah yayi sanyi don ita idan da akwai abun da ta tsana shi ne Daadah ta danganta kanta da mutuwa,
“Daadah ni bana so naji kina magana haka Insha Allah kuma baza ki mutu yanzu ba se kin ga jikokin mu, ɓata mun rai yayi fah shiyasa nace baze bi mu ba,” ta faɗa a sanyaye, murmushi Daadah tayi tace “Toh Nimrah koh ma dae shekara nawa zan ƙara ae dole dae na mutun koh?kuma ma koh me Gidado yayi miki hakuri zaki dunga yi, ba ki ga yanda Ni’imah ta ke yi dashi bane? A koh da yaushe ina faɗa muku ku riƙe haƙuri toh wallahi koh da ba ma gidan duniyan nan zaku iya zama da kowa, shi me hakuri be taɓa taɓewa!!” sosai Daadah tayi musu nasiha me rasa jiki, haka suka fice ta raka su da albarka..
Da sallama suka shiga gidan Gwaggo, tana zaune a tsakar kan tabarmar ita da ƴarta Juwairiyya ta tasa kayan kwalliya a gaba se tsantsara kwalliya take yi zata fita talla,
”Mtwssss!!” Juwairiyya ta buga tsaki tana kawar da kai, sosai ran Nimrah ya sosu amma se ta fuske, suka ƙaraso tare da gaishe da Gwaggo,
“Lafiya!” ta amsa a wulaƙance tana kawar da kanta gefe,
“Gwaggo wae Daadahn mu ce tace muzo idan kin tara ƙanzo ki ba m..” Nimrah ba ta ƙarasa ba ta katse ta,
“Tunda na zama bawar uwar ku baa! Koh da yaushe se dae ta turo ku sungum² ku taho kuyi mun cirko² wae in ba ku ƙanzo se kace ni na ajiye ku! Shi Uban naku meye amfanin shi? Koh kawar ciki ya iya ɗirka mata ni kuma na dunga ci masa da su! toh wallahi na fara gajiya ba zan iya ɗauka ba! har gida naje na bata shawaran akan ta ɗaura muku talla tace ita baza ta iya ba wae ƴaƴa mata anfi so a killace su, toh ae gashi nan se ta cigaba killace kun sannan ku koyi riƙe yunwa! Mu kuma da muka kasa killace ƴaƴan namu a ga wani abu ya faru dasu!!!!” cafewa Juwairiyya tayi,
“Inna toh ke ina ruwanki ma da zaki je kice ta ɗaura musu talla! Ke wani ne yazo yace ki ɗaurawa taki ƴar! ki bari idan suka ga wahala zata kashe su baza ma su jira wani ya basu shawara ba!,” zuciyar Nimrah kawae tafarfasa take yi nasihan Daadah ce kawae ta hana ta tanka musu, itama Ni’imah sam bata ji daɗin zancen ba amma da yake ita me haƙuri ce se ta ƙaƙaro ɗan murmushi tace “Gwaggo kiyi haƙuri! Tabbas mun san kaf ƙauyen nan babu wanda mana abun da kike yi mana! haka zalika koma me zaki faɗa baza mu taɓa ganin lefin ki ba! Kuma Insha Allah koh nan gaba mu ma zaku yi alfahari da m..”
“wanna alfahari za ayi daku? Ku da babu alaman cigaba a rayuwar ku! Ai yanda kuka zo a tsiyan nan toh ina me tabbatar muku a tsiyan nan zaku ƙare! Baza ku taɓa arziƙi ba daga ku har ƴan iskan iyayen ku!!” ta Gwaggo ta katse Ni’imah cike da masifa, wani abu ne ya tasowa Nimrah taji ae an kai matakin da baza ta iya haƙura ba, cikin zafin rai tace “shi arziƙi na Allah ne, shine yake tsiyata bawan shi a duk sanda ya so haka kuma ya azurta bawan sa a lokacin da ya so! Dan haka bawa be isa ya yankewa ɗan uwansa ze yi arziƙi koh baze yi ba kuma idan Allah yayi mana arziƙin idan mutum ya isa ya ƙwace, kuma iyayen mu ba ƴan iska bane!!” tana kaiwa nan ta miƙe tare da karkaɗa hijabin ta ta fice daga gidan ta bar su Gwaggo da baki buɗe,
“La la la la la laaaa!! Cabdijam! Lallai Inna yarinyar nan ta ga gadon baccin ki, ae wannan zagin ki kawae tayi, kiji fah irin maganganun da take faɗa miki!!” Juwairiyya ta ƙarashe maganan tana riƙe haɓa, cike da ɓacin rai Gwaggo tace “aikuwa ta ja masu gabaki ɗayan su daga ita har iyayen nata da in ƙara basu ƙanzon nan gwanda na watsawa karnuka! ku ma ku tashi ku fitarmun daga gida gayyar tsiya kawai! masu kama da mayu! Dama daga ganin wannan kyan naku ae ansan kunyi jiɓi da aljanu!” tashi Ni’imah tayi tare da riƙe hannun Gidado suka fice sum sum daga gidan, cigaba da zagin su suka yi, Gwaggo nayi Juwairiyya ma nayi.
A ƙofar gida suka samu Nimrah hannun ta akan ƙugun ta se girgiza ƙafa take yi, a sanyaye Ni’imah ta kalle ta tace “Nimrah kinga abunda kika jawo mana koh? Gwaggo ta ƙare tace har abada baza ta ƙara bamu ƙanzon ba,”
“Addah bazan iya haƙura bane, kinji irin maganganun da take faɗa mana ne, ni zan iya ɗaukan komai amma bazan juri ganin ana cin mutumcin iyayena ba,” girgiza kai Ni’imah tayi sannan tace “toh shikenan muje se ki san me zaki faɗawa Daadah,” ta ƙarashe faɗa tana jan hannun Gidado, taɓe baki tayi tabi bayan su.
Da sallama suka shiga gidan suka tadda Daadah zaune a inda suka bar ta, Gidado fizge hannun shi yayi ya ƙarasa wajan Daadah da gudu tare da faɗawa jikin ta,
“Oyoyo Gidado nah!” ta faɗa tana ƙara rungume shi a jikin ta, murmushi yayi sannan ya fara bawa Daadah labarin abun da ya faru daki² tun daga farko har ƙarshe, shiru Daadah tayi ba tare da tace komai ba, sosai jikin su Nimrah yayi sanyi dan sun san muddin abu ya ɓataws Daadah rai haka take shiru, haka ranar suka wuni Daadah ta fita harkar Nimrah John magana tayi mata bata kallon inda take sosai hakan ya damu Nimrah.
Da yamma Abboh ya aiko Ballo ɗan gidan Baba Rabe ya kawo musu cefanen abincin dare, Ni’imah ce tayi dan Daadah tace baza ta ƙara sa Nimrah aiki ba tunda bata jin magana, magiyan duniya Nimrah tayi mata amma ta kafe, bayan Sallahr isha’i Abboh ya dawo suka haɗu suka ci abincin su, bayan sun zauna fira Nimrah tayi namijin ƙoƙari tace “Abboh dama ɗazu ne muka je gidan Gwaggo…!” nan ta bawa Abboh labarin abun da ya faru ta ƙara da cewa “Abboh shine Daadah take fushi dani, kuma wallahi Abboh nayi ƙoƙarin dannewa amma na kasa saboda sako da iyaye na da tayi amma wallahi tunda Daadah ta nuna bata so bazan ƙara ba dan Allah Abboh ka taya ni bata hakuri,” shiru Daadah yayi na ƴan mintuna sannan ya kalli Daadah yace “Halimatu fisabilillahi tun yaushe nace bana son kina aika yara na gidan Yaya Lami amsan ƙanzon nan! nace ki barshi a hakan nan zan dunga kawowa!” ƙasa da kai Daadah tayi a sanyaye tace “Ran ka ya daɗe ayi mun afuwa Insha Allah hakan baze ƙara faruwa ba!,” jinjina kai Abboh yayi sannan yace “Toh nasan dae ke me haƙuri ce dan Allah a taimaka a yafewa Mama nah itama baza ta ƙara ba koh,” da sauri Nimrah ta ɗaga kai, murmushi Daadah tayi tace “toh ba komai Insha Allah komai ya wuce, Allah ya shirya mana su gabaki ɗaya suka amsa da Ameen, ɗan gyaran murya Abboh yayi alamun ze yi magana me muhimmanci, nutsuwa suka yi gabaki ɗayan su, a hankali ya fara magana,
“Ina so a koh da yaushe ku kasance masu haƙuri, kwata² rayuwar kwaya nawa ce! Idan yau kaine gobe ba kai bane! Kuma komai lalacewar Yaya dae yar baban ku ce! Dan Allah koh bayan rai na bana so koh da wasa wani abu mara daɗi ya shiga tsakaninku! duk abun da zata yi mu ku kar ku yarda ku ɗaga ido ku kalle ta kunji koh?,” jinjina kai suka yi duk jikin su yayi sanyi, ita dae Daadah kallon shi kawae take, haka suka cigaba da yi musu nasiha me ratsa jiki se 9 yace kowa ya tafi ya kwanta..
_________________________________
Kwance yake a mamakeken gadon su cikin lumtsumamman shi yana bacci cikin kwanciyar hankali, ɗakin nashi ya haɗu iya haɗuwa, white and nude colour ne komai na ɗakin, firgigitt!………
😰😰ina so naga ruwan comments, ta haka zan gane ana bin littafin 💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE ⚔️⛓️💫
*@Hanyluv✍🏻*
*07044454719📲☎️*