GUZIRIN MAI HAILA KASHI NA BIYU
{1} BAYANIN JININ AL’ADA ASAUKAKE
Menene jinin Al’ada? shi dai jinin Al’ada jinine wanda yake fita dan kansa kuma yana fitane daga gaban macen da zata iya daukar ciki kuma ta iya haihuwa wannan shine jinin Al’ada.
Yarda yake :
jinin Al’ada yana da wasu halaye gudu hudu halayen sune:
1 {Kamarsa} :kamarsa dai bakine ko ruwan hanta-hanta.
2 {Yana da karni} : Amma yafi karkata izuwa karnin kifi. amma bai kai karanin kifinba,ko waru, kamar warin danyen nama.
3 {Yanayin Fitarsa} : yana fitane yana izon juna, kamar fitar maniyyi amma shi ba’a jin dadi wajen fitar sa.
4 {Yanayinsa}: Yanayinsa dai mai dumine.
{2} MATA SUN KASU KASO HUDU
{TAFARKO}
Ita ce wace bata tabayin hailaba,Hukuncinta :-
zata saurari daukewar jini ne, saboda bata taba yi ba ballantana tasan kwanakin ta, amma ba zatawuce kwana goma shabiyar ba.
{TA BIYU}
Ta biyu itace wacce ta saba yin Al’ada, to Hukuncinsta shine,zata zata iya kwanakin da ta saba yin Al’ada r misali : tana yin kwa uku a ko wane wata, to duk wata kwana uku zata yi sai tai wanka tai sallah ta iya saduwa da mijinta.
{TA UKU}
Ita ce mai ciki da akwai magganganun malamai cewar wasu sunce mai ciki tana haila, wasu sunce ba ta yi, to amma zan gina maganartane a kan masu ciki da suke Haila, mai cikin dake haila dai idan cikin yana wata uku zuwa sama to zata iya haila daga kwana daya har zuwa kwana goma shabiyar, idan ya wuce wata shida zata yi haila daga kwana daya har izuwa kwana ishirin ko kwana
ishirin da tara.
{TA HUDU}
Ita ce mai istahada shi dai jinin istahada Jane, mai jinin istahada. Hukuncinta kamar macen daba ta yin jini ne. domin wata ta tambayi Manzan rahama (S. A. W.) cewar, tanayin annan jinin har yana zuba da yawa, sai yace: tayi sallah ko da yana zuba akan tabbarmar da take Sallah.
Daga dalibinku
Musa s Zage
Allah yajakanan maulana
Assalamualaikum malam Allah ya saka da alkhairi