[MA ‘ANAR AURE ,TARIHINSA DA HAKIMAR YIN SA A MUSULUN CI]002
KASHI NA FARKO 002
MA ‘ANAR AURE ,TARIHINSA DA
HAKIMAR YIN SA A MUSULUN CI.
Gabatarwa
Daga
dalibin ku
HAKIMAR YIN SA
Hikimar yinsa:- Hikimomin aure suna da yawa, sai. bibiyi abin da ya samu bakin gwargwadon fahimta da kuma karamin sani irin nawa.
1. Cigaba da wanzuwar nau’in dan-Adam a bayan kasa :- Musulunci ya hukunta aure don ya zama hanya
mafi dacewa da dan-Adam zai bi wajen cigaba da wanzuwa tare da yaduwa a doran kasa.
Ta hanyar haihuwa ne irin kowane nau’i na halitta yake tabbata.
Don haka babbar hikimar yin aure ita ce, ta hanyar yin sa dan Adam zai sami halattacciyar hanyar da zai ta
haihuwa har ya cika adadin da Allah Ya yi nufin zai halitta a wannan doron kasa.
Aya ta 68 Suratul Kasas ta na cewa:-
وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخْتَارُ ۗ
Ma’ana:-“ Ubangijinka yana halittar abin da ya so”
A āya ta 16 ta cikin Suratul Buruj Allah (witang )
yana cewa:- فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ
Ma’ana:-“Mai aikatawa ne ga abin da Ya yi nufi”
2- Ta hanyar aure ne rayuwar mutum ta bambanta da ta dabbobi:- Kamar yadda muka sani, mutum kamar
sauran dabbobi, shi ma Allah ya sanya masa dabi’ar sha’awa, don haka namiji da mace suna da bukatar su sadu da juna.
Amma saboda daukakar da Allah Ya yi wa mutum, sai ya zamo bai kyale shi ya rika biyan bukatar sha’awar ta sa kamar sauran dabbobi ba.
Maimakon haka, sai ya tsara masa wata hanya wadda zai biya bukatar wannan sha’awa, saboda kare
mutuncinsa da darajarsa, wannan hanya kuwa ita ce aure.
Allah ((سبجانه و تعالى )) Ya halicci dan-Adam ne don ya
zama halifarSa a bayan kasa, kamar yadda Ya bayyana wa mala’iku yayin da zai halicci Annabi
Adam (عليه السلام).
A āya ta 30 ta cikin Suratul Bakara-: Allah (سبجانه و تعالى)yana cewa:
وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَائِكَةِ إِنِّي جَاعِلٌ فِي الْأَرْضِ خَلِيفَةً ۖ قَالُوا أَتَجْعَلُ فِيهَا مَن يُفْسِدُ فِيهَا وَيَسْفِكُ الدِّمَاءَ وَنَحْنُ نُسَبِّحُ بِحَمْدِكَ وَنُقَدِّسُ لَكَ ۖ قَالَ إِنِّي أَعْلَمُ مَا لَا تَعْلَمُونَ (30)
Ma’ana :- Kuma (yã Ma’aikin Allah ka ambaci) lokacin da Ubangijinka ya fada wa mala’iku, “Lallai ni zan sanya wani halifa a bãyan kasa.” Sai suka ce,
“Yanzu zā ka sanya a cikinta, wanda zai yi fasādi a cikinta, ya rika zubar da jini, alhâlin mu muna yin tasbihi hade da godiya a gare ka, kuma muna tsarkake ka? ” sai Ya ce, “Lallai Ni nā san abin da ba ku sani
ba.”
Da Allah (سبجانه وتعالى) Ya ba wa dan-Adam wannan matsayi sai ya fifita shi a tsarin halittarsa, ya daidaita
shi, ya ba shi hankali, ya kuma ba shi ikon yin amfani da kwakwalwarsa da hankalinsa wajen ilimantuwa da
bambancewa tsakanin al’amura.
To da wadannan darajoji ne aka fifita dan-Adam a kan sauran dabbobi, domin su ba a ba su hankali ba.
A aya ta 6-8 ta cikin Suratul – infidar Allah (سبجانه وتعالى) Yana cewa:-
يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ (6) الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ (7)فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ (8)} سورة [ الانفطار].
Ma’ana:- “Ya kai mutumn! Me ya rude ka game da Ubangijinka, Mai karamci?
Wanda ya halicce ka, sa’an nan ya daidaita ka, ya kuma tsakaita ka.
A cikin kowace irin sura Ya so, Ya gina ka a kanta.”
Haka nan a āya ta 70 ta cikin Suratul Isra’i Allah (سبحانه وتعالى) Yana cewa:-
وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِي آدَمَ وَحَمَلْنَاهُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَرَزَقْنَاهُم مِّنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَىٰ كَثِيرٍ مِّمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلًا (70) .
Ma’ana :- “Lallai hakika Mun girmama ‘yan – Adam,
kuma Muka dauke su a kan kasa da cikin teku, kuma Muka azurta su daga abubuwa masu dadi, kuma muka
fifita su a kan masu yawa daga wadanda Muka halitta,fifitawa.
Saboda hankali da Allah(سبجانه وتعالى) Ya ba wa dan Adam shi ya sa.
A aya ta 242 cikin Suratul Bakara.
“كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ”
Ma’ana:- “Kamar kaka ne Allah Yake yi muku bayanin ayoyinsa don ku zamanto māsu hankalta”.
Domin karin bayani
Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.
written by ceo
Page