Dabarun Rubutun Waka

[DABARUN RUBUTUN WAKA – HAUSA ADABIN BAKA] KASHI NA BIYU

Sponsored Links

     DABARUN RUBUTUN WAKA – 2      
RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA 
Daga
NasirG Ahmad 
 Assalamu alaikum.
A makon jiya mun yi shimfida ne kan adabi da manyan rabe-rabensa don gano muhallin rubutacciyar waka cikinsa. To yau za mu fara magana kan rubutacciyar waka.
Ma’anar Waka
Akwai ta’arifai (bayanin ma’ana) na rubutacciyar waka masu yawa, daga masana daban-daban, wadanda duka suka hadu kan cewa maganar hikima ce. Tsara ta ake yi. Ana zaben kalmomin da za a gina ta da su. Zance ne mai reruwa, wanda ya saba da magana ta yau da kullum. Ga wasu daga wadannan ta’arifai:
“Waka wani salo ne da ake gina shi kan tsararriyar ka’ida ta dango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (kafiya), da sauran ka’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaben su da amfani da su, cikin sigogin da ba lallai ne haka suke a maganar baka ba.” (Dangambo:2007)
“Waka ta bambanta da tadi na yau da kullum. Abu ce da ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna kwarewar harshe. Harshen waka cikakke ne, duk da yakan kauce wa wasu ka’idojin nahawu.” (Gusau:2001)
“Waka dai ita ce tsararriyar maganar hikima, da ta kunshi sako cikin zababbun kalmomi masu azanci da aka auna don maganar ta reru, ba wai a iya fadar ta ba kawai.” (A.B. Yahaya: 2001)
“Rubutacciyar waka ita ce wadda aka tsara, aka rubuta ta a takarda don a karanta.” (Bello Sa’id:1981)
“Rubutacciyar waka, wata hanya ce ta gabatar da wani sako cikin kayyadaddun kalmomi da aka zaba, wadanda ake rerawa a kan kari da kafiya a cikin baitoci.” (Mukhtar:2006)
Ma’as Salam.
    
  Daga.     
    Tsangayar da ta himmatu wajen          
     kulawa da killacewa da taskace       abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.
    
 By
MUSA S ZAGE
      Sai muhadu a Kashi na gaba
Domin samu wasu shirye shiryen mu
Damin kalan ranar ARFAT sa a ziyar ci shafin mu 

Leave a Reply

Back to top button