TUMFAFIYA 36
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/14, 9:04 PM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH
,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,
Muna fitowa ina
rike a hannun maryam dake jana muka fito daga cikin filin zuwa waje lokacin naji wani shakat a zuciyana
jikin mota na dan jingina ina dan fifita da hannuna.
Wani wanda wanan
ta ukun tamu da muka hadu muke tare ta kira tace don Allah ko zai wucene ya
saukemu gida ta fadi sunan gidan su mommy din.
Yace muzo ya kaimu
mommy na kira na sheda matagamu zamu tafi gida don ban yarda inyi wani abinda
bata sani ba ya zama min matsala a karshe.
Mai motan yana
ganin yan mata ya tsaya a wani shop yayi muna sayayyan kayan sanyi da su nama
muka karasa unguwan lokacin dare soma yi.
Bayi na shiga na
samu wanan matar ta gyara dakin ta wanke bayin ta cika robobin dake ciki da
ruwa tayi aiki gwanin ban sha,awa nayi sauri nayi alwala na fito har lokacin su
maryam din ma basu shigo ba.
Ina idar da isha,i
na soma jin muryan mutane a gidan dake nuna an soma dawowa daga wurin taron ke
nan a lokacin na cire kayan jikina na sauya zuwa dan rigan barci saiga maryam
da yarinyar sun shigo sun sameni.
Suna fadin ke ashe
bayan mu anyi fitinane da yan gidan amarya sosai ayyah abu baiyi dadi ba na
fada tace wallahi nan suke ban labari yayin da maryam ta miko min ledan tana
fadin kici fa naga kamar har kina shirin kwanciya.
Ni har nayi sallah
zan kwantane yanzu kallon juna sukayi tace gashi munce zamu fita kuwa ke kuma
kice zaki kwanta.
Ai bani fitan
dareni kome ki akeyi don yana zama min lalura hakan sai daya tayi saurin fadin ashe ba zaki dinner ba ke
nan gobe ?
Kaina gyada idan da
darene sosai ba zani ba gaskiya kici mu bari muyi sallah nace komai ba zan iya
ci ba yanzu saidai gobe kuma ?
Humm,Ummm wanan
akida kamar wata baturiya haka kina da ra,ayi kala kala a rayuwan ki maryam ta
fada toke baki ganin su yayan hutune dama irin su kuma sai aure gidan gwanoni
ko yan majalisa.
Aiko baki fahinceni
ba kowa da kalan ra,ayinshine bana dai cine yanzu karfe takwas nake cin abinci
koda zanci din kuma takwas ya wuce yanzu.
Aishiyasa nace sai
yayan shugaban kasa nace niko kinga tallaka nake son in aura don a nan nake
hango kwanciyan hankali yake sam bani da ra,ayin auren mai kudi ko mulki a
rayuwana.
Ke raba kanki da
wahala yanzu na rabaki da auren tallaka wallahi garama mutum ya auri mai kudin
komai ta famjama fanjau da ka auri tallaka sai kudi yazo kinga hutu a lokacin
zai dauko maki yar gaban mota ace ke baki iya ba baki waye ba .
Ai maza wallahi
barsu nan inda kika gansu kawai matan yanzune daidai dasu mace ta juyasu yadda
ranta yakeso kana kallo in kayi magana ace kishine .
Zaman gidan mune
ya fado min a raina don gaskiya ta fada tunda ga yar uwansu nan a yanzu ta
mayar da Abban mu kamar karamin yaro sai yadda ta juyashi a yanzu.
Mama dake magana ana
ganin kishinta da hauka wai bata son shi da karuwa sai ita da yayanta kawai a
gidan take son ganin shi dasu.
Suna ta zancen su
dai ina jinsu rabi rabi kuma yana ga tunanen zamani dake raina har barci ya
daukeni a hakan na barsu nan suna hira ko sallah basuje sunyi ba a lokacin.
Mommy ta leko ta
samu nayi barci ko ta fita ban falka ba sai washegari da asuba na tashi don
motsin tsohuwar da naji a lokacin ta shigo zuwa bandaki.
Sun shiga gidan sun
samu Shattu ta gama girki har ta kwashe tayi masu shimfida ta aje masu a cikin
rumfar shan iskansu na gidan.
Sukai sallama suka
shigo takewa mijinta sannu da zuwa shima Ahmed din ya gaida ita tayi mai ya
gajiyan hanya ?
Ya amsa da
alhamdullahi ta ga batar masu da abincin ta koma gefe daya ta zauna tana cin
nata bayan sun zauna baban yayi mai bissimillah ga abinci muci.
Ya gyara zama yana
fadin baba kaci ka barmin idan kagama zanci ba zan iya hada hannu da kaiba kada
nayi rashin da,a ga hakan .
Daga can inda shatu
din take zaune tana jiyosu tace dama nayi tunanen hakan yasa nayi dubaran zuma
masa nasa shi kadai gashi can nakai mashi daki na rufe tun dazun ai.
Lalai kana cikkn
mutanen da yaro duk dabi,un ka na tarbiyan kwarai ne ka samu duk wanda ya baka
tarbiya haka bai bayar a wurin banza ba
.
Dakai wani yaron
zamanine zaka zauna mucine ba tare da daukan hakan komai ba samun irin ku
yanzun a cikkn al,umma yana da wuya sosai gaskiya.
Shattu ne ta mike
ta nufi dakin ta dauko abincin ta kawo mashi yayi godiya ya zauna ya fara wanko
hannunshi yazo ya zauna ya bude kwanon abincin .
Kamshin man shanune
ya biyo hancin shi da sauri ya lumshe idanun shi don Allah yayi shi da son man
shanu a rayuwan shi sosai shi samune kawai baiyi yasa ya hakkura dashi.
Bayan sun gama cin
abincin dan hirane suka taba inda tsohin ke bashi labarin irin yadda suke kiwo
su a nan don yanayi yasa komai ya dan banbanta da nasu yanzu.
Shima Ahmed din
yana labarta mashi yadda wurin su yake da irin yanayin da jaharsu yanzun yake
ciki sun dan kai wani lokaci suna hira a tsakanin su shattune ta fara mikewa ta
shiga ciki yayin da Ahmed din shima ya ga ya dace ya shiga masaukin shi ya
barsu su dan gana hakana da iyalan shi.
Yayiwa tsohon
saida safe ya shige dakin ya turo sai lokacin ya tuno da wayanshi daya mutu tun
a cikin mota ya dauko ko dan wuta bata kawowa don ta dauke da kantane.
Zahra yaso ya kira
lokacin yaji lafiyanta saidai hakan bai yuyuwa gareshi yanzu don daukewan da
wayan tasa tayi din.
Don haka ya lafe a
saman gadon karan yana maida numfashi yayi da zuciyar shi ke cike da tunanen
abubuwa kala kala yana nazari.
Da farko mamakin
ganin akuyan nan mai kama da uwargarkenshi yakeyi don yasan babu yadda za ayi
uwargarke ta kawo nan idan ba aikin aljannu ba haka ?
Sai kuma tunanen
yadda zai iya samun mahaifinshi dayai kasadan fitowa gida ba tare daya fadawa
kowa kudirin shi ba ya kamo hanya ya fito da badan Allah daya hadashi da bayin
Allah nan ba da yaya zaiyi a wanan garin ta ina ma zai soma hakan yace yana
neman mahaifinshi a haka.
Sai kuma ya tuna
da Dije wace yasan yanzu ta gama tayar da hankalinta gareshi na rashin dawowan
shi gida din na tsawon kwanaki da baiyi ba kuma bai fada mata inda ya nufa ba
da zai bar gida din.
Donshi baida
babban waya irin ta matasan zamani balle yaga abinda duniya ke ciki da idonshi
ya gane masa yadda aka juye labarin tafiyan shi ya karade gari cewa an masa
kurciyane ya bata.
A karshe kuma ya
koma tunanen zahra a gaskiya yanzun ya gama yarda da cewa skn zahra yakeyi sona
gaskiya da baikoyiwa kansashi.
Amma kuma akwai
abubuwa masu nauyi a tsakanin su din na farko babban shine tabbatarwa mutane
shi din ba shege bane da ubanshi.
Tunda ya fara ganin
kyama a idon mutane dake nuna mai cewa shidin baida asali yasan wanan zancen ba
akan zahra ba kan ko wace mace yaje nema za a fada mashi hakan don ba a aure
babu waliyyai ga mutum najini.
Idan hakan ya taso
mashi tunda ba zai zauna baiyi aure ba suwa zai nuna a matsayin iyayyen shi
yanzu dolene hakan daya yanke din wa kanshi don yasan idan ya tsaya ba Dije
shawara ba zata taba yarda da bukatanshi ba kai tsaye kuma ita ba zuwa zatayi
ba nema mashi mahaifin nasa ba.
Gashi ya kwaso kafa
yazo garin mutane ba tare da sanin komai kan mahaifin nasa ba don baida wani
sheda da zai gabatar da zaisa ayi saurin gano waye mahaifin nasa a yanzu.
Dan dagowa yayi
daga kwancen da yake saman gadon karan da yasha bargo mai laushi ya canza kama
har baka gane cewa ba gadon zamani bane a dakin da sauri.
Don tuno da
lokacin da za a sakashi makarantar boko ake muhawaran sunan da za a saka mashi
son anyi niyar saka mashi sunan kakan shi ladan a lokacin.
Amma sai headmaster
makarantan ya bada shawara a saka mashi sunan mahaifinshi don ko wani da yana
son alfahari da sunan ubanshine ai a duniya.
Sai yaji kakan
nasa yacewa headmaster buba sunan mahaifin nasa sai headmaster ya gyara da
fadin buba ai Abubakar ne akewa lakanin hakan wani lokaci don haka yake da
Ahmed Abubakar a sunan shi.
Lalai wanan zai iya
taimaka masu yanzu wurin gano waye mahaifin shi indai har da sunan nan biyu yake
amfani a nan din to hakan zai iya taimaka masu a ganoshi watakila.
Da wanan zancen ya
kwana a zuciyan shi cewa lalai zai fadawa tsohon wanan maganan ko zai iya
taimakon su agane da sauri.
Da wanan barci ya
daukeshi sai gashi yana mafalki da uwargarke tana binshi tana wani kuka gwanin
ban tausayi jin kukan nata yasa ya tsaya akuyan tazo tana dona kahonta a
jikinshi kamar tana susa.
Ganin haka yasa ya
dauki hannun shi ya dora a bayanta yana shafa a hankali ji yayi ta rage kukan
da takeyi din ya jawo hakki ya mika mata a baki sai taki ci tsugunnawa yayi
yana fuskantan akuyan ya soma fadin.
Uwargarke me kike
so sai yaga akuyan ta juya baya kamar tana nuna mai wani abu ganin hakan
yasashi dago kai ya kalli wurin da akuyan ke kallo.
Baiga komai ba sai
ganyayakin tumfafiya da suke birit a wurin gwanin ban sha,awa dasu suwa wurin
lup lup dasu juyawa akuyan tayi ta nufi wurin da tumfafiyan suke.
Shima mikewa yayi ya
bita suna ta ratsa iccen tumfafiyan dake wajen sai ya hango wani mutum a zaune
saman wata kujera ta alfarma ya bada baya yana zaune shi kadai a wurin.
Tana kaiwa gaban
mutumin daya shadda yana hakince saman kujera sai kamshin turare ke tashi
jikinshi saita ta zube a wurin shima ya karaso yanawa mutumin sallama dago kan
da mutumin zaiyi sai yaga wani dattijo farine.
Mai son kamani
dashi saidai wanan ba yaro bane shi kuma babban mutum ne a yadda ya ganshi
zaune din da kuma kalar shiganshi da kujeran da yake zaune a kai.
Ji yayi kamar an
dukeshi ya tashi daga barcin sai gashi kawai ya bude idanun shi ya ganshi
kwance cikin dakin nan na gidan tsohon da suka bashi ya zauna a ciki.
Duk da yanayin
sanyin dake garin hakan bai hanashi zufa ba dako har rufa yayi don sanyin daya
kama mai jiki kafin barcin ya daukeshi bin dakin yayi da kallo na dan lokaci
kafin mafarkin da yayi din ya dawo mashi sabo a ranshi.
Daki daki yake tuno
da abinda ya gani a cikin mafarkin nasa hakan yasa ya mike zaune yana kokarin
sako kafafuwan shi kasan gadon karan .
Kukan dabbobin
tsohon yake ji daga waje wanda hakan yasa hankalin shi ya dauku a lokacin ya
maida hankalin shi ga sauraren su.
Kuka sosai sukeyi
wanda ke nuna cewa wani abu yana faruwa da dabbobin a lokacin kusan tare suka
bude kofa da tsohon daya fito a gigice shima yana fadin miko min fitilan mai
haske shattu.
Shima Ahmed din
komawa yayi ya lalubo tashi fitilan suka cice daga gidan da sauri shida tsohon
lokaci guda suka nufi wurin dabbobin da sauri suna haska fitila.
Tun daga nisa suka
hango babban bajimin saniyar tsohon a kwance yana shure shure hankali tashi
suka nufi wajen tsohon duk a rude yake yana kiran innalillahi shi kawai yake
ambatowa a lokacin.
Baba kuna da
tumfafiya a unguwar nan Ahmed ya jefo mai wanan tabayan shima a rude lokaci
guda tsohon yace akwaishi can barin kadan yace ta ina ya nuna mai ya juya da
sauri zai nufi wajen.
Dakata muje tare da
sauran dare ayanzu babu komai baba insha Allahu ya sheka guje tsohon bai yarda
ba ya biyoshi a baya gudun kar wani abu ya sameshi.
Suna zuwa da addua
a bakin Ahmed din yakai hannu ya karo wani reshe na tumfafiyan ya juyo da sauri
suka hade da tsohon tare suka juya Ahmed din yana sauri tun a hanya ya kara
wasu ganye yake murzawa a hannun shi.
Tsohon yana biye
dashi ya rike saura ganyen da suka fadi a hannun shi yana zuwa gaban bajimin
san dake kwace ya nemi hancin saniyan ya murza mai wanan tumfafiyan a hancin
shi.
Ya kara kallo wani
ganyen ya murza yabi fuskan saniyan dashi duka har zuwa kahon zuciyar shi
tsohon dai yana tsaye yana kallon ikon Allah don shi bai taba sanin wanan ismin
ba a rayuwan shi.
Zuwa lokacin kuma
har wasu makwabta dake jiyosu sun fito daga gidajen su sunzo inda abin yake
faruwa suna mamakin hakan.
Bin gadon bayan
saniyan yayi yana dan murza mata sauran ganyen a hankali yayin da saniyan kuma
ta rage karfin shure shuren da rakeyi da farko din da alama abin dake damunta
din yana gushewa a hankali gareta lokacin sun koma gefe daya suna kallon ikon
Allah.
Wai mamaki lokaci
guda saiga saniyan ta fara atishawa irin ta dabbobi din nan da karfi zakace
murane takeyi sosai a lokacin take fitar da wanan majinan a hancinta.
Suna nan wajen aka
kira sallah asuba don haka aka soma watsewa don haraman sallah sai tsohon nan
dashi Ahmed din aka bari wanda har lokacin yana saman saniyan dake kwance tana
samun natsuwa a jikinta.
Tsohon ne ya iya
fadin lokacin sallah na shigewa muje muyi sallah a barwa Allah ikonshi duk da
yaga sauki ga saniyan don haka Ahmed din ya mike yabi bayan tsohon suka shiga
gida tare.
Bayan an fito daga
sallah yawanci mutane suka nufo wajen don su jajantawa tsohon abinda ya faru
dashi a tsaye suka samu saniyan yana halbin iska.
Kowa a wurin yana
mamaki zagayawa Ahmed din yayi yana kallon dabbobin dake tsaye cirko cirko suma
da abinda ke damun su a lokacin.
Baba ana samun
rushin garwashi yanzu a kawo ai masu hayakinai kowa dake wurin ya kallo Ahmed
din da mamakin jin hausan shi na yan sokoto a cikin su.
Yarona meka fada
nan ya kara maimaitawa basu gane me yake fadi ba saida yace garwashin wuta a
kawo mashi aiwa dabbobin hayaki dashi san nan suka gane hausan shi.
Tsohon ya juya ya
shiga gida shi kuma Ahmed din ya nufi wanan wajen da suka debo tumfafiya a
cikin dare kamar da mutane a wurin yake fadin sallamu alaikum tumfafiya jiya na
maki laifi na dibeki kina barci ku gafarceni don Allah.
Kaduwa da damuwa ya
sani hakan ku gafarceni dan Allah yanzun ma nazo na dab debikine don Allah ya
danyi shiru na dan lokaci kafin ya kai hannunshi ya mika ya fara kakaban bawan
iccen tumfafiyan daya bushe a jikin iccen nasa saida ya tara da dan yawa yace
ya gode ya juya ya wuce .
Dawowanshi yayi
daidai da da zuwan garwashin wutan ya zuba a cikin wutan ya aje tsakiya hayakin
na bugun duka dabbobin wurin.
Ina sam bankai ido
ga kayab mutum ba wani yayi kadan ya saka min ido ga abina bana bakin ciki ko
kyashi gun abin mutum dan wanda Allah ya bani yanzun kuma za a halaka min su.
Haka ba zai taba
yuyuba saidai muje tare da mutum idan yace zai saka abina a idon shi don ba zan
yafe zalunci ba irin haka da rana tsaka.
Baban ne mai
saukin Ahmed din ke fadin haka kamar ya zare sai hakkuri da ban baki mutane ke
masa suna fadin yayi sa,a ai wanan karon da har saniyan ya tashi bai mutu mushe
irin wancan karon ba.
Ya juyo yana fadin
Allah yaga abinda ya gani ya turomin yaron nan a rayuwana shiyasa alheri yake
da dadi don baka san a inda za a rama makaba.
Yinin ranan dai
sunyishi babu dadi a unguwar don shi da dattijon sun wuni cikin garke suna kula
da lafiyan dabbobin nasu ne ana faman saka masu hayaki da dumi suna ji.
Wanan ya shafar da Ahmed din zancen mafalkin
shi abu daya ya iya tunawa shine cewa tumfafiyan nan da zaiyi amfani dashi ya
gani a mafalkin shi a daren jiya din ke nan.
Jin abu na tabashi
daidai wurin mafalkin nasa har yana danjin zafin wurin ya juya don yaga ko
menene yai karo dashi a lokacin.