Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 46

Sponsored Links

CHAPTER 46

Ba tare daya dago daga abunda yakeyi ba yace”jeki ki dubomun Aisha cikin musu ɗinki,wani irin tuƙuƙin bakin ciki taji ya turnuketa tama rasa meke mata daɗi koba komai ai yabari yaji dame taxo amma sai wani shamƙamshi yake duk uban kuɗin data ɓata wajen yimasa kwalliya dan ganin ta burgesa amma a banza.

Saurin juyawa tayi ta fita tana jawo kufar da karfi yabada sautin garammm ɗan tsuka yayi ya cigaba da abunda yake.

Yau asabar anwayi gari da labarin ɓacewar wasu riƙaƙƙun ƴan ta’adda da hukumar ƴan sanda ke nema ruwa a jallo,wannan abune daya tsorata sauran ƴan click ɗinsu dama manyansu kai duk wani ɗan mafiya ya tashi da tsananin tsoro da fargabar yake da ɓacewar manyan yaransu har guda hudu LION da akafi sani da NO17 sai junior sai kuma kaska da bazuka ɓatansu ya girgiza manyansu dama ƙasa baki ɗaya dan ba wanda yasan taƙa maiman wanda ya ƙwamushe su,hukuman ƴan sanda tuni sukai zaman gaggawa dan acewar su wannan abun kunyane ace suna aiki ba dare ba rana amma ace sungaza kama waƴan nan mutanen saide kawai suji labari agari wai wani ya kamesu ba su ba,wannan abun kunyane gare sosai cikin ɓacin rai IG yamiƙe yana tada jijiyoyin wuya yana faɗa cikin tsananin bacin rai yace yabasu nan da awa 48 dan ganin sun kamo wanda yayi wannan aika aikan kokuma suda aka kaman wannan umurnina yafaɗa da kakkausan murya.
Duka amsa masa sukai da yes sir.

Duk da sunsan abune mai matukar wuya ace susamo waƴan nan mutanen cikin kwana biyu dan duk wanda yayi wannan abun ba karamin shiri yayi ba.

“Alhaji ya ina faɗamaka ga abunda boka yace kana ɓagarar da zance wallahi wannan bokan aikinsa kaman yankan wuƙa yake baya karya duk abunda yace ze faru to ba makawa saiya faru.

A fusace ya ɗaga mata hannu rai aɓace yafara magana”haba mariya sauraramun da zance bokan nan mana haka tun dazu kin isheni da magana ɗaya waima in tambayeki mana”ina jinka ta amsa masa a daƙile.

“Shin da izinin wa kika ɗauki ƙafa zuwa wajen bokan?
Tambaya daya mata a bazata kame kame tasoma yi dan bata da amsa guda dazata bayar dan kare kanta ita kanta sai yanzu ta tuna da katoɓarar da tayi dan tun tuni Alhaji sunusi ya haneta da bin malamai ko bokaye acewar sa idan kishiya take tsoro shi bashi bayi mata ƙari sannan yara wanda ta haifa masa sun isheshi rayuwar duniya shisa suke cin duniyarsu da tsinke duk abunda tanema yimata yake wani abun ma saide kawai taga yasayo mata.

“To daga yau kika sake wanke kafa kikaje wajen wani boka kiyi kuka da kanki idan kinyi wasama ita ƙawar taki mai baki shawara zuwan zanyi muku katanga tsakanin ku,fuuuu yawuce ciki cike da fushi abu ya game masa goma da ishirin.

Suhail duk ya tashi hankalin sa dana ƴan gidan su baki ɗaya da rashin samun sahibar tasa a waya kwana biyu da beyi ba,kira dubu zema khalid amsar ɗayace ba tazo aiki ba koyaje gidan su besame su ba,ganin sa cikin damuwa ya tashi hankulan ahalin sa baki ɗaya musamman ummin sa,yanxun ma zaune yake wayansa riƙe a hannun sa kaman wanda ze ganta taciki ɗagowa yayi yace”Ummi kibani izini inason zuwa Nigeria a yau ɗin nan dan son ganin meyasame ta nasan haka kawai bazata kashe wayarta ba inma wayar tata tasamu matsalane ai dole zanji daga khalid tunda kullu yaumin sai taje aiki,kafin ummin tayi magana suhaiham
dake zaune dan nesa dashi ta taso tazo gaban sa tazube gwiwa a ƙasa tace”yanzu akhi dama duk saboda mace ka shiga wannan halin damuwar dan Allah faɗamun dame tafini,kyau ko asali naɓata lokacina akanka nakori duk wasu samarina masu sona da aure nace sai kai irin sakaiya da zakamun kenan kawai sai ta daura kanta saman cinyarsa tafashe da kuka saida tayi mai isarta sannan ta ɗago tariƙe masa hannu tace dan Allah kasoni ka kaunaceni koda kwata kwatancin sonda nake makane wallahi idan kagujeni koka juyamun baya mutuwa zanyi kawai sai tari ya tsarƙe mata tasomayi ba kakkautawa take duka sukai kaita kira suke suhaima suhaima cikin tsananin tashin hankali ummi take kira ɗaukota muje asibita amma tuni tatafi luuuuuu sai tarota yayi sumamiya cikin tashin hankali ya ɗauketa da gudu yayi waje da ita sakata mota yayi Ummi tashiga ta daura kanta saman cinyarta sai hospital.

*******
Aikinki yana kyau ƙanwata dan murmushi tayi tace”karka damu akwai manya manya boma bomai daxasu tarwatse nan gaba saide tarwatsewar ba zaiwa mutane da yawa daɗi ba.

“Ai wannan ɗinma beyi musu daɗin ba ya amsa mata da faɗin hakan”hhhhh ƴar dariya tayi sannan tace wancan ɗin fa gunduma gunduma ne tashin sa saiya girgiza ƙasan baki ɗaya”Allah de yasa bamu aciki dan gaskiya nayi mamakin aikin da ya ɗaukeni tsawon wata shida inayi amma ke cikin awa ɗaya kika gamashi kai keɗin ta dabance naso ace kina ɗaya daga cikin mu.

“Hmmm bani da ra’ayin aikin ɗan sanda sabida cin hancinsu yayi yawa”kai Aisha bafa duka aka taru aka zama ɗaya bafa”kaga time na ƙurewa zoka maidani gida kar Anty hajiya taga daɗewata dan cemata nayi zani duba ƙawata.

yau yakama mondaya
kowa kagani shirin fita yake ƴan makaranta nayi masu aiki nayi.

Cikin shiri fita aiki take dan yau haka kawai ta tsinci kanta dason leƙawa tun a cikin gida malik yake mata surutun shifa bazata shiga masa bayan mota ba dan shiba driver ɗinta bane,ƴar dariya tayi tana cewa”sha kuruminka malam wanda ma yafika da komai zan dauka driver nan gaba kaɗan wanda kaida kanka iidan kaganshi yana buɗemun mota sai kayi ƙass da kanka ai kaikan a wannan gaɓan saide ko mai gadina zan daukeka”kutt wani irin wawan mangari yakai mata tayi sauri guduwa bayan Anty hajia tana ɓoyewa”kwafa yayi yana cewa”wallahi anty hajjya ashe kekike daure ma yarinyar nan ƙarƙashi take raina mutane.

“Yo kaiko Abdul malik ba dole na nadaure mata ƙarkashi ba surukuwa wasace takare faɗin hakan cike da zolaya,Aisha kuwa rufe fuskanta tayi cike da kunya tana shirin barin wajen shikuwa malik ya ɗauka da yayansa faisal Anty hajiya ke nufi dan haka yayi dariya a ransa yana cewa shisa kwanan nan nake kallon sa makale da ita ashe ba banza ba.

Karfe goma daidai motar sa ya shiga company haka kawai yaji zuciyan sa badadi yau,duk inda ya gilma sai ma’aikatan sa sunzube kasa suna kwasan gaisuwa yauko ɗaga musu hannu dayakeyi bayayi saida direct office ɗinsa yanufa kaman kullum jamila ta tsaftace komai saida ya zauna sosai sannan yashiga duba cctv ɗinsa,tsaye ya hangota tana ɗagawa mai mota daya sauketa hannu da murmushi ƙwance saman fuskarta take yaji wani abu kaman mashi ya sokeshi.

Waya ya dauka idon sa nakan tv yakira mai gadi yana daukawa beko tsaya amsa masa gaisuwa dayake ba”yace turomun wannan yarinyar ya ajiye wayan,tsuke fuskanta tayi kaman wacce aka faɗawa sakon mutuwa kaman bazata ba sai kuma tanufi office ɗin nasa sallama tamasa ƙasan maƙoshi ta tsaya tsakiyar office ɗin batare data rufe ƙofan ba tace”gani saida ya mula kaman badashi take maganan ba sannan ya ɗauke kansa daga allon tv yakalle ta kallo na tsanake”natsani yawan kallo wallahi a rayuwa mutum sai shegen kallon kaman ƙwarto tayi maganan ƙasa ƙasa tana turo bakinta sarai yaji mai tace amma ya shareta.

Saida ya gaji da kallon nata dan kansa sannan yace”meya hanaki zuwa aiki kwana biyu?

“Bani da ra’ayine shisa banzo ba,ta amsa masa kanta tsaye shi wasu lokutan har mamakinta yake wajen tsaurin idonta da son mai dawa mutum magana kanta tsaye ba tare da shakku ko tsoro ba.

“Iska yafesar ta bakin sa yace”amma kinsan ka’idan aikin ko?”eh mana duk wanda yayi fashi zaka zabtare masa albashi sai kuma me?

Tamaida masa da tambayan nufota yayi bata ankara ba taji ya damkota yariƙeta da kyau sannan yace”shikuma wanda ya saukeki a mota yanzu da izinin wa ya ɗaukoki ko kika shigar masa mota.

Marmar tafara yi da ido kaman zatayi kuka duk da haka bakin be mutu ba cike da tsiwa tace”idan tambayata zakayi katsaya inda kake amma mutum kullum saboda kwartanci sai ya raɓi jikin mutum sannanne zakaji daɗin masa magana ai wannan haramune.

Ɗalle mata baki yayi da yatsa”mugu kawai ai wannan ma cin zaline ta faɗa tana kunkuni”eashow nikike kira ƙwarto ko bara yau nanu miki ni cikekken kwarton ne nan gaba kyaji daɗin kirana da sunan beyi wata wata kawai ya haɗe bakunan su guɗaya yafara tsotsan lips ɗinta kaman wanda yasamu lolilpop gashi ya matsata sosai jikinsa ba ta yanda zata kwaci kanta sai hawaye dake fareti saman kyakkyawar fuskanta a haka jamila tashigo ta gansu mutuwar tsaye tayi dan batasan sanda file ɗinda take riƙe dashi yafaɗi ƙasa ba,shi kuwa khalid murmushi yayi kawai yana mai komawa da baya kaman ma bega maike faruwa a gun ba dan shi yajima da sanin abokin nasa yadulmiya ƙogin soyayya ba tare daya sani ba.

Alhji auwali da su Alh hamza harda oga Alh sunusi zamane sukai na sirri kan abunda yake shirin tunkarosu nan Alh auwali ya dubi Alhaji sunusi yace wai shin”ya akai hakan ya farune shin sakacin mune yajawo faruwar hakan kode cikin mu akwai mai mana zagon ƙasane?

Nan suka shiga kallo kallo a tsakanin su kowa da abunda yake kissimawa a ransa”nimade abunda nake tunani kenan gashi ita kanta hukuman ƴan sandan bata da masaniya balle ayi yanda aka saba cewar Alh sunusi ya daura da cewa kama kame waƴan nan yaran namu bafa karamin hatsarine garemu ba”dole akwai masu bibiyarmu Alhaji hamza ya amsa da faɗin hakan”kunfa san yau kwana biyu da kame mana kaya a malesiyya kuma haryau ita kanta hukuman tace bata san mai alhakin yin wannan aikin ba,gashi yanzu lokaci ɗaya aka kame mana yara har hudu kai abun faa abun dubawane.

Alhaji surajo ne ya amsa da cewa”ni abun ms mamaki yake bani wai wata yarinyace taje tasai kaya kusan na dubu ɗari uku zata masa tranfer yaƙiyi shine fa yace tazo suje pos daga nan shikenan ba ita bashi.

“Yarinya kuma?
Har rige rige suke wajen tambayan sa”eh ya amsa su yaɗaura da cewa na LION ba sukuma sauran ance anyi amfani da wayan shi LIONɗin wajen kiransu ɗaya bayan ɗaya da faɗa musu inda zasu haɗu shike nan.

Dolene mutashi tsaye dan kaganin mun kare kawunan mu dama dukiyar mu baki ɗaya,kuma yazame mana dole muyi idon fara dan ganin mun binciko masu bibiyarmu.

Duk wannan tattaunawa dasuke yana kallon su ta tv dake gaban sa kaman ma tare dashi sukai wannan tattaunawar dariya yayi sosai sannan ya miƙe tsaye yakira ɗaya daga cikin yaran sa yana mai bada umurnin”ku binciko mun wanda yakama LION ance yarinyace mai alaƙan ita wannan yarinyar da waƴan nan mutanen ina bukatar sani”angama oga aka amsa masa ɗaya ɓangaren yana barin wajen dan cika aikin ogan nasu.

RUGA FULANI CIKIN WATA BUKKA

Hango wata mata nayi kwance kaman bata numfashi kwance saman katifat yayi gefenta kuma wata ƴar yarinyace zaune tana wasa”ruwa ruwa ruwa matar dake kwance saman katifar yayin ta ambata amma idon ta arufe,kallon ta yarinyar tayi sai kuma ta kwasa da gudu tayi waje tana kira”inna muddibo ƴarɗo kozo yau matar nan tayi magana dukkan su kusan atare suka yo hanyar bukkan harsuna turarreniya gun shiga.

 

Alkalami🖊️yafi
Takobi⚔️

ALLAH YASA MUDACE
[5/27, 4:42 PM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button