Bad Boys Hausa NovelHausa Novels

Bad Boys 7

Sponsored Links

Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By…
Oum Aphnan

007
___________________
“Knock knock knock”

Daga can upstairs taji ana knocking a entrance door ɗin parlourn ta ,wannan ya sata fitowa da sauri tana faɗin “Ana zuwa”

Sanye take da bugujejen jallabiyar Ya Sheikh sai hulan wanka a kanta da falkata falkatan silipas ɗin da take sakawa a ɗaki.

Murza key ɗin ƙofar tayi ta buɗe ƙofar ,cak ta ja ta tsaya ganin very tall handsome man a tsaye , kyakyawar gaske cikin ƙananun kaya ,fuskarsa kewaye da ƙasumba ya ɗan ajiye tumbin kuɗi cif cif a riga

Yana ganin ta buɗe ya saki fara’a har jajayen leɓensa da suka haskaka brown ɗin fatarsa suka sake bayyana.

“Hajiya Barkanmu da rana” yanda yayi maganar a rarrabe ya bata dariya ta lura baida Hausa sosai

“Masa’al khair” Adnan Yana jin ta iya larabci yaji kamar ta taindimashi a Aljannah ,ji yayi kamar ya kamata ya rungume

“Masha’allh A adkhul?”(In shigo)

Yanda ya ruɗe sai kawai Sayyada ta tsinci kanta cikin jin nishadi ,daga gani wannan ɗan comedy ne ,kuma duk yanda akayi mutanen Sheikh ne na wasu ƙasashen

“Tafaddal”(Shigo) ta bashi hanya ya shiga ,itama ta rufo ƙofan ta biyo bayansa .
A tsakiyar falon yaja ya tsaya ,suka gaisa sosai

“….Ammm sunana Dr Adnan Ni Likitan ƙwaƙwalwa ne ina da Asibiti a ƙasar nan ,London Specialist ,nazo ziyarar aikine So nasa a siya mun gidan da innazo zan ringa sauka Inshallah ,shine aka bani wancan gidan da yike kallon nan Compound ɗin.”

A ɗan ɗarare Sayyidah tace “Sannu sir,Ashe maƙoci mukayi”

“Na’am,to shine fa tun safe na sauka da empty stomach ,bansan koina ba ,Inason inci abinci ,amma gaba-daya water system ɗin da wutan gidan na kasa connecting ,bansani ba ko ƙauyanci ne😆Ko tsarin naku na irin na ƙasar mu bane oho”

Dariya Salima ta fashe dashi
“Hummm ɗan gayu kamar ka ai saidai ace baku saba da ganin local one irin namu ba ,na en Nigeria…Nikam yanzu me kake so inyi maka”

“Yawwa don Allah to ki ɗan haɗa mun wai cofee ne insha atleast kafin in samu a gyara mun komai nawa”

Gaban sayyada fadi yayi dam ,a take idanuwarta suka zazzago
Ta fara sosa ƙeya “Ammm eh ,dama ehhhh ,wallahi bamu da kayan shayi ” ɗaga kai yayi yana ƙarewa falon kallo ,gida har gida kudi gasunan basu magana wai ba kayan tea” bai nuna mamakinsa ba sai ma wayancewa yayi irin na gogaggun maza da suka saba hulda da mutane .

“Nop karki damu ai ma taho da nawa kawai ruwan zafi nikeso ” ya mika mata ledan hannunsa ,Plz ki hado mun a ɗan mug.

Amsa tayi a kunyace ,ta wuce Katar Katar ,ɗuwaiwuka da nonuwa suna ta rawa a Jallabiya ,bin bayanta da kallo yayi ,inner side ɗin zuciyarsa tana harbawa da ƙarfi ,a zahiri yace “Wow Original kyau please”

Sai kuma yayi saurin minding business ɗinsa ta hanyar daukan remote Yana canja channel din TV.

Minti kaɗan sai gata ta dawo da ɗan mug din shayi a saman tray ɗinsa da ɗan cokale a gefen cup ɗin.
Ta saman kansa ta miƙo masa

“Gashi ” Hannu biyu yasa ya karɓa yana bin ƙirjinta da kallo
Haka yakai cup din baki ya kurɓa “Shukran”(Nagode) …Amma ina naki?”

Zaro ido tayi ,a ranta tana cewa shi wanann ya faye shishigi Ni ya tashi ya fita kafin ya Sheikh ya dawo.

“Ya zanyi in Sha maka abunka ? Hazha haram,ga sauran kayanka nan” cikin mamaki ya ajiye cup din shayin a saman table yana kallonta .

“Kar kice mun kina da rowa?” girgiza masa kai tayi da sauri

“To Ni kayana na kowane ,in inacin abu Naga wani bayaci gaba-daya abun gundura na ma yake yi,don haka Matsawar bazaki hada naki ba to nima na fasa sha”

Sayyada da tun asali ƙamshin shayin yake damunta ,miƙewa tayi a sanyaye ta samo cup ta ɗiba Dan kaɗan zata mike yace “Wai ku haka kuke shan tea so watery _Ba kauri?_”

“A tattala Mana in ya kare fa kaya na tsada a nan?”

Zaro ido yayi
“Topah ,Add things johhhhrrr”

Lafiyayyen Tea sayyida ta haɗa tazo falon can nesa dashi ta zauna tana sha a ɗarare duk ta ƙosa ya tafi

“Kayi hakuri ba bread ”

“Nop banashan tea da bread ,akwai kaza? Ko soyayyene?”

Zaro ido tayi harda dafe ƙirji
“Kaza? A nan?(kawai sai ma ta fashe da dariya)

“Aah baƙo babu”

“Halan su mama da baba basa nan ne wai?”

“Nan fa gida na ne”

“Oh dama ƴan mata suna iya zama a gidansu su kadai ba aure?”

“Sir I’m married” tsuriii ya kafeta da ido yanason gano asalin gaskiyar

“Hummm Saboda kin ganni baƙo shine zaki mun kora da hali?”

“Aah wlh da gske”

“Wow amma fa mijinki ya iya zaɓe,wlh kin cika duk wasu quality da nike neman mace dasu ,da na sami irinki da tuni nayi aure”

Sai yanzu ta masa kallon ƙurilla ,tabbas ya haɗo kuma tana kallonsa ba abunda ya faɗo mata a rai sai aure. Ji take tamkar ta rungumesa ko zata samu sassauci,lokaci daya bugun nunfashinta ya daɗa hauhawa

“Ƙatotonka dakai ba mata abun kunya”

A shagwaɓe yayi magana gamida langaɓe kai kamar zaiyi kuka

“Hum ban samu taste Dina bane ,nikuma gaskiya bazan iya auren macen da take not active a gado ba,saboda gaskiya Ni maciyi ne,I’m sorry kuma kinsan duk foodie dole yana buƙatar ɗumin active woman a Koda yaushe…”

Sunkuyar da kai tayi cikin jin kunya.

“Sorry na baki kunya ko? Ni namijine ke namiji… magana ake na gender equality ,kinsan komai na sani daga halittan mu aka halicceku ,dole muna da sha’awar jinsin da bamu dashi ko ba haka ba ?”
Shiru ta sake yi Tana jin wasu feelings da ta manta when last ta jishi yana taso mata,Zuciyarta tayi rauni ,hawaye a take ya fara kwanciya a idonta ,babu abunda takeso sai taji ɗumin namiji a kan gadonta,amma ina abun ba da sauki bane ba ,kullum ya Sheikh yana cikin Alwala baya son ko da wasa hannun mace ya shafi jikinsa bare ta karya masa Alwala.

Zumbur tayi ta mike tasa bayan hannunta tana goge ƙwalla
,tana tuna hadisin Manzon Allah da yike cewa duk inda mace da namiji suka kasance na ukunsu shaidan ne.

“Mijina ya kusa dawowa zanje in masa girki”

Dariyar yake yayi “Ok Nagode da karamci,meye sunan ki to”

“Salimat” ta bashi amsa tana nufar ƙofa da sauri ta buɗe masa , Murmushi yayi amma shidai psychologist ne ,ya fahimci akwai abinda ke damun Salima ,kuma ya kudiri aniyar zai bibiyeta a hankali.

A sanyaye ya sakai ya fice saida ya kai saman varendar ɗin ta sanann ya ɗago mata hannu “Bye Nagode fa,kyakyawa”

Dammm! Ta rufo ƙofa ta koma ta maƙale bayanta a ƙofar kawai ta kurma ihu da ƙarfin tsiya kamar zararriya.

 

 

_Plz next update na masu Aurene ,kar a karanta mun in ke budurwace_

 

Leave a Reply

Back to top button