Bakar Ayah 15
Page 🖤15🖤
Tun safe inna laari take abu ɗaya a ɗaki,Allah ya haɗata da doguwar naƙuda.
Danejo kadai ke kai kawo a tsakar gidan,sai Bombee wacce take wasa a zaure,fuskarta bushe da hawaye tayi sabbabben nata wato kuka,a rana tayi kuka yafi sau a kirga,wani lokacin har zazzabi takeyi.
Larai ce tafito daga ɗakin inna laarin ɗauke da ledar mabiyya a hannunta,saida tatsayah tayi shewa tayi guɗa kafin ta kalli inda Danejo take.
“Mashaallah yarinya ta faɗo duniya,kyakykyawa fara jinin fulani usul,kuma Alhamdulillah idonta garau yake kaman na sauran mutane,da alama bayan wacce ta kawo baƙar kaddara ita kuma wannan ɗiyar albarkar farin haske ta kawo cikin gidannan”
Danejo tana jinta bata kulata ba,saboda tasan duk maganar datake da ita take.
“Iyar sule tunda ta haihu ko a zubo ruwan kai?”
Abinne ya ƙular da larai,ganin bata biyeta ba,saima sauya zancen datayi.
Ganin larai bata amsa mata bane yasa ta ɗebi ruwan tashiga dashi.
A zaune inna laarin take akan kujerar tsugunno,jaririyar kuma tana kan gado a naɗe da zani.
“Sannu addah laari,an samu kai kalau?”
“Lafiya kalau Danejo sannu fah da hidima”
“Lahh bakomai,barinaga ƴar tawa”
Cikin zumuɗi da farincikin Danejo ta nufi kan gadon da ɗauko jaririyar,buɗe fuskarta tayi,ba laifi kam kyakykyawa ce kaman yanda larai din ta faɗa,saidai bata da fari da kuma manyan ido irinna Bombee,saika kula ka gano kamanninsu,shima dan hancin baban su dukka suka iya shiyasa.
“Tufarkallah gatanan kam kyakykyawa da ita,addah laari kefa ta iyo,munsake samun Budurwa a gidan,allah ya rayata bisa imani”
Murmushin jin daɗi inna laari tayi,jin yadda ake gwaɗa ƴar tata.
“Ameen ya Allah Danejo,Allah ya bamu ikon rainonsu a bisa daidai dukkansu”
“Ameen”
Suna cikin zancene larai ta dawo ɗakin,harara ta watsawa Danejo,tunda ga kallonta zakasan bata sonta.
“Laari na kaimiki ruwan banɗaki,iyah maiganye ma tana hanyar shigowa yimiki wankan”
“To sannu da kokari larai”
Suna cikin hakane Bombee ta shigo ɗakin jikinta duk ƙasa,taga tsakar gidan babu kowa shiyasa tabiyosu.
Danejo ce takalleta tareda cewa.
“Yaki zokiga ƙanwarki ta iso to yau,kina ta tambayar yaushe zata zo,gashi tazo yau”
Aikuwa tana jin hakan ta taho gudu har tana zubar da kayan tasuke gabanta,wajen Danejo take rike da yarinyar ta nufah,inda itakuma Danejo ta iyo kasa da ita yanda zata ganta dakyau.
Hannu takai abinka da yaro zata tabata,larai ce tayi saurin cewa.
“Tsaya tsaya menene haka Danejo,saikace bakya kula,jaririyar da ko suna ba’ayi ba zaki bar wanann ƴar taki ta daba,idan kuma ta shafamata wannan idonnata fah,ni wlh yanzu haka a takure nake data shigo ɗakin,inaga kuma jaririyar da aka haifa yau”
Dagowa daneji tayi ta kalli larai tareda rike hannun Bombee wacce take ƙokarin taba fuskar jinjirar.
Cikeda bacin rai Danejo tace.
“Wai nikam larai mai na taremiki a rayuwane,koyaushe cikin jifana da kalam mayu kikeyi,ina kawar da idona ina raga miki domin girmanki amma bakya gani koh,fisabilillahi banda abinki yaushe wannan yarinyar tasan kalmar maita. Dazakice zata shafamata idonta,itakuma waya shafa mata kenan?.
Ni inada imani da tawakalli sannan kuma na yarda Allah ne yayi ta haka,domin haka yaso ya ganta,ina da labarin duk izayar da kike saka ƴaƴanki suyi mata a waje,na barine saboda fitina bbau daɗi………”
“Aikin banza kin daɗe baki bari ba,dan Allah ki ɗau mataki kinji,ke bakisan kema ragamiki ake saboda darajar mlm Ahmadu ba,banda haka da tuni an daɗe da korarku daga garinnan keda wannan mayyar ƴar taki,waye bai san irinku da harkar maita ba. Kullum saiki tura ta tana shiga cikin ƴayanmu kalan ta cinye su,hakan bai miki kin kawota kusada jinjira saboda ta lashi samuwar kuruwa koh?”
Suna cikin maganar ne Danejo ta manta tasaki hannun Bombee,aikuwa kaman jira take itama tarigima ta ɗora hannun akan jinjirar.
Tana ɗora hannun yarinyar ta callara ƙara kaman an zare mata rai lokaci guda.
Zaro ido Danejo tayi tareda kallon mai yafaru,dama haka larai take jira,aikuwa da sauri ta sure jinjirar daga hannun Danejo.
“Kingani koh kinga ni ko akan idanki,ke kuma laari barsu su kashe miki ƴa tun bakiji ɗuminta”
Buɗe baki Danejo tayi zatayi magana,inna laari tayi saurin cewa”
“Danejo kiyi haƙuri,amma larai gaskiya tafaɗa,bai kamata a dunga barin Bombee tana zuwa kusada yarinyar ba,musamman da yanzu tana jinjirar,saboda gudun kar wani abu ya faru,idan gaba ta girma babu matsala saita rabeta”
Lokacin da inna laari ta baɗi hakn,daneji ji tayi kaman an doka mata guduma a ranta,saidai yazatayi gaskiya suka faɗa,kowama inshine bazai yardaba,musamman yanda tayi shekara da shekaru babu haihu,lokaci ɗaya Allah yabata,zata iya komai domin kare ƴartata da mungun abu irin ƴar tata.
Ƙoƙarin maida hawayen idonta tayi,tareda jan hannun Bombee suka fita daga ɗakin,wacce take ta yunƙoron kamo jinjirar daga hannun larai,buge hannunta larai tayi tareda gallamata harara.
Hanyar ɗakinta tanufah idonta yana zubar da hawaye.
Zama tayi akan kujera tareda saka Bombee a gabanta tana kallonta.
Duk wanda yaga Bombee zai iya ɗauka cewar badaga nigeria take ba,farace sosai mai kyau,kana ganinta kaga fulani,bayan idanunta wanda su suka rana kamanninta da ƙasar tata,dan idan tana kallonka,mus
musamman idan ka zuba mata ido na wani lokaci,kana ganin yanda ƙwayar idon take girma sannan kuma tana ƙanƙancewa gwargwadon yanayin hasken dayake wajen,ga ƙwayar idon blue shar,kullum sake clear take da tana girma.
Babu wanda zai kalleta yace ba a ƙasashen turawa aka satota ba.
Kama hannunta Danejo tayi ta haɗasu kafin tafara magana cikim karayar zuciya.
“Zakiga jarrabawa a ratuwarki kala kala Bombee,amma kiyi haƙuri ki daure kinji,nidai fatana shine ki dunga haƙuri idan anyi miki abu,wanda yajefeki da sharri ki mayar masa Alkhairi,wanda yaƙyamaceki karki ji haushinsa,kiyi nesa dashi kawai saboda karya cutar dake,idan kinje wajen da bana tareda ke,ki tuna Allah na tareda ke kinji”
Tana gama faɗin hakan ta rungumota jikinta,tareda ƙara sautin kukanta.
A cikin kunnenta tajiyo ƙaramar muryar Bombee.
“Inna ki daina kuka,ko su sulene suka dukaki,insun dukaki bazan barsu ba,saboda dukan su da ciwo sosai”
Ƙara ƙanƙameta tayi jin abinda take cewa.
“Ahah basu dukani ba,in sun dukani ma zai wuce watarana,idan ban ramaba Allah zai ramamin,kuma inya tashi ramamin da zafi zayyi musu,suma suyita kuka”
Ƴar dariyah tayi kafin tace.
“Heer kuma nayi ta musu dariya yanda suke min idan ina kuka koh?,uhm inna barina je wajen yarinya”
“Ahah karkije wanka ake mata,sannan babu kyau a je wajen yarinya idan tana ƙarama,saita girma tukunna sai a goyamiki ita,ina kinaso koh”
“Eh inaso,zan jira ta girma toh saimuje wasa,nima shikenan nasamu ƴar wasa irinna su Sule”
A hankali da lallami Danejo ta dunga amfani da hankalin Bombee,har ta koyamata kartaje kusada ɗakin inna laari,saboda gudun abinda zaije ya dawo.
Ranar suna biki da bidiri akayi,inda yarinyah taci suna khadijah,mahaifiyar inna laari,ana ƙiranta da Innayi.
Haka akaci aka watse kowa yakama gabansa,aka bar mai jego da rainon ƴarta.
Haka rayuwar tasu tacigaba da kasancewa tareda ƴaƴannasu,Danejo ce mai yin girki kasancewar inna laari tana jego.
Ko yaushe idan ka jisu itada Bombee to akan taje wajen innayi ne,sau goma zata shiga ɗakin sau goma zata korota,tun abin yana da damun Danejo har tashafawa ganta lafiyah ta zuba musu.
Duk sanda a yanzu mutum ya zauna da inna laari batada aiki sai zancen ƴar ta,wani lokacin a shiryata a kaita gidan larai,sai tayi kuka a saka sule ya kawota.
Itadai Danejo ido ne nata kawai,dan tafi danganta hakan da inna laari tana son ƴar ne bata son Bombee ta rabeta.
A bangaren mlm Ahmadu kam,tabbas yayi murna ta haihuwar innayi sosai,amma kuma har yanzu soyayyar Bombee a ransa ta dabance,don ko boyewa baya iyayi,abin kwanciyar hankalin ma shine inna laari batada dakuwa da hakan sosai,ita indai tana son ƴar ta shikenan.
Ranar daya gane inna laari bata son Bombee ta dunga kusantar innayi abin yabaci haushi,hakan yasa ya ƙirasu dukka a turakar sa,kallonsu yayi cikin kulawa kafin yace.
“Uhm uhm toda farko dai inason yimuku ƴar nasihane.
Duk garinnan babu wanda baya yabonku a zaman lafiyah,amma kuma sainaga abinda ya batamin rai,shine kuna ƙoƙarin raba kan ƴaƴanku da kakanku,musamman daga bangarenki Laari,kuma wai kece babba,hakan bai dace ba.”
“Mlm kayi haƙuri,gani nayi data tabata ranar haihuwarta tayi kuka,kuma sannan larai tayi min kashedin na kiyaye”
“Saboda ita larai ɗin itace tafiki sanin yakamata,idan akwai abin citarwa a jikin Bombee kaman yanda mutane ke faɗa,ke ya kamata ki rigasu sani. Dan Haka dan Allah karku bari wasu su ruguzamin zaman lafiyar gidana,ku haɗa ƴaƴan ku ku rainesu tare,su tashi cikin ƙaunar juna”
Tundaga wannan lokacin inna laari ta daina abinda take,dan har ƙiran Bombee take tasaka mata ita akan cinyarta. Wannan abin yayiwa Bombee dadi sosai,don sakawa tayi a ranta wataƙila lokacin yayi da innarta tace za’a dunga bata itah.
Shigowa tayi da gudu tareda ɗanewa mlm Ahmadu wanda yake zaune a kan tabarma yanajin rediyo.
“Baba nayi ta ɗaya a makarantar Mlm Alwasu,kagama ya bani biscuit,sai mu raba nida innayi koh”
Tafaɗa tana nuna mlm Ahmadu allonta cikin murna”
Hannunta yakama wanda Allon yake tareda share ƙasar dake kan ciwon wajen,wanda yake fitar da jini.
Cikin tausayawa ya kalleta tareda cewa.
“Wannan kuma uwata a ina kikaji,faɗuwa kikayi?”
“Ahah su bello ne suka tureni akan itace suna cewa ‘mayyah taci na ɗaya’,baba wai sunana mayyah?”
“Ahah ba sunanki mayyah ba,mai kika ce musu toh”
“Ban kulasu ba,kawai cewa nayi idan ban ramaba Allah zai ramamin,yanda inna tace na dunga faɗa”
Kanta yadafa cikeda tsantsar ƙauna kana yace.
“Hakane uwata,hakane ɗiyar albarka,wanda aka zalunta bai ramaba Allah zai saka masa,kinyi daidai kinji,haka nakeso ki kasance kullum,ina alfahari dake uwata,Allah ya albarkaci rayuwarki”
Duk abinda suke su inna laari suna kallonsu,suna gyaran ganyan shayin mlm Ahmadun.
Sai bayan sun gama taɗinsu irinna uba da ƴa kafin ta nufi wajen su danejin ta nuna musu.
Kafin daga baya ta miƙawa innayi nata biscuit ɗin.
*forseen*
…………..Babu wanda yake sonki,kifara son kanki,duk wanda ya ɗaga miki hannu ki karyashi,ke ba sa’ar su bace,muna tare dake fansa fansa fansa
Shuru tayi tanajin maganar da sheɗaniyar muryar takeyi a cikin kanta.!!!……………..
🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03
*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna
______________****_______________