Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 16

Sponsored Links

Chapter 16

Ki karɓa mana kintsaya kallo harda rawan jiki ta faɗa tana miƙomun zoben,ni kuwa kallon sani nakewa zaben aina wajen waye wannan ne bazan iya tunawa ba.
Karɓa nayi da bismillah sauri shammatata tayi ta karɓe tana cewa”kinga mikomun hannunki nasaka miki,hararar ta nayi a wasance nace kinjiki da wata batu saurayina de zai samun zobe a hannu ba wai in miƙa hannu na haka kawai kisamun zobe ni ƴar daɗi zobe ina kare magana nayi saurin warce zoben ina sawa a yatsana bakina ɗauke da bismillah kuwa dumm gaban fadila ya faɗi dan an sheda mata karta bari na anbaci sunan Allah kafin nasaka zobe take wani irin zufa yakaryo mata,niko ko kula da yanayin ta banyi ba,nashiga juya hannuna ina yaba kyan zoben da gudu nayi waje ina zuwa na faɗa jikin Anna.
Shafa kaina tayi tana”kai Aisha kede kan bakya girma goɗe goɗe dake zaki fadamin jiki haka dariya nayi nace”Anna inasonki kece komaina kece duniyata jarumar uwa ɗaya tamkar dubu”kai Aisha bakinki kullum baya gajiya da fadi abu ɗaya”Anna kenan taya zai gaji ai sonda nake maki baki bazai iya fadin irin sa ba,khadija da mubaraq suka hada baki wajen cewa”Anty aisha mufa?”ai kune gaba gaba bayan Anna dariya suka fashe dashi cike da farin ciki da murna nace Anna kinga ƙawar amana ta sayo mana zobe ni da ita iri guda kallon zobe Anna tayi tace masha Allah Allah yasanya alheri yakuma haɗa kanku yabar zumunci”amin muka amsa harda fadila da tafito a dakin hannunta riƙe da wayar ta tace Aisha zo kirakani ku gaisa da shi.
“da to kawai na amsa dan dama da hijabina ajikina muka fito tare daga cikin gida motarsa na tsaye bakin layin mu babban mutum ne kaman a girme yama girmi baban fadila amma saboda ganin kuɗi wai wannan ne saurayin ta,gaidashi nayi cikin sakin fuska ya amsa da tambayata ummana na amsa da lafiya”Aisha ko gyaɗa kai nayi murmushi yayi yace ai kullum sai kawarki ta ambaci sunan ki lalle tana ji da ke”nima murmushin nayi ina kallon fadila nace”ai nima ainaji da ita dariya yayi sallama nayi musu har najuya yatsaida ni yama miƙamun kuɗi yace ki sayawa ƙannenmu sweet godiya namasa na karba nawuce na barsu tsaye jinjine da mota fadila taso yimun tattaki nace gaskiya kikoma kin bar mutum tsaye dole ta koma gunsa nikuma nawuce gida.

“fadee baki da hankaline ko kin mance da sharaɗin shugaba ne?bayan wucewar Aisha yafara yima fadila fada kaman kuwa zeyi duketa,
Fadila tayi rau rau da ido tace”wallahi duk shammatar ta danayi amma bansan yanda akai haka ta faru ba. kuma kai kanka shedane hana Aisha ambaton Allah abune mai matukar wuya kade gani koshi kansa shugaba nasan zemun uzuri zuwa gaba.
Huumm ya sauke numfashi yace”saura aiki na gaba ki kula wallahi kar asamu kuskure idan ko aka samu kema kinsa sauran kinde ga yanda shugaba yakewa iyayen gidanmu faɗa bare kuma ke wallahi kikai wani kuskure keda yin kuɗi saide gani daga nesa amma bade kiyi ba.
Saurin katsashi tayi tana cewa ya kekemun bakine dan Allah daga yin kuskuren farko,hmm”ai ke kike ganin hakan amma shugaba besan uzuri ba kinde ga yanda ranan yake ta balbale Alh sunusi kan wani kuskure da yayi shima kan wani mai irin hali kamande wannan ƙawa taki danko ansha kawo shi matsafa amma wallahi saboda ambaton sunan Allah da kira’a idan yafara kaman a harami har bakin sa ansha ɗaurewa amma baya fasa ambaton sunan Allah a zuci haka har za watsa zaman batare da ankai matsaya guda ba,yau kimanin shekaru takwas ana azabtar da bawan Allahn nan wallahi haryau bata canja zani ba.
Dan shugaba yace a kyale shi kawai idan an matsa kungiya zata iya tarwatsewa.

Ahmad koda yadawo daga masallaci kwaciya yayi saman sofa dake cikin bedroom dinsa mafarkin da yayi daren jiya shi yarinƙa zuwar masa kaman jin abun yake kaman azahiri haka yafaru ba mafarki bane,
Yana cikin tarawa da kwashawa hat bacci yayi awun gaba dashi be tashi farkawa ba sai wajajen karfe 11am bakinsa ɗauke da salati yata yafaɗa toilet wanka yayi yafito ɗaure da towel a ƙugunsa yana yane gashin kansa da karami mayuka masu daɗin kamshi yafashe jikin sa dasu sannan ya saka kananun kaya ya feshe jikin sa da turaruka yanufi main falo dan yunwa yakeji bana wasa ba.

Sallama ɗauke da bakinsa yashiga ya tadda amminsa zaune tana kallon sunna tv,maza yayi ya ɗaura kansa saman cinyarta kaman wani karamin yaro yace”ina kwana Ammi shafa suman kansa tayi tana sakin murmushi tace”lafiya lau Ahmadi fatan de yau lafiyanka kayi irin wannan bacci?
Toro bakin sa ya ɗanyi a shagwaɓa yace”kwanciyane da banyi da wuri ba jiya yana faɗin haka yace”Ammi yunwa nakeji,
Murmushi ɗauke saman fuskarta tace”oya tashi muje nabaka abinci tare suka iso dining table tayi savin ɗinsa saida ya ƙurɓi black tea kaɗan sannan yace”Alhajin ki jiya be kwana a gida ba hala lafiya fitan dare haka?

Fuska da alaman damuwa tace”ahmadi wasu lokuta nima kaina abunda Abbanku yake yana damuna ace mutun kullum idan za ayi meetin sai karfe biyun dare kaman wasu matsafa danayi magana ya hauni da faɗa,shiru ta ɗanyi jin kaman takun sawu suka juya dan kallon mai tafiya illa kuwa shiɗinne”gulmar me kuke kun haɗa kai da ɗanki?
“Ina kwana Alhaji
“Lafiya Ahmad yau baka fita bane?
“Eh yau lahadi ya amsa masa a takaice.
“Zubomun abincin mana Ammin yara kintsaya sai kallona kike kaman kinga wani sabon halitta a gabanki.
Hmmm ta sauke ajiyar zuciya yasan abunda takema shima kuma har ga Allah bayaso yana ɓata mata rai shi kansa besan yadda akai ya tsinci kansa cikin wannan ƙungiya ba tsomo tsoma dan ma shi ba kowani irin sharaɗin su yake bi ba.
Dan a cewarsa bashine yashiga cikin su ba susuka jashi.

Bayan sun gama sun koma falo da zama,Alh badamasi cikin tsare gida yadube su yace”dama inason magana daku,gyara zaman su sukai suna fuskantar sa,ajiya zuciya yasaauke kana yace”jiya mun tsaida auren yaran nan,a zabure Ammi ta miƙe ta zuba masa ido karon farko daya tsinci kansa da jin shakkarta ya haɗiyi ƴawu mai kauri mukut,yi hakuri ki zauna muyi magana mana ma’arufa ya kira sunan ta cikin sanyin murya.

Nunashi tayi da hannu tace”zaman me zanyi saide inaso kasani darajan ɗana yafi asaka ranan auren sa gaban mushirƙai waƴan da suka kwashe kayansu a gaban ma’aiki,shin baka da ƴan uwane koni bani dasu shi uban yariyar da uwar ƴa basuda ƴan uwane da zaku rasa inda zakuyi maganan aure sai karfe biyun dare gaban matsafa to wallahi da ahmad ya auri wannan yarinyar kwara yayi auren wucin gadi a mutunce”enough is enough ya daka mata wani irin tsawa ranshi yakai ƙololuwar ɓaci cikin kakkausan murya yace zancen banza kenan aurene ba fashi nan da wata guda sannan ɗanki shine wanda ze tare gidan surukansa dan yarinya bazata tare a gidan sa ba,wani dummm sukaji maganan nashi katamkar saukar arado.

Leave a Reply

Back to top button