Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 45

Sponsored Links

CHAPTER 45

Aisha koda tashiga garden ɗin zamanta tayi dan wajen yana da daɗin zama ga shukan furannin da kuma kukan tsuntsaye ga wani iska mai ni’ima dake kaɗawa kamshi furanni dake tashi waje luf tayi tana tunanin wai yanzu ita matar aurece,yanzu bata da hurumin yin komai sai da izinin wancan banzan kwarton mai halin bunsuraye kai ina kilama su Ammi dan basusan halin sa bane yasata zo tayi ta rokonta alfarma da tasan halin ɗanta ai baxata wahal da kanta wajen zuwa bata baki ba,yanzu ya xatayi da suhail ita fa shine wanda zuciyarta ta aminta dashi badan kuɗi ko kyansa ba saide dan kyan halin sa da ganin girma da darajan ɗiya mace.

Hajiya mariyah da kawarta hajiya bilkisu gurfane suke gaban wani ɗan tsamurmurin tsohun bokan sun gurfana gaban sa kaman masu neman gafara,hajia balkine cikin rawar jiki tabuɗe baki wajen cewa”ran boka ya daɗe wannan itace ƙawata danake baka labarin ta mungurfana gabanka domin neman taimakonka da agajinka cewar hajia balki bude baki hajia mariyah tayi da nufin koro masa bayani yayi saurin ɗaga mata hannu cikin kakkausan muryarsa mara daɗin sauraro yace”basai kinyi mana bayani ba munsan da zuwanki tunkafin ku zo auta ya sanar dani bukatar ki saide kinyi sake dayawa yaron da kuke son aura masa ɗiyar ku ba ɗiyar taku bace arayuwarsa wata yarinyar ce ta daban.

Wani irin zabura hajia mariya tayi batasan sanda tabuɗe baki ta furta”ya rasulu manzon Allah ba,wani gigitaccen tsawa bokan yadoka mata yana ƙara jaddamata karta kuskura ta sake irin wannan gangancin anan,tsuƙwi da kai tayi tana mai neman gafaran sa.

Wani ƙwarya ya miƙo musu dan madaidaici cikinsa cike yake da ruwa yace”ku kalli ciki ku gani,a tsorace suka leƙo da kawunan su Ahmad ne tsaye sai wata yarinya da basa iya hango fuskata tsaye saide suna iya kallon ta rungume da towel ta juya masa baya.

“Kan bala malam mezan gani?
Karde ace auranta yayi asirrance ita kanta bata san sanda bakinta ya subuce wajen fadin hakan ba.

Girgiza mata kansa yashiga yi yace”ko ɗaya saide sakacin ɗiyarki zesa hakan ya kasance,cikin rawan baki hajia bilki ta amshe da”yanzu malam ina mafita?
Bushewa yayi da dariya saida yayi mai isarsa sannan ya dubesu da ƙananun idonsa yace”mafita ɗayane zan baku magani kuba ɗiyar taku tayi tushe dashi kuma ta tabbata taja ra’ayinsa ya kusance ta sannan duk abunda yafito ta jikin sa ta goge da farin ƙwalle ku kawo nan.

“Amma…..kallon da yawatsa mata yasata haɗiye maganan da takeso tayi hajia balki kuma na zungurinta tayi shiru dole ta haɗiye abunta muƙut…..nunatayayi da yatsansa yace”nan ba wajen gardama bane kuma ba wajen yimana musu bane duk abunda muka faɗi anan gaskiyace bama fadin karya saide mufaɗa ba daidai ba.

Mijinki yana cikin wata ƙungiya to kice dashi yatashi tsaye yayi sake ɗan zaki ya girma akwai wata gagarumar ƙalubale dake tunƙararsu kungiyar tasu zata ruguje kaman ba’ataɓa yinta ba sannan ze dawo faƙirin sa kaman yanda yake daa sakamakon cin amana dayayi.

Hhhhhhhhh yasake kecewa da wata iriyar dariya mara daɗin sauraro da amonta ya amsa duka cikin dajin tsoro fargaba duka yarufe su hajiya mariya”kutashi ku tafi ansallameku kufita da baya ahankali karku take yaran aljanu sukaji wata murya daban wanda bata bokan ba,kululu cikin su duka ya ɗuri daruwa itako hajia mariya har gudawa takeji kaman ze zubo mata saboda tsaban firgici da take ciki.

*******
Aisha shagala tayi zaune a garden harbatasan adadin wani lokaci ta ɗauka ba kaman daka sama iska ta kaɗo wani hoto takafaɗa saman cinyarta,ganin takarda mai kaman hoto yasata saka hannu ta dauka ta juyar da fuskar na cikin hoton sosai tana kare masa kallo ko kiftawa babu can tasaki murmushi ganin anyi rubutu kaman hakan WANTED”aikin banza ta furta a fili suna xaune cikin AC suna saka mutane wahala alhalin su kansu sunsa inda wayan nan miyagun suke dama.

“Aishatu bakiga wani hoto ba,wallahi ina tsaka da tattarewa iska ta barbazasu.

Yah faisal ne ke magana yana ƴan dunbe duben sa a bayanta saida ta juyo taga ashe hotunan suna dayawa bama ɗayan nan bane”gashi nan ta faɗa tare da miƙo masa hannu yasa yana karɓa yace”wallahi aikin nan duka yasani gaba gashi lokaci da aka ɗibarmun harya kusa cimmini amma haryau bawani karin haske daga kowace kusurwa.

“Inako zakaga karin haske bayan dasaka hannun manyanku ake aiwatar da komai”what mekikace?
Yafaɗa yana samun waje yana zama a ɗaya daga cikin kugerun wajen da aka tanadasu dan shan iska.

“Ni bance komai ba,tafaɗa tana ƙoƙarin miƙewa ta bar wajen dan saida yayi maganan tagane ashe fa zancen zucin da take yafito fili.

“Please dan Allah Aishatu kisake maimaita abunda kikace,kinga wannan case ɗin saura mako guda a amsheta daga hannun na kuma wanda za bawa kowa yasan ba mutumin kirki bane ƙilama idan case din yakoma hannunsa komai sai yafi na yanzu lalacewa Aishatu nashiga wannan aikinne da zumman kawo canji kasata da garina amma wallahi tunda na fara aiki nake fuskantar bara zana da rayuwata wataran har tsoro nake karwani abu yasami ahalina duka ta sanadina,yanzu haka na aiyana araina matukar nafaɗi kan wannan bincike zan bar aikinne baki daya dan banga amfaninta ba tunda bazamu iya ceto rayuwar ƙananun yara daga hallakaba bazamu iya ceto yaruwar ƴaƴa mata da ake lalatawa ba,gamu muna amsa sunan jami’ai amma bamuda amfanin komai a kasarmu saide kawai mushiga mota mukunna jiniya muna yawon yin bincike amma babu nasara.
Yaƙare magana yana dauke ƙwallah daya taru a idonsa tare da miƙewa ze bar wajen.

Tausayinsa ne ya darsu a zuciyar Aisha tabude baki dakyar tace”shi na wannan hoto nasan inda yake yana shagon aski JB barbin saloon kusada babban shagon rufaida yogouth shago mai NO17 zaka sameshi kimanin karfe biyar da rabi na yamma dan mafi akasari idan mun tashi a wajen aiki nan muke yawan ganin sa zaune dukda bansan abunda ke kawoshi wajen ba,amma yana da yawan kallon mutane kaman be yarda dasu ba,zan iya taimaka maka idan har kabani daman hakan dan ganin kakamashi amma banson koda munje waje kai kafito daga cikin motanka dawuri sannan karka tafi da motar da aka sanka da ita dan o ready manyanku sun rigada sun basu bayananku dama fuskokinki amfani suke daku dan cinma manufofinsu idan ko kun kamasu wahalan banza kukesha cikin awa da be gaza biyu zuwa uku ba zasu saka kubarsu to me amfanin wahal da kanku dan ganin kunkawo canji,yah faisal canji nan fa baze samu ba harsai muda kanmu munkankare tsatsan dake zukatanmu sannanne canji zezo mana.

“Like father like dauther shekarun baya haka mahaifinki ya tsaya gaban manyan jami’an tsaro da manyan dattawa masu faɗa aji akasar harma da sarakuna yayi wannan maganan saide ko wata biyu ba rufe ba mukaji labarin wai yafita ba ganshi ba.

Ahmad ne dake zaune duk tunanin duniya ya taru yama kansa yawa gashi yau wannan ƙwailar ko gilmawarta be gani ba karde tace zata bar aikinta dan kawai taji ance an aura masa ita tace zata goga ƙafaɗa da kafaɗa dashi hmmm ya sauke ajiyar zuciya daidai secretary ɗinsa mai suna jamila ta buɗe ƙofan office din sa ta shigo sai wani yauƙi take kaman karkashi ita adole ta burge ogannata koda ze kyasa.

 

Hajiya mariya koda suka dawo gida shiganta bayi uku sannan ta ɗan tsahirta koda Alh sunusi yadawo haka ya taddata kwance saman doguwar kugera tayi rajab”mariya lafiya na ganki haka duk kinwani susuce?
“Hmm ba lafiya ba Alh jin amsa data bashi yasashi komawa ya zauna yana cewa”ina sauraronki amma dan Allah kadaki sake dauramun wata damuwan.

Kallon sa tayi ta watsar tana cewa”dadina dakai rashin hakuri to gashi gashi abunda malamin yace da mukaje ɗazu da bilkisu gwara musan nayi tun kafi komi ya kare mana.

 

ALLAH YASA MUDACE

[5/24, 11:43 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button