Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 22

Sponsored Links

Chapter 22

Fadila taji shaƙa sai muzurai take tana jujjuya kai kashedi sosai Alh shehu yayi mata sannan ya yadata gefe faɗi ƙasa tayi tana maida numfashin wahala can ta miƙe jiki ba ƙwari ta saka kayanta ta ɗauki jakarta saida takai ƙofan fita daga falon ta waigo ta kalle sa tace”ni kawa haka ko?to wallahi kasaka a ranka fansar wannan shaƙarda kamun akan aishan zan ramata saide duk abunda zakai kayi amma wallahi ba abunda ze canzan ra’ayina dan tun farko kaine wanda ka ɗaurani wannan hanya kuma a haka zan tafi,tana kare maganan tasaka kai ta fice a falon biyo bayanta yayi ta kwasa aguje tayi waje.

“Basma wai haryanzu kukan kike?
Cewar mummynta data gaji da rarrashinta ta fita zuwa falo amma zuciyarta ta kasa hakura ta sake dawowa ɗakin still samun ta tayi kwance saman gado tayi rubda ciki kawarta salaha na xaune gefenta sai bata baki take amma taki yin shiru.

“Bass tashi muyi magana cewar salaha data gaji da bata baki miƙewa tayi zaune fuskanta a kumbure idanunta yasake ƙanƙancewa sabida kuka data sha.

tambayanki zanyi amma dan Allah karki ɓoyemun komai dan musan inda mafita take,gyaɗa mata kanta tayi sannan salaha ta gyara zamanta ta cigaba da cewa tunda kike da ahmad ya taɓa ɗaukan waya yakiraki da karan kansa?
dan yaji lafiyarki ko irin kuyi hiran nan?
Shiru basma tayi mata bata bata amsa ba,
Ok to na fahinta cewar salaha amma yana tura miki sako irin na morning ko na good night?
“A’a ko sau ɗaya baya kirana ko ya turamun da sako idan ma nakira shi a waya gaskiya baya ɗagawa idan ma ya ɗaga wayan saide yace mun ze kirani yanzu yana busy sannan idan natura masa da sako ba reply basma ta bata amsa wasu hawayen nasake bin ƙuncin ta.

Shiru ɗakin ya ɗauka daga salaha har basma ba wanda yasake yin magana,numfashi salaha ta sauke sai kuma tace”gaskiya basma abunda zance dake anan ahmad baya sonki ne ko baya ra’ayinki idan da aca yana sonki wallahi idan shine agogo sarkin aiki idan yaga kiranki ajiye komai nasa zeyi yabaki lokacin sa idan sako kika tura masa kuwa sai yayi gaggawan maida miki da amsa ba wai ya shareki ba.

riƙo hannun salaha tayi idanun ta na zubda wasu hawaye masu ɗumi tace”dan Allah salaha ya zanyi wallahi inason ahmad idan narasa shi…rufe mata baki salaha tayi da tafin hannunta tana girgiza mata kai,hannu tasa tacire hannun salaha da tarufe masa bakinta tace”barni kawai nafadi abunda yake raina salaha wallahi da ban kamu da soyayyar sa bane da sauki amma meyasa zeyimun haka bayan zuciyata tagama kamuwa da soyayyar sa.
“Saboda bashi ke sonki ba haɗaku akai kuma ƙila shi wannan haɗin beyi masa ba,idan da ace shike sonki hakan bazai faru ba,sannan be dace ace iyayene zasu zama masu haɗa connetion a tsakanin ki da shiba,dolene muyi ƙoƙari wajen fidda iyaye dake kai kawo tsakanin ku,kun sa santa kanku inaga hakan zefi.

Hakade suka cigaba da tattauna matsalan su da kuma yanda zasu magance komai.

“Khalid gaskiya wannan yarinyar akwai abunda ke tattare da ita wannan nakasa fahinta,
“Wacce yarinya kake magana akaine?
Cawar khalid dake tura sakonni wa abokin kasuwancin su-Al bazz dake kasar sudan.

Tsuka yayi dan besan yayi maganan bama da yake abun nacin sa a rai saboda yawan ganinta da yake amafarki tana neman taimakon sa,abun yana daure masa kai dan duk sanda ya kwanta da irin mafarki da yake wani ya tashi a firgice wani kuma yatashi yaji jikinsa yayi masa weak.

Kiran suhail ne yashigo wayan sa ɗagawa yayi suka gaisa nan suhail ɗin ke cewa dashi”haba Ahmad dan Allah waƴan nan dogin rigunan nake so sun mun kyau ko nawane kafaɗa mun fashisu wallahi zan biya munada gasan da za’ayi watan gobe inason muyi amfani da su nasan kuma zamuci wannan gasan kuma kaine wanda ze samu wannan ɗaukakan…dakuma tellah data ɗinka wannan yakan ko yaɗinka please mana ahmad dan Allah karkace a’a wallahi na ƙwallafa rai a wannan kayan tun ranan da ka daura a status ɗinka.

Dariya khalid dake zaune a gefe yayi dan shima yanzu chattin da suka gama yi da Al-bazz kenan akan waƴan nan kayan,dayake wayan a hand free ahmad din yasaka khalid yanajin komai”zanyi shawara ahmad kawai cewar ahmad ya kashe wayan yana mai dafe da kansa dake ɗan sara masa kaɗan kaɗan sakamakon bacci da besamu yayi jiya ba.

“Dazu naji kace yarinya wacce yarinya kake magana akanta sannan wani irin taimako zamu iya mata?

Shiru yayi kaman baze ce komai ba sai kuma can zuciyarsa ta bashi shawaran kawai ya fadawa khalid kawai.

“Khalid ina cikin wani hali da nakasa tantancewa akan wannan yarinyar Aisha jin ya ambaci sunan da beyi tsammanin ji daga bakin sa ba hakan yasa shi maida hankalin sa kaco kan kansa”Aisha kuma broo a iya sanina dakai ban taɓa ganin ko magana tana haɗaka da ita ba bayan na aiki ba.

Numfashi ya sauke kaman ba zai sake yin magana ba har khalid ya fidda rai da zeyi maganan can kuma sai yace”kawai basirarta na bani mamaki dan ban taɓa ɗaukan ma aikaciya wacce take da abun mamaki da ban al’ajabi irinta ba.

Shiru khalid yayi dan yasan ba haka yayi niyan faɗa ba,kawai ya canza zancen ne.

Fadila cikin ƙunan rai da takaicin wai Alh shehu aisha yakeso ba ita ba,bayan ɓata mata rayuwa da lokaci dayayi yanzu zexo ya wani ce,hmm wallahi bazata tsaɓoba.

Dadare Aisha na kwance bacci ya ɗauke ta Anna dake zauna tana tofa mata da addu’a dan yanzu ita abun na Aisha ya fara bata tsoro mutum ace kullum daren duniya bashi da lafiya amma da gari ya waye kuma yatashi lafiyar sa garas sai ɗan abunda ba rasa ba,kuma a tambayeta bazata iya tuna komai ba.

Tayi nisa cikin tunani kawai ta tsikayo muryan Aisha na magana da karfi tana bige bige tana kaukawa,sunan da taji Aisha ta ambata yasata miƙewa a zabure ta riƙe hannun Aisha tana jijjigata da kiran sunan ta.

Leave a Reply

Back to top button