Hausa Novels

Kanwar Matata 2

Sponsored Links

🦜 *_K’ANWAR MATATA_*🦜

_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_

☀️ *ZAFAFA WRITER’S ASSOCIATION*☀️

Page 2

Sarah dake matsar hawaye zaune a bakin gado ta mik’e ta fito ta tsaya nan daga bakin k’ofa ba tare da ta kalli inda su Lamin suke ba. Sama kawai ta zubawa idanu tana kallon hadarin da ke k’ara had’uwa. “Oh ni inzo nan ke nan in same ki ko, shafaffa da mai!” Fad’in Lami a fusace kamar zata yo kanta. A hankali Sarah ta sauko daga kan dandamalin k’ofar d’akin ta nufi inda su Lamin suke tana kallon k’asa. “Munafuka annamimiya, makira! Sai ki rik’a yi sumumi-sumumi kamar ta kirki, ashe a bayan fage Allah kad’ai ya san abubuwan da kike shukawa. Ya kiyi magana ko sai na hamb’are ki a nan wajen?” Lami ta fad’i tana mai kai mata duka Sarah tayi saurin kaucewa. “Lami wannan yarinyar fa ba magana za tayi ba sai ki had’a mata da duka. Kin fi kowa sanin irin taurin kai da kafiyarta tun tana k’ank’anuwarta. Ke kika bamu labari idan tayi zuciya ko nono kika bata bata karb’a, idan kuma kika matsa mata ta kama, to ranar kan nonon ki kamar zai tsinke tsabar cizon da take ganna maki. Ai wannan yarinyar jaraba ce a gidan nan. Ita ta d’ebo halin tsoho kaf!” Fad’in Hassana tana hararar Sarah. Sarah kuwa wani d’agowa tayi ta watsa mata harara tare da fad’in, “Idan ni annoba ce, ke kuma wulak’antacciya tsinanniya mai zagin uban da yayi sanadiyar zuwan ki duniya! Na gwammaci inyi ta d’ebo hali da dabi’un mahaifina har k’arshen rayuwata da in d’auki irin naku halin. Ko kunya bakya ji, babu aure amma kin ajiye y’ay’a uku duk shegu. Kuma a hake kike fita kina yawo kowa ba kallon ki yana nuna ki a unguwa. Ku jawo mana abun fad’a da zai bibiyi tsatson mu har k’arshen mu. Allah ya isa tsakani na daku kun hana ni aure saboda mugayen halayen ku. Duk wanda ya fara zuwa waje na, k’ark’arinsa sati d’aya, shima kamun ya gano asalin su wanene y’an gidan mu. Yana ganowa yake blocking d’ina kuma ba zai sake dawowa ba.” Ta k’arisa maganar tana mai fashewa da kuka. “Kutumar bura uba……! Lami kina jin irin maganganun da y’ar iskar yarinyar take min a cikin gidan nan ko!” Fad’in Hassana tana mai nuna Sarah da hannu tare da girgiza jiki. Kau da fuska Sarah tayi tana mai kallon gefe. Lamin kuwa d’aga hannu tayi ta wanke fuskan Sarah da mari sai da tayi taga-taga zata fad’i, sai Allah ya taimaka ta tsaya da k’afafunta tare da dafe fuskan tana kallon Lamin hawaye na zubo mata. “Dan uban ki Nuhu, ita sa’ar ki ce da zaki tsaya kina mata rashin kunya? Ta tara y’ay’an shegun dan ubanki! Ke menene wannan yanzu a cikin ki? Shegiya kema kina tare da abun gorin amma kike yiwa wata. Za kici ubanki dani a cikin gidan nan idan na kafa maki k’ahon zuk’a.” Fad’in Lami tana mai nuna ta da yatsa. “Lami ke baki gano ta bane? So take ki mance da maganar da kika soma na sai ta fad’a maki uban cikin dake jikinta.” Fad’in Marfu’a. “Kwarai sai yanzu na fahimci zancen Marfu’a. To ban mance ba dan ubanki. Uban wa ya yayi maki tsirara ya kwashi albarkatun roman jikin ki? Nace wani shegen ne yanzu in fita in kwankwasi gidan su?” Fad’in Lami tana mai jawo Sarah gabanta. Sarah kuwa wani kukan ta kuma fashewa dashi tare da duk’awa a wajen tana fad’in, “Ni dai Allah ya san cewa babu namijin da ya tab’a kaiwa ga jikina. Ni ban ta yaya ciki ya shiga jikina ba wallahi.” Baki sake Lami da y’an uwan ta suka bita da idanu. Na’ima ce tayi k’arfin halin fad’in, “To a ruwa kika sha dab kutumar uban ki? Kuji min shegiyar yarinya zata mai damu y’an iska wanda basu san inda ke masu ciwo ba.” Lami kuwa tsabar takaici bata san lokacin da ta kai k’asa inda Sarah take duk’e ta shak’o wuyarta tare da wanke fuskanta da mari hagu da dama sannan ta tura ta baya ta fad’i dab’as sai da ta dafi k’asa da duka hannayenta biyu. “Ku shiga d’aki ko waccen ku ta d’auko lafiyayyan bulalanta kuyi ta jibgar shegiya har sai ta magantu tukun zaku kyaleta. Ni anya kuwa ba canje aka yi min a asibiti ba kuwa?” Lami ta fad’i tana shurin Sarah da k’afafunta. Gab’a d’ayan su kuwa dama cike suke da ita, ko wacce ta d’auko bulalanta a hannunta tayo kan Sarah suka shiga lafta mata bulala ta ko’ina a jikinta. Tsabar zuciya irin na Sarah ko gezau, kuma gashi tana jin azaba duk sanda bulalar ta sauka a fatar jikinta. Don har rige-rige suke yi wajen aje bulalar a kan fatarta. Ita burinta d’aya, Allah yasa wajen dukan nata su zubar da cikin dake jikinta ta huta da mugun abun kunyar nan da take d’auke dashi. “Wallahi duk wacce ta k’ara kai duka jikinta sai ta bar gidan nan a cikin daren nan tunda ba gidan uwar ku bane.” Fad’in mahaifin su da fitowarsa kenan daga cikin d’akinsa. Wani yamutsatstsan tsohe wanda wahalar rayuwa duk ta gama cinyesa ya fad’i hakan hannunsa rik’e da sanda yana dogarawa har ya k’ariso inda Sarah ke duk’e a k’asa. D’aga sandar yayi kamar zai makawa Na’ima da ta kuma d’aga bulalar zata zabgawa Sarah, sai tayi saurin ja baya tare da fad’in, “Kul! Wallahi kar ka kuskura ka tab’a ni da k’azamar sandan nan naka. Don kana sauke min sandar a jiki, kaji na rantse maka sai na rama.” Ta fad’i hakane tana mai zaro masa idanu kamar shima zata kai masa bulalar dake hannunta. Mik’ewa Sarah tayi a zafafe tare da fad’in, “Wallahi kika tab’a jikin mahaifina sai na kashe ki a cikin gidan nan, ai nafi shekaru sha takwas a duniya, hakan na nufin na isa d’auri.” Matsowa kusa da Sarah yayi yana d’ingishi tare da fad’in, “Kul, Saratu! Kar in kuma jin kin sake furta irin wannan maganar. Ke d’in yarinyar albarka ce. Ki barta, duniya ta ishi kowa riga da wando, wanda bai shigo bama jiransa take yi. Kiyi hak’uri kin ji. Koma d’aki. Idan kowa be yarda da ke va, bi na yarda dake y’ata. Ke kuma, kije Allah ya isa tsakani dake. Allah zai min sakayya Lami.” Wani irin gud’a Lami ta saki tare da fad’in, “Wallahi Allah ya isar ka babu inda zata je sai dai ta koma kanka. Ai nice ma ya kamata nayi maka Allah ya isa irin wannan uk’uba da na sha a gidan ka kamun Allah ya wanke y’ay’a mata shidda ya bani. Dan ma dai gud’a d’aya a cikin su azzaluma ce mai irin halin ka wacce bata son share min hawaye. Yanzu wannan akurkin kake tutiya dashi har kake kira gida? Lallai! Bayan da ba dun taimakon su y’ay’an da kullum kake zagi da ikirarin zaka kore su sun taimaka sun d’an yi gyare-gyare a gidan ba, har zai kallu balle ma a kira sa gida. Ka dai ji kunya wallahi Nuhu. Kuma y’ay’ana babu inda zasu je. Zama a cikin gidan nan dole, idan kaji ana daram dam-dam to ni da y’ay’ana kenan a cikin gidan nan. Sai dai idan kai ne zaka fice ka bamu waje don billahil lazi naci gida! Y’ay’a bakwai na haifar maka, d’aya namiji, sai tsala-tsalan mata har shidda. Ni ai wallahi har yau tsinewa soyayya nake yi da har ta rufe min idanu ta jani da kyawuna na fuska da na jiki amma na b’uge da auren fak’iri irin ka wanda aka haifesa da bak’in fentin talauci. Nuhu ka fita harkata da ta y’ay’ana tun kan in kai ka k’ara kotu a raba tsakanin mu.” Wani dogon tsaki Nuratu taja tare da fad’in, “Ni wallahi Lami ban san mai kike yi har yanzu da wannan tsohon ba da baki rabu dashi ba. Ke kan ki da zaki d’au wanka ki fara shafa mayuka masu gyare jiki kina hawa leses masu tsada da atampofi, wallahi da wani mayen mai kud’i zai yi wuff dake kema kije kici arziki ki bar arziki inda yake. Don wallahi ba wani tsufa kika yi ba, kawai wahalar wannan tsohon ne ya mai da ki haka.” Ta k’arisa maganar tana hararen mahaifin nata. Shi kuwa wani irin kukan bak’in ciki ya fashe dashi tare da dogara sandar shi ya juya ya koma d’akinsa wanda ba k’aramin abu yake fitowa dashi ba, ko alwala da sallah a ciki yake yi. Yana da bahon da yake alwala a ciki, sannan kuma akwai wani bokitin penti k’arami da yake yin fitsari ko ba haya a ciki wanda Sarah ce ke d’awainiyar fitar dasu tana zubar da abunda yake ciki tare da wankewa sannan ta dawo masa dashi ta ajiye. Da sauri Sarah tabi bayansa ita ma tana kukan tana kuma bashi hak’uri. Lami kuma harara ta bisu dashi tare da fad’in, “Munafukan banza da wofi! Kin ga yarinyar nan, wallahi za’a iya had’a baki da ita a kashe mu. Kuma zan yi maganin ta.” Tana gama fad’in haka taji an banko gidan da k’arfi an shigo da gudu tare da afkawa d’akin ta. Da idanu duk suka bishi a tsorace, dai-dai lokacin da wani matashi shima ya fad’o gidan ya tsaya tsakar gida hannunsa rik’e da k’atuwar adda yana huci. Gaba d’aya su Na’ima suka koma bayan Lami a tsorace. Shi ko matashin ya k’ariso har inda suke fuska babu rahama tare da karta addan a k’asa yace, “Na rantse da ubangijin Yunusa da Musa, idan ba’a fiddo min da wayar k’anwata da d’an ki ya kwata yanzu ba, duk sai na sassare ku a cikin gidan nan. Ni dashi kar ta san kar billahil lazi. Dalla malama ware ki amso min waya a hannun kafurin d’an ki ko kuma yanzu lahira tayi bak’o.” Ya k’arisa maganar yana zarowa Lami idanu. Jikin Lami da y’ay’anta gaba d’aya babu inda bai rawa saboda kaf cikin gari babu wanda bai san *Naliliyo* ba. D’an daba ne sosai wanda kisan mutum a wajensa kamar take kiyashi ne. Da sauri Lami ta juya zata shiga d’akinta domin karb’o wayar, sauran y’ay’an zasu rufa mata baya ya daka masu wata uwar tsawa tare da fad’in, “Duk wata kafurar da ta motsa a cikin ku sai na kashe a nan waje.” Gaba d’aya suka k’ame k’am kamar an dasa bishiya. Mintuna kad’an sai ga Lami ta fito hannunta d’auke da iPhone 7plus a hannunta ta mik’awa *Naliliyo* har da d’an duk’awa. Fizge wayar yayi tare da nuna Lami da hannu sannan yace, “Ki hawa kafurin d’an ki kunne, wallahi ko da wasa na k’ara ganinsa ya gitta ta k’ofar gidan mu, to gawarsa ma sai tayi maki wuyar gani.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fice daga gidan. Na’ima ta saki dogon tsaki tare da fad’in, “Wannan d’an iskan wata rana sai ya jawo mana abunda zai saka a k’ona mu da ran mu a cikin gidan nan. Kullum fa sai kin bashi kud’i amma duk da haka sai ya fita ya jawo mana magana. To gashi nan dai yau ya d’auko mana maganar *Naliliyo* har yana ikirarin zai kashe shi. Wallahi kiyi masa magana Lami ya fita harkan gidan jarababben d’an DABAN nan. Tom!” Kamun Lami tayi magana Lukman (lucky boy) ya fito a fusace yana mai tsira mata hannu tare da fad’in, “Zan ci uwarki a gidan nan idan kika k’ara saka mun baki a cikin al’amura na. Ke uban wanene bai san cewa ke tantiriyar karuwa bace mai y’ay’a har biyu na shegu, dan ma d’ayan ya fad’i ta hannu hagu (Mutuwa) da yanzu y’ay’an ki uku duk shege. Wallahi kika k’ara saka min baki a cikin al’amura na, sai na maki mugun duka a cikin gidan nan. Y’ar iska taxi no garage!” Kallonsa Lami tayi a fusace tare da fad’in, “Kai! Kai Lukman!! Kayi min shuru a wajen nan. Kar in kuma jin bakin ka. Ba yarka bace ita? To ban so ka k’ara fad’in wannan maganar. Ka shiga d’aki ina zuwa akwai wasu kud’i da na ajiye maka.” Juyawa Lucky boy yayi yana wani tafiya a b’ankare tare da fad’in, “Karfa ki dad’e kin san ban son jira.” Lami kuma mai da dubanta tayi izuwa wajen Na’ima tare da fad’in, “Kin san dai ba hankali bane ya ishe sa, ki rik’a fita harkan sa.” Turo baki Na’ima tayi tare da wucewa fuuuu tana fad’in, “Ai ke Lami sam baki son laifinsa, kullum sai dai ki rik’a d’iban kud’i kina bashi yana zuwa yana shaye-shaye dasu.” Lami bata ce komai ba ta wuce d’aki domin bawa Lucky boy dubu biyar d’in da tayi masa alk’awari jiya. Sauran y’an matan ma duk suka shige d’aki. Sai da Sarah taji shuru a tsakar gidan sannan ta fito ta nufi pampo ta d’auro alwala saboda kwala kiran sallar isha’i da taji ana yi a masallacin dake gaban gidan su kad’an. Dawowa d’akin tayi ta taras da duka yayyinta a ciki ko wacce sai cab’a kwalliya take yi saboda lokacin fitar su yayi. Dama haka suke yi, wasu idan sun fitan ma, sai suyi kwana biyu, uku har sati basu dawo ba. Wata rana kuma a ranar suke dawo can cikin dare. Darduma Sarah ta shimfid’a ta tada sallar isha’i, don dama ita kad’ai ce a cikin su take yin sallar, to Lamin ma bayi take yi ba balle ta saka su a hanya. Sai bayan ta idar ta sallah ne ta saka doguwar riga irin mai kama jikin nan, sai ta d’aura k’atuwar suwaita a kai sabida sanyin da take ji. Tana cikin zuge zip d’in suwaitar aka kwad’a sallama a cikin gidan nasu tare da fad’in, “Wai ana sallama da Sarah inji Farouq.” Ras gaban Sarah ya yanke ya fad’i, don gani take yi kamar tana fita suka hada idanu zai gane akwai ciki a jikinta. Da sauri ta lek’o tsakar gidan tare da fad’in, “Kace tana zuwa yanzu.” Tana gama fad’in haka ta dawo d’akin domin d’aukar hijjab d’in da ta cire yanzu bayan ta idar da sallah. “Kanin ubanta yazo, jikinta sai rawa yake yi domin taje ta gaida shi.” Fad’in Nuratu tana hararar ta. K’ala Sarah bata ce ba, sai ma hijjab d’inta da ta fara k’ok’arin sakawa. “Shegiya ko irin jan ajin nan baki iya ba. Daga ya turo jikin ki na rawa zaki fita.” Fad’in Marfu’a. Sarah kuwa ko kallo basu ishe ta ba, ficewa ma tayi daga d’akin bayan ta gama sanya hijjab d’inta. A k’ofar gidan ta ganshi sanye da wando jeans da blue T-shirt, kansa sanye da facing cap ya jingina da wani k’arfe dake jikin gidan mak’otan su yana kallon d’aid’aikun mutanan da suke fitowa daga masallacin kasancewar ba’a jima sosai da idar da sallah ba. Juyowa yayi tare da zuba mata idanu har ta k’ariso inda yake tare da fad’in, “Sannu da zuwa. Ina wuni?” Kallonta yake yi for almost 2mins kamun ya bud’e baki yace, “Ina kika je d’azu na ganki kin ruwa ya maki duka?” Saurin d’agowa tayi ta zuba masa idanu, sai kuma ta sunkuyar da kanta gabanta na fad’uwa don gani tayi makar zai ga an rubuta _Ina d’auke da ciki_ a kan goshin ta. “Tambayar ki nake yi kin yi min shuru.” Farouq ya sake magana a karo ba biyu. Sai a lokacin Sarah ta bud’e baki tare da fad’in, “Asibiti naje.” Kallonta yayi tare da maimaita “Asibiti.” K’ara d’agowa tayi ta kallesa a karo na biyu, sai kuma tayi saurin kau da kai tana kallon k’asa tare da wasa da zoben dake hannunta. “Are you sick Sarah?” Girgiza kai tayi tare da fad’in, “Dubiya naje yi. Lokacin da na fito kuma ban samu abun hawa ba saboda hadari. Shine ruwan ya duke ni, amma kuma ba fake. Da ruwan yayi sauk’i ne shine na fito shiyasa ka ganni a jik’e.” Ajiyar zuciya Farouq ya sauke tare da fad’in, “Amma baki san hakan da kika yi zai iya jawo maki rashin lafiya ba. Mai yasa ma baki kira ni nazo na d’auko ki na dawo dake gida ba? And ina ta kiran wayar ki bakya d’aga wayar.” Ya fad’i hakan yana mai folding hannunsa. Ko kamun Sarah tace wani abu an banko k’ofar gidan su, cikin sauri duka su biyun suka juya suka kalli k’ofar gidan. D’an duk’awa Farouq yayi tare da fad’in, “Mama ina wuni?” Harara Lami ta watsa masa tare da fad’in, “Uwar ka ba, ka baro ta can gida. Ni ba mamarka bace. Kaga wacce ta haifa nan.” Ta k’arisa maganar tana mai nuna Sarah da hannu sannan ta cigaba da fad’in, “Ba gaisuwa ka na taho nan in amsa ba, zuwa nayi ka fad’a min shin kai ne uban cikin dake jikin Saratu ko kuwa. Don idan kai ne, wallahi na rantse list d’in ka daban ne. Kuma kar kayi tunanin zan yi maka ragi.” Hannu Sarah ta d’aura a kai tare da fad’in………………

*_Chart me up 08128755583_*

Leave a Reply

Back to top button