Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 62

Sponsored Links

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/29, 10:44 PM] +234 703 080 4044: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6️⃣2️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Zahra kiyi hakkuri don Allah nasan duk nina ja maki wanan
abin da yan uwanki ke maki don da ace bani kike aure a yanzu ba wani can
hamshaki nasan da dole sunayi dake.

   Amma yanzu aurena
yasa duk suna ganin ke ba kowa bace a cikinsu yanzu don ban taba zaton har hjy
da girmanta zata iya fadin wanan maganan haka a gabana ba sai gashi a yau ta
fada naji.

   Uhumm ka dauka
donkane take wanan maganan wai itafa hjy haka take ga duk wani dan dakin mu duk
sanda muka hadu ba a kwashewa lafiya da ita saita yaba muna magana.

   Ni na saba da irin
wanan halin nata don ba yau ta fara nuna min hakan tun ina gaban ummah haka
muke kwasa da ita dama.

    Amma duk da haka
na yanzu yafi dukda bansan nada din ba yadda kuken sai nake ganin kamar don
kina aurena a yanzu ina fakiri hakan murmushi kawai nayi ba tare da nayi magana
ba shima bai sake fadin komai ba lokacin.

  Munkai bakin wani
shago ya tsayar da mashin din yana fadin bari na dan shiga in fito ya sauka
saman mashin din zuwa cikin shagon.

   Yadan jima ya fito
dauke da ledoji guda biyu ya miko min na karba ya hau mashin din yana fadin
kayan teane a ciki naga wanan sun kusa karewa kuma zan dade wanan karon ban
dawo ba gashi teane abincin ki ke.

   Na karba har
lokacin banyi magana ba don raina ya gama baci da abinda hjy tayi min a lokacin
don koba komai ya kamata ta raga min tunda muna tare ai.

    Washegari sammako
yayi yabar garin zuwa zaria don haka danayi barcina na tashi na fara gyaran
dakina daduk part dina ina tsaka ga aikinne na fara jin kukan dabbobin har yana
shiga raina.

  Gashi nayi alkawarin
ba zan sake zagawa baya inda suke daure ba don na tsorace da lamarinsu sosai
gaskiya don hakane na kyale ban zaga inga ko kukan me sukeyi ba.

  Kukan yayi yawa don
haka nayi tunanen yunwa sukeji gashi da alama ba wanda ya damu da kukan nasu
lokacin haka kuma nayi tunanen ina Dije take don tana da kokari dasu gaskiya.

   Kamar wace akaba
umurnin tashi haka naga na tashi na nufi wajensu kai tsaye tun daga nisa na
hangosu tsatsaye sai kuka sukeyi.

  Suna ganina duk suka
maida hankalinsu gareni lokaci guda basu da komai na abinci wurin don hakane na
dauki tsitsiyan gyaran wurin a karo na farko na fara share wurin a tsorace.

   Na koma part dina
na debo masu ruwa don ni baya tafiya ba wadatani da ruwa ba sai ya cika min
komai nawa na zuba ruwa yadda zai wadataceni zuwa wani lokaci.

  Na debo na dawo ina
zuba masu naji muryan Dije a bayana tana fadin yauwa yar albarka yanzun nake
fada da yaran banzan nan su taso su duba minsu sunki zuwa shine na lalabo nazo
in duba .

  Tun safe ina daki
kwance bana jin dadin jikin nan nawa sannu nayi mata tare da tambayanta meke
damunta lokacin tace jikintane ke ciwo alaman zazzabi a jkkin nata dai.

   Abincinsu dake
cikin buhu na jawo na zuba masu banyi aune ba saiji nayi a bayana kamar za a
kasheni ashe uwar garkene daga inda take ta sako min kahonta ajiki tana dona
kanta jikina.

   Bansan lokacin dana
sake sauran abincin ba ya zube kasa na kwasa da gudu zuwa wurin Dije ina haki
don na tsorata da hakan.

   Lah akuyan kike
tsoro kuma diyar nan me akuya zatai maki kuma ta fada tana karasawa zuwa wurin
dana fito ta duka tana kwashe abinda ya zube din .

  Aike amarya godiya
take maki da hakan idan dabba taji dadi hakan takewa mutum ta shige a jikinshi
shine godiyansu ai sai kuma ta koma fadin yaudai angon namu ya tafi.

   Allah ya tsare muna
shi ya kare yanzu kan ai yayi nisa ga tafiya da yardan Allah ta fada duk
hankalina nakan wanan bakar akuyan banyi aune ba naji ta saki wani irin kuka
lokaci guda saida na kara kaduwa a hankali na sulale nabar wurin a tsorace da
ita.

    Shigowan ta falon
bai hanashi wayan da yakeyi din ba wanan karon bai kuma fasa fasin abinda yake
magana a kai ba don ta shigo falon lokacin saici gaba da fadin da yayi.

   Dane na cikina
shekara ashirin da bakwai zuwa takwas ke nan yanzu rabona dashi a nan cikin
zamfara suke indai ba barin garin sukayi bayana kai bama inda zasu don kowa
nasu yana garin.

    Gabatane yayi wani
irin mugun faduwa lokaci guda zancen da bata taba kawowa kusa ba ke nan a ranta
sai gashi taji yana waya akan hakan don haka take duk wani annurin jikinta ya
gushe lokaci guda.

    Karfi hali tayi ta
zauna har zuwa lokacin da ya gama sauraren abinda mai wayan ke fada masa a
lokacin don ba jinsu takeyi ba daga inda take zaune din ba.

   Nagode Alh ina
sauraren ka insha Allahu zan kara jira inji inda zancen ya kwana don Allah
aimin kokarin hakan ina cikin wani hali kan wanan zancen a yanzu.

   Nan kan ta kasa
hakuri ta danne zuciyarta don saida ta kalloshi a cikin wani irin razana ya
kashe wayan yana dorawa saman dan karamin table din gabanshi tare da dago kai
ya kalleta .

    Alh wani zancen
naji kanayi yanzu  ta fada daidai lokacin
da yake kawar da kai daga kallonta lokacin hakan yasa yayi wani irin juyowa a
ciki  mamaki ya jefa mata wani irin kallo
lokaci guda kafin yace.

  Meya shafeki da
wayana yanzu ko dama kin zauna ki sauri abinda nake fadane wai inma son ki sani
kikeyi to ina zance akan dana Ahmed mai sunan baba dana haifa da matana ta farko
a zamfarane.

    Zubur ta mike tare
da nunashi ido rufe tana fadin wana
zancen ma karyane wallahi dan da ka samo a cikin duniya kabaro shi can
yanzu zakace zaka daukoshi a matsayin dan cikin ka kuma ?

   Ohh dama haka kuka
dauka shine zatonku bata hanyar sunna na haifeshi ba shine dalilin watsar dashi
danayi a rayuwana kome inma zatonku ke nan ku jaye don dane na halas kamar ko
wani da a cikin gidan nan shima.

   Kaika san wanan
zancen don duniya bata sheda hakan ba gareku don haka ina da ja akan wanan zance
nida yayana kan hakan ta watsa mai wani irin kallo ta nufi hanyar fita daga
falon a fusace.

   Tsuki yaja ya bita
da kallo shima ya mike a fusace ya fito daga falon ko kallon abincin data aje
mai baiyi ba a lokacin driver shi na ganinsa ya taso da sauri ya bude mota suka
shiga sauran motan ma suka biyosu a baya lokaci guda.

   Bai tsaya ko ina ba
sai airport inda jirginsu zai tashi zuwa adamawa daga can zaibi motan dake
jiranshi a can zuwa mambila garinsu na haihuwa.

  Hjy kuwa tana fita
dakinta ta nufa ta figi waya tanayi da
yarta a cikin kuka take labarta mata abinda ya faru tsakanin su hankali
tashe.

    Saida yar nata ta
gama saurarenta ta katseta da fadin ke kam yabi baki da wayau wallahi kin fa
san da zancen nan a baya.

   Don me yanzu zaki
nuna hakan don da daya ya shigo cikin ku yanzu me zai fiku dashi ko me zai
kaiku a rayuwa yaron dama ya rayu a cikin talauci da tsiya yabi in kin kwantar
da hankalin ki aisai yadda kikayi dashi dagashi har uban nasa.

   Dama na fada maku
wanan ranan yana tafe ki shirya mashi kikace a,a keda hjy aikun gama da wanan
matsalan ba zaisake wawayen yaron nasaba a rayuwanshi yanzu gashi ba aje ko ina
ba ya fara wanan zancen.

   Don Allah Nkki ki
bar wanan zancen yazu bashi bane a gabana mafita nake duba a yanzu ta fadawa
yar uwanta cikin zafin rai taci gaba da fadin na kulla Nkki baki san zafin
hakan ba ka hada dan uba da diyanka yafi komai muni a rayuwa.

   Nkki din tace ina
zan sani nida da guda na taba haihuwa  a
duniya ai ba zansa hakan ba yanzu tunda da yan uba na samu ubanshi.

   Yanzun dai ki nuna
masa kinyi kuskure a fili inyaso daga baya in mun gama tunane mayi wanan
maganan mu nemi mafita jin hakan ya dan kwantar mata da hankalinta ta mike zuwa
part din mijin nata.

    Bayan fitan ashi
daga gidan da kamar da minti ashirin ta shiga ta samu baya ciki asalima an rufe
kofan daga baya duban inda abinci yake aje tayi.

  Yadda aka jera mai
ko cibi bai taba ba daga ciki hakana ya barshi ya tafi hakan yasata dan runtse
idonta kadan tayi tana jin wani irin daci a zuciyanta kamar kafafuwanta ba zasu
dauki jikinta ba lokacin.

   Ba komai takewa
takaici ba sai irin kudin data bayar aka kashe don ketarawa cameron wurin karbo
maganin datayi amfani dashi a girkin yanzu duk ya tashi a banza ke nan gareta
don ko sau daya tunda ta fara amfani da maganin tana kula ko ruwan gidan ya
daina sha yanzu balle abincinsu na gidan.

   Ya isa lafiya sai
karfe hudu da rabi ya samu kiran gida yaji lafiyansu inda layin zahra din ya
kira a lokacin don wayan inna yana da wuya ta dauka idan an kira layin.

    Daidai lokacin
nayi wanka na saka dogon riga a jikina sai hula dana kafa a kaina na hada
cornflake ina sha ina zaune ina tatara takarduna da nake bukata wanan zangon.

    Naji wayata yana
ringing daga gefena nakai hannuna dauka bakon lamban kasan wajene naji tsoro da
farko kamar ba zan dauka ba na danna ina fadin Assalamu Alaikum.

   Naji an amsa min da
amsa na musulunci a lokacin hankali ya dan kwanta naji maishi na fadin ko yana
magana da zahra mayanace   zamfara state
?

   Na amsa da eh nice
naso sheda mai maganan a lokacin amma na kasa gane inda na sanshi namijine kuma
nasan wanan muryan a baya gaskiya.

  Kina magana da
brother din ki BISI Abdulbasti dana nan US ko kin tuna da mai sunan ya fada
cikin zolaya sai yai shiru.

   Aiko bai rufe baki
ba na dan sake ihu tare da fadin lah kaine kana ina haka duk dadewan nan bamu
kara jin kaba kuma ?

   Yace ba kun koreni
Naija ba kedasu Mum nace kizo mu gudu muyi aure kinki bina lokacin da sauri na
tareshi da fadin haba dai brother in ace ciki daya muka fito dakai nayi haka
yaya zakaji ?

   Yace to meye tunda
kinbi masoyinkine bazanji komai ba saidai in maku fatan alheri a duk inda kuke
nace yare hoo a zuciyana wani yaren duk da musuluncinsu sai sin hada da al,ada
mai kama da kafirci.

    Amma kasan addinin
mu da yaren mu bai yarda da hakan ba garemu don me ni zan ba iyayyena da yan
uwana kunya a garin mu saboda namiji ?

   Yace hakan dana
sani yasa nabarki ai badon naso ba don lokacin inada hanyoyin da zan iya saceki
cikinsu din amma sai kwanan nan mummy ke fada min wai kunyi aure keda sisters
dinki.

  Ke kin auri wani
tallaka bawa Allah kika zaba akaina sam baji dadin yadda take fada min yanayin
da kike ciki ba tana jin dadin hakan.

   Wanan abin ya bata
min rai sosai wallahi don nasan yadda kike da step mother din ki Alajah komai
zata iya akanki don hakane yanzu na kiraki naji wani taimako zan iyayiw rayuwan
ki a yanzu.

   Ke zan taimaka ko
mijinki zan taimakawa ya samu abin rikeki yanzu ke nake saurare naji amsan da
zaki bani da fatan kuma shi mijin naki yayi karatun gaba da secondary ?

  Shiru nayi ina
sauraren shi don na rasa amsan da zan bashi saida yace kina tare dani kuwa nace
ina jinka duk a cikin harshen turanci muke magana dashi lokacin.

   Yace wa kika zaba a
cikkn ku nace idan zaka taimaka min ka taimaki mijina don ya fini bukata yanzu
yace good nima tunanen da nayi ke nan da farko amma kuma sai nazo nayi tunanen
kanku hausawa don mazan ku basu da rikon amana ko kadan .

  Yana iya cewa zai
rabu dake wata rana idan ya samu wata kinga ya kwaremu a nan ke nan don haka
naga gara ke ki samu din don daman mutum daya nake dashi yanzu kuma na tambaya
ance har yanzu karatu kikeyi ke.

   No ka bashi banda
matsala ga hakan idan ya samu kamar nice na samu ai don zai tallafa min yadda
ya kama daidai gwargwado don ko yanzu yana kokarin shi dani ai.

  Ok alama dai ya nuna
kina matukar son mijin nan naki ba laifi zan turo maki da yadda zaku turo da
takardunku saidai bana son wani ya taba sanin cewa nine na taimaka maku da
wanan aikin understand nace nagode sai naji ya kashe wayanshi a lokacin bai
kara fadin wani magana ba kuma.

   Kallon wayan nayi
na runtse idanuna gabana sai faduwa yakeyi sosai ina kuma tunanen wani irin
aiki bisi din ya samu yanzu da har yake ikirarin taimakawa wani dashi.

   Sai kuma na koma
fadin ni yanzu ta yaya zan fitowa Master da wanan zancen me zan fada mashi
alakata da Bisi idan zancen hakan ya taso a tsakanjn gashi kuma damace muka
samu a hakan kada ya wuce mu duk da bansan ko wani irin aiki bane dai.

   Amma zan gwada mai
magana don haka na fara dan tsara yadda zan shirya mai zancen ko kadan banzan
taba furta mashi zancen cewa Bisi din yaso aurena ba a cikin maganan.

   Zan dai nuna mashi
cewa dan abokin Abbane da muke mutunci dasu yaji labarin baya aiki yake son ya
taimaka muna haka dai na zauna na tsara yadda zan fada mai koda yayi min
tambaya mai zurfi kafin na dawo ga tunanen mommy Bisi data fada mai tana jin
dadi.

  Watau hakan ya nuna
mama tana jin dadin halin danike ciki ke nan to ai ba wani zunubi na aikata ba
da har Allah ya jarabeni da auren master din na tambayi kaina.

   Ina cikin wanan
tunanen ne kiran master din ya shigo a waya na dauka muka gaisa nayi mai ya
hanya yace Alhamdullahi ya isa lafiya har sun fito daga lacturen ranan ai.

   Ya tambayi lafiyan
iyayyen shi nace kowa lafiya sai Dijece bayan tafiyan ka take fama da zazzabi
yanzun ma nake shirin zuwa in gaida ita
in tambaye abinda zataci in girka muna.

   Da sauri naji ya
tambaya badai sosai bane jikin ko nace da sauki gaskiya don har ta fito dazun
da rana yanzun daine ban kara lekata ba yanzun nake shirin zuwa to idan kinje
son Allah ki min flashing zanyi magana da ita.

  Nace to naji ya
kashe wayan lokaci guda ba tare da munkai ga yin maganan ba saidai kuma zancen
ya tsaya min a raina sosai ina tunane har yanzu kan in fada   ko kuma in kyalene.

    Ya samu abokan
nasa su uku dama wasu abokan arziki nasa duk sunzo tariyanshi a lokacin ba bata
lokaci suka dauki hanyar mambila suna isa garin hjy yabi wace yarta ta bata
shawara kan .

  A yanzu kuka ko
bacin rai ba nata bane ta sake jiki ta nuna mashi cewa tayi kuskure a baya ta
nuna ba komai don haka ta daga waya ta kira layinshi.

  Baiki dauka ba ya
dauka take fadin kana ina ne haka ko abinci bakaci ba kafita ba bai tsaya jin
komai ba shima ya bata amsa kalar makircinta da fadin ina mambila yanzu.

   Baki sake take fadi
a rude mambila Alh mambila ka tafi banda labari nan hankalinta ya kara tashi
don gani take idan yaje mambila ba tare da itaba dayan kishiyar nata zata samu
dama a gareta ke nan.

  Asalima itace ke
shirya masu tafiya duk lokcin da bukatan zuwa ya taso masu garin nasu sai gashi
yau shida kanshi ya tafi ba tare daya sanar mata bama.

   Nan hankalinta ya
tashi maimakon lalashin data kirashi tayi mai kamar yadda yarta ta bata shawara
sai gata tana kokarin fada mai bakar magana a lokacin.

   Rabu da irin matan
nan da suke mulki da gadara da isa idan abu
ya kwace masu suna shitin zama powerles a  wurin miji lokaci daya sukeyi kamar sun zare
kan miji.

   Hakane yazu yake
shirin faruwa da ita don gaba daya sai take ganin kamar duniya ta kita a
lokacin ita kadai ta manta irin mulkin da isan da take shimfidawa a baya
gareshi.

  Yanzu Allah ya fara
kwato shi ya fara samun walwala daga daurin boyen datayi mai wanda dama baya
tabba ga bawa idan ba rai ya kare ba gareshi.

   Daga bangareshi
kuwa amsa ya bata da fadin banda niyar saikin sanda zanzo yau don na fara gano
me kike nufi dani yanzu ya kashe wayan ya barta a cikin mamakinshi lokacin.

   Ranan kan zarewa
tayi gaba daya sai fama  kiraye kirayen
waya takeyi hankali tashe duk wanda ta kira sai hannkuri suke bata kan tabishi
sannu in ma asiri akai mai ba inda zaikai.

   Wasu kuma don
daukan alhaki sai su danganta abinda fadin mariyace kishiyarta tayi wani aiki a
kansu yanzu da yaci don itama aiba zata zauna ta zuba maki ido ba dama.

  Jin irin hakan ya
kara tayar mata da hankali sosai lokaci guda duk ta fita hankalinta har zazzabi
mai karfi ya rufeta nan yarta babban ta fara fada da ita tana fadin .

  Akan daddy mummy
kike son halaka kanki ki manta dashi mana yadda shima ya nuna kodake koba ke a
yanzu zaiyi rayuwa .

   Jin hakan yasa ta
dago kai tana fadin kina da hankali kuwa daddy zakice mu kyale duk wani abinda
muke takama dashi da karfin wa muke duk abinda mukeyi a garin nan yanzu.

  Don suwa nake wanan
haukan haka ba duk a kanku bane nake wanan wahalan kina ganin idan ya dauko
wanan shege dan nashi ba zai mayar da hankalinshi bane a kansa ya kyale mu.

   Ko kuma yayi
kokarin yaga ya mayar dashi wani abu yanzu kamar ku duk komai ma zai iya
faruwane akai wanan ne damuwana don ko banza kinsa yana yawan complain cewa
yasir baya jin maganan shi.

  Shiru yar nata tayi
tana saurarenta tare da nazarin abinda uwar nata ke fadi kafin ta bude baki
tace duk da haka mummy ki nuna masa rashin damuwan ki da hakan zaifi sauki.

Leave a Reply

Back to top button