Hausa NovelsKurkukun Kaddara Hausa Novels

Kurkukun Kaddara 4

Sponsored Links

https://chat.whatsapp.com/Fg5z8TEO5Mk0NwptyjrKjq

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Boss Bature ✍️*

dedicated to Aunty kubra❤

قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔

*E4*

Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su,

Ba’a ɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station ɗin, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking ɗin motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station ɗin, Lokacin da ta shiga Ciki, ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi.

Cikin shessheƙar Kuka Ta kalli ƴan sandan tana faɗin “Why why!why pls? Laifin me suka aika ta da za ku yanke masu irin wannan ɗanyen hukuncin,”
Copral ne Ya bata amsa da cewa”Ana zargin su da sace Ƴa’ƴan mutane suna amfani da su”
Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallon su, har bata san lokacin da tace
“Amma baka da hankali Officer, Ka iya bakin ka, Shin kuna da hujja akan a bunda kuke zargin su ne? waye ke baisan Taj da uzair ba…..”bata kai ƙarshen maganarta ba muryar dpo ta katse ta”Muke da ƙwaƙƙwara Hujja akansu,”
Idanuwanta jawur ta ɗago tana kallon Dpo ɗin, Cikin sanyin murya ta furta”where’s the evidence”?

Kafin dpo ya bata amsa sai ga Angel tana fitowa daga Office ɗin shi

A ruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani,

Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel, itace ƙwaƙƙwarar Hujjar da muke da ita, Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka a kan Wannan bawan Allahn daya sace ta, Ya raba ta da iyayen ta don baƙin zalunci,” yakai ƙarshen maganar Yana nuna Tajuddeen,

Hankali amatuƙar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami”You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce,” muryarta a disashe takai ƙarshen maganar,

“Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faɗa mana cewa shi ɗin ba mahaifinta bane satarta Yayi,” acewar dpo,

Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh, Girgiza kai tashi ga yi tana kallon angel,
“Wlh officer Ƴarshi ce sharri take yi mashi, Yarinyar bata da cikakken hankali ne,”
Da buɗe bakin angel sai cewa”Ni ƙarya take yi mun officer itama hada ita suke yi ae”

Curo handcuff Inspector yayi tare da cewa”You are under arrest” ya ambaci hakan yana ƙoƙarin sanya mata ankwa
Ganin dagaske Kamata za su yi ne yasa tayi saurin cewa”Ku dakata kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer, akwai hotunan yarinyar da videos ɗinta a wayar Mahaifinta zaku Iya bincika wayar shi ku gani.
Girgiza kai Dpo yayi”Wannan ba hujja bace duk shirin ku ne”
Jinjina kai tayi to shikenan me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test, this is the Only solution”
Jinjina kai dpo “Good idea Copral”Dpo ne ya kira sunan shi
“Yes sir” ya amsa mashi.
“Ku tafi da Mutumin da yarinyar a yi masu gwajin DNA, ku tabbatar anyi komai agaban ku,”
“Consider it done sir” Ya ambaci hakan tare da sara ma shi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell ɗin, Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa ƙwarin Jikinshi, sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da ƙafafun shi, wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayin shi ba, ko son kallon shi ma ba ta yi,

A cikin mota suka sanya su, Aneelerh kuma Ta shiga motarta tare da angel,

Bayan zuwan su asibiti, Akan idon Police men ɗin akayi komai, Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita,

Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba, Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu Sun sha mamaki, Lamarin Yayi matuƙar girgizasu, Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu, dpo yafi kowa girgiza, har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zargin su da suka yi Anan aka kwantar da Tajuddeen, Sam ya fita hayyacin shi,hada drip suka sanya mashi,

Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da su ka yi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin tsakanin shi da yarinyar ba, A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗa ta da manyan malamai su cire shaiɗanun dake ajikinta, ko kuma a kaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne,

Bin shi da kallo kawai aneelerh tayi don ita tasan Wacece Angel, Lafiyarta ƙalou itace aljanar kanta da kanta, yarinyar da ana yi mata ruƙiya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi Lafiyarta qalou ”

Kwananshi uku a gadon asibitin saboda jikin shi da yaƙi sauƙi, cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya da shi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki ba, da yake suna waya dashi kusan kullum ne sai sun kira su kosu su kirasu, A ƙarshe suka koma gida da yin jinya, Har hutu Aka ba Taj wurin aikinsu jin Abunda ya faru da shi, Uzair ne ya sanar dasu amma bai fada masu ainihin abunda Ya faru ba, kawai ya sanar dasu cewa Sun yi hatsarin motane, ya yi hakan ne saboda sanin halin su na ƴan jarida, yanzu ka ji labari a social media,

Bawan Allah Taj kullum yana kwance saman gado, Wanka da sallah ne kaɗai suke tada shi Wani sa’in yana ɗangya shi haka zai samu ya lalla6a Ya shige toilet, Ko sannu angel bata ta6a furta mashi ba sai in tana jin yunwa ne zata addabe shi wai ya tashi yayi masu girki, in ba haka ba zata je ta daura da kanta,

In ta gaya mashi hakan Jiki na rawa Yake kiran Uzair a waya Ya sanar dashi, dama Cikin ƴan kwanakin nan mai aikin su Uzair hada Su taj take girka ma abinci duk in za ta yi, bisa umarnin Uzair ɗin,

Ana haka Yau kwana Biyar kenan bai zuwa ko’ina Yana gida, Wuraren ƙarfe biyar na marece, ya fitowa daga wanka jikin shi sanye da short baƙi, saman Gado ya haye bacci mai daɗi ya ɗauke shi Yayi nisa acikin Baccin shi, Yadinga Jin Hayaniya acikin gidan jiki a mace Ya miƙe daga saman gadon ya nufi ƙopar ɗakin, Leƙawa yayi don yaga su wanene

Waro ido waje ya yi ganin mutane maƙil Cike da falon, Kasa kunne ya yi yana sauraran me suke cewa
“Allah ya jiƙan shi, Taj mutumin kirki halinshi na gari Ya bishi,”
Can kuma yaji wani yace”A ina ne za’ayi jana’izar ta shi”?
Wani ya ba shi amsa da cewa”Mu jira Mutanan gidan su fito sai muji,”
Shiru yayi la6e bakin ƙopar Ya kasa fitowa, Jikin shi duk yayi sanyi, tunani ya shiga yi wai wanene Ya mutu? dama akwai wani taj ne bayan shi”? sam bai da mu da rashin ganin angel ba yasan bata wuce Gidan su Uzair.

Komawa Cikin ɗakin yayi Jikin shi duk ya mutu, Wayarshi Ya ɗauka da ke a jiye saman gadon Yana kunnata Ya shiga call logs, Nan yaga missed Calls sunyi ɗari uku na mutune, abun ya ɗaure mashi kai,

Number uzair yayi dialing Ya danna mashi kira, Tana fara ringing uzair Ya ɗaga,
“Assalamu alaikum” batare daya amsa sallamar ba Yayi saurin cewa”Uzair kana ina ne”?
On the other hand Uzair yace”Gida mana”
Cike da damuwa yace”Uzair na shiga Uku, Yanzu kawai na farka daga bacci Naga dandazon mutane a falon gidana, Na kuma taras da missed calls a wayata Ya yi ɗari uku na mutane wai meke faruwa ne”?

Muryar uzair da ɗan ruɗi yace”Kodai angel tayi wani abu ne? bata jima da shigowa Gidan mu ba, Take sanar dani cewa Ta ɗauki wayarka kana bacci, Ta sanya yatsan ka ta buɗe ta “tunkafin Uzair yakai ƙarshen maganar ta shi, Taj Yayi rejecting call ɗin, Ya shiga laluban wayar shi, Sai ga Notification na facebook on the top of the screen yayi appearing, Likes ya dinga gani na mutane da kuma Comment da ake tayi, A hanzarce Ya shiga facebook dinshi, a nan Yaga hoton shi dana angel ta ɗauka yana bacci tayi share ɗinshi a facebook, a ƙasa ta rubuta RIJF, Su kuma Mutane da suka Ga posting din dayawan su sunyi tunanin ko matarshi ce Tayi amfani da wayar shi donta sanar masu mutuwar shi, Shine suka kwaso ƙafafuwansu zuwa Gidan don a yi jana’ixa da su.

jiri ne Ya soma ƙoƙarin kwasar shi, lalla6awa ya yi tare da samu wuri gefen gadon ya zauna yana ambaton Allahumma Ajirni fil musibati wa aklifli khairan Minha, Na jima ina tunanin Ranar mutuwa ta, da kuma abunda zai yi silar bari na duniya ashe ƴar Cikina ce, Laifin me nayi mata ne da ta tsane ni? sai ka ce ba mahaifin ta ba,ƴar ƙarama da ita sai Iya mugunta wayyo Allah na,

sai daga bisani Ya tuna inda tasan kalmar RIJF, a tv ne wani ya rasu ana sanar da ta’aziyar shi, daga ƙasan hoton shi aka Sanya RIJF, Rest In jannatul firdaus, shine take tambayar shi wai me yake nufi, da yake ta iya tambaya kamar yar jarida, Bai yi tunanin komai ba ya sanar da ita ma’anar hakan, Shine tayi mashi aika aika.

Kiran Uzair Ne ya shigo wayar shi, A sukwane ya ɗaga Kiran a nan yake sanar da shi abunda ta aikata mashi, Uzair yasha ruwan mamaki

A ƙarshe dai,Uzair da aneerlerh ne suka shigo gidan suna bama mutune hakuri akan cewa Taj bai mutu ba, Yana a raye mistake aka samu wurin Yin posting din, ƙin tafiya sukayi Har sai da suka ga Taj da ƙafafun shi tukunna suka bar gidan suna yi mashi Allah ya kyauta, A falo suka zauna gaba ɗayan su, Uzair da Aneelerh suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Taj kuma yana zaune a saman 2 seater,fuskarshi duk a hautsine,
“Yanzu menene mafita”? taj ne ya yi maganar yana kallonsu,
“Lamarin Angel Yafi ƙarfin mutun sai dai Allah, ae ni tun ranar da aka kira malami yayi mata ruƙiya ta sace takalman shi, tun daga nan Jikina Yayi sanyi,” acewar Uxair,
“Benazir ta tafi tabarmun bala’e” tamkar taj zai fashe da kuka Yayi maganar,.
“Me zai hana ka jaraba Bugunta”? a ɗan firgice ya kalli Aneelerh da tayi maganar,
Cigaba da magana tayi”Idan har ba za ka iya bugunta ba shawarar da zan bada shine, Kasan mafi a kasarin ƙananun yara akwai abunda suke tsoro, Ni ina ganin a jaraba samo Mage ko kare ko kuma ƙadangare, Idan aka samu wanda take tsoro acikinsu, Sai adinga Yi mata Baraza na da shi, Koya kuka Gani”? tayi tambayar tana kallon Taj, wanda ya yi zugudum yana kallonta, yarinyar da take kallon Zombie tsakar dare, Taya zata Ji tsoron waɗannan halittun, Acikin zuciyarshi ne yayi maganar,
Jinjina kai Uxair yayi”Good idea idan na fita Yanzu xansa Almajirai su ɗauko mun ƙadangare a fara jarabata dashi, inyaso gobe sai a kawo karen Nasan dole asamu wanda take matuƙar tsoro acikinsu,”
“Allah yasa dana fi kowa Farin Ciki” acewar Taj,

Sun jima suna tattaunawa kafin Su ka yi ma shi Sallama, Atare suka bar gidan,

Duk dabbobin da aka kawo gidan don angel ta tsorata amma abun ya ba su mamaki bata tsoron su, illa ma ita dabbar da aka kawo taji tsoronta, yarinyar ta zarce tunanin mai tunanin ga karfi Allah Ya yi mata, Ranar da taj yasa aka kawo mage agidan Sai da ya yi dana sani,

A lokacin Yana kwance yana bacci Ya barta a falo ita da magen da ta sanya ma suna Chu chu, suka soma kokawa tana kiciniyar kamata, magen ta watsa aguje tana kuka, tabi bayanta da gudu suka shiga zagaye palourn, Sune har cikin kitchen, Magen ta haye saman Dish racks, inda Jerin Plates na tangaran suke, Angel takai hannu da niyar ta cafkota aikuwa gaba ɗaya Ta 6aro da Kwanukan tangaran din, Suka tarwatse kasa duk suka faffashe, Tsalle magen tayi ta ruƙo jikin Cupboard wasu hadaddun Glass Cups ne dana tangaran, Ruƙo ƙafar magen Angel ta yi, Gaba ɗaya Cups din suka Rikito ƙasa duk suka tarwatse, Kubce mata magen tayi da gudu ta sauko ta nufi Store da kopar shigar shi ke anan cikin kitchen ɗin, Aguje angel tabi bayanta, Suka shiga yin yar tseral, Wasu jerin Crates din kwai Ne Magen Ta hau saman su, A ƙalla sunyi crates goma sha biyu, Gaba ɗaya suka kife kasa eggs ɗin suka faffashe, hayewa sama magen ta yi inda aka jera Sunƙi sunƙin bready, Ganin tsawonta bai kaiwa yasa ta janyo jarkar Manja, Ta haye samanta Ta cakumo wuyan magen, jarkar da ta hau saman kanta ce ta Karkace da ita da magen Da jarkar man, Da Ledojin breadin sunkutukum Suka Kife ƙasa, Nan take murfin jarkar ya buɗe Manjan Ya shiga gangarowa ƙasa, bari in takaice maku zance sai da Angel ta canzama Kitchen din halittarshi, tamkar Bola, uk Ta hargitsa komai ba,

Da ta ga Ta yi 6arna sosai, saita Saki Cucu, Ta ruga da gudu ta nufi gate, A lokacin baba mai gadi Yana Cikin yin alwalar sallar magrib, Ya hangota ta nufo shi,

Tunkafin ta ƙaraso Take nuna mashi gate ya buɗe mata, Sanin Tsiwarta yasa Ya buɗe mata ƙopar jikin gate ɗin ta fuce, Sai gidansu Aneerlerh lokacin da ta shiga Gidan, A bedroom ta samu aneerlerh ta kabbara Sallah, Saman Gadonsu ta haye Taja bargo ta kuɗunɗu ne, Bayan aneelerh ta kammala Yin sallar,t ana daga zaune saman darduma ta kalleta”Angel Lafiyar ki kuwa”

Kasa ƙasa da murya tace”Zazza6i nake yi”

“kin sha magani”

“Eh nasha, daddy ne yace inzo wurin ki kiyi mun wanka,i n ya dawo daga masallaci zaizo ya dauke ni”

Mikewa aneerlah tayi, bayan ta cire hijabin ta tura a wardrobe,

“Tashi muje nayi maki wankan”

Yaye bargon tayi ta sauko daga saman Gadon, rigar jikinta duk ta cukuikuye, hada manjan daya gogu agaban rigar,
“A haka kika hau mun gadona? Ina kika samu manja ajikinki”
Ashagwa6e tace” nace maki bana lafiya, Ni bana iya magana sosai”
Sam aneelerh ba ta yarda da ita ba ta ƙyale ta ne kawai,

Within minutes ta yo mata wankan, suka fito daga cikin toilet, ta shafe ma ta jikinta da mai, canza mata kaya tayi, dama Saboda Ita ta sayi kayan Yara dai dai Size dinta, saboda sun ɗauke ta tamkar ɗiyarsu, pink gown ta sanya mata,ta kuma ɗaure mata sumar kanta da ribbom,ba ƙaramin kyau tayi ba, hada light make up aneelerh tayi mata,

“Aunty aneelerh,Z an koma saman gadon in kwanta, dan Allah ki hadamun fura, A sanya kwakwa da yogurt aciki da ƙanƙara”

Jinjina kai aneerlah tayi fuskarta dauke da murmushi tace”Okey My daughter in law, je ki kwanta,”da gudu taje ta haye saman gadon,

Bayan Aneerlerh ta hado mata furar a cikin Cup ta kawo mata Nan ta zauna tasha ta ƙoshi, kafin ta koma ta kwanta tuni bacci yayi awon gaba da ita,

A 6angaren Taj kuwa, Lokacin daya tashi toilet ya shiga, ya dauro alwala ya dawo Cikin ɗakin Ya dauko Jallabiya Cikin Closet din shi Ya zura ajikinshi, Fitowa ya yi daga ɗakin yana ta faman sauri Ya fuce zuwa masallaci,

Bai tashi sanin aika aikar da Angel tayi mashi ba, Sai daya Dawo daga masallaci, wata irin yunwa ta farmasa, ba arxiƙi Ya nufi kitchen shigar shi keda Wuya Tun abakin ƙopar yaci karo da Fasassun kwanukan da angel ta 6aro, A razane ya dago yana kallon cikin kitchen ɗin, har wani haya ki yake ganin cikin idon shi saboda tsabar 6acin rai, ashe bai ga komai ba sai daya Shiga Cikin store, Hannu ya ɗaura akai yana ambaton”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un! Nashiga Uku! Na bani!

Ya Allah laifin me nayi aka jarrabceni da Angel? wani zunubi na aikata, dafe baki yayi da sauri jin sabon da ya yi yana mai fadin astagfurullah…..” yana cikin sambatun nan yaji kukan Mage, Aikuwa a harzuƙe ya juya ya kalli magen dake a bakin kopar store ɗin, Shaƙo wuyanta yayi tare da jijjigata Yace”Ke da ubanwa ku ka yi wannan”?
Ƙura mashi ido magen tayi tana Cigaba da yin kukan Yunwar da take yi, wurgi yayi da ita, tare da naɗe hannun rigar shi Ya fuce daga gidan, kaitsaye Ya shiga Gidan Uxair, tun a bakin gate mai gadin Gidan Ya soma tambayar shi”Yalla6ai Lafiya”

Baiko tanka mashi ba Idonshi Ya rufe, Angel kawai Yake nema Ko sallama bai tsaya Yi ba Ya faɗa Cikin Falon Gidan, Ganin bakowa Yasa shi fara kwala mata Kira”Angel!Angel!Angel!!’ tamkar makoshin shi zai 6allo,

Da gudun gaske Aneelerh ta fito daga bedroom ɗinta Jin muryar Taj Cikin tashin hankali,

“Me ya faru ne”?tayi tambayar tana kallon shi,
“Where is Angel”?
“Ɗazu ta shigo bata Jin dadin jikinta, yanzu haka bacci take yi adakin”bata kai ƙarshen maganar ta ba, Ya wuce ta a fusace Ya faɗa dakin, Can ya hangota saman gado a kudundune tana ta sharar bacci,”

Hannu biyu yasa ya Cakumeta, da sauri aneerlerh ta biyo bayan shi Tana tambayar shi Meya faru ne,

Da budar bakinshi sai cewa yayi”kashe ta zanyi,”

Yana faɗin hakan ya nufi hanyar fita da ita, gida Ya koma da ita a dakin su Ya jefar da ita saman gado, sai lokacin ta farka tana kallon shi da manyan idanuwanta,

“Daddy what”?

“Zaki Ci ubanki ne” ya faɗi hakan tare da Janyo pillow Ya hau saman gadon Ya turmushi fuskarta dashi, Mutsu mutsu ta shiga yi, tana kokawar fitar da numfashinta, sae faman harba ƙafafunta take Yi, tana neman Ceto,Amma Taj sam Babu alamar zai sarara Mata, Saboda Baya acikin Hayyacinshi Dagasken kasheta Zai yi,

Faɗowa ɗakin aneelerh tayi ko takalma babu a ƙafafuwanta, Anan ta same shi Saman Gadon Ya danne angel Da pillow, A gigice ta fasa ƙara, Tare da yin kukan kura Ta haye saman Gadon, Da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta cakumi wuyan jallabiyar jikin Taj tare da Yin Wurgi dashi gefe guda Ya faɗa saman mattress din,

Cikin shessheƙar kuka take fadin”Taj ban sanka da haka ba, meyasa zaka yanke hukunci Cikin fushi ne? Meye ribar ka idan ka kashe Angel?yarinyar da ba ta wuci 7years ba, idan ka yi hakuri Wata rana zata daina ne,

“Wlh bazan ƙyaleta ba Kafin ta kashe ni, Ni zan fara kashe ta,” ya ambaci hakan tare da yunƙurawa Ya miƙe Yana ƙoƙarin Cakumar Wuyan angel da ta sume, da sauri Aneelerh Ta sanya hannu ta ɗauketa, tana ƙokarin sauko wa da ita daga saman gadon, A ƙokarin Ya damƙo angel Ya janyo wuyan rigar Aneelerh gaba ɗaya aneelerh tayi baya ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi, Angel kuma ta yi gefe ɗaya saman gadon,

Karo na farko da jikinta ya fara ta6a namijin da ba muharraminta ba, shi kan shi bai yi tsammani hakan zata faru ba, saboda ba ita yayi niyar Janyo ba, Angel da ke a hannunta Yaso Ya damƙo, hatta mayafin da aneelerh ta rufe kanta dashi ya warware sumar kanta mai tarin yawa ta sauka har saman kafadarta, wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarci kowan nan su, ƙoƙarin miƙewa aneelerh ta yi sai dai ina wani magnet ne ya ruketa, Runtse idanuwanta tayi da karfi ta soma ambaton a’uzubillahi minasshaiɗanirrajim, tun da ta ambaci hakan sai ga shi ta samu ƙwarin guiwar Raba jikinta daga Na taj, aikuwa A gaggauce ta hanzarta sauka daga saman gadon, ko mayafin ta bata tsaya ɗauka ba ta watsa da gudu tabar ɗakin,

A hankali taj ya lumshe idanuwan shi, ya yin da hancin shi ke shaƙar mashi ƙamshin turaren Jikin aneelerh daya gauraye Jikinshi, bakomai Ya tuna ba face Matarshi da ta gudu tabar shi, maca ce mai matuƙar son ƙamshi, shima kuma ma’abocinsa ne, baisan Ya akai ba Ya tsinci kanshi da tariyo yarda Aneelerh ta faɗo saman ƙirjinshi, da kuma yadda yalwataccen gashin kanta Ya zubo har a jikinshi,da kuma daddaɗan ƙamshin turaren ta,

Ganin Zuciyar shi na ƙokarin Zayyana irin kyawun surarta ne yasa shi saurin Ambaton A uzu billahi minasshaiɗanirrajim, Astagfurullah Ya Allah,

Miƙe wa Ya yi zaune Duk kasala Ta rufe shi, saukowa yayi daga saman gadon ya fito palour, babu kowa Hakan ya tabbatar mashi da cewa Neelerh ta gudu, frigde ya buɗe ya dauko Swan Mai sanyi ya dawo bedroom din shi, daga gefen gadon Ya zauna, buɗe murfin yayi ya tarfa ruwan a hannunshi Ya watsa ma angel asaman fuskarta, nan take Taja dogon numshi,

Slowly ta buɗe idanuwanta akan fuskar shi, Suna hada ido ta fashe da matsanancin kuka,

Natsuwa yayi yana kallonta ko kusa baiji tausayin kukan nata ba, tun da ya lura Ba son shi take Yi ba,

Cikin shessheƙar kuka tace “You want to kill me because you don’t love me, yanzu da na mutu Allah zai kamani, so kake in shiga wuta ko? ta yi tambayar tana kallonshi, har lokacin idanuwanshi na akanta baice uffan ba,
“Kana Jina ka share ni ko”

Gyaran murya ya ɗanyi can kasan makoshin shi ya furta”Dama kina tsoran Mutuwa”!
A tsiwace tace “Eh mana,malamin mu ya karanta mana wani hadithi wanda ke magana akan mai munana ma iyayensa ba zai shiga aljanna ba, A wuta za’a babbaka shi……”

Ƙiris Ya rage taj ya ɗan murmusa”So you know that but u keep hurting me ko”?

Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan, Ganin tasha Jinin jikinta sosai yasa shi kwantowa Yayi mata rumfa da faffadan kirjinshi, cikin sanyin murya ya soma magana Yayin da idanuwan su ke kallon Cikin na Juna,

“Angel, zan sanar dake wani abun da baki sani ba ba ki da wanda yafi ni a duniyar nan, ba ki ta6a tambayata mahaifiyarki ba, Bansani ba ko kina tunanin Namiji yana iya haihuwa ne, Shiyasa kike ganin kamar ni na haife ki, Baki da abun wulaƙantawa Irin mahaifin ki,” shiru ya ɗanyi yana nazarin wani abu, ita kuwa ta kasa kunne tana sauraronshi,

Cigaba da magana yayi”Angel, mahaifiyarki a wulakance ta haife ki, Cikin bathtub tabar min ke, Cikin Jini kina ta kuka, Ni ina bacci kukan ki ne Ya tashe ni haka naje na sameki, Na ɗauke ki na rungume ki ajikina, duk da jinin da ke ajikin ki, Ni ban gudu nabar ki ba, kuma ban bari kin wulaƙanta ba, Sai da na tsaya akan ki angel da taimakon Allah har kika kai wannan lokacin, Tun da ki ke ƙuntatamun dai dai da na rana ɗaya ban ta6a Tunanin na tafi nabarki ba, kuma ban ta6a tunanin in sanya hannuna wurin ta6a lafiyar jikin ba amma angel……”kasa ƙarasa maganar Ya yi jin yadda ta rushe da kuka kamar ranta zai fita, ɗagowa Ya yi zaune yana kallonta.

Hannu ta ɗaura akai tana faɗin “Wayyo Allah na nashiga Uku,Na bani Na lalace!” hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,njin yadda babyn shi take Kuka,

Lallashinta ya soma ƙokarin”Am really sorry daughter, I don’t mean to hurt u darling, Na faɗa maki ne don ki ɗauke ni da muhimmanci, don ki san cewa Ina sonki, kuma ina buƙatar tausayawa daga gare ki,” bata tsaya sauraronshi ba, Ta sauko daga saman Gadon da gudu ta nufi toilet ta shige taja ƙopar ta rufe,

A hanzarce Ya sauko daga saman godon cike da fargabar karta kashe kanta, tura ƙopar yayi ya ji tayi Locking dinta,

Bubbuga ƙopar ya shiga yi yana ambaton sunanta”My angel am sorry, kada hakan Ya ta6a zuciyarki, kinsan ina sonki, banason zubar hawayen ki”

Daga Cikin toilet ɗin yajiyo muryarta Cikin shesshekar kuka tana faɗin”I hate my self daddy, cikin toilet aka haife ni, kuma ta gudu tabar ni saboda bata sona……”
Runtse idanuwan shi Yayi tare da ɗan Cizon lips ɗinshi Calmly ya kira sunanta”Angel pls forget about it, Tunda kina da ni don me zaki damu kanki? Ni ne mom dinki kuma daddyn ki,
Zuƙunnawa Yayi agaban ƙopar, yana ji aran shi cewa tana zaune a gaban ƙopar, tsit ya ji ta daina kukan
“Pls say something to me, ko naji sanyi acikin zuciyata”
Shiru bata tanka mashi ba,
“Ki buɗa mun ƙopar”
Sai Lokacin yajiyo muryarta can ƙasa ƙasa”daddy inaso na mutu, kodan saboda nadaina 6ata maka rai”
Cikin matsananciyar damuwa Yace”idan kika mutu angel shi ne zan shiga Damuwa wadda zatayi silar mutuwata nima, saboda kece Oxygen ɗin da nake shaƙa,”

Yakai ƙarshen maganar tare da kwantar da kanshi jikin door ɗin, don Yaji daɗin Jin muryarta

“I made a mistake daddy, I won’t hurt you anymore,”

Saboda tsabar Mamakin Jin abunda tace har saida Ya ɗan dago da kanshi, yana kwalkwale kunnanshi wai koda Ya samu matsalar hearing ne,

“I love u daddy” ya kuma Jin ta furta mashi aruɗe yace”Repeat it pls”
“I love u daddy”
“sake maimaita mun naji”fuskar shi ɗauke da murmushi Ya yi maganar,
Sake maimaitawa ta yi kamar yarda ya nuna yana son ta yi ma shi,

“I love U daddy, Bani da tamkarka a duniyar nan”
Wani irin ihu ya saki, Irin wanda Ƴan kwallo ke yi idan sunci nasara akan wasan su,

A ƙagare Yace”Come out pls, ina so naji ɗumin ki a jikina”

Yana jiyo alamun tana buɗe ƙopar kamar jira yake yi, tana ƙarasa buɗe wa Ya janyo ta Jikin shi yayi hugging ɗinta very tight, hannun shi na acikin sumarta, Wani irin farin Ciki ne Ya lullu6e shi kamar wanda a ka yi ma Albishir da gidan Aljanna,’ dole Taj ya yi farin ciki cos this is the first time da angel Ta fara furta mashi kalmar tana son shi a mtsayina mahaifinta, Ya ji tausayinta sosai, bai ta6a tunanin akwai lagwanta ba sai yau, da ta ji cewa mahaifiyar ta ta gudu ta barta, Jikinta ya yi sanyi, da yasan da haka da tuni ya faɗa mata, da duk wannan abun bai faru ba,

daukarta Yayi asaman bayanshi, yakaita Cikin motarshi, atare da ita suka je masallaci, Ya barta acikin mota, Bayan ya kammala sallar, ya dawo Ya shiga motar yayi driving ɗinsu zuwa Restaurant, komai take so shiyasa aka kawo masu, sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Suka dawo gida, A palour suka zauna saman Sofa tana rungume ajikin shi, Suna kallon tashar Mbs 3, dama best channel ɗinta ce saboda suna sanya Cartoon, tafi sha’awar kallon Cartoon da kuma zombie,

Tuni bacci ya dauketa ajikinshi, asaman kafaɗar shi ya ɗauke ta Ya nufi bedroom dinsu, don ya kwantar da ita, a hankali Ya tura kopar ɗakin Ya shige, A saman gado Ya kwantar da ita, Sai da ya fara daukar wayar shi dake ajiye agaban mirror, Tukunna Ya haye saman gadon ya janyo ta a jikinshi, Yana shafa sumar kanta, cikin magagin bacci ya ji tana fadin”I luv u daddy” murmushi ya ɗan saki, Tare da manna mata kiss a gefen fuskarta
“Luv u too My own daughter”

Number Uzair Ya kira, tana fara ringing Uzair ya ɗauka,
“Aminina Yanzu nake shirin zuwa duba jikin ka”
“Na hutasshe ka ba sai kazo ba, Jiki ya yi sauƙi Alhamdulillah”
“Naji labarin abun kunyar da kaso ka aikata na kashe ƴarka, Ae ni har na yi shirin zuwa ɗaukar rahoto”
Fashewa Taj yayi da dariya”Ta
6atamin raine, ni kaina bansan nayi wannan yunkurin ba,”
“Yanzu Ina virus ɗin taka take”?a cewar uzair, don tun ranar da ta Sa ƴan sanda su ka kama su akan ƙazafin da ta yi masu na cewa su ƴan yankar kai ne, tun daga ranar Yake kiran ta da Virus,
Murmushi Taj yayi, tare da kai hannu ya shafa sumar kan angel, Virus ta yi bacci, Mutumina ka ta ya ni farin Ciki,”
Uzair yace”Meya faru”?
Nan Taj ya kwashe duk abunda Ya faru tsakanin shi da angel ya sanar mashi,”
Yana jiyo sautin dariyar farin cikin da uzair Yake yi,
“Ja’irar taji ƙamshin mutuwa, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ce tazo, Amma fa nayi farin Ciki,

“Ameen mutumina”
Shiru suka ɗanyi,yana so ya tambaye shi aneelerh amma ya kasa,
“Muyi video call mana”acewar uzair,
Batare da musu ba suka canza Kiran zuwa Video call, A kwance uzair yake saman katafaren gadonsu, ya dan tada kan shi saman pillow, jikin shi na sanye da kayan Bacci,
“Show me her face” murmushi taj ya yi tare da haska mashi fuskar angel, ta sa ki baki da hanci tana ta sharar bacci,
Dariya uzair yayi”waya ga mashasha, wannan ae itace Laca sera jibi yadda ta saki la66a, a haka zata zama surukar mu,”
Fuskar Uzair ɗauke da murmu shi yace”cin mutuncin ya isa haka aminina, kai ka sani Wlh angel koda kuɗin mutun saida rabon shi, koda rabon shi sai in Allah ya nufa”
Jinjina kai Uzair Yayi tare da ɗan yatsina fuska yace”Virus ɗin”?

Taj na ƙoƙarin buɗe baki ya mayar mashi da martani, adai dai Lokacin Aneelerh ta fito daga Cikin toilet, Chest ɗinta ɗaure da farin towel iya guiwarta ya tsaya, Ta cikin Screen ɗin wayar uzair, Taj Ya hangota yanayin kwanciyar da uzair yayi ya juya ma Toilet ɗin ɗakin shi baya, wanda hakan yasa har Taj ya iya hango fitowarta,

Baisan ya a kai ba Ya tsinci kanshi da satar kallonta, Ya bar uzair sai faman zuba yake yi kamar kanyar da bata da daɗi, gaban mirror ta tsaya tana tsane sumar kanta da towel,

“Me kake tunani ne”? a firgice taj Ya mayar da hankalinshi kan Uzair, muryar shi na inda inda yace”Bakomai zan kwanta mutumina, Sae Allah yakaimu,” da sauri ya yi rejecting kiran tunkafin ma uzair ya yi mashi sallama,

Lumshe idanuwan shi ya yi zuciyar shi a cunkushe, duk yadda yaso Ya hana kan shi tunanin abunda ya faru tsakanin shi da aneelerh abun ya faskara, daƙyar ya samu bacci yayi awon gaba da shi,

Tun daga wannan Ranar Angel bata ƙara 6ata mashi rai ba, koda yaushe suna manne da juna wata irin shaƙuwace a tsakanin su, mutu ka raba takalmin kaza, tabbas Angel taba kowa mamaki, irin yadda take son mahaifinta, tarairayarshi take yi, biyayya take yi mashi sau da ƙafa, Xaman Lafiya ya wanzu a tsakanin su

_*daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️*_

_Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne Kacal, Ban tsawwala ba,mutane Dayawa Suna tambayata Shin wannan book din zai kai father of soldiers daɗi? Lokacin dana fara abban sojoji bansan zaiyi daɗi ba, Allah ne ya nufi hakan,To ba lallai bane Kurkukun kaddara yakai shi dadi ba, zai iyayiyuwa kurkukun ƙaddara yafi Abban sojoji daɗi ko akasin hakan, Allah shi ne mafi sanin dai dai👏Bani da tabbacin akan haka, Saboda Salon Labarin Ba iri ɗaya bane, sunsha banban sosai shima wannan wani salon ne na musamman, murɗaɗdiyar cakwakiya ce acikinsa, Sannan banyi maku alƙawarin cewa wannan Littafin Short story bane Zai iya Kasancewa Yana da yawa labarin! na yi maganar nan ne saboda masu ƙorafi akan Story ya yi tsayi, Shiyasa na faɗa masu tun yanzu Su sani 🤣Tun da ku kaji Ance kurkukun ƙaddara, Kunsan inda ma’anar ta dosa ko ban fayyace maku ba,Kowa yasan ma’anar kurkuku da kuma ƙaddara Dan haka kada mutun yazo yana yi mun complain akan waɗannan abubuwan dana lissafa👏then banyi alƙawarin kullun zanyi posting ba, 4 days ne a week, litinin, talata, laraba, Alhamis, after na kammala free pages, wadanda su ka yi payment zan Canza musu salon Posting🤗_
_Abu ɗaya ne zan Yi maku alƙawari🥳 da yardar Allah ba zaku ta6a danasanin siyan Littafina ba in sha Allah🤗🤣tsakani na daku fatan alkhairi ne Allah yabar zumunci daga nan har gidan aljanna😍_

_Ga waɗanda Suka shirya Yin payment Ga details nan👇_

*3196407426*

*First bank*

*Bature hafsat Muhammad,idan mutun baida acct no pls Ya tura ta Pos,saboda bana amfani da Kati,Ƴan uwa ƴan niger,Suyi mun magana ta numberta,wadanda su kayi payment zasu bada shaidar biya ta screenshot kafin a sanya su paid group*

*08103884440*

*08169856268*

Leave a Reply

Back to top button